AUREN FANSA CHAPTER 9 BY ✍🏾 NIMCYLUV
Www.bankinhausanovels.com.ng
Wani kuka ne ya kwacewa Mannal Lokacin data gama tuna irin ɗibar albarkar da Abban Arman yay mata, wani baƙin ciki da take kaici da keji.
Ace mutumin da tafi ƙauna fiye da kowa idan ka ɗauke ta mahaifinta shike nuna mata rashin daraja, mijinta Uban yaronta Arman gashi dalilin wulaƙanci da yay mata har hakan na sawa ɗan cikinta yace yana sonta?.
Yau Ya Heemu ke mata abinda yaga dama abinta a mafarki bata kawo wannan bare a zahiri? Ɗan yaro kamar Ya Heemu har yashe ya gama girman ta gama yi masa wanka ta goyashi a gadon bayanta, ta bashi abinci yay mata tunbuɗi yay mata tsari amma yau shike mgnar yana son auranta? Ina sam ba zata iya wannan abun kunyar ba ta auri Ya Heemu tace ta auri me? Yay mata me? Bayan shi kanshi ta raina sa banda shirme shida Arman mene suka iya? Yadda take kukan sosai iya ƙarfin ta sai riƙe Ya Heemu take sbd yadda take jin zcyarta na zafi tana harbawa kamar zata fito waje.
Idanunsa ya buɗe kaɗan yana kallon yadda take kukan kana ganin kukan kasan bawai iya na yanzu bane, ta daɗe tana tarawa kuma tana neman inda zata sanya kanta tayi kukan wanda zai gamsar da zcyrta, hakan yasa faffaɗan ƙirjinsa ya zame mata mafaka.
Ƙara matsota yay sbd zafin da ƙirjinsa ke masa.
Bai san yaya ake ba bai san kuma ta inda zai fara ba, sam sam bai san yadda zai rarrashi mace ba, baya ƙaunar yaga kukan mace, amma a yanzu kukan Mumy yaushi ma yake basa, ya ɗauka Moha ce kawai mai baki kuka sai gashi yaga kakar Moha na kuka da Dukkan ƙarfinta kasa mgn yay sai hannunsa kawai daya sanya a bayanta ya shiga bubbuga bayanta alamar rarrashi can maƙoshinsa yace “It’s okay Mumy na!” ya faɗa yana janyeta daga jikinsa, hawayen fuskarta ta share tass tai kamar batai kuka ba sai Ɓoyayyiyar ajjiyar kawai da take saukewa a fakaice.
Cikin ƙarfin hali da juriya irin na jarumar mace wacce bata son ko kaɗan aga rauninta ta tsare Ya Heemu da gajiyayyun idanunta wanda sukai ɗan ja kafin ta ɗan cije baki tace.
“look at you! Gaba ɗaya baka gama kaiwa minzinlin wanda za suce suna son aure ba, bare har kayi tunanin yi, amma kai ne za kazo kace kana son…,” Baƙin cikin ƙarasa maganar take sai kawai ta ɗauke kanta tana mai fesar da iska daga bakinta.
Juyawa tayi ta fara ɗaukan Vail ɗinta kana ta ɗauki sauran abunta ta ɗauki trolley dinta ta fara janta zuwa baƙin ƙofa, ta ɗauki niyyar a yau komai dare sai tayi aure da dai ta zauna wannan ɗan cikin nata ya tuzarta.
Ya Heemu kam ko buɗe idanunsa bai ba bare ya san abinda take aikatawa, haka kuma dukkan Mgnar da tayi yay watsi da ita a gefe da baya son iyaye Yes! Yasan Mumy a haife ta haifesa domin idan bai manta yanzu shekarunta kusan 47 a yadda take faɗa to yanzu suna ƙarshen shekara kenan gab take da shiga shekara ta 48, taɓe baki yana ɗan shafa ƙirjinsa sbd tunawa da yay gaba ɗaya shi bai huce 22, kenan ta ninninkasa a shekaru da komai ma.
Da ace zata san dalilin auranta da sam bata tsaya tai masa dugun surutu ba infact ma zai iya sakinta idan buƙatarsa ta biya.
Jin ƙarar buɗe ƙofa yasa ya buɗe idanunsa tare da saukesu a kanta, tayi rolling kanta da Vail hannunta riƙe da hand-bag ɗinta sai phone ɗinta ɗaya hannun kuma tana janye da trolley ɗinta.
Mumy nada ƙiba mai ɗaukan hankali mara muni hakan yasa duk kayan da zata sanya suke bala’in yi mata kyau..
Gata ƴar wanka sam bata yarda da ƙazanta ba, kullum cikin gyara jikinta take da mgani masu kyau irin na gyaran brest, da taushin fata ga yawan shan fruits masu gina jiki, gashi tunda tayi ɓarin nan tasa akai mata ɗinki kullum cikin kula da wajan take tana shan maganin matsi dana Ni’ima badan komai sai tunanin wata rana zata iya komawa gidanta wajan mijinta abin alfaharin ta.
Kallonta yay yaga fuskarta cike annuri ko kaɗan baza ka taɓa cewa tayi wani abu wai shi kuka ba, ta haɗiye dukkan ɓacin ranta ta barshi a Zcy, cikin takon ƙasaita cike da kuzari da nuna shi ɗin Namiji mai cikakken iko wanda yake zaune akan ra’ayinsa idan yace zai yi ba shakka sai yayi dan haka a nasa ɓangaren shima ya ɗauki alwashi sai ya aureta no matter what happen!.
Tana ƙoƙarin buɗe ƙofa yay saurin sanya tattausan hannunsa ya riƙe trolley dinta da sauri ta kallesa fuska ba walwala ba tare kuma da tace komai ba tasa hannunta saman nasa da niyyar zame hannunsa yay saurin riƙe hannunta yace “Uhm sai ina?” Banza tai masa bayan ta zame hannun nasa ta buɗe zata fita yay saurin sanya hannunsa ya danne ƙofar idanunsa ya cilla cikin nata ba tare da shakka ko fargaba ba yace “Tabbas ni Ibrahimul Khalel zan nuna maki na haifu wlh billahi sai na aurenki idan ki kaga hakan bai faru ba to Tabbas sai dai HUKUNCIN ALLAH!” hannu tasa ta wankesa da mari buɗe ido yay sosai this is the first time da aka taɓa marin baƙar fuskarsa mai cike da haiba da Kamala, kafin ya ƙara wani tunanin ta ƙara sauke masa wani marin cikin warning ta shiga nunasa da hannu tace “You’re mad Khaleel, idan ƙwayar da ake baku wajan aiki tasa kake min haka to You better wake up, kai ɗan ciki na ne kuma na rantse maka ko zaka mutu ni Mannal bazan taɓa auranka ba, And mai ƙwaryar sama taci bare ta bawa ta ƙasa? Wait! Wait! I wonder why kace kana sona kana son Aure na kenan zaka iya cewa kana son mahaifiyar ka Ruma?”
Tunda ta fara mgn ya tsare ta da narkakkun idanunsa yana jin abinda take faɗa sam babu regret na abinda ya aikata, baza ka taɓa cewa shi ta mara ba to wanda aka daka a ƙirji har jini ya fita ya shanye dukan bare wani small mari? Jin ta ambaci sunan Ummi yasa yana shafa sumar kansa yana hargitsa ta dan Tabbas idan bai hakan ba zai iya yin abin bashi kenan ba.
Gyara tsaiwa yay ya matsa dab da ita kamar zai shige jikinta ya shiga Kallonta frm head to toe kafin ya ɗan taune bakinsa ya shiga tsotsa da sauri ta janye idanunta tana kallon rashin kunya zallah irinta Ya Heemu ita dai data Auri wannan wlh gwamma ta mutu ba aure ai kunyar duniya ta isheta da gorin mutane ace ta auri ɗan cikinta, saukar kamilalliyar Muryarsa taji yana faɗin “Mene? Ahaaa! I get it mai ƙwaryar sama yaci bare taba na ƙasa ko? Kina nufin me nake dashi bare na wadatar dake dashi ko? Ok bari na nuna maki”
Ya faɗa yana ɗura hannunsa a wandonsa shi kansa ƙarfin hali yake domin nan take tsoro ya kamashi haka kuma kunyar mgnar yake yasan ko me za’ai masa ba zai taɓa aikata abinda yake niyyar yi ba.
Ganin abinda yake ƙoƙarin yi Mumy tai saurin rufe ido zcyarta ta shiga harbawa domin nan take idanunta ya fara gane mata ƙyakƙyawan baƙin gashin da yake kwance lubb saman mararsa sai sheƙi suke alamar suna samun kulawa ga tudun marar data gani.
Tsoro da fargabar abinda zai biyo baya ya gama cikata if ya aikata abinda yake faɗa fa? Da sauri ta ɗauke numfashinta tare da runtsa idanunta tana jin bugawar zcyarta, kafin tayi wani tunani ta jishi kusa da ita dai-dai kunanta yace “Mrs Ibrahimul Khalel be careful ni namiji ne kuma ba lusari ba kuma aure na ni dake babu fashi” ya faɗi hakan ya bata light kiss a goshinta kamar yadda suka saba yi mata Shida Arman.
Yana yin hakan ya fice daga ɗakin yana tafe yana waƙar Arman Maleek!
Yana fita ta ƙarasa gaban mirror sai huci take idanunta yay jajir huci take kamar zata fashe dan baƙin kallon kanta tayi a mirror tace “Uhm Well-done Abban Arman, ka gani? Kaga abinda ka jawa kimata da mutumcin na? Uhm daka barni gidan wazai nemi cimin mutuncin Ohhh! Ya rabb”
Ta faɗa tana sauke huci mai zafi da ɗan hanzari tana kame kanta taja trolley zuwa waje, a downstairs ta samu Khausar da Arman kallo ɗaya yay mata yaga damuwar dake shimfiɗe a saman fuskarta idan zata ɓoyewa kowa damuwarta to tabbas babu shi ita ta haifesa ta kawosa duniya ta goyashi a bayanta wani lokacin ta haɗa da Ya Heemu ta goyasu, kasa ce mata komai yay Khausar tace “Mannal badai tafiya ba” ɗauke kai tayi kamar ba zatai mgn ba sai kuma tace “In sha Allah” Arman ya tashi tsaye tare da ɗaukan trolley zuwa waje Sallama sukai da Khausar tabi bayan Arman, a compound ta samu Ya Heemu da Uncle suna mgn ko inda suke bata kallah ba shi kuma Uncle ya Mannal ya kalli Ya Heemu a ransa yake jinjina ƙarfin rashin kunya irin ta Ya Heemu.
Arman kai tsaye Office ɗin Abbansa ya nufa da ita, Abban Arman na zaune cikin dakakkiyar shadda ƴar gaske shima da sauransa sai zabga ƙamshi yake yana sauraran abokan nasa, Shiru yay sbd ƙamshin turarenta da yaji ba zai taɓa mantawa dashi ba cikin ƙasa da murya ya cewa abokan nasa “Guy’s shiru anzo bikona”
Ya faɗi hakan yana haɗe fuska ya fara duba files ɗin gabansa.
Abokansa nutsuwa sukai suna jiran shigowar ta, domin tun tuni Abban Arman ya gama zubarwa da Mannal mutuncin a idanun abokan nasa basa ganinta da gashi ko kaɗan.
Turo ƙofar tayi a hankali ta shigo kana ta rufe Arman kuma ya tsaya a cikin mota.
Kallonta yay sosai kana ya tuntsire da dry yana buga table ɗin gabansa, ɗauke kai tayi tana cije baki tana sauraran yadda bugub zcyarta ya ƙara gudu da ƙarfin gaske! Kujera taja zata zauna yay saurin cewa “is Not allowed” cije baki tayi tana ɗan bubbuga ƙirjinta yace “Meke tafe dake zaki faɗo min office without my permission ƴar tsuhuwa?”
Saurin Kallonsa tayi taga gskyar abinda ya faɗa a cikin idanunsa, Shiru tayi abokinsa mai suna Kamis yace “Haba tsuhuwa mgn ake maki fa?” Haɗiye hawayenta tayi domin ba zata taɓa yi masa kuka ba da ƙyar ta samu damar faɗin “Son yace kana nema na”
Abban Arman ya juya chair yace “Ohhh! Yazo akan yana son ki koma ɗakin ki, shiyasa nace ya turoki idan kin shirya bani hqr”
Runtsa idanunta tayi kafin tace “Hqr?” Yace “eh! Nasan girman kanki bazai barki ba, amma da zan baki shawara da kin durƙosa bisa kafaffuwanki kince AM SORRY sweetheart, am sorry Abban Arman nasan nayi laifi ka yafe min ka mayar dani gidanka, nasan idan bakai babu wani namjin da zai aure ni a wannan age ɗin nawa harya gamsar dani buƙatar da kake min, kayi hqr ka yafe min bazan sake ba na tuba na bika Abban Arman, kina faɗin hakan shkknan zaki koma gidan ki” kallonsa tayi ido cikin ido tana ɗan yin Murmushin takaice ba tare da tace komai ba tai saurin Juyawa sbd hawayen daya kawo idanunta Kamis yace “Haba tsuhuwa za kiyiwa kanki da wannan zan kaɗeɗan saurayin, nasa zai wahala ki samu kamarsa sai dai wanda ya kusa tafiya lahira”
Sarai taji mgnar da ɗan sassarfa ta nufi motar Arman na ganinta ya fito tana zuwa ta faɗa jikin ɗan nata tana sakin kuka.
Abban Arman yace “Uhm bana faɗa maku girman kai yay mata yawa ba, kuma wlh Allah shi ne shai data i love my wife ban bari kowa ya aureta bare nasan babu mai auranta ina son na ladamtar da ita na nuna mata ƙarshen ta, bani takewa gayya da jikinta ba uhm zamu gani dole taban hqr”
A airport Arman ya sauke Mannal ba jimawa jirginta ya tashi zuwa Kano zcyrta sam babu daɗi har wani duhu take gani cikin idanunta.+
Washe gari Ya Heemu ya shirya cikin wani Amy colour ɗin wando na uniform ɗin sojoji ya sanya farar Armless mai zip wacce akaiwa ado da zanan rainbow, rigar mai shoulder ce sai p.cap daya ɗura saman sumar kansa itama irinta sojoji, sai baza ƙamshi yake kana kallonsa kasan babu abinda ya damesa a Parlo ya samu Ummi tana watching TV ya zauna kusa da ita yana faɗin “Evening Ummi” shafa kansa tayi tace “Ya Heemu na sannu Allah yay maka albarka kaji, ka kula da lfyarka” kai ya jinjina mata yace “Ummi aure zanyi” da sauri ta kallesu tace “Khaleel Aure? Dawa? when?” Miƙewa tsaye yay yana kissing goshinta yace “Soon zaki sani Ummi, but a week ɗin nan ne” da ido kawai ta bisa tabbas yay yaro dayin Aure amma kuma Aure gareshi shine fa’ida ita kanta zata fi samun nutsuwa da hakan, burinta kuma taga Grandchildrens ɗinta, sosai take fargabar dalilin daya sanya Ya Heemu yin aure domin yin duniya tayi dashi amma ya nuna sam auren baya gabansa.
Driving take cike da nutsuwa ko securities bai fita dasu ba, office ya nufa suka tattauna mgn kana yay nufi gidan Baffa yana son yay masa mgnar Auran sannan yay kewar ɗan tsohuwan nasa, rabonsa da Baffa tun abinda Ya Omer yay masa haka rabon daya sanya Ya Omer shida Moha a idanunsa ya manta yana kallon miss calls ɗinsa ko takai baya bi.
Parking yay ya fito yana ɗan kaɗa key ɗin hannunsa, a tsakar gida ya samu Inna da Hanna suna gyara kaji, tsayawa yay yana Kallon kajin jin ƙarni zai damesa ya nufi ɗakin Baffa, Inna na faɗin “Malam ɗin baya nan” Amma sam bai tsaya ba Hannah tunda taji kamaninsa ta rasa nutsuwarta ta shiga juya kajin bata san lokacin da wuƙa ta yanke ta ba sai jini da taga yana zuba a hannunta.
Cike da kamewa da kammala Haɗi da kuzari Ya Heemu ya nufi ɗakin Baffa yana ɗaga Labule idanunsa ya sauka akan Ya Omer dake ƙoƙarin haɗe bakinsa dana Moha ita kuma tana tirjewa da sauri ya saki labulan ya shiga yin tari yana buga ƙirjinsa..A hankali yake shafa saitin ƙahon zcyarsa dake masa ɗan zafi, cikin dauriya da kuma juriya ya shiga jan numfashi yana saukewa domin samun sauƙin azaba haɗi da kuma raɗaɗin zafi da tiririn da zcyarsa ke masa.
Ganin yadda yake tari yana ɗan buga ƙirjinsa yasa Hannah tsame hannunta da sauri ta ɗauki jug ta ɗebo masa ruwa mai sanyi a randa.
Tana zuwa garesa kafin ta idda ƙarasawa yay saurin juyawa ya nufi ɗakin Inna yana zuwa ya kwanta saman gadon ƙarfenta ya lafe a jiki yana taune leɓansa na ƙasa yadda zucyarsa ke gana masa a zaba shine kwatankwacin taune lips ɗinsa da yake.
Ya Omer Murmushi ya sauke yana ɗan jaa baya tare da zamewa ya zauna yana faɗin “Matsoraciya” turo baki Moha tayi tace “Uhm Allah kaban tsoro Salan dai kayi min ciki” zare ido waje yay yana mai ƙare mata kallo lallai Moha ba hankali daga kiss kuma sai ciki? Ɗauke zan can yay a ransa yana faɗin
“Shalele week ɗin nan Za’ai resuming school”
Baki ta turo tana kwaɓe fuska nan da nan hawaye ya shiga sintiri a saman ƙyakkyawar farar fuskarta mai cike da ƙuruciya.
Cikin kuka tace
“Ni wlh bazan koma ba salan kawai wata ta aureka”
Narkakkun idanunsa ya zuba mata yana ƙara karantar halinta.
Sosai ya fahimci da dukkan zcyarta tayi mgnar amma kuma ya fahimci bata san muhimmancin abinda take faɗa bane, tayi la’akari da kalmar da yake yawan faɗa mata na zai aureta itace happiness ɗinsa.
Har kuma zuwa lokacin ya kasa faɗawa kowa yana son Moha sbd bai san yadda zasu fahimci lamarin ba.
Ajjiyar zuciya ya sauke sbd tsoro da fargabar daya dira a zyrsa mene makomar soyayyyar daya kewa Aysherh ne? If wani ya aureta before he coming back? Anya zai iya barin wannan abun kunya, ina bazai iya dauriyar da ABU_MALEEK yayi ba har ya rasa ƴar makauniyar sa, ya jure bulala kusan 50 akan Hawwa kulunsa kuma Jidderh sa amma sabuwar ƙaddarar mai tafiya da kalar imanin mutum tai fatali da rayuwar ABU MALEEK har ya manta da batun wata Bafulatanarsa (JULDE).
Shi daya ɗauke wasu shekaru da soyayyar Indo fa? Baya son wannan Soyayyar ta zama Makauniyar soyayyyar ko kuma kurumtacciyar soyayya.
Sauke numfashi Ya Omer yay kafin ya kalli Moha da take kuka bil haƙƙi, tana sanye da riga da wando na Pakistan ruwan huda, sunyi masifar yi mata kyau kasancewar ta fara mace.
Idanunta me kama dana Ya Heemu sak suke zubar da hawaye dan kaf familyn Baffa babu wanda yay kama da Ya Heemu irin Moha bambancin fata yasa wasu basu ganin kamar tasu.
Moha fara ce tass kaf jikokin Baffa ita ta ɗauki farar fatarsa sai Murgayiya Safa, sai Ya Omer sai kuma Hannah, daga nan sai Shoona sai kuma Amatu wacce ake shirin yin bikinta da Yayan Shoona Areef.
Tana da manyan ido irin na Ya Heemu sai yalwatacciyar gira mai ɗauke da baƙin gashi masu kyau wanda suka kusa haɗe girarta, Moha tana da sahihin kyau wanda yake bai yana kansa a koda yaushe tana da shiga rai tana kuma da faɗin Gsky bata da ƙarya sam, shiyasa wasu take basu haushi kamar yadda Ya Heemu bai ƙaunar ta haka itama bata ƙaunar sa, abin mmki kuma Ya Heemu shi ne ya zaɓa mata sunan Aysuhtul humaira, kuma ya bata nickname Moha.
Amma koda wasa babu sunan da akaji ya taɓa da bakinsa tsakanin Moha da kuma Aysuhtul humaira.
Ajjiyar zuciya Ya Omer ya sauke yana son gasgata abinda yake ransa wanda yake harshashen zai iya faruwa shiyasa lokacin da yaji ƙamshin turaren Ya Heemu yay ƙoƙarin kissing Moha amma sam ba haka a ransa, Son Moha Ya Heemu yake ko mene, kishi yake ko mene? No babu wata halitta da Ya Heemu ya tsana sama da Moha duk familyn babu wanda bai san wannan ba, san haka babu ta yadda za’ai ya so Moha.
Miƙewa tsaye yay yace “Stop cry Shalele”
Cikin kuka tace “Nidai wlh bana son makarantar” kwantar da murya yay sosai cikin sigar rarrashi yace “Me kike so yanzu”
Tana ƙara birgima kamar yarinyar goye tace
“Kawai kaje wajan waccan baƙin mugun mai baƙar zcy kace masa ka sauya makaranta”
Zaro ido Ya Omer yay shikam ko yasha giyar wake ai bai isa yaje wajan Ibrahim ɗin Baffa ba, kallon ta yay cike da soyayya yace “Shalele kina ganin baya kulani”
Turo baki tayi tana ƙara fasa ihu wanda har sai da Inna taji tace
“Yau mun shiga uku fa”
Moha tana kuka tace
“ai dai kai ma baka kyauta ba, meyasa zaka dakesa”
Da mmki Ya Omer ya kalleta yaga iyakar gskyar ta kenan, kamar zai kuka sbd yadda yaga ta ɓata rai yace
“To me zanyi Shelele? Kina kallo dokanki zaiyi, ni kuma bazan iya jurewa ba”
Miƙewa tsaye tayi kamar mai aljanu ta shiga goge Idanunta kamar ba ita ga gama kukan ba tace
“To basai ka rabu dashi ya daken ba, ni kuma sai na haɗasa da Ummi kaga yana son Umminsa sosai yana jin mgnarta haka kuma yana son Mamana sosai (Anut Meera) ko kuma kai ma ka buɗe masa ido kamar yadda yake zaro wannan manyan idanun nasa kamar na mage”
Kallon baki san yaya na keji a zcyta ba Ya Omer yay mata, yana da aiki sosai dole ya zama mutum na farko kuma na ƙarshe daya samu waje a zcyar Moha amma ta yaya, da sauri yace “Shalele akwai wani labari mai daɗi”
Da sauri ta matsa kusa dashi sai kuma taja baya kaɗan tana washe fararan jerarrun teeths ɗinta tace “Dan bani labarin na cartoon ne”
A zcyarsa yace “Ikon Allah”
A fili kuma yace “A’a, novel ne mai daɗi na marubuciya Nimcyluv”
Shiru tayi sai Idanunta ta zuba masa wanda yake ƙara dagula masa lissafi yace “Zan baki wayata ki sauke application ɗin wattpad, kiyi searching sunan marubuciyar kisa F@y@l ko Nimcyluv, saiki follow daga nan saiki duba littafin SIRRIN MU ko UNCLE NE ki karanta after nan sai muyi mgn”
Wayar hannunsa ya bata bayan ya zare sim ɗaya, karɓa tayi da sauri tai waje da sauri yace.
“kee! Shalele!! Shalele!!”
Amma tuni tayi waje, tana zuwa wajansu Inna taga lodin siyayyar tafiya makarantar su, wacce yanzu Ya Areef ya sauke masu ita a mota tare da sabbin uniform da school bag da littafai da system, wacce duk siyayyar Ya Heemu ya bada kuɗin.
Hannu tasa aka ta kurma ihu tace “Na shiga uku” sai kuma tayi ɗakin Inna da gudu tana sakin sabon wani ihun.
Yana kwance lubb saman gadon Inna da sauri ya runtse idanunsa sbd bugun da zcyarsa tai masa kamar zatai tsalle ta faso ƙirjinsa.
Ƙara narkewa yay jikin gadon tare da ƙanƙame idanunsa yana jin zcyarsa yana buga duk abin Ya Heemu baya son ihu da ɗaga Murya a kansa ko mgn mutum yay yanzu sai ce yana masa ihu, bare yanzu da take kurma masa ihu a saman kansa dake barazanar tarwatsewa gida biyu.
Moha sam bata kula da Ya Heemu ba,ta faɗa gadon ta hau birgima tana ihu tare faɗin.
“Wlh ko kafi ƙoda naci ba zani ba gidan Baba Haroon (Mahaifin Hannah Yaya ƙani a wajan Mahaifin Ya Heemu).
Marai-raice fuska Ya Heemu yay kamar zai sanya kuka sbd ihun da take masa, gashi a dai-dai saitin kunansa take haushin nata.
Mirginawa yay kaɗan yana danne kunansa da pillow.
Jin motsi yasa tai saurin juyawa domin Allah yay mata tsoron mage
Tsitt tayi sbd ganinsa kusa da ita idanunsa a lumshe, duk da kasancewar sa baƙi amma hakan bai hana fuskarsa sauyawa ba kana hango wani jaa da tayi na ɓacin rai.
Ga jijiyoyin kansa sun Miƙe sosai.
Sai huci yake jikinsa duk tsoma yake gargasa jikinsa ta miƙe sosai.
Kuka tasa tana ja baya tana faɗin
“Dan darajar Annabi kayi hqr wlh suɓutul kalam nayi, dan Allah kada kai min komai dan son da kakewa Ummi”
A hankali ya shiga buɗe nauyayyen idanunsa wanda sukai jajirr.
Ya sauke a kanta tsanar da yaywa Yarinyar yasa yake ganin fuskarta nada munu a idanunsa.
Ɗauke idanunsa yay hakan yasa ganinsa ya sauka akan wayar hannunta zare ido yay.
A hankali kuma ya miƙa hannunsa da sauri tai baya zata sauka yay saurin cafke Hannunta ya shiga kallon wayar hannunta kafin ya kalleta fuskarsa kamar hadari babu walwala.
Kallon da yake mata yasa tace “Wlh ba ruwana Ya Omer yaban wai nai karatun littafi.
Baice mata komai ba ya kama hannunta tare da sauka daga saman bed ɗin jikinsa duk rawa yake, Moha kam gaba ɗaya ta firgita da Ganin Ya Heemu bata taɓa ganinsa a haka ba.
A waje ya samu Ya Omer da Ya Areef suna Mgnar gidan gonar Ya Heemu, tun daga nesa Ya Areef yaja baya domin shima ya tsorata duk da cewa shi ne gaba da Ya Heemu gaba ɗaya Ya Heemu shi ne ƙarami a cikinsu.
Shima Ya Omer gyara tsaiwa yay domin yasan kwanan zan can tunda yaga wayarsa a hannunsa ga Moha daya riƙe kamar zai ɓalla ta.
Idanun Ya Heemu har ruwa yake sbd zallar bala’i yana zuwa bai tsaya jiran komai ba yasa ya zabgawa Ya Omer mari zafi da ƙarfin marin yasa Ya Omer yin baya yana dafe kunci abinka da mai Zcy shima ya nufi Ya Heemu zai mara Moha na ganin haka tai saurin ƙanƙame Ya Heemu tana sakin kuka tsayawa Yay cak yana kallon Mmki.
Baffa da Baba Haroon da Kawo Shuriem (Mahaifin Shoona da Areef) suka tsaya cak suna kallon ikon Allah domin basu taɓa sanin akwai saɓani a tsakanin Yaran nasu ba.
Baffa kam Murmushi Yay sbd abinda Moha tayi ga wanda ta saba dashi ta shaƙo dashi an maresa batai komai ba amma wanda ta tsana anzo marinsa ta hana.
Ya Omer yace
“ka maran?”
Ya Heemu ta huci yana son zare Moha daga jikinsa amma tai masa mahaukacin riƙo yana fesar da iska yace “Sai na mallaka yanzun nan, ashe girman banza gareka ashe baka da hankali yarinyar da an zuba mata ido wacce Allah ya kaya bare ka ɗauki waya ka bata, abin takaicin bama karatu makaranta zatai ma wai Hausa novels ka bata ta karanta, what the fuck? Heeee!! What’s this answers my questions OMER ALIYU AL’AMEEN?” Murmushi Baffa yay yace “AL’AMEEN sunana ke nan”
Bai ko kalli inda Baffa yake ba yace “Baka da amsa ko? Sbd kana son ka gina soyayyyar ka a zcyrta shi ne baka son komai ka bata waya tai karatu may be she understands very well ko? Well-done Omer Aliyu Al’ameen”
Ya faɗin hakan yana buga wayar a ƙasa ta watse nan take.
Baffa ne ya samu damar faɗin “Malam Ibrahimul Khalel meya faru kai da waye jikalle?”
Hucie kawai yake ganin hakan yasa Kawo Shuriem ya ƙara so wajan tare dasa hannayensa ya riƙe hannun Moha kuka tasa tace “Kawo dukansa Ya Omer zai yi haka kwanaki ya dakesa a ƙirji”
Kallon juna sukai wato faɗan bana yanzu bane kenan.
Ya Omer kam duk ihun da Ya Heemu yake baya fahimta fargaba da tsoro suka kamsa, ganin yadda Moha take nuna kariya ga Ya Heemu.
Da sauri ya zube gaban Baffa yana riƙe ƙafafuwansa yace “Baffa dan Allah dan Annabi kayi min rai ka aura min Aysherh idan duk akanta yake wannan abun zan kawo ƙarshen abun yazo, dan Allah Baffa nai maka al’ƙawarin duk abinda za kace amma ka fara aura min ita wlh zan iya rasa rai na idan ban sameta ba”
Baba Haroon ne yace “Omaru baka da hankali amma dai ko, wannan yarinyar zaka aura gaba ɗaya nawa take?”
Baffa ne yace “Haruna kira min Aliyu yanzun nan, sannan ka kira min Al’mustapha yanzu shima”
Da mmki Baba Haroon yace “Amma Baffa kiran na mene?”
Baffa yace “Bana son mgn” yana faɗin haka ya kama hannun Khalel da jikinsa ke rawa kana ya riƙe na Ya Omer yace “Kawo min matar nan” ya faɗi hakan yana nufar cikin ɗakinsa.
Driving daya ɗauko Mannal nayin parking ta fito daga cikin motar a nutse take tafiya amma hankalinta gaba ɗaya baya jikinta tana shiga cikin babban parlo Dad ɗinta na fitowa da sauri ta nufi inda yake yana ganinta yasan akwai matsala, tana zuwa ta faɗa jikinsa tana sakin kuka tana riƙe tana faɗin “Dad!! Dad!! Dad Abban Arman” sai kuma ta ƙara saka wani kukan, janta yau zuwa wajan kujerar ya shiga rarrashinta sai da tayi Shiru tana manne jikinsa tana sakin ajjiyar zcy kamar wata yarinya Dad yace “Ƙara zuwa kikai ko? Ashe kin girma ba zaki hankali Ba Daughter na? Kinfi son ki zauna da wanda zaici mutuncin ki yaci mutuncin mahaifin ki? Ke kika hanani kaishi Court da al’ƙawarin ba zaki sake mgn dashi ba yanzu shine kika karya al’ƙawarin ko?” Waya ya ɗauka ba tare daya janyeta daga jikinta ba ya kira yace “Kamal kazo kai da Jamil” yana faɗin hakan ya da ɗa kiran wata number yace “Yace Sufyan har yanzu kana sha’awar Auran Daughter?” Kai ya jinjina kana yace “Ok meet me right now” gaban Mannal ya bada sauti rasss rasss dam! Miƙewa tayi tace “Dad?” Hannu ya ɗaga mata yace “Kinyi abinda ki kaga dama yanzu nima zanyi abinda naga dama a matsayi na mahaifinki”
Wayarsa tayi ƙara bayan sun gaisa ya tsaya yana jin abinda ake cewa shiru yay sai kuma yace “Ikon Allah”
Baffa ya kalli yaransa, Baba Haroon da kawo Shuriem sai kuma Uncle Aliyu, da kuma Al’mustapha mahaifin Moha wanda dawowarsa daga ƙasar kenan, Baffa ya kalli Ya Heemu dake gefen damarsa wanda har yanzu jikinsa rawa yake, kana ya kalli Ya Omer sai kuma ya kalli Moha yace “Aysuhtul humaira wa kike son Aura tsakanin Yayanki Ibrahimul Khalel da Omaru?”.
Narkakkun idanunsa Ya Heemu ya ɗaga ya sauke akanta yaci Sa’a suka haɗa ido tsuro tayi tana kallonsa kamar yadda shima yake kallonta a lokaci na farko da tasan cewa shi ɗan uwanta ne kuma jininta domin Moha ƴar wajan Al’mustapha shi kuma Al’mustapha ɗan uwan Ummi ne, Anut Meera kuma ƴar ce wajan Baffa, sai yanzu take ganin kamar su sosai da Ya Heemu hatta dimples teeths gave da tusar jakinsu duk iri guda ce, kallonsa take kamar yadda yake kallonta hawaye ya sakko mata bata taɓa sanin kalmar aure ba sai a bakin Ya Omer dan haka ta juya ta kalli Ya Omer kana ta kalli mahaifinta mutum mai karamci da kuma alkunya muryarta na rawa tana son sakin kuka tace “Baffa Ya Omer na keson ya auran”
Da sauri Ya Heemu ya miƙe yana haɗa hanya ya bar ɗakin yana ɗan sakin gajeran tari.