AUREN FANSA CHAPTER 1 BY ✍🏾 NIMCYLUV
Www.bankinhausanovels.com.ng
ALLAHAMDULILLAH! As your wish and my wish,ga AUREN FANSA nan FREE BOOK, all i want your support accepte it share it to All your GROUPS, #Love# Destiny#Romantic#Fiction! So you can share and share and share fisabilillahi!.
Peachvine Marquee Wedding & Event Center
Shine event daya samu halartar mutane da yawa kama da maza da mata,kowa ka gani yana cikin farin ciki da kuma walwala, Yadda event ya cika da manyan mutane kaɗai zai tabbatar maka cewa taron da ake ko kuma dinner da ake bata ƙanan mutane bace, babu hayaniya ko kaɗan kowa yana wajansa a zaune, kasancewar kowa akwai number seat ɗinsa ajikin gate pass ɗin da aka bada, yadda Mutanan wajan suke sanye da white colour na kaya sai red head zai tabbatar maka cewa colour of the day aka bada. Babu abinda yake tashi a cikin hall ɗin sai waƙar Arman Maleek dake dashi mai taken TUM HI HO a hankali waƙar ke ƙara cikin hall wasu kaɗan daga cikin mutanan dake cikin hall ɗin suna bi kamar haka:
_🎻🎸Hum tere bin ab reh nahi sakte_
_Tere bina kya wajood mera (x2)_
_Tujhse juda gar ho jaayenge
_Toh khud se hi ho jaayenge_ _judaa_
_Kyunki tum hi ho_
_Ab tum hi ho_
_Zindagi ab tum hi ho_
_Chain bhi, mera dard bhi_
_Meri aashiqui ab tum hi ho_
_Tera mera rishta hai kaisa_
_Ik pal door gawara nahi_
_Tere liye har roz hai jeete_
_Tujh ko diya mera waqt_ _sabhi_
_Koi lamha mera na ho tere bina_
_Har saans pe naam tera_
_Kyunki tum hi ho_
_Ab tum hi ho_
_Zindagi ab tum hi ho_
_Chain bhi, mera dard bhi_
_Meri aashiqui ab tum hi ho_
_Tumhi ho… Tumhi ho…_
_Tere liye hi jiya main_
_Khud ko jo yun de diya hai_
_Teri wafa ne mujhko sambhala_
_Saare ghamon ko dil se nikala_
_Tere saath mera hai naseeb juda_
_Tujhe paake adhoora naa raha hmm.. Kyunki tum hi ho_
_Ab tum hi ho_
_Zindagi ab tum hi ho.._
_Chain bhi, mera dard bhi_
_Meri aashiqui ab tum hi ho (x2)🎻🎸_
Kowa harkar gabansa yake,wasu na danna waya wasu kuma na bin waƙa wasu na yin shira,kana ganin wajan kasan bikin da ake bana ƙananun mutane bane,biki ne na manyan mutane Ajeboters the richers people’s, yanayin kayan da jekin
mutane yasa na fahimci bawai anko bane kawai an bada colour of the day ne, suna sanye da white ɗin Lace sai red head maza ma sun sanya gezner hular kansu zanna ta kasance red. Most of people da akai invite ɗinsu sun halarci wajan amma both sides ɗin na bride and groom babu wanda yay attending dinner. Gefe guda a cikin hall ɗin wasu securities ne da suke bawa mutanan wajan tsaro, right side ƴan jarida ne both sides T.v Redio, left side kuma Photographies ne irinsu Majida Balancy da sauransu. maganar da M.c yayi da ankarar da mutane cewa Groom family ne suka ƙarasu wajan, by now ana they’re waiting for bride and groom. Kowa da wajan zamansa number gate pass ɗinka itace number seat ɗinka. Turo Ƙofar bedroom ɗin akai a hankali ta ɗago jajayen idanunta ta sauke akan wanda ya shigo kallo guda tayi masa ta ɗauke kanta, yana tsaye sanye da wata mahaukaciyar shadda Gezner anyi masa ɗinkin wando da Jamper sai babbar riga, idanunsa ya mayar saman Rolex ɗinsa Jaeger-LeCoultre yay kyau sosai gaba ɗaya shekarunsa sun ɓoye, fuskarsa cike da farin ciki da walwala ya dubu matashiyar matar dake haɗa kayanta a cikin Trolly hanunsa ya miƙa zai riƙeta tai saurin zamewa still kuma tun kallon farko da tayi masa bata sake kallon inda yake tsaye ba, Murmushi yay yace “Kina wahalar da kanki MANNAL meye ribarki na tafiya gida? Ko dan kawai zanyi aure shi ne zaki ɗauki damuwar duniya ki ɗurawa kanki?”. Ya faɗa yana ƙara kallon yadda ta gama haɗa kayan ta ɗauki hand bag ɗinta da wayarta, wani haushinta ne ya kamasa domin babu abinda ya tsana masa da shariya idan kuma da sabo yaci ace ya saba domin MANNAL macace wacce sam bata ƙaunar hayaniya da yawon takura, milk ɗin veil ta ɗauka ta ɗura saman kanta hakan kuma ba ƙaramin kyau ya ƙara mata ba, Trolly ɗin ta kama sai a lokacin kuma ta ɗaga Idanunta wanda sukai jajirr a hakan kuma ko ɗigwan hawaye ba tayi ba, cikin sassanyar Muryar tace “Zan huce” Kallonta yay yace “Wato kin rantse sai kin tafi gida ko? Meye matsalarki da Auren da zanyi Maman Arman?” Kallon tsaf tayi masa tana jin yadda zcyarta keyin tsalle kamar zata faso ƙirjinta ta fito cikin kaushashiyar Murya ta kalli cikin idanunsa tace “Bani da matsala da Aurenka Abban Arman,hasali ma Auren baya kaina amma i have my own reasons da zai sanya na bar maka gidanka” Kallonta yay yace “Uhm mene Reason ɗin?” Kai tsaye tace “Mene yasa duk matan duniyar nan ka rasa wacce zaka auran sai SAFA? She’s like daughter to you Abban Arman, kai ka raini yarinyar nan har lokacin da mahaifinta yabar duniya, idan tunani na bai bani dai-dai ba ka girmi mahaifinta, SAFA kusan jika take a wajanka bawai ƴar ba amma idanunka ya rufe sbd son abin duniya dan Allah mene zaka cewa ɗan ka ARMAN bayan kasan shike son yarinyar nan, And mene zaka faɗawa Yayan Safa kasan cewa yafika ɗan yan kai ko? Akan ƴar uwarsa babu abinda ba zai ba, ko kuma sbd babu ran mahaifinsu shiyasa kake son tauyewa yarinya haƙƙinta..,” cikin tsawa yace “Enough! MANNAL ya isa haka, thank God kince ni abokin uban wacce zan aura ne bawai maƙiyinsa ba, Am 76 years old a duniya Safa nada 17yrs , Yeah you’re right zata iya zama jika a wajena amma babu haramcin aure tsakaninmu ko? Besides ma Kakan yarinyar ya bani ita ya yarda da Auren, dan haka ki daina wahalar da kanki idan kuma ki kaga ban Auri Safa ba to ki tabbatar bana raye” ƙwafa tayi tace “And so what? Nace sai me danka Auri Safa? Ina da hankali na San mene nake wlh billahi bazan taɓa zama dakai ba bare uwar yarinyar tai min wani kallo zan bar maka gidanka, and ina jiran Divorce paper idan ba haka ba Court zata rabani dakai kuma ka shirya abinda zaka faɗawa ɗan daka haifa cewa kai masa snatching yarinyar da yake mafarkin samu a Matsayin Mata” hannu ya watsa Irin i don’t care ɗin nan kafin yace “at least kije wajan dinner kafin ki tafi,mgnar Divorce paper kuma wlh baki isa ba bazan taɓa aurenki ba” ko takan sa bata biba ta nufi compound ɗin gidan, da sauri driver ya ƙarasu yana faɗin “Barka da fitowa Hjy yaya akaji da ta…,” Wani kallo da tayi masa yasa ya haɗiye sauran Maganar key ɗin hannunta ta cilla masa jikinsa na rawa ya buɗe mata ƙofa ta shiga tana jin yadda yake tambayarta ina zai kaita amma ko Kallonsa ba tayi ba sai ajjiyar zuciya da take saukewa,sai da suka ɗauki titi sosai kafin tace “Kai ni Airport”. Da kallo kawai Alhj Ishaq ya bita yana sauke numfashi yasan dole zata dawo garesa wannan fushin ba mai ɗorewa bane, wayarsa dake ƙara ya duba tare dayin picking call ɗin yana tafiya yana faɗin “Am on my way” yana faɗin haka ya fice daga cikin gidan zuwa compound Mmki ne ya cikasa ganin babu motar Mannal a wajan, ganin time ɗin dinner na tafiya yasa ya shiga motarsa yay mata key tare dayin reverse yaja da gudu,tun kafin ya ƙarasa gate keeper ya buɗe masa, da wani irin speed ya cilla motar saman titi. Bai tsaya ko ina ba sai ƙofar gidansu amarya a nan ya samu dukkan abokansa suna jiransa, ɗaya daga jikinsu ne ya kalli Alhj Ishaq yace “Time is not our side ya kamata kayi mgnar Amaryar ta fito” wayarsa ya ɗauka ya kira number Anut Suwaiba shi kaɗai yace “Ok no problems” Babban gida ne wanda kana ganinsa kasan basai anyi mgn ba,mamallaka gidan sun tara abin duniya Musamman idan kayi duba da yawan securities ɗin da suke gidan, hatta gate keeper soldier ne. Babban compound ne wanda ya cika da manyan motoci na zamani kusan guda ashirin rabin cars ɗin wajan sabbi ne. Ga wasu haɗaɗɗun green flowers masu daɗin ƙamshin wanda sukaiwa gefe da gefen gidan ƙawanya. Daga can upstairs na ɗan fara jiyo mgnar mutane, a parlon farko naga wata magidanciyar mata fara tass da ita tana sanye cikin wani farin lace mai kyau da tsari, fuskarta ba yabo ba fasallasa amma kallo guda zakai mata ka tabbatar ta zurfafa cikin tunani, Anut Suwaiba ce tace “Hjy Ruma ga Abban Arman can a outside yana jira amarya,yin duniya amma SAFA taƙi bari make up artists ta ɗaura mata head ɗin gwon ɗin” ajjiyar zcy Hjy Ruma ta sauke tace “Sumaiba me kike nayi akai? Na faɗa maki gsky abinda ke zcyta wlh billahi am not happy about this marriage, Abbi ya yanke abu ba tare da shawara ba,nasan yana da ikon akan jikarsa amma sai ya kalli mutumin da yace zai aure ta, Abban Arman matsayin Uba yake wajan Safa tun ba yanzu ba ɗan sa Arman yake ƙaunar Safa,amma yana tsaka goɗai² dakai kace zaka auri ƴar cikinka ko jikarka,gaba ɗaya Safa nawa take? Ko Yayanta gaba ɗayan sa nawa yake bare ƙanwarsa, ina yin shiru sbd Safa bana son ta fara bijirewa umarnin na samanta,kuma ni ban isa na hana Auren ba” Ajjiyar zuciya Anut Suwaiba ta sauke tace “Mai faruwa dai ta faru Ubangiji kaɗai yasan abinda ke ɓoye, kawai kibi Auta da addu’a shi ne” miƙewa Hjy Ruma tayi zuwa wani bedroom tana shiga Safa tayo wajanta da gudu ta Rungome tana kuka tace “Ummi i don’t like him,bana son Auren Ummi,shi Babana ne not my lover wlh Ummi zan mutu idan na auresa” rungometa sosai Ummi tayi tace “It’s okay my dear, you know what? My Mother tell me and yanzu kuma zan faɗa maki, Ki yadda da ƙaddara mai kyau ko akasinta, ki ɗauka hakan wata jarrabawa ce daga Ubangijin ki kiyiwa Grandfa ɗinki biyayya,nasan daman kina ilimi zaki biyayya ga Dukkan abinda aka umarce ki akai muddin bai kauce hanya ba, so stop all this ki manta da baya just farcing your future” cikin kuka Safa tace “Ummi cewa yayfa yana sona” da sauri Ummi tace “Uhm let him say my dear, kiyi addu’a wata rana zaki farin ciki kinji ko?” Kai ta ɗaga tace “You’re the best mother thank God for giving a good mother ina sonki Ummi” Murmushin takaice Ummi tayi tace _”You’re a darling”_ (ke abarso ce). Mmki ne ya cika Anut Suwaiba cikin ƙaramin lokaci Ummi ta shawo kanta, lallai uwata musamman ce a duniya. Cikin nasihar Ummi aka shirya Safa cikin light blue ɗin gwon wacce tai mata masifar kyau sai walwali take,kana ganinta kasan kwalliya ta saba zama a jikinta, kyakkywa ce ajin farko kamarta ɗaya da mahaifiyar ta, amma kallo guda zakaiwa Safa kasan cewa Ruwa biyu ce (Half-caste). Tana da ɗan tsayi da faffaɗan west dai-dai da jikinta ga wani ƙwantaccen kyau dake saman fuskarta, fuskarta Oval ce sai beaut point dage kumatunta na dama guda ɗaya, shirya ta aka gama yi ita ɗaya ce domin duk ƙawayenta bata faɗa masu ba, gaba ɗaya bikin cikin 3days aka shirya yin sa. Marai-raice fuska Safa tayi tace “Umm!” Ummi tace “Yes! Dear” kamar zata kuka tace “YAYA HEEMU i can’t find him duk sanda na kira wyarsa switch off, i missed him a lot he’s my brother my father and my best friend” hannunta Ummi ta kama tace “You’re right dear, He’s my father too, but your brother is very stubborn, anytime baya ƙasa yasan Bama da kowa sama da shi da yanana ai shine waliyinki” Shiru Safa tayi suna da komai najin daɗin rayuwa suna zaune Cikin farin da walwala rana ɗaya damuwa tai fatali da farin cikin da suke ciki, side hug Ummi ta bawa Safa tace “Allah yay maki albarka keda Yaya Heemu, kune komai nawa ki kula da kanki Sweeie” tsayawa Safa tayi tace “Ummi ba zaki wajan dinner” tana yin flat ɗinta tana faɗin “Not sure! Nasan Mannal ba zata sake ba idan ta ganni” tana faɗin haka ta shige flat ɗinta Anut Suwaiba ta kama hannun Safa zuwa downstairs. Tun daga nesa Abban Arman ya tsora mata shanyayyun idanunsa yana jin wani so da ƙaunar Safa na ƙara ratsa ko wanne lungu na zcyarsa. Kanta a ƙasa suka ƙarasa wajan da yake tsaye ya jingina da jikin motarsa,da Murmushi a fuskarsa yace “Sannu da ƙoƙari Anut Suwaiba” kaita ɗauke sbd itama haushi yake bata ba tare data kallesa ba tace “it’s my pleasure” yace “Ok! We really appreciate” ba ƙara jin mene zaice ba ta juya da sauri ta shige cikin gidan. Kamar ya haɗiye Safa sbd so da ƙauna haka Abban Arman yake ji a ransa, sauke numfashi yay ya buɗe mata back seat ba tai musu ba ta shiga sbd ta ɗauki niyyar tarinta bai isa yaji bare yaji sautin muryarta, tana shiga shima ya shiga akaja motar da gudu daman alrdy gate ɗin a buɗe yake yana fita motocin abokansa suka mara masa baya. Ƙara sauke ajjiyar zcy yay kafin ya ɗan matsa kusa da ita a taushashe yace “Darling ya akai?” Wani baƙin ciki ne ya turnuƙe Safa wai Darling? Shi ko kunyarta baya ji ta hau bayansa tai masa fitsari idan ance ta taɓa yi masa kashi a jiki ma baza tai musu amma shi ne yau yake son aurenta har ya haɗa shimfiɗa da ita, jin tayi Shiru yasa Abban Arman miƙa hannu zai jawota jikinsa yana ɗura hannunsa a jikinta Safa ta fasa wata gigitacciyyar ƙara…..
*DAN ALLAH DAN ANNABI IDAN KINJI DAƊIN LITTAFIN KIYI MIN SHARE NASA SBD SOYAYYYAR ANNABI*
SIRRIN MU TODAY PROMO
Dukkan wanda bai karanta SIRRIN MU wallahi bai karanta littafi Mai cike da soyayya tausayi, kuje ku karanta kuji yadda ɗa keson matar Ubansa, Littafin nada banne Yafi *UNCLE NE, yafi MOON, haka nan yafi AUREN FANSA🔥🔥* promo ne akan 400 via 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616.
SARAUTA 👑