AMAREN BANA CHAPTER 6

AMAREN BANA CHAPTER 6

AMAREN BANA CHAPTER 7 Suna gama jarabawar, ranar ta yi tunanin ta wuce gidan Radiyya ta dubota, don tunda suka je farkon auren ita da Yaya Fawzaan, ba ta sake zuwa ba, yanzu ko watan su uku da aure. Kuka ta samu tana ta risga sharbe-sharbe!+ Gaba daya ta fita hayyacinta, ta yi fici-fici da ita, hankalin Rumaysah ya yi mummunar tashi. Da sauri ta isa gareta. Handkerchief dinta ta fitar ta shimfida kan Tiles din Varendar da Radiyya ke zaune. “Sis, lafiya na ganki a nan ki na irin wannan kukan? Me ya faru? Deeni ne ya mutu?” Nan da nan ta kara sautin kukan nata, tana buga kafa cikin gunji ta-ce. “Muguwa, Ba shi bane ya mutu”.4 Cikin tashin hankali Rumaysah ta zare idanu ta-ce. “Yau kin shiga uku, to me ya faru ki ke wannan irin kukan, kin kashe auren ki ne?” “Da Deeni da aurena duka da ransu, ba wanda ya mutu.” “Kin ga yadda ki ke risgar kuka kuwa, ki ka yi fici-fici da ke, dube ki fa?” Da kyar Rumaysah ta samu ta fada mata. “Ba tun safe bane babu wuta, kuma ga shi zafi ya dameni, sannan ban iya tada Generator din ba. Deeni kuma ya ce sai maghriba zai dawo gida?”16 Rumaysah idanunta ta juya cikin takaici, sannan ta rike hannun ‘yar-uwarta. “To shi ne kawai damuwar? Ba sai ki sa Deeni ya koya miki ba, idan ya dawo, tashi mu shiga ciki”. Da kyar ta yarda ta bi-ta, suka koma cikin gidan, kan (3-Seater), ta yi zamanta, yayin da Rumaysah ta wuce kitchen, tana duba fridge. “Sis, ba ki da abinci ne a kicin dinki?” Daga kwance Radiyya ta-ce. “Babu. Ban yi ba tukun”. “Ko sauran Breakfast babu?” Nan ne Rumaysah ta-ci karo da wani Plate din (Sliced Bread) akan fridge an shafa masa Butter har ya fara fusa, ba a ci ba. Yuck! Da sauri ta sake bredin. Juyawan da za ta yi ne, ta sake wani irin ihu, sai da Radiyya ta antayo da gudu zuwa kicin din. “Sis, ba ki da lafiya ne?” “Ni ce ban da lafiya ko ke? Kin ji ihun da ki ka sa? Me ya faru?” Rumaysah ta dubi kan Cupboard da cikin Sink, ta ga kwanuka suna shirin yin ambaliya. Kai har da tukwane uku a kasan kicin din an jikasu. “Tunda ki ka zo gidan nan, kin taba yin wanke-wanke kuwa?” Radiyya ta sauke ajiyar zuciya. “Har kin ban tsoro, na dauka wani abu ne, au wannan na shakaranjiya waccan ne da shekaranjiya da jiya da na yau da safe.”5 Rumaysah ta fiddo idanu ta na kallon yarta. “Kin shiga uku, haka ki ke kazanta? dubeki ko wanka ba ki yi ba, ta yaya Deeni zai rinka zama a gida?”4 “Bar masa na ke yi, idan ya gaji da gani ya wanke, wanda zai yi amfani da shi, ya dauka.” Rumaysa ta kwance dan-kwalinta ta dubi kwanukan nan ta shiga jika wanda suka soma fusa da ruwan dumi, ta zuba (Liquid Soap) a ciki, ta ware sauran, sannan ta-ce. “Oya, sako Slippers, wanke-wanke za mu yi.”4 STORY CONTINUES BELOW “Gaskiya ni dai dauraya zan yi.” Kallonta kawai Rumaysah ta yi, sannan ta toshe hancinta da dan-kwalinta, suka shiga aiki, sun fi awa suna wanke-wanken. Ta goge mata kicin, suna komawa falo. Ta dauko tsintsiya. Radiyya ta zaro idanu. “Ba dai shara za ki yi ba?” “Shara zan yi ko shara za mu yi? Ki je ki dauko wata tsintsiyar dai ki kamo daga can (Dining Section).” Suna turo sharar ne himili guda. Rumaysah ta-ce. “Anya tunda ki ka zo kin taba amfani da tsintsiyarki? Wata uku da aure, amma gidanki datti ya yi kamar wata biyar ba ayi shara ba?” Sun yi awa uku suna kalelaye gidan. Rumaysah ta bunka mata turaren wuta, nan da nan gidan ya koma kamshin gidan AMAREN BANA, saboda ya sha gyara.4 “Wallahi zan fadawa Abba ya zo ya ga yadda ya yi asarar kudin kayan daki, duk kin fara lalata naki.” Ta jibgu kan kujera. “Wallah, a samo min abin jika makoshi, kin ji na yadda makogwarona ya bushe, ga yunwa ga aiki?” Radiyya ta tura baki, sannan ta wuce kicin tana fadin bayanta ke mata azabar ciwo. Bayan minti talatin, sai ga ta ta fito da tire ta ajiyewa Rumaysah, ta koma ta dauko wani a Plate an kifa wani Plate din a kai. “Ki na so ki ce min ni kadai zan cinye wannan, ko me, ina zan kai shi?” “A’ah tare za mu ci” Ta fada hade da dauko masu drinks da ruwa a fridge. “To wancan fa da ki ka sa a Plate?” “Wannan, na Deeni ne.” Rumaysah sai da ta kusa kwarewa da ruwa. “Ban gane na Deeni ba, yaya za ki dafa taliya tun yanzu ki sa a Plate ke da ki ka ce sai Six zai dawo? Haka ki ke masa?”7 Radiyya ta bata fuska ta-ce. “To da yaya zan yi masa?” Rumaysah ta kasa yarda Radiyya yayarta ce, anya ba coge akai mata ba aka ce Radiyya ce babba a kanta?2 “Ba ki da Warmers ne?” “Tab! Yadda na sha wanke-wanken nan, wasu Warmers zan bata? Ai ni da wanke-wanke sai jibi, kin ga idan Plates ne, ba zai cika Sink din da wuri ba.”4 Shiru kawai Rumaysah ta yi, ta kai lomar taliyar da aka yi ta fara sol! Babu ko kwayar hanta bare aje ga Peas da su Carrots. Da sauri ta tofar, don da ta zaci a ido ne bai yi kyau ba, amma tana afawa a baki, ta ji kaf! Daya. “Wallahi ki kwashe abincin ki, don kuwa bai yi dadi ba, gaskiya ya kamata ki cewa Deeni ya saki a (Culinary School) makarantar koyon girki, ki koyi girki, don wataran za ki kashe shi, za ki ba ku guba, ga kazanta, ga rashin iya girki?” Radiyya ta bude baki ta-ce. “Kin ga shi ya sa ba na son ki rinka zuwa gidan nan, kin faye kakale da surutu.” Kai tsaye ta wuce kicin da tiren ta juye abincin a Dustbin. “Ki sake dafa wani, wannan ba dadi.” “Wallahi, fita ki bar min gida, ke ma sai na zo gidan ki, na ga me ki ke yi.” Rumaysah ta yi murmushi ta-ce. “Ke ma kin san ai ni kam ba daga nan ba.” Baram-baram! Suka yi da Radiyya, sannan ta koma gidanta, tana zuwa Estate din gidanta ta nufa kai tsaye, ai ko ta ji shi a garkame, bai dawo ba. Haushi ne ya kamata, kai tsaye gidan makwabciyarta Anty Safiyya ta shiga. “Anty don Allah ki na da abinci, yunwa na ke ji kamar me, kuma Yaya Fawzaan bai dawo ba, ni kuma na manta key dina a ciki, sai da na isa makaranta na tuna.” Ai kuwa nan da nan ta shiga ta kawo mata lafiyayyar shinkafa da miya da ta ji naman kaza, sai dafaffen Dankali a kai da Salad. Haka Rumaysah ta soma ci hannu baka, hannu kwarya. Anty Safiyya na son mata magana ne, amma ta yi shiru, sai da ta gama tas! Tukun, ta daga kwanon. “Me zai hana to mu shiga ki dan dafa masa wani abu, tunda ba key kar ya dawo da yunwa?” STORY CONTINUES BELOW “Bar shi kawai zai ci a can, tunda ko na yi, ba cin nawa yake yi ba.” Ta fada hade da kai kwanukan kicin, sai da ta dawo ne. Anty Safiyya ta-ce. “Al’amarinki da Yaya Fawzaan na ba ni mamaki fa, wai to idan ku ku na fada, ta yaya za ayi ku shirya, iyayen na ku su daidaita?” “Hmm! Ki na ganin iya kokarina ina yi akan wannan al’amari, musamman na ke ware lokaci, don ganin na kula da al’amuransa, duk da makarantata, haka zan zage nai masa abinci ko kallo baya isan sa, idan kuwa fannin kwalliya ne. Ke ma kin sanni ba daga nan ba, amma yadda ki ka san wani dutse ko a jikinsa. Shi ya sa ni ma na fara gajiya, na bar shi ya yi yadda yake so, kowa ma ya yi zamansa.” “Anya ayi haka kuwa? Dole dai a samu wata dabarar, na ga alama sonshi yana wahalar min da ‘yar kanwa.” “Wannan kam kuma tsohon tasha kenan, ai ba a ma zancen ya so-ni, tunda bai ma damu da ni ba, yanzu ma ina ga ya kusa daura aurensa, don ranar na ji Aasim kaninsa na cewa anyi masa tambayar matar son sa.” “Ke haba, dama maganar da ki ke fada min da gaske ne?” Hawaye kawai Rumaysah ta shiga yi. “Ni na riga na hakura tuntuni, domin ba zai taba so na ba.” “Ai kuwa ke mai shiga rai ce, karya yake yi ya-ce tsawon watannin ku biyar da aure ko kadan bai ji kin kwanta masa a rai ba, hala ma yana son ki miskilanci yake gwada miki. Share hawayenki, yanzu kam sai dai mu bawa Barrister kuka ba dai ya ba mu ba.”4 Dariya Rumaysah ta yi a tsakiyar kukanta ta-ce. “Tabdi! Da anyi gurguwar soyayya kuwa a nan. Mutumin da zance miki zan iya kirga sau nawa muka zauna muka yi magana da sunan hira a cikin gidan mu, ai kin ga ba zancen soyayya. Kwata-kwata baya ma nuna Efforts ko wani yunkuri na ya bada hadin kansa. Ni dai don tsakanina da Allah na ke zaune da shi, idan ba haka ba, an fada miki da ban dade da komawa gidan Abba na bane? Momi fa wata biyu ta dauka ba ta min magana, duk don saboda shi, amma ko a jikinsa, tun ina dagewa, ina surfa masa nawa, idan yai min har na hakura, sai idanu. Gaishe da Momi ma sai da na tursasa masa, sannan ya taba sau daya, idan banda tsantsar kiyayya meye wannan? Tunda mahaifiyata ma bai ba ta daraja ba bare ni.” Anty Safiyya ta jinjina zancen, sannan ta-ce. “Ki kara masa lokaci kadan ki gani, ko auren ma ya-ce zai yi, ki daure ki zuba masa idanu, idan ya ga ya samu abin da yake so, hankalinsa zai kwanta, nan ne zai fara ganin kokarinki, kiyi shirunki, mu ma za mu bullo masa da namu salon.” “Na gode Anty Safiyya. Allah ya bar mana ke. Ya barki da Baban su Fadila HAR GABAN ABADA!2 Anty Safiyya ta yi dariya ta-ce. “Wai wannan addu’a haka, lallai sai mu dage da wuri tun kafin Yaya Fawzaan ya nakasa mana zuciya.” Ana kiran sallar maghriba Fawzaan ya dawo, bai shigo gidan ba, sai da ya yi sallah tukun, a kofar gidan ya sameta, ta hada kai da gwiwa, ko uffan bai ce mata ba, ya sa key ya yi shigewarsa Ranta ya kara baci matuka, akan me ya sa bayan ta fada masa ta manta key dinta a gida, sannan zai dade bai dawo ba. Wanka ta yi, sannan ta mike a saman kujera tana buga (Game). Koda ya sauko sallar Issha ya wuce, haka ya je ya dawo, ya sameta ba ta motsa ba. “Ke tashi ki je ki yi sallah, idan kin rike wayar nan, kamar wata mayya.” Kallonsa kawai take yi kamar ba ta san yana yi ba. Ta ki ta amsa masa bare ta mike. “Ba da ke na ke magana bane?” “Ina tsammanin dai a iya karatunka, ya kamata ka san akwai lokutan da mata suke fashin sallah, ko ka manta wannan?” STORY CONTINUES BELOW Bai sake ce mata komai ba, ya zauna ya duba wayarsa, ya samu sakwanni, don haka ya fara maida amsa. Lokaci-lokaci yana duban bangaren da take zaune, tunani ne ya cika masa zuciya game da ita, haka nan hankalinsa a tashe yake, gaba daya tun jiya da yamma ya shiga wannan rudanin. Ya kuma rasa yadda zai fara fada mata zancen. Amma dole ya fada mata ko za ta taimake shi, ta fidda shi cikin rudaninsa, tausayinta ya fi damunsa fiye da komai. “Rumaysah, ina da magana dake.” Ya fada daga karshe, don haka ta zauna ta ajiye wayar hannunta. Ta sani ai yau zai mata maganar aurensa. Daurewa ta yi ta-ce. “Ina sauraronka.” Nuna gefensa ya yi ya-ce. “Zauna a nan.” A darare ta isa ta zauna, zuciyarta kuwa sai bugawa take yi, saboda sai take ji dama ya yi hakuri kar ya fada mata, nan da nan ta shiga jin wani balli-balli yana taso mata a kirji, ko ya-ce ya fasa, ko kuwa ya-ce ya gane yana sonta, koma dai wani abu daban, ba zancen auren Meena ba. “Kin yarda da ni Rumaysah?” Idanunta tuni sun cikoda hawaye. “Yaya Fawzaan wace irin tambaya ce wannan? Kwarai kuwa na yarda da kai mana.” “Da kyau, tunda kin amince da hakan, ina so na fada miki lokaci ya yi da za ki ajiye alkawarin da ki ka yi na zama da ni har karshen rayuwarmu.” Nan da nan ta shiga raba idanu. “Ban gane ba?” “Rumaysah lokacin rabuwarmu ta zo.” Wani dif! Ta ji, rayuwarta ne ta ji ta tsaya cak! Hankalinta ya yi masifar tashi, sai ta ji kamar tana shidewa. Da kyar ta tattaro sauran numfashinta ta-ce. “Yaya Fawzan… Wani abu nayi maka?” “Ki kwantar da hankalinki, ba ki min komai ba, kawai dai lokacin ne ya zo.”4 “To ni kuma zan fada maka, sai dai ka yi hakuri, domin haka kawai ba ka da dalili, ba zan rabu da kai ba, alhali na fada maka auren mu, sai dai randa dayan mu ya fadi ya mutu. Amma idan banda haka, ba inda zan je.” “Dole ki yi hakuri da wannan kudurin, domin ko na so zama dake, ya zamo lallai mu hakura.” Mikewa ta yi cikin zafin rai ta-ce. “Don za ka yi aure, za ka auri zabinka abin son ka, shi ne za ka min haka Yaya Fawzaan? Ni na san ba ka sona tun farkon auren mu, amma na zabi da mu zauna haka tare. Na gwammaci rayuwar haka, ni da kaina na amince, kai waye da za ka ce min za ka rabu da ni? Ba inda zan je, ka ma canja shawara.”4 Cikin tsawa ya-ce mata. “Dole ki tafi Rumaysah.” Shi din ma idanunsa hawaye ne suka cicciko. “Zan so ka maimaita kalamanka a gaban Baffa, ko kuwa Abbana da ya ba ka amanata ka amince za ka rike masa. Ni na ke zaune da kai, alhali ba ka damu da al’amarina ba. Ni na ke zaune da kai, alhali cikin dare ka na rikoni ka na kirana da sunan budurwarka, ni na ke zaune da kai, alhali na san bayan kai, ba zan iya kara wani auren ba, kuma ni na amince zan zauna da kai, don me za ka samu matsala? To ya aka yi lamarin har ya kai haka Yaya Fawzaan? Ko kuwa rashin ilimin addini laifi ne har haka? Ina tunanin komai ilimin Malami da saninsa, sai da ya nema ya samu. Kuma imani a zuciya take, na sauke kaina na amince, har na ke daukar karatu a wurinka, saboda na samu ilimin addini na, ka fada min dalili daya, da ya saka zamanka da ni, ya zama kunci a tare da kai? Shiru ya yi, bai ba ta amsa ba, don haka ta-ce. “Right, ni ma na yi tunanin hakan.” Ta sa kai ta wuce sama, ta bar Fawzaan da hannu biyu tallafe da kai. “Rumaysah dole ki ajiye taurin kanki da kafiya, ki koma gidan Abba, domin hakan ne kawai mafita a gareni da ke gaba daya.” Wani irin sarar kai ne, ya dirar mata da ta tuno kalaman Fawzaan, me ya sa zai mata haka rana tsaka, sai da ya bari ta saba da shi, zuciyarta ta so shi, sannan zai ce zai rabu da ita. STORY CONTINUES BELOW Me ya sa tun kan ta fara son sa, bai rabu da ita ba? Me ya sa? Kwana ta yi tana kuka. Don haka ciwon kai kam sai abinda ya yi gaba. Tana sallar asuba, ta sauko falo ta jira Yaya Fawzaan ya shigo. Gaishe shi ta yi, zai wuce ta-ce masa. ‘Yaya Fawzaan karatun mu?” Me ya sa take sa wannan al’amarin ya zamo masa mai wuya ne? Ya tambayi kansa. “Ba na jin dadi, sai wani lokacin.” “Ka na nufin sai na koma gidan Abba?” Ya dago ya dubeta, saboda ya san idan ta koma kam sun rabu har abada, sai dai wani ikon Allah. “Bude mu yi.” Ya fada hade da zama kan kujerar. Da gangan ta yi ta bata, saboda ya tsaya mata gyara, har su dade suna karatun. Zuciyarta cike fal! Da damuwa. Sai da suka gama ne, ta zo tashi kawai jiri ya kwasheta ta zube. A tsorace Fawzaan ya juyo gareta, ya tareta, fuskarta sharkaf! Da zufa ya rasa me zai yi da farko, sai kawai ya kwantar da ita akan doguwar kujera. Ruwa ya sa mata a fuska, sannan ya kira Abba ya fada masa Rumaysah ba lafiya, ga shi ma har ta suma. Ko me zai ba ta? Abba ya-ce ya yi saurin wucewa da ita asibiti. Cikin kankanin lokaci ya kimtsa, ya dagata ya sa a mota. Ko me ya sameta, har da suma? Ba dai maganar jiya bace, kai haba me zai sa har ta daga hankalinta haka? Suna isa suka samu Abba na jiransu a asibitin, da kansa ya tsaya aka dubata sosai. Abba kuwa yana tsoron ciwon da ta taba yi kwanaki ne ya taso. Don haka ya bukaci a mata wasu gwaje-gwaje. (National Hospital), suka tafi domin gwajin. Hankalinsa ya tashi, amma bai nuna masu ba. Kafin hantsi gaba daya gidan sun ji labari, kuma sun dungumo, domin dubiya. Kawai sai ga Momi da Mama a daki guda, ko qala Momi ba ta cewa Mama ba, don Mama na tambayar mai jiki ma, kamar ke da ba kya nan. Ran Fawzaan ya baci kwarai, amma ya danne. Fatan sa dai Allah ya bawa Rumaysah lafiya. Tana farfadowa, ta fara kukan ciwon kirji, take akai mata wata allura, a cikin karin ruwan da ake mata. Da dare Momi ce ta-ce za ta zauna a kan Rumaysah, sai da kowa ya watse, sannan Fawzaan ya tashi komawa gida. Momi ta duba ta ga Idanun Rumaysah a rufe, sannan ta-ce. “Ka dai fahimci abin da na fada maka, kuma ina so tun kan lokaci ya kure, na ga hakan.” Jikin Fawzaan a sanyaye ya-ce. “Insha-Allah.” Sannan ya juya ya bar dakin. Rumaysah kuwa ta jisu sama-sama, don haka ta shiga tunanin wace magana ce ta hada Momi da Fawazaan? Da har za tai masa kashedi? Nan take ta kudura a ranta za ta tambaye shi da safe. Kwankinta biyu a asibiti. Fawzaan yana kanta daga ya fito Break, sai ya je asibiti ya ganta, haka ana tashi a aiki, nan yake zuwa, sai barci ke kai shi gida. Amma sam Rumaysah ta kasa samun lokacin da za tayi masa tambayar abin da yake damunta. Sannan ko ganin rashin lafiyar da take yi ne, ba ta ji ya sake mata maganar rabuwa ba tukun. Hala ganin idon su Mama ne, yake sa shi hakan. Koda aka sallameta. Likitan ya-ce tana bukatar hutu sosai, ya dubi Fawzaan ya-ce. “Kar ta zamo Costumer din mu fa, sai mu rike ta gaba daya. Barrister ka kula da ita sosai.” Kasancewar duka asibitin sun san shi ne mijinta. Ai daga asibitin. Baffa ya-ce. “Ina ga Rumaysah na bukatar hutu, saboda haka ta dawo gida ta dan samu hutu tukuna. Don haka Muneera da Fawzaan suka koma gida, suka hado mata abinda za ta bukata. Momi ko tana jira ta ga Rumaysah ta dawo gidanta, sai ta ji shiru, ashe gidan Baffa ta sauka. Abin ya sosa mata rai, amma ta danne, saboda na lokaci kalilan ne. Daki musamman Mama ta shirya mata. Da dare Fawzaan ya shigo dakin, a bakin gadonta ya zauna tana kwance, saboda rashin karfin jikin da take fama da shi. Hawaye ne a gefen idanunta. “Yaya jikin naki?” Ya fada yana taba goshinta. STORY CONTINUES BELOW “Da sauki, sai abinda ba za a rasa ba.” “Allah ya karo miki lafiya.” A sanyaye ta amsa da ameen. “Abba ya fada maka abin da yake damuna? Ya ki ya fada min.” Murmushi ya yi, sannan ya-ce. “Ba komai, Stress ne da kin samu hutu, za ki koma kamar da, kar ki damu, kin ji?” Ta san da kyar idan duka gaskiyar Yaya Fawzaan ya fada mata. Ya mike zai tafi ne, ya ji ta rike masa hannu, don haka ya riko nata a hankali, sannan ya koma ya zauna. “Har yau ba ka fada min dalilinka ba na rabuwa da ni, ko kuma dai wayo ka ke son min, daga kawoni jinya, ka gudu ka bar ni?” Zuciyarsa ya ji ta masa nauyi, kwarai yake tausayin Rumaysah. Karfin hali ya yi ya-ce mata. “Ke dai ki samu lafiya, sai mu yi maganar.” Yana fita a dakin, ya share kwallar dake makale a idanunsa. Mamaki ne kwarai ya kama shi, da ya samu wayar Momi ta kuma bukaci ganinsa idan ya taso a aiki, wannan ya sa kai tsaye ranar daga ofis ya wuce gidan Abba, har falonta na kasa ta-ce a isar da shi. Bayan sun gaisa ne, ta-ce masa. “Fawzaan, na san ka ji mamakin nemanka da na yi.” Tabbas ya yi mamaki, amma tunda ga shi nan, koma menene dalili, yana dab da sani. “Ba komai bane ya sa na kiraka, illa na fada maka cewa lokacin rabuwarka da ‘yata Rumaysah ya zo.” A razane ya dubeta, wace irin magana ce wannan? “Ka kwana da sanin cewa da kai da mahaifiyarka duka ba kwa cikin tsarin mutanen da zan so bare kuma wani nawa ya so. Sogiji ta yi nasarar raba ni da ‘yata a karo na farko, ban san da me ta yi amfani ba, ko tsafi tai mata ma dai ya rage nata, domin ni bai kamani ba, idanuna a bude suke.”4 Ran Fawzaan ya yi mummunar baci, jin irin sharrin da take yiwa mahaifiyarsa, ta-ci albarkacin shekarunta da kuma auren ‘yarta da yake yi, idan ba haka ba da tuni ya wanke ta da mari. “Saboda haka na ke son na fada maka, idan har Rumaysah na da wata kima ko ka damu da ita, komai kankantar damuwar ya kamata ka san yadda muhimmancina a rayuwarta take, yau din nan na ke so ka sallami ‘yata ka saketa. Kuma kai mata sakin da ba mahalukin da ya isa ya mayar da auren ku. Idan kuma ba haka ba, na yi maka alkawarin da kai da ita za ku dauki gawata, domin zan kashe kaina muddin ta ci-gaba da zama da kai.”15 Hankalin Fawzaan ya yi mummunar tashi, wace irin uwa ce za ta so illata rayuwar ‘yarta, wace irin uwa ce za ta kashe auren ‘yarta ba tare da wani dalili na hankali ba? Tabbas tausayin Rumaysah ya kama shi matuka, yana tausayinta da ta kasance ta fito ta tsatson Momi, yana tausayinta na rashin dacen uwa ta-gari da ta yi.2 A daidai wannan lokacin ne ya fuskanci ba zai iya rabuwa da Rumaysah ba, ba zai iya rabuwa da ita ba, saboda dalilai da dama. Amma kuma idan Momi ta ida manufarta fa? “Ka yi shiru ka na jina, ina jiran na gani a aikace, idan kuma ka kuskura ka fadawa kowa abin da na sa ka, kafin ka aiwatar, dukkan mu kowa zai yi asara.” Jikinsa a sanyaye ya koma gida, tun daren yake kallon Rumaysah da nufin fada mata abin da ake ciki, sai ya yi tunanin rabuwa da itan kawai, shi ya fi alkhairi. Shi ya sa ya sanar da ita manufarsa, to ga shi dalilin maganar da ya fada mata, ya haddasa mata larura a zuciyarta.4 Yaya zai yi da rayuwarsa? A bangare guda ya san ba karamin kuskure zai yi ba, idan ya rabu da Rumaysah. Ba a ta batun hankulan da za su tashi cikin zuri’arsu. Baffa ya dauki amana ya damka masa, idan ya yi fatali da hakan, shin Baffa zai kara amince masa kenan? Kwanaki biyu ta yi a gidan Baffa. Abba ko ya tusa Momi a gaba akan lallai sai su je su dubo jikinta. Haka suka tafi ranta bai mata dadi ba, sai dai ta samu Rumaysah cikin kyawun yanayi, ga shi Mama na kula da ita sosai, don a gefenta ma suka sameta. STORY CONTINUES BELOW Ta balli magani tana ba ta. Duk Likita ne ya jawo mata da bai bari ta yi jinyar diyarta ba? Kamar a kan wuta take zaune, haka take jin ta, da kyar ta gama gaisuwar, don dai diyarta ke kwance, idan banda haka, me zai shigo da ita nan gidan? Washegari Fawzaan ya zo ya samu Mama. “Rumaysah ta shirya da yamma, sai mu koma gida.” “To har ta wartsaken kenan?” “Ai ina ga yanzu kam ta samu karfin jikinta.” “To shi kenan, ka sameta a ciki ka fada mata. Amma don Allah zauna nan, ina fatan ba kuntatawa ‘yar mutane ka ke yi ba Fawzaan. Zuciyata ta kan yabe ka ta-ce ba za ka iya wulakanta Dan-Adam ba, amma daya zuciyar sai ta gargade ni da shaidar dan yau.” “Ko kadan Mama.” “To ya yi kyau, don kar ka kuskura na sameka da laifin batawa Rumaysa’u, ka ga irin ciwonta, idan ka kuskura ka zamo sanadin shiganta kunci, za mu bata da kai, domin kuwa za ka ga bacin raina.” Kan Fawzaan na kasa, ya gama jin maaganar Mama, sannan ya shiga ciki. Ta idar da sallar azahar ya sameta, ya fada mata akan ta shirya. Da dare za su koma. Kai kawai ta daga masa ta ci-gaba da Ma’athuraat dinta, da ya ga ba ta da niyyar cewa komai ne, ya mike ya bar dakin. Har an sa jakarta a mota. Rumaysah ta ja ta tsaya. Fawzaan ya dubeta ya-ce. “Za ki ci-gaba da tsayuwa a can ne, duk tsawon daren nan ko kuwa za mu tafi?” Rumaysah ta-ce. “Yaya Fawzaan ni fa ba zan bi-ka ba.” Fawzaan ya dubeta a rikice, ya matso kusa da ita, ya yi kasa da murya sannan ya-ce. “Rumaysah, shin kin manta da alkawuran da ki ka dauka ne a ranar auren mu?” Ajiyar zuciya ta yi ta-ce. “Ban manta ba sam, amma ina son na san dalilinka da zai sa ka ce na koma, bayan kai ka ce ka gaji da ni, ka na so mu rabu. Ko kuwa ka canja ra’ayinka game da ni ne? Shin ka damu da al’amarina, ko kuwa abin da ka ke ji game da ni ne ya canza yanzu?” Fawzaan ya kara matsawa daf da ita, ya tsaya yana kallon fuskarta, cikin idanunta. “Jiki na yana ba ni, akwai dimbin alkhairan da za su biyo baya, idan har ki ka koma gidana, saboda haka don Allah ki yi hakuri, ki zo mu tafi. Za mu iya haduwa mu yaki abinda yake shiga tsakanin mu, amma ba za mu iya gujewa juna ba, don haka kar ki gujeni Rumaysah. Idan ki ka zauna, labarin mu a nan zai tsaya, ni kuma ina son ganin cikakken labarin” “Yaya Fawzan idan na zauna, labarin mu zai sauya, kuma ina ga hakan ya faye mana gaba daya za mu kasance cikin farin-ciki.” “Rumaysah za ki zo mu tafi ko ba za ki zo ba?” Ya fada har muryarsa kamar tana rawa. “Sai ka min alqawari.” “Ni ba zan maki alqawarin komai ba, koda na sonki ne kuwa, saboda rayuwa ba ta da tabbas.” Zuciyarta ne ta yi mata wani irin bugu, cikin rauni ta-ce. “To na ji, amma kai min alqawarin za ka daina min wulakanci, sannan za ka fada min dalilin ka na son rabuwar mu a karo na farko, da abinda ya canza maka ra’ayinka daga baya”. “Na ji, amma ba duka ba.” “Promise?” Ta mika masa hannunta na dama. “Promise.” Ya amshi hannunta yana murmushi, sannan suka shiga mota, suka koma gidansu. Mama ta sauke labulen falonta, bayan ta ga duk abin da yake faruwa daga falonta na sama, don ta tashi sauke labulaye, ta ga Rumaysah ta ja da baya. Za ta yi magana, sai kuma ta tsaya, don ganin me yake faruwa. Baffa ta samu da maganar. “Alhaji, anya ba za ka kira yaron nan ka ji daga bakinsa ba, don dai ni kam kullum idan na tambaye shi yanayin zaman su, sai ya ce min komai lafiya, amma sai na ga kamar ba haka bane. Watakila kai ya bude maka komai.” STORY CONTINUES BELOW “Ah, Sogiji banda abinki, tunda har ki ka tambaya ya-ce miki babu, ai babun ne, ai da da akwai da zai fada miki. Watakila ya ga zai iya maganin akwai din, kuma shi ya sa bai fadawa na gaba da shi ba.” “To Allah ya sa haka, amma cikin kwanakin ciwon yarinyar nan, sai na ke ga kamar da wani abin a tsakaninsu, shi ya sa na ga ya dace na fada maka. Idan kuma shi ba za ayi masa magana ba, ka sa ko Likita ne ya tuntubi Rumaysa’u mu ji, ka ga duk wani gyara tun da wuri ake yi, tun kafin abin ya dawo wata rigima.” “To tunda kin matsa, zan fadawa Umarun.” Yana fadin haka, sai ta ji dadi a ranta. Momi kuwa ranta ya baci da Raa’id ya shaida mata Rumaysah ta koma gidanta, wato Fawzan ya ma maidata mahaukaciya kenan, za ta fada masa magana, sannan ya yi fatali da ita ko? Dr. Umar ya gama jin bayanin Baffa, ya kuma yi masa alqawarin da kansa zai je ya ji koma menene. Sai da ya bari ya san zai samu Fawzaan a gida, sannan ya nufi gidan na su. Rumaysah ta ji dadin ganin Abban, a tunaninta ya zo duba jikinta ne kawai. Za ta kawo masa ruwa ne, ya-ce. “A’a zauna abin ki. Wata maganar ce ta kawo ni daban.” Don haka sai suka mayar da hankulansu kan zancen Abba. “Shin dayanku zai fada min abin da ke faruwa a tsakanin ku?” Nan take Fawzaan ya dubi Rumaysah, ita ma ta dube shi. Me Abba yake nufi? “Abba, abin da yake faruwa kuma? Babu komai fa”. “Ki min shiru, ke kadai na ke tambaya ne? Kullum idan an maku magana, sai ku ce babu, alhali ina sane da abinda ku ke boyewa. Fawzaan kai ne babba, babu wata matsala ka tabbata tsakaninka da Allah?” “Babu Abba, idan ma wani abin ya taso ma ai zan sameka a asibiti mu tattauna. Insha-Allahu ai ba za mu boye maka komai ba.” “To shi kenan, ya yi kyau. Allah ya ba ku zaman lafiya ya hada kawunanku. Baby yaya jikin naki?” “Da sauki Abba.” “To ki kula da lafiyarki sosai, ba na so ki na sa kanki a cikin damuwa, kin ji? Da zarar wani abu na damunki, ki fadawa mijinki ko ki sameni ko Baffa ki fada mana, kin ji ai?” “Na ji Abba. Insha-Allahu zan kiyaye.” “To ya yi kyau.” Nan dai Abba yai masu sallama ya wuce. Fawzaan na dawowa ciki ya-ce. “Kin fadawa Mama wani abu ne da ki ke gidan Baffa?” “A’a ni ban fada ba, ban san me ya sa Abba ya yi tunanin koda wani abin ba.” “To shi kenan.” Ba tare da wani bata lokaci ba Fawzaan ya bi Abba ya fada masa duk yadda suka yi da Momi. “Sannan Abba abin da ya sa ban fada a gaban Rumaysah ba, saboda yanayin ciwonta, na san za ta tada hankalinta.” “Lallai ka kyauta da ba ka fada mata ba, kwarai ka yi tunani. Kuma ina son ka zauna da hakan. Insha-Allahu zan yi maganin komai. Ka je ka ci-gaba da rike matarka tsakani da Allah, ka kara hakuri.” “Ba komai Abba, na gode.” Fawzaan ya fita ya bar Abba cikin rudani da tunanin mafita, dole dai duk yadda yake kin kai maganar nan wa Baban Gusau, dole sai ya sa baki a ciki. Don shi kam Allah ya gani ya gaji da dabi’ar Atika. Ga shi jiyan nan ya gama fama da Case din Khadija da Labeeb. Labeeb yana dawowa daga wurin aiki, ya samu Khadija a bakin gate za ta fita, don haka ya tsaya ya-ce. “Madam sai ina kuma? Bayan ki na ganin ina shigowa gida.” “Wallahi ina son na je na leka Momi ne, ya kwana biyu, ba mu hadu ba?” “Shi ne za ki yi tafiyar ki, ni kam ko oho, ban isa da ke ba kenan, to ki koma gida na hana fitar.” Sauka ta yi daga motar ta-ce. “Yaya za ka ce min na koma, ai dai gidan mu, ba za ka hanani zuwa ba, tunda ka hanani zuwa kasuwa.” “Duk inda na ga daman hanaki zuwa, ina da wannan right din, saboda na gaji da tsiyarki ta shegen yawo, marar amfani.” Ai yana fadan haka. Khadija ta sa masa kuka. “Yanzu Labeeb, Momin ce ba ta da amfani?” Kafin ya ba ta amsa, ta danna lambar Momi ta kirata. “Momi, Wallahi ni da Labeeb ne, ki na ganin wai don tsabar wulakanci, raba ni yake so ya yi da dangina, har ke fa, wai don Allah kar na zo na ganki. Kwana na nawa rabona dake?” Momi ta-ce. “Labeeb din ya hanaki zuwa gidan ubanki? A ina ya ganki, ya aura? Ba sai da muka haifa masa ke ba, ya gani ya-ce yana so? Ba shi wayar, ki gani.”4 Cikin kuka ta mikawa Labeeb wayar, ransa a bace ya karbi wayar, don a gabansa ta fadawa Momi komai. Ya fara gaida Momi. Ta katse shi. “Ka ba ni kunya Wallahi, ina daukar ka mutumin kirki, ashe haka ka ke? Yaya za ka raba yarinya da danginta? Ko ka dauka ba mu sonta muka dauka muka ba ka ita ne? Gaskiya ba na son haka. Ina laifi duk sati ka bar ta ko sau daya ta zo nan dai, ta ga gida, abu ana gari daya, amma sai shegen sa doka da takura? Ai sai ku gunduri juna, kullum ku na kulle tare.” Ta inda Momi take shiga, ba ta nan take fita ba. Kai karshe ma Labeeb bai jira sauran bayanin nata ba, ya kashe wayar, ya karasa gyara Parking a cikin Compound din na su. Har gate din ya dawo, ya mika mata wayar, ya-ce. “Ki je can ki zauna a cikin dangin naki, na gaji ba zan iya ba. Ni na ke auren ki, ko ke ki ke aurena?” “Labeeb!” Ta kwala masa kira, amma ya wuce cikin gidan a fusace. Maimakon ta koma ta ba shi hakuri, sai ta zabura ita ma ta figi motarta ta yi gidan Abba, nan ta fadawa Momi abin da ya-ce. “Shi kenan, mu muna sonki ai, sai ki zauna har Likita ya dawo, a san abin yi.”A daren Abba ya shigo ya samu wannan rikicin, sun kakkara akan wanda ya faru. Abba kuwa bai yanke hukunci ba. Baffa ya fadawa komai, da yake shi ne waliyin Khadija, aka nemo Labeeb. Ganin su Baffa ke neman sa, ya sa ya yi hakuri ya je. Nan ya zayyane masu tun daga farkon auren su, dramar da suke yi da ita kan fita yawon kasuwa da gidan kawaye, ko yana gari, ko baya gari. Wannan ba ta dauke shi a matsayin komai ba, fitarta take yi, ya sha mata magana.4 Amma ba ta canza ba, sannan caba masa magana take yi son ranta, ba tare da la’akarin shi mijinta bane. Kwarai sun ga kokarinsa ma kan wani abin da ya fada, nan ma ya rage masu tsaurin. “Tabbas, na ji dadin yadda ka fada mana komai, na kuma yaba da hakurinka, amma lallai Khadija ba ta kyauta ba.” Nan ya juya ya dubi inda Khadijan take zaune. “Ke yanzu ashe rashin mutuncin da ki ke yi a gidan mijin naki kenan? Magana za ki jawo mana, ko me? Don ma kin samu miji mai saukin kai da hakuri, ai da tuni kin tsufa a gida. Wannan shashanci ne da hauka. Kuma ba na son na sake jin koda wasa kin fita ko makwabta ne, ba tare da sanin mijinki ba. Ko Atika ce take jinya, ki ka kuskura ki ka fita, bai sani ba, to tsinuwa ki ke tarawa kanki, ki na kuma kwashewa kanki albarka. Domin duk halittun Ubangiji tsine miki suke yi, hatta kasar da ki ke takawa har ki je ki dawo.2 Kin ga dai Atika uwarki ce ko? To ko ita. Ba ki da labarin kissar matar da mijinta ya ya yi tafiya, bayan tafiyarsa ciwo ya kama mahaifinta, ta sanar da Manzon Allah (S.A.W) mahaifinta ba lafiya, kuma mijinta baya nan, za ta iya zuwa ta dubo shi? Manzon Allah ya ce ta yi hakuri, ta bari har sai mijinta ya dawo. Ta hakura ta zauna, bayan kwanaki aka aiko mata jikin mahaifin ya tsananta. Nan ma dai ta sake fadawa Manzon Allah (S.A.W). Ya sake ba ta amsa irin na baya, ta kara hakura. Haka iyayen nata ma ba su daga hankali ba, ganin ‘yar su ba ta zo dubiya ba. Tunda umarnin Manzo (S.A.W) ne, yana gaba da komai. A haka har Allah ya yiwa mahaifin nata rasuwa. Ta aikawa Manzon Allah, nan ma ya-ce ta yi hakuri, sai mijinta ya dawo. Ta hakura ba ta je ba, a wata ruwayar ma mahaifiyarta ta zo ta rasu, ba ta je ba. Ranar da mijinta ya dawo. Za ta je gaisuwar ita kuma sai Allah ya dauki ranta, a sanadiyyar wannan hakurin da ta yi, ta bi umarnin Manzon Allah. Allah ya gafartawa iyayenta da kuma ita kanta gaba ki daya.9 To ashe kuwa kin ga ba karamin laifi bane fita gararamba, ba izinin miji. Ko kuwa satar hanya ki fita da sunan zuwa wuri guda, sai kin bi gida goma, wannan duk ba daidai bane.” Khadija dai kanta a kasa, ai fadan da Baffa yai mata wasa ne, na Abba sai da ya doke nasa ya shanye, shi kam har da Momin ya hada ya surfe. Sannan suka bawa Labeeb hakuri akan ya koma da matarsa. STORY CONTINUES BELOW Yanzu kuma ga wannan zance da Fawzaan ya zo masa da shi. Sai da ya tabbatar da ya mika komai hannun manyan abokan aikinsa na asibiti, sannan ya dauki hanyar Gusau. Bai dawo Abuja ba, sai tare da Alhajin Momi, wato Baban Gusau, kowa ya yi mamakin ganinsa, ganin cewa sai abu ya yi tsamari ko wani abin ya taso yake zuwa Abuja. Momi kam na ganinsa, ta sha jinin jikinta, musamman da ta fahimci Likita ne ya taho da shi. Sai dai sam ba ta zaci zancen Fawzaan bane ya kawo shi.5 Da yamma bayan ya huta ne. Momi ta shigo falon Abba ta samesu, hira suke yi, amma suna ganin shigowarta, kowa ya zuba mata idanu. “Alhaji yaya gajiyar hanya? Ya ka baro su Hajiya?” Baban Gusau bai ko kalleta ba, bare ya amsa, don haka ta gyara zama akan kafet din, tana jiran jin laifinta. “Atika! Atika! Ki kiyayi rayuwa, ki kiyayi fushin Ubangiji a kanki. Yanzu ace ke koda yaushe ba ki da abin yi, sai ja da ikon Allah? Ke kullum kenan, ki na cikin aikata abin da zai bata rayukan jama’a? Kin san dai da na ce ba zan sake shiga maganar da ta shafe ki ba. To amma na ga abin naki ya wuce gona da iri, yanzu kuma bi ki ke yi ki na kashewa ‘ya’yanki aure? Sai ki tarasu ku zauna, a ina? Idan ke ma kin karasa naki igiyar auren? Na rasa ke wace irin mutum ce. Kin san kuwa girman gaba da Dan-uwanka musulmi a musulunci? Koda kwana uku ki ka yi, ki na gaba da mutum, ki ka ki yi masa magana, to sallar ki ma ba a karbarta. Yanzu ki fada min tsakaninki da Allah, shekaru nawa ki ka dauka ki na gaba da Hajiya Sogiji? So ki ke yi ke a tarihin zuri’a ta, ki fita daban? Kowa ya yi ta tofin Allah tsine dake. Ni dai na yi rayuwata cikin zaman lafiya da jama’a, kuma sunana ba zai baci ba, saboda rashin mutuncin da ki ke janyo mana. Yanzu me ya hada ki da mijin ‘yarki da har zai sa ki sa shi a gaba, ki tursasa masa rabuwa da matarsa. Wai idan ba haka ba, za ki kashe kanki? Ai da kin bar batawa kowa lokaci, kin kashe kan naki da ya fi wa kowa alkhairi, tunda ke ba ki iya zaman lafiya da mutane ba. Ban ga amfanin ilimin da na tsaya kika samu ba, idan ba zai nuna miki gaskiya ba.7 Ki na sane da girman zamantakewa tsakanin musulmi da musulmi, bayan haka tsakanin makwabci da makwabci, sannan ku ‘Yan-uwan juna ne. Kin ga hakkoki uku da suka rataya a kanki, duk kin sa kafa, kin shure, kin yi fatali da su. Domin kuwa Sogiji, ‘yar-uwarki ce musulma, sannan makwabciyarki ce, haka kuma ‘yar-uwarki ce, tunda ku na auren wa da kani. Ni dai muddin ba ki gyara halayyarki ba. Allah ya isa tsakanina da ke, domin ba tarbiyyar da na ba ki ba kenan.” Nan Momi ta kara gunjin kukanta, don tunda Baban Gusau ya soma bayani take kuka. “Duk kukan da za ki yi, shin zai gyara bacin ran da ki ka haddasawa mutanen nan shekara da shekaru? Sam ba zai kare ba, hatta ‘ya’yanki kin janyo masu. Saboda ki na ganin yadda ‘yarki ta ta sam ma raina miji, saboda abin da ta tashi ta ga uwarta na yi kenan. Haka ki ka kuntatawa Rumaysah, lokacin aurenta, ki ka hanata kwanciyar hankali a dakinta. Shin kin kyautawa kanki kenan? Umaru yake fada min ciwon zuciyar da ki ka haddasawa ‘yarki kwanan nan ya sake tashi, saboda abin da ki ka sa mijinta ya je mata da shi na zancen rabuwa, so ki ke yi sai kin ga gawarta ne, ko na mijinki.2 Ko kuwa nawa a kasa, sannan ki san cewa abin da ki ke yi ba kyau, bai kuma dace ba. Ki na tsammanin Allah zai yafe miki wata cutarwa da ke tsakaninki da ‘yar-uwarki ne? STORY CONTINUES BELOW Ina, sai dai ya yafe miki abin da ki kai masa na sabo, cikin rahamarsa, idan kin tuba, amma tsakaninki da mutum kam, yana tsakaninku. Ko mugun kallo ki ka taba yi mata, sai an maku hisabi bare irin wannan gabar, har ki na cewa za ki iya kisa, kin san ma hukuncin wanda ya raba tsakanin zumunci kuwa? To Allah ya la’anci mai yin hakan, bayan haka kuma ki ka so raba tsakanin ma’aurata. Da kin san girman laifinki, da kin zauna kin yi kuka har idanunki sun fita.” Alhaji nan ya cire gogul dinsa na tsoffafi, ya hau matsar kwalla.2 Hankalin Hajiya Atika ya yi mummunar tashi, yau ita take sa Alhajinta kuka? Abin da ba ta taba ganin ya yi ba, ko a mutuwar mahaifiyarsu, bai yi kuka a idon su ba, amma yau bakin-cikinta ya sa shi zubda kwalla.7 “Alhaji don Allah ka bar kuka, don Allah na roke ka, ka yi hakuri, ba zan sake ba.” “Tuban ki na muzuru? Ina ce haka na zaunar dake, ki ka yi min alkawarin ba za ki tada hankulan mutane ba kan wannan maganar, ko shekara daya ba a rufa ba, shi ne za ki gwada halinkin yana nan.” “Wallahi, Alhaji ba na son tashin hankalin kowa, sharrin zuciya ce. Na kuma gane kuskure na. Alhaji ka yafe min, ka daina kuka.” “Na ji, zan bar zubda hawaye, gafara kuma ki nemi na Ubangiji, sannan ki nemi sulhu da wadanda ki ka cutar, ku kuma kulla kyakkyawar mu’amala, idan kuma ba haka ba ko bayan raina ne, ki ka koma gaba da Sogiji, to Wallahi ban yafe miki ba.” Ai nan ta kife kan kafet, ta ci kuka, har ta gaji.2 “Allah ya kara maka tsawon rai Alhaji, amma Insha-Allahu daga yau na soke duk wani kyashi da gaba da yake kulle a zuciyata game da Sogiji, koda man tun can sharrin shaidan ne, da yadda na ga Likita yake ba su muhimmanci fiye da ni, wannan ya sa min muguwar tsanarta, amma Wallahi na gane kuskure na.”2 Alhaji ya saki ajiyar zuciya, ya-ce. “Umar ka na jin abin da ta fada ko? Tashi ka min magana da Alhaji Lamido, idan yana gida, da kaina zan je ta fada a gaban kowa.” “Alhaji Wallahi ba sai ka je ba, a shirye na ke na je da kaina na ba su hakuri.”2 Ko Dr. Umar sai da ya saki ajiyar zuciya, saboda abin da ya dade yana neman ya gani a tattare da Atika yau ya gan shi, wato ita-ce nadama. Gaba daya sun hallara a gidan kamar yadda Abba ya bukaci su tambayi izinin mazajensu su zo. Mamaki ne ya tuke Hajiya Sogiji da ta sauko wurin bakin da aka ce ta yi, domin ko kadan ba ta taba gamuwa da Hajiya Atika haka ba, ba masifa ba zage-zage da tsinuwar albarka. Zaune ta samesu da Dr. Umar sai kuma wani dattijo da tana ganin sa ta san mahaifin Hajiya Atika domin irin kamar da suka yi da shi, ga su Radiyya nan da su Rumaysah ko wacce da mijinta, Khansa’u ce da Sajeeda kawai ba su nan. Nan ta kwashi gaisuwa wurin Mahaifin Hajiya Atika da kuma kanin mijinta sannan ta shiga ta yiwa Baffa magana, sai ga shi ya fito nan ya gaida Baban Gusau cikin girmamawa. Kafin ko wannen su ya yi magana Momi ce ta fara. “hakika ba ni da bakin da zan soma magana, domin kuwa duk wani abin da baki na ya taba furta maku da ku da ‘ya’yanku to babu alkhairi a ciki, Baffa na san ka so ‘ya’yana, na san kuma ka na kaunar mijina matuka. Wato kaninka, idan banda haka duk abin da na ke yi ya-ci tsakaninku ya rabu, sharrin da ke tare da ni, ya kai ya raba zuri’a. Amma ku ka daure, ku ka rufe ido, duk da kun san al’amarina sai Allah. Ku ka rungume ni da zuri’ata har ku ka hada jininku da nawa, bayan kuna sane jinina a gurbace yake da son kai, da son zuciya da kin gaskiya. Ku ka sa danku ya auri ‘yata, duk don ku gyara tsakani. STORY CONTINUES BELOW Sogiji ba wanda na fi muzantawa irinki, ban san ta ina zan fara neman gafarar ki ba. Hakika da danku bai yi hobbasa wurin kawo gyara a al’amarina ba, da na aikata abin da ba ni da sauran lokacin yin da na saninsa. Domin kuwa da gaske na ke yi, da ya kai tsawon wani lokaci bai rabu da Rumaysah ba, ji na ke zan iya yi wa kaina illa. Amma da ikon Allah ya ki yin hakan, ya kuma fadawa na gaba da shi, domin a sa baki. Yau ina alfaharin aure a cikin zuri’ar nan da har na samu ‘ya’ya masu albarka suka nemi kubutar da ni daga sharrin kaina. Sogiji don Allah ki rufe idanunki, idan zai yiwu ki daure ki yafe min duk wani bacin rai da na taba kunsa miki cikin sanina da rashin sani na.” Gaba daya falon kowa ya yi tsit! Wasu har ga Allah ba don a gabansu Momi take magana ba, ba za su taba amincewa ita bace ta fadi wannan kalaman ba, sai ga ta sharbe-sharbe! Tana hawaye tana rokon gafara.5 Hajiya Sogiji ko banda kukan farin-ciki, ba abinda take yi. Sai godiyar Allah. “Atika ni kullum a matsayin ‘yar-uwata na dauke ki, kuma na godewa Allah da har ya ganar dake. Allah ya gafarta mana gaba ki daya.”5 Haka ta juya ta roki Baffa ma. Sai da aka gaama kalaman sulhu ne. Baban Gusau ya nisa ya-ce. “To Alhamdulillah! Sai mu yi addu’a Allah ya kade mana musiba da bala’i, ya kuma kawo albarka cikin gidan nan.” Nan suka shiga rero salati, suka rinke dire addu’o’i kyawawa, ranar farin-ciki, idan ana kwasar buhu-buhu, to an same shi a cikin gidan.1 Baffa ya dubi Abba da dare ya-ce. “Hakika ka yi gaskiya, domin kuwa wannan hadin da ka dage ayi shi, ya zamo sanadin kawo gyara a tsakani, sai fatan Allah ya sa farin-cikin ya dore. Allah ya nuna mana jikokinmu, wadanda za su sanya zuri’ar mu ta bunkasa”. “Ameen Yaya Lamido. Allah ya ba mu masu albarka.” Gaba daya yayyinsu sun ji dadin samun wannan kyakkyawar labarin, ba ma Yaya Shatu, cewa ta yi ta huta zuwa shari’a.2 Cikin dare ne ta turo kofar Mai-gidan ta shiga, ta samu yana wani bincike na su na Likitoci a cikin komfutarsa. Yana ganinta, ya zare madubin idonsa. Kasan kafafunsa ta durkusa har kasa, kawai sai ta sa masa kuka. “Lafiya Atika?” “Likita, ban san yadda zan hada idanu na da kai ba, bayan irin zaluncin da nai maka, amma kai alheri ka ke sona da shi, hassada da son kai sun sa na ke neman raba ka da dan-uwanka, amma wannan bai hana ka ci-gaba da zama da ni ba. Don Allah ka gafarta min, ban san yadda zan yi da rayuwata ba.2 Hakika na san na yi sa’ar samun miji na-gari, sai dai ni kuma ban zama matar kwarai ba a gareka, ba abin da nai maka a rayuwar zaman mu, sai sa ka kunci. Na sa ka kaina a gaba da komai da kowa.” Dr. Umar ya sa hannu biyu ya dago ta, daga durkuson da ta yi yana kallon cikin idanunta ya-ce. “Haba Atika, ke fa mutunce kuma mutum ajizi ne, dukkan mu da ki ka gani mu masu laifi ne wurin Ubangiji.1 Kuma sai Allah ya so ka da rahamarsa ne, zai ankarar da kai zuwa ga laifin naka, har ma idan ya so kuma ya dora ka kan hanya madaidaiciya. To amma idan ya so, sai ya bar ka da kayanka, ka zaci wayonka ko dabarar ka ne za su kubutar da kai. Babban farin-ciki na kuma abinda ya sa na ke kara godewa Allah, saboda Allah ya nuna miki gaskiya kuma kin rungumeta. Sannan kin ba ni dukkan farin-cikin da mutum yake nema, saboda kin haifa min ‘ya’ya masu albarka. Duk da na san da ni dake mun yi kuskure wurin nuna masu ko ina gata ne a duniya. Amma Alhamdulillahi! STORY CONTINUES BELOW Da samun mazaje na-gari da suka yi. Kin ba ni soyayyarki, kin kuma kasance ‘ya ta-gari tunda ki ka bi maganar mahaifinki. Allah ya ganar da mu baki daya, ya kuma yafe mana kura-kuran mu.” “Ameen, na gode.” Jawota ya yi ya sa a sashin jikinsa ya goge mata hawayenta.10 ************** Juyi ta sake yi, tana kallonsa ta-ce. “Allah Yaya Fawzaan na kasa yarda wai yau Momi ta nemi gafarar Mama.” Murmushi ya yi ya-ce. “Ba a mamaki da ikon Allah, komai lokacin sa yake jira.” A ranta ta-ce hala ita ma sonta lokaci yake jira, kafin ya dasu a zuciyar Yaya Fawzaan. “Yanzu dama Momi ce ta-ce ka rabu da ni, ko ta kashe kanta? Me ya sa ka ki fada min?” “Saboda ba ki da lafiya lokacin, a bar maganar, ba ga shi yanzu ya wuce ba?” “Haka ne. Allah kuma ya kiyaye gaba.” “Ameen.” Sai lokacin ta gyara rufuwarta ta bar lekensa, inda yake kwance a kasan dakin. Tabbas Yaya Fawzaan na da babbar matsala. Ta fada a ranta, sannan ta rufe idanu. ******* Yaya Sajeeda ce ta dira a Abuja, tun zuwanta Rumaysah ta matsa Yaya Fawzaan ya kai ta gidan Baffa. “Ke ki yi hakuri mana, za ta zo miki ai”. Haka ta gama kumburinta ta hakura. Sai washegari ta zo nan, suka yi ta murnan abin da ya faru. “Yaya Sajeeda nace miki har yau na kasa yarda, kullum sai na nanatawa Yaya Fawzaan.” “Hmm! Ke dai bari addu’ar mu ce ta karbu.” Rumaysah ta dubi Yaya Sajeeda ta-ce. “Yaya nauyin jiki?” “Alhamdulillah! Ga mu nan.” “Allah ya raba lafiya. Yaya Uncle Ahmad shi ne har da ajiye ki ya juya ko?” “Me ki ke so ya zo ya miki?” “A’a kawai dai na tambaya ne.” “Gobe ma zai juyo Insha-Allahu, za mu bi mu yi gaishe-gaishe, kafin mu koma.” “Kun yi kokari, kin ga ko mu fa tun biki Yaya Fawzaan, ya ki mu je Dan-Sadau, kullum wai baida lokaci, har kunyar su Goggo Zainabu na ke ji Wallahi.” “Zai kai ki Insha-Alalhu.” “Tab! Yanzu kam ai sai dai ya hadamu da amaryarsa ya kai mu tare.” Sajeeda ta bude idanu ta-ce. “Yanzu da gaske su Abba sun je sun masa tambayar Meenan ne?” “Tsohon zance kenan, yanzu haka ma idan kin bibiya yana can, don wurin hirar sa kenan, ko ba su gajiya ne da shi. Oho?”4 Sajeeda ta yi dariya sannan ta-ce. “Lallai a gaida Yaya Fawzaan, ke kuma sai ki ka tsaya, ki ka zuba masa idanu.” “Yaya Sajeda, ba abinda ba na yi masa a cikin gidan nan, amma tsakanina da shi, ido, don bai taba yabawa da ko daya ba, ina ga bai ma san ina yi ba.” STORY CONTINUES BELOW “To ke ko dan irin outing din nan ba ku fita ne, yana kara shakuwa sosai tsakanin miji da mata.” “Outing? Yaushe na gan shi a gidan, daga ofis sai barci ke dawo da shi gida, idan kin ga mun fita, to gidan Baffa za mu je. ” “Ki bar ni da shi, na san me zan masa. Ki zauna da shirinki gobe Insha-Allahu.” “Kai Yaya Sajeeda, ni fa ba na son ya zo ya surfa min masifa, ya-ce na faye shisshigi, shi ya sa ma ban fiye shige masa ba.” “Ke da mijinki? Bar ni da shi ki gani.” Haka suka wuni suna hirarsu. Yawancin shawarwarin da Anty Safiyya ta ba ta. Su Yaya Sajeeda ta ba ta, ita kuma gaskiya wancan din ma ba za ta iya bane, shi ya sa ta bar su. Amma tunda sun dage shi kenan. Washegari ya kama Asabar, don haka Sajeeda ta kira wayar Fawzaan ta-ce. “Yaya Fawzaan don Allah ka karasa (Ceddi Plaza) mana Rumaysah ta ce za ta same mu a can, mun bi wani wuri da Ahmad, amma yanzu za mu zo mu sameku.” “Yaya za ku shirya fita, ban sani ba?” “Surprise ne, sai ka je.” “To shi kenan, a ina za mu jiraku?” “Idan ka je, ka nemi wayarta za ta fada maka inda take.” Zuciyarsa na kitsa masa, ko me yake jiransa a can oho? Kai tsaye ya wuce can, sai dai yana zuwa, don tsiya (Network) ya yi halinsa, ya nemi layin Rumaysah bai samu ba, ya zo fita ne, don ya jirasu a waje ko zai gwada samun wayar ta, can ma sai kawai ya ga Meena za ta shiga ciki. “Ke, Ameena Abdulhameed.”4 Da sauri ta juyo, suna hada idanu ta sauke ajiyar zuciya. “Wai ma da izinin wa ki ka fito, ban sani ba?” “Oh, haka ko? Har ka fara ko? Na zo sayawa Hajiya wani abu ne.” Ta fada tana dariya. “Kai fa me ya kawoka?” Zai ce mata jiran Rumaysah yake yi, sai kuma ya-ce. “Na zo yawo, za ki sha (Ice Cream?” Ta dan tsaya za ta yi tunani, sai kuma ya-ce. “Kawai ki fadi flavor din da ki ke so, na san mata da son zaki.” Kai tsaye ya wuce wurin wasu masu (Ice Cream), ya saya mata, suka koma gefe suka zauna. Tana sha a hankali, suna hirar su kamar dama ita ya zo gani, lokaci-lokaci yana gwada wayar Rumaysah, amma har yanzu (Not reacheable). Rumaysah kuma tun isowarta take neman wayarsa, ba ta samu, don haka ta koma nemansa a kasa. Ta gaji ta zo sayan ruwa, don ta jika makoshinta ne, kawai sai ta hango mijinta da wata suna dariya. Ya dauki Tissue yana goge mata gefen baki.4 Wani jiri ne tukun ta ji yana kwasarta. Da kyar ta dafe bango. Yanzu dama Yaya Fawzan da budurwarsa ya zo. Bayan ita ta-ce tana son ganinsa? Wannan cin fuskar da yake mata ya kai intaha. Hawaye ne kawai ta ji suna zuba mata. Da kyar ta koma motarta tana gauraya hanya, ta dade tana sauke hucin numfashi. Ta kasa cire hoton su a idanuwanta. Can ta zuciya ta janye motarta ta kama hanyar gida, sai dai kan ta ma isa, numfashinta ya fara fita sama-sama, da kyar ta kai gida, cikin matsanancin ciwo. Shi kuwa Fawzan yana tare da Meena, amma hankalinsa yana kan me ya hana Rumaysah isowa har yanzu. Can dai ya-ce. “Meena, bari na bar ki haka kar mu yi laifi wa Hajiya. Ki kai mata sakonta.” STORY CONTINUES BELOW “To na gode, sai anjima”. Bai ko rakata mota ba, ya fita yana gwada neman Rumaysah, amma bai samu ba, haka ya hau sama ya sauko, duk neman Rumaysah. Da ya gaji ne, ya fito daga Plaza din, yana gwada lambar. Ya samu ta shiga, sai dai ta yi ta ringing, ba tare da an daga ba, hankalinsa ya soma tashi. Ya nemi Sajeeda. “Kin ce za ku taho, na ji ku shiru fiye da awa guda. Ku na tare da Rumaysan ne?” “A’a, har yanzu ba ta zo ba? Tun dazu muka yi da ita fa za ta tafi. Don har mun koma gida…” Sai kuma Sajeedah ta datse harcenta, ganin za ta fallasa kanta, daman su suke son hadawa kawai, ba wani zuwan da za ta yi da Ahmad. To ina Rumaysah ta tsaya? Kai tsaye gida ya nufa, ya dubo ko ina a kasa, ba ta nan. Falon sama ya wuce, tana kwance a daki, tana kuka ya bude kofar ya shigo, wata irin ajiyar zuciya ya sake, ganin tana lafiya, ba abin da ya sameta. Tana ganinsa, wani haushi ya kamata, ta mike za ta fice daga dakin ne ya-ce. “Ina ki ka shiga, kin daga min hankali, sai nemanki na ke yi. Sajeeda ta-ce ki na jirana a Ceddi, ba (Network), na yi ta nemanki, ban sameki ba.” Wani malolon bakin-ciki ne ya rufeta, idanunta suka ciccikoda hawaye, ita zai raina wa wayo. Ya je suna soyewa da budurwarsa, sai yanzu zai zo ya ce ya damu da rashin ganinta da ya yi? Ta juya za ta fita daga dakin ne, ya riko hannunta ta dawo jikinsa, ya mayar da ita ya hada da jikin wardrobe din dakin. Hannunta ya rike ta bayanta gam! Yadda ba za ta motsa ba. “Magana na ke miki Rumaysah?” “Ka sake ni yaya Fawzaan”. Fawzaan ya kara riko hannunta, ya hada ta da jikin wardrobe din. “Ka sakeni, ka na ji min ciwo”. Idanunta sun yi narai-narai! Saura kiris! Ta sa masa kuka. “Ciwo? Ni kuma fa ciwon da ki ke haddasa min na yi yaya da shi?” Ya kalleta da idanunsa masu kunshe da abubuwa da dama, a halin yanzu dai narka mata ‘ya’yan hanji suke yi. Cikin kidima ta-ce. “Wane irin ciwo na ke haddasa maka?” Cikin kunar rai ya-ce. “Me yake damunki ne? Ki daina min wasa da hankali, ki daina min yadda ki ke so. Me ya sa sai kin gwada min wani abin, sai ki sauya tamkar ba manufarki ba kenan, me ki ke so na fahimta a tare dake?” Har yanzu dai kokarin cire hannunta take yi daga nasa. “Wani irin wasa, da gaske fa ni ka na ji min ciwo ka sakeni.” “Ki fada min abin da yake bakin ki, ki fada min Rumaysah! A raunane maganar ta fito. “Nace maka ka sakar min hannu na, ka rabu da ni.” Da tsawa ta fadi maganar, ba shiri ya saketa cikin fushi ya-ce. “Na sake miki hannunki, kuma na rabu da ke, ki yi yadda ki ke so.” Yana sake ta, ya fice a dakin, zuciyarsa na tafarfasa hade da bugawa. A jikin wardrobe din ta sulale ta fara kuka sosai. Wayyo! Yaya za ta yi da rayuwarta? Zuciyarta ba tai mata adalci ba da ta so mata Yaya Fawzaan, alhali shi kuwa ba ita yake so ba. Meenar sa yake so. Ba abinda take tariyowa a kwanyarta, irin yadda ta ga yake gogewa Meena (Ice cream) a baki da handkerchief dinsa, wato dama duk karya ne, sai ya yi ta yin abu kamar Ustaz din gaske, alhali har taba fuskar budurwarsa yana yi. Hmmm! Ta yi kwafa.4 STORY CONTINUES BELOW A nan ta kwanta tana kuka har lokacin sallah ya yi, ta rarrafa da kyar, don ta kasa tashi kam, sai dai kafin dare zazzabi mai zafi ya rufeta a dakin. Da kyar ta laluba ta dauki sauran magungunan da aka rubuta mata kwanaki ta sha. Har safiya cikin matsanancin ciwo take. Da ta ga ba haza ne, ta danna wayarsa. Da kyar ya daga saboda fushi yake yi da ita. Sai dai da ya daga maimakon ya ji muryarta, wani irin numfashi ya ji yana fita. Yar da wayar ta sa ya yi, ya sauka zuwa dakinta da gudu, nan ya sameta a jirkice. “Subhallah! Rumaysah.” Ya duba gefen gado ya ga abin magungunanta ta sha. Hankalinsa ya dan kwanta, gyara mata kwanciyarta ya yi, sannan ya kimtsa ya zo suka wuce asibiti, bai kira ko Abba a waya ba, don baya son ya daga masu hankali. Allurarta aka mata kawai, ta dan huta, sannan suka koma gida zuwa yamma. Fitarsu ya fadawa Anty Safiyya abin da ake ciki a waya, suna dawowa suka samu ta shiryawa Rumaysah abinci. Ita ta zauna a kanta har sai da aka yi maghriba, ta koma gida. Shiru ya yi, yana tunanin tabbas ciwon Rumaysa yana kara lalacewa ne, domin a kankanin lokaci ya sake faruwa. Anya ba shi zai kashe yarinyar nan ba kuwa? Don ya kula bacin ran sa ke haddasa mata, samun Attacks. Tana tashi a barci, ya taimaka mata ta ci abincin, duk da ta so masa gardama, sai da yai mata jan ido tukun, sannan ya tambaya ko za ta iya sallah. Kai ta gyada masa. Amma kuma tana mikewa jiri ya fara dibarta, don haka rike ta ya yi, ya kai ta har bandaki, ya sa mata ruwa, sannan ya-ce ta yi alwalar, ya fito ya ba ta wuri, karar faduwar buta ya ji, ya sa ya banke kofar ya shiga (Toilet) din da sauri. “Anya ba za mu koma asibitin nan ba?” A’a ta-ce masa, a hankali ya debi ruwan da kansa ya taimaka mata ta yi alwala, sannan ya rikota zuwa daki. A zaune ta biya sallolin nata, ya fito mata da wata riga. Ya shiga ya tara mata ruwa sannan ya-ce. “Idan kin huta, ki shiga ki yi wanka ko za ki ji dadin jikinki.” Haka ya zauna a kofar yana gadinta har ta gama wankan, ta fito, sai da ta fito ne, ya ba ta wuri don ta shirya. Nan ta zura rigarta, ta bi gado ta kwanta. A kujerar dakin ya zauna, yana kallo har barci ya dauketa, sai lokacin ya samu natsuwa, ya fita shi ma ya-ci abinci, ya watsa ruwa, sannan ya koma kujerar, ya kwanta yau kuma gadin nasa ne, ba nata ba. Da safe ya tashi ya rasa yadda zai yi, ga shi zai wuce ofis, don haka waya ya yiwa Anty Safiyya. “Maman Fadila, don Allah ki yi hakuri da mu, ina son na fita, amma ba ta tashi ba, ita kadai ce a gida, idan ba zan takuraki ba, don Allah ki rinka leka min ita, zan je na bada uzuri wurin aiki na dawo kafin nan.” “Haba, ai ba damuwa.” “Na gode. Allah ya saka da alkhairi, zan bar miki makulli a wurin Mai-gadi, sai ki bude, idan kin tashi.” Ya tafi zuciyarsa fal! Da damuwa. Da wuri ya bar wurin aiki, kasancewar ya fadawa ogansa yana da Patient. Komawarsa ya dan ji dadin ganinta, domin ta yi wanka, ta ci abinci, sai dai a kishingide take. Amma dai ta yi fes! Da ita. Nan ya ji wani abu ya dirar masa, bai saurari komai ba ya isa inda take kwance, ya sumbaci goshinta. Rumaysah kuwa tsikar jikinta sai da ya tashi har tsakar tafin kafarta, ta ji wani abu ya taso mata. “Yaya Fawzaan,” “Yaa Salam, ki na tsoratani Rumaysah, don Allah ki rinka min sassauci, ki daina wannan ciwo farad dayan. Ba ki san yadda hankalina yake tashi ba. Allah ya ba ki lafiya.” Ya fada hannunta a cikin nasa. STORY CONTINUES BELOW Anty Safiyya dai sai ta bayan kujeru ta sulale ta bar falon, don ta ga alama Mai-gidan bai san da wata a gidan ba, sai matar sa kawai yake iya gani. Rumaysah kuwa abinda ta so fada masa kenan, motsi ya ji, ya juya ya-ce. “Kamar an taba kofa?” “Anty Safiyya ce ta fita, abinda na ke son na fada maka kenan.” “Inna-Lillahi’wa-Inna-Ilaihir-Raji’un!” Take ya ji wata kunya ta kama shi, sai kuma ya juyo ya dubi Rumaysah. “To ba ke bace duk ki ka daga min hankali”. Rumaysah dai jinsa take yi kawai, don ita kam ta riga ta san matsayinta a wurinsa. “Yaya ki ka yi shiru da yawa, ki ce wani abu mana?” “Me zance?” “Oho! Just say something, idan ba kya surutu ko fada, sai na ji kamar ba ki da lafiya ne.” “Hmm! Don ni ce sarauniyar tsiwa ko? Ni da na san ka na tahowa ma da ka taho min da Agwaluma ko danyan mangoro abu mai tsami-tsami na ke sha’awar ci.” Cikin razana Fawzaan ya sake hannunta ya-ce. “Rumaysah! Ciki ki ke da shi?”6 Ita ma a razane ta dube shi, ciki! Yaya za ayi ya-ce tana da ciki?2 Ba tare da ya jira abin da za ta ce ba, kawai ta ga ya sunkumi waya ya fadawa Mama wai sun kusa samun karuwa. Rumaysah ba lafiya. Kunya duk ya bi ya rufe Rumaysah, ita in dama da gaske ne, to da sauki, to amma abinda babu shi, ya bi har yana bazawa duniya. Sunan wani wai Gandoki!4 “To ka na gani ne, ko kuwa ka tabbatar, ku je dai asibiti a auna ta tukun.” “To Mama, amma fa irin kwadayin nan na masu ciki duk tana yi, sannan jiya ma da zazzabi ta kwana.” Mama dai maganar ta mata nauyi, don haka kashe wayar ta yi ta rabu da shirmensu. Ai kuwa Likitan asibitin Abba ce masu ta yi, zai iya kasancewa zazzabi ne, ita ta fi kyautata zaton ciwon ta ne ma ya tashi, don haka ana bukatar gwaji kafin a tabbatar. Momi ko da suka hallara a gidan Rumaysah, bayan sun koma gida, cewa ta yi ta rinka kula tunda tana da juna. Mama ta-ce a dai jira a tabbatar tukun, sannan ta-ce. “Me za ki ci a dafa miki?” Rumaysah dai ta yi shiru kawai tana jinsu kaf! Don ita girman al’amarin ya shallake tunaninta, a ruwa, ta sha cikin ko yaya?9 Sai da kowa ya watse. Fawzaan ya shigo dakin ya tura kofa. “Me ya sa ki ka yarda cewa ki na da ciki, ba ki fada masu gaskiya ba?” “Ko na yi shiru, ba kai ka gano kayanka ba, kuma kai ka fara fada? Ta yaya ma za ayi mu haihu? Yaya za ka ce masu ina da ciki, bayan ka san ba hakan bane.” Ta fada tana kallonsa ta gefen ido. Fiddo idanu ya yi ya-ce. “To ni na sani ne? Ranar na yi rashin lafiya na san ko kin yi yadda ki ke so da ni?” Bude baki ta yi cikin mamaki da razana, ta kasa yarda da abin da ya fada mata ta-ce “Ah!” Ta bi shi da filo, tana dukan sa. Dariya ya sa.16 Ta-ce “Seriously, idan muka je asibiti aka gwada fa? Za a gane babu komai, me za ka ce masu?” “Idan kuma yanzu muka ce ba hakan bane kuma fa? Za su tambaye mu, yaya aka yi muka san babu cikin Kin ga asirinmu ya tonu”. Kau da kai ta yi gefe. A ranta ta-ce “To ni zan maka komai?” Koda suka tashi tafiya yin gwajin. Fawzaan ya-ce zai fada masu. Rumaysah ta hana shi ta-ce. “Idan suka san mun je za su damu da sanin sakamakon me za mu ce masu?” Tabbas! An samu matsala yanzu, yaya zai bi kowa ya fara ce masu karya ne matarsa ba ta da ciki, asali ma bai taba saninta ‘ya mace ba! Har sun shiga wurin daukar jini. Fawzaan ya-cewa ma’aikaciyar ta dakata. Ya samu Abba da su Ra’id, kai har da Mama ko yaya aka yi suka zo duka, oho? Rumaysah ta mayar zai fadawa Mama gaskiyar magana ne, ga Yaya Ra’id a wurin ma. Sai ta ji ya-ce. “Allurar sabuwa ce?” Matar (Lab) din ta bata rai ta-ce. “Da sabo muke daukar ko wani Sample na jini.” Fawzan ya duba Allurar ya-ce. “Haba ke kuwa, da kin samo dan siririn allura, ai ba zai yi zafi ba, amma wannan zundumemen, ai sai ki kumbura mata jijiya.” Ra’id ya-ce. “To su Yaya Fawzaan masu mata. Idan ba ka bari an ja jinin ba, mu ka ke bari a suspense, don Allah matsa, ayi a fada mana sakamako”. “Hmm! Ku na gida, ni za ta fi damu da raki, muddin aka ja mata mai zafi. ” Matar ta-ce. “Barrister, ka kwantar da hankalinka, muna daukar na kananan yara ma ba tare da sun ji zafi ba, yanzu za mu gama.” Fawzaan ya damko hannun Rumaysah ya rike, yana lekawa a hankali. Sai Abba ne ya-ce. “To Fawzaan sakar mata hannu, an gama diban jinin.” Duka suka sa masa dariya. Sai kuma ya ji kunya, bai san Abba ya shigo ba. Ra’id ne ya-ce. “Yaushe za a zo a karbi sakamakon?” “Ko zuwa yamma ma za a samu.” Radiyya ko har ta bugo waya, wai ita za ta sanyawa Baby suna. Kai wannan Baby din ina ma da gaske ne. Gidan Baffa suka wuce, don kowa ya-ce sai ya ji sakamako tukun, murna fa kai ka ce a kansu aka fara haihuwa. Abu ya hadu da dan gaban goshin gidan, ga kuma ‘yar auta ‘yar gatan Abba da Baffa. Ai ko can sai ga Ra’id ya shigo da sakamako, ana dubawa aka samu negative, babu ciki. Jikin kowa ya mutu, amma sai aka shiga addu’ar Allah ya kawo masu albarka. Mama ko cewa ta yi, daman ta san shirmen Fawzaan ne kawai. Can sama ya samota a dakinta na gidan, jikinta duk ya yi wani iri. “Come on Rumaysah, yaya na ga kin bata rai? Ke da za ki yi farin-ciki ma ga result din ya fadi gaskiya, ba sai mun yi masu bayanin alaqar mu ba, bare su gano komai? Besides da sakamako ya dawo positive, sai kin tafi kin nemo uban dan. Ko kuwa ki amince kin dau advantage dina.” Filon da ya fi kusa da ita ta dauka, ta kai masa bugu mai kyau, sai da ya-ce. “Ouch! Karya na yi?” Ya fada sannan, ya fice yana dariya, ita kuwa ta sunne kanta tana ta murna, har da rungume filon hannunta. Ko ba komai dai, sun fara zama abokan juna.4 *************

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *