RUBUTACCIYA BOOK 4 CHAPTER 7 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
Sultan ya dake, ya shafi kumatunta ya matso da ita jikinsa sosai, “Ke rubutacciya ce. Ina fatan shikenan kin fahimci ke wacece ko? Oya tashi mu je mu kwanta ko kuma in zane dan bakin nan da bulala.”Nasreen ta yi murmushi tace, “Lahh ai ba a zane baki Deena.”
A kunne ya rada mata wata magana ta sunkuyar da kai kunyarsa ta kama ta, ta ruga da gudu tana WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG KyalKyaltar dariya. Sultan ya saki ajiyar zuciya da Karfi ya mayar da kai ya jinginar a jikin bangon yana nazarin ta hanyar da ya kamata ya biyo wa Nasreen. A ganinsa lokacin boye-boye ya wuce, yana ganin fada mata gaskiyar za tafi, domin lokacin da zai sada ta da danginta ya yi. Yana tunanin lokacin da zai mayar da hankalinsa akan matsalolin Nasreen ya yi. Ko babu komai a yanzu ya riga ya gama da matsalar idanunta, tana iya ganin kowa. Yana nan zaune bai tashi ba, ya ji hannaye masu taushi suka rufe masa idanu, sannan aka sumbace shi a goshi, “Nasreen
kin Kware a wasa ko? Idan na kama ki ba zan
ZAMU TASHI
yi maki da kyau ba.” Dai-dai saitin kunnensa ta yi masa magana, wanda ya haddasawa tsigan jikinsa tashi, “Idan ka kama ni zaka yi min da kyau, hasalima tarairayata zaka dinga yi kana tattalina, bana tunanin zaka iya barin dai-dai da kuda ya taba ni. Kayi min duk yadda kake so Dee.” Hannunsa ya sa ya jawota ta zauna a jikinsa. “Nasreen komai naki mai kyau ne, naso a ce kowa yana ganin muninki ni daya nake da ikon • ganin kyawun matata har intasata a gaba in yi ta kallonta kamar zanen hoto a gabana. Mu je ciki sanyi nake ji sosai.” Suna shiga ciki wasan ya fara sauyawa, don haka na tattara `yan takarduna na koma dakin su Jidda, su kansu abin ba a cewa komai, na juya
wurin Naufal da ya nausa cikin dogon tunani. Tambayoyi ne cike da cikinsa, amma Sultan yaqi bashi fuskar da zai aiwatar da wannan tambayar Www.bankinhausanovels.com.ng Kansa yana sake daurewa ganin dangin Abba ne kawai suka damu da su. Ya sha alwashin suna dawowa zai bi diddigin gaskiyar lamari.
Cikin ikon Allah suka dawo kasarmu Najeriya, basu yi yungurin dawowa Abuja ba, sai da suka kwana a Lagos sannan suka dawo cike da gajiya. Zakiyya suka samu a falon tana shan kida abinta. Sultan ya zauna yana rike kansa. Nasreen kuwa kafe Zakiyya tayi da idanunta tana mamakin yadda take. Duk a zatonta wata kyakkyawa ce ta nunawa duniya ce, bata taba ganinta ba, ko can tana da idanunta. Kallo daya ta yi mata ta ji ko alama bata sonta, don haka ta kawar da kanta ta zauna tana lumshe dare-daran idanunta. Zakiyya ta dago suka hada ido a karo na farko gaban Zakiyya ya fadi Bata taba sanin haka idanun Nasreen suke da kyau da daukar hankali ba, da babu abinda zai sa ta bari a bude su. Www.bankinhausanovels.com.ng Kowannen su da abinda ke zuciyarsa, ta so ta yi magana ganin Jidda a wurin ya sa ta yi shiru, dan tana tsoron Jidda. Jidda ta dubi Nasreen ta ce, “Tashi mu shiga kitchen mu samar masu abinda za su ci, kinsan Abban Muhsin baya cin abincin masu aiki.”
Babu musu suka mike. Sultan ya bi bayan matarsa da kallo, yana ayyanawa kansa abubuwa. Zakiyya ta sake cika ta yi fam. Ya dubeta yace “Ke baki iya sannu da zuwa bane?” Ta turo baki tana magana ciki-ciki, “Ba a koya min ba.Ya zaro ido kamar yaji me take cewa, yace, “Me kika ce?” Ta dan Kara murya tace, “Sannun ku da zuwa. Al-ameen ya kauda kansa ba tare da ya tanka ba, haka ya yi kamar bai san suna yi ba, daga Karshe yasa waya a kunne ya fice.
Sultan yana kula da Al-ameen idan yana waya ko da Ashmaan ko Mahbub, baya son yi a gabansa, idan kuwa aka Kira suna tare ya dosa kame-kame kenan’ har su fahimci yana tare da Sultan su kashe wayar. Abin yana damun Sultan gani yake ko sun cire shi a cikin abokai ne? Ya rasa gane irin wannan abin. Haka yayi wa kansa alKawarin ba zai komai ba tukun, sai yaga iya gudun ruwansu. Www.bankinhausanovels.com.ng Zakiyya ta dawo kusa da shi ta manne masa, bai ce komai ba ya kauda hancinsa yana duban gefe. Ta kama hannunsa ta mayar bayanta tana magana, “Ba ka damu da ni ba ko?” Ya dan dube ta ya ce, “Namiji yana ajiye matar da bai damu da ita ba ne?” A lokacin Nasreen ta shigo falon daukarwa Jidda wayarta. Ganinsa yasa ta gigice, ta rasa hanyar da za ta bi ta koma. lokacin ya dago kai suka yi ido hudu, jikinsa ya yi sanyi ya kuma karanci damuwa a kwayar idanunta. Juyawa ta yi kawai ta koma kitchen din. Yadda ta yi shiru yasa Jidda wanke hannunta ta karaso kusa da ita, “Menene kuma Nasreen?” Ta dago idanunta cike da hawaye ta ce, “Jidda me yasa maza basa da kunya ne? Yanzu namiji zai gaya maki duk duniya ke kadai yake so, da za ki leka dayan dakin za ki sha mamakin irin kalaman da zai yi mata. Ni duk soyayyar da zai yi da matarsa ban hana shi ba, amma kada ya yi a gabana. Baki gansu a falo ba, Wallahi zuciyata ta sosu. Www.bankinhausanovels.com.ng Dama in zauna da makanta ta, da na fi samun sauki tunda ban gani ba. Jidda ta ce. “Subhanafillahi. Haba Nasreen, ke fa malama ce bai kamata kishi yasa ki mance matsayinki na Musulma ba. Kuma idan kika ce gara kina makanta kamar baki gode wa Allah ba kenan. Kin ganni nan? Har Anti Bintu ta bar gidan duniya ban san wani kishinta ba, ni lokacin yaushe rashin hankalina ma ya bami nasan kaina bare wani kishi? Na ji dadi a raina da Allah ya haneni da inn wannan kishin, gashi mun rabu lafiya. Kada ki soma ki ce za ki sa damuwar wata a ranki bare ki kasa samun natsuwar zaman aure. Kuma su maza haka sake, ko ina suka je za su gayawa matansu suna son su, amma ke kinsan wacece yake so. Ba sai an tambaya ba, kina kallon kwayar idanunsa kinsan Nasreen dinsa ce kadai a cikin zuciyarsa ba wata banza wai ita Zakiyya ba.” Nasreen ta dan sami natsuwa, amma kuma yanayin da ta Gansu ya ki goge mata a zuciya, tana jin zafinsa da gaske, da bata iya boye irin wannan abin a gaban ko waye. Tana jin Www.bankinhausanovels.com.ng ba za ta iya zama a falon ba, ba za ta iya ci gaba da kallon Zakiyya a jikin mijinta ba. Haka suka karasa aikin jikinta a sanyaye. Shi kuwa tashi ya yi ya shiga ciki ya watsa ruwa sannan ya sauya kaya zuwa kanana. Yana fitowa falon ya sami Al-ameen ya dawo suka ci gaba da maganarsu. A lokacin su Jidda suka shigo da abinci. Kowa ya zauna suna ci ana hira amma Nasreen ta kasa ci sai danna cokalin take a cikin abinci amma ta kasa ci. Duk suna kula da ita, Naufal da shigowarsa kenan ya dube ta cike da kulawa ya ce, “Menene Nasreen?” Sultan ya dago habarta, yana murmushi. “Ashe haka Babyna take da kishi?” Nasreen ta yi iya bakin kokarinta don ta danne abin ya faskara, sai hawaye. Ya jawo ta gaba daya jikinsa yana bubbuga bayanta, “Ki yi hakuri kin ji? Na tuba ba zan sake ba. Ci abincin mu gama muje yawo abin mu.” Tayi shiru tana goge hawayenta, sannan ta janye jikinta tana cin abincin. Jidda ta dubi mijinta suka yi murmushi. Www.bankinhausanovels.com.ng Bayan sun kintsa ne suka fito zuwa gida FAtima Doctor Yummah, Nasreen ta dubi Yumnah cike da farin cikin ganinta a fuska. Suka rungume juna Nasreen ta ce, “Masha Allah. Jaruman ‘Yar Borno dukkansu Masha Allah. Na ji dadin ganinki fiye da tunanin mutum Yumnah ta yi dariya ta ce, “Na ji dadin samun lafiyar idanunki.allah kara tsarewa.” Suka saki juna, suka shige suka bar mazajen a falo. A nan suka sake zama suna hira. Jidda ta zage Yumnah tsaf akan yadda take boye mata abubuwa akan kayan kamshi Yumnah ta mike ta ce bari inbaku wani abu ku ji. Ta dauko wani humra ta dan fesa masu duk suka shaki kamshin suna dubanta, “Wannan kuma fa Yumnah? A ina kika samu?” Yumnah ta miko masu Humran ta ce ku karanta da kanku. Dukkan su suka kafa kai, “HUMRA. Uwargida kafarki kafata. Tana sanya kamshin fata ta zauna a jikinki, tana kuma kara jawo hankalin mai gida ya kasa barin kusa da ke.”
Dubanta suka yi idanu a waje. Ta yi dariya ta zauna tana dubansu, “Wannan humrar daban ne, yadda kika san da Suratul Yusuf aka hada shi. Duk yadda zan gaga maki haduwarsa ya wuce nan, sai kin kwatanta.” Jidda ta sake matsowa ta ce, “Yumma Aminu ina zan sami Humran nan? Kuma haka sake a gore?” Ta gyada kai, “A shagon Jafar dinnan zaki samu, Bashi da tsada. Boye boyeta yake yi baya siyarwa kowa sai idan kinsan sirrinsa ka tambaye shi, shi ne yake daukowa. Kina zuwa shagon ki ce masa Uwargida (kafata Rafarki kike nema wato Humra. Ni saboda zalama, kwalin na siya gaba daya. guda Boma she biyu ne a ciki. Bari in baku dai-dai ku kwatanta za ku ba ni labari.” Jidda ta ce, “Kin san Allah:? Tunda ta Zaria zamu bi sai Uncle ya kaini her shagon nayi siyhyyana. Harda sabulan gyaran fata duk zan siya a wurinsa. Bani lambarsa don Allah.” Yumnah tana dariya ta ayyano lambar, 07038882560. Suka ci gaba da hirar su. Su Jidda dai sun koma gidan su, don haka gidan yayi shiru Jidda ta gyara bangarenta Www.bankinhausanovels.com.ng sai tashin karnshi yake yi, ta shiga baYi ta wanke jikinta da sabulan shagon Jafar, ita kanta ta gamsu da irin kamshin da ke fita a jikinta, ta shafe jikinta da humra mai sanyi wanda Yummah ta bata. Ta haye gado ta yi kwanciyarta. Shi kam tunda ya fita har aka kira Magriba bai dawo ba. Saida ta idar da Sallar isha’i ta sake tsala jwalika, ta shafe Humran ta gyara gashinta yana ta tashin kamshi, sannan ta koma ta kwanta. Sultan yana shigowa gidan ya shigo hannunsa dauke da kaji da abubuwan sha kala-kala ya shiga dakin Zakiyya ya mika mata ledanta zai fito tasha gabansa, “Kamata ya yi yau ka kwana a wurina, tunda dai kunje London. tare.” Dubanta yayi da wani irin duba sannan ya fice abinsa. Dakin Nasreen ya wuce hakan yasa Zakiyya bin baYansa ba tare da ya sani ba. Labe ta yi tana hangensu ta cikin makulli. Kan gadon ya bita ya mata sumba, sun jima a irin yanayin nan sannan ta zare kanta, ta rintse idanunta ta fara magana cikin wani yanayi, “Bai kama ta kana wahalar da karamar kwakwalwa kamar tawa ba. ina jin ka Www.bankinhausanovels.com.ng ba zan iya amsar wadannan bayanan naka ba sun yi min girma.” Dubanta ya yi idanunsa sun sauya, ya dubi kafafunta farare tas masu kyau da su, ya kai bakinsa ya yi kissing kafafun, ta yi saurin janyewa tana fadin, “Babu kyau fa,” Murmushi ya sakar mata, ya mika mata hannu ta rike suka sauko. A baki ya dinga bata naman tana ci ta • ture hannunsa tana kaiwa bakinsa, wai dole sai shima yaci. Haka suka
Gama yaje ya wanko hannunsa ya sake yin brush ya daga ta cak sai bandaki ya wanke mata baki suka dawo kan gado. A hankali ya rada mata, “Baby wani kamshi nakejia jikin ki maisa kasala a ina kika samu. Yummah ko?” Yana maganar tare da zuge mata
zif din rigar wanda gabansa dogon zif ne. Hannunsa ta rike tan girgiza kai. Wutar dakin ya kashe gaba daya. Zakiyya ta nemi ta kurma ihu, cikin ikon Allah ta toshe bakinta. Mamaki ya kashe ta, dama haka Sultan ya iya soyayya yake kin yi mata Ta gigice iya gigicewa kamar za ta yi hauka haka take ji. Ta ci alwashin bai isa ya aikata wani abu da Nasreen a wannan daren ba, don haka ta
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG