AUREN FANSA CHAPTER 12 BY ✍🏾 NIMCYLUV
Www.bankinhausanovels.com.ng
Cikin tashin hankali Ya Areef ya yi kan Ya Omer yana kiran sunansa tare da jijjiga sa.
Amma sam ko mutsi ba yayi ga jinin daya shiga tsartuwa ta cikin hancinsa da bakinsa.
Kafin kace me gaba ɗaya jini ya gama wanke jikin Ya Omer sai jan numfashi yake a wahalarce.
Cikin ƙara ji Ya Areef ya shiga kiran Doctors na cikin asibitin.
Da sauri suka ƙarasu wajan ɗauke da gadon marasa lafiya suka ɗura Ya Omer akai.
Shi kuma Ya Areef ya shiga kiran Number Baffa da kuma Baba Haroon sai Kawo Shuriem.
Da gudu motar take tafiya kamar zata tashi sama, sosai sukai tafiya mai nisa, Moha kam hankalinta ya daɗe da goshewa sbd abinda suka shaƙa mata.
Waya ce maƙale a kunansa yana zaune a office ɗinsa Shida abokinsa yana amsa kira na wani babban abu mai muhimmanci gyara zama yay yace.
“Look, ban son Shirme kana kallon yadda aka fara yi mana illa, ana binmu ɗaya bayan ɗaya ana kashewa, to idan ka shirya mutuwa yanzu nikam sam ban shirya mata ba, then Tayaya kayi sake baka samu shiga hospital ɗin ba? Bayan kafi kowa sanin muhimmancin abinda muke ko?”
Daga can ɓangaren wanda ake mgna dashi yace.
“Sorry sir, nayi try na shiga but i can’t, cos yau akwai securities sosai a cikin hospital ɗin”
Gyara zama Abban Arman yay cikin sanin son Abinda yake faruwa yace.
“Securities? Akan mene ko ka samu impormation ɗin akan tsaron da aka bayar ɗin?”
Mutumin dake tsaye can nesa da gate ɗin asibitin ya gyara zaman face mars ɗinsa yace.
“Da alama dai wani babban mutum ne mai muƙamin gske ne yazo Asibitin, kuma ba ɗan wannan garin bane gsky duba da yadda nake sunan number motar”
Miƙewa tsaye Abban Arman yay yana fesar da numfashi yace.
“Wacce number ce?”
Kai tsaye B.guy yace
“Naga an saya A.M 1, to gaba ɗaya number motar haka suke dga ɗaya har zuwa 10, sai kuma wasu motocin nada ban”
System ɗinsa ya jawo ya shiga searching amma ya kasa, Abokin nasa yace.
“You’re mad, kasan cewa baka san kan net ba, Then baka iya komai daya shafi na’ura ba, mutum ɗaya kaf faɗin 9ja dake datse na’ura ko a ina take,kuma take ƙirƙirar abu na musamman, kwanan nan ma ta ƙirƙiri wata na’ura wacce za’a iya sanyata cikin jikin Mutum a sarrafa ce bisa Dukkan umarnin daga masa, amma har yanzu Mijinta bai mata damar sakin wannan na’urar ba, sbd illar dake jikin na’urar, sannan a lokacin guda na’urar tana iya sanya ƙarfin Mutum ya riɓanya sau 20, jijiyoyin mutum su kumbura haka kuma girman mutum ya ƙaro, mutum sai ya iya faɗa da mutum 100 ba tare da gajiya ba, amma kuma idan aka danna na’urar gaba ɗaya 5mts take a jikin mutum, lokaci na cika mutum yake faɗuwa yay baccin Sa’a biyu, sbd jijiyoyin jikin mutum suna saki ne su daina aiki a lokacin”.
Gumi Abban Arman ya share kana ya gyara zaman wayar kunnansa, yana kallon Abokin nasa yace.
“Wacece wannan?”
Gyara zama Jibril yay yace.
“Zuwa yanzu babu wanda yasan impormation ɗin komai a kanta, sbd ta shiga ta shafe komai nata a yanar gizo, kuma tana da ɗaure gindi manyan securities na ƙasar da kuma ƙetare sun tabbatar cewa aikinta akan tsari yake, kuma makaranta tayi ta karanci komai, tana kuma taimaka masu akan kidnappers, domin lokaci kaɗan take gano inda suke”
Abban Arman yaja dugun numfashi yace.
“Kenan babu wanda yasan komai nata even her name or picture ko ina take zama”
Dry Jibril yay yace.
“You’re mad, da an san inda take da tuni an jima da kasheta ko kuma a sace ta, amma dai ana raɗe raɗin cewa ita ɗin itace raunin _ABU_MALEEK_ itace komai nasa, domin itace remote ɗin juya akalar rayuwarsa, duk da cewa babu wanda yasan tsakaninsa da ita, amma ina tunanin cewa ko dai best friend ɗin sa ce, ko family ko kuma his wife”
Shiru Abban Arman yay yana nazarin abinda Jibril yake faɗa kafin yace.
“Abu Maleek? The richer young man ɗin nan, ahaaa the prince the king, and kuma the professional footballer wato yariman masarautar England”
Dry Jibril yay sosai yace
“Amma dai a baki kasan sunan ba wai ka taɓa ganin ko photon mai sunan bane ko? Yeah Shine Dr. Footballer, Aremo JALALULDEEN TUNDE MUHAMMAD JALAL, matashin saurayi mai ji da ilimi nasaba, arziƙi uwa uba addini”
Jinjina kai Abban Arman yay yace
“Amma ai ance mahaukaci ne ko? Ko kuma ƙarya ne, ni dai yanzu ba wannan ba tayaya zan samu impormation akan wannan muguwar matar”
Jibril ya zare ido yace.
“Muguwa kuma? To wannan ita jin daɗi da kuma kwanciyar hankalin Abu Maleek, ita kaɗai zatai mgn ya saurara da abinda yake, kasan idan abin nasa ya Motsa ya karya mutum ko kuma ya kashe ba wani abu bane a wajansa, kuma No one talk sbd yana da shaida a gidan mahaukata, to wannan matar ko yarinya itace kambu kuma linzamin Abu Maleek, itace jigo farin ciki jin daɗi da walwalar Abu Maleek, idan yay dry itace a wajan idan yay mgn itace a wajan, amma yana da ɓoyayyan abu wanda ko ita bata sani ba bare jama’ar garin”
Abban Arman yace.
“Banza uban surutu kai gidan ubanwa ka samu wannan bayanan?”
Murmushi Jibril yay yace.
“Yau kimanin shekaru biyu kenan ina son sanin Wacece wannan yarinyar domin tayi min illa ƙwarai wacce ita kanta bata sani ba, idan kuma ina da rai da lfy Tabbas sai na rama abinda tayi min akan wannan Abu Maleek ɗin”
Jinjina kai Abban Arman yay kana ya saita murya yace.
“B.guy ka tabbatar ka samu bayanan akan wannan tsaron da aka samar kaji menene dalili”.
Cikin girmamawa B.guys yace.
“Ka ɗauka ka san komai kuma ka tsumayi wayana a koda yaushe”
Yana faɗin hakan ya kashe kiran.
B.guys tsaye yay cikin Sa’a aka buɗe gate ɗin da sauri kuma yabi bayan wasu mutane ya shiga.
Ashe duk wannan abun baiga komai ba.
Securitie’s ne a wajan tako ina lungu da saƙo.
A sukwane kuma yaga wata mota ta shigo da gudun gske mai bala’in kyau.
Tsayawa yay yaga wanda yake cikin motar da sauri ya zare ido waje.
Ganin Captain Ibrahimul Khalel ya fito sanye da uniform na Soldiers wanda sukai masa kyau ainun ka san cewar sa baƙin mutum sai Amy colour ɗin ya haska dark skin ɗinsa.
Ya Heemu gyara zaman glass ɗinsa yay yana ɗan tsosatar laɓɓansa masu kyau.
Da sassarfa haɗi da gudu kuma ya shige cikin reception ɗin hospital ɗin..
Daga gefe B.guy ya tambayi wani saurayi nan ya faɗa masa komai.
Cikin sauri kuma ya kira Abban Arman yana ɗauka yace.
“Akwai matsala fa, ashe Abu Maleek ne ya diro garin nan kamar wani mikiya”
Abban Arman yace.
“Sai kace jirgi mai saukar ungulo?”
Jibril yace.
“Gashi nan ya faɗa maka sunan, MIKIYA, shine abinda wasu mutanan suke faɗa masa, yana sauka a waje ne ba tare daya faɗawa kowa ba, sai dai kawai a ganshi, abinda baka sani ba, zuwa yanzu kuma shi ba Yarima bane, yanzu ya zama SARKI, kuma ina mai tabbatar maka wannan zuwan da yay bana haka kurum ba ne, akwai dalilin dan haka ka sanarwar da B.guy ya hanzarta barin wajan”
Mutanan da suka ɗauki Moha masu tsaya ko ina ba, sai wani ƙaton baƙin kango mai duhun gske da kuma ciyayi.
Suna zuwa suka sanyata saman kujera tare da ɗaure ta da igiya har yanzun kuma bata farka ba.
Wata waya suka ɗauka suka haɗa lantarki kana suka juna mata a jiki, wata zabura tayi sbd azabar da taji jikinta duk rawa yake tama kasa mgna.
Ga wani shock dake janta mai ɗan bala’in zafi.
Nan da nan ta fice a hayyacinta, tsayawa sukai da abinda sukai mata ɗaya ya ɗauki ruwa mai sanyin gaske ya kwara mata, azaba biyu ya haɗe mata sarai sun san Asma gareta kuma bata son abu mai sanyi ko kuma ƙura.
A hankali ta shiga kokawa da numfashinta tana jansa da ƙyar.
Tije yace.
“Maza kira wani ya taimaka miki”
Runtsa idanunta tayi abubuwan Shekaru masu yawa suka fara dawo mata, lokacin da gubara ta kama gidansu kuma ya rage ita ɗaya ce a ciki, ga wutar naci sosai, cikin tashin hankali ta shiga kiran sunan Ya Heemu.
Buɗe ido tayi taga gaba ɗayansu sun rufe fuskarsu, shiru tayi domin sam bata jin zata iya mgna.
Wayar lantarkin Tije ya ɗauka zai juna mata tai saurin faɗin.
“Dan Allah, kayi hqr ka rabo dani ina jin azaba idan ka sanya min, me kake so? Me nayi maka? Kaji tsoran Allah ka sake ni kana kallo bana da lfy”
Dry sukai Tije yace.
“Kawai ki kira sunan wani wanda zai taimaka miki ni kuma zan rabu dake”
Hawaye ne suka sami mata tace.
“Me za kuyi masa? Kada ko cutar da shi Mamana na son sa, Ummi na tana son sa shi ɗaya ya rage mata, Baffa na yana son sa yana kallonsa ma dadin Ɗan daya rasa, kayi min komai amma ka rabo dashi”
Wani gigitaccen mari ya sakar mata wanda yasa ta zubar da haɓo cikin neman taimako tace.
“Wayyoooo Teddy na”
Kallon juna sukai sai kuma sukace.
“Teddy? To ina jerry kuma?”
Kuka ta shiga hakan yasa suka ɗura mata Camera suka danna vedio’n, duk yadda suka su ta ambaci sunan wani ƙi tayi abu ɗaya ta faɗa tace.
“Teddy U promised me ba zaka ƙara bari wani illata ni ba, Teddy na stop pretending pls come back to your Jerry, I love you, na kasa jure wannan game ɗin I’m sorry Teddy”
Ta ƙare maganar tana kuka, da sauri suka danna sending wa Abban Arman, suna tsaye aka buɗe ƙofar wajan aka shigo wata budurwa ce mai kyau ta shigo, ta rufe fuskarta.
Cikin isa tace
“Ina son bayan kun gama komai ka kasheta kada ku barta da rai, domin muddin tana raye bazan samu cikar muradin rai na ba”
Kwallon ta sukai sai kuma sukace.
“To nawa zaki bamu?”
Dry tayi tace.
“Duk abinda kuka yanke shi zan baku, amma Tabbas kada ku barta da rai”
A razane Moha take kallon budurwar domin har abada baza ta taɓa mance wannan Muryar ba.
Amma Wacece wannan she look like familiar.
Gane cewa Moha na son gane ta yasa ta kwashi ƙasa mai yawa ta watsawa Moha a fuska sai kuma ta shiga kaɗa mata ƙura.
Ya Heemu suna zaune a office ɗin wanda yake ɗauke da manyan mutane masu faɗa a wajan, wani ne yace.
“Ko yau da safe an kwashe jarirai sama guda 20 a wannan Asibitin, Bama sanin yaushe ake satar sai dai a shafa aga babu wani jariri”
Ya Heemu kansa a ƙasa domin yana cikin damuwa sosai, musamman rashin wannan m.card ɗin da ace ya samu da tuni ya gama bayyana gsky kowa ya gani da idanunsa.
Wani magidancin mutum ne, mai cikar zati da haiba ga kwarjini na musamman a saman fuskarsa.
Yana cikin shiga ta Maroon ɗin Alkyabba, ma ratsin milk ɗin zare.
Ga farar Crown a kansa irinta SARAKAI.
Sai kuma wata lafiyayyiyar sandaar azurfa mai kyau sosai.
Sai manyan murjani a wuyansu wanda suka ƙarawa shigarsa kyau.
Kana ganinsa kaga a salin bayarabe.
Idanunsa a lumshe duk wannan Mgnar da ake baice komai, a zahiri ma bluetooth ɗin dake maƙale a kunnansa yake saurara.
Yana sauraran daddaɗar sautin muryarta mai cike da ƙuruciya da take tashi cikin sautin ƙira’a mai daɗin gske.
Yawan karatun kuma da take masa ne yasa gaba ɗaya ya sauya ya zama nagartaccen mutum mai riƙo da addini, ya kuya masa abubuwa da yawa musamman Azumin Alhamis da Litinin.
ABU MALEEK kenan.
A haka dai zance ya watse Abu Maleek ta bayan ƙofa yabi cikin kamala da nutsuwa ya shige mota kai tsaye sai airport.
Ya Heemu wajan marasa lafiya ya shiga dumawa.
Yazo dai-dai gadon wani tsuhu wanda yay kashi ya ɓata jikinsa, gashi duk suma ta cika masa fuska.
Kallon Dr yay yace.
“Meyesa ba’a kula da shi?”
Dr yace.
“Wannan yafi Shekaru a nan,duk sati akwai matar da take zuwa dubasa, amma kwana biyu shiru”
Lumshe idanunsa Ya Heemu yay yana jin bugun zcyarsa na ƙaruwa.
Cikin rashin jin daɗi ya tattare hannun rigarsa ya shiga gyara mutumin.
Sai da ya gyara sa tsaf ya sauya masa riga da kuma sheet.
Tsuhun hannunsa ya ɗura saman sumar Ya Heemu yana tunawa ka ɗan, tare kuma da hargitsawa ba tare da yay mgna ba.
Shiru Ya Heemu yay sbd wani sayi da daɗi daya shiga ratsa zcyarsa.
Zame hannun yay kana ya shiga kallon Ya Heemu baku ƙiftawa, shima kallonsa yake yana jin Wayarsa tayi ƙara amma yay banza da ita.
Da ƙyar yabar wajan da kuma al’ƙawarin dawowa.
Ya Heemu na shiga mota kiran Alhaji Al’mustapha ya shigo, zare ido yay ganin miss call sama da 50 gana Ummi Anuty Meera da Baba Haroon sai na Ya Areef, Answering yay yace.
“Uncle”
Alhj Al’mustapha yace
“How long wannan secret zai kasance? Gashi kana yin kuskure na biyu, bayan rashin samunta matsayin mata kana gab da rasata a rayuwar baki ɗaya”
Cije baki Ya Heemu yay yace
“Uncle what happened? Everything will be fine soon Uncle believe komai zaiyi dai-dai, amma kabar wannan Mgnar”
Alhj Al’mustapha yace.
“Na barta, tunda ka jure rashinta matsayin mata I’m sure zaka jure rashinta a duniya domin an sace Ayshatul-humaira”
Cikin ƙara ji Ya Heemu yace
“What? An sace Humairahhhhhh? When? How”.
Sai kuma ya kashe wayar a nan yaga vedio’n ɗin da aka tura masa, idanunsa har ruwa mai kama da jini yake fitarwa.
Muryarsa na rawa yace.
“Notin will happen to you Jerry”.
Yana faɗin hakan yaja motar da gudu yay gida.
A can hospital kam Likitoci sun duƙofa kan Ya Omer amma har yanzu ba’a samu kansa ba, sunan Moha kawai yake kira.
Ya Heemu yana zuwa gidan yaga babu kowa ciki hatta Ummi bata nan, Sharp-Sharp ya ɗauki abu ya sanya cikin aljihunsa, kiran Ya Areef ya sake shigowa ɗauka yay lokacin da Ya Areef ya shaida masa abinda yake faruwa da da harbin da akaiwa Ya Omer kashe wayar kawai yay ba tare da yace komai ba.
Yana gamawa ya fita waje Mannal dake cikin shigar pech ɗin jallabiya hannunta riƙe da waya ta tsaya ganin sun yi ido huɗu da Ya Heemu.
Kallon tsaf yay mata ganin tana shirin fita yace.
“Da izinin wa?”
Harara ta watsa masa tace
“Sai wani yaban izini? Kaji min yaro”
Inda take ya ƙara so ya shiga Kallonta tsaf idanunsa da sukai ja ya sauke a fuskarta..
Cikin tarin takaici ya sanya hannunsa ya riƙe Booms ɗinta da ƙarfi yace.
“Sbd kina da ƙaton Booms shi ne kike faɗin yaro ko, to bai birgeni ni bai taɓa birgeni ba, Ni nan da kika kallo na ba ƙaramin ɗan iskan yaro bane, ki shiga hankalinki da ina son nuna maki cewa ni ɗan iska ne a wannan har kar da tuni kin gane kuranki, idan haka ki iya bakinki, ina respect ɗin ki matsayin kin girman amma naci ƙaniyar girman, matsayi miji nake gareki mgnar wanka Tsarki kuma don’t worry yanzun da nake babba ma wlh sai kinyi bari na gama da abinda yake gaba na”
Kasa mgn tayi kanta a ƙasa tana jin yadda yake sauke ruwan bala’i kamar wani ubanta.
Matsawa tayi zata fita cikin wata gigitacciyyar tsawa yace.
“Nace da izinin wa?”
Zubewa tayi a wajan tare da sanya masa kuka tana buga ƙafafuwansa.
Tsaki yaja kana yasa duk hannayensa biyu ya sunkuceta ya mannata da ƙirjinsa, yana jin sanda ta sanya baki ta sakar masa cizo tana faɗin.
“Allah sai na faɗawa Ummi tayi min tsakani da kai, daka san inda zani da baka hanani ba, Allah ba zan yafe ba”
Banza yay mata dan bata gabansa har part ɗinta ya kaita kana ya cilla ta saman bed.
Da sauri ya juya ya sanyawa Ƙofar key.
Yana fita kiran Abban Arman yazo masa answering yay lokacin da yake shiga mota yace..
“Ka sakar min mata idan kana son na baka Yar uwarka, idan kuma ka shirya sakinta kazo ka ɗauki zcyr taka a nan gidan gona ta”
Murmushin jin daɗi Arman yay kana kuma ya sanya m.card ɗin a system cikin sauri Abban Arman ya miƙe yace.
“It’s fack, wannan ba shi ne m.card ɗin ba, wannan yaron wanne Irin tantiri ne”
Da sauri ya ƙara kiran Ya Heemu ya shaida masa yanzu m.card yake buƙata, Murmushi kawai Ya Heemu yay kana yace su haɗu sai ya bashi.
Da sauri kuma Abban Arman da Arman ɗin suka shiga mota, duk cewa har kawo lokacin bai san menene a cikin m.card ɗin ba.
Moha tayi suma yakai sau biyar gaba ɗaya kuma suka haɗu wajan.
Kallo ɗaya Ya Heemu yaywa Moha ya ɗauke kansa ba tare da wani abu ba ya ɗauki m.card ɗin ya bashi.
Kana suka kunce masa Moha, da sauri ya ƙarasa wajanta tare da tattaro ta gaba ɗaya zuwa Jikinta.
Dry Abban Arman yay sosai, kana yace.
“My boy jeka waje”
Fita Arman yay shi kuma Abban Arman ya kalli Ya Heemu daya ɗago Moha zuwa Jikinta, wacce take a sume.
“How market Captain Ibrahimul Khalel? Ya kake ji yanzu? Kasu tuna min asiri ko? To bari kaji nina kashe ubanka ta hanyar bashi goba, sannan ni na kashe maka Safa ta hanyar zura mata ƙarfe a gabanta aka shanye jininta tass, daman badan Allah na aureta ba”
Cak Ya Heemu ya tsaya sai kuma ya kalli Abban Arman yace.
“Abin me sauke yanzu na faɗa maka, kuma babu yadda zakai ka tuna min asiri, kuma zanci gaba dayin abinda nake”
Wani ruwa ne ya taro a idanun Ya Heemu yana kallon Abban Arman yace.
“You killed my father?”
Kamar daga sama yaji saukar Mannal tace
“You’re father is still alive”
Da sauri Abban Arman ya juya ya kalli Mannal wacce idanunta Yay jaa sosai, kasa mgn Ya Heemu yay sai Kallonta kawai da yake da sauri Abban Arman yace.
“Ƙarya kike kuma yanzu zan maida aure na dake”
Murmushi kuma Ya Heemu yay yana gyara Murya da kuma riƙe Moha a jikinsa yace.
“In”
Kafin wani tunani kuma wasu jami’an tsaro suka shigo wajan, kana ya zaro sabon m.card a cikin aljihunsa ya cillawa wani ɗan sanda.
Kana ya juya sai fita kenan yaji saukar alburushi a tsakiyar bayansa.
Runtsa idanunsa yay sosai sbd a zaba da kuma raɗaɗin zafin daya ziyarce sa.
Ganin Moha ta buɗe idanunta yasa ya cilla idanunsa cikin nata, suka shiga kallon juna idanunsa yana fidda hawaye kaɗan.
Tashin hankali kenan Mannal kasa motsi tayi sbd wanda taga an harba ga kuma budurwar dake tsaye a bayan Ya Heemu riƙe da bindiga.
Ƙara saita bindigar tayi ta ɗan yi ƙara hakan yasa Moha ƙoƙarin juyawa da sauri yasa tattausan hannunsa ya mayar da Idanunta cikin nasa wanda a lokacin sosai hawaye suke fita daga cikin idanunsa.
Da sauri kuma jami’an tsaro suka nufi kan budurwar kafin su ƙarasa ta ƙara sakarwa Ya Heemu wani harbin a tsakiyar bayansa ƴar ƙara ya saki tare da ƙanƙame Moha dake jikinsa, da gudu Mannal tayi kansa tana faɗin.
“No Ibrahimmm”
Bai yarda ya faɗi ta gaba ba dan haka yay baya idanunsa na lumshe yana ƙara ƙanƙame Moha a jikinsa tare da ambaton sunan Allah.
Kafin ya faɗi Mannal tayi saurin ƙarasawa ta zube a bayansa ya faɗa Jikinta Moha kuma idanunta ne ya sauka kan budurwar da mmki tace SHOONA….