AUREN KWANGILA BOOK 1 CHAPTER 8 BY SUMAYYAH ABDULKADIR
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
Ibrahima autan Adda ne ya taho cikin gidan don kiran Daddy ya gaya masa ya yi wasu manyan bakin daga lagos, sai ya tadda su a haka a soro. Da sauri ya juya zai koma, suka saki juna Daddy ya kira shi. Ya dawo kansa a sunkuye ya fadi sakonsa, Mammah ta koma cikin gida, shi kuma ya fita. Hafsat ta shigo tana dingishi ta sha plasta a baki da kafafu. Tun kafin ta zauna Mammah ta taso ta taro ta tana tambayarta, “Garin ya ya ki ka fadi?”
Kowa sai sannu yake yi mata, bakin ya haye ya yi suntum. Halim ya dube ta, sai ya kyalkyace da dariya. Ta harare shi da kumburarrun idanunta, ya yunkura zai fice yana ta dariya yana yi mata sannu, sannan yace “Ina ruwan alkubus! Ya hau ya yi fam!”
Baba Azumi ta kai masa duka ya fice da gudu.
Ta ce, “Mommah tuntube na yi da dutse. Ga katin wayar ga canjinki”. Ta mika mata abin da ta kudundune a hannunta na dama. Duk azabar da ta sha bai sa ta zubar dasu ba. Tsabar girmama komai na Maman ta. Mammah ta karba tana fadin, “Ni wannan katin waya da ba a je siyansa ba!”. Wata zuciyar tace da ita. Gara da aka je siyansa, watakila shi ne silar dawowar Daddy kan kyakkyawar turba”’.
ZAMU TASHI
Da aka yi sadakar bakwai Mammah ta sa direba ya dauki Baba Azumi suka kama hanyar Sokoto, domin ta ga `ya’ ya da danginta kafin lokacin wucewarsu Brussels (Belgium).
Haka suka ci gaba da rayuwarsu cikin `yan uwa cike da alhinin rashin Inna Ramatu. Sati biyu a tsakani suka wuce Abuja. Abdul’ azeez bai san da rasuwar Inna Ramatu ba, ya samu gurbin da ya nema a jami’ar Ibadan, sun ba shi kwas din da yake matukar so, wato LAW, inda zai karanci LLB tsayin shekaru biyar. Kafin isorwar mutanen Jeddah ya fara jarrabawar zangonsa na farko, Daddy na sane da hakan shi ya sa ya kyale shi kawai don kada ya raba masa hankali. Inna ta riga ta tafi, babu wanda ya isa ya dawo da ita. Azumi ta samu `ya’yanta da jikokinta lafiya a gida Sokkoto, ta sauke musu sha tara ta arzikin da ta tara musu. Maimaikon su ga
tsufa mai yawa tare da ita, sai suka ganta ras! Kamar an kwashe mata shekaru goma an zubar, da ma kuma aike ba ya yankewa tsakaninta da su, duk shekara in an zo aikin hajji daga Sokoto. Sun riga sun san a gi-dan Ambasada ta ke cikin kwanciyar hankali. Ba ta dawo Abuja ba, sai a satin da za su tashi zuwa Brussels, dukkan shirye-shiryen tafiyar tasu ya kammala. Hankalin Mammah da na `yarta ya kwanta sun zama cikin nutsuwa da kwanciyar hankali domin da gaske Daddy ya canza a kan Addar Mammah ya cure ta cikin su Isma’el, Usman Www.bankinhausanovels.com.ng da Halim. Babu nuna bambanci, babu duk wannan hayagagar. Sau da yawa sai ya yi mata abu su bai yi musu ba. Ya bude mata (account) a Brussels kamar yadda ya bude wa gabadaya `ya’yansa duk wata yana sanya musu kudi daga albashinsa saboda lalurar rayuwa mai zuwar ma dan Adam watarana ba tare da ya shirya ba. Daddy na shiga office dinsa da sati daya ya sanya `ya’yansa duka a makaranta, bayan ya karbo musu (transfer) daga makarantunsu na Jed-dah. Amma kasancewar ba su iya Dutch, Wallon-ian ko German languages ba daga Larabci sai Tu-ranci, dole ya sanya su a wata makarantar daban inda ake koyar da wadannan harsunan, don da su suke amfani (as formal language) a kasar baki-daya.
`ST. John Berchmans Collage’ ita ce makaran-tar su Hafsat Dakata a Brussels. A nan din ma an bai wa Ambassador gida a jerin gidajen jakadodinsu, mota da direbobi kamar a Jeddah, direbobi su kai shi office, su kai `ya’yanshi makaranta su dauko su. An sanya Hafsat aji daya na sakandire, Halim aji hudu, Usman da Isma’ eel an sanya su cikin masu zana jarrabawar shiga jami’ a na shekarar gabadayansu dama tsiran aji daya ne tsakaninsu, Ismael ya kammala sakandirensa a Jeddah har ya yi jarrabawar shiga jami’a. Amma da suka zo nan Brussels tsarin jarrabawar nasu ba iri daya ba ne da na Saudiyyah, suka ce dole ya jira zuwa shekara mai zuwa ya maimaita irin tasu don haka zasu zana lokaci daya da Usman kafinnan shi Usman ya kammala. Babban burinsa ya samu gurbi a jami’ar ‘Harvard’ , jami’ar nan mai tsohon tarihi a Amurka, don haka ya dage da karatu baya wasa kafin lokacin jarabawar ya zo tareda malami Bel-gian da Daddy ya daukar masa, Usman ma in yana gida yana zama a yi dashi, ba ya wasa ko kadan don ganin cikar mafarkin sa na zuwa Har-vard. Yau da gobe aka ce ba ta bar komai ba. Hafsat na girma tana kwankwadar ilimi mai tsada, kwak-walwarta na kara budewa da ilimin zamani. Bur-inta na zurfafa shi na kara karuwa a zuciyarta. Ta samu kanta da wani mayataccen ‘determination’ na son yin ilimi mai zurfi domin ta zama wani abu a rayuwa ta dogara da kanta. Tana ganin yadda Daddy ke wahala da su, shekaru na kara tura musu shi da Mammah, sun karar da kuruci-yarsu bakidaya wajen hidimarsu, cinsu, shansu, sutturarsu da iliminsu. Tana so ta zama uwa ka-mar Mammah, ta yi wa `ya’yanta abin da Mammah ke musu ko ta kwatanta. Tana sha’ awar Daddy da zurfin iliminsa wanda ta tabbata shi ne silar matakin da yake kai a yau. Don haka hafsat ta kudiri aniyar yin ilimi har sai ta kure shi in ana kurewa, za ta iya yin komai a kan a barta ta yi karatun zamani mai zurfi. Tun a Jeddah sun yi haddar Alqur’ ani mai girma, sun yi ilimin addini sosai, shi ma tana so ta fadada shi har fiye da ilimin bokon in ta samu dama. Mammah da kanta ta yi tunanin daukar musu shehin malami da zai ci gaba da ba su karatun ad-dinin musulunci a gida, a ranakun karshen mako. Ta gaya wa Daddy, ya samo wani Malami Basu-dane ya ci gaba da ba su karatun littattafan ad-dini. A gefe daya suna tisa haddar su. Yadda suke fahimtar boko haka suke fahimtar addinin musu-lunci fiye dashi, sabida foundation dinsa da suka ginu akai tun suna kankana. A tsayin shekarun da suka yi a Belgium sun je gida sau uku, su Baffa Atiku, Adda da sauran dangi sun zo Brussels sau biyu, Baffansa Ab-dulkarim duk sanda ya samu sarari yana zuwa da iyalinsa su yi hutu. Abdul’ azeez bai zo ko sau daya ba. Ba shi da sha’awar Belgium, wani kin mutum ne murdadde mai ra’ayi da akida, babu abin da ya isa ya sauya shi daga kan perceptions dinsa (beliefs), burinsa ya zama babban attorney wanda kasarshi za ta yi alfahari da shi. Yana so ya zama lawyer na farko da zai kawo sauyi cikin tsarin shari’ar da kasarmu ke tafiya a kai ta son zuciya da danne mara karfi. Yana so ya kauda cin hanci da rashawa da suka yi wa kotunan kasarsmu katutu. A kauda karya a tsayar da gaskiya, ba shi da burin zama lauya mai zaman kansa; lauyan gwamnati yake son zama. Ta haka ne zai samu damar taimakon al’umma marasa karfin kwatar hakkinsu. Hakan ba zai kasance ba sai ya kai kololuwa a karatunsa na lauya, sannan sai in ya zabi ‘CIVIL LAW’ ya zama gawurtacce a cikinta. In haka ne kuwa ashe yawon hutawa a kasashen Turai ba nashi ba ne. Lokacin hutunshi shi ya ka-mata ya zame masa lokacin jajircewa don cimma burin rayuwarsa. Daddy ya dade da kama masa dan kyakkyawan muhalli daura da makaranta a garin na Ibadan tun Www.bankinhausanovels.com.ng
lokacin da ya ce ba zai samu dinga zuwar musu hutu ba saboda yanayin karatunsa. A waya suke jin lafiyarsa, ita din ma sai karshen mako yake kunnata. Minister Abdulkarim da `ya’yansa su Farhan sa’o’insa kan yi tattaki lokaci zuwa lokaci su ziyarce shi har Ibadan, idan ka ganshi ba za ka ce dan Ambassador ba ne, sabida irin rayuwar (typical Nigerian) da yake ciki, gwagwarmayar neman ilimi yake yi yadda sauran masu rangwa-men Bata ke yi a jami’o’inmu na kudu dana arewa. Ba shi da wanda za a kira abokinsa na jiki sai ko abokin karatu. Ba ya tambayar Babansa kudi shi da kansa yake sanya masa duk wata. A ganin Abdul’azeez Hamzah Attikou, jin dadi da rayuwar jin dadi, za su biyo baya ne sa’ilin da dan Adam ya samu cikar burinsa. Amma gwa-mutsa seeking goal attainment (neman cimma burl) da rayuwar hutu da jin dadi irin ta gidansu is a barrier to goal achievement (shinge ne ga cikar burl). Saudiyyah ma da ya yarda yake zuwa sabida ita dole ce ga kowanne musulmi, kuma yana koyon karatun Alqur’ ani da sauran karatun addini, yana Ibadah a Makkah da Madinah.
A wannan shekarar da ake ciki ya fito da (LLB) mai daraja ta farko. Duk wani masoyin Dr. Hamza ya taya shi murnar wannan hazikanci na Abdul’ azeez, gabadayansu sun zo gida don yin bikin sallah karama. Sun yi sati daya a Kano suna cin bikin sallah su Hafsat na zuwa cikin gari kallon hawan sarkin Kano (Durbar) kullum ita da su Haleem da `ya’ yan su Furerah, Hafsat abin ya burge ta saboda ba ta taba gani ba sai wannan Www.bankinhausanovels.com.ng
karon. Ta shige cikin sa’anninta ta saki jiki yadda Mammah ke so. In tana gwara hausarta su Hal-ima `yar Anty Mariya da su Saimasu yi ta cin dariya. Wani zubin ma sai Haleem ya maimaita musu abin da ta fada suke ganewa, yaren Dutch (Flemish) ya mamaye bakinta ko turanci ba sosai ta iya ba, larabcin ma ta dade da manta yadda ake yi sai `yan kananan kalmomi saboda rashin abokinyi. Mammah ta hula mata hanci gefen dama da `yar barima ta danyen ‘gold’ wadda ba karamin kara mata kyau ya yi ba. Har suka koma Abuja Abdul’ azeez bai zo Kano ba yana Ibadan, sati biyu dama yaran za su yi dan hutun nasu ba mai yawa ba ne. Za su koma tare da Baba Azumi su yaran saboda makaranta. Daddy da Mammah za su tsaya ‘convocation’ din Abdul’ azeez a Ibadan wanda za a yi sati na sama. Su Hafsat suka tafi cike da kewar iyayen nasu.
Hajiya Maryam ta daga ido tana kallon babban dan nata, wanda ta kwashe lokaci mai tsawo ba ta sanya shi a idonta ba. Yana cikin kayansa na barin jami’ a kamar sauran dalibai ‘graduates’ `yan uwansa, a cikin jami’ar Ibadan-Nigeria. Ya zama babban matashi fiye da tunaninta. Wasu kin ilhamomi sun bayyana a tare da shi da ba duk maza Allah ya halitta da su ba. Ga wani siririn saje da ya kwanta gefe da gefen fuskarsa. Sauran `ya’ yanta duk sun fi shi haske, amma kalar fa-tarsa ta fi ta kowa ban sha’awa. Ya fi kama da mutanen Qatar din Misra ko ko larabawan Habasha da aka fi sani da Ethiopians. Www.bankinhausanovels.com.ng A yau ne ya cika shekara ashirin da biyar idan har lissafin da ta ke yi daidai ne. Ga tabon sujoud nan ya bayyana a saman goshinsa. Alamu ne na ba ya wasa da sallolinsa biyar kamar yadda ta hore su bakidaya. Wani matsanancin farin ciki ya ziyarci zuciyarta. Ta daga hannayenta biyu sama tana kara rokon Ubangijin sammai da kassai; “Rabbi ja’ alni muqimassalata wa min zurriyy-aty, Rabbana wataqabbal du’ a!” Fassara; “Ya Ubangiji ka sanya na zamo mai tsaida sal-lah ni da zurriyata, Ubangiji ka amshi addu’ata”. Daga Ibadan Kano suka wuce, Baban su Sha’a-ban ya hada get-together-party a Dakata na taya yaran nasu murnar kammala digirin, Farhan da Sha’aban ma sun gama duka da sakamako mai kyawu, daga jami’ ar Nsukka. Su-ya-su suka yi abinsu, babu wani bare a ciki. Daga `ya’ yansu sai jikokinsu, sai iyayensu da Kakanninsu. Walimar ta kayatar. An yi vedio, an yi hotuna don tarihi. Daddy ya nemi jin ta bakin Azeez ko zai bi su Brussels kafin tafiyarsu Law school? Abdul’ azeez ya ce, “Daddy, akwai wani course na shekara daya da zan je a kan kwamfuta a Kazaure (informatics) ina so na samu wadataccen ilimin na’ura mai kwakwalwa kafin zuwan lokacin tafiya ta hidimar kasa, in na gama NYSC zan taho, na yi maka alkawarin ranar da na zama cikakken lauya, wanda ya yi dukkan karatunsa a kasarsa ta hai-huwa zan zauna tare da ku a duk inda ku ke”. Ambassador ya dan daga kafada alamar ba shi da matsala a kan hakan, ” Do as you wish Ab-dul’ azeez, ina girmama ra’ayinka, babu laifi a cikinsa, dukkaninku na ba ku `yancin gudanar da Www.bankinhausanovels.com.ng
rayuwarku yadda ku ke so in har ba zaku karkace daga kan tarbiyyar da muke dora ku a kai ba. Ku ji tsoron Allah a duk inda kuke ku kasance masu tsaida sallah a duk inda kuka samu kanku. Itace tushen kasancewa cikin nutsuwa da kowacce nasarar rayuwa (sallah)!”.
Bai bar Najeriya ba sai da ya gama masa komai na shiga institute din ya wuce Kazaure ya fara shiga aji, sannan suka taho Brussels shi da Mammah. **** Ba su dade da dawowa ba ciwon Hafsat ya tashi, wai sun je Beach kawarta Aalimah ta ce su shiga su yi wanka, ta ce a’ a ita ba ta shiga ruwa mai sanyi, Mammah ta hana ta. Aalimah ta dauka tsoro ta ke ji shi ya sa ta ce hakan. Can ta iso inda take tana swimming ta ce, “Suhaana miko min float din can”. Ta kuwa juya don ta miko mata, kawai sai ta jata ta baya cikin ruwan ji ka ke “tsundum!” Ita dai Aalimah tana dariya tana karawa sai gani ta yi Suhaana ta sassankare idanunta na kakkafewa. Da sauri ta fito ta janyo ta waje, ta maida kayan jikinta, jikinta yana rawa ta zura da gudu neman taimako. Kwanansu biyu a asibiti kamin da a sallame su. Tun daga ranar Mamma ta raba ta da kawaye ta ce ko me ta ke so a aboki ta yi da ita, ba ta yarda wata alaka ta shiga tsakaninta da kowa ba bayan bangaren karatu. Isma’ eel ya dade da samun gurbi a Jami’ar Har-vard, shekarunsa uku kenan a Amurka, yana karantar (Sofware Engineering). Usman na bab-bar jami’ar Brussels, kai daya suke tafiya a karatun shi da Ishma. Halim na shekarar farko a wata jami’ a a Sweden. Shi kansa Usman da ke cikin Brusseels suna dadewa ba su sanya shi a ido ba, ya tattara kayansa gaba daya ya yi kaura zuwa cikin hostel wai an fi karatu in mutum yana makaranta. (Ina ruwan `ya’ yan Farfesa).
Don haka gidan daga Mammah sai autarta, wadda ke shirin zana jarrabawar karshe a high school din ST. John Berchmans College’, fitacci-yar sakandiren birnin Brussels. Sai ko Baba Azumi. Haka Hafsat ke rayuwarta cikin kwanci-yar hankali da soyayyar iyayenta uku, Daddy, Mammah da Baba Azumi. Sune duniyarta data budi ido dasu, sune farin cikin ta. Bata san wata rayuwa ba a duniya bayan wacce suke ciki. Don haka ta taso cikin wata kin nutsuwa da nutsuwar zuciya. Bata san kowanne irikin kalubale na rayuwa ba. A shekarar da ta kammala karatun sakandire a shekarar ne suka samu wani sauyin rayuwa mai taba zuciya.
***** AUREN KWANGILA! Sabuwar gwamnati ce ta hau, daga sabuwar jam’iyya mai farin jini NRC (Northern Region Congress) a kasar mu ta gado, Nigeria. Bayan an rantsar da ita ta shiga ofis, abu na farko da ta fara yi shi ne; sauke Ambassadodi na dukkan kasashen duniya tana dora sababbi masu jini a jika. Cikin Ambassadodin da aka sauke har da Ambassador Hamzah Atiku Dakata. To komai na duniya ai ba shi da tabbas ko? Haka ita kanta rayuwar, komai na cikinta fararre ne kuma kararre. Shekaruna goma sha takwas ina jakadanci, don yanzu an sauke ni bai kamata ku damu ba. Ai mun sha miya, don an bai wa matasan kasarmu kujerunmu ba abin damuwa ba ne, ku kwantar da hankalinku, ku maida hankali a kan karatunku, ku kawo min sakamakon da zan yi farin ciki irin na Yayanku, shi ne kawai abin da za ku yi min in ji dadi”.
Daddy kenan, ke lallashin samarin `ya’ yansa, wadanda hankalinsu ya tashi da wannan sabon al’ amari da ya tunkaro su. Wayar safe daban, ta dare daban suke bugowa don jin halin da ma-haifinsu ke ciki. Isma’el ya yi ajiyar zuciya cikin karyayyar murya yake magana. “Daddy ba barin Europe da za mu yi ba ne yake damuna ba, don kamar yadda bata dada Ya Azeez da kasa ba haka ni ma bata dada ni ba. Ina zaune ne don ta zama muhallin iyayena, amma nafi son zama a Nigeria. Ko yau ka ce in bar Harvard in taho mu taho gida tare zan barta in taho. Damuwa ta Daddy in ka koma gida me za ka yi? Shekarunka ba su kai a ce ka yi ritaya ba, me za ka yi Daddy ka ci gaba da daukar nauyinmu?” Murmushi Prof. Dr. Hamza ya yi, don yanzun mun cire masa lakanin Ambassador , jiya ba yau ba! Shi ya sa aka ce dan Adam taka a sannu, kada ka bari mulkin duniya ya rude ka, domin komai na duniya mai karewa ne. Mai tunani kadai ke yarda da wannan a lokacin da yake kan ganiyar
mulki ko mukami ko kololuwar jin dadin rayuwa. “Classroom zan koma mana Isma’el? A karkade ‘duster’ a dauki alli (marker) a koma yadda ake a baya, (duniya rawar `yammata, wai na gaba ya koma baya.) President Na-Dabo ya dade da rasuwa (wanda Daddy yayiwa Parmanent Secretary kuma abokin mahaifinsa na kuruciya wanda ya bashi Ambassadorship). Classroom din shi ne tushen duk wani mataki da na taka a rayuwa ta, ya ya you zan guje shi don na yi aikin jakadanci na lokaci mai tsawo? Ku kwantar da hankalinku, ku yi addu’ a Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi a gare mu bakidaya”.
Da wadannan kalaman ya samu ya taushi dukkan `ya’ yan nasa, ita kam Suhaana kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha don dadi. Allah ya gani ba son kasar Belgium din nan ta ke ba, tana zaune ne sabida iyayenta, in ta barsu ina zata? Har gobe bata manta Jeddah ba da memories din cikinta. Tafi son kasar Saudiyyah fiyeda kowacce kasa a duniya. Tana kuma son Nigeria. Tunda suke zuwa Nigeria ta ke matukar son garin Kano yana matukar burge ta saboda cikowar jama’ arsa da hada-hadar kasuwancinsa, wuraren tarihi da hawan (Durbar) na duk shekara. Tana son Adda Hafsatu da Baffa Atiku, tana son girkin Addar mai miyar taushe da miyar kuka, kubewa da kalkashi wanda in ba zuwa suka yi Mammah ta yi guzurinsu ba ba sa samu. Da a ce za ta iya barin Mammah da ta roke ta in sun koma Najeriya a barta a Kano, ba ta son Abuja. Sau daya taje gi-dansu na Asokoro suka sauka suka kwana bakwai bata ji dadin garin ba ko kadan. To ba za ta iya barin Mammah ba ko na sati guda, sai dai in tare Www.bankinhausanovels.com.ng za su zauna Daddy ya sai musu gida ko su zauna a Dakata dakin marigayiya Inna, tunda babu kowa. “Ina ruwan Hafsatu?” In ji Baba Azumi a lokacin da ta ke gaya mata abin da ke ranta game da Kano da Abuja. Baba Azumi ta ce, “To shi kuma Daddy fa? A hannun wa ku ka barshi a Abuja in anyi yadda kike tunani din?” Hafsat ta ce, “Sai ya dinga zuwa mana week-end”. Baba Azumi ta ce, “Wa zai dinga ba shi abinci to? Sai dai in kin yarda ya kara auren wata matar bayan Mamanki”. Hafsat ta girgiza kai da karfi, “In haka ne gara in yarda mu zauna a Abuja tare”. Baba Azumi ta kyalkyale da dariya, ta ce, “Na lura Hansai kishi za ki yi”. Hafsat ta ce, “Mene ne kishi?” “Dadina da ke Hausa ba ta ishe ki ba, kishi shi ne ka ji ba ka son hada abin da ka ke so da wani, ku amfana dashi tare, kin gane?” “Na gane, to dama wa zai so ya yi sharing abinda yake so? Ai abin da ka ke so ba ka son shi da kishiya”. Mammah na kicin tana jinsu tana murmushi. Baba Azumi ta dafe haba, “Ke nan ba za ki auri mai mata ba ko ke a karo miki Hafsatu? Ni kin ga kishiyoyi uku na zauna da su a aurena na fari. Ra-nar da mijinki zai kara aure ki ce sai mun zo da katafila danne kirji?”
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG