AUREN KWANGILA BOOK 2 CHAPTER 3 BY SUMAYYAH ABDULKADIR
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
A cikin wannan (African parlour) kofofi ne guda biyu wadanda suka kunshi dakunan barci biyu, daya Www.bankinhausanovels.com.ng nasa, daya na matar gidan. Daddy ya kawo shi ya ga gidan tun sanda ake gininsa don haka ya san kansa. A kowanne dakin barci akwai makewayi, kicin (madafi) yana gab da shiga kofar falon farko, wato ba a cikin falon aka yi shi ba. Akwai ‘yar doguwar baranda a kofar shigowa falon, wadda aka aje fararen tukwanen fulawoyi masu kyawun gani da fararen kujerun roba. Harabar gidan za ta iya cin motoci uku ba tare da kowacce ta gogi ‘yar uwarta ba. Dakin maigadi na jikin gate, dakin mai aiki yana daga bayan ginin falon, wato sai an fito daga ‘main building’ din an zagaya ta baya za a tadda dakin mai aiki. Yadda su ESQ Abdallah suka nemi wuri suka zauna cikin tausasan kujerun falon haka shi ma ya nema ya zauna. Barrister Taufeeq shi ne karshen shigowa yana janye da jakunkunansa yana daga tsaye ya ce, “Dare fa ya yi, ka shigar da kayan Malam ka fito mana da amarya mu saya maka bakinta, mu yi muku addu’a mu koma namu gidajen”.
Harararsa ya yi ya mike ya karbi jakunkunan ya yi ciki. A ransa ya ce, wai su saya min bakinta, to in yi me da shi?
ZAMU TASHI
Tsakanin dakunan biyu zai yi rantsuwa bai san wanne aka bata ba, wato ba zai iya cewa ga nasa ga nata ba.
Tsayawa ya yi yana bin kofofin guda biyu da wani kallo mai kama da harara. Ba wata amarya da ya yi niyyar kai musu, su yi abin da za su yi kawai su tafi. Ya ce ta zo cikin abokansa ma ai sai ta raina shi. Ya yi kundunbala ya murda handle din kofar dama ya tura jakunkunansa. Cikin ikon Allah shi ne nasa, ya jefar da jakunkunan ya fito ya tadda su.
“Yaya ina amarya ka fito kai kadai? Hannu na dukan cinya?” Barrister Taufeeq ya tambaya, sauran kuma suka bi shi da ido kamar sa cinyeshi. “Ta yi barci”.
Ya samu bakinsa da fadin hakan ba tare da ya shirya kalaman akan harshensa ba. Duk suka mike, “To sai mu wuce, randa muka zo idonta biyu mun yi muku Www.bankinhausanovels.com.ng addu’ar, dare ya yi’. Ni na yafe addu’ar taku in ba za ku yi min ni kadai ba”. Ya fada yana daure fuska.
Dariya suka yi, Taufeeq na fadin, Ka fadi gaskiya Malam!”Duk suka mike suka wuce Ahmad na fadin, “Da gaskiyarsa fa, wannan al’adar babu kyau ko kadan. Mai kishin iyalinsa ba zai yarda da ita ba”. Baki ya kama yana kallon Ahmad cikin takaici, Kishi???”
Ya ambata cikin sigar tambaya da nauyin baki.
ESQ Ahmad bai bashi amsa ba, ya daga masa gira ya yi murmushi, ya bashi hannu. Amma Abdul’azeez ya noke ya hana shi nasa. “Ka yi min sharri, sannan ka bani hannu? Wuce ka tafi. Na gode zan rama’Suka yi tafiyarsu kowannensu da irin dariyar da yake yi masa. Da wannan haushin ya dawo ciki. Ya rasa abin da zai yi. Har ga Allah bai yi niyyar shiga inda ta ke a daren nan ba, sai kawai ya shige dakinsa ya rufo, ya dauki (remote) ya kunna na’urar sanyaya daki ya hau shirya kayansa, daga jakunkuna zuwa sif din jikin bango. Sai karfe biyu na dare ya gama, ya yi sallar nafila ya kashe wuta ya kwanta. Wayarshi da ya bari a kunne a gefen kansa ita ta tashe shi da kiran Mu’azatu da assalatun fari. Kansa ya yi masa gingirin sabida bacci da gajiya. Ba zai iya magana ba don haka ya matsar da ita gefe ya koma ya ci gaba da barcinsa. Wannan ya kara daga hankalin Mu’azatu wadda yadda ta ga rana haka ta ga dare, cikin matsanancin tashin hankali. Sai karfe biyar da rabi ‘alarm’ din da ya saita ya tashe shi, ya dauro Www.bankinhausanovels.com.ng alwala ya gabatar da (raka’atainil fajr), sannan ya bada farali. Haka kawai ya ji ya kamata ya tashe ta ta yi sallah in ba ta tashi_ ba, ko ransa na so ko ba ya so, ko don tashi sallahr ta karbu. Dan karamin tsaki ya yi, sannan ya mike daga inda ya yi sallah. Haka kawai an dora masa nauyin mutum yana zaman-zaman sa. Har zuwa lokacin wayarsa na ci gaba da ruri, jinjinawa naci irin na Mu’azatu ya yi, in ya tuno yadda suka yi sai haushinta ya sake kama shi, ya kasa amsa wayar. Da ya ga ba ta da niyyar daina kiran sai ya kashe wayar gabadaya ya mike ya
nufi dakin Hafsat. Kwankwasawa ya yi sau biyu ya saurara babu amsa, ya sake (knocking) har yanzu babu motsinta, sai kawai ya murda kofar ya shiga a sike, ba tare da tunanin komai ba. Tana lullube cikin bargo bakidayanta, zazzabi, masassara da ciwon kai sun taru sun rufe ta tun daren jiya. Allah kadai ya san yadda ta yi ta kawo yanzu.
Gabadaya ta rufu ko don yatsanta babu a waje, sai karkarwa ta ke. Shi kansa bargon da filon da ta ke kai karkarwa suke. Ya lura da hakan, ya dan yamutsa fuska. “Ba ki da lafiya ne?”
Daga cikin bargon ta daga kai, bai san ta yi ba, wai kunu a makota, haushi ya soma kama shi, ba ya son shiga shirginta ko kankani, kuma ba ya son yana magana a kyale shi. To kuma ta dukunkune cikin bargo bai san halin da ta ke ciki ba, tana ta faman karkarwa wanda ke nuna bata da lafiya. What could he do ? He actually don’t know . Yana wannan sake-saken ya jiyo motsin mutum a falo. Da sauri ya juya ya fito. Da farko har ya so ya tsorata don bai yi zaton akwai wani mahaluki a gidan bayan su biyu ba, kawai sai ya ga mace a tsakiyar falo da tsintsiya a hannu. Gari ya dan soma haske wanda ya ratso daga fararen curtains din falon ya haska masa matar sosai. Da mamaki ya ce. Daga ina?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Harira ta zube tana gaishe shi da sakkwatancinta. Da sauri ya amsa, so yake ya ji daga ina ta bullo.
“Sunana Harira, ‘yar Baba Azumi ce”. Ya yi ajiyar zuciya, a take ya ji kamar an yi masa rahama. Ya wuce dakinsa yana mata magana ciki-ciki.
“Ki shiga ki duba ta, nake jin ba ta da lafiya, idan akwai bukatar taimako in zan fito anjima ki sanar da ni’. A cikin ransa in banda godewa Mammah ba abinda yake yi da ta samar da ‘third party’ a tsakaninsa da Hafsat, da ina zai sa ransa? Zuciyarsa ba za ta juri shiga harkarta ba, sannan zai je ko’ina hankalinsa kwance ya dawo sanda yake so ba tare da tunanin ya ajiye wani ba. Kowa ya ci gashin kansa.
Harira ta shiga da sallama, amma Hafsat ta kasa amsawa, ta daure dai ta yi motsi daga cikin bargonta. Harira ta isa gaban gadon ta yaye bargon, sai Hafsat ta kara dunkule jikinta. Karkarwa ta ke sosai, wadda ta bai wa Harira tsoro. Abinda tayi zato ba shi ta gani ba. Tun kayan data zo dasu ne a jikinta har sarka da dan kunne suna nan a muhallin su. Ta hau gadon ta ciccibo ta, ta taimaka mata ta shiga bayi ta yi fitsa ri, ita ta yi mata alwala ta ce ko a zaune ne ta yi sallah sai ta gaya wa maigida su je asibiti, ya ce inda matsalar rashin lafiya a sanar da shi. Ta ba ta katon mayafi ta yafa, ta shimfida mata darduma. Daga zaune ta yi sallar. Harira ta taimaka mata tana daga zaune ta canza kaYan jikinta zuwa doguwar riga yellow da mayafinta ta kamo ta suka fito falo, ta zaunar da ita a (three seater), tana dunkule jikinta cikin karkarwar jiki kanta cikin cinyoyinta.
Tun Harira tana kallon kofar dakinsa da tunanin zai fito, har ta hakura da kallon kofar tasa ta mayar kan baiwar Allah wadda ke cikin wani hali na neman taimako na masassara da zazzabi mai zafi da matsanancin ciwon kai. Ita ba abun ta je ta buga masa kofa ba tunda bai ba ta umarnin hakan ba. Haka ta zauna shiru, ta tallafo Hafsat jikinta.
A daidai lokacin ya murdo kofar dakin nasa ya fito, lokacin gari ya idasa wayewa sosai. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kallo daya ya yi musu ya dauke kansa wayar da ke hannunsa ta fara ruri. Ba ta da lafiya ne?” Ya tambayi Harira. Zazzabi ne ya rufe ta, ina ga gajiyar biki ne”. Ya wuce gaba yana amsa wayarsa, bayan ya ce da ita, “Ku biyo ni mu je asibiti”.
Harira ta kamata, ta taimaka mata suka bi bayansa.
Baya suka shiga duk su biyun. Ya tada motar a ransa yana fadin, “Lallai direba ya samu”. Ya ja dan karamin tsaki. Yarinyar ta faya langwai, she’s not strong anymore kamar lagwanin risho. How could he be the husband of such a fragile and delicate woman? He’s bold and energetic, yana son jarumar mace kamarsa ba dangin ta-kitse-ta-narke ba.
Asibitin da ‘file’ din gidansu yake ya kai ta wato (DIFF Hospital). Nan da nan likitoci suka karbe ta, ashe tana ma da ‘file’ da su bai sani ba. Yadda Mammah ba ta sakaci da lafiyarta tun dawowarsu Abuja ta ke kawo ta ‘check up’ lokaci zuwa lokaci na nimoniyarta. Kulawa ta musamman suka shiga ba ta a daki na musamman. Ya nuna wa Harira inda za ta zauna ya yi tafiyarsa gida, ya manta da su. Wanka ya yi, tare da yin shirin (office) don shi ba wani hutu da ya dauka don bai dauki kansa ango ko sabon aure ba. Yana nan a (single Abdul’azeez) dinsa, he will never answer the name ‘married’ sai ranar da Mu’azatu ta zamo matarsa. A office ya tadda sabon case mai tsauri, don haka ya zama ( occupied ) a yinin ranar bakidaya bai kara tunawa da wata Suhaana ba. Aiki ya dukufa yi ka’in da na’in kamar yadda ya saba a kullum. Sai da Suhaana ta samu barci zazzabin da ciwon kan suka sauka, likitocin suka fito suka Www.bankinhausanovels.com.ng kyale ta. Suka ba wa Harira izinin shiga da umarnin kada ta yi wani kwakkwaran motsin da zai tashe ta, sai ta tashi don kanta. Tun Harira na kallon kofa tana tsammanin shigowar Abdul’azeez har ta gaji ita ma barci ya yi awon gaba da ita a kan kujerar da ta ke zaune a gaban Hafsat. Ba ita ta farka ba sai ana kiran sallar azahar. Ta bude ido ta kalli Hafsat da ke barci ta ga ta tashi itama tana kwance ne kawai lamo a kan filo. Ta ce, “Hafsatu kin tashi?”
Kai ta daga mata. Nurse ta turo kofa ta shigo da keken magunguna, ta dubi Hafsat ta yi mata murmushi, “Kin tashi?” Ita ma kai aka gyada mata.
Ta dubi Harira ta ce, “Ki hada ‘tea’ ki bata mai kauri, sannan in ba ta magungunanta”. Harira ta ware ido tana kallon dakin, babu komai na ci a dakin. Ta rausayar da kai ta ce da Nos din, Don Allah ko za ki taimako da shayin? Maigidan nata bai dawo ba tunda ya kawo mu”. Nos din cikin mamaki ta ce, “Ya zai kawo matarsa ba lafiya ya tafi bai ajiye muku komai ba?” Harira ta yi shiru, don ita ma abin ya ba ta mamaki. Amarya ce fa, amarya guda! Da aka kai masa jiya-jiya? Za ta iya tunawa ko sallama bai yi mata ba da zai tafi. Ta ce da Nos din, “Wattakila uzziri yarrike shi, kiddai taimakko mat ta da shayin”’.
Nos din ta fita a harzuke, can ta dawo da shayin a kofi. A wajen wasu marasa lafiyan ta karbo. Harira za ta kama Hafsat ta tashi, ta dakatar da ita ta tashi da kanta. Nos ta ba ta shayin ta karba tana sha a hankali, kamar ba ta so.
Sai da ta shanye ta ba ta magungunan da ruwa, ta ce ta koma ta huta. Ta sa hannu a wuyanta da goshinta, zazzabin ya sauka sai zufa ta ke. Ta ce, “Good, ki kara hutawa zuwa yamma in Doctor ya zo ya kara ganinki za ku iya tafiya gida”. Ta amsa daga can kasan makoshinta, “Toh”. Karfe shidda na yamma Abdul’azeez ya tashi aiki. A matukar gajiye ga yunwa, coffee kawai ya sha tun safe. Ya harhada komatsansa da system zuwa black robe dinsa da wig ya zuba a kujerar gaban motarsa. A hankali yake tuki idanunsa na lumshe sabida gajiya, a kan hanyarsa ya gifta ta asibitin da ya zube su Hafsat. A take ta fado masa a rai, ya tuno da su.
Da hanzari ya yi reverse ya shiga asibitin yana fadi a zuciyarsa. “Haka kawai an dora wa mutum nauyi, yana fama da kansa. Ni kaina kulawar nake bukata. A yadda na kwaso gajiyar nan kulawar mace nake bukata, ba ni in yi ta fama da ita ba”. Sosai ya yi dogon tsaki, amma a take ya yi istigfari cikin zuciyarsa a lokacin da zuciyarsa ta tambaye shi, “Wa ka ke wa tsakin???” Www.bankinhausanovels.com.ng
Daga shi sai bakaken suit din jikinsa ya fito kansa babu hula. Cikin takunsa na nutsuwa ya nufi cikin asibitin. Ya murda kofar dakin ya shiga da sallamarsa can kasan makoshi. Doctor da Nos din nan ya tarar a dakin suna kan Hafsat. A fusace Nos Hindatu ta dago ta dube shi don ta kudure a zuciyarta sai ta kare wa mijin yarinyar nan Hafsat tanadi idan ya zo, don hatta abincin rana ita ta ba su. Amma me? Kwarjini da kamalar Abdul’azeez Dakata, sai ya disashe ganinta ya kashe kuzarinta, ya warware mata duk wasu kalami da ta shirya na cin mutuncinsa.
Fuskarsa a daure ta ke tamau, ya ba wa likitan hannu suka yi musabiha. Likitan ya ce, za su iya tafiya gida ya rubuta musu sallama yanzun nan, don ta warware, stress ne kawai wanda ba ta saba da shi ba. Ba sai ya biya bill ba, yana cikin bill din gidansu.
A takaice ya yi masa godiya ya juya zai fita, sai kuma ya kalli Harira a fizge, “Ina jiranku a mota”.
Da sauri ta mike tana yafa mayafi, sosai ta ke jin shakkarsa ba ta san me ya sa ba. Yana da tsare gida sosai kuma da alama ba ya son wargi. Hafsat da kanta ta mike ta yafa mayafin doguwar rigarta
ta sauko daga gadon ta zura takalminta suka bi shi a baya. Tunda ya shigo idanunta suka sauka a kansa sau daya, ta ga yadda ya yi murtuk da fuskar nan ba ta kara marmarin kallon inda yake ba, kuma da ma ita ba gwana ba ce a kan kallon nasa ba, ba tun yau ba. Abu ne da ta horu da shi tun tana karama ta ganshi ta sunkuyar da kai. Da ma ya tula shirginsa a kan kujerar gaban motar don haka baya suka shiga dukkansu, kuma ko kujerar (empty) ce babu fuskar zamanta kusa da shi. Ko da wasa ita ma ba za ta fara ba. Ko da suka iso gida ya kwashi shirginsa ya kule a dakinsa, ba su kara ganinsa ba. Zama suka yi zugum-zugum a falo daga ita har Harira, kowacce ta yi tagumi cikinta na kugi. Zuwa yanzu Harira ta fahimci wannan auren da matsala, ba auren SO ba ne. Don ta lura ita ma amaryar ba ya gabanta. Amma dai ko ya ya ne a shekarunsa ya kamata a ce ya san cewa, akwai hakkin ciyarwa a kansa.
Ta dubi hafsat sai ta ji tausayinta ya kamata. A ganinta wannan salihar yarinyar mai kyau da kamala ta wuce auren RASHIN SO! To ba ta san wace irin kaddara ke tare da ita ba. Mikewa ta yi ta nufi kicin don ta ga ko za su samu abin da za su Cl.
A daidai wannan lokacin Abdul’azeez ya fito. Ya yi wanka ya sauya kayan jikinsa zuwa kananan kaya. Rike yake da mukullin motarsa da wayarsa ya wuce Hafsat a falon ba tare da ya ce mata uffan ba. Ba ta tsammanin ma ya kalle ta, ya fice. Wata irin Www.bankinhausanovels.com.ng ajiyar zuciya ta saki ta sauke tagumin da ta yi ta mike ta nufi dakinta, ta ajiye mayafinta ta fada ‘toilet’ ta sakar wa kanta shower na ruwa mai dumi. Ruwan na sauka a jikinta a hankali, sai ta ke ji kamar yana wanke mata zuciya, yana tafiya da ‘yar damuwar da ta samu kanta a ciki tun shigowarta gidan. Rashin kulawar Abdul’azeez gare ta bai dame ta ba ko kadan, tunda ta fi kowa sanin wane irin aure ke tsakaninsu. Horon yunwa da ta soma cin karo da shi a cikin auren shi ya so ya taba zuciyarta, musamman da yake ga mutum a tsakaninsu ko don ita ai ya rufa asirin rashin son nasa gare ta. Tana zaune a gaban madubi tana shafa ta ji ana dan kwankwasa mata kofa. Rigar wanka ce a jikinta ta tawul ta kame gashin kanta a tsakiya da katon (hair-bound).
“Shigo”. Kawai ta ce, don ta san Harira ce.
Murda kofar ya yi ya shiga, ya tsaya daga jikin kofa hannayensa duka biyu rike da fararen ledoji guda biyu. Ta cikin madubi ta ga wanda ya shigo din, sai ta kasa juyowa ta yi kasa da kwayar idanunta. Ajiye ledojin ya yi ya juya ya fita tare da rufo mata kofar. Sun kusa gwabza karo da Harira wadda ta taho rike da plate shake da jallop din taliya, ta ja gefe da sauri ta ba shi hanya ya wuce. A ransa yana fadin, “Abincin ma sai an dafa mata, gata mugun abu. To da babu wannan matar ni zan dafa kenan? Ko kuwa ana nufin kullum in je restaurant in sayo abinci sau uku a rana? Mtsew!”
A yadda ransa yake a jagule din nan ya san Mu’azatu ce kawai za ta iya tafiyar da damuwarsa, ga shi ya mata laifi, ya bata mata rai tun jiya yake ‘ignoring call’ dinta. Tun kafin ya karasa dakinsa ya kira ta. Ya manna wayar a kunnensa ya murda kofar dakinsa ya shige ya mayar ya rufe, har da murza key.
Kamar a mafarki Mu’azatu Rufa’i wadda ta fita hayyacinta cikin kwana biyu ta yi firgai-firgai saboda tashin hankalin da ta samu kanta a ciki, ta ga sunan ‘habeeb-qalby’ da ta sanya wa Abdul’azeez Dakata na yawo a screen din wayarta. Sai ta dauka gizo ne idanunta ke mata kamar yadda suke mata tun jiya, don haka har kiran ya kare bata taba wayar ba, sai ma wasu azababbun hawaye masu dan banzan yaji da ta ji sun kwaranyo mata. A karo na biyu wayar ta ci gaba da ba da ruri da ‘Habeeb-qalby’, ta kai hannunta ta damke gashin kanta tana ta cije labbanta na kasa da hakoranta, tana rokon Allah in mafarki ta ke ta farka.
A nasa bangaren Abdul’azeez jikinsa ne ya yi sanyi, ya tabbatar bai kyautawa masoyiyarsa ba, kamar wani wanda ya yi auren soyayya da zai janye jiki daga gare ta don kawai an kawo masa amrya? To me ye gaminsa da amaryar da ya janye wa Mu’azatu dominta? Wata zuciyar ta ce da shi, “Ba don amarya ba ne, kalamin bakinta ne. Ba ta iya magana ba!”. Ba ya so kowa ya shiga (personal life) dinshi hatta iyayensa haka Allah ya halicce shi, don haka yake kara kyamatar wannan auren, don a ganinsa Www.bankinhausanovels.com.ng Mammah ta shiga rayuwarsa da yawa ta rushe masa future ta hanyar aura masa yarinyar da ba ta yi daidai da tsarin rayuwarsa ba. Zai kuma bi duk hanyar da zai bi ya gyara rayuwarsa yadda ya riga ya tsara ta tun lokacin da ya mallaki hankalin kansa. Ya yi fushi da Mu’azatu amma ya huce, ya kuma kara tabbatarwa kansa ba zai iya rayuwa ba tare da ita
ba, dole ya lallashe ta. Ki yi hakuri Mu’azatu”.
Abin da ya rubuta kenan ya tura mata.
Mu’azatu ta karanta abin da Abdul’azeez ya turo mata. Lumshe idanunta ta yi, wata rahma ta sauka a zuciyarta. Kalaman (are short, yet they mean alot to her) girmansu ya yi na ruwan kogi ya wanke zuciyarta. Duk da haka ba ta mayar da amsa ba, ba ta kuma kira shi ba sai da ya kara ragaita. Ya turo mata sako na biyu. “Mu’azatu please, I’m sorry”.
Sannan ya sake kira. Wannan karon ta amsa kiran, amma maimakon ta ce komai, kuka ta sanya masa. Kyale ta ya yi ta yi har ta gaji. Ta share hawayenta sannan ta ce, Na huce!”’Murmushi ya yi, ya gyara kwanciyarsa cikin ni’imtaccen gadonsa, ya ja ‘quilt’ ya rufe rabin jikinsa, ya canza rikon wayar daga dama zuwa hagu. “So soon haka?” Murmushi ta yi kamar yana ganinta. Idanunta jajir don kuka.
“Tunda ka san ka yi min laifin, ka kuma amsa ka yi, ka bani hakuri, ci gaba da fushin nawa na mene ne?”
“Au, ni ba ki san kin yi min laifi ba? Ki dubi tsabar idona ki ce wai…..” “In ana sulhu ba’a tone-tone”. Ta katse shi. “Ki yarda to ba ni kadai na yi laifi ba, dukkanmu mun yi wa juna. Kuma naki yafi yawa.
Mu’azatu bana son raini, ko da aure tsakaninmu
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG