AUREN KWANGILA BOOK 1 CHAPTER 3 BY SUMAYYAH ABDULKADIR
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
Da gudu ya jefar da littafin ya nufo falon. Habiba ce ta fadi a kasa ga ta nan tana murkususu male-male cikin jini. Fate-faten ya watse a kasa, plate din tangaran din ya tarwatse ba abin da yake ambato saboda gigicewa sai “Subhnallah, zamewa ki ka yi?” Babban abin da ya ruda shi wannan jinin da ke malelekuwa daga kafafunta. Ya rasa me zai yi ya taimaka mata, ba a kiran Mammah a waya in tana islamiyya, bari kawai ya kira asibiti kai tsaye, don Daddy ma ba ya gari yana garin ‘ABHA’.
Kan wayar falo ya nufa da sauri ya duba ‘code’ na kiran (Accident & Emergency) na asibitin su ya kira, a takaice ya yi musu bayani suka ce suna
ZAMU TASHI
tafe da ambulance . Isowar jiniyar motar asibitin gate din gidan ya yi daidai da dawowar Mammah, direba ya dauko ta daga islamiyya ta ga an fito da mutum kwance bisa gadon daukar marasa lafiya, jini kaca-kaca an shiga ambulance an ja motar an tafi. A sukwane ta fada cikin gidan suka gabza karo da danta Abdul’azeez shi ma a firgicen yake, gabadaya ya gigice ya kamata ya rukunkume ya ce, “Mammah Habiba ce, faduwa ta yi”. Kamo hannunsa ta yi suka fito, direban nasu ba bahaushe ba ne, dan Sudan ne sunanshi Salah, motar suka fada Mammah ta ce da Salah su bi bayan ambulance din. Www.bankinhausanovels.com.ng
Likitoci ne rankatakaf a kan Habiba, abinki da kasar da aka san darajar rayuwar dan Adam fiye da ko’ina. Mammah da Abdul’azeez na bakin kofar dakin da aka shigar da Habiba suna ta safah da marwah, bakin Hajiya Maryam dauke da Habiba, ta rabo baiwar Allah da kasar haihuwarta ba tare da ta san komai a kanta ba, ko inda ta fito. Allah ya
gani duk masu aikin da ta ke yi ta san asalinsu da yawansu har kauyensu tana zuwa, amma Habiba ta karbe ta (while she was desperate) a neman mai aikin ba tare da wani bincike ba, kuma tunda suka zo ba ta bincike ta a kan komai nata ba, idan ta mutu a ina za ta nemo danginta? Sannan me za ta ce musu ya kashe ta? Hawayen tausayi da tashin hankali ya zubo mata, ta kai bakin hijabinta tana sharewa.
Abdul’ azeez ya yi tagumi a zaune kan wata kujera ta silver. Rokon Allah yake cikin zuciyarsa, Ya sa ba wani mummunan lahani ya samu Habiba a dalilin yi masa girki ba. Ya dauki alhakin hakan kacokam ya dora a kansa. Tana cikin aikinta yazo ya sata aiki. Duk da haka bai yi hawaye kamar Mammah ba, idanunsa ne suka kada suka yi jazir, hankalinsa na kara tashi in ya tuna sanda ta ce masa ai ta gama, ya zauna ya ci a kicin din, ya ce shi a’ah sai dai a biyo shi da shi library . Www.bankinhausanovels.com.ng
Wajen mintuna talatin suka kwashe a haka kafin daya daga likitocin ta fito, likiciyar Balarabiya ce mutuniyar Egypt, ta ce da Mamma ta biyo ta ofishinta. Mammah jiki na rawa ta bi ta.
Wayar Mamma na hannun Abdul’azeez ya ga shigowar kiran Daddy. Da sauri ya amsa, ya ce, “Daddy ka dawo?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya ce, “A’ah Azeez ina bisa hanyar dawowar, ina Mamarku ba ni ita, jikina na ba ni wani abu na faruwa shi ya sa na kira ta”.
Abdul’ azeez ya ce, “Eh Daddy, muna asibiti ma yanzun Doctor ta yi kiranta”. “Waye ba lafiya?” Ambasador ya furta cikin faduwar gaba, sannan cikin sanyin murya.
Abdul’azeez ya gaya masa duk abin da ya faru, a karshe cikin rawar murya ya ce, “Ni na jawo ko Daddy? Da ban sa ta aikin ba da ba ta fadi har ta ji ciwo jini na zuba daga jikinta ba ko Daddy?”
Daddy ya ce, “Cool down my son, kwantar da hankalinka ba kai ka jawo ba, tsautsayi ne wanda ba ya wuce ranarsa. Ko ba ka sa ta girki ba in Allah ya yi za ta fadi a yau ta ji ciwo za ta fadi ne.
So kwantar da hankalinka za ta warware insha Allahu, kai wa Maman wayar har ofishin likitar a gaya min ko me ke nan’.
Hajiya Maryam, uwargidan Ambassada Hamza Dakata na can ta daskare a zaune ta zama mutummutuma a kujerar da ke fuskantar likitar mata Dr. Unaisa Jamaal da takardu a hannu. Ta fi yarda da ba daidai likitocin suka dubo ba dai, wai Habiba za a cire wa baby (CS) dan wata takwas saboda ba za ta iya haihuwa da kanta ba, ta zubda jini, sannan ta bugu ta inda har mahaifarta ta samu lahani, idan kuma ba a gaggauta raba ta da babyn ba za a iya rasa su bakidayansu. Rayuwarsu cikin hatsari ta ke. “Ciki!
Hajiya Maryam ta tambaya tana zaro wa likiciyar manyan fararen firgitattun idanunta. Dr. Unaisa ta gyada kai cikin tabbatar mata.
“Kuma bai kai lokacin haihuwa ba, za mu cire shi ne don tserar da rayuwarta da ta abin da ta haifa. Ku yi gaggawar sanya hannu don a shiga da ita dakin tiyata. Www.bankinhausanovels.com.ng
Tsananin rudewa Hajiya Maryam ta gama fita hayyacinta, shin da ma da ciki ta dauko Habiba, ko a nan Jeddah ta samu abinta? Tsananin rudewa ya sa ta kasa lissafa iya watannin da ta yi da Habiban. Yau watansu shida tare a birnin Jeddah in haka ne Habiba da abinta ta zo yana dan watanni biyu.
Jikinta yana karkarwa ta zura hannu a jaka don dauko wayarta ta kira Ambasada, tsabar rudewa ta ma manta wayar na hannun Abdul’azeez.
Daidai lokacin yaron ya murdo kofar bayan likita ta bashi iznin shigowa ya mika mata wayar. Ta kira Ambassador da sauri, bai bata lokaci ba ya amsa don a lokacin ya gama magana da Abdul’ azeez, wayar tana hannunsa.
“Daddy zo ka sa hannu don Allah a yi wa Habiba tiyata, baby za a cire mata. Wai ashe duk tsawon lokacin nan Habiba ciki ne da ita ba ta fada min ba, ni kuma ban taba ganewa ba, ni wawuyar ina ce Daddy?”
Dariya Ambassada ya yi, “Ah toh! Wanda bai ji bari ba ai ya ji hoho. Garin kwashe-kwashenki watarana fin haka za ki kwaso. Ina cikin Jeddah ku ba ni minti goma zan karaso, ba ni likitan”.
Ta mika wa Dr. Unaisa wayarta jikinta yana ta mar-mar, Ungo maigidana zai yi magana da ke”.
Ta karba suka yi magana kadan, ta mayar mata. Mammah ta kara a kunnenta, Daddy ya ce, “Ke da ki ka kwaso abinki sai ki sa hannu, sun ce ba za su iya jirana ba, babu lokaci”. Ya kashe wayarsa.
Jiki na rawa ta karbi takardun ta rattaba hannu suka mike tare ita da likitar suka fito. Nan inda ta bar Azeez ta tadda shi suka hadu suka zauna jigum-jigum ta kasa gaya masa ko me ke akwai. Ita kuma Doctor ta wuce su suka shigar da Habiba dakin tiyata. Www.bankinhausanovels.com.ng
**********
An dauki awanni biyu kenan, daidai lokacin da aka kira sallar la’asar. A lokacin ne Abdul’ azeez ya tuna ko sallar azahar ba su yi ba shi da
Mammah. Yana mamakin yanayin da ya ga Mammah a ciki na gigita fiye da sanda suka zo tun lokacin da likita ta kira ta ofishinta. Ya zarce na ace ciwon Habiba ne kadai ya sanya ta a wannan hali.
“Mammah mu je mu yi sallah”. Ya fada har sau biyu, kafin Hajiya Maryam ta ji me yake cewa, da yake tana cikin lalura sai ta ce, “Je ka kayi, zan zo daga baya”’Ya mike ya bar reception din zuwa masallacin cikin asibitin. Tashinsa da fitarsa ya yi daidai da fitowar likitoci biyu daga dakin da aka shigar da Habiba daya daga cikinsu rungume da jariri sai kyanyara kuka yake nannade cikin shawul fari kal, wanda ta san ita dai ba ita ta ba su ba. Mikewa ta yi tsaye cikin hailala ta tare su tun kamin su iso ta mika hannu ta karbi jaririn da ba ta san mace ne ko namiji ba. Ta maida dubanta ga likitar cikin zakuwa, “Habiban fa?” Sai a lokacin ta lura da fuskokinsu dukkaninsu babu mai walwala. “We are sorry…”. Dr. Unaisa ta fada cikin turanci. Ba tare da damuwa da yadda Hajiya Maryam ta fiddo ido cikin dimaucewa ba ta ci gaba da yi mata bayani cikin lallashi.
“Mun yi duk iya kokarinmu mu yi saving dinta Allah bai ba mu nasara ba. Ta zubar da jini da yawa, kuma tana da hawan jinin da ba ya samun ranta sun datse harshenta da muka sa mata ruwan nakuda ba tare da sanin cewa tana da hawan jini ba (induced labour). Dole muka yi fida don ceton ranta bama ta abinda ke cikinta ba, ko kafin mu Www.bankinhausanovels.com.ng
gama, ta cika”. Hawaye suka ziraro daga idanun Mammah masu zafi na kewa, sabo, tausayi da kauna. Ta rungume jaririn tsam a kirjinta. Daidai lokacin da Abdul’ azeez da Daddynsa suka shigo, Dr. Unaisa ta ce ta ba su jaririn za su binciki lafiyarsa don ba ya numfashi yadda ya kamata. Kasa mika mata ta yi don gani ta ke in ta ba su za su kara dawowa hannu rabbana su ce jaririn ma ya cika. Kaunar da ta ke yi wa Habiba daga Allah ne saboda kyawawan halayenta. Daddy ne ya kwakulo jaririn daga hannunta ya ba su suka juya wani daki na musamman da ake kira (day-old). Shi kuma ya kama hannunta ya ja ta har kan kujerun reception din ya rungumo ta yana lallashi. Kullu nafsin za’ikatul maut Maryama, cool yourself…” Ya fada yana bubbuga bayanta, sai ta fashe da kuka. Abdul’ azeez yace, “Daddy Habiba ta rasu?”Ya daga masa kai. To wannan Baby din fa? Haifarsa ta yi?” Ya kara daga masa kai. Bai san sanda shi ma ya fashe da kuka ba. Haka Daddy ya zama dan lallashi, ya lallashi uwar ya lallashi dan. Daga karshe su duka biyun ya hada ya rungume. A haka aka turo gawar Habiba ta gabansu aka saka a ambulance duk suka mike suka bi bayan motar a tasu motar zuwa gida. Tun a mota Ambasada ke waya da abokan aikinsa na Embassy Of Nigeria da makotansa yana fada musu akwai Janaiza a gidansa, don haka kafin su isa har mutane sun fara cika get dinsa. Hajiya Maryam da matar makocinsu Hajiya Sugrah su suka wanke Habiba suka shirya ta, mutane sama da Www.bankinhausanovels.com.ng hamsin duk ‘yan Nigeria ne suka sallace ta suka yi mata rakiya zuwa gidanta na gaskiya. RAI ba a bakin komai ba! Duk haka za mu tafi daya bayan daya. Ya Allah ka sa mu cika da kyau da imani (hawaye).
Sai dare mutane suka daina shigowa, ya rage daga Hajiya Maryam sai yaranta. Sun hadu su biyar har ita sun yi jigum-jigum a babban falo. Da gani cikinsu duka babu wanda gushewar Habiba ba ta doka ba. Musamman Abdulazeez. Hatta Halim da yake karami ya yi sanyi ya daina walwala, ya fi kowa sabawa da Habiba, ya fi kowa hawa bayanta ta goya shi. Sai ta yi awanni biyu da shi goye a bayanta tana ayyukanta ba tare da ta gaji ba. Suna yi suna hira tana biyewa shirmensa babu kosawa. Tun safe bai ganta ba, ya kuma ga sanda aka fita da ita kwance kan wani gado ya tambayi Mammah ina za a kai Habiba sai ta sa mishi kuka, tun daga nan bai kara tambaya ba, sai dai kuzarinsa ya zube, ya yi shiru a kwance saman kujera kamar yadda ya ga kowa ya yi shirun.
A lokacin Hajiya ta tuna da babyn da suka baro a asibiti. Zumbur ta mike ta tadda Daddy a (bedroom) dinsa. Yana zaune a bakin tankareren gadonsa yana waya, shi fa da alama mutuwar nan ba ta doke shi ba, harkokin gabansa yake yi tunda ya tsaya ya yi wa gawar Habiba gata, ya yi duk abin da musulunci ya umarce shi tuni ya koma sabgoginsa.Dukkansu tun karin kumallon safe ba abin da ya kara shiga bakinsu, amma tana
kallonsa ya je kicin ya dafa shayi da kansa ya aika direba ya sayo masa Dajaj (KFC) ya shige daki ba ta kara jin duriyarsa ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Da sallama ta shiga dakin, bai fasa wayar da yake yi ba. Ya daga ido ya dube ta, ta zauna gefensa tana kallon yadda ya ci kaza ya bar kasusuwa haushinsa ya kama ta, wato ba ya taya su makokin da suke ciki balle ya je ya lallashe su ita da ‘yan samarin ‘ya’ yanta. Ya sanya hannunsa cikin tafukanta ya matse da karfi, a lokaci guda yana ci gaba da wayarsa inda ta fahimci da kawunsa Sanata Abdulkarim yake yi. Kawun da ya zame masa kamar aboki sabida shekarunsu daya kuma tare sukayi karatu tun daga sakandire har jami’a. Sai da ya kammala ya ba ta (attention) dinsa. A sanyaye ta ce, “Zan koma asibiti ne in ji halin da Baby ke ciki’.
Sosai ya kalle ta, yini guda duk ta zuge, ta fige. Yana mamakin wannan kauna ta ‘yan aiki da Allah ya dora wa maidakinsa. “A dawo lafiya, Allah ya jikanta, Ya ba ku hakuri’”. Tace, “Amin”. Tare da mikewa za ta fita. Maryama!” Ambassada ya ambata cikin sanyin murya. Ta dakata ba tare da ta juyo ba. Ya mige ya tako zuwa jikin kofar, har inda ta ke tsaye rike da (handle) din kofar. Hannayensa ya kai ya zagayo da su cikinta, wato ya rungume ta ta baya. Ya dora kansa saman kafadunta. “Yau ko sumba daya ban samu daga Maryam dina ba. ‘m sure kina son Habiba. Ko kanwarki ce ta ciki daya sai haka! My condolence dear, Allah ya yi mata rahma’”. Sosai hawaye suke sauka a kan kumatunta. Ta juyo ta rungume shi ta sumbaci goshinsa, Na gode Daddy”. Ta sake shi da sauri ta fita. Bayan fitarta Ambassador zancen zuci ya shiga yi, “Allah ya sa kada ta ce ita za ta rige abin da mai aikinta ta bari. Abin da ba zai taba yiwuwa ba ne, ko ‘ya’yan ‘yan uwansa ba ya dauka riko balle ‘yar mai aiki, duk wani taimako zai yi maka, amma ban da dauko ka ya tsoma cikin iyalinsa. Yana da kakkarfan ra’ayi a kan ‘single nuclear family life’, ta yadda ko bako ne ya zo zai kwana daya ba ya sakewa cikin iyalinsa har sai bakon nan ya tafi. Ji yake kamar a kansa yake zaune. Ya girgiza kai, ya ci gaba da kiraye-kirayen wayoyinsa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Hajiya Maryam a gaban tebirin likita Unaisa, “Jaririyar mace ce, an haife tada cutar pneumonia , numfashinta ba ya fita yadda ya kamata. Da alama uwarta na yawan ta’ammali da ruwa, da shan ruwan sanyi ko? Za mu rike ta cikin kwalba (incubator) har sai ta cika watanni tara’’. Hajiya Maryam ta ce, “An gode Doctor, Allah ya raya ta. Zan iya ganinta?”
Sosai kuwa. Zo mu je, don yanzu za a cire (oxygen cylinder) din a sanya ta a kwalba. In ta cika watanni tara sai ki zo ki tafi da ita”. Hajiya Maryam ta tsura wa jaririyar ido, ta dade
ba ta ga kyakkyawar halitta ta fulanin usul irin wannan ba. Komai nata na Habiba ne. A very cute baby. Ta kai bakinta ta sumbaci goshinta, kumatunta da bakinta wata irin kauna ta UWA ga DA na ratsa zuciyarta daga Ubangiji subhana. Allah bai taba nufarta da haihuwar diya mace ba, abin da kullum ta ke wa addu’a, amma tun daga kan Halim haihuwar ma ta dakata mata ko batan wata ba ta kara yi ba. Ba ta jin ko dangin Habiba da uban yarinyar nan za ta yarda su raba ta da wannan jaririya da ta sanya wani irin sanyi a idanu da zuciyarta. Da kyar Dr. Unaisa ta karbe jaririyar ta shiga wani daki na musamman da ita. Direba ya dauko Hajiya Maryam suka dawo gida. Www.bankinhausanovels.com.ng
Bayan kwana bakwai da rasuwar Habiba, Hajiya Maryam tana zaune a falo ta kira Hajiya Halima aminiyarta. Wato wadda ta samo mata Habiba. Bayan sun gaisa da tambayar lafiyar iyali, Hajiya Maryam ta ce, “Halima, ko kin san asalin inda Habiba ta fito? Ina nufin garinsu na ainihi, miji da iyayenta?” Hajiya Halima ta ce, “Tabdijam! Wallahi ba ni da sani a kan ko daya. Ni ma wata mai aikin Rabi’a ce (kanwarta) mai suna Asabe ta kawo min ita, kuma ta ce haduwa suka yi a motar haya sabo ya shiga tsakaninsu, duk da lokacin Habiban ba ta cikin hayyacinta ta ganta kamar wata mai iskoki. Saida ta kwana uku a wurinta tana yi mata addu’a sannan ta warware. Ta ce tana son ta samar mata gidan aiki ta fito neman aikatau ne. Asaben ta ce, ita ma aikatau ta ke a Abuja, su wuce can za ta samo mata. Suka zauna tare a gidan Rabi’a na tsayin watanni biyu tana bincika mata gidan aiki, shi ne da na ce ina so ta kawo min ita, washegari kuma na ba ki da na lura kin fi ni bukatarta. Ita kanta Asaben yanzu sun dade da rabuwa da Rabi’a ta koma kasar su Ghana. Ba mu yi wani zama mai tsawo ba da har zan binciki wani abu nata”. Hajiya Maryam ta nisa, “Halima Allah ya yi wa Habiba rasuwa”’Hajiya Halima ta ce, “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un…”
Mama ta katse wayar, ba ta so Hajiya Halima ta sa ta kukan da ta samu ya tsaya mata tun kwana uku da rasuwar Habiba.
Kullum cikin kirga kwanaki ta ke na ranar da za ta amso jaririyarta. Haka duk sati tana tafe ganin baby a cikin kwalba daga nesa cikin rakiyar Dr. Unaisa. Tana gaya wa Halim kwanan nan za ta kawo masa kanwa, ya samu abokiyar wasa da zuwa makaranta.
Hutun Abdul’azeez na wata uku ne, don haka Daddy bai barshi ya zauna a gida ba ya komai ba har watanni uku, ya dauke shi ya sanya a Tahfiz inda yake daukar haddar Alqur’ani mai tsarki daga islamiyyar wasu Larabawan Madinah da sauran littattafan addini shi da sauran ‘yan uwansa a ranakun karshen sati, wato Alhamis da Juma’ah, in sun tafi tun safe sai karfe shidda na Www.bankinhausanovels.com.ng
yamma, don haka Hajiya Maryam ba ta cikin matsalar rashin mai aiki sosai a dan tsukin, kafin kowannensu ya tafi tahfiz ta raba musu aikin
cikin gida da za su yi a tsakaninsu don ita sam bata son harka da Takari. Abdul’azeez shara, Isma’eel wanke-wanke, Usman (mopping), Halim kara bata wuri, sauran ayyukan gidan na waje maza masu aiki ke yi, kamar wanki da guga, gyaran furanni da ba su ruwa.
Rayuwar gidan Ambassador Hamza Atiku abar sha’awa ce abar koyi. Ba su da abin da ya fi tarbiyyar ‘ya’yansu da nema musu ilimi muhimmanci a gare su. Yaransu nitsattsu masu hankali da sanin yakamata. Uwar da uban kuma soyayya da shakuwa mai karfi ce a tare da su, ta yadda in ka lura za ka fahimci ba soyayyar aure ce kadai a tsakaninsu ba, akwai ta jini mai gudana a cikin jiki da jijiyoyi. Kaunar da suke yi wa yaran ba ta hanawa su ba su ingantacciyar tarbiyya, su kwabe su in sun yi ba daidai ba cikin nasiha da jansu a jiki. Sai dai fa kaunar Abdul’azeez daban ta ke da ta kowa a zuciyar Www.bankinhausanovels.com.ng Ambasada. Idan da abin da Abdul’azeez ya tsana shi ne a yi masa tsawa, ya fi son ko ya yi ba daidai ba ka fada masa a hankali shi ya sa ya fi son Daddy, ya fi sakin jiki da shi tunda Mammah tana yin tsawa. Rannan ya yi laifin yin kwallo (ball) da Magenta (qiddah) inji larabawa, sabida ta sa masa baki a abinci, Mammah ta yi tsawa. Yatsunsa biyu ya sa ya toshe kunnuwansa ya rufe ido jikinsa yana bari da karkarwa, cikin karkarwar jiki data murya ya ce.
‘“Mammah please… tell me what you want to me to do, but please don’t shout…….”. Sai ga
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG