SHU’UMIN NAMIJI CHAPTER 7 BY FATYMA SARDAUNA

SHU’UMIN NAMIJI CHAPTER 7 BY FATYMA SARDAUNA

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

Cikin rashin kuzari yamiƙe haɗe da nufar hanyar barin falon, ko kaɗan babu nutsuwa acikin zuciyarsa, ko sake bi takan abincin nasa baiyi ba, haka yafice daga cikin falon. kaitsaye ɓangarensa yanufa. Shirya kansa yayi cikin riga da wando na suit. kaitsaye asibiti ya wuce domin kuwa akwai wasu patient da zai gani.

Gaba ɗaya tunanin Zahrah ya kulle, hartakai ta kawo ko makaranta taje ma bata da wani aiki saina tunani, ko karatun ma da ake koyar dasu bata fahimta, abubuwane sukai mata yawa, tayi matuƙar danasanin marin da tayi mawa Dr Sadeeq, haƙiƙa idanunta sun rufe, batare da tayi tunanin komai ba ta yanke hukunci, sai dai kuma har yanzu tunaninta daya gushe bai dawo gareta ba, takasa yanke hukunci, haka kuma takasayin tunani mai kyau, saidai tayarda da abu ɗaya. shine Doctor Sadeeq sam basa’an auren ta bane, yafi ƙarfinta. Yau kimanin kwana huɗu kenan da faruwar haka a tsakaninsu, tundaga wannan daren kuwa harzuwa yau, Dr baisake zuwa gareta ba, saidai fa kullum safiya, yana turo drivern sa akan yaɗauketa yakaita makaranta. amma zancen dai ɗayane, bata taɓa yarda tashiga motar, koma sauraran driver’n nasa batayi.

Dariya sosai Mahmud yashiga yi, a lokacin da yagama jin matsalolin abokin nasa, haƙiƙa Sadeeq yabasa dariya, ko da wasa bai taɓa tunanin wai Namiji kamar Sadeeq zaiji tsoron furtawa mace kalmar soyayya ba.

Tsuka Dr Sadeeq yaja haɗe da ɓata fuska cike da takaicin dariyan da Mahmud ɗin ke masa yace

” Bawai nafaɗa maka matsalata bane don kasani a gaba kayita min dariya ba, mafita nake nema Mahmud, gaba ɗaya kaina ya kulle, inasonta banakuma tunanin zan’iya barinta, amma kuma naga alamomin cewa zan rasata a fili!” Dr Sadeeq yafaɗi maganar cikin son abokinnasa ya ƙarfafa masa guiwa.

Ƙoƙari Mahmud yayi wajen tsaida dariyar tasa haɗe da gyara zama

“Yazama dole nayi maka dariya Sadeeq, a matsayinka na likita bokan turai, ka kasa jure zafin soyayya, amma kuma ko kaɗan banga laifinka ba, sai dai kuma, akwai ƙalubale a gabanka!” Mahmud yaƙare maganar yana mai waina pen ɗin dake riƙe a hanunsa.

“Wani irin ƙalubale kenan Mahmud?” Dr Sadeeq yatambaya cike da zaƙuwa, saboda shi mafita kawai yake nema.

“Nasara ko kuma akasinta, sune babban ƙalubalen da zaka fuskanta, amma ina mai maka fatan nasara, duk dacewa banganta ba, amma nasan tahaɗu sosai, saboda nasan abokina ya’iya zaɓe!” Mahmud yafaɗi hakan cike da barkwanci, wanda hakan kuma halinsa ne.

“Bazaka taɓa canjawa ba Mahmud, kai ko da yaushe idan ana magana mai amfani saikayi yanda kayi ka sako wasa a ciki.” Dr Sadeeq yafaɗi hakan yana mai shafa suman kansa.

Ƴar ƙaramar dariya Mahmud yayi haɗe da ɗaukan cup ɗin juice ɗin dake gabansa yakai zuwa bakinsa.

“Babu amfanin ƙara tada zancen a gareta Sadeeq, tunda ta nuna maka bata sonka, inaganin kabata lokaci, ko ba komai zatayi tunani mai kyau, amma fa hakan danace bawai yana nufin kada kasake zuwa gareta bane, zaka iya zuwa gareta ako da yaushe, amma kada ka sake ɗago mata da zancen inaga haka zaifi!” Mahmud yafaɗi hakan cike da son ƙarfafamawa abokinsa guiwa.

STORY CONTINUES BELOW

Ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya Dr Sadeeq ya sauƙe, haɗe da haɗiyar yawu, sai yanzu yasomajin sanyi a cikin zuciyarsa, domin kuwa da gaba ɗaya kansa ne ya kulle.

“Zanyi yanda kace Mahmud, sai dai kuma inajiyewa kaina tsoro, kada a gaba taƙi amsata, sannan kuma yanzu bansan da wani ido zan kalle ta ba!” Dr Sadeeq ya faɗi haka cikin ɗar ɗar.

Dariya Mahmud yakuma kwashewa dashi a karo na biyu, lallai yayarda cewa so mugun abune, domin kuwa shi kaɗai ke sa jarumi kuma gwarzon namiji acikin tsoro dakuma ɗar ɗar.

“Yanaga jikinka gaba ɗaya yaɗau rawa, kada dai kabani kunya, tsoronta kakeji tun yanzu, idan kuma akayi auren yaya kenan?” Mahmud yatambaya cike da shaƙiyanci.

Tsuka kawai Dr Sadeeq yakuma ja, haɗe da miƙewa tsaye, domin idan yabiye ta Mahmud to baƙin ciki sai ya cika masa zuciya, domin kuwa halin Mahmud ne tsokana da yawan barkwanci.

“Gwamma nayi tafiyata zaifi min, kayi dariyanka ka ƙoshi, ai nine nakawo kaina office ɗinka, kana da right ɗin da zaka iyamin komai” Dr Sadeeq yakare maganar yana mai gyara zaman suit ɗin dake jikinsa.

Ko sake sauraran Mahmud dake ta faman dariya baiyi ba, yayi ficewarsa daga office ɗin Mahmud ɗin.

Cikin ɗan kuzarin da yasamu yake tuƙa motar tasa, yanzu kam yagama aminta da shawaran da zuciyarsa ta basa. Kai tsaye gida ya koma, wanka yayi haɗe da shirya kansa cikin wani haɗaɗɗen riga da wando na jeans masu kyaun gaske, sosai kayan sukai masa kyau a jiki, suka kuma fito da asalin kyawu da kwarjininsa, babu abun dake tashi ajikinsa sai daddaɗan ƙamshin turare. Makullin motarsa ya ɗauka haɗe dasakai yafice daga cikin ɗakin.

Zaune take akan ƴar katifarta, daga ita sai wata riga marar nauyi, jakan kayan shafanta ne aje a gabanta, da’alama daga wanka tafito, domin kuwa wani sashi na jikinta ɗauke yake da danshin ruwa. Kallo ɗaya zakai mata kafuskanci irin ramar da tayi lokaci guda, gaba ɗaya ta zabge ta faɗa, hips da breast ɗin tane kawai suke a cike a jikinta. A hankali take shafa Vaseline ɗin dake riƙe a hanunta, Yanayin yanda take shafa vaseline ɗin idan ka gani, kace dole akai mata. tana gama shafa mai ɗin, ta murza powder kaɗan akan fuskarta, haɗe da shafa kwalli a cikin idanunta, take fuskarta ta tasakeyin fayau, yayinda idanunta, suka sake bayyana girmansu a fili,kasancewar kwallin yana taimakawa wajen bayyana girman ido.

Kallonta tamayar kan ɗan ƙaramin agogon bangon dake ɗakin nata, ƙarfe 5 na yamma kenan, kuma dai dai lokacin sukayi da Husnah cewa zataje ta sameta a gida. Cikin rashin kuzari, ta miƙe haɗe da ɗaukan kayanta riga da sket na atamfa tashiga sanyawa, duk da cewa atamfar mai sauƙin kuɗi ne, amma hakan baihana ta yi mata kyau a jikinta ba. Wani irin zazzaɓi takeji yana sanɗan jikin ta, idan ba don tariga da tamawa Husnah alƙawarin cewa zata zo yau ɗin ba, to tabbas da ta ɗage zuwa gidansu Husna’n saboda bata wani jin daɗin jikinta, takumasan cewa damuwace kurum tayi mata yawa.

Inna ce tashigo cikin ɗakin, adai dai sanda Zahrah ta gama sanya hijab ɗinta.

“Au ashema kinsan da zuwansa kenan?” Inna tatambaya tana mai ƙarewa Zahrah kallo.

“Banganeba Inna, zuwan waye kuma?” Zahrah taje fawa Inna tambaya cikin rashin fahimtan inda kalaman Inna’n suka dosa.

“Naga kinshirya tsab kamar kinsan da zuwansa, to koma dai menene kije yanajiranki a waje!” Inna tafaɗi hakan tana mai ƙoƙarin barin ɗakin.

“Waye Inna? kuma ni shirin nan da kika ga nayi, gidansu Husnah zani, amma waye ke nemana ?” Zahrah takuma tambaya cike da son ƙarin bayani.

“Waye kuwa zaizo neman ki a yanda kike ɗinnan, ai sai dai shiɗin da har ya yarda zaiyi JIHADI ya aure ki a haka, amma wai saboda son zuciya da butulci irin naki, kike neman watsa masa ƙasa a idanu!” Inna taƙare maganar dai dai sanda tayificewarta daga cikin ɗakin.

STORY CONTINUES BELOW

Wasu irin siraran hawayene suka samu nasaran gangarowa daga cikin idanun Zahrah, tabbas gaskia Inna ta faɗa, babu wani mai nemanta sai shi ɗin shi kaɗai, kuma tabbas tayadda shima JIHADI yayi kamar yadda Inna tafaɗa, ashe dagaske ne itakam ƙaddaranta tayi mata mummunan zane a goshinta, saurin share hawayenta tayi haɗe da sakai tafice daga cikin ɗakin.

Tsaye yake a jikin motarsa yayinda kansa ke duƙe a ƙasa, ɗan makullin motarsa ce riƙe a hanunsa yana kaɗawa, wannan karon kam sosai yake yaƙi da zuciyarsa don bayaso tasake sanya masa tsoro kokuma ɗarɗar.

A hankali take taku cike da nutsuwa har ta ƙaraso garesa, ɗan nesa dashi ta tsaya haɗe da yimasa sallama cikin sassanyar muryarta wadda bata fita sosai.

Lumshe idanunsa yayi haɗi da buɗesu a lokaci guda, badon komai ba sai don yanda sassanyar muryarta ta daki jiki da zuciyarsa.

“ZAHRAH!” yaƙira sunanta cikin murya marar fidda ƙaƙƙarfan sauti.

“Um!” Zahrah ta amasa masa batare da ta’iya motsa bakinta ba, haka kuma kanta a duƙe yake tunda tazo bata’iya ɗaga kai ta kallesa ba.

Kallonta yashiga yi tundaga ƙasanta har sama, tabbas duk da cewa a cikin hijab take, amma hakan bai hanasa hango rahamar da tayi ba, take yaji zuciyarsa tayi sanyi, tausayinta yasake kamasa.

“Inaso kimini iso cikin gida, inaga maganar mu acan zaifi, domin ina buƙatar zama!” yafaɗa cike da ƙosawa da tsayuwan da yakeyi.

Sumi sumi haka ta juya ta nufi cikin gida, harta shige cikin gidan bai ɗauke idanunsa daga kanta ba, “Wallahi Zahrah ta haɗu, komai nata mai kyau ne!” yafaɗi hakan a fili, cike kuma da shauƙin soyayya.

Jim kaɗan Zahrah tafito, tana mai wasa da yatsun hanunta, “Kashigo!” kawai ta’iya furtawa cikin murya mai sanyi. Tana gaba yana biye da’ita haka suka doshi cikin gidan.

Katuwar tabarma tabaje musu a hanyar zaure, yayinda ta je ta zauna a can ƙarshen tabarman ta takure waje ɗaya, tamkar amaryar da aka kaita ɗakin miji yau yau, lol.

Murmushi Dr Sadeeq yayi bayan yayimawa kansa mazauni, dole dai shi zai ci gaba da zama jarumi ako da yaushe.

” Miye haka? ai ko da yanka naman jikin mutane nake, ya kamata ace kin matso kusa dani, balle ma kuma ni ba’abun da nakeyi, ko na taɓa miki wani abune ?” Dr yafaɗi hakan cike da kulawa.

Saurin ɗago da kanta tayi ta kallesa, domin yadawo mata asalin Likitan da tasani, kuma gaba ɗaya ya sauya wasu ɗabi’un nasa.

Giransa ɗaya yaɗage sama, haɗe da cewa “Yadai, ko nayi wani sabon laifi ne akan wancan banda labari?”

Girgiza kanta tashiga yi ita kaɗai tamkar ƙadan garuwa, domin ita tama rasa maizata ce dashi domin kuwa da wani salon yadawo.

“Matso kusa dani mana!” yafaɗa cikin sanyin murya, mai ɗauke da lallashi.

Cikin rashin kuzari, ta koma tsakiyar ta barman ta zauna, bayan ta haɗa jikinta duka ta takure waje ɗaya.

Ajiyar zuciya Dr Sadeeq ya sauƙe haɗe da sanya hanunsa yashafi ƙasumbar dake kwance akan fuskarsa.

“Maiyasa zakisa kanki a damuwa Zahrah? yawan kuka dakuma yawan tunani marassa amfani, basa haifar da komai sai gajiyar da ƙwaƙwalwa, please banso kina wahalar da ƙwaƙwalwarki, nasan cewa abaya banine sila ba, amma yanzu nine sila.!” ɗanjim yayi kana yaci gaba da cewa…” Kiyi haƙuri Zahrah, nasan bankyauta ba, amma inaso kimanta komai, inaso ki fuskanci karatunki, ki maida hankali sosai kinji ƙanwata, bawanda zaimiki dole, ke mutumce kuma kowani ɗan adam yana da ƴanci, kema kina da ƴanci, saboda haka ki daina kuka kinji ƙanwar Likita!” Yanayin yanda yaƙare maganar kaɗai ya’isa yasanya zuciya hucewa daga cikin fushi.

STORY CONTINUES BELOW

Kuka kawai Zahrah ta fashe dashi mai sauti, domin kuwa sai yanzu nadaman abun da ta’aikata a garesa yadawo mata sabo fil. A hankali ta ɗago idanunta da suke ɗigan hawaye tamaida kallonta garesa, wannan fuskar ta mara? ta tambayi kanta, tabbas batayiwa kanta adalci ba, Dr Sadeeq baicancan ci mari daga gareta ba. kukane yakuma ƙwace mata, don batasan tayanda zata soma basa haƙuri akan abun da tayi masa ba.

Cike da damuwa ya dawo kusa da’ita, har suna iya juyo ƙamshin turaren juna.

“Subahanallah Zahrah kuka kuma? kinfasan banaso, kidaina kuka kinji, ki faɗamin idan ganina ne bakiso, yanzu zantafi Zahrah, nazo ne dama nabaki haƙuri akan abun da yafaru tsakanina dake, kiyi haƙuri Zahrah haka bazata….” Kasa ƙarasa maganar yayi sakamakon Zahrah da ta sanya duka hannayenta biyu ta toshe masa baki.

“Dan Allah kada ka ƙasƙantar da kanka awajen wacce bata dace ba, bata kuma cancanta ba, bakaine yakamata kabani haƙuri ba, nice yakamata na baka haƙuri, bai kyautu ace na mareka ba, nayi nadama Doctor, dan Allah kayi haƙuri, bansan yanda zanyi ba ne banda zaɓi, kayafemin!” Zahrah ta ƙare maganar cikin kuka, haɗe da karyewar zuciya.

Take yaji tausayinta yasake ninkuwa acikin zuciyarsa.

A hankali ya sanya hanu yazame hannayenta dake kan bakinsa, domin kuwa hakan da tayi masa har ya sanya tsikar jikinsa sun soma motsawa.

“Kinaso nayi haƙuri?” Dr yatambayeta.

Kaitashiga kaɗawa cikin kuka alamar “Eh”

“To kidaina kuka, domin kuwa daina kukanki shikaɗaine zaisanya nayi haƙuri nakuma manta da komai, kuma ko dama ni Zahrah batayi mini laifi ba, ƙanwata bata laifi a wajena, saboda haka share hawayenki kinji!” yaƙare maganar yana me miƙomata wani farin handkerchief wanda yafito dashi daga cikin aljihun wandonsa.

Karɓan handkerchief ɗin Zahrah tayi, cike da shagwaɓa tashiga share hawayen dake gudana akan fuskarta, ajiyar zuciya kawai take sauƙewa akai akai domin kuwa ko ba komai tarage wani nauyi dake maƙare a gefen zuciyarta.

“Yauwa ƙanwata, kinga kinfi kyau idan kina murmushi dakuma dariya, inaso akoda yaushe kikasance cikin farinciki!” Dr yafaɗa cikin nishaɗi, domin kuwa sosai yaji daɗin yanda Zahrah ta sauƙo daga fushin da takeyi dashi.

Tana gama share hawayen nata ta miƙamasa handkerchief ɗinnasa.

Kai yagirgiza alamar a’a haɗe da gyara zamansa “Nabaki kyauta, ki ajiye a wajenki, ko saboda gaba, domin naga ke kuka baya baki wahala, kinga duk lokacin da kika soma koke koken ki saiki share hawayenki da shi!”

Hararan wasa ta jefesa dashi, haɗe da murguɗa masa ɗan ƙaramin bakinta.

Dariya yayi domin sarai yana lure da’ita kuma yaga abun da tayi masa.

“Inazakije kikaci uban kwalliya haka? gashi kuma kinzo kinɓata shi da kuka.” Yafaɗi maganar alokacin dayake ciro wayarsa daga cikin aljihunsa.

Turo bakinta tayi gaba, cike da ƙunƙuni tasoma motsa bakinta, da’alama wani abu takeson faɗa, “wai a hakanne nayi kwalliya, kawai dai yace banyi masa kyau ba” Zahrah tafaɗi hakan a cikin zuciyarta.

“Wayace miki hakane a zuciyata? ni na’isa nace kyakkyawar ƙanwata batayi kyau ba, to ma duk cikin garin Abuja wayakai ki kyau ne? babu fa!”

Dariya tasanya, wanda tajima batayi shiba, cab aikuwa ko da acikin makarantarsu akwai waƴanda suka fita kyau dayawa, balle kuma duka garin Abujan baki ɗaya.

Tsayawa yayi yana kallon yanda take dariyan, komai tayi ƙara kyau take.

Hanunsa ya sanya acikin aljihun wandonsa haɗe da ciro wani haɗaɗɗen choculate, ɓare ledan choculate ɗin yayi haɗe da miƙo ma ta. Kyawawan idanunta ta ɗago haɗe da watsa masa su, girgiza kanta tayi, alamar bata buƙata.

STORY CONTINUES BELOW

Kwaɓe fuska Dr Sadeeq yayi haɗe da marairaice idanunsa, take taji tsikar jikinta ya zuba, yayinda gabanta yayi wani irin mummunan faɗuwa, domin kuwa hakan da yayi yasanya fuskarsa ta koma yanayi da fuskar Zaid, saurin ɗauke kanta tayi daga garesa, haɗe da sauƙe idanunta ƙasa, yabuɗe baki zaiyi magana kenan wayarsa tasoma ƙara, alamar shigowar ƙira, cike da girmamawa yaɗauki ƙiran ganin cewa ƙiran daga Hajiyarsa ce.

“Kana’ina?” Hajiya tatambaya a kausashe.

Baikai ga bata amsaba taci gaba da cewa “Koma mekakeyi kabari, Inaso kaje gidansu Salima yanzu, umarni ne ba shawaraba!” ƙit takashe wayan batare da tajira taji mai zai ceba.

Ajiyar zuciya ya sauƙe haɗe da maida kallonsa ga Zahrah.

“Wani uzuri yatasomin, zantafi kikula da kanki!” yafaɗi maganar yana me miƙewa tsaye.

Miƙewa itama Zahrah tayi batare da tace dashi komai ba tashiga naɗe tabarman da suka tashi akai.

Wani irin kallo haɗe da murmushi mai tsayawa a zuciya yayi mata, kana yasa kai yafice daga zauren gidan nasu, yana fita yafaɗa motarsa yayi mata key.

Tanajin ƙaran tashin motarsa ta sauƙe a jiyar zuciya haɗe da komawa cikin gida.

Kamar yanda mahaifiyarsa ta umarcesa hakan yayi domin kuwa yaje gidan su Salima sungana da’ita, yarinyar bata da wani aibu, amma kwata kwata jininsa danata baizo ɗaya ba, domin kuwa sam bata burgesa kasancewarta mace mai rawan kai da shegen girman kan tsiya, har gwamma masa Zabba’u akan Salima, domin dai shikam Salima batayi masa ba. Haka dai suka gaisa sama sama, ko minti 20 baiyiba yabaro gidan nasu..

Bayan Sati Ɗaya.

Kusan ko da yaushe sai Doctor Sadeeq yazo gidan su Zahrah, amma kuma tundaga wannan lokacin baisake koda ɗago wani zance makamancin wancan ba, sai dai yana’iya ƙoƙarinsa wajen bata kyakkyawan kulawa. Sannan kuma dake ita ɗin me raunin zuciya ce take ta sake bashi yardanta akaro na biyu.

Ɓangaren gidansu Dr Sadeeq kuwa harsun fara shirye shiryen bikinsa, domin kuwa Hajiyarsa wannan karon bada wasa take ba, tace acikin 3 weeks takeso ayi bikin. Shi dai Dr Sadeeq idanu kawai ya zuba musu, domin kwata kwata baijin auren a jikinsa, da za’afasa auren to dazai fi kowa murna, saboda Zahrah yakeso Zahrah ce muradinsa, amma kuma haryanzu yakasa samun wani gamsashshiyar amsa daga gareta.

Ƙarfe 3 dai dai jirginsu ya sauƙa a babban airport ɗin dake cikin garin Abuja, motoci ne iri da kala har guda shida suka zo tarbansa, ciki kuwa hadda Dad ɗinsa, a hankali yake sauƙowa daga cikin matakalar jirgin sanyen yake da kayan sanyi hadda hula, yayinda fuskarsa ke ɗauƙe da wani haɗaɗɗen baƙin glass na maza, sosai yaƙara kyau da fari, kallo ɗaya zakai masa katabbatar da cewa yakai cikekke kuma gwarzon namiji, a gaskia yana da kyau da kuma kwarjini, uwa uba kuɗaɗe sun samu mazauni a jikinsa. Bakowacce mace bace zatayi tozali da haɗaɗɗen namiji kamar Zaid, kuma takau da idanunta ba, saboda Zaid yahaɗa duk wani abu da kowacce mace zata so awajen ɗa namiji, shidai matsalan sa ɗaya munanan halaiyansa. Yanda yake tafiya cike da izza shiyafi komai ɗaukar hankali, dakuma jan hankali zuwa garesa. Cike da farinciki Alhaji Ma’aruf yarungume ɗa’nnasa, duk da cewa babu wani shaƙuwa me ƙarfi a tsakaninsu amma yana matuƙar son Zaid.

Mota ɗaya suka shiga shida Dad ɗinsa, yayinda guard ɗinsu suka mara musu baya a cikin sauran motocin. Kwanciya yayi lamo ajikin kujeran motar haɗe da lumshe idanunsa, wani irin sanyi yakeji acikin zuciyarsa, koda wasa baitaɓa tunanin haka zai kasance dashi ba, kamarshi Zaid ace tunanin mace yahanasa sukuni harsaida yabaro duka abun da yakeyi ya dawo zuwa gareta, amma zaiyi maganin abun a yau bawai sai gobe ba yake da buƙatar ganin sugar baby’nsa, sai dai kuma wannan lokacin bada wasa yazo ba…

Zahrah ne keta kai kawo a tsakiyar ɗakinta, tabbas tayarda da duk wani shawara da zuciyarta ta bata, zuwa yanzu yakamata ace tayi abunda ya dace. Wayarta ne yasoma ƙara alamar shigowar ƙira, tana ɗaga wayar Dr Sadeeq yace “Gani na’iso ina ƙofar gida!”

“To” tace haɗe da aje wayar, ajiyar zuciya ta sauƙe haɗi da cije lips ɗinta, dama ɗaya kawai take dashi kuma tabbas idan tarasa wannan daman to zaiyi mata wahala tasake samun wani daman.

Hijib ɗinta ta sanya, koda tafito tsakar gida bata taradda Inna ba tana kuma da tabbacin cewa bama ta gidan.

Zaune yake acikin motar tasa, dagani kasan cewa yana cikin damuwa, domin gaba ɗaya har rama tasoma bayyana a jikinsa. Murfin motar tabuɗe tashiga, bakinta ɗauke da sallama, amsa mata sallaman nata yayi haɗe da gyara zamansa yafuskance ta ” Baki taɓa min irin wannan ƙiran ba, naƙosa naji wace maganace zaki faɗamin mai matuƙar mahimmanci haka” gaba ɗaya hankalinsa ya tattara zuwa gareta.

“Dagaske kake Zaka aure ni?” Zahrah tajefo masa tambayar

dabai taɓa zata ba balle tsammani.

Kansa yashiga kaɗawa muryarsa har rawa take yace “Dagaske nake Zahrah, wallahi auren ki nakeso nayi, samunki a matsayin mata shine babban burina a yanzu.” yafaɗi hakan da iya gaskiya’rsa

“So na kakeyi kokuma tausayina?” Zahrah takuma jifansa da wata tambayar.

“Sonki nake Zahrah, inamiki so mai tsanani, wlh inasonki da duka zuciyata!” Dr Sadeeq yabata amsa, cike da kulawa.

“Nayarda na Amince Zan aureka, muyi zama na har abada!” Abun da yafito daga bakin Zahrah kenan bayan tagamajin amsar da take buƙata daga garesa, cikin tsananin mamaki Dr Sadeeq yashiga kallonta, jin sauƙar maganarta yayi tamkar daga sama, kodai kunnuwan sa basu jiye masa dakyau bane?….Kasa motsa koda laɓɓansa yayi balle har yakai ga furta wata kalman, “dagaske ne abun da kunnuwansa suka jiye masa kokuwa mafarki yake?” yafaɗi hakan a cikin zuciyarsa.+

“Kada kayi kokonto kokuma shakka, dagaske nake, na amince da aurenka, amma ina mai roƙon wata alfarma a gareka”….”Dan Allah kada ka wulaƙantani aduk yanda kasameni, kada kuma ka tozartani, nasan cewa tausayina yafi yawa acikin zuciyarka fiye da soyayya ta, saboda haka ina da tabbacin cewa ko gaba zaka iya sake samun wata mace,wacce itace zata kasance zaɓinka, kada haka yasa ka wulaƙantani dan Allah, kada kuma kacutar da rayuwata!” cikin sanyin murya ta ƙare maganarta ta, yayinda hawaye suka shiga fitowa daga cikin idanunta,suna sauƙa akan ƙuncinta.

Jiyayi gaba ɗaya wani irin matsanancin farinciki ya lulluɓesa, gani yake tamkar wasa Zahrah take masa, amma kuma ba’abun mamaki bane, saboda babu abun da yagagari Allah.

“Bansan ta’ina kokuma tayaya zan fara godemiki ba Zahrah, kin gusarmin da duk wata damuwa dake damuna, kinbani farinciki cikin ƴan mintuna ƙalilan, kiyarda dani Zahrah, inamiki Soyayyace ta gaskiya bawai, irin soyayyarnan tako oho ba, zan’iya sadaukar da duk wani abu nawa akanki Zahrah, soyayyar da nake miki, yasanya bana ganin laifi ko kuma aibun duk wani abun da kikamin, burina da fatana shine murayu tare dani dake amatsayin miji da mata, kuma aƙarƙashin inuwa ɗaya, Inasonki Zahrah, kuma namiki alƙawari komai wuya komai tsanani bazan taɓa gujemiki ba, ZANRAYU DAKE Zahrah!!” Dr Sadeeq yafaɗa cike da matsanancin farinciki, jiyake tamkar yajawo Zahrah jikinsa yabata kyakkyawan runguma.

Kuka Zahrah ta fashe dashi, wanda batasan dalilin yinsaba, ita ta amincewa kanta cewa zata auri Dr Sadeeq amma saitakeji tamkar dole tayimawa kanta.

Batayi zato ba saiji tayi Dr Sadeeq yajawota jikinsa haɗe da sanya hannayensa duka biyu ya rungumeta. “Inasonki Zahrah, kuma nayi maki alƙawarin bazantaɓa wulaƙanta ki ba har’abada, kidaina kuka kinji princess ɗina!” yaƙare maganar tasa cikin sigar lallashi.

Daddaɗan ƙamshinsa shiyaso birkita mata tunani don haka tayi saurin janyewa daga jikinsa, tana mai yin ƙasa da kanta.

Sam shikam ma yamanta da cewa hakan da yayi ba’abu bane mai kyau, gaba ɗaya murna yacika masa zuciya.

“Uh sorry baby, gaba ɗaya kece kikamantar dani komai!!” Dr Sadeeq yafaɗi hakan yana mai dafe goshinsa.

Ƙasa ƙasa Zahrah tayi murmushi haɗe da kawar da kanta gefe, hakanan taji wani irin nauyin Dr Sadeeq ɗin yaƙaru acikin zuciyarta, haka kuma yaƙara girma acikin idanunta.

Wani irin kallo Dr Sadeeq yashiga yimawa Zahrah duk dacewa takau da kanta gefe, sai yanzu nema yake ƙara ganin haɗuwarta fiye da da, tabbas da Zahrah bata amince dashi ba to da ya tabka babban rashi, domin kuwa Zahrah tahaɗu, macece ita da kowanni Namiji zaiyi fatan mallaka.

STORY CONTINUES BELOW

Sam batayi tunanin kallonta yake ba, don haka taɗan juyo dan itama ta saci kallonsa, aikuwa karab idanunsu suka sauƙa akan najuna, da sauri Zahrah tayi ƙasa da kanta haɗe da cusa fuskarta tsakan kanun cinyoyinta.

Dariya Dr Sadeeq yayi cike da shauƙi haɗe da shafa sajen dake kwance akan fuskarsa. “Yaushe kika farajin kunyana? lallai zamu ɓata idan harkinajin kunyana!” ya faɗi hakan cike da zolaya.

Ɗan ƙaramin bakinta taturo gaba, haɗe da marairaice fuska cike da shagwaɓa tace “To bakaine kaketa kallo na ba, saikace baka sanni ba!”

Lumshe idanunsa yayi haɗe da buɗesu a lokaci guda, irin wannan salon shagwaɓan ai saita sashi bacci batare da yashiryawa hakan ba,lol.

“Ki faɗamin laifi ne don nakalli abar sona? saidai kiyi haƙuri amma kallonki yanzuma na fara, tunda kinamin kyau, kina kuma burgeni!” yanayin yanda yayi maganar abun burgewa ne, ga macen da tasan daɗin soyayya.

“Nidai kada ka wani ce inada kyau, daɗin bakine kawai nasan kakemin!” still da yanayin shagwaɓa tayi maganan.

Lumshe idanunsa yayi haɗe da fitar da iskan numfashi daga bakinsa, yanayin shagwaɓan Zahrah yafi komai burgesa a tattare da’ita, haka kuma sosai yake sauƙar masa da kasala. “Princess!!” yaƙira sunanta dawani irin murya mai taɓa zuciya.

A hankali ta ɗago idanunta ta kallesa, batare da ta amsa masa ba, ganin idanunsa a rufe, yasanya taɗan tsaya ƙaremawa fuskarsa kallo. “Duk kallona ɗaya da zaki yi bazai tafi a banza ba, sai kin biya kuɗi, gwamma ma kisani!” Dr Sadeeq yafaɗi haka batare da ya buɗe idanunsa ba.

Saurin ɗauke kanta tayi daga kallonsa haɗe da cewa “Niba kallonka nake ba”

“Zaki iya rantsewa cewa bani kike kallo ba?” yaje fo mata tambayar da batayi zato ba.

kanta tashiga girgizawa haɗe da cewa “Ai bankalleka sosai ba, kaɗan nakalleka!”

Dariya Dr Sadeeq yasanya wanda harsaida dimple ɗinsa suka bayyana, yanzu yayarda cewa Zahrah yarinyace ƙarama, kuma zakayi saurin kamata idan tamaka laifi.

Ƙoƙarin buɗe murfin motar Zahrah tasomayi, cikin mamaki Dr yace “ina zaki?”

“Zankoma gida ne, dama magana zan faɗa ma, shiyasa na ƙiraka, kuma nafaɗa ma, inada karatu, gobe muna da test a makaranta” Zahrah tafaɗi hakan dai dai lokacin da ta gama sanya ƙafafunta waje.

“Shikenan to My Princess kikulamin da kanki kinji, inasonki sosai!” Dr Sadeeq yafaɗa cike da kulawa.

Wani irin muguwar kunyarsace takama Zahrah, bashiri ta wuce cikin gida tana mai rufe fuskanta da tafukan hanunta.

Shima Dr ɗin murmushi yayi cike da jindaɗi, lallai idan ya auri Zahrah yakasance mutum mai sa’a, acikin satinnan insha Allah, zai sanarda ƙanin mahaifinsa azo a nemamasa auren Zahrah, a wajen Baffa.

“Aurenka da Salima fa?” Wata zuciyar ta jefo masa wannan tambayar, wani irin bugawa yaji ƙirjinsa yayi, gaba ɗaya amincewa dashi da Zahrah tayi yasanyashi manta halin da yake ciki na batun auren sa da Salima. Jiyayi gaba ɗaya jikinsa yayi sanyi, tabbas akwai ƙalubale a gabansa, domin kuwa yanada tabbacin cewa Hajiyarsa bazata taɓa sanja maganarta ba, gashi har ansoma shirye shiryen bikinsa da Salima, kuma shi a tsarinsa bai sha’awar auren mata biyu, Zahrah ita kaɗai ta’ishesa rayuwa, amma kuma tabbas yasan zai fuskanci matsaloli da yawa daga ƴan uwansa, matuƙar ya jajirce akan cewa Zahrah yakeso ba Salima ba, to amma dole zai jarraba sa’ansa, domin a gaskiya baijin cewa zai’iya haƙura da Zahrah.

Cike da sanyin jiki yayimawa motar tasa key, haɗe da nausawa kan titi.

Suna isa katafaren gidannasu, adai dai parking space motar tasu ta tsaya.

Bawani jinkiri Zaid yabuɗe murfin motar yafito, batare da yatsaya sauraran Mahaifinnasa ba, yanufi ɓangarensa kai tsaye.

STORY CONTINUES BELOW

Komai dake cikin ɓangaren nasa a gyare yake tsab, tamkar akwai wani wanda ke rayuwa a cikinsa, hakan kuma yasamo asaline da yawan gyara part ɗin da akeyi duk bayan kwana biyu, kasancewar Zaid mutum ne da bayason ƙazanta.

Direct bedroom ɗinsa yanufa, yanashiga yasoma rage kayan dake jikinsa, rigan wanka irin na maza mai gashi gashi a jiki yasanya, haɗe da sanya badroom slippers a ƙafafunsa, kai tsaye wajen fridge ɗin dake aje cikin ɗakin yanufa, maltina can yaciro haɗe da ɓalle ɗan ƙarfen da aka rufe bakin can ɗin dashi, yakai bakinsa, tunda yakai maltina can ɗin nan bakinsa bai ɗauke ba harsaida yatabbatar da cewa bakomai ciki ya shanye, cikin dustbin ɗin dake aje a ɗakin ya jefa can ɗin. Bathroom ya wuce haɗe da sakarmawa kansa shower. Wanka yakeyi amma gaba ɗaya tunaninsa baya garesa, yanaga shugar baby’nsa, amatuƙar matse yake da sha’awarta, haryanajin bazai iya daurewa yakai zuwa wani ɗan lokaci mai tsawo batare da’ita ba.

Bayan yafito a wanka yashiga shirya kansa cikin, haɗaɗɗun riga da wando masu kyau da tsadar gaske, gaskia komai na Zaid me kyau ne, domin kuwa kowani kaya yasanya saiya yi kyau, bakuma kayanne yake masa kyauba, shi ɗin kansa ne yake mawa kayan kyau,lol.1

Haɗaɗɗen takalminsa sau ciki ƙiran kamfanin Gucci yasanya, aƙafansa, bayan ya ɗaura tsadadden agogon nan na Rolex a hanunsa mai kyau da burgewa. Daddaɗan ƙamshi ne kawai ke fita daga jikin shi, ƙamshine mai wahalar mantawa.

Black facing cap, yasanya akansa, domin kuwa yanayin garin ana ɗan busa sanyi, duk dakuwa cewa daga cikin sanyin yafito.

Wayarsa yaɗauka haɗe da car key ɗinsa, kai tsaye yafice daga cikin ɗakinnasa. Ɓangaren Mom ɗinsa yanufa. Hajiya Safara’u ne tsaye a gaban ƙatoton teburin cin abinci, yayinda Alhaji Ma’aruf ke zaune tana serving ɗinsa, batasan da shigowarsa ba saiji tayi ya rungumeta ta baya haɗe da ɗaura kansa akan kafaɗarta, cike da soyayyar mahaifiyarta sa yace “Barka da gida Momy!”

Cike da tsananin farinciki itama ta rungumesa haɗe da basa sumba a kan kumatunsa, “Barkanka da dawowa my son, ya gajiyar hanyar?”

“Alhmdlh!” Zaid yafaɗa a taƙaice, bayan ya janye jikinsa daga na mahaifiyartasa. Ƙoƙarin juyawa yakeyi, Mom tace “Inakuma zaka my son ba abinci kazo ciba?” cike da kulawa ta tambayesa.

Ɗan ɓata fuska Zaid yayi haɗe da cewa “Banajin yunwa Mom, idan nadawo zanci!” baijira jin maizasu ceba yasakai yafice daga cikin falon.

Da kallo kawai Mom tabisa har yafice, fuskarta ɗauke da damuwa, itakam ta rasa wani irin haline da Zaid, sam ba’a iya gane gabansa da bayansa.

“Miye abun shiga damuwa Hajiya Safara’u? zuwa yanzu yakamata ace duk wani hali na yaronnan Zaid kin gama saninsa!” Alhaji Ma’aruf yafaɗi hakan cike da nuna kulawa ga matar tasa.

“Nasan halinsa Alhaji, amma kuma ace mutum shi baya taɓa sanjawa, ko da yaushe fa Zaid bayason zama a cikin mu, sannan kuma sam baya sakewa damu!” Mom tafaɗi hakan cike da damuwa.

“Zauna muci abincin mu, aishi ba ƙaramin yaro bane, yasan me yakeyi!” Alhaji Ma’aruf yafaɗi hakan yana mai kama hanun Mom yazaunar da’ita a kusa dashi.

Zaid kuwa yana fita daga ɓangaren mahaifiyartasa, kai tsaye wajen motarsa yanufa, koda driver yanemi da yabarsa ya tuƙasa, ɗaga masa hanu yayi alamar baya buƙata, shida kansa yayimawa motar key, ya harbata zuwa kan titi.

Tafiya yake cikin nutsuwa yayinda airpiece ke saƙale a kunnuwansa, wayarsa ce tasoma ƙara alamar shigowar ƙira, ganin cewa babban manager’n company’nsa dake nan gida Nigeria ne ke ƙiransa yasanya shi ɗaga ƙiran. Banji mai Manager’n nasa yace masa ba, sai gani nayi ya’aje wayan, haɗe da buga dogon tsaki, lokaci ɗaya yakarkata akalar motar tasa zuwa wata hanya daban saɓanin hanayar daya nufa, wanda zai sadasa da unguwar su Zahrah.

Dr Sadeeq kuwa yana barin unguwar su Zahrah kaitsaye gidansu yanufa, acewarsa gwamma yayi maganin matsalarsa tunkafun tayi nisa.

Usaina mai aikin ɓangaren Hajiyarsa yasanya tane ma masa iso awajen Hajiyar tasa, domin kuwa bai isketa a falo ba.

Da sallama yashiga cikin ɗakin Hajiyar tasa, fuskarta ɗauke da fari’a ta amsa masa sallaman da yakeyi. Zaune take akan gado, yayinda take duba wasu kayayyaki dake zube a gabanta.

“Barka da huwatawa Hajiya!” yafaɗa cike da ladabi.

“Yauwa barkanka, kamar kuwa kasan ina nemanka, wai me kake nufi da auren nan ne Sadeeq? har yanzufa banga kana wani cuku cuku ba, kayan lefe ma saini kabarmawa ɗawainiyar haɗasu, gashi kuma Salima tacemin tunda kaje sau ɗaya baka sake zuwa ba, mai ke damunka ne wai?” Hajiya tatambayesa cike da kulawa.

Kansa yashiga sosawa haɗe da sake yin ƙasa da kansa, “Am…dama Am….” “Dakata banson wani kwana kwana, kafaɗi abunda zaka faɗa kai tsaye kawai” Hajiya ta katsesa daga kame kamen maganan dayake ƙoƙarin yi mata.

“Hajiya kamar dai yanda na faɗamiki ne, wallahi Hajiya dagaske nake, yanzu nasamu wacce nakeso kuma idan harkin yarda aurenmu bazai wuce nan da Sati uku ba, kamar yanda kikeso!” yafaɗi hakan cike da ladabi.

Sororo haka Hajiya ta tsaya tana kallonsa, “anya kuwa Sadeeq yana lafiya? ” tatambayi kanta.

“Inagadai bakasan mekake cewa ba Sadeeq, wato nikakeson watsamawa ƙasa a cikin idanu ko, ya yi maka kyau, to inaso kabuɗe kunnuwanka da kyau ka saurareni, wallahi ko da wasa kakuma zuwamin da irin wannan zancen saina ɓata maka rai, nagama baka duk wata dama dazan baka, bakuma zan sake baka wata daman ba, tashi kabani waje, tunda nalura kai baka da tunani!” Hajiya ta ƙare maganan cikin faɗa.

Cikin rashin kuzari haɗe da sanyayewar guiwa Dr Sadeeq yamiƙe daga gaban mahaifiyartasa, haɗe da nufar ƙofar fita daga cikin ɗakin,

Saida yakai ɓaƙin ƙofar fita ckafun yatsaya cak, haɗe da juyo da kallonsa ga Hajiyar tasa cikin murya mai rauni yace “Hajiya dan Allah..”

“Fita kabani waje nace!!” Hajiya takuma faɗa cikin ɓacin rai tanamai yi masa nuni da ƙofar fita daga ɗakin…Cikin sanyin jiki Dr Sadeeq yafita daga cikin ɗakin mahaifiyarta sa. Gaba ɗaya jiyayi zuciyarsa ta cika da ƙunci. Yana isa ɓangarensa ya zube akan ɗaya daga cikin kujerun falonnasa, “yanzu wazai je yasamu da wannan matsalar? tabbas yasan Hajiyarsa mutum ce mai kafiya, idan tace eh zai yi wuya ta dawo tace a’a”

hanunsa yasanya cikin sumar dake kwance akansa haɗe da yamutsa ta, sunan Aunty Raliya ce yafaɗo masa arai, tabbas ita kaɗaice ƴar uwarsa da zai kai mata matsalansa har ma ta tayasa magancewa, sai dai kuma yanatunanin itama ra’ayinta ɗayane da Hajiya, amma yasan idan yayi mata kyakkyawan bayani zata fahimcesa, zumbur yamiƙe daga zaunen dayake.

Ko bedroom baishiga ba yakuma ficewa daga cikin falon, mota ya koma, haɗe da kunnata, mai gadi ne ya wangale masa gate ɗin gidan yafice.

Hajiya najin ƙarar ficewar motarsa daga cikin gidan ta sauƙe ajiyar zuciya.

“Gaba ɗaya tunaninta ya kulle, batasan wani irin abu Sadeeq keshirin shigo mata dashi cikin gida ba, kusan sau uku kenan tana bashi dama, akan yafito da matar aure, amma dazaran lokacin da ta ibar masa yacika, sai ya farayi mata kame kame, yanzu da tagaji da sakarcinsa ta zaɓa masa mata, sai yake nema yawatsa mata ƙasa a idanu, bakuma zata lamunci hakanba.

Direct Dr Sadeeq gidan Aunty Raliya yanufa, domin baida wata ƴar uwa da ta wuce ta a duniyar nan.

Yanashiga gidan tunbai gama fitowa daga cikin motarsa ba, su Meenal da Affan ƴaƴan Aunty Raliya, suka rugo da gudu zuwa garesa, dama wasan ball suke a farfajiyan gidan nasu, hakan yasa duk wanda yashigo da kuma wanda zaifita zasu gansa.

Rungumesu yayi a jikinsa, haɗe da shafa kawunansu, “Oyoyo babies ɗina, ashe girma yazo muku, har wasan ball kukeyi!” yafaɗi hakan cike da nishaɗi.

“Eh Uncle ai harma nafita iyawa!” Affan yafaɗi haka cike da zumuɗi.

“Ƙaryayake Uncle baifini iyawa ba” Meenal tafaɗi hakan tana mai kama ƙugu, alaman ƙarya Affan ɗin yakeyi.

Murmushi kawai Dr yayi haɗe da sake shafa kansu, “kuyi wasa da kyau, idan nafito zan baku alewa!” yafaɗa yana mai nufar kofar da zata sadashi da babban falon gidan. Yayinda yabar su meenal sunata tsallen murna saboda yace zai basu alawa.

Da sallama ɗauke a bakinsa yashiga cikin falon.

Aunty Raliya dake zaune tana kallon tv, ta amsa amsa masa sallamar tasa, fuskarta ɗauke da fari’a, haɗe da yi masa iso.

Ƙarasowa yayi yazauna akan kujera, haɗe da sauƙe ajiyar zuciya, gaba ɗaya a gajiye yakejinsa, domin tun safe yau baisamu nutsuwa ya huta ba.

Aunty Raliya da kanta, ta jere masa kayan fruit da juice agabansa, cikin tsokana tace dashi

“Ango kasha ƙamshi, duk gajiyar shirye shiryen bikinne haka?”

Ɗan ɓata fuska yayi haɗe da ɗaukan apple ƙwaya ɗaya ya kai bakinsa.

“Ango labari ya sauya salo” yafaɗi hakan bayan ya cinye gutsuren apple ɗin dake bakinsa.

Cikin mamaki Aunty Raliya tace “bangane ba mekake nufi?”

STORY CONTINUES BELOW

Ajiyar zuciya yasauƙe haɗe da gyara zamansa.

“Akwai matsala Aunty!” yafaɗi hakan lokacin da gaba ɗaya yanayin fuskarsa ya sauya.

“Matsala! wace irin matsala Uncle?” Aunty Raliya tatambaya cike da ɗaurewar kai.

“Akwai wacce nakeso na aura, yarinyar tana matuƙar buƙatar taimakona, nayi ƙoƙarin na fahimtar da Hajiya hakan, amma taƙi saurarata, yanzu haka daga gida nake, nasoma yi mata bayani, tace natashi na bata waje, gaba ɗaya kaina yakulle bansan yazanyiba Aunty Raliya!”

Ya faɗi haka cikin damuwa.

Ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya Aunty Raliya ta sauƙe “Turƙashi, lallai kuwa kazo da babbar magana, amma maiyasa tunda baka bayyana wacce kake so ɗinba, sai yanzu da komai yariga da yayi nisa? kafasan Hajiya da kafiya balallai ne ta fahimce ka ba, shawarata a gareka shine, kamabar wannan zancen, domin balallai kasamu abun da kakeso ba!” Aunty Raliya tafaɗi hakan da’iyaka gaskiyarta.

Cike da rauni Dr Sadeeq ya kalli Yayartasa. “Dan Allah taimakona zakiyi Aunty, kije kisameta kibata baki, wallahi inamatuƙar son Zahrah, sannan kuma yarinyar tana buƙatar kulawata, nikaɗai nasan matsalarta, please Aunty!!” yafaɗi haka yana me marairaice fuska, hadda haɗa hannuwansa biyu ga Aunty Raliya’n alamar roƙo.

Kallon mamaki Aunty Raliya tashiga binsa dashi, “wai yaushe Sadeeq yazama bawan soyayya ne?” ta tambayi kanta.

“Abune me matuƙar wuya amincewar Hajiya, amma zan jarraba, saidai kafun naje gareta, dole sainasan wacece yarinyar kuma su waye iyayenta, saboda kada aje Hajiya ta amince, akuma zo asamu wani mummunan labari akan ta”

Wani irin bugawa ƙirjin Dr Sadeeq yayi, domin kuwa anzo wajen, lallai baizama dole kowa yafahimcesa ba domin sanin sirrin Zahrah, zai iya sanyawa kowama yaƙi amincewa da aurensa da’ita, wanda shi a wajensa baiga ta’inda aurensu zai zamanto rashin dacewa ba, amma ba’a ƴar ɓoye a harkan aure, domin koda anɓoye tofa sai ya bayyana.

“Sunanta Zahrah, a unguwar Maraba take, sannan kuma marainiyace bata da uwa bata da uba, baffanta ne yake riƙonta, yarinyar tana da hankali sosai Aunty, sannan kuma tana da tarbiya, bata da wani aibu ko abun kushewa a tattare da’ita, saidai kuma…” kasa ƙarasa maganar yayi, domin kuwa baisan yanda yayartasa zata ɗauki maganar ba.

“Umm inajinka saidai kuma me?” Aunty Raliya tatambayesa cike da zaƙuwa.

“Ƙaddarace kuma tana kan kowa, haka kuma babu wanda ya’isa ya tsallake mata idan har tafaɗo kansa, akwai wani tsohon saurayinta da ya yaudareta yayi mata fyaɗe, watannin baya da suka wuce, wanda hakanne ma sanadin haɗuwata da’ita, amma ni banɗauki hakan amatsayin wani abu ba dazai hanani aurenta, kasancewar kowa da’irin tasa ƙaddaran a rayuwa!”

Sororo haka Aunty Raliya ta hangame ido da baki tana kallon Dr Sadeeq har ya idar da zancensa mai kama da tatsuniya.

Salati Aunty Raliya tasanya cike da tsantsar mamaki haɗi da al’ajabi, lallai Sadeeq baisan meyake faɗa ba.

“Fyaɗe! fyaɗe fa kace Sadeeq, anya kuwa kansan mekake faɗa? yanzu kai saboda rashin hankali irin naka, karasa wacce zaka gani kace kanaso, sai yarinyar da taraba budurcinta wa ƙattin maza, yarinyar da wani yagama sanin sirrinta!” Aunty Raliya ta faɗi haka cike da ɓacin rai.

Saurin rumtse idanunsa yayi domin jin magananganun Aunty Raliya’n yake tamkar sauƙan aradu, a kunnuwansa.

Cigaba tayi da cewa ” Lallai yanzu na tabbatar dacewa ba lafiyanka lau ba, taya kana cikekken namiji mai hankali da kuma kamala, karasa wacce zaka aminta da ta zamo uwar ƴaƴanka sai wacce wani ƙato ya haiƙemawa, yazama dole kasanja tunani Sadeeq, wannan ma ai zancen banzane, to gwarama kasani wannan yarinyar ba zaka taɓa aurenta ba matuƙar mu jininka ne!” Aunty Raliya ta ƙare maganar cikin hargowa.

STORY CONTINUES BELOW

“Haba Aunty maikikeson cewa ne? dan Allah kada kimin haka, nafaɗamiki matsalatane don bani da wacce tafiyemin ke, dama nasan za’a samu rashin fahimta, domin zakuga kamar Zahrah ba kamemmiyar mace bace, alhalin kuma bahaka take ba, tsautsayine yafaɗa mata, amma ni nayarda na amince zan aureta a haka, kada fa kimanta duk wanda yarufa asirin wani to Allah zai rufa masa nasa asirin, kitaimaka mu inganta rayuwar Zahrah, kitaimaka mucireta daga ƙunci, musanyata cikin farinciki!” yafaɗi haka cike da rauni.

Wani irin kallo Aunty Raliya tashiga yimasa, lallai Sadeeq baya cikin hankalinsa.

Murmushi mai ciwo Aunty Raliya tayi haɗe da cize laɓɓanta cikin takaici ta ce dashi.

“Kuskurenka na farko a rayuwa shine yarda dakayi cewa da gaske fyaɗe aka mata, shin ka ko san ƴan matan yanzu kuwa Sadeeq? to bari kaji wani abu, a shegen son kuɗi irin na ƴan matan yanzu, su da kansu suke saida budurcinsu ga wani daban, idan suka samu makahon da’idanunsa ya rufe ruf har yazo musu da zancen aure, sai su taƙarƙare su zabgamasa ƙarya kan cewa fyaɗe akamusu, bayan suda kansu suka kasa budurcin nasu a faifayi suka kai tallanshi kasuwa, ni ƴar uwarka ce ta jini bazan taɓa son wani abun da zai cutar da kai ba, saboda haka tun muna mubiyu nidakai, mubunne maganarnan anan, tun kafun ma yaje ga kunnen Hajiya, domin kasan idan taji cewa wacce kake shirin kawo mata ita amatsayin suruka, ba mutumiyar ƙwarai bace to zatayi mugun saɓa maka!!”

Take idanun Dr Sadeeq suka kaɗa sukayi ja, bakomaine ya sanya hakan ba face irin munanan kalaman da Aunty Raliya ta dinga jifan Zahrah dashi, tabbas yasan cewa mafi ƴawancin ƴan matan yanzu suna sayarda budurcinsu saboda abun duniya, amma banda Zahrah’nsa aciki, yasan Zahrah macece mai kamun kai, kuma duk wanda yayarda da ƙaddara dole ne ya tausayawa mata masu tsintar kansu a irin halin da Zahrah ta tsinci kanta a ciki.

“Ita bakamar yanda kike tunani bane Aunty Raliya, ki saurareni saina baki gaba ɗaya labarinta, marainiyace ta cancanci a tausaya mata, nima Namiji na tausaya mata balle ke mace, kuma dama ance ciwon ƴa mace na ƴa mace ne!” Dr yafaɗi hakan cike da son ganar da Yayarta sa, cewa ba bu wani aibu agame da aurensa da Zahrah.

Gaba ɗaya duk iya abun da yasani agame da Zahrah, bai ɓoye mata ba, sai da yasanar mata, atunaninsa hakan zai sanya Aunty Raliya ta ƙaunaci Zahrah, amma me sai gani yayi tana taɓe baki haɗe da kawar da kanta gefe alamar ma ta’inda maganar tasa take shiga tanan take fita.

Yana idar da zancen ta dubeshi haɗe da ɓata fuska tace “Kagama? kai a tunaninka zaka bani wata hujja dazata sanya naga dacewar aurenka da’ita ne, hmm niba yarinya bace Sadeeq, yakuma zama dole kasanja tunani, kakuma manta da maganar wata wai ita Zahrah, idan kuma kafison kafuskanci ɓacin rai daga wajen Hajiya, to kaci gaba da zama akan bakan ka harmaganan takai ga kunnen Hajiya!!” tanakaiwa nan a zancenta ta miƙe fuuu tawuce cikin ɗakinta tabarshi zaune.

Hannayensa yasanya duka biyu ya tallafi kansa, lallai akwai babban ƙalubale a gareshi, agun Aunty Raliya ma kaɗai ga’irin ɓacin ran daya fuskanta, inaga Hajiyarsa kuma.?

Miƙewa yayi daga zaunen da yake tamkar wanda ƙwai ya fashewa a jiki haka yake tafiya, gaba ɗaya ƙwaƙwalwarsa tasake dagulewa, yazone don yasamu mafita amma sai gashi abubuwa sun sake dagulewa.

Da ƙyar yake iya tuƙa motar tasa. Haka yanufi gida cikin rashin kuzari, sai dai fa haryanzu bai saduda da maganar Auren Zahrah ba, yanaji ajikinsa cewa Zahrah zata zamo matarsa Insha Allah.

Gagarumin meeting su ZAID suka gudanar mai zafi, a babban hotel ɗin nan wato SHERATON, sosai aka samu riba dakuma ƙarin buɗi a ɗaya daga cikin company’n nasa da suke Nigeria, hakan yasa yaƙarawa gaba ɗaƴa ma’akatansa albashi.

Sunjima suna meeting ɗin dan haka amatuƙar gajiye suka fito dukansu, lokacin har dare yasoma rufawa. Kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa, yayi yaga karfe 6 daidai na yammaci, ɗan ƙaramin tsuka yayi haɗe da soma yunƙurin cire rigan suit ɗin jikinsa wada yaɗaura akan kayan dake jikinsa,

saboda gajiyan da yayi bai iya tuƙi da kansa ba, sai driver’nsa yaƙira yayi driving ɗinsa.

STORY CONTINUES BELOW

Gyara kwanciyansa yayi ajikin kujeran motar haɗe da lumshe idanunsa, wani irin sarawa kansa keyi masa, daga wani ɓangare na zuciyarsa kuwa sosai meeting ɗinnan ya ɓata masa rai, domin kuwa ya hanasa ƙarasawa ga ZAHRAH’nsa, wacce saboda itane ma gaba ki ɗaya yadawo ƙasar, yayi missing din Zahrah sosai, yayi missing kyakkyawan murmushinta haɗi da kyawawan idanunta, yayi missing kallon kyawawan laɓɓanta masu daɗin tsotso. Gaskiya dole ya killace Zahrah tayanda zata zama nasa shi kaɗai.

Suna isa gida kai tsaye ɓangarensa ya wuce, a gajiye yashiga bathroom yayi wanka, koda yafito a wankan, direct masallaci ya wuce donyin sallan magriba. Sai da yajira aka yi sallan isha tare dashi a masallaci, kafun ya siɗaɗo yadawo ɗaki ya kwanta, yau ko abar ƙaunar tasa wato wine baisha ba bacci ɓarawo yayi gaba dashi.

Zahrah ce kwance akan katifarta sai juyi take ta kasa bacci, gaba ɗaya kanta ya kulle zuciyarta cike take da tarin tunanuka kala kala. “Anya banyi sauri kokuma gangancin yarda da kuma amincewa da soyayyar Dr da nayi ba?” zuciyarta ta tambayeta.

Zumbur haka ta miƙe zaune, haɗe da soma girgiza kanta

” A’a banyi kuskure ba, tabbas bayan shi babu wani maiso da nuna tausayi gareni!” tabawa kanta amsa a bayyane.

Wayartace takawo haske alamar shigowar ƙira, kasancewar ta sanya wayar a silent hakan yasanya wayar batayi ƙaraba.

“Doctor” shine sunan dake yawo akan screen ɗin wayar.

“Shima baiyi bacci ba kenan” tafaɗi hakan a bayyane.

Saida wayar ta kusa katsewa kafun Zahrah ta ɗaga ƙiran haɗe da kara wayan akan kunnenta.

“My princess bakiyi bacci ba kenan?” Dr Sadeeq yatambayeta cikin muryarsa mai ɗauke da damuwa.

“Um, kaifa me yahanaka bacci” Zahrah itama tatambayeshi.

“So da ƙauna dakuma tunaninki susuka hanani bacci! kefa mai yahanaki bacci?” yatambaya cike da son jin amsar da zata fito daga bakinta, “Allah yasa itama tunani na ne ya hanata bacci” yafaɗi hakan a zuciyarsa.

Kunyane yaɗan kamata amma sai ta basar haɗe da sauƙe ajiyar zuciya “A’a nikam karatu nake, shiyasanya banyi bacci ba, amma yanzuma zanyi baccin.” tafaɗi hakan a taƙaice.

Ko kaɗan baiji daɗin amsar da ta basa ba, amma yasan cewa wataran dole zatayi tunaninsa kamar yanda shima yake nata tunanin.

“Naji daɗi sosai da kika amince dani Zahrah na! hakan yasa na ƙara jin sonki sosai da sosai a cikin zuciyata!!” cikin shauƙin so yafaɗi maganar.

“Umm banji mai ka faɗa ba!” Zahrah tafaɗi hakan cikin wani irin salo wanda batasan ma tayi shi ba, duk da kuwa cewa taji mai yace, iskancine kawai irin nata.

Lumshe idanunsa yayi da suka soma sauya kala, sosai yanayin yanda tayi maganar ya sauƙar masa da kasala.

“Bacci kika farane Zahrah na?” yatambayeta cike da kulawa, domin kuwa shi anasa zaton dagaske batajisa ba.

“Um!” Zahrah ta basa amsa a taƙaice cikin ƙasa ƙasa da murya, domin kuwa tanaso yayarda cewa baccin takeji, saboda har yanzu, bata gama amanna dacewa sonsa take ba, kuma koda za’a kasheta tasan cewa ba sonsa take ba, kawai dai ta tsinci kantane da amince masa, amma batun soyayya kam babu shi.

“To kiyi bacci mai daɗi kinji My princess, inasonki sosai, ki kulamin da kanki, banson koda ɗigon wani a bune ya raɓe ki!” Dr ya faɗi haka cikin shauƙin SO (Sisters kujisafa su likita ashe an iya kalaman love, lol.)

“Uhumm sai da safe.” Zahrah tafaɗa a taƙaice bayan ta zare wayar daga kunnenta.

“Gaskiya abune mai matuƙar wahala koyawa zuciya So’n abun da bata so, ya Allah kataimakeni, haƙiƙa banajin tsanarsa haka kuma banajin soyayyarsa a zuciyata, sannan kuma inaji ajikina cewa zan’iya rayuwa dashi, to me hakan ke nufi, ba so bane kuma ba ƙi bane to menene?” tatambayi kanta a bayya ne, saidai kuma bata da amsar da zata bawa kanta.

Komawa tayi ta kwanta bayan ta kashe wayarta ta gaba ɗaya.

Cike da saƙe saƙe bacci yayi awungaba da ita.

Ɓangaren Dr Sadeeq ma, sai da yajima yana saƙawa da kuncewa, ba abun da yake ɗaure masa kai, kamar yanda ya kasa fahimtar cewa Zahrah, na son sane ko bata sonsa. da ƙyar dai shima bacci ya’iya ɗaukarsa.

Washe Gari.

Yau tun saven thirty suke da lecture, dan haka da wuri tasoma shirya kanta, sosai tayi kyau cikin shigar jar abaya haɗe da jan hijab ɗin dake jikinta, hand bag ɗinta ta rayata a bisa kafaɗanta. Kana tafice zuwa tsakar gida. Zama tayi akan taburma haɗe da jawo farantin ƙosai da kuma kofin kunun da Inna ta aje mata tasoma sha. Baffa ne yafito daga cikin ɗakin sa yanaganin Zahrah yace

“Yauwa kinfito ko, tun ɗazu kuwa likita yake jiranki a waje”

“Eh Baffa nafito” tabashi amsa cike da mamakin jin cewa wai Dr yajima da zuwa, yanama jiranta a waje, amma kuma bai ƙira ta a waya yasanar mata ba.

Aƙagauce taci abincin kasancewar har bakwai tayi.

Tana fitowa yasakar mata kyakkyawan murmushi, itama murmushin ta sakarmasa bayan tagama ƙaremawa kwalliyarsa ta yau kallo.

“Kinyi kyau my princess!” yafaɗa cike da nishaɗi, domin kuwa sosai tayi masa kyau, jan kayan da tasa ya karɓi kalan fatarta.

“Kaima haka” tabashi amsa a taƙaice.

Murmushi yakumayi haɗe da buɗe mata murfin motar nuni yayi mata da hanunsa alamar tashiga, wani murmushi mai tsayawa a zuciya tayi masa haɗe da shigewa cikin motar tayi mawa kanta mazauni.

Tafe suke suna hira cike da nishaɗi, wanda gaba ɗaya yawan hiran Dr ne maiyi mata shi.

A haka har suka iso cikin makarantar, ƙoƙarin buɗe murfin motar ta soma yi.

“Ya haka? baki sallameni ba fa, kike ƙoƙarin tafiya” Dr Sadeeq yafaɗi hakan cikin sigar zolaya.

Murmushi Zahrah tayi masa haɗe da yin fari da’idanunta “Bangane ba” tafaɗi haka cikin salo.

Lumshe idanunsa yayi haɗe da sanya hanu yashafi sajensa, “Inanufin bakice kina sona ba”

Dariya haɗe da kunyane suka kama Zahrah sai kawai ta buɗe murfin motar tayi ficewarta, domin kuwa bazata iya masa abun da yakeso ba.

Saida yaga shigewarta cikin hall kafun yaɗauke idanunsa daga kanta, yanason mace mai kunya gashi Zahrah takasance me kunya. Cike da tarin tunaninta yabar cikin makarantar.

Ita da Husnah suna fitowa a lecture sukayi mawa kansu ma zauni a inda suka saba zama ko da yaushe.

Cike da tsananin farinciki Husnah tace “Naji daɗi ƙwarai Zahrah da kika amincewa Dr, wallahi gayen ya haɗu da yawa ƙawata, tabbas idan kika auresa kin more don nasan za kisha madaran soyayya!”

Hararan wasa Zahrah ta wurgamawa Husnah, cike da son basar da zancen tashiga shafa cikin ta ” Nifa yunwa nakeji” tafaɗa tana mai turo baki gaba.

“Kada dai kice zakimin sakalci, domin niba Doctor bane” Husnah tafaɗa cikin tsokana. dukan wasa Zahrah takai mawa Husnah, da sauri Husnah ta kauce.

Cafeteria suka nufa acan suka cika cikinsu, daganan suka sake shiga cikin wani lecture’n.

Jikin wata bishiya dake kusa da ƙofar fita daga makarantar yayi parking motar sa, gyara zama yayi haɗe da duba agogon dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa. Kallonsa ya mayar zuwa bakin tangamemen gate ɗin makarantar tasu, hakanan yakejin ba zai iya fuskantar ta gaba da gaba ba.

Amatuƙar gajiye su Zahrah suka fito a lecture. Tare suke tafe ita da Husnah, domin yau zataimawa Husnah rakiya ne zuwa super market. kai tsaye suka nufi ƙofar fita daga makarantar kasancewa driver’n gidansu Husnah najiransu a waje.

Wani irin faɗuwar gaba taji, ya risketa adai dai lokacin da ta fito daga cikin makarantar.

Daga ɓanagaren Zaid kuwa zuciyarsa ne tashiga dukan uku uku, alokacin da’idanunsa suka sauƙa akan Zahrah, hanu yasa ya murje idanunsa domin tabbatarwa da kansa cewa ita ɗince kokuwa gizo idanunsa suke masa.

Tabbas itaɗince Zahrah’n sane, har yanzu tananan da kyawunta, dakuma surarta mai ɗaukar hankalin duk wani lafiyayyen ɗa Namiji.

“ZAHRAH!” yaƙira sunanta a bayyane, duk da kuwa yasan cewa bazata ji sa ba. dai dai lokacin daya soma yunƙurin buɗe murfin motarsa don yaƙarasa gareta, dai dai lokacin itakuma ta shige cikin mota tare da Husnah.Cikin Hanzari ya buɗe murfin motar tasa ya fito, sai dai baikai ga ƙarasawa garesu ba, motar su ta gangara kan titi haɗe da ɗaukar hanya.+

Hannayensa duka biyu yasanya ya kama ƙugunsa, haɗe da furzar da iskan numfashi ta bakinsa, sam baiso haka ba, amma babu yanda ya’iya dole binsu zaiyi.

Kallonsa yamaida ga sauran cincirindon ɗaliban da suke tsaye a bakin gate ɗin makarantar.

Gani yayi gaba ɗaya sun saki baki da hanci suna kallonsa, sai kace wanda suka ga baƙon halitta, bama kamar ƴan matan dake tsaye a wajen.

Tsuka mai sauti yayi haɗe da komawa cikin motarsa, da gudun gaske ya cilla motar tasa kan titi, haɗe da rufa mawa motar su Zahrah baya.

“Yadai, naga lokaci ɗaya duk kinyi wata iri dake?” Husnah tatambayi Zahrah wacce tazama silently lokaci ɗaya.

A jiyar zuciya ta sauƙe haɗe da maida kallonta ga Husnah ” Faɗuwar gaba nakeji Husnah, ban kuma san dalilin hakan ba” Zahrah ta faɗi haka cikin damuwa.

“To fa, Allah dai ya tsare, amma ki yawanta addu’a, domin hakanne zaisa koma mene ne yazo da sauƙi” inji cewar Husnah.

“Insha Allah!” Zahrah tafaɗi hakan tana mai kwantar da kanta a jikin kujeran motar, tanajin Husnah tace da Driver’n ya karkata akalar motar, ta sanja shawara shoprite kawai zasuje, bamusu kuwa ya sanja hanya zuwa Shoprite ɗin. Itadai Zahrah batace dasu komai ba.

Basu wani jima suna tafiya ba, suka iso tangamemen Shoprite ɗin. “Muje ko” Husnah tace da Zahrah tana mai ƙoƙarin buɗe murfin motar.

Cikin sanyin jiki Zahrah, tafito daga cikin motar suka nufi cikin shoprite ɗin.

Basket biyu Husnah ta ɗauka nata ɗaya na Zahrah ma ɗaya, acewarta Zahrah ta zaɓi duk wani abun da take so, sam bahaka Zahrah tasoba amma babu yanda ta’iya, domin kuwa Husnah kafiya gareta, idan tace kayi abu tofa wai dole sai kayi.

Kayan shafa suka soma ɗauka, kafun suka garzaya zuwa kan su jaka da takalma ƴan yayi, basu tsaya anan ba hadda kayan ciye ciye sai da suka ɗauka.

Cike da gajiyawa Zahrah ke tura Basket ɗin da kayanta ke ciki, ita mamaki ma take yanda Husnah tasa suka jidi kaya mai yawa har haka, amma idan tayi la’akari da irin gata da kuma kuɗin da mahaifin Husnah ke dashi, to sai tagama ba wani abun mamaki bane, kuma kuɗin kayan bazai mawa Husnah wahalar biya ba, domin kuwa anshagwaɓata sosai agida.

Daki daki aka lissafa kayan nasu, inda Zahrah ta ɗauki kayan dubu ishirin Husnah kuwa na dubu ishirin da biyar ta eba, ƙoƙarin miƙa wa Cashier ATM card ɗin dake hanunta Husnah ta soma yi. Amma sai Cashier’n yayi murmushi haɗe da cewa

“Ai Hajiya ba’a buƙatar kuɗin ku, domin kuwa an riga da an biya muku, tunkafun ku kammala sayayyan, sannan wanda yabiya muku yace idan ma kuna da buƙatar ƙari, to kukoma ku ƙara, duk shi zai biya kuɗin”

Cike da mamaki Zahrah da Husnah suka shiga kallon juna.

“Anbiyamana fa kace Cashier? shin ka kosan me kake cewa?” Husnah tatambayeshi cike da mamaki.

STORY CONTINUES BELOW

“Ƙwarai kuwa nasan me nake cewa, kudai ku ɗau kayanku kawai kuje, sannan ku gode mawa Allah, don shi yaje fo muku tsuntsu daga sama gasashshe ” Cashier’n nan yafaɗi haka yana mai washe baki, kasan cewar shima anbarmasa kyautan ragowan canjin su.

Mamakine ya lulluɓe su Zahrah domin su a iyaka sanin su basu da wani wanda zai biya musu kuɗin siyayyan da sukayi, domin kuwa basu zo da kowa ba banda driver, inakuwa driver zaisamu maƙudan kuɗaɗe irin haka har ya biya musu kuɗin siyayya alhali shima yana fama da kansa.

“Kozaka iya faɗamana wanda ya biya mana kuɗin ?” Husnah ta tambaya.

“A gaskia bansan saba, sai dai da duk kan alamu irin larabawan nan ne da suke zuwa Nigeria lokaci zuwa lokaci” Cashier ɗin nan yafaɗa musu haka, domin shi a yanda yafahimta, da dukkan alamu wanda.yabiya musu kuɗin baiyi zubi da ƴan nan gida Nigeria ba, duk da kuwa cewa muma muna da kyawawan maza amma kuma kyawun wani ya ɗare na wani.

Idanu Zahrah da Husnah suka zaro atare, sakamakon jin abun da Cashier yace.

“Balarabe fa kace?” Husnah ta sake tambaya cike da mamaki.

“Eh Balarabe, kece Zahrah ko?” Cashier’n nan ya tambaya yana mai nuna Zahrah da hanunsa.

“Ya’akayi kasan sunana ?” Zahrah ta tambayesa cike da mamaki.

Murmushi kawai yayi haɗe da miƙa mata wata farar takarda.

“Ungo yace inbaki”

Cikin tsoro Zahrah ta karɓi takardan da Cashier ke miƙo mata, haɗe da buɗewa.

_”Kiɗauki duk wani abun da kikeso MY ZAHRAH! ban damuba koda duka Shoprite ɗin zaki ce kinaso, zan iya mallaka miki kome kikeso a duniyar nan, ko da kuwa dukiyata zata ƙare”_ abun da aka rubuta a jikin takardan kenan.

Wani irin bugawa Zahrah taji ƙirjinta yayi, “To waye?” tatambayi kanta a fili.

“Yadai me aka rubuta acikin takarda’n?” Husnah ta tambayi Zahrah cike da zaƙuwa.

Bata takarda’n Zahrah tayi domin batasan me zatace da’ita ba.

Husnah tana gama karanta takarda’n tasaki murmushi haɗe da kallon Cashier’n nan daya zura musu idanu… “Mungode sosai, idan ka haɗu da wanda yabiyamana kuɗin, ka isar mana da saƙon godiya” daga haka ta kama hanun Zahrah suka fice daga cikin Shoprite ɗin, bayan sun ɗau ledodin siyayyarsu.

“Saida sukazo bakin mota kafun Husnah ta saki hanun Zahrah, still fuskarta ɗauke da murmushi tace “Mekika fahimta game da wannan takardan, da kuma biya mana kuɗin sayayya da akayi?”

Cikin ɗaurewar kai Zahrah tace “Ni ban fahimci komai ba, sai ma tsananin mamaki da nake, taya haka zata kasance, anya kuwa ba wata maƙarƙashiyan ake shirin ƙulla mana ba Husnah?”

Dariya sosai Husnah ta kwashe dashi, domin kuwa maganar Zahrah takai a dara.

“Maƙarƙashiyan soyayya ba, babu wani aljanu, kawai dai inaga wani ne yaganki kuma ya yaba, shine kawai” Husnah tafaɗa tana mai danne dariyanta.

“Bangane ba me kike nufi?” Zahrah ta tambaya cike da ruɗu, domin ita kwata kwata ma bata fahimci inda kalaman Husnah suka dosa ba.

“Kada ki damu zaki gane mushiga mota”

Jiki a sanyaye Zahrah tabuɗe murfin motar tashiga, a gidan baya sukai mawa kansu masauƙi ita da Husnah..

Suna shiga driver yayi mawa motar key suka ɗauki hanyar Suleja unguwar su Zahrah.

(yauwa kuyi haƙuri jiya nayi mistake sunan unguwar su Zahrah ba Maraba bane, sunan unguwarsu Zahrah Suleja ne, kainane ya ɗau charge shiyasa)

Yanaganin tafiyarsu yasaki ƙawataccen murmushinsa, “Haryanzu tananan da halinta na tsoro, yayi imani Zahrah bazata taɓa sanjawa ba”

” komai naki yana burgeni Zahrah, inason komai naki!” Zaid dake cikin motarsa yafaɗi haka cike da shauƙi.

STORY CONTINUES BELOW

“Nifa gaba ɗaya kaina ya kulle, kimin bayani mana Husnah, me takardan nan take nufi ne?” Zahrah tafaɗi haka cikin zaƙuwa.

“Ki kwantar da hankalinki ƙawata, kawai dai bazai wuce irin mutanen nan masu alkhairi bane suka aikata hakan, wayasani ma ko Dr Sadeeq ne” Husnah tafaɗi hakan tana mai kallon Zahrah.

“Mene? kinanufin wai Doctor ne zaiyi haka? gaskiya banjin cewa shi ne, domin idan da shi ne, dole zai bayyana kansa na gansa, kodai ke akeso amawa wannan hidiman akayi mistake aka ambaceni” Zahrah tafaɗi haka cikin kokonto.

Dariya Husnah takuma sawa, haɗe da dafa kafaɗan Zahrah..

“Wai lafiyanki kuwa Zahrah? kinga yanda kika firgice lokaci ɗaya sai kace wacce ta aikata aikin rashin gaskiya, to ni miye ma abun damuwa ne don wani yabiyamana kuɗin sayayya? kinga bafa mu muka sa sa ba, ko ma waye shi yasanya kansa, kishare kawai ƙawata” Husnah taƙare maganar ta ta bayan ta ɓare sweet ta jefa acikin bakinta.

“Hmmm” kawai Zahrah ta’iya cewa, haɗe da mai da kanta jikin kujera, itakam gaba ɗaya kanta ya kulle, taya za’ace bakasan mutum ba, amma kuma ya biyamaka kuɗin siyayyan da kayi, irin haka ne mutum sai yaje ya jefa kansa a matsala.

Tafiya suke amma Zahrah ta kasa cewa komai, sai ma Husnah ce keta ƙoƙarin janta da hira, amma jefi jefi take amsa mata, domin kuwa wannan faɗuwar gaban da takeji har yanzu baidaina ba.

A haka har suka iso ƙofar gidan su Zahrah’n… Har cikin gida Husnah tayimawa Zahrah rakiya, kana ta fito tashiga mota suka tafi.

Zama tayi akan katifarta haɗe da zubawa kayan siyayya da sukayi ido, sam zuciyarta bata kwanta da wanda yabiya musu kuɗin kayan ba, zuwa yanzu ya kamata ace tayi hankali, domin sarai yanzu tasan salon yaudaran maza baida ƙarshe, suna iya yimaka komai don su samu biyan buƙatarsu, wannan yana ɗaya daga cikin babban dalilin da yasanya ta amince da auren Dr Sadeeq, ko ba komai idan ya aureta ta tsallake wani babban siraɗi na daga yaudaran da Maza sukeyi mawa ƴan mata a wannan zamanin.

Ƙaran wayartane yakatseta daga tunanin da takeyi, cikin sanyin jiki ta ɗaga ƙiran nasa, haɗe da kara wayar akan kunnen ta.

“Barkanki da hutawa My Princess!”

Dr Sadeeq yafaɗa cike da tsantsar kulawa.

Ɗan guntun murmushi tayi haɗe da cewa “Kaima barkanka dai ya aiki?”

Ɓata fuska yayi tamkar dai tana ganinsa haɗe da cewa “Aiki ba daɗi kokaɗan, ya kundawo a super market ɗin kenan?”

“Eh” tabashi amsa a taƙaice. Domin tsabar gajiyan da ta kwaso har wani bacci bacci takeji.

“Naga kamar kingaji da yawa, ki samu ki ɗan huta, zuwa anjima zanzo gida, inaso na samu Baffa, idan yabani dama zanturo magabata na ayi maganar auren mu, domin banso akai nanda wata ɗaya ban mallakeki ba!” yaƙare maganar cikin yanayin shauƙi.

Wani irin bugawa taji zuciyarta tayi, sakamakon jin abun da Dr Sadeeq yace. Wani irin yanayi ta tsinci kanta ciki, wanda baza’a ƙirasa da farinciki ba, ba kuma za’a ƙirasa da yanayin baƙin ciki ba.

“Zahrah na!” yaƙira sunanta jin cewa tayi shiru batace dashi komai ba.

“Umm” ta’amsa masa a kasalance.

“Naji kinyi shiru, ko dai bakiyi farinciki da hakan bane?”

Yajefo mata tambayar da batayi zaton zai mata shi a yanzu ba..

“A’a nayi farinciki mana, kawai dai kainane ke ɗan min ciwo” tafaɗi haka don ta kare kanta, gudun kada yafuskanci wani abu.

“Ayya kiyi haƙuri, anjima idan zanzo zan tahomiki da magani ko, yanzu ki kwanta ki huta, nasan ma stress ne, insha Allah zuwa anjima zaki ji ki normal” yafaɗi hakan cike da kulawa.

STORY CONTINUES BELOW

“To” kawai ta’iya cewa dashi, haɗi da zare wayar akan kunnen ta.

Nannauyar ajiyar zuciya ta sauƙe, haɗe da share ruwan hawayen da suka fito daga cikin idanunta. “Yazama dole nakoyi soyayyarka Dr Sadeeq, domin bayan kai babu wani wanda zai bani kulawa kamar haka, ya Allah kamin maganin matsalolina!” tafaɗi hakan a bayyane, bayan ta ɗaga idanunta zuwa sama.

Da ƙƴar ma ta’iya cusa abincin da Inna ta bata, domin kuwa hakanan taji zuciyarta ta cunkushe.

Kwanciya tayi akan katifarta tana ƴan tunani, take bacci ɓarawo ya siɗaɗo ya ɗauketa, batare da tashiryawa hakan ba….

Zaune yake akan wata haɗaɗɗiyar kujera, wanda take ita kaɗaice kuma na mussaman acikin bedroom ɗinsa, dake cikin guest hause nashi. ɗan ƙaramin table ne aje a gabansa, wanda samansa ke ɗauke da zungureriyar kwalbar wine da kuma glass cup.

Wayar sace riƙe a hanunsa, gaba ɗaya hankalinsa akan wayartasa yake, murmushine ɗauke akan fuskarsa, yayinda yake playback ɗin vedi’on daya mata ɗazu fitowarta daga cikin shoprite, batare da ta sani ba.

Harzuwa yanzu bai tantance mai yakeji a jiki da zuciyarsa ba a game da Zahrah, abu ɗaya yasani shine, yasan cewa “yana matuƙar buƙatarta a kusa dashi, fiye da tunanin mai tunani, yakuma ɗauki haka, amatsayin fitinanniyar sha’awarta da yake” sake playback ɗin vedion yayi bayan yakai ƙarshe akaro na barkatai domin kuwa yayi playback ɗin vedi’on yafi sau goma daga zamansa a wajen zuwa yanzu.

Wani irin sanyi haɗe da kewarta ne suke ratsa zuciyarsa alokaci guda.

“A hankali zankuma cimma burina akanki Zahrah, akaro na biyu ma ina da tabbacin cewa zanyi nasara akan ki, domin niban kasance Loser ba, bakuma zantaɓa kasancewa Loser ba, har abada !” yafaɗi haka cike da son ƙarfafamawa kansa guiwa.. A taƙaice dai haka Zaid yayita playback na vedio ɗin da yayi mawa Zahrah yana kallo, zuciyarsa cike da nishaɗi, abu ɗayane zai hanasa zuwa gareta a yanzu, shine plan ɗin daya shirya mata, bakuma zai je gareta ba, harsai ya tabbatar da cewa ta gama rufzawa cikin tarkonsa, da ya ɗana mata a karo na biyu….

(😲)

Doctor Sadeeq ne tsugune a gaban Baffa Amadu, wato ƙanin mahaifinsa. Bayan ya gama kora masa bayanin duk abun dake faruwa, hatta fƴaɗe’n da akayimawa Zahrah bai ɓoye masa ba, domin kuwa a yanzu Baffa Amadu shine Uba a garesu, kasancewarsa ƙanin mahaifi’nsu.

Ajiyar zuciya Baffa Amadu yasauƙe, haɗe dayin gyaran murya irin tasu ta manya…

“Haƙiƙa kazo da babbar magana Sadeeq, amma kuma duk na fahimceka, bakuma zanyi ƙasa a guiwa ba wajen ganar da mahaifiyarka dakuma ƴar uwarka, amma kuma kasan dole sai an haɗa da haƙuri, kasan su mata koda yaushe tunaninsu baya zurfafa, bakuma ko da yaushe suke gane abun da ake so su fahimta ba, amma tunda kakawo matsalan nan wajena, ka kwantar da hankalinka, ni nan zanje har gida na samu mahaifiyartaka, zamu tattauna akan matsalan!”

Wani irin sanyin daɗi ne yashiga huda zuciyar Dr Sadeeq, sai yanzu yakejin nutsuwa na sauƙar masa, yanzu fatan sa ɗaya, shine Allah yasa mahaifiyarsa ta amince, amma tabbas Zahrah itace burin ran sa…

Daga haka sukayi sallama da Baffa Amadu, bayan ya tabbatar masa cewa lallai zaice yasamu mahaifiyartasa da batun…

Cike da farinciki Dr Sadeeq yabaro gidan Baffan nasa, kai tsaye gidansu ya nufa….

Zama yayi dirshan akan kujeran dake falonsa, haɗe da soma cire safar ƙafansa, fuskarsa cike take da annuri dagani kai kasan yanacikin farinciki…

Turo ƙofar falon nasa akayi da ƙarfin gaske, wanda hakan yatilasta masa ɗago kansa da sauri, don ganin ko waye.

Dammm haka yaji ƙirjinsa yabuga, sakamakon ganin fuskar Hajiyarsa da yayi babu ko ɗigon annuri akanta, saima wani irin mugun kallo da take jifansa dashi.

STORY CONTINUES BELOW

Cike da girmamawa yace “Hajiya Barkanki da…..”

Saurin ɗaga masa hanu tayi, alaman batason jin komai daga garesa..

Cikin ɓacin rai da tuƙuƙin zuciya Hajiya tasoma cewa….

“Lallai ka haifu Sadeeq, tunda har zaka iya kai ƙarana wajen ƙanin mahaifinka, yanzu akan wata watsatstsiyar yarinya, ka ke neman ka bijirewa auren ƴar uwa kuma aminiyata da aka baka? Ashe dama wacce kake ikirarin kana so ɗin, ba cikakkiyar mace bace, sauran layine? kaban mamaki ƙwarai Sadeeq, amma bakomai ni na sakema har haka ta faru, kuma tabbas zanɗauki ƙwaƙƙwaran mataki akan ka, daga kai har sakaryar yarinyar da ka bawa soyayyarta amanna, bansan cewa rashin hankalin naka har yakai haka ba, ashe har zuwa kamun ƙafa wajen mutane kakeyi, akan cewa azo a bani baki, nabarka ka auri wacce tagama raba budurcinta ga mazan layi, hmmm wallahi kasaurari hukuncin da zan yanke, kuma tun wuri ka gaggauta cire tunanin auren wannan yarinyar aranka, domin kuwa bamai yi wuwa bane!” fuuu haka Hajiya ta juya ta fice daga falon nasa ranta amatuƙar ɓace…

Kalmar “Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un!”

Shine abun da yafito daga bakin Dr Sadeeq, wanda yasanya hannayensa gaba ɗaya ya dafe kansa… “Me yasa Aunty Raliya? meyasa zakimin haka?” yatambayi kansa cikin takaici dakuma ɓacin rai. Tabbas yasan Aunty Raliya ce ta sanar da Hajiyansa komai, domin kuwa lokacin da yake gaban Baffa Amadu ta ƙirasa, bai ɓoyemata ba kuma yashaida mata cewa yana gidan Baffa Amadu’n, ashe ita harta gane mai yakawosa, shine kuma tasanar da Hajiyarsu komai… Take idanunsa suka kaɗa sukai ja,, ba abun da yake masa ciwo kamar aibata Zahrah da akeyi, kowa idan yatashi sai yajefeta da sunan wacce ta watsar da mutumcinta a waje, alhalin kuma itama ba laifinta bane, ƙaddarace dakuma tsautsayi, domin kuwa shi kansa sheda ne akan abun da yafaru da’ita, tunda har kusan haukacewa tayi. Rasama me yake masa daɗi yayi, da wanne zaiji ne? da soyayyar Zahrah, ko kuma da fushin da Hajiyarsa keyi dashi. Gaba ɗaya ma ji yayi zazzaɓi nason kamasa don haka kawai sai ya koma ɗakinsa ya kwanta, ba abunda yake ambata sai sunan Allah, domin kuwa shi kaɗai ne zai iya kawo masa ɗoki,, dama kuma mu dashi muka dogara shine mai kowa kuma mai komai, sarkin da babu kamarsa, Allah kenan buwayi gagara misali, maiyin duk yanda yaso mai kuma ƙwacewa da kuma bayarwa alokacin da yaso, ga kuma duk wanda yaso…..

Zahrah kuwa tunda ta faɗa duniyar bacci ba’ita tafarka ba, sai gaf da’ana ƙiraye ƙirayen sallan magriba.. Kaitsaye banɗaki ta wuce taje tayi wanka haɗe da ɗauro alwala tazo ta kabbara sallan magriba.

Kayanta marar nauyi tasanya haɗe da ɗauƙan wayarta dakuma ledan da kayan siyayyanta ke ciki, tafito farfajiyar gidan nasu, zaune ta iske Inna tana faman ƙoƙarin kunna redio’nta, wanda koda yaushe take tare dashi kamar jaraba.

“Barka da dare Inna” Zahrah tafaɗa lokacin da tayi mawa kanta mazauni a kusa da Inna’n.

Inna bata amsata ba, saima kafe ledar dake hanun Zahrah’n da tayi da ido, Allah Allah take taga mene acikin ledar, domin dama bakinta ya bushe neman abun lasawa takeyi, kasancewar tuwo ta tuƙa abincin dare, bakuma tajin cinsa, tafison tasamu ƙwalam taɗan lasa, like o’o da o’o lol.

Tun Zahrah batakai ga buɗe ledar ba inna tayi gajen haƙuri haɗe da fusge ledar daga hanun Zahrah tashiga dubawa.

Ganin cewa tarkacen su Chocolate’s da kuma su biscuit’s ne acikin ledar yasanya Inna jan uban tsuka haɗe da bankamawa Zahrah harara.

“Aikin kenan gayyar tsiya, mutum yasan bakacin abu, amma saboda tsinannen baƙinciki dakuma mugunta, ko da yaushe shiyake saya bini bini, bazai sayo abun da duka gida za’a amfana ba mcheeww!” cikin ƙufula Inna taƙare maganar, domin kuwa ita duk wannan shirmen banzan basonsu take ba, tafiso taga daƙwalen kaza, kokuma gasheshshen nama mai zafi, yauwa tanan tafi kauri, amma kwata kwata kayan kantin nan ita ba zaɓinta bane.

Da ƙyar Zahrah ta iya danne dariyan Inna dake cikinta aciki.

Buɗe ledan tayi gaba ɗaya haɗe sa sanya hanunta taciro wani ɗan madaidaicin cake wanda daganinsa kasan yasha madara.

“Ungo wannan Inna shikan nasan zaki iyaci, saboda kema nasayoshi” Zahrah tafaɗi haka tana mai miƙamawa Inna cake ɗin.

“Yauwa kokefa, amma da kya bani wasu tarkacen banza”

Take Inna ta ɓare cake ɗin, tahau ci har lumshe idanu take, domin dai sosai cake ɗin yamata daɗi.

Murmushi kawai Zahrah tayi haɗe da gyara zamanta, tasoma latsa wayarta….

Wani yarone yashigo cikin gidan bakinsa ɗauke da sallama, atare Inna da Zahrah suka amsa masa.

“Wai ana ƙiran Zahrah a waje” inji cewar yaron..

Wani irin faɗuwa Zahrah taji gabanta yayi harsaida tasanya hanu ta dafe ƙirjinta……Wani irin faɗuwa Zahrah taji gabanta yayi har saida ta sa hanu ta dafe kirjinta daya fara dukan uku uku…..+

“Jekace tana zuwa” Inna tace da yaron,, bamusu yaron yajuya yafice daga cikin gidan…

“Yadai lafiyanki kuwa naga kinwani dafe ƙirji?” Inna tatambayi Zahrah, wacce lokaci ɗaya yanayinta ya sauya.

“Bakomai” Zahrah tafaɗa a taƙaice domin kuwa ko tayi ƙoƙarin ganar da Inna halin da take ciki tofa bazata gane ba…

“Tashi maza kije, ba kyau yin watsi da baƙo, wata ƙilama da alkhairi yazo miki, domin na lura keɗin baki da ƙashin tsiya” Inna tafaɗi hakan lokacin da ta miƙe daga zaunen da take.

Cikin sanyin jiki Zahrah takoma ɗaki ta ɗauko ƙaton hijab ɗinta ta sanya.

Tun kafun ta ƙarasa fita daga zauren gidannasu zuciyarta tasoma bugawa, wanda batasan dalilin hakan ba.

Wata mota ce tagani fake a ƙofar gidan nasu, kasancewar akwai hasken wuta, yasanya har kalan motar tana’iya hangowa.

Tsayawa tayi cak daga inda take, domin bazata sake tabka babban kuskuren da ta tabka a baya ba,  batasan waye ba don haka bazata ƙarasa ba, idan wanda ke cikin motar yagaji ya fito, ya isketa daga inda take tsaye…

Cikin hanzari wani wanda baza’a ƙirasa da suna matashi ba,  bakuma za’a ƙirasa da suna tsoho ba, yafito daga cikin motar hanunsa ɗauke da wani kwali, yayinda aka ɗaura wani kyakkyawan flower a saman kwalin… Ganin yanufota kaitsaye yasanya ta ɗan sake ja da baya..

“Sannu da fitowa ranki shi daɗe” mutumin nan yafaɗa..

“yauwa sannu” Zahrah ta bashi amsa a taƙaice…

” dama saƙone aka bani nakawomiki” wannan mutumin ya kuma faɗa cikin rusunawa haɗi da girmamawa, duk da kuwa cewa shiɗin ba yaro bane, domin yakusan haifar  Zahrah’n ma, domin itama bawani yawan shekaru ne da’ita ba…

Cike da tsananin mamaki Zahrah, ta saki baki da hanci tana kallon mutumin dake tsaye a gabanta, yana miƙomata saƙon dake hanunsa…

“Wayekai?” shine kawai abun da ya iya fitowa daga bakinta, saboda gaba ɗaya kanta ya kulle…

Murmushi mutumin yayi haɗe da cewa “Ba’a bani daman sanar  dake koni waye ba, kawai dai an umarceni dana kawomiki wannan saƙon, sannan dan Allah kada kice bazaki ansaba, saƙone mai mahimmanci, yanada kyau ki karɓa, sannan daganinki ke mai ilimi ce, kinsan bakyau maida hanun kyauta baya!” mutumin yafaɗi haka still yana mai sake miƙo mata kwali da flowern dake riƙe a hanunsa…

Kai Zahrah tashiga gyaɗawa, cike da tsarguwa tace ” Kana da girma da kuma mutumcin da bazanyimaka gardama ba, amma kuma saidai kayi haƙuri, bazan karɓi abu daga wanda bansani ba, bankuma san menene nufinku a kai na ba” tafaɗi hakan da iyaka gaskiyarta….

STORY CONTINUES BELOW

“Hakane, amma ki ceci aikina, domin wanda ya ban saƙonnan nakawo zuwa gareki ya tabbatarmin da cewa, idan har baki karɓi saƙon ba, to abakin aikina, kitaimaka, ina da iyalai, kuma da aikina na dogara” mutumin yafaɗi haka cikin rauni.

Zaro idanu Zahrah tayi haɗe da jinjina maganar mutumin aranta, lallai kuwa kowaye ya aikosa yacika ɗan jin kai,  ita kuma irin mutanen da tafi tsana kenan a rayuwarta wato mutum mai jin kansa….

Cike da kokonto haɗi da zullumi tasanya hanu ta karɓi abun da mutumin ke miƙomata.

“Zankarɓane kawai saboda kai, domin na fuskanci rashin karɓana zai iya sanyaka acikin matsala, amma koma waye ya turoka kace masa injini ya sanja hali, domin wannan ba hali mai kyau bane” daga haka tasakai tayi komawarta cikin gida..

Cike da murna’n cewa ta karɓi saƙon wannan mutumin yakoma mota haɗe da yi mata key yabar area’n unguwar tasu….

Zahrah tana shiga gida kaitsaye ɗakinta ta wuce, yayinda Inna ta rakata da  idanu…

Zama tayi akan katifa, haɗe da tsurawa kyakykyawan kwalin nan idanu, ba iya shi kaɗai bane, abun ɗaukar hankali, hadda wannan haɗaɗɗen flower’n dake samansa ma abun burgewane, alal haƙiƙa ma ita flower’n ne yafi ɗaukar hankalinta….

Cikin sanyin jiki tasa hanu ta ɗauki flower’n haɗe da matso dashi kusa da fuskarta….lokaci ɗaya ta zabura haɗe da wurgi da flower’n gefe, take idanunta suka kaɗa sukai jajur dasu, jitayi kanta yafara juyawa,  tabbas bazata taɓa mantawa da wannan ƙamshinba har abada kuwa, ajikin mutum ɗaya tasan wannan ƙamshi, bayan shi kuma batasakejin ƙamshin a jikin kowa ba,, hannayenta ta sanya duka biyu haɗe da dafe kanta dayake sara mata,, tabbas irin ƙamshinsa fulawar nan keyi, take taji wani irin tsanar flower’n  ya cika mata zuciya,  san nan kuma tsanarsa tasake dawo mata sabuwa fil, cike da ɓacin rai ta ɗauki flowern haɗe da fita waje da’ita, ko son ganinta ma batason yi,   kai tsaye wajen da suke aje  shara ta nufa, cike da tsanar  flower’n ta jefa ta cikin kwandon shara, haɗe da furzar da yawu akan flower’n duk wani abu da zai tuna mata da Zaid ta tsanesa…

Ranta a ɓace takoma ɗaki, ita dai Inna dake zaune a tsakar gidan haka ta saki baki galala tana ganin ikon Allah..

“Wallahi na tsaneka, tsana mafi muni, bantaɓajin tsanar wani a raina sama da wanda nakeyi maka ba,  ya Allah kada ka sake haɗa fuskata da tasa!” tafaɗi hakan a bayyane, kuma cikin tuƙewar murya…

Gaba ɗaya ƙamshin da taji flower’n nan nayi ya ɗaga mata hankali,  sabuwar tsanar Zaid yasake ɗarsuwa acikin zuciyarta…

Lallai da zataga wanda yasanya akawo mata flower’n nan da ta gargaɗesa da kada ya sake kawo mata komai nasa, don bata so, domin kuwa duk wani abu da zai sanya tayi tunanin Zaid bata ƙaunarsa, koda sunansa nema batason ji”

Kwanciya tayi lamo akan gado, tana mai da numfashi, ji takeyi gaba ɗaya ta tsani ɗakin nata, domin kuwa ɗakin gaba ɗaya ya ɗau ƙamshin turaren dake jikin flower’ ɗin nan….

Wayartace tasoma ƙara alamar shigowar ƙira, ganin Dr Sadeeq ne me ƙira yasanya ta ɗaga wayan, cikin son ɓoye damuwarta..

“Inaƙofar gida” abun da Dr Sadeeq yafaɗa kenan, a cikin wayar, domin kuwa shima dai yauɗin yana cikin damuwa….

Babban tabarma ta shumfuɗa musu a tsakar gida, kafun tanufi ƙofar gida don yi masa iso..

Kusan tare suka shigo cikin gidan, tana gaba yana biye da’ita a baya.. Gaba ɗaya yagama karantar yanayinta, ya kuma gane cewa tana cikin damuwa.

Zama yayi akan tabarman da ta shumfuɗa musu,  haɗe da tanƙwashe ƙafafunsa.. Gaba ɗaya nutsuwarsa ya miƙa zuwa gareta, ta hanyar zuba mata idanu….

Gyara zama Zahrah tayi haɗe da ɗaga idanunta ta saci kallonsa, aikuwa karab idanunsu suka sauƙa akan na juna.. Cikin son basarwa tace ” Sannu da zuwa, ya hanya?”

STORY CONTINUES BELOW

Ajiyar zuciya ya sauƙe haɗe da lumshe idanu…”Hanya ba daɗi duk nagaji da tuƙin ma, i hope you will find a driver that will take me home” cikin zolaya yaƙare maganar..

Kallonsa tayi kawai,  haɗe da yin ɗan murmushi, shiru tayi batare da tace dashi komai ba…

“Meke damunki naganki haka, ko dai ciwon kanne?” Yatambayeta cike da kulawa..

“No bashi bane, ka wai dai gajiya ne, baisakeni ba haryanzu” tafaɗi hakan a taƙaice…

“Kansa yajinjina, haɗe da sake lumshe idanunsa,  shi ɗinma ƙarfin haline kawai yasa sa yazo, amma tabbas damuwar dake damunsa tana da yawa.

“Meke damunka, naga gaba ɗaya kamar baka cikin farinciki?” Zahrah ta tambaya cikin siga da yanayi na nuna damuwa..

Wani irin sanyin daɗi yaji a zuciyarsa, badon komai ba, saidon kulawa da yasamu daga gareta.

Gyara zamansa yayi haɗe da bata duka nutsuwarsa….”Bazan ɓoyemiki ba Zahrah, tabbas inacikin damuwa, kuma duk akan kine,  Ina tsananin sonki Zahrah, ina da burin baki farinciki a cikin rayuwarki,  amma sai dai na  haɗu dake a ƙurarren lokaci, inafata zaki fahimci abun da zance dake?”

Cike da ɗaurewar kai Zahrah take kallon Dr Sadeeq, domin kuwa sam ita bata fahimci inda kalamansa suka dosa ba.

“Mahaifiyata ta zaɓamin matar da zan aura, yanzu haka maganar da nakeyi miki, har ansanya mana rana, saura sati uku”

dummm haka Zahrah taji ƙirjinta yabuga, duk da cewa bata wani jin son Dr Sadeeq a ranta, amma bazata taɓa so kyakkyawan namiji mai nagarta kamarsa ya kuɓuce mata ba, take idanunta suka ciko da ƙwalla wanda batasan na menene ba.

“Dan Allah kada kiyi kuka kinji Zahrah na, nafaɗamiki hakane don kisan halin da nake ciki, amma bawai hakan nanufin bazan aureki bane ba”

Cike da kulawa yakama duka hannayenta biyu, haɗe da kafeta da idanu.  Gaba ɗaya abun da yake wakana ya kwashe ya faɗa mata, hatta maganarsa da Baffa Amadu, saida  ya sanar da’ita, sai dai ya ɓoye mata ƙiyayya dakuma maganganun da yayarsa da kuma mahaifiyarsa suka faɗa akan ta na ɓatanci.

Cigaba yayi da cewa “Ki kwantar da hankalinki, na miki alƙawari nan bada jimawa ba, zaki zamo mallaki a gareni, insha Allah zanzamo mijinki Zahrah!”

Hawayene suka shiga zirya akan fuskan Zahrah, cikin murya mai rauni tace ” Dama nasan cewa nayi ganganci, domin kuwa kai ba sa’an aure na bane,  nagode sosai da irin kulawa da kuma ƙoƙarin da kayi a kaina, bakuma zan taɓa mantawa da hakan ba, na yarda da ƙaddara mai kyau ko marar kyau, idan aurena dakai baiyi wu ba, na yarda haka Allah yatsara,  tun da  fari shiya gurɓatamin rayuwa, ya cutar dani, cuta mafi muni, ta yanda babu wani wanda  zai lamuncewa haɗa zuri’a dani, tabbas daman nasan koda kai ka aminta da aurena, ba lallai iyayenka su aminta ba?….Kukane ya ƙwace mata sosai.

Sake damƙe hannayenta yayi acikin nasa, haɗe da kafeta da idanu, sosai tausayinta ya sake kamasa.

“Kinaso nasake shiga cikin damuwa ne Zahrah?” yayi maganar cikin tausasa murya.

Bata iya amasa masa ba, sai gyaɗa masa kai da tayi alamar “A’a”

“To idan har bakyaso nasake shiga damuwa, ki daina kuka kinji Zahrah na, insha Allah, zamu rayu tare dake, harma ki haifamin kyawawan babies, masu kyau kamarki, masu irin idanunki, da bakinki, harma da irin hancinki, da kuma…” sai yayi shiru, yana mai dariya ƙasa ƙasa.

Kunyane ya kama Zahrah haɗe da dariya, duk da kuwa cewa tana cikin halin damuwa, sai kawai ta kawar da kanta gefe, gaba ɗaya jinta take a tsarge sakamakon hanunta da ke saƙale acikin nasa…

“Zantafi saboda naga dare yasoma yi, amma saikinmin alƙawarin cewa bazakiyi kuka ba, bakuma za kisa kanki a damuwa ba, idan kikayi haka zanji daɗi sosai”

STORY CONTINUES BELOW

Abune mai matuƙar wuya, a dake ka sannan a hanaka kuka, amma tabbas zata jarraba wajen daure zuciyarta.

“Bazanyi kuka ba” tafaɗa cikin muryar da bata fita sosai, da badon yana kusa da’ita sosai bana ma  to tabbas da bazaiji maitace ba..

“Kinyi alƙawari?” yatambayeta

“Eh” tafaɗi haka  bayan taɗanyi jim…..

“Yauwa Zahrah na, nasan ai kina da cika alƙawari, taso muje mota na baki magungunanki”  babu musu ta miƙe daga zaunen da take, haɗe da rufa masa baya.

Murfin motar ya buɗe haɗe da fiddo  wata ƙatuwar leda.

“Ungo magungunan suna ciki, akwai bayanin yanda zakisha a jiki, please ki kulamin da kanki kinji” yafaɗi haka cikin lallashi, haɗe da miƙa mata ledan dake hanunsa.

Kasa amsan ledar tayi, saima kawar da kanta gefe da tayi.

Murmushi Dr Sadeeq yayi, domin kuwa sarai ya fuskanci hakan da tayi metake nufi.

“Kiyi haƙuri ki karɓa kinji Zahrah na” yakuma faɗan hakan cikin lallashi.

Baki Zahrah taturo gaba haɗe da cewa …

“Kasan tun ba yauba nafaɗama cewa banaso domin kuwa hidiman da kakemin yayi yawa, mai yasa bazaka bari haka ba!” ta tambayesa cike da sakalci..

“Saboda kina da mahimmanci, kinkuma cancani namiki fiye da haka,  amma yanzu dai banso kice a’a ki karɓa kinji” still cikin lallashi yayi maganar.. Badon ranta yasoba haka ta karɓi ledan.  

“Saida safe” tace dashi cikin sanyin murya haɗe da juyawa ta nufi hanyar shiga gida.

“Kada kimanta kin ɗauki alƙawarin cewa bazakiyi kuka ba, bakuma zaki shiga damuwa ba, kada ki karya alƙawari kinji mai kyau na!”

Murmushi kawai tayi masa haɗe da ɗaga masa kai alamar taji.

Yana ganin shigewarta cikin gida, shima yashiga motarsa haɗe da bata wuta yabar unguwar tasu..

Tanashiga cikin gida, Inna tayo kanta haɗe da fusge ledar dake hanunta,   babu magana ba komai ta shiga zazzage ledan akan tabarma, kallonta kawai Zahrah ta tsayayi cike da takaici, sai yanzu take godewa Allah dayasanya ba Inna bace ta haifeta, domin kuwa da Innace ta haifeta to tabbas da nan gaba kaɗan zuciyarta zata fashe, saboda  wannan halin da Inna keyi ba hali bane na iyayen ƙwarai, batama tsaya ganin menene acikin ledar ba, ta wuce cikin ɗakinta, domin ita dama ba wannan bane a gabanta, yanzu babban damuwarta shine, yanda zata samo maganin matsalarta.

Ɗaukan kwalin nan da aka kawo mata  tayi, haɗe da soma kiciniyar buɗewa, kasancewar bakin kwalin a nane yake da wani gam me kyau..

Tana buɗe cikin kwalin wani tsadadde kuma kyayyawan agogo na mata ya bayya, gefen sa kuwa wani irin awarwarone haɗe da zobe  masu kyaun gaske, wanda dagani kasan na gold ne, domin kuwa kyawunsu kaɗai ya’isa ya bayyana haka, ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya ta sauƙe haɗe da mai da murfin kwalin ta rufe kamar yanda ta samu,   ɗaukan kwalin tayi dukansa, haɗe da ɓoyesa a cikin kayanta, dawowa tayi kan katifarta ta kwanta zuciyarta cike tab da tunanin son gano wanda  ya soma

bibiyar rayuwarta…

Hajiya Habiba (mahaifiyar Dr Sadeeq) ne zaune  akan kujera gaba ɗaya ta tattara nutsuwarta ta miƙasa ga Baffa Amadu dake zaune akan ɗaya daga cikin  kujerun falon…

Baffa Amadu ne yaci gaba da cewa ” Banzo nan don na yi miki dole ba, amma Hajiya Habiba yana da kyau  wasu lokutan muna ƙoƙari wajen bawa ƴaƴanmu dama akan abun da suka nuna zuciyarsu naso, musamman ma aɓangaren abun da yashafi aure, haƙiƙa Sadeeq yasameni da wannan maganar yakuma min bayani tayanda zan fahimta, Alhmdlh nakuma fahimta, yanzu saura ke,  kada kice wai don ƙaddara ya taɓa faɗa mata, ɗanki bazai aure ta ba,  kada kiyi haka, domin ita ƙaddara tanakan kowa mai kyau da marar kyau,  sannan abu nagaba danakeso kisani, ko da ace alal misali yarinyar  ta kasance karuwa ce,  addini bai hana masa auren taba, wala Allah saboda auren saiki ga ta shiryu, balle kuma ma bahakan take ba, amma bazan miki dole akan cewa saikin amince ba, ɗan kine kuma kina da iko akansa”…

STORY CONTINUES BELOW

Nannauyar ajiyar zuciya Hajiya ta sauƙe, haƙiƙa Baffa Amadu yazo mata da magana mai girma.

ɗan nisawa tayi haɗe da cewa “Bawai naƙi aurensa da ita bane, saboda wani abu ba ne, kawai dai inajiye masa yanda tarbiyan yaransa zai kasance  ne matuƙar takasance tana cikin gidansa, domin na tabbatar rashin wadataccen tarbiyan da aka bata a gidansu, shiya jawo faruwar haka a kanta,  kaga itama bata samu tarbiya mai kyau ba, balle tayi ƙoƙarin bawa nata yaran, haƙiƙa Sadeeq yarone mai biyayya agareni,  kuma harcikin zuciyata na ƙudurta aniyar cewa bazai taɓa auren wannan yarinyar ba, amma tunda harka shigo cikin al’amarin shikenan na’amince, amma kuma fa sai dai idan su biyun duka zai haɗasu ya aura, kaga dai Salima ƴar wajen ƴar uwata ne, haka kuma mamarta aminiyata ce, bayanda za’ayi na watsa musu ƙasa a ido, tahanyar cewa Sadeeq bazai auri Salima ba, kuma kaga yanzu saura ƴan satika ne suka rage, har anriga da anfara shirye shiryen biki”

“Ƙwarai kina da gaskiya ta wani wajen, amma kuma bamu iya ja da haɗin Allah, yanzu zansanar da Sadeeq ɗin duk yanda mukayi dake, zan kuma faɗa masa amincewarki,   nasan shi ɗinma zai amince da umarninki, amma inaga zaifi kyau ayi bikin nasu a rana ɗaya, domin babu amfanin jan lokaci”

“Eh duk yanda kukace shikenan” Hajiya tafaɗi haka badon ranta yaso ba.

“Shikenan to duk dai yanda ake ciki, zai zo yasanar dake” Baffa Amadu yafaɗi haka bayan yamiƙe tsaye ya gyara zaman garen dake jikinsa…

Cike da mutun ta juna sukayi sallama shida Hajiya…

Zama Hajiya tayi afalon haɗe da yin jigum, tabbas ba’ason ranta ta amince da wannan auren ba, saboda ita gani take tamkar yarinyar ba kimtsatstsiya bace,  ta amince ne kawai saboda Baffa Amadu yashigo cikin maganar, kuma tana matuƙar darajasa haɗe da basa girma, domin tana masa kallo ne tamkar marigayi mijinta,  amma da ba haka ba da bazata taɓa amincewa ba, yanzu dai kawai sai dai tayi addu’an Allah yabasu zaman lafiya, amma ta wani ɓangare na zuciyarta, tunani take taya zataje ta tunkari ƴar uwarta Hajiya Furaira da wannan maganar, tasan Hajiya Furaira macece mai zafi,  bazata taɓa son hakan ba, domin saboda bala’inta da zafin kishin ta, ne ma yasanya mijinta haryau yakasa ƙara aure bawai kuma don baya so ba, to ina kuma da idan taji cewa ƴarta ɗaya tilo zata haɗa miji  da wata daban wacce bata da galihu, gaskiya zaiyi wuya ta amince… Haka dai Hajiya tadinga saƙawa da kuncewa daga ƙarshe ta tashi ta wuce ɗakinta….

Cikin matsanancin farinciki Dr S.S ke kallon Baffa Amadu sakamakon jin cewa wai mahaifiyarsa ta amince da aurensa da Zahrah, masha Allah ashe  dai mafarkinsa zai zamanto gaskia, sai dai kuma farincikin nasa bai zama cikakke ba, domin kuwa sosai maganar haɗa auren Zahrah da Salima ya daki zuciyarsa, saboda shi a tsarin sa baida burin aje mata biyu acikin gidansa.

“Yanaji kayi shiru ne Sadeeq, ko baka amince da sharaɗin mahaifiyartaka bane?” Baffa Amadu yatambayeshi cike da kulawa.

Kansa yashiga sosawa yamakasa ce da Baffan nasa komai..

Murmushi Baffa Amadu yayi domin yafahimci halin da Sadeeq ɗin yake ciki.    “Kada ka ɗaga hankalinka Sadeeq,  atunanina ka kai namiji wanda zai iya riƙe mace sama da biyu, don haka wannan ba abun damuwa bane, kayarda da sharaɗin mahaifiyartaka, addu’anmu shine Allah yatayaka riƙo, yakuma baka dama da ikon yin adalci a tsakaninsu, yanzu yaushe kakeso muje gidansu ita yarinyar?”

Gaba ɗaya jiyayi jikinsa yayi sanyi, zuciyarsa kuwa jiyayi tayi masa wani iri. “Zansanarda Baffan yarinyar idan yafaɗamin ranan da zakuzo, saina faɗa maka” inji cewar Dr Sadeeq..

“To shikenan Allah yakaimu” daga haka sukayi sallama, Dr S.S yabaro gidan Baffa Amadu zuciyarsa cike da tarin tunani kala kala, yana farincikin cewa Zahrah zata zamo matarsa, amma kuma ta wani ɓangare na zuciyarsa kwata kwata bayajin daɗi.   Zahrah tana buƙatar farinciki da kuma kulawa mai kyau, baikamata ace anraba mata farinciki ita da wata ba, to amma “Miye mafita?” yatambayi kansa, bayan yasan baida amsar tambayan nasa, amma koma dai mene ayau zaije yasamu Baffa yasanar dashi cewa yana neman abashi izini yaturo magabatansa don abasa auren Zahrah, yakuma ƙudurta aransa cewa, dakansa zai bada order a Dubai, na kayan lefen Zahrah, domin kuwa zaiyi rawar gani sosai, wajen ganin komai na Zahrah yafita da ban….

Amatuƙar mamakance Alhaji Ma’aruf ke kallon Zaid wanda yafaɗi maganar daya matuƙar basa mamaki…. “Aure fa kace Zaid, dagaske kake, yanzu kashirya zakayi aure?”

“Da gaske nake Dad aure zanyi, kuma inaso kaje da kanka ka tambayamin, banaso auren yawuce nan da sati biyu Dad”

Cike da tsananin farinciki Alhaji Ma’aruf yace “Alhmdlh! naji daɗi ƙwarai da gaske, domin zuwa yanzu yakamata ace ka aje iyali, insha Allah, zan je na tambaya maka aurenta, ƴar wayene kuma a ina take?”

“Ba ƴar kowa bace Dad, talakawa ne ma, amma ni ahaka naji na aminta ina kuma son na aureta” yafaɗi haka da iyaka gaskiyarsa..

Jinjina kai Alhaji Ma’aruf yayi haɗe da cewa “Zan sa rana sainaje naga mahaifinta”

“To” kawai Zaid yace haɗe da tashi yabar falon Dad ɗinnasa….

Fitowarta amakaranta kenan, tana sauri ta samu abun hawa, don bata son tsayuwa a bakin makarantar, kasancewar Dr Sadeeq aiki yamasa yawa bazai samu daman  zuwa ɗauko ta ba…

Wani matashin saurayine yanufo wajenta, hanunsa ɗauke da wani babban kwali wanda aka rufesa da wani irin abu mai kyau, aka kuma ƙawatasa da flower mai walwali..

“Ranki ya daɗe barka da yammaci”  saurayin yafaɗa.

“Yauwa barkan ka dai” itama ta mayarmasa amsa cikin ɗari ɗari dashi..

“Saƙo aka bani nakawomiki” yafaɗi maganar yana me miƙa mata kwalin dake hanunsa..

Cikin mamaki Zahrah ta shiga kallon saurayin nan dake tsaye a gabanta..

Murmushi saurayin yayi mata haɗe da sake miƙo mata kyakkyawan gift ɗin dake hanunsa.

“Waye ya aikoka?” tayi masa tambayar cikin dakiya…

“amsar tambayarki duka suna cikin nan” yaƙare maganar yana me nuna mata kwalin dake hanunsa.

Hakanan taji zuciyarta ta aminta da ta karɓi saƙon.. Hanu biyu tasa ta karɓa,  batace dashi komai ba tayi wucewarta dai dai lokacin mai taxi ya ƙaraso tashiga.

Tsurawa  kyakkyawan kwalin  idanu tayi, sosai adon jikinsa yayi kyau haɗe da ɗaukar hankali, gaba ɗaya ta ƙosa, tabuɗe kwalin don ganin ko wanene yake son yin wasa da hankalinta, ta hanyar turo mata da saƙonni, batare da yabari tasan kowaye shiɗin ba.

Tana shiga gida direct ta wuce ɗakinta,  ko mayafinta bata cire ba, ta zauna haɗe da soma yaye ledan da akayimawa kwalinnan ado dashi,   tana buɗe kwalin tayi arba da wani ƙatuwar ta karda wanda aka naɗeta,  cikin sauri ta ɗago takardan haɗe da soma warwareta, amatuƙar razane tayi wurgi da takardan sakamakon idanunta da sukayi mata tozali da zanen hoton dake jikin takardan.

(🤔Ga Zaid ga Sadeeq ko waye cikinsu zai mallaki Zahrah🤷‍♀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *