AMAREN BANA CHAPTER 6

AMAREN BANA CHAPTER 6

Cikin bacin rai Rumaysah ta cire Seatbelt dinta ta sauka, kuma tsakaninsa da Allah bar mata jakarta ya yi, ta dauko. Makulli kawai ya karba a (Reception) kasancewar ya riga ya sa wani abokinsa yayi masa booking komai. Bayansa kawai take bi har suka isa dakin. Ta ajiye jakarta a dakin. Ganin ya sake fita, ya sa ta shiga wanka. Ba ta ji shigowarsa ba, har sai da ta fito ta gan shi a dakin ya kunna T.V. Amma magana yake yi a waya. Jakarta ta bude ta fidda kayan barci, sannan ta yi shafarta, ko kadan ba ta gwada masa ta damu da shi ba. Har ta gama shirinta. Fawzaan kuwa waya yake yi, amma rabin hankalinsa na kan Rumaysah. Sai can ya gama wayarsa, ko ba ta tambaya ba, ta san da Meena suke magana. Ta kai wuya wajen jin haushi, haka kawai me ya dauki kansa ne da sam bai damu da abin da mutum yake ciki ba? “Wai wannan wane irin mai ne mai warin magani haka? Don Allah ki daina bude shi a nan, yana samin tashin zuciya.” “Ko ni ce na ke sa tashin zuciya, sai dai zuciyar ta tashi, har ka amayar da ita, amma ba ka isa ka sani canza kaya na ba.”4 Mikewa kawai ta ga ya yi, ya ajiye wayarsa, ba shiri ta ga ya cire T-shirt dinsa, ko kunyarta bai ji ba, ganin haka ya sa ta yi saurin juya bayanta, ta runtse idanu.4 Ta sa hannu ta rufe fuskarta. Tsoronta Allah, tsoronta kar ya kuskura ya-ce zai mata wani abu, domin kuwa idan ya kuskura ya-ce zai taba ta, za a kwashi ‘yan kallo, don ba za ta bar shi ba. Yana ganin yadda ta wani juya baya, tana wani mutsuke ido, ya bata rai, aikin banza bayan ya san duk abin da ta yi da, me kuma za tai masa wani Pretending. Yarinya karama ta iya munafurci. Zuwa ya yi daf! Ita, ita kuwa ta gama kankame jikinta, tana matsawa gefe, har sai da ya rankwafo kusa da jikinta a hankali, ta bude ido daya, sai da ta ga ya sa hannu a kan kujera ya dauki tawul dinsa dake ajiye kan jaka. Nan ne ta saki ajiyar zuciya, sannan ta juyo. Ai kuwa bai bar bayanta ba ashe, nan ta angaje shi ta yi kansa. Fawzaan kuwa da wuri ya taro ta.6 Yana kallon cikin idanunta, sai da ya ga tamkar ta kusa barin duniya cikin tunani, sannan ya saketa ta fadi dabas! Akan kujerar dakin, sai da jakarsa ta zungure ta. “Wash!” Ta fada tana goga cinyarta, ko bi ta kanta bai yi ba, ya shige wankansa abin sa. Ya fito daga wankan ne, ya samu ta jera filo a kasa, ta yi shimfida. “Yau kuma a kasa za ki kwana? Da ya fi miki kam”. “A kasa zan kwana, ko a kasa za ka kwana? Ban isa ba ka je ka cire min ido a barci.” Zaro idanu yayi yana dubanta cikin rashin yarda. “Ni ban ce za ki cire min ido ba, sai ke?” “Koma dai menene, ga shimfidirka, saboda haka mu kwana lafiya.” Ta kwanta abin ta, ya bubbuga filon, kasan yai masa yadda yake so, sannan ya kwanta bai ce mata komai ba. Da dare ta tashi fitsari, ta gan shi a kwance a kasa, sai ta ji tausayinsa ya kamata, ta koma ta kwanta a gadon, tana leken sa, fuskarta a saman nasa. Idan yana barci, ba za ka taba cewa dan rikici bane, amma yana bude ido, to ya san hanyoyin bata mata rai. Lumsassun gashin idanunsa take kallo, ta dawo kan hancinsa da kuma labbansa da kuma siririn gashin bakin saman su, kallon tas! Tayi masa, ta kuma san cewa mijinta kyakkyawa ne na gaske, sai dai daga ita har shi ba su son juna. Musamman ma shi da ya fi kowa tsanarta, baran ma da ta tuno abubuwan da yake fada mata.4 Suna ta tara, matar kaddara, da kuma cin kaniyarta da ya dage sai ya yi. Mugu! Ta fada a ranta. Hucin numfashinta ya ji a fuskarsa, wannan ne ya sa ya bude idanu, ai kuwa caraf! Ya kamata tana kallonsa kasancewar ta kunna (Dim Light) din dakin, da ta tashi shiga bandaki. STORY CONTINUES BELOW Suna hada idanu, ta yi saurin komawa kan gadon ta kwanta sosai, hade da jan mayafinta ta rufe fuskarta gaba daya, a hankali ya sa hannu ya janye bargon daga fuskarta. “Idan kallona ki ke son yi, ki ce na dawo sama ki kalleni mana da kyau, za ki rika satan hanya, cikin dare ki na leke na.” Bude idanunta ta yi a hankali ta-ce. “Allah ya sawwaka na kalleka, har ma meye abin kallon a nan? Sauro na tsaya gani, yana zuke maka jini, buri na daya, ya harba maka zazzabin sauro.”10 Murmushi ya yi, ya mike ya shiga bandaki, ya fito da alwala. “Kin yi sallah ne ko kuwa kallo na kawai ki ka tsaya yi?” “Asuba ta yi ne? Yanzu fa karfe…” Ta ga har biyar ta yi ashe. “Wayyo yaushe na kwanta? “Sai ki tashi ki yi alwala ai, sarkin barci.” Haka ta ture bargon, ta je ta yi alwala ta fito, ta samu yana sallah, amma ta idar ta bar shi bai gama ba, har ta kwanta. Fawzaan na idar da sallah ya-ce. “Ke, zo nan.” Cikin tsattsaurar murya yake maganar. Bakinta ta tura ta-ce. “Ni fa barci na ke ji, meye za ka wani ce na zo?.” “Wace irin sallah ki ke yi ne? Ki na karatu kuwa a cikin sallah haka ki ke gamawa da wuri? Kin san dai sallah ba abar wasa bace ko?” Zama ta yi dabas! A kan gadon ta-ce masa. “Fatiha da Qulhuwa mana.”2 Kallonta ya tsaya yi kasake. “Fatiha da Qulhuwa kawai ki ke karantawa a duka sallolinki a cikin ko wane raka’a?” Kai ta gyada masa. Fawzaan ya shafo fuskarsa, cikin damuwa. “Duba, na san ba laifi bane karanta ko wace Surah ko bangaren Sura a cikin sallah, amma ki na karantawa ne, don ki na son Surar ko kuma don ita ne kawai ki ka iya?”‘ Kunya ta kama Rumaysah, yaya za ta dubi Yaya Fawzaan ta-ce masa surori shida kawai ta iya karantawa da ka?4 “Na iya wasu, amma dai na fi iya wadannan da kyau.” “Ki na so ki ce min ba kya karatun Alqur’ani, haka kawai sai a cikin sallah?” Kai ta gyada masa. “Wataran ina yi mana.” Ya ji mamaki kwarai da ya ga Abba ya ba ta Al-qur’ani ranar auren su. “Ba ki taba zuwa Islamiyya bane?” Lokacin ne dariya ya kubce mata, saboda ta tuno sanadin daina Islamiyyarsu tun suna yara. Kullum Abba Malami yake sama masu ya zo har gida. A duniya kuma ba abinda Rumaysah ta tsana irin zuwan Malam Salmanu, gwamma su Yaya Khans sun yi nisa. Ita kam ga ta da kwakwalwar. Amma a lokacin ba nacin, sai dan kara surutu da fada. Don haka kullum sai ta ki fita da wuri, wataran ta zuga Radiyya su ki zuwa makarantar. Kullum Malam sai ya bugesu, amma wannan ba ya hana su sake fashin zuwa washegari ko kuwa yin latti. Ranar suna zaune ana hirar, ta-ce masu. “Ai yau idan Malam ya-ce zai bugeni, zai sha mamaki kuwa.” Duk suka dubeta. “Ki rufawa kanki asiri, ke ma kin san Malam Salmanu.” Ai kuwa ta share su, ana karatu tana ciye-ciyen cakulet dinta, tana surutu. Malam ko ya ganta ya nufota da bulala. Yana kawo bulala, tana cafkewa, ai sai ga ta da cin kwalar Malam. A take anan Malam ya-ce, sai ya ga ubanta yau. Abba na dawowa Malam ya ba shi labari, ya-ce kuma ya bar koyarwa a gidan. Ranar har duka sai da ta sha a hannun Abba ya-ce kuma. “Daga yau na daina daukar maku Malami, ku je Momi ta koya maku karatun.” Wai Momi kuma, ina ta ga lokaci? Daga nan magana ta salwance. Fawzan ya dubeta ya-ce. “Ba ki da hankali ne? Yaya ina miki magana, ki na min dariya?” Yadda ta ga ya hada rai ne, ya sa ta ji tsoro, nan da nan ta-ce. “Ba da kai na ke ba fa.” STORY CONTINUES BELOW “Na ji, daga yau ina so ki sani, karatunki ya dawo kaina, tun daga koyan alwala, sallah da karatun Al’qur’ani, don na ga dungure kawai ki ka iya, kin ma san kabli da ba’adi kuwa?” Haushi ya kamata, ta ga alama ma har da tsokana abin nasa, sai dai kuma ta ji dadin haka, don ita ma ta dade tana son ta koya, sai dai ba ta da lokaci. “To, na ji.” “Da safe zan kara miki, da dare ke kuma ki fada min abinda ki ka koya. Idan kuma ki ka yi fashin kawowa, ki samu hukunci tsattsaura, shirme kawai kin iya tsiwa da surutun tsiya, amma ba abinda ki ka iya, sai danne-dannen waya. Kin dai gane me na fada miki ko?” Kai ta daga masa, ya-ce. “Yawwa, to sauko mu fara.” Tana kokarin rufuwa da bargo yayi maganar, don haka ta bar abun da ta-ke yi “Tabdi! Yanzu? Ni fa gaskiya barci na ke ji.” “Har za ki iya barci, bayan ba ki da guzurin abinda zai ceceki a lahira?” Jin hakan ya sa ta daure, ta maida barcinta ta sauko, hijabinta ta mayar jikinta, sannan ta zauna a gefensa suka fara karatu. Ayoyi biyu ya fara karanta mata a Nasi. Rumaysah dai ta dade ba ta ji karatu mai dadi haka ba. Ji ta yi kamar wani Limamin Makkah ke rero karantun. Da ta amsa ne, ya ji da gaske ta iya, shi ne ya-ce ta karanta iya wanda ta iya, sai su bar karin sai gobe. Tana zuwa Qulyaa ta yi dif! Qulyaan (Suratul Kaafirun) ma sai da ya-ci gyaranta. Fawzaan ya yi shiru, sai ya ji tausayinta ma yake ji, ace mutum ya girma har ya kai matsayin kusan gama jami’a, ya yi aure, amma bai iya karatu ba, bare ya san hukuncin sallah? Subhanallah, ko ina iyaye suke kallo, irin haka ke faruwa?6 Sai Allah, idan ba za ka bawa danka lokaci ba, abinda za kai masa shi ne ka tabbatar ka yi wani abin da zai samu ilimin a wani wuri, bare Abba, ba kudin kai su makarantar ya rasa ba, ya rasa yaya aka yi shi ma yana gani, ya yi wannan sakacin haka.5 Suna gamawa, anan ta yi barci jikin gadon, ba tare da ta matsa ba, shi kuwa Fawzaan ya zo tashi, ya ga ta zauna masa kan jallabiyya, tsaki ya ja, kamar ya tunkude ta yake ji, amma ya ga barcin nata ya yi nisa. Haka ya hakura ya zauna yana wuridi, har sai da ta gama barcinta ta tashi. Farkawa ta yi ta ganta a jikin kafadarsa. Da sauri ta mike tamkar wuta ya konata. “Wakey-Wakey, haka dama ki ke da nauyi kamar wata Saniya?” Ya fada yana murza kafadarsa. “Duk, kinsa jiki na ciwo.”4 “Ina da nauyin ai ka iya kinkimata zuwa saman matakala.” Dariya ya yi da ya tuno ranar, saboda ya ji dadin yadda ya lasa mata zuma, ya kuma kwace, ya lasa mata madaci.6 Sun gama shirinsu zuwa karfe tara, don haka suka yi (Checking Out) suka nufi gari, domin Sajeeda ta yi ta jaddada masu tai masu abin karyawa kar su ci komai. Murna kamar yai mata me. Don tun bikinsu, Baffa ne kawai ya taba zuwa shi da Abba, amma banda su, ba wanda ya zo, yanzu watanni uku kenan. Rumaysah ta dubi Sajeeda, bayan sun gama karyawa tun zuwansu, abin yake damunta can dai ta-ce. “Yaya Sajeeda ciwo ki ke yi ne, na ga kin rame, kin yi fari sosai?” Sajeeda ta yi murmushi ta-ce. “Hmm! Na yi shiru, ke ma ki na hanya ai.” Rumaysah ta zare idanu ta-ce. “Yaya Sajeeda fatan da za ki min kenan na yi ta ciwo har na rame, na dauka ke kam ki na so-na, ba kamar Yaya Fawzaan ba.” Sajeeda ta yi dariya ta-ce. “Yaya Fawzaan din baya son ki ne, aka ce miki?” “Tab! Ba ki san shi ba kenan. Amma yanzu kam ke ma kin mara masa baya.” “To banda abinki, ai wannan rashin lafiyar na karuwa ne, shi ya sa nai miki fatansa.” Sai lokacin Rumaysah ta gane ta-ce. “Oh, haihuwa za ki yi, shi ya sa ki ke ciwo? Dama haka ake yi? Amma kawata Firdausi ban ga tana ciwo ba, ita kyau na ga ta yi”. STORY CONTINUES BELOW “Kowa da yadda yake zuwa masa, wani ya zo da sauki, sai dai gaskiya ni kam ina cin kaniyata.” “Ayya! Allah ya ba ki lafiya.” “Ameen, saura ke, hala ki samu mai sauki.” “Hmmm! Ni kam ba zan haihu ba ai.” Mamaki ya kama Sajeeda ta-ce. “Me ya sa za ki ce haka?” “Ba sai mutum yana son matarsa bane suke haihuwa? Ni kuma Yaya Fawzaan ya-ce baya so-na.”4 “Ke ki na son sa kenan?” “Ni kuma na so shi? Allah ya sawwaka, mugu ba ki san me yake ce min bane, shi ya sa za ki ce na so shi.” Sajeeda ta yi dariya, ta san shirmen Rumaysah. Don haka ta-ce. “Ki daina fadawa Mutune baya sonki, wannan tsakanin ku ne, tunda bai nuna hakan wa mutane ba, yana zaune da ke lafiya, ai shi ne babba, ke ma kuma ki rinka son sa, tunda kin ga mijinki ne, ki na da wanda ya fi shi ne?” “Tab! Abba na ya fi min shi sau dubu miliyan.” “Ai Abba daban, kuma shi ma a da ne ya fi shi, amma yanzu a musulunci mijinki ya fi kowa cancantan samun girma da kima a wurinki, kuma ya zamo dole ki rinka kyautata masa ki rinka jan hankalinsa zuwa gareki, za ki ga shi ma ya damu dake, yana nuna miki kulawa.”1 “Yaya Sajeeda ba ki san ba wanda Yaya Fawzaan zai taba so ba, sai Meena, saboda baya ko jin nauyin, ina wuri, waya yake yi da ita abin sa.” “Yaya Fawzaan din? Kodai da gangan yake yi, don ki ji haushi?” “Da gaske waya suke yi, ai ya fadawa abokinsa ma, wai ni a matan ma suna na tara.” Tabbas Sajeeda ta ji mamaki, domin ta san Yayanta da daraja mutane da kuma ba su matsayi na mutumtaka, hakan kuma da yake yi cin fuska ne, koda i Rumaysah ba ta gane bane? Koda yake ba za ka yi shaidan mutum ba a zamanin nan, watakila son Meena ke rufe masa idanuwa, yake aikata komai. “Ki kwantar da hankalinki, a hankali zai dawo da hankalinsa kanki. Kin ji ko? Ki yi ta addu’a, kuma a cikin sujjadarki. Allah ya hada kanki da mijinki.” Suna cikin magana ne. Mijin Sajeeda. Ahmad ya shigo falon Sajeedan ya-ce. “Idan kun gama yana falo, ya-ce ki zo ku gaisa, suna kan hanya.” “To.” Nan suka wuce falon, wurin Fawzan, ba su kara minti ashirin ba, suka masu sallama, suka dauki hanyar Abuja. Tun daga gidan Yaya Sajeeda Rumaysah ke satar kallon Fawzaan, yanzu wai matsayinsa ya fi na kowa a rayuwarta? Yanzu wannan mugun ne za ta tausayawa, ta so, ta kuma yiwa biyayya? Daidai Lokacin ne kuma dai ta tuno wasu lokutan da baida muguntar, yadda ya nuna damuwarsa dazu, duk da ya ba ta haushi da farko, da ya fahimci tana bukatar karatu. Da kuma yadda ya rinka mata fada da ya ganta da MS, da kuma yadda ya nuna kulawarsa gareta da Momi ta ji mata ciwo. Watakila ita ce ba ta ba shi dama, don ya nuna mata asalinsa ba, daya zuciyar kuma ta-ce mata, wane asalinsa ne bai nuna miki ba ran aurenku, kin manta me ya-ce miki ne? “Welcome to hell.” Tunda suka koma, mu’amala daya ke hada Rumaysah da Fawzaan, wato karatun da yake koya mata, kullum ayoyi biyar yake kara mata a karatu, sannan ya ba ta littafai ta karanta na ibada da hukunci, da su Siffatus-Salatun Nabiyyu. Ya hado mata har da na Video wanda Sheikh Albaniy ya yi. Aikinta kenan tun da ta gama (Regsitration), ta sa karatunta a gaba, har mamaki yake yi, yadda take da saurin dauka. Idan banda wannan, kullum duka suna sabgarsu, ita ta tafi makaranta, shi kuwa ya tafi ofis. Sai lokacin ta san cewa duk tabokara take ta yi a lamarinta na ibada, domin kuwa gyara sosai take cin karo da su, duk sanda ta yi karatu, tabbas neman sani yana da dadi. Damuwar Rumaysah daya, kullum ta yi sallah sai ta yi addu’a Allah ya karkato da hankalin Momi kanta, ya kuma ba ta hakuri. STORY CONTINUES BELOW Don sai dai su je gidan Baffa ta shiga ciki, amma gidan Abba iyakarta falon Abban. Su yi hirarsu, su koma. Bayan ta taso daga makaranta ne, ta bi gidan, nan ne ta samu labari an sa ranar auren Radiyya da Deeni. (Nuruddeen), bayan babban sallah da sati biyu. “Wai, Sis gaskiya na yi murna, yaya kin gama shirye-shirye, an sayi komai? A ina za ku zauna? Wayyo kamar na matso da ranar na ke ji.” “Hey! Rumaysah ki natsu, ni amaryar ma ban yi murnar da ki ke yi ba.” “Me ya sa ba kya murna, ke da ki ka samu za ki auri wanda ki ke so?” Radiyya ta rike hannayen Rumaysah ta-ce. “Ke ma, Yaya Fawzaan zai so ki, ya kula da ke, har ma ki fi kowa a idanunsa.” Murmushi ta yi. Ta rufe fuskarta. Radiyya ta sa ihu ta-ce. “Kin ga ta kanki, ki na son Yaya Fawzaan! Ho! Allah na gode maka da ka nuna min wanan ranar.” “Ni wa ya-ce miki son shi na ke yi? Allah ya sawwaka na so shi, ba ki zauna da shi bane, da za ki gane kirkinsa kadan ne.” Radiyya dai shiru kawai ta yi tana jin ta, amma tana tantamar hakan. ************** Fawzaan kuwa har yau ya kasa gane asalin alaqarsa da Rumaysah, domin dai a bangare guda ba zai iya bata matsayin matarsa ba, don zai cutar da ita da shi kansa, shi ba sonta yake yi ba, ya dauka duk wani kunci zai iya dorawa Rumaysah. Don ya huce, amma ya fahimci hakan duk ba zai sa ya samu yadda yake so ba, sannan kuma ba zai iya ya-ce zai sallameta ta tafi ba, bai san iya lokacin da zai dauka yana hakan ba. Maganarsa da Meena ya tuno jiya da yamma. “Meena, ban san me ya sa ki ke ta juya ni ba, har yanzu kin ki fada min abin da ake ciki. Baffa ya-ce min har yanzu Baba bai ce masa komai ba, shin dai ko kin tureni gefe ne haka? Ni na zaci iyanzu har mun tsufa da aure. Don ban zaci kaiwa warhaka ba.” “Ko kadan Barrister, ni ba haka bane. Wallahi matsalar dai Hajiya ce, tun ba yau ba da ta samu labarin auren ka, ta-ce sai dai na hakura da kai, na samu wani mijin, shi ya sa na ke cikin damuwa, yanzun ma ko zuwan da ka ke yi, ba ta zaci kai bane, saboda na daina fada mata ka na zuwa. Sai dai na fadawa Baba ya-ce zai mata magana.” Fawzaan ya ji wata gajiya ta sauko masa, shi ya dade da sanin an samu matsala, idan banda haka, yadda yake son Meena ta kasance matarsa, ya san ita ma hakan ne a wajen ta. “Ba komai. Insha-Allahu za ta amince. Kar ki damu, kin ji?” Duk da ya fada mata hakan, sai ya zamana shi ne ya shiga damuwar, sai da ya ji wani saran kai tukun. Ransa a cunkushe ya koma gida, ko abinci bai nema ba. Ya samu Rumaysah a falo tana Note, bai ce mata komai ba, ya wuce daki. Kallo ta bi-shi da shi, sannan ta ci-gaba da Note dinta. Da safe ta shirya za ta tafi makaranta, har ta gama karyawa, ba ta san Fawzaan bai fito ba, don haka ta yi fitarta, sai da ta fito ta ga motarsa a waje, ta san cewa ba fita ya yi ba. Da kamar ta wuce makaratarta, tunda jiya shi ma da ya dawo, bai ko kula ta ba. Amma ta ji dai gwamma ta koma ko gaisuwa ne su yi. Halin da ta gan shi a ciki ne, ya sa a firgice ta isa gare shi da gudu, da kyar ta juya shi daga ruf da cikin da ya yi. Yana ta nishi, duk jikinsa ya yi zafi, sannan sai rawar sanyi yake yi. Bakinta ta rufe da hannu bibbiyu ta shiga rudu, kawai sai ta samu kanta da kuka. “Yaya Fawzaan, me ya sameka? Bude idonka don Allah.” Sama-sama yake jin ta, ga wani irin ciwon kai da yake ji. Da sauri ta ajiye mayafinta, ta shiga (Toilet) ta jiko Towel ta zo ta zauna a gefensa, tana sa masa a saman kai da wuyan sa, ko zazzabin zai sauka. Ya motsa idanunsa, suka budu da kyar. Da hannu ya nuna mata Drawer dinsa. STORY CONTINUES BELOW Cikin hanzari ta isa ta bude, ta ga magunguna, haka ta kwaso su gaba daya ta zauna tana karanta sunayensu, a ciki ta ga Opthalidon da sauri ta balla, ta sauka ta kawo masa ruwa daga falonta, sannan ta dawo, da kyar ta taimaka masa ya zauna ya sha maganin. Ai yana sha, ya fara hararwa, kasancewar cikinsa ba komai, nan ne ya sake galabaita. Cikin lokaci kadan ta kimtsa wurin ta-ce. “Yaya Fawzaan, ka kokarta ka canza kaya, sai mu tafi asibiti.”3 “Ki bari kawai…” “Yaya za ka ce na bari, bari na kawo maka Tea kafin nan ka sa kayanka.” Za ta tafi ya riko hannunta a hankali, ta juyo ta dubi hannayensu, sannan ta dube shi kafin ta durkusa a gaban gadon. “Fito min da kayan to.” Kwarai ta tausaya masa, ta kuma tsorata, don ba ta taba ganin babba a yanayin da yake yanzu ba. Nan da nan ta aikata hakan, sannan ta sauka ta hado masa Tea mai kauri, ta kawo masa. Tana shigowa cikin dakin ne, ta samu yana tsaye yana fama da Shirt din sa, za ta juya, ta ga ya tafi kamar zai fadi, da sauri ta ajiye Tray din Tea din a kan Table din dakin, ta nufi inda yake ta tare shi. Ya daidaita tsayuwarsa. Kanta na kallon kasa ta-ce. “Ba ka da karfi, da ka sa rigar a zaune ai. Kuma don Allah tun jiya ba ka da lafiya, ba za ka tasheni ba, za ka kwana cikin rashin lafiya? Saura kadan fa na tafi makaranta, ban san halin da ka ke ciki ba. Da wani abin ya sameka kuma, sai na yi yaya?” Tana ta fada, idanunta sun yi narai-Narai! Ture hannunsa ta yi daga kokarin da yake ta yi, don saka maballan rigar. Sannan ta karasa sa masa su, sai da ta gama ne, ta kula da abin da ta yi. Da sauri ta mike ta-ce. “Ka yi hakuri.” Nan ta fita ta bar masa Tea din, sai bayan minti biyar ta dawo, ta-ce. “Mu tafi asibitin, za ka iya tashi?” Kai ya daga mata, amma yana mikewa, ya sake yin luu! Bango ya dafa wannan karon, haka ya yi ta bin jikin bango har suka sauka. Ta bude masa motarta, ya shiga. Gudu kawai take yi, har suka isa asibitin Abba. Wani irin zazzabi ne ya dira masa cikin dare, kuma ya san har da damuwar da maganar Meena ta haddasa masa, dama kuma yana da Migraine duka suka hadu suka rafke shi.4 Suna zuwa Abba da kansa ya gan shi, sannan ya-ce za suyi masa karin ruwa, saboda ya samu karfin jikinsa. Sannan su daura shi kan magungunan sa, kan su koma gida. Rumaysah dai sai waya ta yi makaranta ta cewa Naja’ah ba za ta shigo ba. Fawzaan na asibiti. Can sai ga su Mama sun iso asibitin, suna mamaki, don Fawzaan ya kan dade bai yi ciwo ba, ko ya yi ma a tsattsaye yake yi, ba dai ya kwanta ba, idan kuwa ciwo ya kwantar da shi, to sai dai Migraine dinsa (Ciwon barin kai). Haka Rumaysah ta kasa zaune bare tsaye. Su Munirah da su Radiyya duk sun zo duba shi. Zuwa yamma dai ya fara samun karfin jikinsa, hakan ya sa Abba ya-ce ko zuwa safiya zai iya komawa gida. Yana jin hakan ya-ce. “Abba, da gaske na warke ko yanzu ma na tafi ba matsala.” Mama ta-ce. “Anya, da safen nan fa juyuwa Rumaysa’u ta-ce ka ke yi, yanzu ka koma gida, ai ya yi sauri. Ka dai bari ciwon kan ya sauka tukuna”. Baffa ya-ce. “Ku rabu da shi, tunda ya-ce ya warke.” Don haka a daren aka sallame shi, suka koma gida, suna zuwa Rumaysah ta dora (Pepper Soup). Sannan ta haura dakinsa ta canza zanin gadon, ta feshe dakin da turaren daki na (‘Aroos). A kishingide ta zo ta same shi. “Ba ga irinta ba, su Mama duk sun ce ka zauna a asibitin, amma kai ka ki, ga ka sarkin jarumta.” Murmushi ya yi na karfin hali ya-ce. “Har yaushe mutum zai ta kwanciya a asibiti? Bayan kawai zazzabi ne, kuma ya sauka. Ciwon kan a hankali zai sakeni zuwa gobe Insha-Allahu.” “Ai da lafiya ake komai, an fada maka wadanda suke asibitin, don kansu ne suke zuwa su kwanta din? Za ka sha (Pepper Soup) din yanzu ko sai anjima?” “Sa min dan kadan, don har yanzu Taste din baki na yana min wani iri.” Wucewa kicin din ta yi, ta karasa hadin girkin, sannan ta zubo masa yadda ya-ce din. Tana kallo ya dan taba kadan, a zaton ta ko jikin ne ya sa bai sha sosai ba. Sai kuma ta yi tunani ta-ce. “Kodai bai maka dadi bane?” “A’a, dole na fada miki. I’m pleasantly surprised.” ya fada cikin murmushi “Mamakin me? Saboda na iya farfesu, ko kuwa saboda na kula da kai?” “Za ki iya cewa duka. Ni zan je na kwanta.” Bin sa ta yi da kallo ta-ce. “Ka jirani na zo.” Ta bi ta tattara komai ta kashe komai, sannan ta rufe kofa, ta bi bayansa. “Idan ka ji jiri, ka ba ni Notice tun kan ka rikito min kaina, mu dungura mu karairaye.”9 Ta ba shi dariya, amma baya jin yi. Ruwa ta sa masa ya yi wanka, sannan ya sa kayan barci, har ya kwanta, ya ga ta zo ta ja bargon ita ma za ta kwanta. Ya dubeta ta-ce. “Meye? So ka ke yi na fita da safe, na zo na samu ka mutu min, na rasa yadda zan yi? Gyara ta can na kwanta.”4 Fitinar Rumaysah sai ita. Haka ta sa filon ta yadda ta yi a ranar aurensu. Ya-ce “Ban yarda ba, dawo da kanki nan, idan ki ka buge min kaina da kafafunkin nan, za ki karasani.” Dariya ta yi, ta maida filon gefen kansa, sannan suka kwanta, sai dai dukansu ba wanda barci ya dauka da wuri. Rumaysah tunaninta shi ne, yadda ta tsorata ganin halin da Fawzaan ya shiga da safe, sai ta rantse zuciyarta ta kusa bugawa. Don tsabar tsorata, ta mayar, idan ta taba shi za ta ji bai da rai. Sannan a bangare guda, ta ji mamakin kanta kwarai, don tun aurensu ba ta taba nuna kulawarta gare shi ba irin na yau. Me ya sa ta damu da Fawzaan haka? Koda yake akwai tausayi, duk wanda ya gan shi a halin da ta gan shi. Tabbas zai tausaya masa.4 Shi kuwa Fawzaan tunanin sa, ya rabu kashi biyu ne a bangare guda, ya ji mamakin kokarin yarinyar, duk da dai yana matsayin mijinta, shi ya san zaman da suke yi da ita, kuma har ta iya yarda da shi za ta kwana a gadonsa, don ta kula da shi. A daya bangaren kuma yana tunanin muddin ya rasa Meena, yaya zai yi da rayuwarsa? Dole ya je koda kansa ne ya roki Hajiyarta, ko kuwa ya dora Rayyan bisa wannan aikin. Can ta ji alamar numfashinsa kamar barci ya dauke shi, don haka ta gyara masa rufuwarsa, sannan ta koma ta kwanta. Cikin barci ta ji hannu a jikinta, a hankali ta bude idanu za ta juya, ta ji ko wani abin Fawzaan yake so. Ga mamakinta sai ta kasa juyawa, saboda rikon da yai mata, gaba daya ya kwakumeta ta baya, hankalinta ya tashi, matuka. Amma ta rasa yadda za ta yi, kamar daga sama ta ji yana magana. Da farko ba ta ji me ya-ce ba. “To ko zafin zazzabi ne ya sa shi magana cikin barcinsa?” Kafin ta ida tunaninta, ta ji yana cewa. “Ki yi hakuri don Allah kar ki bar ni.” Mamaki ya kamata. Me Yaya Fawzaan yake nufi? Me zai sa ya fada mata hakan? A hankali ta daga hannunsa, don ta juya, kawai sai ta ga barci yake yi. Za ta matsa ne, ta sauka daga gadon, ta ji ya-ce. “Meena KE NA KE SO.”16 Kalaman Fawzaan sun bata matukar mamaki, sun dimauta ta, ta shiga wani irin tashin hankali, tamkar wanda ya watsa mata ruwan zafi, haka ta ji tasirinsu. Yanzu daman ciwon son budurwarsa yake yi? Ta zauna ta bata lokacinta take jinyar sa? Wannan bai ishe shi ba, shi ne har zai rikota yana kiranta da sunan budurwarsa cikin barci. Ranta ya yi masifar baci, ta mike ta bar dakin, ta koma nata dakin, amma sai barci ya kaurace mata gaba ki daya, sai juyi take yi. Da zafin yai mata yawa, kawai sai ta samu kanta da fashewa da kuka. Ya kai karfe biyu, kafin ta samu ta koma barcinta.2 Da safe ba ta bi ta kansa ba. Ta gama shirinta ta tafi makaranta, don Allah ya gani, ba za ta tsaya tana shan wuya a kansa ba, alhali tana gani yana ciwon son budurwarsa ne kawai, ina za ta sabu, kura da shan bugu, Gardi da amsar kudi.9 Sai dai koda ta je kwata-kwata hankalinta baya kan Lectures din, sai tunani take yi, kar ace yana mayuwacin hali irin na jiya? “Ba sai ya yi ta shiga halin ba, ina ruwa na, Meenar ta zo tai masa jinyar.” Ta fada a ranta. Sai wajen karfe uku ta isa gida, tana zuwa ta same shi a falo sanye yake da T-shirt da jeans, idanunsa har yanzu ba su gama fitowa ba, amma dai ya fi kyan gani akan jiya, wata ajiyar zuciya ta sake, da ta ga ba abinda ya same shi, sai kuma ta dauke kanta za ta shige ciki. “Su Mama sun zo dazu, suna tambayarki.” Cak! Ta tsaya, yau ta ga ta kanta, me za su dauketa? Mijinta ba lafiya, ta kade kafa ta tafi makaranta, bayan ba wani zafi karatun ya yi ba. Komawa ta yi ta zauna a kujera. Ganin damuwar fuskarta ya sa ya-ce. “Nace masu ki na barci, ba su ma dade ba, suka tafi.” “Me ya sa ka fada masu haka? Sai ka fada masu fita na yi ai, da sun duba, ba na ciki fa?” “Na san muhimmancin abin da ya fitar dake, alhali mijinki na kwance? Shi ya sa ban ce komai ba.” Ta gane magana ya fada mata a dunkule. “Makaranta na tafi, tunda ka ce min ka warke, ban ga amfanin zama a gidan ba.” Ta fada cikin fushi, har yanzu da take duban sa, sai take jin wani munduku yana taso mata. Ta yi kamar ta fada masa abinda ya yi mata jiya, amma ta danne ta ki magana, za ta ga iya gudun ruwansa ai. Sam bai yi mamakin canjin da ya gani a tare da ita ba, don ko jiyan ma ya dauka ganinsa a halin neman taimako ne, ya sa ta yi masa abin da ta yi. Wanka ta yi, ta yi sallah sannan ta sauko, ga mamakinta, ji ta yi yana waya da Meena, don baya taba kwantar da murya da kowa, idan yana magana, sai ita. Bakin-ciki ya sauka a zuciyarta, ta shiga kicin ta fara aiki, ba ji, ba gani, ba da niyyar girki ta sauko ba, amma sai ga ta ta hada abinci. Ga shi ta yi mai yawa, ta rasa ma yadda za ta fara yi da abincin. Fatan ta su yi baki. Amma ta fito ta gyara Table, ta ce masa ga abinci. Ganinsa ta yi ya canza kaya cikin shirin fita. Baki a bude, da kyar ta samu furucinta ta-ce. “Fita za ka yi? Yaushe ka warke za ka fita?” Wannan muguwar murmushinsa na gefen ya yi mata. “Ki ajiye min abincin, ba dadewa zan yi ba.” “Idan ka je can, ta ba ka wanda ta shirya ma ka ci, idan ka ga dama ka zauna a can ta gama jinyar taka ma da ya fi.”. Ta fada a fusace. Fawzaan ya bi-ta da kallo. Hakan bai hana shi fitar ba, ita kuwa tun fitarsa, ta bude shafin kuka. A haka Anty Safiyya ta shigo ta same ta. “Lafiya Rumaysah me ya faru haka? Yanzu Mai-gadi ya fada min wai jiya kun tafi asibiti oga ba lafiya, sai kuma ya-ce kun dawo. Jikin nasa ne ya tashi, ki ke kuka?” STORY CONTINUES BELOW Girgiza kanta ta yi ta-ce. “A’a jikinsa da sauki, ba komai Anty Safiyya”. “To me ya sa ki ka shiga wannan halin? Ki yi hakuri, ki bar kuka haka nan. Ko ke ma so ki ke yi ki kwanta ciwon?” “To na ji Anty Safiyya, zan bar kuka, na kasa bari ne tun dazu, sai na yi shiru, sai kuma ya dawo min sabo.” “Ki yi addu’a, sai ki ji sanyi a ranki, kar ki sa damuwa a zuciyarki tai miki illa.” Da kyar dai ta lallashin ta, ta yi shiru. Har ma ta sa mata abinci a (Food Flask) akan ta kaiwa su Fadila ‘ya’yanta. Tana shirin fita ne. Mai-gidan ya dawo, ta gaishe shi da jiki, a lokacin ne ta ga yadda Rumaysah ta kwada masa wata harara, ko ba ta fada ba, ta gano dai matsala suka samu, don haka tayi masu sallama, ta tafi. Da nufin ta yi magana da Rumaysah, daga baya ko a waya ne. Da dare da ya nemi abincin da ta-ce ta yi masa. Ta- ce. “Ai na dauka ka ci a can ne ai, sai na kyautar.” “Kin kyautar fa ki ka ce? To ai sai ki shiga ki dafa wani, tunda dai kin hana ni cin komai, na dawo zan ci naki kuma za ki ce kin kyautar, daman ban saba cin naki ba, wannan kuma ba zai hana ni nema a inda na ke samu ba kullum.” Mikewa ta yi cikin bacin rai, ta ma rasa me za ta soma dorawa, da ta debawa Anty Safiyya kamar ta rage kadan, sai kuma ta ji haushinsa, hakan ya sa ta zuba mata mai yawa, ta ci kadan. Don haka kunun Semovita kawai tai masa, ta dafa Indomie da yaji kayan lambu da dafaffiyar kwai ta kawo ta dire masa su a kan Table. Yana kallon idanunta, ya san ta sha kuka, amma gogan ya ki ya tambayeta dalili. Sai ma kiranta da ya yi ya-ce. “Meye wannan kuma? Ni yaro ne da za ki dafa min Indomie?” “Idan za ka ci, ka ci, idan kuma ba ka so, ka bar shi anan, saboda na gaji, tun rana na ke kan kafata, na bata lokaci na hada maka abinci, amma me? Ba ka da lokacina bare na abinci na, ka tafi inda ka ke da lokaci. Meye laifina, don na kyautar da abincin naka? A halin yanzu kuma abin da na ga zan iya dafawa kenan, idan ka ga ba za ka iya ci ba, za ka iya kyautarwa ko ka zubar, wannan duk matsalarka ce, ya rage naka.” Ba ta jira amsar sa ba, ta wuce daki. “Kuma na daina kuka saboda kai kenan, wannan ya kare daga yau, ka yi yadda ka ke so.” Ta fadawa kanta a bayyane lokacin da ta isa dakinta. Tun daga ranar suka koma zaman (HALIN KO IN KULA), Ta koma sabgar ta, ga shi satin da za a shiga ne, za ayi babbar sallah, ko maganar tsarin yadda za su yi ma, bai mata ba, haka ita ma ba ta dago masa ba. Sai da suka je gidan Baffa ne. Mama ta-ce ya bar abin yankansa a gida, idan an tashi masu yi mata aiki, duk sai su hada su yi da na su. Ba haka ya so ba, ya so ya hada Rumaysah da aikin, don ya ga kwanan nan kanta, wani fizga yake yi, duk abin da ta ga dama shi take yi.1 “Mama, da kin bar mata ai, sai ta koyi yadda ake yi, wani lokacin ma haka za ta kawo gidan ai mata aiki?” Kut! Lallai ma Yaya Fawzaan yaya za ta fara aikin lahiyya ita kadai, sai dai Wallahi kar a ci naman. Haka kawai, jira take yi ta ji me Mama za ta fada, don ta san ba za ta biye masa ba. “Kai idan an hada ka da rago guda yaya za ka yi da shi? Ka ji min wani mugunta a nan, kwanan nan ka yi jinya, ta sha dawainiyar jinyarka, sannan don rashin tausayi za ka kama ka ce a bar mata aikin lahiyya. Kai hatta abinci ma anan za a sa maku. Ke dai Rumaysa’u idan ki na sha’awar wani abin, sai ki yi kayanki, ki rabu da shi.”4 Zuciyarta fal! Da farin-ciki, ta juya ta kalle shi, ta sakar masa mugun kallo, bai tanka mata ba, asali ma daure fuska ya yi, ya tashi ya bar masu falon. Ita Rumaysah mamakin muguntar sa take yi, da abin bai dameta ba, amma duk lokacin da ya nuna rashin damuwarsa a al’amarinta, yanzu sai abin ya yi mata ciwo. STORY CONTINUES BELOW Ana gobe sallah kwatsam! Bayan an sha ruwan azumin ranar Arfa, sai ga Rayyan ya zo gidan su, Rumaysah ko ba ta yi kasa da gwiwa ba, ta wadata shi da kayan tabe-tabe da ta yi na sallah, don tun wajen la’asar ta gama gasa Cake dinta na (Red Velvet) mai dadi. Haka ta yi abin sha, ta kawo ta ajiye masa suka gaisa. “Wato, Yaya Rayyan kai ka ke dauke min miji koda yaushe ko? Abu kadan sai ya-ce kun fita tare.” Rayyan ya kusa kwarewa, jin maganar Rumaysah, ya dubi abokinsa ya-ce. “Ina, Madam, ayi haka? Shi dai ya fada miki gaskiyar inda yake zuwa. Don waka a bakin mai ita, ta fi dadi”. “Ka rabu da shi, nace masa ko ya yi azamar yin wani abu a kai, ko kuwa ni nai masa komai, don na ga alama kamar tsoronta yake ji.” Dukansu tsit! Suka yi, ganin ta san ko ma menene suke boyewar. Fawzaan kam sarai ya san ta sani, amma bai yi tsammanin za ta dagowa Rayyan maganar ba, ganin Meena Cousin dinsa ce. Sai da ta kara cakalkala su da magana, sannan ta wuce kicin. Rayyan ya sauke ajiyar zuciya sannan ya-ce. “Allah, Madam dinkan nan Hot Fire ce, kai gaskiya ina ganin kokarinka, to ka ji dai me ta-ce.”6 “Ka rabu da ita ka ji, neman magana take yi.” Fawzaan kuwa wani abin ne a lokacin yake damunsa, har Rayyan ya tashi tafiya. Rumaysah kuwa ta gama aikinta na kimtsa kicin ta fito falo. Sai ta ji ana danna Bell ta leka ta ga Mai-gidan. Da alama ya bar makullinsa ne da ya fita rakiyan, kasancewar Jam Lock ne, dole sai ta bude masa daga ciki. Ta bude masa kofar, tana budewa maimakon ya wuce, sai ya tura kofar ya rufe, sannan ya ritsata jikin kofar. Kallonta yake yi da idanunsa masu razanarwa. “Wace irin dabi’ace wannan za ki na fitowa falo da ‘yar riga da skirt a jikinki? Bayan ki na ganina da bako? Su wadanda suke zuwa din muharramanki ne?” Ya kara dubanta daga sama har kasa. (Pencil Skirt) ne (Navy Blue) a jikinta. Sai Blouse mai gajeren hannu na farin Silk da siririn Blue gyale a saman kanta. Rumaysah ta yi kokarin fita daga tarkon sa, amma ta kasa. “Meye damuwarka da shigata, kai kanka ka sani, haka na ke sa kaya, tun kan ka aureni, saboda haka ba damuwarka bace.” Ransa ya yi masa wani zafi ya-ce. “Damuwata ce, saboda idan ana ganinki ki na haka a gidan ku, ba a hana ki ba, to ni hakki na ne na kare ki daga fitina, na kuma hana fitina shigowa gidana, don haka daga yau duk sanda ki ka ji wani ya zo gidan nan, ki sa hijabi, saboda ban amince kowa ya rinka kalla min mata, ana min kallon wawa ba.”4 Wata irin dariya ta sake. “Allah, masu mata, ina ce wasu matan suna suka tara, musamman matan qaddara ashe, wadanda suka tara sunan ma da darajar su kenan.” Lumshe idanunta ta yi sannan ta-ce. “Na ji bukatarka, za ka iya matsawa yanzu na wuce ko kuwa ka na da sauran abin cewa?”6 Shiru ya yi yana kallon idanunta, kafin wani lokaci, idanunsa cikin radin kansu suka kai kan jajayen labbanta, wadanda daga gani laushi ne garesu. Cikin bugun zuciya daya ya aikata abinda ya zo masa kwakwalwarsa. Ba ta ankara ba kawai, ta ji labbansa akan nata, nan take zuciyarta ta shiga bugawa da sauri-sauri, kamar yadda ba ta san lokacin da ya yi hakan ba, haka ba ta san yaushe ya saketa ba.2 Kallon sa ta tsaya tana yi, sai haki yake yi, yayin da ita kuma ta sa kuka da gudu ta haura sama. Fawzaan kuwa kaiwa bango duka ya yi. “Wai me yake damuna ne? Subhanallah!” Gaba daya ya rasa me ya shiga kansa, har ya yi tunanin yin hakan. Nan take ya ji ya tsani kansa.4 Wane irin abu ne a kwakwalwarsa? Ya yi ta ingiza shi kawai ya yi abinda ya yi. Haba ya rasa wacce zai ji sha’awa, sai wannan ballagazar yarinyar? Cikin bacin rai da tashin hankali ya sake bude kofar ya fita waje, wannan karon ya tabbatar sai da ya dau makullansa kan ya fice. Don ko kallonta baya tsammanin zai iya sake yi. Ya dade a zaune kan kujerar robar dake kofar gidan nasa. STORY CONTINUES BELOW “Ingizar kwakwalwa be damned, me ya sa na ke jin haka game da ita? Me ya sa idanuwana suke rufewa dangane da al’amuranta? Shin sonta ne yake shigata? Kai ina! Ba na sonta, ba zan taba sonta ba, ko kuma na yi tunanin sonta. Ba ta burgeni, na tsani duk wasu al’amura nata. Sannan duk wani abin da ya jibanceta, ba na son su, amma kuma…” Kawar da tunaninta kawai ya yi a zuciyarsa, ya shiga lalubo wani abin daban.4 Ga yanayin garin gwanin sha’awa, iska ce ke kadawa kamar za ayi ruwa, duk da dai an bawa damina baya, amma hunturu bai gama shigowa ba. Sai ya ji kamar ya kira Meena su yi hira, sai ya tuna abin da ya yi na cin amanarta dazun, don haka nan ya yi ta zamansa, har sai wajen karfe sha daya na dare, sannan ya koma cikin gidan.5 Bai neme ta ba, haka ita ma tunda ta shige dakinta ta kulle kofa, ta yi kwanciyarta, hawaye take yi, amma ba ta san na meye ba, yatsunta ta sa tana shafa labbanta, take bugun zuciyarta ya koma bugawa da sauri-sauri. “Wai me Yaya Fawzaan yake nufi da ni ne me ya sa yake min haka? Alhali ba ni a zuciyarsa? Bai san me na ke ji a raina ba game da shi bane, me zai sa ya min haka?” Haka ta raba dare tana tunanin abin da ya faru, alhali shi kuwa ya mayar da abin a matsayin kuskure ne kawai. Kasancewar ba aikin da za ta yi, tana gama share-sharenta, ta cancada wankanta, ta ci gaye sosai cikin wani Lace mai ruwan hodan da ya turu, an masa ado da Blue zare, ya mata kyau sosai kayan, dinkin riga da Skirt ne ya kama duk tudu da gangaren jikinta, ta yi kyau kamar wata (Doll Baby). Dankali ta dafa, ta yi (Egg Sauce), sannan ta sa ruwan zafi ta ajiye a Table, duk da ta san sai anyi yanka zai karya, hala ma ya ci a gidan Baffa, don ko gida zai dawo, ba lallai bane ya ci wanda ta yi. Ranta fari kal! Abbanta ta fara bugawa waya, ta gaishe shi tare da masa fatan ayi sallah lafiya. Abba ya-ce. “Da ke da Radiyya zan yi maganin ku, wannan sallar nama ne, ba na kudi ba, saboda haka babu barka da sallah.” “Tab! Abba, sallah sau biyu a shekara, ai dole ka kawo mu banbari rabon mu.” “To shi kenan, sai kin zo, za ki gani, ita ma da take AMARYAR BANA, ba zan ba ta ba, bare ke.” “Za mu zo anjima ai. Abba don Allah ka zauna a gida, idan na zo ko Momi za ta amsa gaisuwata.” “Yau kam Insha-Allahu sai ta amsa, sallah guda? Kar ki yi kuka, ki bata kwalliyarki, sai na gani kin ji?” Tana goge hawaye a gefen idanunta, ta ce masa ta ji. Suna gama waya, ta bi kan su Baffa da Mama duk ta gaishe su. Juyawar da za ta yi, ta ga Yaya Fawzaan ya sauko da ga matakala, farar shadda ce a jikinsa gare da ‘yar cikinta, sai kamshin turare yake yi, ya sa bakar hula da bakaken sau ciki, sai ya fi kama da ango. Take ta ji wani alfahari ya kamata, da wani dadi a zuciyarta, saboda Yaya Fawzaan mijinta ne, sai dai tana tuno maganganunsa cikin barci ta-ce Mijinta ne, amma shi ba nata bane. Suna hada idanu, ta tuna jiya, maza ta yi saurin juya masa baya, shi din ma sunne kai ya yi, don sai ya ji nauyin abin da yaI mata. Har ya kai kofa ta-ce masa. “Ayi Idi Lafiya.” Bai ce mata komai ba ya fita, don abin da zai kubutar da shi kenan kawai. Haushi ta ji, da za ta yaba kwalliyarsa, sai ta fasa, tunda shi ko kallonta bai yi ba ma bare ya-ce ta yi kyau. Koda aka sauko Idi, gidan Baffa ya wuce suka yi yanka tukun, sannan ya koma gidan domin dauko ta. Ya samu ta gama shirinta, tana zaune Ready, shi take jira ya dawo, ba don sun yi tare za su fita ba, da tuni ya samu ta tafi da motarta. Ta zuba Snacks din da ta yi wasu Abba da Baffa a motar. Har ta zauna a mota ne, ya shigo ya-ce. “Haba Rumaysah, sallah dai ta Allah ba gaisuwa?” Ya fada cikin gatse. STORY CONTINUES BELOW “Cewa na yi ba ka bukatar tawa gaisuwar ai, tunda nai maka fatan alkhairi ma ko amsa min ba ka yi ba.” “To ayi hakuri, barka da sallah. By the way, kayan sun miki kyau. Sai dai ba na son wannan kalar jan-bakin”. Ya fada hade da kai hannunsa kusa da bakinta da niyyar gogewa, da sauri ta buge hannunsa, ta juya fuskarta a daure tamau! Dariyarta ya yi, sannan ya ja motar. Oh, ashe idanunsa suna iya ganin kyawunta, ai ta zaci kyan Meena kawai yake gani, nan dai ta yi kwafa ita kadai, sai tunane-tunane take yi har suka isa. Har falon Baffa ta shiga suka gaisa, sannan ta wuce cikin gida, nan ta tadda Muneerah ta zo. “Yaya Muneerah, ya gida da yaya Abdullaahi? Yaya na ganki a gida yau sallah?” “Yanzu Abdullaahi ya ajiyeni, anjima zan koma.” Fawzaan ya shigo ya-ce. “Ai ni na rasa AMAREN BANAN nan. Sallah ta Allah ba za ku zauna a gidajenku ku yi aiki ba, ku samu lada, kun wani ci kwaras! Kun tafi yawo.” “Ah, Yaya Fawzaan ka bar mu mu yi, lokacin mu ne, yawon ma ai sada zumunci ne, haka kawai ni a gidan Sister din Abdullaahi ma za ayi mana aikin namu, yana can iyaka ya yanka, a mika aikin cikin gida, ni kuwa na yi aikin ci. Ko me ki ka ce Rumaysah?” “Gaskiyarki, wa ya ki hutu a zamanin nan?” Yaya Fawzaan ya-ce. “Zan fadawa Mama wata shekarar, kar ta amince da wannan wayon” “A’a ku bari idan ku ka kawo, wadanda suka saba aikin sai su yi maku, mu kam ‘ya’yan hutu ne.” Rumaysah na fada tana kallon Yaya Fawzaan. Da kansa ya dauke idanun sa, ya-ce. “To ni kam muna waje da su Baffa.” Ba ta amsa masa ba, nan ya tafi ya bar su suna hira da Munnira. Can Rumaysah ta-cewa Mama za ta shiga gidan Abba. Cikinsu kaf! Khansa’u ce ba ta nan. Khadija ma baro aikinta ta yi, sai washegari za ta yi. Farin-ciki ne a zukatansu, duka sun hadu a falon Abba, ana ta hira, sai wasa da dariya ake yi, suna yiwa Ra’id tsiya, wai ya zauna cikin mata. Lokacin ne Momi ta shigo falon. Rumaysah ta gaisheta, hade da mata barka da sallah. “Sai yanzu ki ka san ina gidan? Ai kin gayar da wadanda suka fi miki komai daraja, don haka ki rike gaisuwarki.” “Momi, na shiga na samu ki na waya, shi ya sa na sauko kasa.” Duka ‘Yan-uwanta suna jinsu. Ra’id ya-ce. “Momi ayi mata hakuri mana, yau sallah ta Allah.” “Ni na fada mata ai, muddin tana son ganin fuskata, to amsar guda ce ta rabu da Fawzaan.”3 Fadan hakan da ta yi, ya yi daidai da shigowar Abba, ya-ce. “Kar ki kulata, idan kin ga dama har karshen rayuwarki, amma Rumaysah ba za ta rabu da Fawzaan ba, idan ta rabu da shi, ki yi yaya da ita? Yanzu ta fara auren sa, idan za ki amsa gaisuwarta, ki amsa, idan ba za ki amsa ba kuwa, ba ta da hakkinki a kanta, saboda dalilinki na wofi ne, za ki umarce ta da sabon Allah, wato raba zumunci da kuma bijirewa mijinta.” “Na san haka za ayi ai, don haka ta-ci-gaba da auren Fawzaan, ni kuma na yafe masa ita.” Hankalin Rumaysah ya yi mummunar tashi, jin kalaman mahaifiyarta, da sauri ta tari gabanta ta-ce. “Don Allah Momi ki yi hakuri, kar ki min mummunar baki, fushin ki fa guba ce a gareni bare kuma dafin bakinki na mahaifiya, don Allah ki sanya min albarka ko rayuwata za ta samu sassauci. Ba ki san halin da na ke ciki ba, ki yi hakuri Momi, ni gudan jininki ne, kar ki kaurace min. Ke ce jigon rayuwata, kuncin da na ke ciki game da halin da na sa ki a ciki zai iya zama hatsari a gare ni. Ki yi hakuri ki gafarta min. Momi ki kalleni da idanunki na mahaifiya mai sanyi ga diyoyinta.” Gabaki daya falon sai da jikinsu ya mutu, yau kam har da Khadija aka sa baki aka bawa Momi hakuri. Ganin sun sa ta a gaba, duk suna mata kuka, suna kwantar da kai, ya sa ta-ce. “Shi kenan na ji, na yi hakuri na yafe miki.”10 STORY CONTINUES BELOW Wani irin ajiyar zuciya Rumaysah ta sauke, sai ta fashe da kuka, tana hamdala da sauri ta rungume mahaifiyarta, tana kukan dadi. Haba nan da nan yanayin gidan ya canja kowa farin-cikinsa ya ninku fiye da da. Abba ma ya ji dadin hakan kwarai, ya san a hankali za ta sauko, kuma hakan ya faru da ikon Allah. Har dare tana gidan Abba, kamar ta yi kuka da Fawzaan yai mata waya akan ta zo su tafi gida. Momi tana kallon yadda Rumaysah take farin-ciki, a ranta kuwa, ita kadai ta san kudurinta. Tun daga mota take ta faman murna. “Yaya Fawzaan ka san yau Momi ta sauko, mun gaisa mun yi hira da ita? Yau ba wanda ya kai ni farin-ciki duk duniya, Alhamdulillah.” Kwarai ya ji dadin zancenta ya kuma taya ta farin-ciki, a hankali dai ta dage sai ta cimma burinta, ga shi ta dau mataki na farko cikin abin da bai fi watanni biyu ba. A zahiri ko ce mata ya yi. “Kin ji dadi, burinki ya soma cika.” Haka nan ya sa murnarta ta koma ciki, sai can ta-ce don me za ta bari maganarsa ta dame ta? Shi ya jiyo, ko zai mutu kuma tana farin-ciki. *************** Haka ta ci-gaba da zuwa makaranta, har suka shiga shirye-shriyen auren Radiyya da Deeni, tunda aka soma hidimar, kusan barci ne kawai yake kai ta gida. Don haka haduwarta da Yaya Fawzaan ma ba sosai ba. Sai dai ba abinda take so. Irin lokutan daukar karatunta, don lokacin ne kawai take samu nata ita da Yaya Fawzaan, musamman idan tana sauraren muryarsa, yana mata bayani cikin natsuwa. Wasu lokutan ba asalin saurarensa take yi ba, kallon sa take yi kawai, tana jin muryarsa, wani irin dadi ke gewayeta a wadannan lokutan.6 A hankali dai Rumaysah ta fuskanci ba karya son Fawzaan ne ya yi mummunar mata kamu, ga shi kuwa kwata-kwata hankalinsa baya ma kanta, banda surfa mata wulakanci, ba abinda yake yi, ita kuwa koda wasa ba ta taba nuna masa cewa tana sonsa ba, bare ya karasa murkusheta a kasa. Ranar asabar da safe ne ta roke shi, da kyar da sudin goshi ya kai ta kasuwa ta dan yi sayayya, saboda suna da bukatar wasu kayan. “Kin san za ki je kasuwa, me ya sa ki na gani Muftahu ya tafi da motarki wurin Service?” “Don Allah ka yi hakuri, ka ajiyeni.” Hada shi da Allah da ta yi ne, ya sa ya sassauto ya yarda ya kai ta. Suna isa ya-ce mata. “Idan ki ka fi minti talatin kuma sai dai ki san yadda za ki yi ki koma gida.” “Yaya Fawzaan, yaya minti talatin zai isheni? Gudu zan rinka yi a kasuwan ne, na gama da wuri haka?” “Ni dai na fada miki.” Ita kuwa ta yi murmushi, ta dauki kudin da ya ajiye mata, saman list din a gefenta. Ta sa a cikin jaka ta yi ficewarta. Wurin masu gyaran kaji ta fara zuwa, don su gama da wuri, sannan ta shige ta yi sauran sayayyar. Nan ma sai da ta hada da kiran su Laminde, suna mata kwatancen kwastomominsu. Ta gama sayayyarta gaba daya, ta koma ma’adanar motoci, sai dai wata sabuwar, neman Yaya Fawzaan ta yi sama da kasa ta rasa. Ga mai Baro ya biyo ta da kaya. Da sauri ta lalubi wayarta a jaka ta nemi lambarsa, sai dai tana ta ringing, amma bai daga ba. Hankalinta ya tashi, ta duba lokaci. Sai a sannan ta kula da ta yi awa guda a cikin kasuwar. “Tabdi! Wato yanzu da gaske yake yi tafiya zai yi ya bar ni?” Ai ba ta ida rufe baki ba, sai ga ruwa ya sauko, kamar da bakin kwarya, ana ganin damina ya tafi ashe da saura.6 Da sauri ta-cewa mai baron ya biyota, suka wuce wurin da ‘yan Tasi suka yi Parking, daurewa kawai ta yi ta rufe idanu, ta shiga, domin tunda ta zo duniya ba ta taba shiga motar haya ita kadai ba. Da Allah ya taimaketa, tana fada masa sunan unguwarsu ya fahimta. Ta biya mai Baro, ta shiga tana ta addu’o’i. A bangare guda kuma mamakin Yaya Fawzaan ne a zuciyarta. Ashe yanzu sai ka tafi ka bar mutum a cikin wani hali? Ba ta san yadda aka yi zuciyarta take son mutum irinsa ba ma. STORY CONTINUES BELOW Mai Drop ya shigo da ita har gida, bayan Mai-gadi ya leko, cikin mota, don ya tabbatar ba bata suka yi ba, da ya ga Rumaysah ne ya ce. “Oh, Madam na you?” Murmushi ta yi kawai na yake, saboda tsabar takaicin Fawzaan da take ciki. Ta sallami mai Drop. Mai-gadi ya tayata shigar da kaya, kasancewar ruwan ya dada karfi, kafin su gama ta jike cakwaf! Kulle kofar ta yi, ta wuce sama, domin canza kayan jikinta, a falonta ta same shi yana duba jarida. Tamkar baida wata damuwa a duniya, jin shigowarta ne, ya sa ya daga jaridar daga fuskarsa, ya ganta a tsaye. “Yaya za ki tsaya, ki na diga mana a wuri.” Wucewa ciki ta yi ta watsa ruwa a jikinta, sannan ta matse kayan jikinta. Ta sako T-shirt da wandon ¾ Ta fito. Jaridarsa ta warce ta ajiye a gefe. Sannan ta-ce. “A da ina tunanin mun ci-gaba daga inda muka fara, amma kuma rashin fahimtata ce kuma yau na gane hakan. Na gane da ni da kai bakin juna ne, kuma har yau wannan bai sauya ba. Idan mutumcin dangantaka bai sa ka tausaya min ka jirani ba, ai kara ta zamantakewa za ta sa ka ji nauyin abin da ka yi. A yayin da ka ke aikatawa. Yau da wani abu ya sameni Yaya Fawzaan dole ne ka yi kuka da kanka, saboda ka jefa ni a hadarin da ban taba shiga ba. Ba ka san sau nawa na taba zuwa kasuwa ba bare ka san ko na san yadda zan yi na koma gida, bugu da kari ka na sane da yanayin garin nan, ka iya juyawa ka bar ni a bakon yanayi. Na gode da komai, ba ka yi kuskure ba, da ka ce za ka sa ni a hell. Na gani kuma nai maka alkawarin daga yau. Sai dai wata Rumaysan, amma ba ni ba, na gama wasan hankalin da ka ke yi da ni. (I’m done with your mind games). Ka fada min duk wata manufarka game da ni a yau din nan.3 Duk abinda kuma ka yanke, ina tabbatar maka da ka sani ba zan kara ko Second daya a cikin gidan nan ba, idan ka budi baki ka ce min na yi tafiyata.” Ta goge hawayenta, ta koma daki ta ja bargo ta rufe kanta a ciki, yayin da ta bar Fawzaan jiki a mace a kan kujerar falonta. Shiru ta yi cikin bargo, saboda ranar ba ta samu sa’idar ZUBAR KWALLAR ba ma. “Mutumin da na ke matukar so ne, shi kuma yake matukar ki na, da har zai iya jefa rayuwata a cikin garari, saboda kawai ya kasa hakuri da wata doka da ya kafa min, na takurawa. Kamar ba tare za mu yi amfani da kayan sayayyar ba.” Wasa, gaske har suka cika watanni hudu da aure, bai ce mata komai ba, amma zaman na su ba canji. ******** Ranar lahadi ta je gidan Abba suna hira da Momi ne, take ce mata. “Oh, Sis tana can ko yaya take yi da barcinta, sai Allah.” Momi ta-ce. “Ai Radiyya za ta sha wuya da wannan shegen barcin, sai dai Deenin ya yi ta fama kafin ta saba.” “Momi ya yi ta fama kamar yaya, shi zai mata aikin gidan nata?” “Ah to, yaya ya iya, idan ya ga ba ta da niyya.” “Tab! Lallai ai da kunya, ni kam ni na ke komai da kaina, har yaushe Yaya Fawzaan zai tsaya min aikin gida? Ashe aikin zai shekara kenan ba ayi ba.” Momi ta-ce. “Saboda me ba zai taya ki ba? Ai akwai taimakekeniya a tsakanin miji da mata, ki ga mijinki baya tayaki aiki, baya tausayinki kenan bare so.” Ran Rumaysah ya dan sosu, tabbas ta san Fawzan ba ya sonta, amma ta san dai yana dan tausayinta kam. Kuma yana iya kokarinsa wurin kula da ita, idan aka yi la’akari da rashin son da yake mata. “Ba haka bane Momi, muna zaune lafiya ba tashin hankali, ai hakan ya fi komai.” Yake Momin kawai tai mata, sannan suka shiga wata hirar daban. Ba ta sake dago mata maganar Fawzaan ba, koda ya zo daukarta, yana falon Abba ta-ce. “Bari na yiwa Momi magana ku gaisa.” Hada rai ya yi ya-ce. “Ki bari kawai, sai wani lokacin ma gaisa, yanzu ina sauri, kin san na fada miki mun yi baki suna jiran mu a gida.” Jikin Rumaysah ya mutu, zama ta yi a kujerar kusa da shi ta-ce. “Har yanzu da akwai wani abu kenan tsakaninka da Momi, idan ba haka ba, wane sauri ka ke yi da zai hana ka jira minti biyu, ka gaida mahaifiyata?” Ta fadi hakan dai kawai, duk da ta san ita kanta ba ta da wani matsayi a wurinsa, bare Momin nata. Kuma dai ta fi shi gaskiya, ganin tunda aka yi bikinsu, Momi ba ta ma kula ‘yarta ba bare aje ga wanda ake kin kulata dominsa, ga shi yanzu sun daidaita, amma ko sau daya bai taba yunkurin kammala wannan daidaituwar ba. Ajiyar zuciya ya yi, ya danne fushinsa ya-ce. “To ki mata magana, da sauri, ki zo.” Cikin farin-ciki Rumaysah ta mike ta haura sama, yayin da Fawzaan ya bi-ta da kallo ya sauke ajiyar zuciya. Ya yi mamaki kwarai da gaske da ya ga Momin ta biyo ta, ya zaci za ta ki fitowa, ganin yadda ta ki jininsa. Har kasa ya durkusa ya gaidata, ba yabo, ba fallasa ta amsa gaisuwarsa, a karo na farko kenan, yana tsammanin tun zuwansa duniya. Suna gama gaisawa, ta mike ta bar falon. Shi ma ya tashi daga durkuson da ya yi. Rumaysah ko don tsabar farin-ciki, zuwa ta yi kusa da shi ta rike hannunsa ta-ce. “Ba ga shi ba na fada maka. Komai ya yi daidai.” Fawzaan dai bai yarda da abin da ya gani ba, sai dai watakila da gasken ta canza. Momi na fita, ta ga yadda Rumaysah ta rike hannun Fawzaan, ranta ya murda kwarai kamar ta sa ihu.3 Sai da suka iso kofar falon, ta kula da hannayensu dake manne da juna, da sauri ta zare nata ta matsa gefe, hade da saukar da kai cikin jin nauyi. Gyaran murya ya yi, sannan ya wuce gaba. Haka suka isa gida, kowa yana saka wani abu a zuciyarsa. ************

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *