AUREN KWANGILA BOOK 2 CHAPTER 10 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

AUREN KWANGILA BOOK 2 CHAPTER 10 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

                   Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA 

Sai ga Baba Azumi ta bullo daga corridor din kicin tana dauke da katon din ruwan sha mai sanyi na FARO. Da Hafsat ta fara tozali fuskarta ta washe, bakinta ya fadada, ta rasa dalilin wannan gashin kuma na Hajiya Maryam, wai ba za su je wajen Hafsat ba sai ta shekara a gidan miji, ga shi ai su sun kasa jurewa sun zabi mai fishshe su. Tunda sun zo ai ba za ta kore su ba. Oyoyo da ‘yar Baba, oyoyo da ‘yar Mammah, lale da amarya mai abin mamaki”.
Turbunewa Hafsat ta yi tana cuno baki, “Da na zo da kaina Baba Azumi? Wai kema har da ke Baba, ba kya nemana… kin manta da ni…”Ina kaka za ta manta da babbar jikanyarta? Wane mutum!!!”
Gabadaya aka yi dariya, sabida irin yadda ta jinjina girman al’amarin. Hafsat ta karasa gare ta ta rungume ta. I missed you so much Baba…”
Baba Azumi na jin turanci sama-sama ta ji abin da Hafsat ta ce. “Kin yi fari, kin yi kiba, Babban Yaya ya iya kiwo. Mu ma mun yi kewarki ‘yar Mammah, kullum ma muna yi (kewar)”. Ta fada tana bubbuga bayanta. Da kyar Baba Azumi ta samu Adda ta sake ta.

ZAMU TASHI 

Hafsat na ji Mammah na tambayar Abdul’ azeez ko ciwon Hafsat ya taba tashi?” Dago kai ya yi ya dubi mahaifiyarsa cikin mamaki, “dama tana da wani ciwo ne?”

“Mantawa ka yi tun haihuwarta tana da pneumonia ? Habiba na shan ruwan sanyi sosai da yin ta’ammali dashi”

Tsit falon ya yi, kowannensu na tuno Habiban da rayuwarta ta dan gajeren lokaci tare da su, wadda ba za su taba mantawa ba. Hafsat ji ta yi kamar an yi mata shocking a lokutta da dama mantawa ta ke tana da wata uwar_ bayan Mammah, tunda ita dai ba ta santa ba ko a hoto. Ga shi Mammah ba ta so a yi zancen. Yau tunda ita ta tado shi ba wani ya sa ta ba, sai ta gaya mata cikakken asalinta.

Www.bankinhausanovels.com.ng

Shesshekar kukanta kawai aka ji ya ratsa shirun da aka yi, “Don Allah don Annabi Mommah ki gaya min wace ce ni a cikinku? Na san ba ki yi min haihuwa ta jini ba da ba ki hada aurena da Yaya Abdul’azeez ba. Na dade da sanin wannan, ina da wata uwar daban bayan ke. To amma uba fa? Ko shege ne ta yi ta kawo muku…”

Sunkuyar da kai suka yi bakidayansu, saboda su ma ba su da wannan amsar. Abdul’azeez ne ya katse shirun da shesshekar kukanta ya ce,

“Suhaana, Hafsat -Suhaana”. Har sau biyu.

Ta amsa cikin rishin kuka, “Na’am” “Dago ki dube ni”. Dagowar ta yi ta dube shi, in lissafin da ta ke yi daidai ne shekarunta goma sha takwas jiya, su gaya mata ko ma wane iri ne asalinta za ta iya dauka. Don haka_ with eager ( da zakuwa) ta ke kallon mijin nata, tsakiyar iyaye da ‘yan
uwansa idanunta cike da hawaye.

“Ba shegenki ta yi ba, ni ta gaya min kina da uba kamar kowa da ‘yan uwa na ciki daya har ukku, kuma ba ta yi kama da mutuniyar banza ba. Mace ce mai cikar mutunci, mai kirkin gaske. Da yardar Allah sai na nemo mahaifinki da ‘yan uwanki Hafsat na sadar da ke gare su. Ki ba ni wata uku, I promised”.

Daga kai ta yi cikin amincewa, “ Wipe-off the tears… (goge hawayen)’. Ya _ fada_ cikin kankanuwar murya.

Kunya ya bata sosai, tasa gyalen abayarta ta rufe fuskar bakidaya. Dariya kowa yake mata, zuciyar Hajiya Maryam kamar koramar madara da zuma don dadi na kulawar da Abdul’azeez ya nuna akan Hafsat a gaban kowa. Ita dai haka ta ke so, Abdul’azeez ya so Suhaanah da zuciya daya, in ya yi hakan ya gama mata komai, kuma albarkarta gare shi ba za ta taba yankewa ba. Www.bankinhausanovels.com.ng

A yau Hafsat-Suhaana ta san ko wace ce ita a cikin iyalin gidannan, daga bakin uwarta/surukarta Maryam Dakata. Labarin da ya tsaya mata a zuciya ya kasa wucewa; ‘yar mai aikinta ce ita! Babu wata alakar jini ko ta yaya! Her mum is her servant, her maid. Ba ta san daga inda ta ke ba, amma ta raine ta, raino irin na fisabilillahi, wanda dan cikinka kawai za ka iya yi mawa, duk hakan bai isa ba, Abdul’ azeez ta zaba mata a matsayin miji. Dan gatan da bai rasa komai ba, mai asali da ilimi. Mutane irinta nawa ne a cikin al’umma???

Yanzu ta gano dalilin da ya sa Abdul’azeez ya kasa sonta! Allah sarki!! Ai ya yi kokari ma,

kokarin da maza irinsa da yawa ba za su iya ba. A yau ta karbi uzurinsa da hannu bibbiyu, na son rabuwa da ita a gaba, za ta taimaka masa ya cika burin rayuwarsa ya yi auren da maza masu gata irinsa ke yi, wanda hankalinsa zai kwanta da shi. Ba don Mammah ce ta haife shi ba, da ta ce ta zalunce shi da ta hada shi aure da ita don kawai tana sonta. Wannan bai isa hujja ba a ganinta. Ta gyara mata rayuwa shi ta gurgunta tashi, ta hanyar aura masa yarinya irinta mara galihu mara asali mai kaskantaccen matsayi a gidansu. Amma faruwar wannan al’amarin a yau da abin da Abdul’ azeez ya yi mata na karamci a gaban tyaye da ‘yan uwansa sai ya kawo wani SABON AL’AMARI mai girma a zuciyarta a kansa. Wani bakon feeling da ba ta san daga ina yake fitowa ba tsakanin zuciya, ruhi da gangar jikinta. Ya dasa wata katotuwar bishiya cikin zuciyarta mai yawan ganyayyaki, sai yabanya (yado) suke a rassan jikinta. Babu wani bangare na wadannan halittu guda uku tsakanin zuciya, ruhi da gangar jiki da ba ya ambaton sunansa a wannan lokacin da murya mai tsananin amo da _ amsa kuwwa……. ‘ABDUL’AZEEZ HAMZAH ATTIKOU…..’. cikin sauti ma’abocin amo da karsashi. Jinsa ta ke yi a ko’ina na sassan jikinta da wannan ‘sabon al’amari’ mai ban mamaki da ba ta taba tsintar kanta a ciki ba. Www.bankinhausanovels.com.ng

Kowa ya dubi Hafsat ya san ta zama ‘cool’ a kan yadda ta zo a farko. Da fara’a da faramfaram, da dokin kowa nata.

Sai babu wanda ya bai wa canzawarta hankalinsa. Hatta Mammah kuwa, sun alakanta

hakan da sabon labarin rayuwarta da ta ji. Ab

dul’azeez ne kawai ya lura da canzawarta mai harshen damo ce (mai ma’ana biyu), kasancewarsa wanda yake kwana ya tashi gida daya da ita a halin yanzu, kuma a irin shakuwar da suka yi a wannan lokacin zai iya cewa ko Mammah ba za ta gaya masa wace ce Hafsat ba, sai dai ta gaya masa (little Hafsat) amma ba baligar ba.

Hafsat-Suhaana mai sanyin hali ce, ba ta da daukar duniya da fadi, mai kirki ce, mai girmama na gaba da ita. Mai gudun zuciya da karbar rayuwa a duk yadda ta zo mata ba tare da ta yi jayayya da ita ba. Yanayinta ba ya iya boye abin da ke zuciyarta. Wadannan sune manyan halayenta da ya fahimta a tsayin zamansa tareda ita.

Sosai ya fahimci hayaniyar gidan ta daina burge ta, tana bukatar privacy na yin nazarin sabon labarin da ta ji da kuma yadda zuciyarta za ta karbe shi, ta saba da shi, tana bukatar kadaicewa ta yi jinyar zuciyarta.

Mammah dai duk abin da ta san Hafsat na so shi ta ke kokarin yi mata yau. Ta kawo wannan ta kawo wancan. Duk don ta kawar mata da damuwar. Baba Azumi na can kitchen tana yi mata awara kwano guda da za ta sanya a firji ta dinga soyawa in ta ji marmari kasancewar tana sonta. Ishma ya yi mata tsaraba sosai na (English wears) da takalma da jaka leda guda. Ta idar da sallar magriba a dakin Mammah, ta ci gaba da zama shiru a kan sallayar ita ba lazimi ba ita ba addu’a ba; deep in thought.

Abdul’azeez ya shigo dakin ya isa har inda ta ke zaune ya tsaya a kanta, Mammah na gefe tana shirya mata kayan girki da ta siya mata a Bacco.

Bai ma lura Mammah tana gefe ba yake magana.

“Hafsat, mu tafi gida ko?’”’. Www.bankinhausanovels.com.ng

Dagowa ta yi ta dube shi da kwayan idanunta da suka kankance. Wani irin kallo ta ke masa a yau with utmost respect da ita kanta ba ta san irinsa ba. Samun kanta kawai ta yi da daga masa kai. Ita ma za ta fi son hakan, kadaicin kawai ta ke so. Ta yi jinyar sabon al’amarin nan da ke faruwa da zuciyarta.

Harararsa Mammah ta yi, amma fuskarta annuri ta ke fitarwa.

“To Alhaji, ai ka bari ku ci abinci ko? We’re having a get-to-gether dinner today in honour of Hafsat’s eighteenth birthday. Za’a yi hotuna da vedio, a aje don tarihi’”’.

“Za mu dawo”. Ya fada tare da kama hannun Hafsat ya mikar da ita tsaye, ita kuma ta kwace cikin jin kunya.

“She’s not in the mood Mammah, za mu dawo in an kwana biyu”.

Daure fuska Hajiya Maryam ta yi, ganin yadda yasa Hafsat ke jin kunya kamar ta shige cikin kasa da rike hannunta da ya yi din a gabanta.

“Na fi ka sanin she’s not in the mood din ai, a haka nake so a yi hotunan da vedion. Na so in yi mata ne tun jiya ranar da ta cika shekara sha takwas Allah bai yi ba. Ko hawaye ta ke a haka za a yi, ka je ka sauko da Daddy”.

Murmushi ya yi ya saki hannun Hafsat ya juya ya fita, sosai Mammah ta ba shi dariya, wai ya je ya sauko da Daddy sai ka ce wani dan karamin yaro? Kawai tana neman hanyar da zata kore shi

ya bar musu dakin ne. Www.bankinhausanovels.com.ng
Tare suka ci abinci gabadaya a makeken ‘family dining’ din gidan, uwar da uban da ‘ya’yan su biyar, su Farhan sun jima da tafiya. Abdul’ azeez kusa da Hafsat, Isma’eel ne ya dauko digital camera dinsa ya dinga daukar hotuna da vedio. Duk abin da wannan ‘family’ suka san zai faranta wa Hafsat yau shi suke mata har Daddy. Ko ita butulu ce dole ta manta komai ta saki jikinta ta koma cikin walwala.

Hotuna sun yi kyau sosai, Isma’el ya ce zai wanko ya kawo musu gida. Sannan zai tura ma Hafsat ta waya. Mammah ta gama hada mata komai suka rako su har bakin mota suka shiga suka nufo gida.

Ba wanda ya yi magana a tsakaninsu har suka shigo gida. Kowa ya nemi dakinsa, wanka ta yi don ta ji dadin jikinta tayi brush yadda ta saba duk dare sannan ta fito ta sanya kayan barci. Ta shafa turaren ( Rihanna Rogue ) don ita bata da tsayayyen turare, duk wanda yayi mata dadi fesawa takeyi. Mamanta ta cika mata kan mudubi da su na lefenta, data gama ta bi lafiyar gado.

Ya jawo (files) din da ya dawo dasu daga office

bayan ya fito daga wanka, ya daura wasu tausasan pajamas ruwan makuba na ( Neiman Marcus ) ya yi amfani da turarukan da yake amfani da su da daddare ( before midnight da midnight oud), wai zai yi aiki don kore wa kansa tension din da yake ciki, amma abin mamaki ba ya fahimtar komai a cikin takardun, dole ya mayar ya rufe saboda Hafsat kawai yake gani tana gilmawa a cikinsu, da yanayin da ta ke ciki a yau. Www.bankinhausanovels.com.ng

Tana bukatar mai kaunarta a kusa da ita, kada kadaicin rayuwar ya yi mata yawa. To amma ya

yi wa kansa alkawarin ba shi ba sake shiga turakarta tun lokaci n da ya tsallake rijiya da baya. M e zai tya yi (as a brother) ya nuna mata yana tare da ita cikin kowanne hali da ta samu kanta a ciki?

“Be with her today, the whole night ”. (Ka kasance tare da ita yau, a tsayin daren bakidayansa).

Kaso tamanin na zuciyarsa ya amince da hakan, kaso ashirin yana kalubalanta. Ba don komai ba sai don gudun abin da hakan zai haifar, sai dai yana da tabbacin ya yarda da kansa ba zai iya cutar da Hafsat ba, rayuwarta bakidaya amana ce yanzu a hannunsa. Faruwar wani abu da ya danganci auratayya a tsakaninsu ko ya ya yake don kankanta; zalunci ne da cutarwa a gare ta.

Yana da yakinin zai rike amanar Hafsat kamar yadda zai rike Haleem, ko da shi zai cutu, albarkacin mahaifiyarsa da halayen kwarai na yarinyar, wadanda suka ba ta matsayi na musamman a zuciyarsa.

Wayarsa ya mika hannu ya dauko, sai kuma ga kiran Mu’azatu ya shigo. Ga mamakinsa sai bai ji dadin kiran da ta yi masa a wannan lokacin ba. Bayan kuma ba wannan ne karo na farko data kira shi a irin lokacin ba. Ko bai fada ba muryarsa ta nuna hakan a sanda ya amsa wayar.

“Mu’azatu ya aka yi?” Www.bankinhausanovels.com.ng

Ta yi dan jim, don ba haka ya saba amsa mata waya ba, muryarsa a dusashe. Ba abinda ba ta kissima a zuciyarta ba da cewa shi ke faruwa, wato tare yake da matar da yake cewa ba ya so ta shiga lokacin su. Ta yi magana a kai cibi ya zama

kari. Makoshinta da lebban bakinta suka bushe rayas, ta kasa ce masa komai saboda wani bakin ciki da wutar kishi da ya zo ya tokare ta, sai ji ya yi ta kashe wayarta.

Ya duba sosai ya tabbatar kashewa ta yi, sal yake tambayar kansa laifin da ya yi mata? Iyaka hangensa bai gani ba don haka ya rabu da ita, ya kira Hafsat.

Kwance ta ke kawai tsakiyar ni’imtaccen gadonta, barci ya ki zuwa, ta rufe rabin jikinta da duvet da wayarta a hannunta tana duba hotunan da Isma’el ya turo mata da suka dauka dazu, ta tsayar a kan wanda ya dauke su ita da Abdul’azeez ya rankwafo ta bayanta kanshi bisa kafadarta ta dama kamar tare aka halicce su. Duk sun yi murmushi. Zooming hoton ta sake yi tana hango abubuwa da dama. In dai ba yaudararta zuciyarta ke yi ba, to kuwa tana gaya mata kyawawan fuskokinsu sunyi kyau sun dace da juna. Ya fi ta tsayi, ya fi ta fadi (physique chest) gare shi. Komai na halittarsa abin mace ta tsaya ta kare wa kallo ne. Ko shi ya sa Mu’azatu ta kasa hakura da shi ta bar mata, duk da ya aure ta? Ta ke jira ayo waje da ita domin ita ta shigo? Ko ita mene ne aibunta da Abdul’azeez ya kasa sonta?

Tambayoyin da zuciyarta ke mata da abubuwan da ta ke darsa mata a yau sun fara ba ta tsoro saboda ba ta ga dalilinsu ba. Tunda bai boye ba ya fada mata ita ba matar aurensa ba ce, matar wucin gadi ce, ta samu kanta da tambayar zuciyarta; mene ne bambancin matar aure da matar wucingadi? Ina ma tana da karfin zuciyar da za ta iya yi
masa wannan tambayar??? Www.bankinhausanovels.com.ng

Daidai wannan lokacin kiransa ya shigo cikin wayar da sunan da ta yi saving dinsa wanda sai a yanzu ta ke kalubalantar kanta kan dalilin ajiye lambarsa da wannan sunan Hussy wato “ Husband ”. Amma kuma ta kasa gogewa. Ai shi ma ya fada; “Aure kowanne iri ne sunansa aure, yana da martaba da mutuncinsa’”. Aurenku ma aure ne tunda ana tare ba a rabu ba, thus, he’s indeed your husband wanda kowa ya shaida, ku kadai kuka san kun bashi wa’ adi.

Amma wadanda suka daura shi da kyakkyawar niyya suka daura da sadaki da waliyyyai da shaidu yadda addinin muslunci yayi umarni kamar kowanne auren sunnah. Amma ga mamakinta ta kasa amsa wayar tasa, a kan dalilin da ba za ta ce mene ne shi ba. Ta yi har ta katse, ya sake kira a karo na biyu.

Hafsat ta ce cikin ranta, “Ko sau dari za ka kira ba zan amsa ba Yaya Azeez, me ya kai matar wucin-gadi zuwa turakar maigida a daidai wannan lokacin? Gara in rage shige maka, in tsaya a matsayina kafin zuciya ta ta kumbura a kanka da al’amuranka masu ban mamaki. Na kasa gane inda ka sa gaba, na kasa gane inda ni kaina nake heading a kan al’amarinmu. Yau kadaicin kawai nake bukata. I want to be alone!” .

Ta mike hannu ta yi (light up) daga makunnin da ke jikin gadonta. Fitilu masu sassaucin haske suka maye gurbin masu hasken. Hoton nasu ta ci gaba da kallo, tana ta ci gaba da zooming dinsa, kamar ta zuko Abdul’azeez din daga cikinsa ta mayar jikinta su zama abu guda till eternity saboda wani irin intense feeling dake bakuntarta, zuwa lokacin ya gaji da kiran ta ya kyale ta, don

— °
ya tabbatar bazata amsa ba.

Tana cikin wannan halin ta ji an zura mukulli a jikin kofarta ana budewa. Sosai ta razana, sai dai kuma ta san ba mai yin hakan sai mamallakin gidan. Don haka tsoron nata ya ragu, ta baiwa kofar attention dinta tare da boye wayarta da sauri cikin quilt har ya bude ya shigo. Rufe ido ta yi ita a dole ga wadda ta yi nisa a barci. Ta yi zaton zai koma ne daga bakin kofa kamar yadda ya saba, amma shari’a sabanin hankali.

Kai tsaye gadon ya nufo, ya hawo shi bakidaya ya bude duvet din ya shige ciki ya kwanta a gefenta. Ji ya yi kafarsa ta shuri abu ya sa hannu ya dauko, wayar Hafsat ce, wadda ta suma a kwance sabida kaduwa da mamaki, Abdul’ azeez a kan gadon barcinta?

Ba ta son ta yi motsin da zai fahimci idonta biyu, tunda dai bai rabe ta ba, sai dai kamshin jikinsa ya mamayeta, ya yi amfani da daya filon ne ya kwanta a kusa da ita, don haka ta ci gaba da tamke idonta a cewa bacci take yi. Sai dai zuciyarta harbawa ta ke yi kamar ta faso allon kirjinta ta fito saboda gigicewa. Ba ta sani ba wayarta na hannunsa, kuma tana nan a yadda ta boye ta. Www.bankinhausanovels.com.ng

Kyakkyawar fuskarsa ce a hoton ta cika screen din da alamar zooming ake ta yi. Da ya matse shi sai ya ga ashe ma ita da shi ne wanda Isma’el ya dauke su dazu, amma ba kanta ta ke kallo ba, shi kawai ta ke kallo. Sosai mamaki da al’ajabi suka taru suka lullube shi, ya kuma tabbatar idonta biyu ba barci ta ke yi ba, abin da ta ke yi kenan kafin ya shigo. Ba ya so ya yarda da abin da zuciyarsa ke gaya masa, don haka shi ma ya boye wayar a kasan filo a zuwan bai gani ba, yana mai

karyata zargin da zuciyarsa ke nanatawa.

‘“Mene ne a cikin kallon hoto? Babu komai. Kawai tana gani ne ba da wata manufa ba. She’s very young… hakan ba zai kasance da ita ba at this tender age..” . In ji wani bangare na zuciyarsa.

Sai kuma wani irin tausayi da bai san dalilinsa ba ya tsirga masa. Duk yadda yake gudun yin zalunci a cikin tafiyar nan anya zai tsira daga aikatashin?

Hafsat ba mutum ba ce? Ko kuwa babu zuciya a cikin kirjinta? Ko kuwa halittar ta daban ce da ta sauran ‘ya’ya mata? In babu so babu sha’awa? Idan ya katange kansa daga soyayyar kowacce diya mace bayan Mu’ azatu zai iya katange Hafsat daga hakan a kansa a matsayinsa na mijin aurenta da ba ta da wani makusanci da ya wuce shi a yanzu? Su kwana gida daya su wayi gari tare su wuni gida daya? Abin da ya faru dazu tsakaninta da saurayi ya fado masa. Wani irin yanayi ya shiga mai wuyar fassarawa fiye da tsammaninsa.

Dakin ya dauki shiru ga zafi ya dameshi kasancewar Hafsat bata amfani da AC, ta saba da rayuwar ta a haka, don tsira da lafiyarta. Ba ka jin komai sai bugun zuciyoyinsu. Saukar numfashin kowannensu ya sauya ya koma akai-akai yake sauka. Hafsat ta rasa a duniyar da ta tsinci kanta a yau kasantuwar Abdul’azeez tare da ita, a gado daya, cikin mayafi daya. Wata irin nutsuwa ta ji na sauka a zuciya da ruhinta. Zuciyarta ta shiga wani irin kai-kawo tsakanin kirjinta da kwakwalwarta. Anya kuwa kadaici ta ke so kamar yadda

ta yi tsammani a farko, ko kadaicewa da Abdul’ azeez?

Idan haka mata ke samun nutsuwa in suna tare da mazansu na halal a makwanci daya, cikin mayafi daya, ashe kuwa babu wadda zata so a sake ta, ashe kuwa babu wadda za ta so wata mace ta rabi mijinta. Ina kuma a ce da ‘baby’ kwance a tsakani yana kicking (in between) a tsakaninsu?

Ba ta san sanda ta yi motsi ba don ta gaji da kwanciya a kan barinta na dama. Tana so ta sauya barin kwanciya ba ta so ya san idonta biyu, kuma ba ta sani ba ko babu space mai yawa a tsakaninsu ta goge shi? Ta takura sosai, ga wannan abin data rasa da sunan dazata kira shi da ke tsakiyar kirjinta yana yawo shi ma ya takura mata…. Abubuwa kawai yake gaya mata kalakala wadanda suka faru, da wadanda za su faru ranar da ta rabu da Abdul’azeez ya _ auri Mu’ azatu…… Www.bankinhausanovels.com.ng

Shin wai ita wace irin shashasha ce da ta yarda ta zauna ya gindaya mata abin da ya ga dama ta hau kai ta zauna don kawai tana so ta yi karatu ta ga danginta? Me ta rasa na dangi? Da me Daddy ya rage ta na mahaifi? Me ta rasa a uwa? Su Isma’eel aren’t enough? Isn’t Baba Azumi a great Grandma? lyalin Abdullahi Dakata bakidaya ba su ishe ta rayuwa ba?

KARATU! Zuciyarta ta ambato. Ko da ace Abdul’ azeez bai kai ta makaranta ba, ba ta da ilimin da zai isheta ta rayu da shi har karshen rayuwarta? Nasa ba zai ishe su ba? Gabadaya kwangilar na nufin……. za ta samu duk wadannan abubuwan, amma shi za ta rasa shi!!!

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *