AUREN KWANGILA BOOK 2 CHAPTER 7 BY SUMAYYAH ABDULKADIR
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
Kuma na fara samun abin da nake so alhamdulillah. A jiya na fahimta. Duk da haka kuna bukatar karin ‘lokaci’ ki gafarce ni, ki kara min watanni biyu a gaba kafin in tako kafafuna gidanku. Amma daga yanzu na amince ki kira ni duk yadda ki ke so, ko sau dari ne a rana”’. Dariya ta yi, dadi har cikin ranta. Duk da in Hausa mai tsauri ce ba ta fahimtarta. Yanzun ma ba ta fahimci wani muhimmin abu cikin zantukan Mamarta ba. Ta dai fahimci ba daina sonta ta yi ba, tana da dalilinta na rashin zuwan da rashin kiran. Tana so sai sun shirya sun saba da juna sun kaunaci juna don kansu. Tausayin Hajiya Maryam ya tsirga a zuciyarta, shin ya ya za ta ji ranar da ta fahimci duk wannan hakilon nata a tutar babu zai tashi? Abdul’azeez ba fara sonta zai yi ba? Kuma ba zai taba son nata ba, yana da wadda zuciyarsa ta riga ta mutu ta rube a kanta?
Hawayen tausayin Mammah suka zubo mata, don ta kawar da tunanin da ya addabi zuciyarta Sai ta ce,
Mommah ya cike min JAMB”. Fassara farin cikin zuciyar Hajiya Maryam ba zai rubutu ba, “Na ji dadi sosai Addah, wane ‘course’ ya sa maki?” Ban sani ba Mommah, kuma ba ni da zabi. Na
ZAMU TASHI
bar mishi wuka da nama. Ni dai in yi karatu kowanne iri ne Mommah”. Murmushi Hajiya Maryam ta yi ta sanya wa Abdul’ azeez albarka cikin zuciyarta.
“Ni na san me zai sa miki, tunda shi karatu in ba shari’ah ba (Bar and the Bench) to ba karatu ba ne”.
Dariya Hafsat ta yi, “Kuma Mommah duk sai mu taru
mu tare a kotu?” Mammah ta ce, “Eh toh!! Ku haifi ‘ya’ ya ma ku maka su a kotu”. Kunya ce ta lullube ta don haka ta sauya zancen. Mommah ba ni Baba Azumi”. Ba ta nan, ta je Sokkoto auren babbar ’yar Harira, ta samu miji’”. Murna sosai ta yi wa Harira, “Kuma Mommah sai ki ka dandana mana Harira ki ka zo kuma ki ka kwace?” Ta yi dariya ta ce. “Dandani Www.bankinhausanovels.com.ng haukaci kenan. Gani na yi gara ke ma ki dage kamar sauran mata ki nemo aljannarki da kanki ba tare da mataimaki ba. Ki zama (total house-wife), ranar da ki ka haihu na yi miki alkawarin mai aiki, don haka ki
Rufe ido ta yi cikin jin kunya kamar Mommah din na kallonta. Mommah ki daina kira min haihuwa, I’m still your baby!” “You are still my baby Addah! Na daina”.
Dariya suka yi tare. Ki ka ce in kira ki sau dari a rana Mommah? Ai sai Daddy ya ce ba lafiya ba’.
‘To ai ke ce Addah kin bi kin daga min hankali a kan abin da bai kai ya kawo ba, don na aurar da ke sai in yi ta zarya a gidanki? Kina so mijin ya ce surukar ba ta kwarai ba ce?”Dariya ta ke yi sosai wadda rabon da ta yi irinta har ta manta. Kwanaki da watanni sun shude sun tafiyar da farin cikinta na gida, sun dasa wata sabuwar rayuwa a gare ta a gidan Abdul’azeez Dakata. Rayuwa mara dadi da ba ta ko son tunawa. Amma yau ta zo mata da farin ciki mai yawa a dalilai masu yawa, wadanda suka shafe duka bacin ran baya; There’s compassion in him today Www.bankinhausanovels.com.ng (Abdul’azeez), Mommah’s love … Abu daya ya rage da zai cika wannan farin cikin… brother’s love…!!!
‘“Mommah ina Amerikawa? Ina Belgians? Ina Haleem?” Murmushi Mammah ta yi, “Duk za su samu hutu lokaci daya. Watan April. Na yi miki alkawari ranar da zan zo gidanki, Usman da Isma’el sune masu take min baya. Haleem ba yanzu ba”. Wani dan ihu ta saki, sai da Mammah ta toshe kunnenta ta kashe wayar tana murmushi. Daddy ya shigo, fuskarta kawai ya kalla ya ga annurin da ta ke ciki, zuciyarsa ta gaya masa ta gaji da takunkumin da ta sanya wa kan nata ta yi magana da ‘yarta. Dariya ya yi ya zauna yana fadin. “Har an shekara ne?” Cikin rashin fahimta ta ce, “Da me fa?” “Da kai Hafsa gidan miji’”.
Abin ya ba ta dariya sosai, ta ce, “Ai da ma ban ce shekara ba, cewa na yi sai sun shirya kansu. Kuma ita ta kirawo ni da kanta ni ban san ma ita bace tana ta kuka wai na daina sonta”’Cikinsa kamar ya fashe don dariya ya dora, “Ke kuma dama a kan gwiwa ki ke, tana kira ki ka haife?” Harararsa ta yi, harara irin tasu ta manya, “A’ah ka manta nakudurta nake yi’.
“To ai da alama Hausa ba ta ishe ki ba, in aka ce mace na kan gwiwa ai nakuda ake nufi. Yau kin haihu kowa ya huta”. Dakin ta bar masa don ta lura yau zolaya yake ji, ta ce, “In ka fito wanka table is ready”
“Ba fa abincin da zan ci sai kin ba ni labarin wayar nan”. Dakatawa ta yi a bakin kofa, ta juyo ta dube shi hannunta biyu harde a kirjinta. To Daddy me ka ke so ka ji?” “Sun shirya?”Su wa?” Ta yi kamar ba ta gane ba. Ya’yanki mana”. “Danka dai, ni ba ni da wasu ‘ya’ya bayan Suhaana’”To na ji, ina nufin da na da ‘yarki, sun shirya?” “Har ya saya mata waya da jamb form ya cike mata’. Ta fada tana kada masa ido.
Tausayi ta bashi sosai, don shi ya fi kowa sanin Www.bankinhausanovels.com.ng Abdul’azeez da kyar in babu yaudarar mahaifiyarsa cikin al’amarinsa. In zai so abu ba ya sonsa da sauki sai ya gane yana da matukar amfani a gare shi. Tun sanda ya zo babu damuwa ya ce ya amince da auren Suhaanah bayan da fari ya yi tawaye he didn’t trust him! Ko zai so Hafsat not that soon , watakila har sai ta haifa masa ‘ya’ya. Kuma shi a satin nan Attorney General Habib Rufa’i ya kai masa ziyara har Gwags (Gwawalada) karkashin rakiyar Attorneys da yawa, bayan sun gaisa yake gaya masa shi ne Baban Mu’azatu yarinyar da yaron wajensa ke nema ya ce sai ta kare (Law-school), yanzu ta ci karfin karatun nata su zauna su tsayar da lokaci da ta kare sai a yi biki ba sai an kuma jan lokaci ba. Bai ce komai ba saboda kwarjinin mutumin da mutuncinsa hakan kuma ya ganar da shi cewa, Abdul’ azeez bai bar neman Mu’ azatu ba.
Tun ranar yake jin tausayin Hajiya Maryam, yake kirkiro duk abin da zai sa ta farin ciki, ba abinda ya fi ka kasa juya Dan da ka haifa muni a zuciya. Ya kuma yi alkawarin ba zai yi mata zancen ba Abdul’ azeez din zai zuba wa ido ya ga iya gudun ruwansa.
Tun a ranar da hakan ta faru yake cewa su je su ga Suhaanah tana cewa “a’ah da sauran lokaci”. Wayar da ta ce ya saya wa Suhaanah da makaranta da zai maida ta, ya tabbata akwai dalilinsa amma ba SO ba, kamar yadda ita Maryam ta ke tsammani. Ajiyar zuciya ya yi yana kallonta tana ta jera mishi abinci a ‘dining’ ya mike ya isa gare ta ya rike hannunta. Dakatawa ta yi ta juyo ta dube shi, murmushin tausayi ya yi mata. “Ki bar abincin nan bana jin yunwa, mu je ki cuda ni a wanka”. Www.bankinhausanovels.com.ng
A sanyaye ta ce, “Toh”. Don ta ga Daddyn shi ma a sanyaye yake. Haka kawai sai ta ji nata jikin ma ya yi sanyi. Saboda murnar maganar da ta yi da Mammah yau ko abinci ba ta girka ba (quaker oat) ta dauko ta dama cikin sayayyar da ya yo musu. Ta sha ta koshi ta shige daki sai barci cikin kwanciyar hankali.
Ba shi ya dawo gidan ba sai dare, akwai abin da ya rike shi. Wani abun al’ajabi ne ya faru cikin kudurah da Iradar Ubangiji wanda ya gigita Abdul’azeez Dakata, yana tsaka da shirin tafiya garin Adamawa a washegari don fara binciken al’amarin Hafsat duk da cewa bai san kowa a garin ba bincike kawai ya fara ta yanar gizo. Wani sabon Lawyer aka kawo ofishinsu yau wanda haka kawai yake yi masa yanayi da matarsa Hafsat; Barrister Sagir Babbah. Ba halinsa ba ne shisshigi, ko shiga sha’anin mutane ba amma yau sai da ya san yadda ya yi ya shigewa Sagir a bisa dalilai masu yawa. Da suka tashi suka fito ya tadda Sagir ya bude ‘bannet’ din motarshi yana ta tabe-tabe. Kusa da shi ya yi parking’ ya bude motarsa ya watsa shirginsa ya rufe ya iso gare shi, ya ce, Ya ya dai Barrister? Magriba ta kawo kai muna nan”. Ya girgiza kai cikin takaici, “Kai dai bari, karfen nasara ne da ba shi da tabbas. Jiya na karbo motar nan daga gareji, amma har ta kara kwafsa mani. Akwai (Mechanics) a nan kusa ne? Ka san ni bako ne a garin naku duka-duka yau satina biyu a cikin Abuja. Garejin da aka duba min ita can ne kusa da gidana a Kubwa”Dadi ne ya kama Abdul’azeez, ba abinda yake nema yanzu sai kusanci da bakon Barrister wanda ke sanya shi ayyana abubuwa da yawa a kansa a zuciyarsa, tun ganinsa na farko da shi. “Ina ganin mu je yanzu na sauke ka a gida,
Kubwa ba nan ba ce, in dare ya rufa maka a nan da kyar za ka samu abin hawa. Gobe sai in yi wa (mechanic) dina waya ya zo nan ya duba maka ita”.
Sagir ya rufe ‘bannet’ din yana fadin, “Ai kuwa na gode da wannan taimako. Na gode sosai”’. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ba damuwa”. In ji Abdul’azeez, ya fada yana bude masa gaban motarsa ya shiga suka tafi.
Suna tafe suna hira. Abdul’azeez da mawuyaci ne ko shekara ku ka yi ya tsaya yana gaya maka abin da ba ka tambaye shi ba, yau sai ya bude ciki yana ta yi wa Sagir hira rututu, ya gaya amsa shi dan Kano ne ‘yan unguwar Dakata, amma a nan aka haife su a nan suka girma. Last year ya yi aure.
Lawyer ake yi wa lauyanci, amma bai gane ba. Bai kware da hausa ba, bafullatani ne don haka rabin hirarsa da Turanci yake yi wa Abdul’ azeez. Ya ce shi dan asalin Adamawa ne, ya yi dukkan karatunshi a FUTY, ya yi (Law School) a Lagos. Ya dade da fara aiki, kasancewar gwamnatin tarayya yake wa aiki sau biyu ana canza masa wajen aiki. Ya zauna a Kaduna, ya zauna a Jigawa yanzu kuma aka dawo da shi nan Abuja. Yana da mata ‘yar uwarsa da yara biyu.
Daidai lokacin da suka shigo Kubwa yana nuna masa hanya har kofar gidan da ya kama a unguwar. Abdul’azeez ya sauke shi, ya yi nufin juyawa amma Sagir ya dage sai ya shigo sun gaisa da matarsa Rabi’a, ya ce da shi ya yi dare ya baro matarsa ita kadai, amma Sagir ya nace saboda ya ji dadin taimakon da ya yi masa sosai. Www.bankinhausanovels.com.ng
Suna shiga falon zuciyar Abdul’azeez ta yi wani irin harbawa, wata yarinya ya gani mai yawan sumar kai fara sol, an kame mata gashin a tsakiyar kanta da ribbon. Ba za ta wuce shekaru biyar ba, idan har ba warkewa ya yi daga makanta ba wannan Suhaanah ce tana karama, lokacin da suke Jeddah yana ganinta in ya je hutu. Da gudu ta sheko ta rungume mahaifinta, shi kuma ya daga ta sama suna ta magana cikin fulatanci da ba ya ji. Sai ga Mamanta ta billo daga kicin dauke da yaro a hannunta, fara kyakkyawa amma babu wayewar matan zamani sosai a tare da ita, ta gaishe su, mijin na mata bayanin Abdul’azeez da taimakon da ya yi masa cikin fulatanci. Kara rusunawa ta yi tana kara gaishe shi, ta ce cikin ‘yar hausarta mara amo. “Don Allah ka zauna ku ci abincin dare a nan”. Murmushi ya yi, ya ce, “Na baro Madam ita kadai”. “Babu damuwa, ka ba ni waya in yi mata magana”. Dariya ya yi, “Ba za ta fahimci hausarki ba”Ta dan turbune fuska, “Duk gidanmu na fi su iya hausa saboda ni na zauna a cikin Hausawa a Kaduna da Jigawa”’. Murmushi yayi. Yace. Sagir ya gaya mini”. Jan hannunsa Sagir ya yi ya ba shi ruwan alwala ya nuna masa bayin da ke cikin falon, yana gaya masa Rabia bata gajiya da magana ya shiga ya yi alwala, al’ajabin zuciyarsa na kara ninkuwa.
Tabbas in ya rantse ba zai yi kaffara ba yana tare da jinin Hafsat. Idan a da yana kokwanton kamanninta da Sagir kamanni ne kawai ganin wannan yarinyar ya kara tabbatar masa da zarginsa, sannan Adamawa ai Yola kenan. Kuma a cikin Yola JIMETA take. Last week da yayi browsing garin a kokarin sa na soma binciken ya gano Jimetan a cikin Yola ne, itace (Yola North). Idan har bai manta ba shi ne garin da mahaifiyar Suhaanah ta gaya masa nan ne garinsu (Sunan garinmu JIMETA). Allah mai karfin iko! Buwayi gagara misali. Www.bankinhausanovels.com.ng
Shi da Sagir suka yi sallar magriba, ya ja shi ‘dining’ suka ci abinci, tuwon shinkafa ne miyar taushe, ta ji tantakwashi da man shanu. Yaushe rabon da ya ci tuwon shinkafa! Sosai ya ji dadin abincin ya yi musu godiya. Naira dubu biyar ya ba wa ‘yarsu, ya ce ta sha (choculate). Uwar ta yi godiya suka rako shi har bakin motarsa ya ja ya tafi suna daga masa hannu.
Yana tafe a kan titi yana tunani, sanyin A.Cn motarshi na ratsa kasusuwa da bargonsa. Allah ya dube shi ya kusa yanke masa wahala insha Allahu. Zai cika wa Hafsat alkawurrurukan da ya daukar mata a kan lokaci, zai ci gaba da mannewa Sagir tare da bincikarsa a hankali har ya tabbatar da zarginsa ba zai saka gaggawa ba, amma ba zai hada su da Hafsat ba in har ya zamanto da gaske sune ‘yan uwanta, sai wa’adin da ya dibarwa aurensu ya cika. Don haka ko da ya shigo ta dade da yin bacci. Bai damu da ya neme ta ba ya wuce dakinsa don ya san yau ba ta da damuwa tunda ta yi magana da Mammanta, hankalinta ya kwanta.
**********
Kiran lambobi masu tsayi ne ya tashe ta daga barci bayan ta yi sallar asubah ta koma. Code ne na kasar Amurka. Barcin idonta ya wartsake nan da nan sai dai kafin ta amsa kiran, ya katse. Ta ciji yatsa za ta kira, kiran ya sake shigowa. Wannan karon ta yi nasarar amsawa. “Bride of the year”. In ji Www.bankinhausanovels.com.ng (Brothern) da babu kamarsa a wajenta. Tla’ila…” Ta amsa tana dariya. Sunan da ta ke kiransa kenan tana yarinya, ba ta iya cewa Isma’eela ba ko Ishma.
“Mammah’s doll (‘yar tsanar Mammah)”. Shi ma ya rama, kafin ya rufe baki ta rama, “ Bachelors of the century…” (tuzuran wannan karnin).
“Brides of the moment ” (amaren bana). Isma’el ya amsa cooly , muryarsa cike da kulawa da tsokana ga ‘yar uwar tasa wadda ya shafe watanni bai yi magana da ita ba. Ya yi-ya yi Mammah ta ba shi lambarta ta ce ba ta da waya, Yayan nasa kuwa tunda ya bada masa kasa a ido a kan bukatarsa na a hada baki da shi a yaudari Mammah a kan sister n da bai dauketa da irin matsayin da shi ya dauketa ba ya kulla gaba da shi. Jiya kamar daga sama kawai sai ga lamba Mammah ta turo masa wai ta Suhaanah ce. Tun a lokacin ya so kiranta ya yi tunanin dare ne sosai a wajensu, haka ya yi ta daurewa har gari ya waye. He so much missed her, she so much missed him . Akwai wata irin shakuwa a tsakaninsu wadda ta samo asali tun lokacin da suke taya Mammah rainon ta a Jeddah. Ta san da suna tare da ba ta shiga damuwar da ta shiga a baya ba. Hira suka shiga yi, amma ko kadan ban da zancen aurenta ko halin da auren ke ciki, hirarsu suke irin wadda suka saba tun ta yarinta. Ta tambaye shi ina labarin Usman, ya ce yazo America daga Brussels suna tare, ya je excursion birnin Orlando. Tana jin fitar motar Abdul’azeez wajejen karfe takwas na safe, ba su yi sallama ba sai da cajin wayarta ya kare, wayar ta kashe kanta. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta sauko daga gadon ta sanya wayar a caji. Ta duba agogo, karfe takwas na safe. Bandaki ta shiga ta yi wanka, wanke baki, alwala sannan ta fito. Ta samu kanta da yin kwalliya sosai da (lace) mai tsananin taushi, kalar pusher pink da ratsin baki. Sosai kalar da leshin suka karbeta suka kwanta a sassalkar fatar jikinta. Ta fesa turare (christian dior) ta fada kitchen ta daura apron ta hau girki.
Wata zuciyar na cewa, ta dafa da Abdul’ azeez, wata na cewa a’a, ko kin dafa da shi ba ci zai yi ba, ina ma ki ka ganshi? Motsi ta ji ana zura mukulli a jikin kofar falon, ko kadan ba ta ji karar shigowar motarshi ba, domin ta kure qira’ar Abdurrahman Sudaith a gidan gabadaya cikin Suratul Ma’idah, ko ba don haka ba motar Abdu’azeez GMC Terrain ba ta kara, sai in shi ya yi horn . Ba ta fito ba ci gaba ta yi da abin da ta ke yi, tana mamakin me ya dawo da shi a wannan lokacin? Misalin karfe goma sha daya na safe.Zama ta yi ta ci dankali na turawa da agadan data soya da farfesun kaza, ta wanke WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG hannunta da liquid soap ta cire apron din ta adana a mazauninsa ta kora da gwangwanin fanta sannan ta fito zuwa falon. Ya watsar da gown dinsa da wig a tsakar falon, hatta briefcase din ta yi nata wurin. Kwance yake a kujerar da ta fi kowacce tsayi a falon, ko takalmin kafarsa da socks bai cire ba, he don’t even loose his tie, kwanciyar da daga gani za ka fahimci ba ta lafiya ba ce ya yi. Ji ta yi gabanta ya yi mummunan faduwa, ta rabe ta bayan kujerar da yake kwance ta wuce dakinta ta rufo kofa a hankali. Amma ga mamakinta ta kasa zaune ta kasa tsaye, so ta ke ta san me ya same shi, sai dai ta san ba ta da wannan matsayin. To amma ai ko babu aure Abdul’azeez dan uwanta ne kamar Isma’el tunda Mammah ce ta haife shi, ba za ta taba son wani mummunan abu ya faru da shi ba ko rashin lafiya. A haka lokacin sallar azahar ya yi mata, da ma tana da alwala ta matsa wajen ibadarta ta tada sallah.
Samun kanta ta yi a cikin sujjadarta tana yi wa Abdul’azeez addu’a har da hawayenta, a kan ko ma me ye ke damunshi, Allah ya sa ya zo masa da sauki. Da ta idar tana so ta fito falo ta ga halin da yake ciki, amma ta kasa. Zama ta yi ta hada kai da gwiwa sai a lokacin ta tuna da wayarta, ko Mammah za ta kira ta gaya mata ya dawo a cikin wani irin yanayi ba lokacin da ya saba dawowa ba? Wata zuciyar ta ce. “Akul! Ki je ki tabbatar da abin da ya same shi din tukunna, yanzu haka ma ya bar gidan”’.
Mikewa ta yi cikin sanda kamar marar gaskiya ta bude kofa ta fito falon. Yana nan yadda ta barshi awanni uku da suka wuce, ko juyawa bai
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG