RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 1 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
duk ka sallame su su tafi. Kana sakin su jibi zan daura maka aure da tsala-tsalan ‘yan mata wadanda suka fi ku, ku kuwa sai ku yi shekaru goma kuna yawo babu mashinshini, da anzo neman aurenku ace ai fada suke yi da kishiyoyi, suna ya lalace. Shi namiji yake, ko me zai yi ado ne akan ku. Kananan ‘yan iska. Kada ka sake kula kowa ni zanji da su, zo ka wuce.” Www.bankinhausanovels.com.ng Zakiyya da ta ji maganar takarda sai kuma idanunta suka bude. Duk da haka sai da ta mike tana duban Umma sama da Kasa ta dubi Nasreen ta fara bata amsa, “Uwarki arniyar nan ita ce kare ba ni ba. Ke kuma da kike cewa ya sake mu, ai ni ko ya sake ni babu inda zanje domin naci gida Wallahi, saboda abinda ke cikina dole shi ne magajinsa. ”
Sultan ya ja ya tsaya cak! Daga barazanar dukan da yake shirin kai mata. Maganar ciki ya razana dukkan mutanen da ke cikin dakin daga ciki har da Umma.
ZAMU TASHI
Sultan yana jin maganar ciki ya cika da farin ciki, Allah ya dora masa son haihuwa a rayuwarsa, har addu’a ya sha tashi cikin dare ya yi akan Allah ya amshi addu’arsa. Danasanin dukan da ya yi mata kawai yake yi. Tsoron kada cikin ya zube ya shige shi. Ita kuwa Zakiyya tana ganin tarkonta ya kama abinda take so ta saki ajiyar zuciya. Umma kuwa kamar za ta yi hauka jin Zakiyya tana dauke da ciki. Nasreen kuma har cikin zuciyarta ta ji dadin cikin nan, a ganinta za ta riKe dan Dee dinta kamar yadda take fata. Umma ta liliyo wani ashar ta watsa tana duban Zakiyya, “Allah ya tsareni da hada Www.bankinhausanovels.com.ng zuri’a da ku.
Wailahi idan ina numfashi baki isa ki haihu a gidan nan ba. Yaushe za ki haifo mana masifa kamar yadda uwarki ta haifawa mahaifinki masifa.”
Nasreen dai tana farin ciki amma kuma ta kasa daina maimaita arniya. Idan ta fahimta mahaifiyar da ta kawota duniya ba ta Sallah kenan? Ya zama dole Sultan ya amsa mata wannan tambayar. Zakiyya kuwa juyawa ta yi ta shige daki abinta.
Sultan ya koma gun mahaifiyarsa yana ce mata bai kamata tana irin kalaman nan ba, kawai ta yi masu addu’a. Umma fa duk ta rude tana mamakin yadda akayi har Zakiyya ta yi ciki. Shi kuwa Sultan barin gidan ya yi cike da farin ciki ya rasa me zai yi wa Zakiyya ne domin ya faranta mata? Gaba daya ya mance da wata Nasreen, har sai da yamma-da ya dawo daga Office ya tarar da ita zaune a Kofar gida. Don haka ya daure fuska kamar tana ganinsa, zai wuce ya ji sassanyar muryata tana magana, “Sannu da zuwa Dee. Da. gaske mahaifiyata – arniya ce? Su waye mu? Bamu da dangi ne?” Ta Karashe muryarta tana rawa. Wani irin tausayinta ya karyo masa, dole ya dawo da baya yana dubanta. .
A gabanta ya durkusa yana Kare mata kallo. Fuskar nan ta rame babu abinda kake hange sai dogon hancinta, da dan bakinta mai kyau. “Nasreen kuna da dangi, ni Abdullahi Lukman ni ne danginki, ki gayawa kowa da babbar murya, ni ne danginku,Www.bankinhausanovels.com.ng haka babu wanda ya isa ya cire ni daga cikin danginki. Na san idan na gaya maki magana za ki yarda da ni, Wallahi mahaifiyarki ta rasu tana cikakkiyar musulma, ita ba arniya bace Zakiyya ta gaya maki hakanne dan ta Bata maki rai, ba dan tana da tabbaci akan hakan ba. Bana son ki baiwa wani.fuskar da zai iya baga maki rai, haka bana son kalaman Batacin ya zauna a zuciyarki. Ina fatan kin fahimce ni?” Cikin shessheKa ta daga kanta. Yau bai da lokacin lallashin ta, don haka ya mike ya shige ciki babu ko waiwaye.
Zakiyya an hau dokin zuciya, da Kyar ya lallashe ta suka koma gidan jiya, ko ta kan Umma bai bi ba, wacce take can cikin tashin hankalin cikin da Zakiyya take dauke da shi. Ita kuwa Nasreen jin mahaifiyarta musulma ce ya rage mata irin radadin da take ji.
**************
A cikin wani katafaren falo mai tsananin girma, haka yana dauke da kayan alatu. Karya ne ka tsinci kanka a cikin falon nan ba ka rude ka gigice ba, domin kai tsaye zaka Karyata kanka idan aka tabbatar maka a cikin Kasarmu Najeriya kake. Wasu manyan mutane ne, wadanda kallo daya zaka yi masu ka tabbatar da sun ci sun Koshi, haka naira ta zauna masu.
Kai tsaye idan akace akwai rashin imani a tattare da su. za ka Karyata hakan. Gaban su kayan marmari ne cike, wanda a Kalla sai su kwashe fiye da Sati suna sha basu Kare ba. Haka daga fasan kafet din da ke malale a tsakiyar falon, wasu banKararrun, kaji ne, da naman rago sai tashin Kamshi suke, sun ji tattasai da albasa. A gabansu wasu yara ne ‘yan kanana da aka kawo masu, Www.bankinhausanovels.com.ng kowanne yana duba wacce tayi masa. A Kalla yaran ba za su wuce shekaru goma goma a duniya ba.
Kallon wata Katuwa Alhaji Kabir ya yi yana zare idanu, daga bisani_.ya dubi murdeden mutumin da ke tsaye kamar andasa bishiya yace, “Kai Boy ya akayi ka kawo mana yarinyar da ta . wuce shekarun da muke nema?
Wannan yarinyar ai ta san namiji idan ka kula da yadda take zazzare idanu.”
Gaba daya manyan mutanen suka yi dariya suna sake duban yaran da kayan Makaranta a jikinsu hakan ke nuna cewa daga Makarantar aka kwaso su. Akwai wani Alhaji a cikin su wanda magana bata dame shi ba, da alamun dai shi ne babba a cikin su, domin kalan girmamawan da ake yi masa daban ne. Tunda ake abubuwan nan
sai yanzu ya dago yana duban yarinyar da aka ce ta cika girma. Da hannu ya yi masa alamun ya fita da yarinyar, babu musu daya daga cikin su ya fita da ita. Daya bayan daya yake duban su, sannan ya mike yatsa ya nuna wata wacce duk ta fi su Kankanta ya kuma nuna dakin da za u shiga da ita. Wannan ce dabi’ar manyan mutanen masu lalluBe cikin kayan mutunci wato Babbar riga. Dabi’arsu ce a kawo masu yara Kanana su aikata fyade da su, su mayar su watsar a tith, Wannan mummunar aikin ya jawo tarin matsaloli a garin Kaduna, wasu suna mutuwa, wasu kuma suna kamuwa da cutar yoyon fitsan, a ya yin da wasu suke Kare rayuwarsu a gadon asibiti. Haka anrasa su waye suke aikata irin wannan muguwar Barnar a cikin al’ummarmu? Da yawa ana ganin samarin kan layi ne, hakan yasa aka sa masu idanu, tun basu damu da lamarin ba, har su kansu idanunsu ya bude da aikata irin wannan barnar. Babu tausayi bare imani, babu tunanin makoma, bare a tuna cewar watarana za ayi wa ‘ya’yan su. Ko da yake suna ganin suna da wayo ne sun killace nasu suna bata na wasu, abinda suka manta shi Allah babu ruwansa ba a yi masa wayo ko dabara. Su Alhaji Kabiru suna nan zaune suna jin ihun yarinyar nan har ta sume, a Www.bankinhausanovels.com.ng lokacin ya kammala da biyan buKatarsa ya sa a ka fita da ita aka kawo wata. Sai da ya tara da yara biyar a lokaci guda, kamar wani injin sannan ya fito ya sa a watsa sauran a cikin daki zuwa anjima. Su Alhaji Kabiru su ma suka shiga da nasu. Sai bayan sun natsa ne, sannan ya dubi Alhaji Kabir yana magana cike da nishadi, “Alhaji Kabir ya maganar case dinnan da yaran nan marasa kunya suke bi? Sun isa su tona min asiri? Tun kafin a haife su nake shaKar numfashi a duniyar nan, kuma nake aiwatar da aikina babu kuskure, me yasa rana tsaka suke tunanin za su iya tona min asiri?”
Alhaji Kabir ya saki dariya ya ce, “Mai ja da kai ba a haifi uwarsa ba, bare shi kansa. Ai idan zan yi waya can in da ka turani anan nake yi in cillar da layin. Yanzu halin da ake ciki dai sun . ki hakura, idan ka je wajen garejin nan, za ka sami ‘yan sandansu sun badda kama. Yanzu haka an tabbatar min Nora da iyalanta suna wurin su, sun sama mata wuri mai kyau. Sai dai kuma Nora bata san komai akan mu ba, hakan yasa dukkan bayananta suka zama masu rauni. Ka kwantar da hankalinka ka ci gaba da dukkan abubuwanka idan muna raye babu wanda ya isa ya taba ka. Ka dauka kamar an gama wulaKanta nufin su. Yanzu dai mu yi maganar yara biyar din da Malam ya ce ka tara da su, zuwa anjima sai inkai masa saKon kenan?” Bai amsa ba, sai gyada kansa da ya yi. Yana nan zaune aka dinga fita da yaran da ya lalata masu rayuwa, yana jin wani nishadi a ransa, gani yake duk duniya babu wanda ya kai shi zama cikin natsuwa. Can kamar an tsikare shi ya ce, “Saudatu ta mutu da cikinta, sakamakon sassare ta da yarana suka yi, me zai sa mu amincewa wata barazana akan akwai yara? Wannan ba abinda hankali zai iya dauka ba ne. Shi kuma Khamis S. Idris da yake nuna jarumta da shi kansa Ashmaaan din da muka nemi hadin kansa ya Ki amincewa zamu iya kawo Karshen rayuwarsu kowa ya huta. ‘Yan jarida nawa suka yi mana Www.bankinhausanovels.com.ng girman kai muka gama da su? Nawa suka botsare mana muka afka da su cikin rami? Bare wadannan Kananun Kwarin. Idan muka ga da gaske suna son fitar da dayan fuskarmu ina ganin sai a gama masu aiki, ba wai don yana soja ne zai ba mu tsoro ba, sojojin da yawa suna suka tara. Mu sojojin mu da muka basu training kisa suka iya ba duka ba. Wai waye dan sandan da aka ce shima ya tsaya akan lamarin?”
Alhaji Kabir ya ce, “Allah ya taimake ka. Ina ganin kamar IG ne ya tsaya a kan lamarin.”
Sai yanzu Alhajin ya yi wani shu’umin murmushi wanda ake yi masa lakabi da Alhaji na titi, ya ce, “Mu Allah na tuba ko J ne da Z bai dame ni ba, ban jin ma zai dameni. Kada ku neme shi ku bar su da kansu za su Zo su ce sun – janye maganar. Ban ga dalilin shisshigi a cikin abinda bai shafeka ba, na fahimci neman suna ne. da kuma neman ace IG yana da gaskiya ga shi ya binciko abinda kowa ya kasa bincikowa. Ni kuma ba zan taba barin sunan IG ya bunKasa nawa kuma ya zama a Kasa ba, har gobe ban yarda da rashi ba, nafi yarda da samu.” A nan suka ci gaba da tattaunawa suna yi suna shan kayan itatuwan da ke gaban su.
Sultan ya kasa tsaye ya kasa zaune wajen shirye-shiryen tafiyan Nasreen, za ayi tafiyan ne da Jidda matar Al-ameen, da kuma Naufal. Kan Sultan ya dau zafi, haka ya hada Nasrcen da dan sanda suka je akayi mata duk wani abinda ake buKata na tafiya. E passport dinta yana hannunta. Don haka lokaci kawai suke jira jirginsu ya tashi. Ta Lagos za su wuce, don haka za su bi jirgi zuwa Lagos daga can za su wuce. Al-ameen shi zai jagoranci tafiyar tunda Sultan babu dama, kuma daman Al-ameen shi ke da masaniya da asibitin. Asibitin mai suna THE LONDON CLINIC (EYE HOSPITAL AND OPHTHALMOLOGY) Duk wanda yasan fitaccen asibitin London Clinic yasan Eye Centre – ne mai kyau da Kwarewa wajen sanin makaman aiki,Www.bankinhausanovels.com.ng Karin abin burgewa dan uwanmu ne musulmi zai yi wannan aiki. Sai da ya gama komai sannan ya sanarwa Umma, aikuwa ta ce ita a kasheta a rufe bata yarda Nasreen ta bar Kasar nan ba. Hankalin Sultan ya tashi, yasan abokansa sun yi masa kara, ba zai yuwu sun gama kashe kudinsu sannan ya zo ya ce masu tafiyar babu ita ba. Gabadaya ya fita hayyacinsa, ga rigiman Zakiyya da kullum kwanan mita take yi akan zai fita da Nasreen waje Yau ya gaji ya dubi Zakiyya da yake rasa sonta yake ko kuma Kinta? Ya ce “Haba Zakiyya ya kuke son in yi? Nasreen amana ce agurina a kan me zan bar rayuwar idanunta ya salwanta? Haka zalika babu wasu kudina abokaina ne suka yi min wannan karan Sai in ce bana so? Ko Nasreen ba matata ba ce dole zan nema mata lafiyarta, wannan hakkina ne. Da za ki kwantar da hankalinki idan ~ za ki haihu sai infita da ke ki haihu a duk Kasan__ . da kike so.” Zakiyya ta yi shiru, saboda tana sane da bata da komai a cikinta, ita kanta ta Kosa ta sami cikin nan dan ta kula shi ne farin cikin Sultan. Haka ta Kara samun matsayi ne a ranar da ta furta maganar ciki. – Bayan ya samu ya shawo kan Zakiyya, sai ya koma gun mahaifiyarsa yana rokon ta, amma fir taki yin magana, dole ya danganta maganar ga mahaifinsa, ransa ya yi matukar baci don haka ya kira Hafsat a waya ya ce ta kai mata wayar. Tana dauka ya lullube ta da fada ta in da yake shiga bata nan yake fita ba, ya kuma Ja mata layi akan abinda take shirin aikatawa. Dole Www.bankinhausanovels.com.ng
ta janye Kudurinta, amma kuma ta gaya masa ana dawowa da ita ya tabbatar ya dawo da ita Kaduna, domin itama komawa za ta yi, ta gaji sosai da rashin mutuncin Zakiyya, uwarta kawai take son gani a wannan gabar. An shirya Sultan shi zai yi masu rakiya har zuwa Lagos. Ana gobe za su tafi, su Yumnah da ibtihal da dukkan sauran jaruman mata suka sami isowa. Umma ta karbe su hannu bibbiyu sai daga baya aka bar matan suna tattaunawa. Sai dai ita Nasreen bata iya cewa komai ba, ta yi nisa a cikin tunani.
Yumnah ta tabota ta ce, “Wai me ke damun ki ne haka? Tun da muka zo na fahimci kina cikin damuwa. Ga shi duk kin rame kin lalace. Ko dai tunanin tafiya ki bar Yaya Sultan kike yi? Idan ba SIRRI ba ne ki sanar da mu Kila mu taimaka.”
Ibtihal ta dube ta ta ce, “Gara ke, ba jimawa za ku yi ba, ni kuma da na bar Najeriya tun ina da cikin ‘yan biyu fa? Wallahi Yumnah yadda kika san zan mutu da rashin mijina. Babu waya babu wata hanya da zan ganshi. Ai nasha wahala duk da AKARAN KAINA, na hakura da hakan, don ina da tabbacin yana can yana Kwato min ‘yancina.
Tasleem ta kafe wayarta da ido tana murmushi, hakan yasa Yumnah ta fizge wayar tana harararta. Kallon su ta yi, sannan ta saki murmushi. “Ni kuma da miskilancin mijina na sha wahala. A lokacin da kaina nake cewa KOWA YA KWANA LAFIYA, shi ya so. Amma yanzu ai na sauke komai. Ki cire damuwa a ranki Nasreen, akwai ranar da za ki yi dariya, indai da gaske ke din Jarumar ‘yar mutan Borno _ ce, za ta kawo maki mafita cikin ruwan sanyi, har ma ta tsatso maki girma da mutunci a idon duniya.” ”
Shahida ta musKuta ta ce, “Ni har gobe ZUCIYA ta kasa mance Yaya Shahid, sai dai Karfin karamcin Yaya Haisam ya danne komai. Kamar duk cikin ku babu wacce ta kaini shan wahala, tunda har hauka na yi na bi titi. Wallahi sai na ga kamar ni ce ‘yar mutan Borno ba ta so a duk cikin jarumanta.”Www.bankinhausanovels.com.ng Khairi ta dube su ta ce, “A’a Shahida, nima nayi rayuwar daji, rayuwar rashin dace da Kawar arziki. Ganin komai nake yi kamar A MAFARKINA. Amma yanzu ai ya zama labari.”
Jidda ta yi tagumi daga bisani ta janye tana cewa, “Allah ka sakawa mijina da alkhairi. Uncle Al-ameen ya bani kulawa a lokacin da ya kamata ya daure ni ya jefar a masai. Na ba shi ciwon kai Www.bankinhausanovels.com.ng amma yana tare da ni. Daga Karshe ya kawo ni cikin zuri’arsu na sa masu damuwa, a lokacin da na shaKu da su aka kashe min su. Tabbas na amince AKWAI LOKACI, da komai zai zama labari. Mu dai ci gaba da bin ‘yar mutan Borno na tabbata za ta ci gaba da hada mana zumunci mai Karfi ta yadda mutanen duniya za su yi koyi da mu, wajen hada kai da tallafawa dukkan macen da take da buKatar taimako. Zumuncin mu ya fita daban ba irin nasu bane. Nasreen ki gaya mana damuwarki ko muna da shawarwari, idan kuma abin ya fi Karfin mu sai mu dangana da uwar dakin mu Fatima Dan Borno.”
Gabadaya suka yi na’am da zancen. Muslima ta ce, “Ni ma nasha wahala, har dan fashi na aura. Allah ya saka wa Mahbub da alkhairi ya Kara masa kwarjini a idon duniya. Idan kana yin abu baka tuna MAFARIN LAMARIN, dole abin zai kwabe maka, da muka dogara ga Allah ba ga shi yanzu ya zama labari
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG