DAN ADAM CHAPTER 32

DAN ADAM CHAPTER 32

Sanye ya ke da shadda kalar sararin samaniya sai hula shima bulu, sai murmushi ya ke bugawa yana gaisawa da yan uwa har da mikawa Dada hannu suna gaisawa gami da dariya. Ummi bata iya motsi ba hakanan ta kasa cewa uffan saida ta tsinci muryar Amina na fadin. “Wai daman *ABUBAKAR* dan uwa ne gareku?” Ta girgiza kai sannan ta maida dubanta ga Amina kamar wata doluwa. “Wallahi bani da masaniya nima.” Basu kai ga tsinkewa da lamarin ba saida suka ga shigowar Alhaji Kabiru Jimeta da sallamarsa. Mamaki, rud’ani da tsananin faduwar gaba duk suka tararwa Ummi da Amina, aka rasa mai magana cikinsu har wasu cikin mutanen Jar Kwami suka shigo wasu rirrike da jakunkunan kaya. “Wai ina Amaryar?” Cewar wata mace da zata kai shekaru arba’in a duniya. Da sauri ta ja baya daga jikin windon tana sussunne kai, wata gwaggonta ta riko hannunta tana dariya. “Oh 6uya ki ke? To fito nan ga uwarki da ba ki sani ba, Safina, sannan kuma (ta nuna wata doguwa mai rike da bebi a hannunta, bazata wuce talatin da tara ba) itama uwarki ce Nafisa sunanta, duk yaran gwaggonki ce Binta.” Sukayi dariya, wacce aka kira da Nafisa ta ce. “Maza fito na kaiki ku gaisa da Innarmu ta ga Innonta ta dawo.” Amina ta hau janyo musu ita don ta mak’ale a bayanta, ita kanta dauriya kawai ta ke yi saidai jikinta ya yi mugun sanyi, tambayar da kowannensu ke yiwa zuciyarsa bai wuce na son sanin dangantakar Alhaji Kabiru da mutanen gidan ba. Ummi na kallo suka ja ta har rumfar Dada inda ake zazzaune ana gaisawa, kan Ummi a k’asa yayinda aka zaunar da ita gefen wata dattijuwa wacce shekaru suka ja saidai garas tana gane mutane sannan tana fahimta. Da harshen fulatanci ta ji wacce ta zaunar da ita ta yi magana. Abinda ta fada ne ya janyo hankalin sauran bak’in duk suka dubeta, Abubakar da hankalinsa ke kan wayarsa yana kokarin turawa uwargidansa sak’on isowarsu lafiya, shima ya dago kai yana duban wacce aka kira da Amarya kuma jininsa mai kama da Innonsa. Mamaki k’arara ya bayyana saman fuskarsa, a yayinda shi kuwa Alhaji Kabiru ke kallon Ummi cike da al’ajabi na kamanninta da Antinsa Inno wacce a girme ma ya girmeta saidai duk da hakan kanwa ce ga mahaifiyarsa GWAGGO BINTA babbar Yaya ga Manu Lamido uba ga marigayiya Hasiya…! Hannun Gwaggo Binta na rawa ta kamo na Ummi tana mai rike kafadarta da hannun damanta. “Sannu Hasiya, shakka babu wannan jininmu ce diya ga diyata Hasiya, ashe da rabon mu k’ara sanyaki a idanunmu?” Sai ta janyota jiki tana hawayen farinciki ga kuma bakinta da ya k’i rufuwa don murna. “Ke ce?” Cewar Abubakar da mamaki yana nunota da yatsa, hakan yasa duk wanda ke fahimtar hausa sosai ya kalloshi don ba kowa cikinsu ne ke jin hausa ba, Malam Balarabe da Alhaji Kabiru har suna hada baki wajen fadin. “Ka ta6a ganinta ne?” Ya jinjina kai yana murmushi mai bayyana hakora. “Tabbas Dad ita nace maka na gani fa a gidansu Abban Kano mai kama da Inno. Saidai…” Sai kuma ya yi shiru, har lokacin bai bar mamaki ba. Kallon Ummi kawai ya ke yi kamar Innonsa, Innonsa Zahra mai matukar kaunarsa, sun shaku sosai, ayi wasa ayi dariya, yana mata kallo kamar wata sa’arsa kuma kanwa gareshi don koda zata girmeshi ba da wasu shekaru na azo a gani bane sannan gajeriya ce bata da jikin girma. Sune har guje-guje, komai na shawararsa idan ya dauko to fa da Inno zasuyi ta, sau da yawa kafin iyayensa su san wani abu nashi, Inno ta sani don gaba daya tare suke zaune har Gwaggo Binta a gidan Baffansa Kabiru. Bai mantawa ana shirin bikinta ta yi bankwana da duniya, mutuwar da sosai sun ji ta a zukatansu don har kwantar da shi ta yi, hakanan mahaifiyarsa Hajiya Salma ita kanta saida ta yi kamar ba zata rayu ba tsabar razanar da ta shiga sanadin mutuwarta. To me ya kaita Kano? Me kuma ta ke yi gidan su Ihsan? A ina Faruk ya ganta ya ce yana so? Wannan shine tambayoyin dake yawo a kwanyarsa da ba shi da mai amsa mishi. Kowa a wajen ya cika da mamaki banda wadanda sukasan silar zaman Ummi a Kano da Abuja.+ Bayan gama gaggaisawa mazan suka fita, itama Gwaggo daki ta koma. Ummi ta ja Amina suka koma sashen Anti Halima. “Kinga ikon Allah ko Anti?” “Allah kenan, ashe duk firiritar Ihsan kuma danginku za ta shigo? Wannan lamari saidai Allah, ya dangantakar ta ke?” “Gwaggo Binta kakarsa uwa ce ga Ummana. Nima tana matsayin kakata.” Amina ta hau gyada kai sai kuma ta soma dariya Ummi na tayata tana tambayar ko lafiya. Girgiza kai ta yi. “Wallahi Ihsan gwanar wulakanci ce ta ban tausayi kawai, yanzun ko da wane idon zata kalleki? Shiyasa a duniya ba’ason ka dunga wulakanta DAN ADAM don bakasan mai yi maka rana ba gobe.” Murmushi Ummi ta yi kawai tana kokarin goge wayarta wacce ta koma yaluwa saboda kurkum. Sai dare Abubakar ya samu damar ke6ewa da Ummi sadda ita da Amina suka je kai mishi damammiyar fura inda ya je zaune tare da Gidado (wanda shima bai jima da zuwa ba daga Jar Kwami) suna hira. Kusan ma a kyau har Gidado ya tsere Abubakar saidai shi zai nunamishi wayewa da hutu sosai da kuma zurfi a ilimin boko don kuwa shi Gidado iyakarsa sakandire ya watsar ya fada kasuwanci, Kano ya ke zuwa saro kayan sawa na mata ya ke siyarwa, sosai yana samu don asirinsa a rufe. Matarsa daya Aisha wacce sukayi auren soyayya sai dansu da baifi shekara daya ba don duka-duka aurensa ko shekara biyu baiyi ba saidai idan Gidado ya sanya sutura sai ka rantse ba mazaunin Jar Kwami bane musamman idan Abubakar ya mishi aiken suturu daga Adamawa. Da sallama suka shiga suka ajiye furar kafin su gaishesu, suka amsa. Ummi ta dubi Gidado da murmushi saman fuskarta. “Yaushe ka zo?” Shima murmushin ya mayarmata. “Ko awa biyu cikakku banyi ba.” Ta gyada kai sannan ta mike zata bi bayan Amina wacce daman suna ajiyewa ta fito, Abubakar ya dakatar da ita. “Ummi.” “Naam.” Ta amsa tana dubansa gabanta na dukan tara-tara. “Please ke ce dai wacce na sani a Kano gidansu Ihsan?” Ta gyada kai a sanyaye. “To meya kaiki can?” Gidado ya cafe. “Au ka ta6a ganinta acan kenan? Ai ta zauna can.” Jin haka Ummi ta mike da sauri, tana jin Gidado ya soma labartamishi yanda lamura suka kasance ita kuwa tuni ta soma zura takalminta, suka kama hanya da Amina tana sanarmata yanda akayi, Amina murmushi ta yi. “Allah Sarki.” Shine abinda ta ce kawai. *** *** *** ABUJA Tun bayan sati da kwanaki da tafiyar Ummi, Ikram bata cikin nutsuwarta, gaba daya ta rame ta koma wata shiru-shiru, koyaushe bata da aiki sai na kuka ga wani ciwon so da ya addabi zuciyarta har tana ji idan bata samu cikar burinta ba zata iya rasa rayuwarta. Har mutanen Kano suka iso Abuja bata da walwala sosai, kowa sai ya tanbayeta damuwarta amman ta nuna ba komai kawai bata jin dadi ne, Ridwan har dubata ya yi ya kuma gano damuwa ce kawai ta sanyawa kanta, tanbayar duniya ya yi mata amman babu amsa. Daidai da dinkin ankon da sukayi kala biyu ya yi mata yawa sakamakon ramar da ta yi. Yau ma babu kowa a gidan, Hajiya sun fita tare da su Mami ganin gida, ita kuwa Ihsan da su Maryam sun tafi gidan Baraka can zasu wuni har da wasu cikin bak’in Adamawa, manyan kuwa suna can kwatas suna hira da Hajjah wacce ta zo ko don jikanta. Tana kwance daga ita sai shimi da dogon wando wanda da kadan ya wuce gwuiwa, wuf ta mike tsaye, kai tsaye kofa ta nufa, babu kowa a falon, hakan ya bata damar zarar mukullin kofarta wanda ana iya amfani da shi wajen bude kofar dakin Baraka inda ya zama na Ummi a yanzun. Ta bude dakin ta shiga gami da sakayawa yanda ba za’a gane ba, dakin a gyare tsaf don duk bayan kwana uku sai Binta ta gyarashi, ta hau rarraba idanu har Allah Ya taimaketa ta hango jakar Islamiyyar Ummi rataye a jikin wani dogon karfe na rataye kaya. Da sauri-sauri ta isa wajen ta janyo jakar ta soma bincikawa, ba ta ci wuyar ganin hoton da ta ke nema ba, ta kurawa hoton Gidado ido hawaye suka zubo a kuncinta, shine saurayin da a iyakar tsawon rayuwarta bata ta6a ganinsa ba sai a hoto, ba kuma ta ta6a son wani ba kamar yanda ta ke sonshi, da sauri ta dubi kofa sannan ta shiga maida litattafan Ummin cikin jaka gudun kada wani ya zo ya isketa, ta sanya hoton cikin rigarta ta fito ta maida kofar ta rufe. Shigarta dakinta nan ma hoton ta yi ta kallo tana murmushi, bata ta6a zaton zata so wani namiji haka ba, kuma wai dan kauye. “Ba kauye ba, ko cikin daji ka ke rayuwa zan iya binka Hubbyna, bansan sunanka ba na kamu da sonka, ban ta6a ganinka ba ido da ido, amman na ganka a mafarki fin sau uku har dariya ka yimin. I so much love you.” Ta rungume hoton, ranar kam kowa ya ga chanji a tattare da ita don ta yi wuni na dadin rai, babban burinta yanzu bai wuce na son ganin zuwan su Ummi Abuja ba ko Allah zai taimaketa da ganin sanyin idaniyarta. Mami na dakin Hajiya zaune suna hira da yan uwanta, wayarta ta yi k’ara, kai tsaye ta daga da sauri ganin Hajiya Binta abokiyar zamanta. Suka gaisa a mutunce suka sha hira tana tambayar mutanen Abuja sannan sukayi sallama, sai kuma ga kiran mijinta. Labarin da ya zo mata da shi yasa jikinta wani mugun sanyi, banda ikon Allah kenan babu abinda ta ke ambata a fili hakan yasa su Hajiya Mama da Hajiya Babba harma da Hajiya Karima (cousin) dinsu ta Adamawa suka zubomata idanu. Bayan ajiye wayar ta dubesu. “Kun ji ikon Allah ko?” “Meyafaru?” Cewarsu har suna hada baki. Mami ta numfasa. “Ashe Alhaji Kabiru Jimeta uba ne wajen Ummi? Dan uwan mahaifiyar Ummin ce.” Mamaki ya cika kowannensu banda Hajiya Karima da batasan kan zancen ba saidai tasan Alhaji Kabirun. “Lallai fa ikon Allah!” Cewar Hajiya Mama. “Yanzu suka yi waya da Alhaji Kabirun ya ke sanarmishi, don su suna ma Gomben.” Murmushi Hajiya Babba da Hajiya Mama sukayi wannan karon, banda hamdala babu abinda kowannensu ke yi a zuci musamman Hajiya Mama da ke jin kamar ta yi ta kyakyata dariya ga yar uwarta. Ai kuwa ta kasa hadiyewa ta hau yinsa, Mami duk kunya ta isheta ta yi shiru kawai tana Umm. KANDALA”Allah Sarki rayuwa.” Shine kawai furucin da Hajiya Mama ta yi bayan kammala dariyarta. “Wai duk meyafaru ne?” Cewar Hajiya Karima. Hajiya Mama ta dubeta. “Ba zaki gane ba Karima, bari har mu je Gombe gobe za ki gane komai.” “Toh ganar dani mana.” Mami ta ta6e baki gami da mikewa. “Ina zuwa.” Ficewa ta yi tsabar ta rasa abin cewa, suka bita da kallo kawai. Hajiya Babba ta ce. “Ki share batun Sadiya, kinsan ita fa abin dariya ba ya mata kadan.” Hajiya Mama ta k’arawa darawa kawai. Hajiya Babba ta share maganar gami da sanyo maganar yanda zasu yi tsare-tsarensu. *** *** *** GOMBE+ Misalin bakwai na safe matan gidan suka tashi da aiki tuk’uru sakamakon bak’in da zasu yi daga Abuja masu kawo lefe da sauran kaya na al’ada. Wajen karfe goma sha daya ita kuwa Ummi tana dakin Abida tana gwada kayanta kaloli biyar da Mahaifinta ya dinkamata na fitar biki anan, kaya masu tsada wanda acewarsa tunda bai yi na daki ba to wannan bazai gagareshi ba. Dinki na zamani akayi mata wanda ya zauna d’abas a jikinya, daidai da Amina saida ya siyamata ankon da yan uwan Ummi mata na Gombe suka yi, abinka da aikin kudi telar washegari sukayi zata je kar6a don a ranar sauran kwana daya bikin. ABUJA Su kuwa mutanen Abuja mutane shida kawai suka tafi kai lefe, Hajiya Mama da Hajiya Karima suna ciki, sai kuwa Hajiya Hadiza da Hajiya Bahijja, kanne ga Gen. Ahmad Danzaki sai kuwa wata Yayarsu da cikon mutum daya daga Adamawa. Sauran jama’a kuwa da zasu halarci yini da budar kai sai washegari zasu iso cikinsu kuwa harda su Mami da su Jidda. Ikram ji ta yi kamar ta zuab ruwa a k’asa ta sha jin cewar zaaje Gombe daga can a taho da Amarya ayi na nan. Murnarta har mamaki ya bawa su Jidda balle kuma Ihsan wacce bata ta6a zaton hakan ba. Koda ta ga yanda Ikram ke rawar jikin hada kaya tun ma lokacin tafiyar baiyi ba ta gyada kai. “DAN ADAM kenan, yanzu ke ba abun ki tayani bakin ciki bane Ikram, ba abun ki tayani zubar da hawaye bane, ko labarin matsayin Ummi ga Abubakar mai iso ga kunnuwanki ba?” Ikram ta dubeta jiki a sanyaye. “To ya zamu yi Ihsan banda mu yi hakuri, komai fa na Allah ne, ba yanda zamu yi tunda haka Ya tsaro za ki auri dan uwan Ummi, ni ai ba zuwan farinciki zanyi ba, ba kyaso ki ga yanda zasuyi shagalinsu ba?” Ihsan ta ja tsaki yayinda idanunta suka cika da ruwan hawaye, shikenan fa k’aryarta ta k’are, wani aji da jijji da kai yanzu saidai ta yiwa wata ba Ummi ba tunda dan uwanta zata aura, ita kam tasan ko giyar wake ta sha, ba zata tunkari Abbanta ta ce ta fasa auren Abubakar ba, sannan bayan wannan ma ga sonsa da ta ke ji a ranta. Sam, ba zata iya hakura da shi ba a yanzun, da ya ya ma ta soma sonsa da har za ta soma tunanin guje mishi? Ita kuwa babu Gomben da kafafunta zasu taka. ‘Ko ba ki je yanzu ba dole ki je a gaba tunda za ki auri dan Gomben.’ Cewar wani sashe na zuciyarta. *** *** *** Bayan Azhar su Hajiya Mama suka isa, alokacin Ummi suna dakin Abida suna faman kwasar hira, Mariya wacce itama Malam Balarabe bai jima da daukota daga gidan kakanninta ba saboda bikin ta shigo a guje da yaran gidan. “Adda Ummi, Adda Ummi!” Haka ta ke fad’a kamar yanda ta ji sauran yaran gidan na fadawa Ummin. Ta zube gabanta tana numfarfashi, yarinyar gaba daya ta chanja ta yi ki6a kamanninta da Saude na nan kamar an tsaga kara an karyashi. “Meyafaru?” Cewar Ummi wacce duk kiran ya rudar da ita. “An kawo lefenki.” Ta ja guntun tsaki tana tureta, su kuwa su Amina suka dara, nan suka ja mayafi suka nufi hanyar fita Amina na fadin. “Ah, bari muje na gaisa da mutan Abuja.” Gaba daya kowa ya tafi aka bar Ummi nan zaune ta yi shiru don gani ta ke kamar mafarki ta ke yi, wai lefenta? Ta yi tsuru tana rarraba ido. Hajiya Mama ta kama baki ganin Amina lokacin da ta ke gaisheta. “Ke kam ai kin zama ‘yar gida shiyasa tunda ki ka kira ki ka ce kunzo lafiya ban k’ara ganin kiranki ba.” Akayi dariya, Amina ta hau sunkuyar da kai itama tana darawar. Masaukin da aka tanadarmusu(wato gidan da ke makwaftaka da wannan, wanda ya kasance na Aminin Malam, Manu kakan Ummi saidai ba wanda ke ciki sai kuwa bak’i da ake saukewa) nan aka kai kayansu, saida suka yi sallah sannan aka hau gaggaisawa daga nan suka ci abinci, nan kuma aka hau buda lefe, ita dai Ummi banda sautin bud’a babu abinda ta ke ji, kaya ne masu tsada aka sanyamata, akwatinta saiti cif, harma da wani daban na kayan lalle da na budar kai da sauransu, cikin suturu kuwa har da dinkakku. Ummi na faman zirga-zirga ta yi can ta koma nan ba zato ta ji Amina ta d’ane bayanta tana tsalle da dariya. A farko ta tsorata don har gabanta ya fadi saidai jin muryar yasa ta numfasawa. “Kai don Allah Anti.” Kafin ta kai ga juyowa ta ji Amina na kuka har da sheshsheka, da sauri ta juyo daman itama karfin hali ta ke yi kawai, nan suka hau kuka babu mai rarrashin wani. Kusan duk abu guda suke tunawa. Amina ta dubeta. “Ki godewa Allah Ummi, ki godemiShi, Ya so ki da rahmarSa, Ya baki matsayin da kudi ko karfinki bazai ba ki ba har abada. Na ta6a ce miki Yaya Faruk ya fi karfinki, matsayinki da na shi ya sha bamban, a wancan lokacin ina jiyemiki tsoron shiga wahalar rayuwa ne, shiga cikin wadanda suka fiki da komai. Ga shi da Allah Ya yi ke din matarsa ce, sai Ya maida komai ba komai ba, ma’ana tulin matsalolin da muke hange ba wasu matsaloli ba, shakka babu ayau na k’ara godewa Allah da naga lefenki, na kalli dama da haguna naga dangin Ummina cike a daki, Ummina ‘yar dangi ce! Allah Ya baku zaman lafiya da Yaya Faruk, Ya baku ikon rike juna bisa amana har abada.” Ummi ta kasa komai sai murmushi ga hawaye na zuba, Amina ta ja ta suka zauna ta hau share mata hawayen, kafin waninsu ya ce komai, wayar Ummi ta hau ringing, suka kai dubansu ga wayar sannan Amina ta dara. “Bari na koma wajensu Hajiya Mama, ki gyara fuskarki fa don nasan zasu buk’aci ganinki.” Daga haka ta fice, haka ya bata damar janyo wayar, gogannata ne kuwa. Dakyar ta iya dagawa, tana dagawa kuwa ta ji ya sakarmata gud’a a kunne, batasan sadda ta tuntsire da dariya ba sosai, shima yana tayata, saida suka yi mai isarsu sannan suka tsagaita. “Kai don Allah.” Ta fada a shagwa6ance, yanzu kam ta saba da Faruk ta saki jiki da shi. “Kai don Allah me? Ko ba Amaryar Faruk din bace?” Murmushi kawai ta yi. “Ina zuwa, kiran Daddy na shigowa, zan k’ara nemanki.” “Toh.” Ta fada sannan sukayi sallama, kafin ya k’ara kira su Abu da sauransu suka shigo tafiya da ita gaisawa da surukai. Haka suka sanya ta lullu6e fuskarta da mayafi sannan suka fita. Ba yanda ta iya dole saida sukaa budemata fuskarta, kowannensu ya yaba, to idan ma basu yaba din ba ya zasuyi tunda an riga da an daura? Hajiya Mama ita mamakin kyawun da Ummi ta k’ara kawai ta ke yi, ashe rashin samun hutu da gyara ne ya sanya ta koma gatanan? Bayan fitar su Ummi, matasan gidan suma suka shigo aka gaggaisa, Hajiya Mama bata yi mamakin ganin Abubakar ba tunda labari ya iso gareta, acewarta ma sai ko baa fada ba za’a ga kamannin Alhaji Kabiru da wasu cikin yan uwan Ummin. Anan ne kuma sauran abokaan tafiyarta suka ga mijin da Ihsan zata aura, sun yaba kwarai. Dangin Ummi suka hada su da(snacks) da kwalayen lemuka da suka yi musu aka kai masaukinsu aka ajiye. Washegari wajen daya da mintuna su Ikram su Mami aka iso, Mami ta dake matuk’a don yanzu jikinta ba karamin la’asar ya yi ba musamman ma ganin kawarta mahaifiya ga Abubakar, Hajiya Salma. A ranar ne kuma ake lalle.Tun zuwansu basu sanya Amaryar a idanu ba sai da aka soma biki.Ummi ta shirya cikin wata koriyar atamfa mai adon kaloli jiki, ta yi kyau matuk’a a wannan rana, filin taro sosai Abubakar ya kama, shi ya biya komai, abinka da aikin kudi, nan aka gyare wajen aka yi kwalliyar kumbo a gefe da gefe inda amarya zata zauna sai kuwa tuntun da aka aka sanya, da katon darduma inda akai kawayen amarya zasu zauna sai kujeru. Sai awajen taron Mami suka hadu da Amarya Ummi, Ikram tun zuwanta ta ke rarraba idanu na son ganin inda zata ga rabin rannata saidai bata ganshi ba. Wajen ya burgesu ainun, da ka gansu kaga zuri’ar Modibbo da ta Danzaki, sunyi kyau har sun gaji, suma dangin Ummi, sun cekare abinsu. Kowannensu da baiwar kyan da Allah Ya yi mishi bakake da fararensu. Amarya ta sha lik’i a wajen dangin mijinta hakanan suma danginta ba’a barsu a baya ba. Mami koda ta je lik’amata har saida ta rungumeta, wannan abu da ta yi yasa Hajiya Mama jin dadi matuka har batasan sadda ta hau lik’a musu kudi ba. Ummi har hawaye ta yi don dadi, shakka babu wannan ya nuna Mami ta sauko. Jidda kam su dai yan bin yarima asha kida ne, to me zasu ce tunda wacce suke ganin kusan ba’a kyauta mata ba itama ta sauko? Ina ga su ‘yan karan kada miya? Sai wajen Magriba suka tashi.+ Misalin karfe takwas da dare, Amarya ta kammala waya da Angonnata wanda sai gobe zasu iso da tawagarsa don budar kai, tana tare da yan uwanta ana hira da dariya, Ikram ta shigo da sallama. Duk suka dubeta suna masu amsawa, Ummi ta saki fuska saidai can kasan ranta gabanta ne ke dukan tara-tara to da me kuma ta zo mata? “Amaryata ki zo mijinki na kira.” Fuskar kowannensu da mamaki, sauran mamakinsu na zuwan ango, Amina da Ummi kuwa bayan haka harma da na sabuwar fuska da suka ga Ikram da shi wanda basu saba ganinta da shi ba akan lamura na Ummin, wato fuskarta a sake saidai idan ka nutsu za ka fahimci a kunyace ta ke dakewa kawai ta ke yi. To ya zata yi? Tunda tana son dan uwan Ummi ai dolenta ta sauko. “Wai Angon ne ya zo?” Cewar wata budurwa. Ikram ta dubeta tana ‘yar dariya. “Gani nan, ai nima miji ce tunda kanwar mijin ce.” Sukayi dariya gaba daya har Ummi, ta saci kallon Amina, Amina ta yi mata alama da ta je. Ta mike ta bi bayanta, anan kofar dakin suka tsaya. Ikram ta ga shirun ba zai amfaneta ba ta yi magana cikin sanyin murya. “Don Allah Ummi ki yafemin abubuwan da na yi…” Sai kuma ta ji kunya, hakan yasa ta yin shiru. ‘Rayuwa kenan.” Cewar Ummi a zuciyarta. A fili fad’ad’a fara’arta ta yi don dagaske ta ji dadi kamar ta shid’e. Hannunta ta riko. “Kai haba, ni ban rike ki da komai ba, daman nafi daukar hakan a rashin fahimta, na yafemiki duniya da lahira nima don Allah ki yafemin.” Dariya ta yi ta dafa kafadarta. “Nagode Ummi.” Ummi ta ja hannunta. “Zo muje kiga yan uwana.” Daman haka ta ke so, ta bi bayanta suka koma ciki. Zama sukayi ana hirar tare, yawanci duk Ummi suke koyawa yanda ake kula da miji ita kam shiru ta yi don ta ga su babu ruwansu, Ikram dinma da ta ke kunyar ita dinma ta biyemusu. Sallamar Gidado ce ta katsesu, suka amsa, yana daga kofa yana dubansu, sanye ya ke da shadda ruwan toka babu hula akansa, gashinsa ya yi luf-luf. “Me ake tattaunawa ne aka manta da kawomin furata?” Cewarsa yana duban Matarsa Hafsa dake aikin dama mishi fura, ita kuwa baiwar Allah Ikram tun shigowarsa ta daskare a wajen gami da k’ura mishi idanu. Shi kam sau daya ya kalleta kallo na ganin bak’uwar fuska daga nan bai k’ara dubanta ba. Hafsa ta bishi da murmushi. “Na gama yanzu zan kawo.” “To saiki hanzarta, kinzo kin biyemusu kun samin kanwa a gaba kuna cikata da surutu ko?” Aka dara, Ikram murmushin yak’e ta yi gabanta na bugu da sauri-sauri jin wai Gidado na da mata, ta dubi matarsa, babu laifi bata daga sahun munana amma a diri na halittar jiki ba zata nunamata ba, babu gaba balle baya. Ta kara satar kallonsa. Ta ko’ina ya kere matarsa saidai ta kula kallon ma da ya ke jifar matartasa da shi wacce ta ji a dazun sun ambata da Hafsa, kallo ne na musamman mai nuni da tsantsar so da kauna. Ta sauke ajiyar zuciya yayinda ta ke ji kamar ta dora hannu aka ta hau rusa ihun kuka. “Kai Yaya Gidado, ba kunyar idanu irin wannan kallon?” Cewar wata Maimuna abokiyar wasansa, ya kai mata duka ta kauce. “Kefa kin raina ni yarinyarnan, kinga taso ki ji zan dan fita ne da Abubakar.” Ba musu Hafsa ta mike ta bi bayan mijinta, su kuwa yan dakin aka sanya dariya banda Ikram. Duk zaman ya gundureta, ji ta ke kamar ta bar wajen, ai kuwa da sauri ta mike. “Bari na tafi na kwanta na gaji.” Ta yi maganar a sanyaye tana duban Ummi, Ummi bata kawo komai ba bayan rashin sabo don kuwa ita kanta bata sake da ita ba ganin abin ta ke banbarakwai wai namiji da suna HAJARA. A nan soron gidan ta yi kici6us da Gidado da Hafsa, ya wani kankance murya yana magana kamar saurayi gaban budurwa, suka dubi juna ya jefeta da murmushi. “Sannu da bakunta.” Ya bata haushi saidai ta danne. “Yauwa.” Ta amsa a dakile kafin ta wuce da saurinta zuwa wajen yan uwanta. Koda ta shiga su Jidda ke kwasar hira akan yan uwan Ummi kowacce na tofa albarkacin bakinta, sam basu dauka zasu gansu kai a waye ba, sun yi zaton kauyen da zasu je yafi haka muni sai kuma abin ya basu mamaki ganin komai tsaf. “Ke kuma daga ina?” Cewar Baraka. Ta yamutse fuska. “Wajen matar Yaya mana.” Mamaki yasa su sakin baki kafin su hau dariya. “Shishshigi ko?” Cewar Fadila. Ta daure fuska gami da kwanciya saman katifa ta basu baya. “Ba ruwan mutum.” Suka shareta. Wannan daren har hawaye ta zubar na tausayawa kanta haka kuma bata ji komai na digon son Gidado ya ragu a zuciyarta ba…! WASHEGARI BUDAR KAI….! Karfe biyu Ango ya iso da tawagarsa saidai a Otal suka sauka….!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *