AUREN KWANGILA BOOK 2 CHAPTER 5 BY SUMAYYAH ABDULKADIR
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
Kokarin jan motarsa ya soma don sun soma ba shi haushi. Maganganun Harira sun yi masa wani iri, Sai ya ji kamar da shi ta ke. Hafsat ta ja baya ta rufe mata kofar ya fizgi motar da gudu. Bashakka da cikin kasa ne da ya bule ta da kura, sai aka yi sa’a kananan fararen duwatsu ne shimfide da harabar gidan bakidayanta. Ciki ta koma ta fada gadonta tana kuka riris, kuka mai dalilai da yawa. Mammah ta daina sonta ne? Isma’el, Usman da Halim ma? Baba Azumi ma? Tunda Mammah ta yi mata aure kuma shi kenan ta rabu da ita? Auren da ta tabbatar ba dadinsa ta ke ji ba. ‘Yar Harirar da ta bata tana debe mata kewa ta dauke abarta duk don a takura WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG ta a nuna mata yanzu ba mai sonta? Ya ya Za ta yi rayuwa a gidan nan daga ita sai Abdul’azeez din da shara ta fita daraja a idonsa? “Ya Allah ka kawo min sauki ni Hafsatu, idan kuma mutuwa za ta fi min sauki ka gaggauta daukar raina in huta da zaman gidan nan”. Hafsat ta fada a fili.
*********
Kusan kwanan da ta yi tana kuka shi ya sa washegari ta makara, don bayan ta idar da sallar asubah a nan kan sallayar barci ya sake yin awon gaba da ita. Ba ita ta farka ba sai bakwai da rabi, kuma lokacin ne Abdul’azeez ya ke tafiya aiki. Salati ta yi ta mike da ta dubi agogo ta fada toilet ta rage mararta ta wanko bakinta ta fito falo don wucewa kicin ta gani ko akwai abin da za ta iya ba shi na gaggawa duk da ta san da kyar ne in bai
ZAMU TASHI
fice ba. Amma ga mamakinta yana tsaye jikin dining yana daura agogo, ya shirya tsaf cikin suit bakake da farin ‘tie’ a wuyansa kamar kullum yana kurbar ‘tea’ din da ya hada cikin ‘cup’ a gurguje.
Karfe tara daidai zai shiga kotu a kan ‘case’ din wasu yara da kanin mahaifinsu ya cinye musu gado, tun daren jiya ya gama (compiling) duk wasu hujjoji da ya tara, amma ya manta da wani (recording) da ya yi saving dinsa a kan desktop dinsa ta ofis dole ya yi sauri ya je ya yi burning dinsa zuwa disc yadda in ta kama za’a iya playing dinsa a kotun saboda haka kusan a gurguje ya kammala shirinsa yau ya fito. Ya samu ya hada shayin don ba ya jin yau yana bukatar abinci daga safe har dare, sai ya ga abin da ya turewa buzu nadi a kan
wannan case din kamar yadda ya saba, musamman case na ‘marayu’ ba ya daukarsa da sauki. Jiya saboda wannan aikin bai samu ya kwanta da wuri ba don haka a dan makare ya Www.bankinhausanovels.com.ng tashi ya shirya ya fito falon. Sanyin A.C da ya ratsa shi a falon ya ba shi mamaki, don ya lura duk lokacin da ta fito da asuba sai ta kashe ta, amma yanzu ya tabbatar yadda ya barta jiya da daddare ya shiga daki ya kwanta haka ta kwana tana aiki. Talbijin a kunne, wutar falo a kunne, wadanda kullum sai ta kashe su ta ke kwanciya. Ya kafa wa kofar dakinta ido kamar hakan ne zai tabbatar masa tun shigarta daki jiya tana kukan tafiyar Harira ba ta kara fitowa ba. Sai ya matsa ya kashe A.Cn da sauran kayan wutar gabadaya ya tsaya nan jikin dining ya hada tea din da yake sha wanda ya dafa da butar
ruwan zafi (kettle) yana sha daga tsayen da yake yana daura agogo.
A daidai lokacin Hafsat-Suhaana ta murdo kofar dakinta ta fito. Sanye ta ke cikin riga da wando na barci masu kauri, kanta cikin hular wanka (shower-cap), bai juyo ya dube ta ba da yake ya bata baya, tunda har ta fito to lafiya ta ke kenan. Ya karasa shanye shayinsa ya ajiye kofin a kan (table) ya dora (wig) dinsa a kansa ya suri rigar lauyoyinsa da (briefcase) ya fice zuwa harabar gidan. Ya bude motarsa ya shiga, ya ajiye kayan hannunsa a kujerar gefensa ya yi wa motarsa ‘key’ Danfulani ya bude masa get ya murza kan motar ya nufi (office).
Barin Harira gidan maimakon ya kawo shakuwa kamar yadda Hajiya Maryam ta yi zato, sai ya kara lalata zaman gidan. Hafsat sai ta yi kwana biyu ba ta sanya Abdul’azeez a idanunta ba. Da safe ya daina bi ta kan abincinta, da ma Harira ke cewa ta dauka ta bishi ta sanya mishi a mota, shi kuma ba ya musantawa in ta kawo ko in ta ce masa “Ga breakfast” yanzu kuwa da babu Harira ba ta da wannan kwarin gwiwar, shi ma ba ya nuna yana bukata, in ya fito zai hada ‘tea’ ko ‘coffee’ ya sha ya fice, ita kuma ta kama kanta sosai, ba ta yi masa shisshigi ta tsaya a matsayin da ya ajiye ta na mai yi masa gadin gida. Ya daina turo direbansa daukar abincin rana tun tafiyar Harira ko me ye dalili ba za ta iya cewa ba. Da ya dawo karfe shida wanka yake yi ya shiga kicin ya kama girkinsa ya yi ta bare-barensa duk ya baba mata kicin ya tara mata kayan wanke wanke. Tunda ta lura ya daina cin abincinta ta daina dafawa da shi, iya cikinta ta ke dafawa don duk ranar da ta ajiye masa na dare, a ganinta lokacin yana gida. To yadda ta ajiye shi haka za ta dawo ta samu abinta, ta dauka ta sa a firji washegari da safe ta yi ‘steaming’ dinsa ta cinye don uwarta ba ta koya mata almubazzaranci da abinci ba, ko ta dumama ta mika wa maigadinsu. Www.bankinhausanovels.com.ng
Yana ganin abincinta wanda ya san don shi ta ajiye, amma tunda ta daina ce masa ga abinci zai tsallake shi ya yi abinsa. Girki ba bakonsa ba ne, don kuwa shi ya raini kansa a Ibadan ba wani ne ya raine shi ba.
Da ya gama ya zai zauna a ‘dining’ din kicin din ya ci abinsa don ba ta wasa da tsaftar madafin nasu. Yana gamawa zai shige daki ya hau aiki, in kuma ba ta a falon to zai yi zamansa ne a nan ya baje takardunsa da ‘system’ dinsa ya yi aikinsa. Shi kadai ya san yaushe yake shiga daki ya kwanta.
Hafsat ba ta kara shiga shirginsa, wanka ta ke yi ta dauro alwala ta gurfana a ‘side’ din da ta ware ta yi shimfida cikin dakin ta ya zama muhallin ibadarta, ta gurfana gaban mahaliccinta tana kai masa bukatunta.
**********
Haka kwanakin ke mirgina musu har tsayin watanni ukku, rayuwar tasu ba wani abu mai dadi da za a dorar, ‘connection’ dinsa da Mu’azatu ya yi rauni saboda ta samu tafiya (Law School) a jihar Adamawa (Yola) dole ta maida kai ta ajiye
soyayyar a gefe, shi ma cikin lokacin nan fama yake da ‘cases’ iri-iri masu zafi saboda a hankali fasaharsa da kwarewarsa a kan aikinsa ke fitowa sarari. Ya shiga sahun lauyoyi “yan gaban-goshin gwamnatin tarayya wadanda ake damkawa duk wani ‘case’ na marassa galihu, (private individuals) sun fara son janye Abdu’ azeez Dakata, amma ya tsaya a ra’ayinsa kadai na kasancewa lauyan gwamnatin tarayya mai rajin kare hakkin ‘yan kasa. Wanda babban burinsa a can gaba shi ne, barin ‘Bar’ zuwa ‘Bench’. Wato daga lauya zuwa mai shari’ah (justice). Yau yana zaune a ‘office’ wata abokiyar aikinsa Barrister Surayyah Tanko ta isko shi rike da wasu ‘files’ a hannunta. Tana zuwa ta dire masa su. Aiki yake yi, amma ya dago ya dube ta, “Taimaka ka duba min su Barrister Abdul’ azeez ka gani ko akwai abin da ya kamata mu kara ni da Adebayo. Zan je (Jamb Office) na dawo yanzu, zan sayo wa Suhaima ‘jamb form’, saura kwana uku a rufe. In aka rufe kuma sai wata shekarar”’. Www.bankinhausanovels.com.ng
Idonsa ya dan kafa mata, matar aure ce amma tana son shiga sha’aninsa da yawa bai san dalili ba. Sai kuma ya ji kamar ta yi masa tuni game da wani nauyi da ke kansa. Hafsat!”’. Sunan ya fado masa a rai (with a low tune).Surayyah ta gyara tsayuwa ganin sai kallonta yake yi, amma in ka dubi tsakiyar idonsa za ka lura ba ita yake kallo ba, tunani yake yi. Ta kada masa yatsunta a fuska, ya dauke kai daga kallonta ya Mayar bisa (computer). Tunanin me ka ke ta yi haka Barrister ina ta magana ba ka jina?”
Ina jinki’”“To amma ka yi shiru?”
“Ki yi hakuri ba zan iya duba miki ‘files’ din nan ba, amma zan baiwa Abdallah. Ni ma in zan samu mai rage min nawa ayyukan zan so”. Surayyah ta dan bata rai, “Ka ce dai kana tunanin budurwarka, amma ba ka da ayyuka da yawa, tunda jiya ku ka gama shari’ar da ka ke Murmushi ya yi har ‘dimple’ dinsa ya lotsa gashin saman idonsa ya kwanta sosai a kan lumsassun idanunsa. Ba tare da ya dube ta ba, hannunsa a kan (system) dinsa ya ce, ‘“Budurwa kuma? Ai an dade da wuce wurin Surayyah. I’m married”. Sai bayan ya fada zuciyarsa ta jefo masa tambaya. “Are you really married?” Ya girgiza kai da sauri, a fili ya ce. No, not really”.
Ita dai Barrister Surayyah ta saki ido da baki da kunne duka tana kallonsa tana _saurarensa, shaidaniyar zuciyarta na kara kawata mata shi ta kowacce fuska, shikadai ke burgeta duk fadin kotun, akan sa mantawa take ita matar aure ce, ba ta ma fahimci me yake fada ba. Ya kashe system din ya dube ta. “Ki wuce gaba a motarki zan bi ki a baya, sai dai bana gudu a titi ni kada ki bace mini. Ni ma zan Sayi Jamb form To mu yi amfani da mota ta mana?”
“Haram, in shiga motar matar mutane”Ni zan shiga taka”Allah ya kiyashe ni daukar mace a gaban mota ba Mu’azatu ba”. Sosai abin da ya fada din ya yi mata ciwo, ta ce. “Ai sai ka tafi kai kadai, ni ban iya tafiya a hankali ba”. Ta juya, ya bi bayanta yana fadin, “Ga shi kuma bana niyyar yin abu in fasa”.
Ta zumburo baki suka fice tare, kowa ya shiga tasa motar a haka suka tafi. Da gayya Surayyah
ke sharara gudu shi kuma bai yi kasa a gwiwa ba wajen binta, har suka isa. Suka nemi wuri suka yi ‘parking’ ita ta shige gaba suka sayi ‘forms’ din, babbar ‘yarta ta sayawa, shi kuma ya saya da sunan Hafsat Hamza Atiku Dakata. A hanyarsu ta dawowa ya yi mata ‘signal’ ya dauke kan motarsa ya nufi gida, bai koma (office) ba duk da lokacin tashinsa bai yi ba. Yana so ya cike mata da sauri tunda ya ji cewa babu isasshen lokaci. “Yaushe rabon duniya da Www.bankinhausanovels.com.ng ayyaraye!” Suhaanah ta ce a ranta, lokacin da ta tsinkayi muryar mijinta Abdul’azeez na yi mata sallama a kofar kicin, ta bada baya tana soya miya a kan ‘gass’ wadda za ta sanya a firji ta yi mata kwana biyu tana amfani da ita, don kayan abincin da ke cike da firji da freezer da nama da kifi duk sun kamo hanyar karewa, girke-girken da ta saba dole ta hakura ta koma cin fara da miya. Su kansu kayan miyar daga wadannan da ta ke soyawa babu wasu, cancana abinta za ta yi tunda ba tasan ina za ta nemo wasu ba. Kayan abinci kam suna nan a shake a buhunhuna da katon-katon ta san har gaba da shekara ba za su kare ba. Yau kwananta hudu ba ta sanya Abdul’azeez a idonta ba, ta kan dai jiyo bare-barensa a kicin in ya dawo kafin magriba, lokacin kam ita ta kammala abin da ta ke yi ta shige daki, don ta lura yana jin dadin yin aiki a falon in tana nan kuma sai ya kule a daki, shi ya sa ta haramta wa kanta zaman falon don ya sake a gidansa. Amma abin mamaki yau ga shi a gidan karfe hudu na yamma, wai yana yi mata sallama. Amsawa ta yi ciki-ciki ba tare da ta juyo ba. Sosai ta ke jin kiyayyarsa a ranta don ta lura bayan rashin so ba shi da imani ko kankani, ba shi da kirki, ba shi da adalci. Wasu tawagar hawaye suka shimfido a kan kundukukinta, ba ta yi wani hobbasa na hana su zuba ko share su ba. Zubar tasu ne kawai zai sa ta ji Sanyi a zuciyarta. Ko da ya ce za su yi AUREN KWANGILA, auren cin gashin kai, auren kowa yayi zaman kansa, ba ta zaci har da rashin sanin halin da junansu ke ciki ba, yanzu in mutuwa ta yi haka gawarta za ta rube ta lalace a daki sai ta fara doyi zai sani? In ciwo ta ke sai ya ci ya cinye ta zai sa ni? Www.bankinhausanovels.com.ng
Tun tana tunanin Mammah da mutanen gidansu, har ta hakura ta daina, ta yarda Mammah ta aurar da ita ga azzalumin danta ne don ta gaji da ita, ya kashe ta da bakin cikinsa duk su huta. Hawayen suka fara gudu suna sauka a kan kirjinta, hakoranta na karkarwa suna haduwa da junansu saboda kuka mai cin rai, amma ta sa hannu ta toshe bakinta ba ta son amon kukan nata ya fito fili. Abdul’azeez ransa ya so ya baci da yadda ta yi watsin Allah-tsine da shi a bakin kofa, ta kuma amsa sallamarsa kamar ba ta so. Sannan ta ki juyowa. Kwafa ya yi ya zuro jikinsa ya idasa shigowa cikin kicin din yana kallon abin da ta ke yi. A matsayinsa na wanda rabonsa da abinci tun daren jiya, sosai miyansa ya tsinke da wannan hadaddiyar miyar wadda ta ji naman saniya zukuzuku sai tashin kamshin spices da mushroom curry ta ke yi. Ya hadiye miyau mukut! Ya bi ta da harara duk kuwa da ance aikin banza harara cikin duhu don kuwa bayanta kawai yake iya gani. “Sallama fa nake yi amma ki ka yi banza da ni?” Haushi ya ba ta sosai, kamar ta juyo ta dalla masa mari amma ina! Ko tsakiyar idanunsa ba za ta iya kalla ba balle mummunar magana ta hada su har akai ga abin da zuciyarta ke kissima mata. Na amsa ai”. Ta sake amsawa ciki-cikin. Cikin hadiye kukanta gabadaya. Kwafa ya sake yi ya juya ya fice yana fadin,
“In kin ga dama ki zo ki yi min bayani in cike, form dinki ne na jamb Ai ba ta san lokacin da ta saki ludayin miyar a kasa ba ta biyo bayansa. Jin karar faduwar ludayin ne ya sa Abdul’ azeez ya juyo sai ganinta ya yi har ta kusa cimmasa, fuskarta jage-jage da hawaye. Wani abu mai kama da tausayi ya so ya tsirga masa, yana mamakin son karatu irin nata, wato fushi ta ke da shi sosai a kan laifin da bai
sani ba, amma jin zancen jamb ta manta komai ta biyo shi har ta manta ta bar wuta a kunne.
Dakatawa ya yi, ta zo ta shige shi ta yi falo ya dawo ya kashe ‘gass cooker’ din da kansa, ya rufe mata miyar sannan ya bar kicin din. A falon ya same ta a tsaye, zama ya yi cikin (3 seater) ya jawo ‘briefcase’ dinsa ya fito da ‘scratch card’ din da ‘receipt’ ya daga lumsassun idanunsa ya dube ta, “Kawo takardunki, sai ki zauna mu cike”. Zan iya cikewa da kaina”“Kina da ‘system’ ne?” “Akwai tawa ta gida, amma babu ‘internet connection”. Ga mamakinta sai ya tura mata jakar ‘laptop’ dinsa.
“Dauki wannan ki yi da ita, ki hanzarta ki gama zuwa gobe sun kusa rufewa’”Dauka ta yi ta matsa gabansa ta karbi ‘scratch’ din da sauran takardun sai kuma ta tsugunna a gabansa ta yi shiru. Tunanin me ya tsayar da ita yake yi, sai ji ya yi can a tsakar kansa tana fadin, “Na gode sosai!’”’. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya bude idanunsa sosai a kanta daga lumshewar da suke yi da kansu, “You don’t need to thank me. It’s part of our contract, kin manta ne?” Girgiza kai ta
yi, a sanyaye ta ce. “Ban manta ba, duk da haka na gode!”Sai ya kasa ba ta amsa ya bi ta da ido har ta mike ta shige daki dauke da ‘system’ din cikin nutsuwa. Barrister Abdul’azeez Dakata ya koma da bayansa ya jingina a jikin kujerar da yake zaune. Kewar Mu’azatu ta sauko masa, yau kwana uku ba su yi magana ba, ya san kuma bai isa ya kira ta a wannan lokacin ba (as a law-school student). Fassara reactions din Suhaanah yake so ya yi, wadanda ta yi yau a gabansa ya gane inda ta sa gaba, ya kasa. Idan haushinsa ta ke ji me ya yi mata? Da ma can ya yi mata alkawarin samun kulawa irin ta ma’aurata ne da yanzu ya saba alkawari ya bata mata rai? Ya yi zaton ya fada mata kowa zai yi zaman kansa ne ba tare da shiga rayuwar dan uwansa ba? In ta manta ne zai iya sake zaunar da ita ya sake yi mata rehearsal na rayuwar da za su yi har zuwa wa’adin auren. Idan bukata gare ta na wani abu, ko kayan abinci ta bude baki ta ce babu kaza mana, shi yake hana ayi zalinci balle shi a kankaran-kansa ya zalunci na kasa da shi. Ya ci gaba da lalubawa cikin kwakwalwarsa yana nemo ta inda ya kuskure mata. Wata zuciyar ta ce, ‘Kitchen … waya… audugar mata…!!!
Kansa ya sara, wadannan ma bukatu ne masu muhimmanci a wajen mace tunda ya san ba zai iya bukatar da ta fi kowacce din ba. Mikewa ya yi ya nufi kicin yana dube-dube, abubuwa da yawa irin su dankali, albasa, doya, kayan miya duk babu. Ya bude ‘freezer’ da sauri ya mayar ya rufe. Babu komai! Ya bude firji nan ma babu komai na kayan girki, irinsu (Veggies), babu lemuka, babu ruwan sha komai na_ kayan masarufin gida babu a kicin din. Ya so ya fahimci hakan tun da jimawa abubuwan da ke kansa suka mantar dashi. To don me ba za ta bude baki ta
gaya masa ba? Ko bata da baki ne? Zuciya mai gaskiya da adalci a tsakiyar kirjinsa ta ce da shi.
“A ina ta ganka? In ka dawo ba ka nemanta, in za ka fita ba ka gaya mata. Kowanne irin aure akwai bincikar lafiyar iyali a cikinsa, banda naka”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kikkifta ido ya shiga yi, irin na guilty conscience, ya fito daga kicin din. Ya sa a ransa zai dinga bincikar lafiyarta ko da bayan kwana daidaya ne.
Dakinsa ya shige ya yi wanka, ya yi sallar la’asar ya sanya kananan kaya marassa nauyi ya dauki makullin motarsa ya fice.
Kasuwa da supermarkets ya shiga, duk abin da ya kamata maigida ya ajiye a gidansa ya sayo, wanda zai jima bai kare ba. Hatta ‘pad’ katon guda ya saya. Waya ce dai har yanzu zuciyarsa ta ki amince masa da ya sai mata a kan dalilai masu dama. Ya juyo kan motarsa ya nufo gida, booth dinsa da kujerar bayansa shake taf da kaya. Danfulani ya sa ya kwaso kayan ya shiga da su kicin ya tsaya yana nuna masa inda zai adana kowanne.
***********
Sanda Hafsat ta dauki ‘computer’ din Abdul’azeez ta shiga daki tsakiyar gadonta ta ajiye ta, tana cike da doki ta nemo takardun karatunta cikin ‘lockers’ din da ta adana wasu muhimman takardunta da littattafai na makarantarsu ta (St. John Berchman’s College). Lokacin da Mammah ta hadasu cikin kayanta don ta san watarana za ta bukace su.
A dokance ta ke komai, amma me? Tana kunna ‘system’ din fuskar wata kyakkyawar mace ne a ‘home-screen’ din tana kwance a kan hannayenta tana sakin wani irin tattausan murmushi.
An ce ko ba SO aure daban yake, Allah (Subhanahu wata’ala) shi kadai ya san iyakacin karfin izzarSa a cikinsa. Ji ta yi ranta ya wani irin jagule, zuciyarta ta matse, idanunta sun rufe da kansu. Ko bai gaya mata ba wannan ce Mu’azatu kenan. Wadda Abdul’azeez ya yarda ya saba wa iyayensa a kanta, ya jefa Mammah cikin dawwamammen bakin ciki da bacin rai a kanta. Ta ji ta tsani Mu’azatu, wata irin tsana da ba ta taba yi wa dan-Adam dan uwanta ba. Bacin ran da ya sanya ta kasa yin abin da ta ke dokance da yi, zuciyarta ta yi duhu matsananci. Kawai sai ta kashe komai ta ture gefe ta koma ta kwanta, ta lumshe idanunta. Www.bankinhausanovels.com.ng
Sai da suka gama kimtsa komai ya sallami Danfulani, ya zuba ruwa a karamar tukunya ya dora a ‘gass’ ya kunna. Nan da nan ya yi zafi, ya dauko ledar “‘cous-cous’ cikin katon dinsa ya farke ya juye rabi. Ya kashe ‘gass’ din. Ya kwashe gabadaya a (food-warmer) ya diba a ‘plate’. Miyar da ransa ya biya da ita tun dazu ya diba ya zuba a kai ya sanya mata sauran a firji yadda ya ganta, ya ja gefe kan karamin ‘dining’ din cikin ‘kitchen’ din ya ci ya koshi.
Ya kora da ruwa mai sanyi ya fito ya yi dakinsa.
Karo ya ci da katon din (sanitary pad) da macleans din ( beverly hills formula ) da ya saya mata a falo har da shampoo din (pert-plus) a cikin
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG A KODA YAUSHE