AUREN KWANGILA BOOK 1 CHAPTER 2 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

AUREN KWANGILA BOOK 1 CHAPTER 2 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

                Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA

Allah ya karbi ran Inna Rabi Idris na da shekaru ashirin da biyar.

Baffa Atiku wanda ya zamo shi ne babba a zuri’ar Malam Abdullahi shi ne mahaifi ga Dr. Hamza da suka haifa da maidakinsa Inna Ramatu. Sun manyanta, amma ba za a kira su tsofaffi ba. Dr. Hamza kadai suka haifa, mai bin Baffa Atiku a maza wato Abdulkarim Dakata a yanzu haka Sanata ne mai wakiltar Kano ta tsakiya, yana Abuja da iyalansa, Adda Hafsatu ‘ya ta biyu ga Malam Abdullahi ita ce, mahaifiya ga Hajiya Maryam, Hajiya Maryam din ce babbar ‘yarta sai kannenta hudu mata Anty Luba, Anty Furairah, Anty Mariya, Aunty Murja da autan Adda Ibrahima wanda ke karatunsa yanzu a jami’ar Ahmadu Bello mataki na farko, yana karantar tsimi da tanadi. Lubabatu, Furairah, Mariya da Murja duk an aurar da su bayan kammala karatun sakandire, su da nasu iyalin duk a Kano suke 

 ZAMU TASHI

Zaune.
Autan Malam Abdullahi wato Idris Dakata, yana karatun likitanci ne a jami’ar Maiduguri, bai kai ga yin auren fari ba, yana amsa sunan Uncle Idris daga bakin yara da manyan wannan zuri’a mai albarka.
Adda Hafsatu mahaifiyarsu Hajiya Maryam ta yi aikin gwamnati na tsayin shekaru talatin. A yanzu ta yi ritaya bayan rasuwar mijinta ta zauna a gida ta rungume ‘ya’yanta kasancewar maigidanta Alhaji Hassan ya jima da rasuwa. Kenan Hajiya Maryam da Dr. Hamza ‘yan uwan juna ne, “yar

mace da Dan Www.bankinhausanovels.com.ng namiji suke. Sun tashi gida daya, sun samu tarbiyya iri daya. Aurensu ba na hadin zumunci ba ne, shi ya ce yana sonta tun tana karama. Amma ba wanda suka yi wa auren zumunci bayansu cikin zuri’arsu, kowanne daga waje yake kawo abokin rayuwarsa in ka cire Hamza da Maryam. An yi musu aure tun kafin ta kammala digirinta na farko, shi kuma yana koyarwa a jami’ar Bayero. Ya samu mugamin Farfesa a shekarun kuruciyarsa saboda hazaqarsa wajen_ rubucerubuce da wallafe-wallafe a fanninsa na (political science). Ya rike muqaman gwamnati guda uku a Federal Government kafin Allah ya kai shi ga samun matsayin (parmanent secretary) na ofishin shugaban kasa. Wanda abokin mahaifinsa ne tun na kuruciya ya dauki mukamin ya bashi. Suka tattara suka koma Abuja da iyalinsa.
Gidan Mal. Abdullahi ya kara yin fice a unguwar Dakata ko don mukaman dansa da babban jikansa; Parmanent Secretary Hamza da babban dan siyasa Abdulkarim, wadanda ba dare ba rana duk sanda suka zo garin Kano taimako suke yi wa al’ummar unguwar su da kewayenta ba na wasa ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
A yanzu haka ciki gidan marigayi Malam Abdullahi babban dansa Baffa Atiku da maidakinsa Hajiya Ramatu mahaifan Dr. Hamza ne a ciki, sai Idris wanda in ya zo hutu gida a karshen kowanne zangon karatu dakinsa yana nan a soro na biyu. Adda Hafsatu ma bayan an sayar da gidan gadon ‘ya’yanta su Hajiya Maryam an raba musu gadon mahaifinsu, nan gidan ta dawo ta share dakin mahaifiyarsu marigayiya Inna Rabi ta yi zamanta kusa da dan uwanta Baffa Atiku da maidakinsa Ramatu, suna zamansu lafiya. Babu yaro gabansu sai autan Adda Ibrahim wanda ya fara karatun jami’a. Duk da haka ba ka raba dakin Adda da yara haka dakin Inna Ramatu sabida ‘ya’yan su Luba, Mariya, Furairah da Murja duk hutu suna gidan ko ranar da ba makaranta. Adda Hafsatu na baiwa Inna Ramatu girma yadda ya kamata kasancewarta matar Yayanta kuma suruka a gare ta. Amma wani zubin sukan manta surkuntar su yi ta harkar arzikinsu da kula da jikokinsu. Inna Ramatu ta rike girmanta ta hada shi da kyautatawa. Don haka ake zama na aminci da kwanciyar hankali da wadata a gidan marigayi Abdullahi Dakata. ‘Ya’yansu sun wadata su da komi na rayuwa, sun dauke duk wani nauyi na rayuwar iyayen nan nasu bakidaya. Dr. Hamza ke dauke da nauyin karatun Uncle Idris da Ibrahima don ya fi Sanata Abdulkarim sakin hannu.

**********

An gama komai na shirin hijirar Ambasada Hamza Atiku Dakata, da _ iyalinsa_ kasar Saudiyyah. Washegari suka wuto gida Kano. Babban gidan ya kacame da murnar zuwansu. Ga shi ya kama lahadi ce, su Luba da yaransu duk sun zo kamar yadda suka saba duk lahadin karshen mako. Uncle Idris ma ya zo daga Maiduguri yana (housemanship) a asibitin Www.bankinhausanovels.com.ng Malam. Iyalin Sanata Abdulkarim ne kawai babu suna Abuja kuma dama dai akwai matsala ta fanninsa domin abin a zahiri yake, babu iyalin da zai yiwu ace babu baraka ko yaya take a cikin su, hakika Sanata Abdulkarim Abdullahi Dakata, bai yi sa’ar mata ba. Ko kusa Anty Zuwaira (matarsa) ba ta so ya rabi danginsa ko ya wahalta musu, ba kuma ta so suma su rabe shi. Da wuya ka gansu a Kano sai dai ya yiwo waya ko aike, kowa a cikin zuri’ar ya kwana da sanin wannan.
“Ya’ yansa ba su saba da ‘yan uwansa ba, sai na mamarsu da yake ita ma diyar wani kusa ce a Abuja. Ta kan dan yi zumuncin da Hajiya Maryam tunda ita ma mijinta mai matsayi ne kamar su koma fiye da su. Akwai sanayya tsakanin yaranta uku Farhan, Ramadhan da Sha’ aban da su Abdul’azeez, amma ban da na sauran dangi da ke Kano.
Gidan ya cika sosai da zuri’ar Malam Abdullahi mazansu da matansu da ‘ya’yansu. Adda Hafsatu da mai aikin gidan nata zirga-zirga tsakanin madafi (kicin) da tsakar gida don hada abin da za
aci da rana. Kuma da ma kafin su zo labarin abin alkhairin da ya samu Dr. Hamza ya riga su isa. Don haka ana zaune ne a babban falon marigayi ana sallama da juna, da hirar zumunci. Dr. Hamza ke tambayar kawunsa Idris (autan su Baffa Atiku) wanda malam Abdullahi ya haifa a shekarun girmansa matakin karatunsa, ya sanar da shi yana (housemanship) ne yanzun a nan Kano. Ya koma kan su Lubabatu kannen Hajiya Maryam, Luba koyarwa ta ke a_ karamar sakandire da yake NCE kadai gare ta. Ya ba ta shawarar ya kamata ta tafi karo karatu (in-service), haka nan zai dauki nauyin karatun. Luba ta ce, insha Allah zatayi amfani da shawarar sa. Furairah ba ta aiki da yake maigidanta ba ya so. Dr. Hamza ya dade da ba ta jari tana kasuwanci yanzun ma kara mata ya yi don ta fadada kasuwancin nata. Murja na yin (masters) ta ce a barta ta kammala kafin a nema mata aikin ba ta son hada taura biyu a baka. Ya gaya wa Gyatumarsa Www.bankinhausanovels.com.ng Inna Ramatu da surakuwarsa kuma uwarsa Adda Hafsatu su zamo cikin shiri tunda duk suna da (passport) na Hajj da Umrah da yake kai su duk shekara, da sun yi (settling) a sabon muhallinsu zai aiko musu su tafi su ga sabon matsugunninsu.
Da dare a dakin Adda Hafsatu, ita da babbar diyarta Hajiya Maryam suna hirar sallama irin ta Da da mahaifi, Adda ke tambayar dan gaban goshinta, wato Abdul’azeez ba ta ganshi tare da su ba. Hajiya Maryam ta fada mata duk yadda suka yi da shi, da amincewa da Babansa ya yi ya
maida shi makarantarsu ta kwana (Regent, Abuja) kafin su taho Kano. Adda ta yi dariya, ta ce, “Dan baiwa kenan, mai ra’ayi da akida ba irin na kowa ba kamar Kakansa. Ni ina ki ka samo sabuwar mai aiki ne, ina Jamilar? Kyakkyawa da ita kamar ba mai aiki ba. Da ganinta bafullatana ce. Ke kam ba kya gajiya da canza masu aiki”.
“Adda, Jamila ta yi aure. Kuma Adda masu aiki ba sa zama ne, kowacce sai an saba da ita, sai ta ce ga uzurinta za ta koma gida”. Ita wannan din tare za ku tafi har Jeddan?” Eh Adda, gara na dau ta gida da in je can in neman mai aiki Takari, da yawansu basu da amana kuma yawancinsu ba mutanen kirki bane kuma basu da takardar shaidar zama (igama)”.
‘Har yanzu kina nan da halinki na saurin yarda da mutane Maryama? Da za ki dauki wadda ba ki san asalinta ba ki tafi da ita inda ke ma ba ki da kowa? Ba kya fada a nema miki cikin dangi tunda babu wanda zai samu wannan damar ya ce a’ah?”
Hajiya Maryam ta girgiza kai da sauri tareda gyara zama, “Adda, bana so jinina su yi min aiki, sabida hali irin na dan Adam. Dan uwanka in ya zama mai aikinka ba ka da sirri a dangi, kuma ko me za ka yi masa ba zai gode ba. Bar ni dai da baren. Ki kwantar da hankalinki a kan Habiba Adda. Wallahi haka nan na ji ta kwanta mani a rai tun ganina da ita na farko. Ba ki ga yadda ta ke kula da yara ba bilhaqqi ga zafin nama da tsafta’”’. Adda ta gaji da koda Habiba da Maryam ke tayi ta tare ta da cewa, “Allah ya Www.bankinhausanovels.com.ng zaunar da ku lafiya da juna, Ya kade sharri, Ya hada ku da alherin da ke tare da ita”Ameen, da addu’o’inku gare mu Adda ba za’a cutar da mu ba,insha Allahu”’.
Adda ta janyo katuwar (Ghana Must Go) ta ajiye mata a gabanta. Tanadin tafiya ne ta yi mata na kayan girki, yaji, daddawa, kubewa busasshiya, busasshen kifi, kayan kamshi na gargajiya, kuka da sauransu. Ba karamin dadi Hajiya Maryam ta ji ba, wani abu sai mahaifiya. Ta yi ta godiya tana kara son Addar tata a zuciyarta. Washegari suka kamo hanyar Abuja cike da kewar gida, iyaye da ‘yan uwansu. Ranar Asabar, biyu ga watan biyu, na shekarar alif dari tara da casa’in da shidda (2/2/1996). Ambassador Dr. Hamza Atiku Dakata da iyalinsa suka daga kasar Saudiyyah. Ko da jirgi ya sauke su a birnin Jeddah ba su shiga gidansu ba, wucewa suka yi Madinah suka fara aikin umrah. Habiba ta kasa gasgata abin da idanunta suke gane mata, wai yau ita ce a kabarin Manzo sallallahu alaihi wasallam. Ko da wannan ta tsira kadai ta san Allah ya fara yi mata sakayyah ne akan abin da ya rabo ta da gida. Ta faki idon Hajiya Maryam ta share hawayen da suka zubo mata data tuno kananan ‘ya’yanta. Kwanansu biyar a Madinah suka nufo Makkah suka cika umararsu, sannan suka wuce Jeddah inda gidansu yake a unguwar (Albasatin). Ambasada ya shiga sabon ofishinsa a ranar Litinin.

***********

Aikin Habiba a gidan Ambasada kullum shi ne, kafin Daddy da Hajiya su fito ta shirya yara shirin zuwa makaranta, sunan makarantar da suke zuwa (Hala International School). Direba ya debe su zuwa makaranta har Halim shi ma an sanya shi ajin rainon yara. Daga nan ta dora wa Hajiya sanwar safe kafin ta fito ta karasa, ta share ko’ina na Kayataccen gidan duk da yana da girma, Habiba ba ta raki. In ta tashi da asuba ba ta komawa barci, ta yi (mopping) ko’ina, in Mama ta sakko kasa ta kama mata su hada (breakfast) na Daddy, na yaran ita Habiban ce ke yi. Ta kwashe ta jera a tebirin cin abinci, ta gyara dakin yara ta tattare kayansu da suka wargaza. Ta wanke duka bayin gidan (toilet, ban da na Daddy, wannan Mammah ce ke yi da kanta. Sannan ne za ta wuce dakinta ta yi wanka ta kintsa kafin Mama da Daddy su gama karyawa ya tafi office. Www.bankinhausanovels.com.ng
Daga Daddy har ‘ya’yansa da mota uku suke amfani, direbansa daban na yara daban, wata babbar (Limousine) ce baka wuluk ta kai yaran makaranta, shikuma wadda yake shiga karama ce (Hyundai). Bayan ita akwai babbar cherokee jeep duk na hawansa ne shi kadai. Yaran na riga shi fita kullum.
Basu rufa watanni uku ba Hajiya Maryam ma ta shiga makarantar islamiyyah ta karfe sha dayan rana zuwa azahar, don haka ya zamo duk al’ummar gidan ba sa zama sai Habiba.
Cikin watanni hudu sai ga Habiba ta soma canzawa, sakamakon cima mai kyau da muhalli mai kyau. Kyawunta na fulanin usli ya bayyana mu
raran, duk da ba kwalliya ta ke ba, kullum cikin bakaken jallabiyoyi ta ke, wadanda Mammah ke sai musu ita da Habiban don fita waje da zuwa Harami. Duk juma’ah suke shiga harami su yi Dawafi da sallar juma’ah, sai yamma lis suke dawowa Jeddah.
Watanninsu hudu kenan a Saudiyyah, Habiba ta dade tana samun wasu sauyuka a tattare da ita. Amma jarumtarta ba ta bari ko ya ya Mammah ta ga gazawarta ba. Inna Ramatu da Adda Hafsatu sun zo sun yi sati biyu sun shiga Makka da Madinah sun yi umrah sun koma.
Yawan kasala, zazzabin dare, da tashin zuciya suke damun Habiba. In gari ya waye kuma sai ta yi garau. Duk da haka ba ta gaza komai a ayyukanta ba, tana daurewa tana yi don ba za ta iya barin Mammah da aiki ba, kuma in ta hadiyi (Paracetamol) da suke da shi a kicin tana samun karfin jikinta.
Yau da gobe Habiba ta gane cikin jikinta ne ke girma. Wanda ta dade da manta yana tare da ita. Don dai ita doguwa ce, shiyasa bai fito sosai ba. Ba ta yi wani mamaki ba, don tun a gida ta san da hakan, soyayyar abin da ke cikin nata ya lullube ta. Ta kara kaimi Www.bankinhausanovels.com.ng wajen lullube jikinta ruf da manyan bakaken abayoyinta. Wani lokacin Hajiya Maryam kan ce da ita ta dinga cirewa tana shan iska mana, sai in za su fita. Ba ta cewa komai sai dai kawai ta yi mumushi.
Haka Habiba ta ci gaba da rainon cikinta har tsayin watanni takwas wanda yabi tsayin jikinta da fadin jikinta ya yi kwanciyarsa ba tare da
sanin uwargijiyarta ba.

*********

Abdul’ azeez ne ya zo hutu, zuwansa na uku kenan tun dawowarsu Jeddah, don haka gaba daya iyayen da ‘ya’ yansu cikin farin ciki suke. Duk da shan kamshinsa yana son Habiba, sabida yadda ta ke haba-haba da shi idan ya zo. Duk wata hidimarsa a wuyanta take, kulawar data ke masa daban ce da wadda take yiwa kowa a gidan, yaron ya shiga ranta sabida kyawunsa da sanyin halinsa. Shima AbdulAziz yana son Habiba ne saboda a cewarsa yana son girkinta, ta iya girki. Sannan ita din mai tsafTa ce yadda yake so fiye da duk masu aikin da Mammah ke yi. A kicin Abdul’ azeez ya tadda Habiba tana aikin abincin rana. Lokacin Mammah tana makaranta, iyakacin shi bakin kofa ya dube ta da murmushi a ransa yana cewa, ta yi kiba, ta zama katuwa kamar ana hura ta. Anty Habiba abin nan da ki ka yi wa Mammah jiya nake so in kara ci”. Ya fada da tattausar muryarsa. Habiba ta juyo da murmushi, “Dan gidana wanne a ciki? Jiya girki uku na yi wa Mammah, akwai dan wake, akwai burabusko akwai kuma faten acca”. Ya dan kanne ido alamar tunani, har ya ba ta dariya, “Mai ruwa-ruwan, ba mai Www.bankinhausanovels.com.ng duwatsun ba”. Habiba ta yi dariya ta ce, “Faten acca ba burabusko ba?” Ya ce, “Ehh, ba mai kwaya-kwayan ba”. Abdul’azeez ba zai daina ba ta dariya ba, ta sake murmusawa, Ba ni minti goma sha biyar toh”. Ya shigo kicin din ya ja kujera a gefe ya zauna,
“Bari to in jira ki a nan, kina yi kina yi min hirar garinku, ina son labarin kauye. Duk masu aikin Mammah daga kauye suke, suna yi min tatsuniya irin ta garinsu”’Murmushin fuskar Habiba ya dauke nan take, kafin tace. Ni ba daga kauye nake ba Abdul’azeez, daga cikin birni nake. Halin rayuwa ya sa na zabi in yi nisa da gida”’Abdul’azeez ya tattara hankalinsa ya bai wa Habiba,
“Na sha yin tunanin ba daga kauye ki ke ba Anty Habiba. Sam ba ki yi kama da kauyawa ba, sannan ba ki da kauyanci. Anty Habiba ya sunan garinku?”
Haka kawai ranta ke son yaron, saboda yaro ne mai tarin baiwar hankali da nutsuwa. Ba shi da sakin jiki da mutane, amma ita yana sonta. Alkawari ta yi wa zuciyarta babu wanda za ta fada wa daga inda ta fito ko abin da ya rabo ta da gida, don kada a ce za a maida ita. Yin nisanta da mijinta da ‘ya’yanta shi ne babban abin da ya fi mata kwanciyar hankali. Yanzu ji ta ke kamar tana rayuwa a kan gajimare don dadi da kwanciyar hankali, tunda ta rabu dasu, duk da lokacilokaci tana tuna su ta ji kewarsu. Wani dan guntun hawaye ya tsattsafo cikin fararen idanunta, Abdulaziz na lura da ita ya kara tattara hankalinsa a kanta, Ki yi hakuri in don na ce ya sunan garinku ne ki ke kuka Anti Habiba……. insha Allah bazan kara tambayar ki ba”. Ta juyo ta dube shi cikin girgiza kai, “Sunan garinmu JIMETA cikin jihar Adamawa”“To Anty Habiba ina mijinki? Ba ki da ‘ya’ ya?” Ta tsura wa AbdulAziz ido, kaunar yaron na shiga ranta. Shi ne mutum na farko da ya tambaye ta wani abu da ya shafi rayuwarta tun fitowarta gida. Duk wadanda ta hadu da su a gaba suna duba amfanin da za ta yi musu ne kawai, ba ruwansu da (personal life) dinta. Ta yi masa murmushi, ta ce, ““Abdul’aziz duk ina da su’’Cikin mamaki ya ce, Www.bankinhausanovels.com.ng
Kuma mijinki ya yarda ki tafi aikatau ki barshi da yaran?” Ta kura wa yaron ido cikin tunanin abin da za ta ce masa, amma ta rasa. Sai idanu da ta zuba masa, irin yaran nan ne masu son bin kwakkwafin abu da ake kira (inquisitive), wayonsa da nisan tunaninsa ya wuce shekarunsa. Da ya tabbatar Habiba ba ta da amsar da za ta ba shi, sai ya ce, “Ya’yanki nawa ne Anty Habiba?” Yatsunta uku ta daga masa, wato su uku ne. Ba ta kara ce masa komai ba, sai hawaye da ta ke sharewa. Hankalinsa ne ya gaya masa cewa ya kyale ta, ga dukkan alamu ba ta son zancen mijin da ‘ya’ yan da yake yi mata kamar yana yi mata fami a kan wani gyambo ne. Mikewa ya yi ya nufi hanyar fita daga madafin, ita kuma ta ce, “Ai ya kusa nuna faten, bari in juye maka”. Ya ce, “Miko min library, wani littafi zan duba ina da ‘holiday assignment”.
Da haka ya karasa ficewa daga kicin din yana jin tausayinta, ta ko’ina ba ta yi kama da ‘yan aiki ba, and she has her own family (tana da nata iyalin), amma ta zabi ta bauta wa wasu iyalin ta bar nata a kan dalilin da ya tabbata ba kudi ba ne (talauci) kamar sauran masu aikin Mammah. Habiba ta juye kyakkyawan faten accan da ta kammala a karamin (foodflask) ta hada da plate da cokali ta nufi dakin karatun yaran gidan, wanda ke kan wata matattakala guda uku a cikin babban falo. Sai an bi ta kan matattakalar ne za a shiga (study room) din. Ta hau matattakala ta farko ta hau ta biyu, santsin (marbles) da silifan kafarta dan madina ya kwashe ta, ji ka ke timm! Ta yi wata mummunar faduwa rub-da-ciki a kan cikinta. Ta saki wata irin kara mai amo, wadda ta ratsa har kwanyar Abdul’azeez da ke zakulo littattafai daga kan kantarsu. Www.bankinhausanovels.com.ng
Da gudu ya jefar da littafin ya nufo falon. Habiba ce ta fadi a kasa ga ta nan tana murkususu male-male cikin jini. Fate-faten ya watse a kasa, plate din tangaran din ya tarwatse ba abin da yake ambato saboda gigicewa sai “Subhnallah, zamewa ki ka yi?” Babban abin da ya ruda shi wannan jinin da ke malelekuwa daga kafafunta. Ya rasa me zai yi ya taimaka mata, ba a kiran Mammah a waya in tana islamiyya, bari kawai ya kira asibiti kai tsaye, don Daddy ma ba ya gari yana garin ‘ABHA’.
Kan wayar falo ya nufa da sauri ya duba ‘code’ na kiran (Accident & Emergency) na asibitin su ya kira, a takaice ya yi musu bayani suka ce suna

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *