AUREN FANSA CHAPTER 7 BY ✍🏾 NIMCYLUV

AUREN FANSA CHAPTER 7 BY ✍🏾 NIMCYLUV

                   Www.bankinhausanovels.com.ng 

Safa ta rasu? Shi ne abinda Abban Arman ya shiga faɗa yana girgiza kansa alamar sam bai yarda da wannan zan can na Baba Ladi, bai tsaya jin me zata faɗa ba yay saurin shigewa ɗakin, kwance ya sameta samɓal fatar jikinta ta ƙara hske alamar jinin dake cikinta ne ya ƙare.

Idanunsa ya mayar kan bedsheet ɗin yaga har da gudan jini zubewa yay wajan yana faɗin “Na shiga uku na kashe Safa, da wanne bakin zanwa ƴan uwanta bayani? Da wanne ido zan kalli Ruma? Da wann ido zan kalli Ya Heemu?”.

Da sauri kuma ya miƙe yana ɗan ɗaukan wata kwalba ya shige wani room ya rufe, ya daɗe ciki kafin ya fito sanye da fararan kaya.

Wajan bed ɗin ya ƙarasa yaja duvet ya rufe mata jiki kafin ya ɗauki wayarsa zuwa waje.

Lumshe idanunsa Ya Heemu yay haka kawai yay bacci ya kasa ɗaukan idanunsa daya rufe sai yaga Safa nayi masa gizo tana kuka, Mirginawa yay yana ɗan shafa ƙirjinsa a lokacin kuma wayarsa tayi ƙarar ganin sunan _My Luv_ na yawo yasa yay answering call ɗin tare da mannawa a kunansa yana ɗan fidda emotional sound mara sauti, kukan Safa ya daki dodon kunansa.

Da sauri kuma ya miƙe tsaye yana dafe kansa sbd jin tana kiran sunansa, ya buɗe baki zai mata mgn kenan yaji wayar tayi ƙara daga nan kuma ya fara jiyo surutan Abban Arman jin Safa na ihun neman ɗauki yasa Ya Heemu yay saurin katse kiran dan ya riga ya tabbatar da abinda Abban Arman yake mata shi wlh yama manta cewa ana wannan abun idan anyi aure.

Fasa kwanciyar yayi ya kashe wayar baki ɗaya yay waje abinsa, yana fita ya samu Ummi a Parlo tana zirga-zirga, tana ganinsa ta nufesa tana faɗin “Ya Heemu mene ya fito da kai?” Juya mata idanunsa yana karantar yanayin ta, ganin kamar bata nutsuwarta yasa ya ɗan fito da hannunsa daga aljihu ya riƙeta, walking slowly ya nufi part ɗinta da ita, yana zuwa yaja ya tsaya kamar bazai magana sai kuma yace “Enter Ummi” hawaye ne ya sauka idanunta wanda yasa Ya Heemu saurin Kallonta domin Rabon da yaga hawaye a fuskar Ummi harya manta, cike da soyayyar mahaifiyar sa yay saurin riƙeta yana faɗin “Ummi kuka, at this hour? Ya rabb” ya faɗa yana taune bakinsa riƙe hannunsa tayi tace “Ibrahim Khalel wlh ina jin kamar wani abu zai faru, tsoro na keji na kasa bacci tunanin Mahaifinku da Auta ya hanani sakat” Ajjiyar zuciya ya sauke sbd fahimtar rashin Safa ke damunta, shima the same da abinda ta keji ya keji amma shi baya barin damuwa tayi tasiri a kansa ne, ganin Yadda duk ta kiɗime yasa ya rungome ta cikin ƙasa da murya yace _”Ummi”_ kansa ta shafa tana sauke ajjiyar zuciya tace “Ya Heemu na” lumshe idanunsa yay yace “Just pray, nothing will happen in sha Allah!” Kaita ɗaga tace “I hope so…Aboki” Lallausan murmushi yay domin duk sanda Ummi tace masa _Aboki_ to ta tuna mahaifinsa ne, kwantar da ita yay kana ya kashe mata hasken ɗakin yay waje abinsa.

A babban parlo ya zauna tare da miƙar da ƙafafuwansa a saman senter table, daga shi sai boxer domin bai son ko kayan bacci ne, wannan dalilin yasa Anut Meera ke tsokanarsa tana faɗin haka zai ta zama tsirara bako kwailliya domin Ya Heemu bai taɓa sanya manyan kaya ba.

Idanunsa yaja ya rufe sai a lokacin ya samu damar yin tunani akan guy Asibitin nan, har yanzu ya kasa fahimtar ta ina zai fara.

Cikin dare Moha ta buɗe idanunta ganin ɗakin duhu yasa tai saurin miƙewa tana mmkin wanda ya sauya mata kaya zuwa na bacci, rigace iya cinyarta gashinta a tufke ya sauka bayanta, ko bedroom sleeper bata tsaya nema ba tai waje bayan ta buɗe kofar, tsoro fal cikinta dan bata ita bacci idan babu wani kusa da ita, ga wata yunwa da ta keji domin ya zame mata jiki shan tea cikin dare.

Siririyar Ajjiyar zuciya ta sauke ganin ɗan ƙaramin hske a parlon kai tsaye ta nufi kitchen tana addu’ar samun ko black tea ne, dubawa ta farayi babu dan haka ta kunna heater ruwan na zafi ta haɗa komai ta zuba a mug ta ɗauki spoon ta fara juyawa, tsaki taja kana ta kafa mug ɗin a bakinta, da sauri ta janye tana sakin kuka sbd wani azababban zafi daya ratsa mata harshe nan take kuma harshen ya fara mata zugi da raɗaɗi, ajjiyewa tayi tai waje da sauri, tana cikin tafiya tai karo da ƙafarsa wacce take saman table yana jinta tun fitowar ta ta farko amma miskilanci irin na Ya Heemu bai sa ko ido ya buɗe ba bare yay tunanin zuwa yaga mene ya sata kuka.

Moha ganin baƙar ƙafarsa mai ɗauke da wasu dugwayen gashi masu kyau da ɗaukan idanu, yasa ta sauke ajjiyar sai kuma ta murguɗa baki, zafi ne ya ƙara ratsa ta wanda yasa tai saurin zama kusa dashi tana fito da harshen ta waje sbd ta samu salama, idanunta ta buɗe ta sauke saman ƙyakkyawar fuskarsa mai kyau da haiba, tun daga kan haɗaɗɗiyar kirarsa ta fara Kallonsa zuwa dugun sirirn hancinsa irin nata, sai kuma jajayen laɓɓansa masu ɗan kauri wanda gashin baki yay masu ƙawanya kaɗan hakan ya ƙara haddasa fitar jansu.

Tsaki tayi a fili tace “Black is beauty, Ya Heemu kana da kyau baƙar fatarka irin ta mugwaye nada kyau, amma sam Zcyarka bata da kyau” ta faɗa tana ƙara murguɗa masa baki kai kace yana kallonta.

Duk abinda take faɗa yana jinta a hankali ya sanya hannunsa ya kashe raguwar hasken parlon, nan take Parlon yay duhu ko hannunta bata iya gani, tsoro ya kama Moha, ga azabar da harshen ta yake mata har tana ji kamar fatar wajan ta sutale, ganin da gske Ya Heemu bacci yake ta lallaɓa a hankali ta haye jikinsa tare da ɗura kanta a ƙirjinsa ta zagaye hannayenta a west ɗinsa, Ɓoyayyiyar ajjiyar Zcy Ya Heemu ya sauke bata tare daya bari ta bayyana ba, daddaɗan ƙamshin turarensa ya daki hancinta ga wani iska mai daɗi dake fita ta bakinsa, taɓe baki tayi tana karkaɗa harshe ta sbd azabar da yake bata tace “Lallai gayan nan hancinsa na son ƙamshi sai faɗin rai” sai kuma tai sama da fuskarta zuwa dai-dai tasa tana jin yadda Numfashinsa ke fita cike da nutsuwa ga iskar dake fita daga bakinsa daya ɗan buɗe, iskar ta daki harshen ta, sai taji zugin ya ragu wani sanyi na fara ratsa tongue ɗin nata, runtsa idanunta tayi tana kwaɓe fuska tare da sakin kuka sbd wani kalar raɗaɗi da yake mata ganin bakin Ya Heemu a ɗan buɗe yasa a hankali kamar mai tsoro ba tare da tunanin abu bai ko sanin muhimmancin abinda take ta ɗura bakinta saman nasa tare da zura tongue ɗinta, Wata lafiyayyiyar ajjiyar zcy ta sauke sbd sanyin daya ratsa harshen ta, Ya Heemu kam mutuwar zaune yay a ransa yake faɗin “Shigiya da fuska kamar gurasa, kamar an silala kazar Bature, yarinya ƙarama tasan tasa bakinta ana wani”..

Datse bakinsa yay da harshen ta a ciki Moha ta shiga zare ido sai zafin ya ƙaro sbd wajan ciwon ya datse, da sauri ta ƙanƙamesa tana sakin kuka, fararan idanunsa ya buɗe kafin a hankali ya danna light ɗin Parlo dumn light ya bayyana, idanunta ƙuri a kansa, fuskarta ya shiga ƙare wa kallo ganin yadda tai jajir sai zufa take haɗawa a nan kuma ya fahimci azabar da take sha, bakinsa ya buɗe da sauri ta zame harshe ta tana fito dashi tare da firfitawa da hannunta, duk abinda take kuka take mara sauti hawaye na sharara idanunta, narkakkun idanunsa ya sauke a kanta na wani lokaci kafin ya sanya tattausan hannunsa ya juyo da fuskarta garesa, matsuwa yay sosai kamar zai haɗe fuskarsu tana Shirin yin kuka yasa hannu ya buge bakin can ƙasan maƙoshinsa yace “Shiru dan Ubanki” jin muyarsa a kaushashe yasa tai shiru tana zubar da hawayen, kamar bazai magana ba sai kuma ya ware baki yace “Meye?” Da hannu ta nuna masa tsinin harshen ta wanda yay jaa tana shassheƙar kuka tace “Tea ya ƙonani Bapii yake min” fesar da iska yay “Uhm” kawai yace yana ƙarewa wajan kallo sosai fatar wajan ta cire wajan yay jaa, a kasalance yace “Kina son na hura maki?” Kaita ɗaga masa, baki ya taɓe yana yasanya hannunsa ya gyara mata zama sosai saman ƙirjinsa kafin yay copping face ɗinsu, “Muga” ya faɗa yana tattare mata gashin kanta harshen ta fito dashi, ganin haka yasa yaja idanunsa ya rufe yana ware bakinsa tongue ɗinta ya faɗa ciki, ƙamshin strowbeery ya daki hancinta tai saurin kallon bakinsa taka nrml yake sai saliva daya jiƙa laɓɓansa, a hankali ya haɗe bakinsu kana ya ɗura tsinin harshen sa, saman nata kafin yasa laɓɓansa ya kama wajan cikin nutsuwa ya fara wura mata iska, Ajjiyar zuciya ta fara sakin tana ɗan ƙanƙamesa, zata iya cewa rabon da suyi very close da Ya Heemu ta manta Tun tana yarinya ba shiri suke ba duk da yanzun ma yarinyar ce ita.

A hankali Ya Heemu ya dinga hura mata iska ganin kamar ta samu sassauci, yasa ya tsaya yana fesar da numfashi still idanunsa a rufe yake, tongue ɗin ya bari cikin nasa yana jin bacci na ɗan fisgarsa, Moha ji tayi zafin ya dawo cikin baccinta ta buɗe baki zatai kuka yay saurin cakfar harshen ya fara mata wani small tsotsa dai-dai wajan wanda shi kansa bai san yayi ba, bacci ne sosai a idanunsa, tsitt tayi ta maida idanunta ta rufe a haka bacci ya ɗauke ta.

Kiran sallar farko na Subhi Ya Heemu ya buɗe idanunsa da sauri ya ƙarasa buɗe su sbd ganin Moha maƙale a jikinsa da manna bakinta a ƙirjin shi kuma ya kifa kansa a wuyanta.

Miƙewa yay da ita a jikinsa yana jan tsaki, yana tashi ya saketa a ƙasa yana jine da sanya ihu kota kanta bai bi ya shige part ɗinsa yana ɗan haɗa hanya, sam ban san yaya akai harya sakewa wannan yarinyar ta raina sa haka ba, tsakie ya ƙara ja a ransa yake faɗin “Da ido kamar gurjiya” bathroom ya faɗa ya sakarwa kansa shower then ya ɗaura alwala tare da zura wata farar Jallabiya mai taushi, part ɗin Ummi ya nufa yana zuwa ya sameta saman Dadduma, daga nan ya shige part ɗin su Anut Meera da Anut Suwaiba yaga suma sun tashi.

Mai tsaye Mosque ya nufa ana idar da sallah ya dawo gida sbd zai mutsa jiki, harya shige part ɗinsa sai ya dawo da baya ya nufi wani part nada ban inda su Shoona suka kwana zaune ya samesu suna azkar, idanunsa ya shiga juyawa yaga bai ganta ba kamar Shoona ta shiga ransa tace “Mrng Ya Heemu, Moha taƙi tashi” shigewa ciki yay ba tare daya amsa gaisuwar Shoona ba, tayi ɗai² a saman bed ta a sharar bacci ɗauke kai yay ya nufi fridge ya ɗauki gorar ruwa mai sanyi ya sakar mata a jiki, wata Ajjiyar zuciya ta sauke tare hantsilawa gefe ta buɗe baki zatai ihu ganinsa tsaye a kanta yasa ta kumbura fuska, Miƙewa tayi ta nufi bathroom a fili yace “Da jikin kamar ganye” murguɗa masa baki tayi tace “Eh ɗin kai kuma kullum ƙara baƙi kake” hannu ya miƙa zai riƙeta ta kurma Ihu tana shigewa cikin bathroom.+

STORY CONTINUES BELOW

Abban Arman kasa bacci yay tun daran ya faɗawa Arman har yanzu Arman ya kasa cewa komai da idanu kawai yake kallon Mahaifinsa so yake yaji wacce Moha ɗin ce ta rasu domin ya kasa fahimtar komai, lokacin da labari ya jewa Su Ya Heemu Ummi ɗan ƙaramin hauka ta kusayi, Ya Heemu sam baka gane halin daya shiga, Moha,Hannah, Shoona sunci Kuka kamar me, Baffa addu’a kawai yake, Ya Heemu banda sakin ajjiyar zcy da fesar da numfashi babu abinda yake da kansa ya sanya Safa a kabari, a lokacin Arman ya sanya kuka yana jin kamar ya bita da ƙyar aka kanyesa, lokacin da Mannal taji rasuwar sosai ta girgiza dan haka ta shirya zuwa yiwa Ummi Ta’aziyya., har zuwa sati guda ko Ummi bata sanya Ya Heemu a idanunta ba, bata sanin inda yake bare tasan halin da yake ciki, ita kanta ta rame tai wani iri rasuwar Autar ta Safa ya girgiza ta, yanzu bata da wanda ya huce Ya Heemu shi kawai take kalla taji daɗi, har lokacin kuma basu san dalilin rasuwar Safa sbd ba wani bincike akai akan gawar ba.

_After 40 days_

Baffa ne zaune a ɗakinsa yana cin zogala sai Moha dake kusa dashi tana kuka “Allah Baffa bana son boarding school ɗin nan, dan Allah kayi wa Ya Heemu mgn ya barni a nan, sai Ya Omer ya kaini Day school tunda ya dawo” Shoona dry kawai tana so taji me Baffa zai ce mata, sai daya kammala cin zogalan kafin yace “Matar na baki shawara zaki ɗauka?” Kai ta ɗaga tana kwanciya saman cinyoyinsa yace “Ki kwantar da hankali kije gidan Ruma ki samu Yayan naki a nutse ki faɗa masa ra’ayinki kinga idan kikai hakan zafi fahimtar ki, amma ni bana da iko akan hakan kin san fa Ibrahimul Khalel kaifi guda ne, yanzu nima zai fara fushi dani daman rabon dana gansa harna manta” shiru Moha tayi tama rasa me za tayi harga Allah bata ko ƙaunar Ya Heemu ta tsane sa tsana kuma mai yawa, baki ta buɗe zatai mgn taji sallamar Ya Omer ta sauri ta tashi tana ihu tuni hular kanta ya zame gashinta ya sauka ƙasa, Ya Omer ita kawai yake son ganin dan yay missed a lot of things nata, Tunda ta fito yake kallonta musamman da yaga ta ƙara girma ƙirar jikinta sun fara bayyana a fili, tana ganinsa ta nufi inda yake zata faɗa jikinsa tana ihu, da Sauri Ya Heemu dake tsaye bayan Ya Omer ya juya tare da ficewa daga gidan baki ɗaya.

Bata ƙarasa inda yake ba yay saurin kaucewa yana girgiza mata kai tare da sakar mata murmushi, marai-raice fuska tayi zatai kuka yay saurin riƙe hannunta yana faɗin “Sorry abar ƙauna, ba kinga kin zama big gal, idan kika rungome ni ai sai a samu matsala” ita bata gane karatun nasa ba tace “Wlcm Ya Omer, wlh nayi missed naka” Yana nufar ɗakin Baffa yana faɗin “Nima nai kewarki sosai abar ƙauna” Ya Omer fari ne tass saɓanin  Ya Heemu wanda yake baƙi irin asalin baƙaƙen nan, amma duk kallo guda zakai masu kasan ƴan uwa ne, Zama Ya Omer yay dab da Baffa idanunsa akan Moha wacce girmanta yake bashi mmki, yace “Baffa Na sameku lafiya?” Baffa dake kallonsa yake kallon Moha yaga yadda take farin ciki don rabonsa da yaga tana farin ciki haka harya manta hakan yasa yake sha’awar wani abu a ransa “Umaru ka iso Lfy? Ya garin turawa” Moha ta ɓata fuska tace “Haba Baffa yaya zaka ɓata masa suna” Ya Omer yace “Allahamdulillah ɗan tsuhu mai ran ƙarfe”  Shoona tace “Ya Omer sannu da zuwa” Kallonta Yay yace “A’a Indo ykk ina Hannah” taɓe baki Moha tayi tace “Ya Omer ban san me nai mata ba, ko inda nake bata zama ko mgn nai mata ba amsawa shiyasa nima na rabo ita” Ya Omer yace “Are sure baki mata komai ba?” Kai ta ɗaga masa yace “Ok bari tazo” Shoona tace “Tana ɗakin Inna” kafin Yay mgn an buɗe labulan ɗakin an shigo, Dadɗan ƙamshi _nautica voyage_ ɗinsa ne ya kawo wa hancinta ziyara da sauri ta haɗe fuska tana turo baki gaba, cikin ƙaramin lokaci fara’ar fuskarta ya ɗauke,  yana sanye da wata royal blue suit wacce ta fito da zallar kyansa ta haska baƙar fatarsa, idanunsa a ɗan Lumshe yaja ya tsaya yana cije lips ɗinsa, ganin hakan yasa Baffa faɗin “Ibrahimul Khalel mutanan sun Mutsa kenan?” Ko buɗe ido bai ba bare yay mgn, Hanna ce ta shigo ɗakin taɓe baki Moha tayi Shoona kam a ranta take faɗin “Iska na wahalar dame kayan kara” shigowa tayi sarai taga Ya Omer tai kamar bata ganshi ba sai da ya sakar mata Murmushi yace “Indo kenan bari ni na gaida ki” Tsaki Moha taja kafin ta miƙe tsaye tabar ɗakin Ya Heemu kallon Baffa yay yace “Baffa zani Bangkok” Baffa yace “To tafiyar ce baka so kake haɗa rai ko mene?” Hanna idanunta ta sauke a kansa suka haɗa ido saurin janye nata tayi Baffa yace “To kwana nawa zakai?” Ya e nayin waje yana faɗin “Shekaru dai” yana faɗin hakan yay waje tare da nufar ɗakin Inna, tana zaune tana faɗin “To ni da kike min kuka a nan me nayi maki? Kaji ni da yarinya” Ya Heemu yana daga bakin ƙofa ya leƙa fuskarsa yaga Moha kwance a ƙasa tana birgima taɓe bakinsa yay kafin yace “Inna Zani Bangkok wasu Shekaru” Da sauri Moha tace “Allahamdulillah Ya Allah” da mmki yake kallonta lallai Allah kaɗai yasan tsanar da yarinyar nan take masa shiyasa gaba ɗaya ta fice a ransa, bai tsaya jiran me Inna za tace ba yay waje abinsa.

Mannal ce zaune da Ummi suna Shira tun safe ta sauka daga nan gidan Uncle ɗinta zata huce, Miƙewa tayi tace “Bari naje bada mota nazo ba kada dare yayi”  tana sanye da blue ɗin Abaya wacce tai masa kyau sosai ta ƙara ɓoye shekarunta, tai fresh da ita, Miƙewa Ummi tayi suka fara fita waje suna zuwa motar Ya Heemu na parking Ummi tace “Bari Ya Heemu ya kaiki” kamar Mannal ba zatai mgn sai kawai tace “Ashe yana nan” Ummi tace “Yana nan fa” Mannal kam rabonta dashi tunda ya kaita asibiti tace “Ya Heemu manya” tsaiwa ta gyara sbd sabon da sukai duk inda take shi da Arman idan suka ganta sai sun rungome ta, ga mmkinta ko inda take bai kalla ba,  Yana shirin shigesu Ummi tace “Ka sauke wannan juyayyiyar fuskar taka ka kai Mumynku gidan Uncle” juyawa yay ya shiga motar Mannal tabi bayansa bayan sun yi Sallama da Ummi, tunda suka ɗauki hanya mgn wanna bata haɗa su, sai ajjiyar zcy kawai da yake saukewa har mmkin Ajjiyar zuciya take bawa Mannal, driving kawai yakee yana fesar da numfashi a hankali kuma ya fara parking gaban wani tafkeken ruwa wanda ake shan iska a wajan ga mutane nan kala daban-daban, ganin Yay parking yasa Mannal kallonsa tace “Ya Heemu lfy dai? Meke damunka?” A karo na farko ya ɗaga narkakkun idanunsa ya sauke a kanta da sauri ta janye nata idon taji gabanta ya faɗi ɗauke idanunsa yay yana kallon cikin ruwan kamar daga sama taji yace _”I LOVE YOU MANNAL”_ da sauri ta juya taga ko inda take baya kallo ita dai duk wani iri take jinta ganin bai sake cewa komai ba yasa ta sauke Ɓoyayyiyar ajjiyar domin ta tsorata, wayarta ta ɗauka ta fara dubawa taga ko anyi Posting littafin SIRRIN MU domin tana son taji Soyayyar SHEIKH da FANNAH, wannan karan a hankali taji saukar Muryarsa yace “You’ll marry me MANNAL?” A gigice ta ɗaga Idanunta wannan karan suka haɗa ido zcyarta ta shiga bugawa da ƙarfi, anya Ya Heemu yasan me yake cewa? She’s like mother to him amma yake faɗin haka, ita da take sa’ar mahaifiyarsa da babu bambanci a shekarunta dana Ummi yake faɗin haka, Ya Heemu dake sa’an ɗan cikinta, kasa mgn sai ta buɗe motar zata fita yay saurin danne hannunta da tattausan hannunsa ya sawa motar key!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *