SHU’UMIN NAMIJI CHAPTER 8 BY FATYMA SARDAUNA
Www.bankinhausanovels.com.ng
Idanu ta ƙara zarowa domin tabbatar mawa kanta cewa abun da tagani gaskiya ne, ko kuwa, gizo idanunta keyi mata.
Tabbas dagaske ne bawai gizo bane, hoton zanen fuskarta ne raɗau ajikin takardan. Hanunta na rawa haka ta durƙusa ƙasa, haɗe da sanya hanu ta sake ware takardan, tabbas itaɗince babu ko kokonto, zanen fuskarta ce kwance ajikin takardan, amma saboda tsananin kyawun da zanen yayi tamkar azahiri haka zaka gani, hanu tasanya ta shafi zanen, cike da fargaba haɗe da ɗaurewar kai.
Lallai yazama dole a gareta tanemo wanda yake aikata mata waƴan nan abubuwan, kusan kwana uku yanzu kenan ana turo mata da saƙonni, bata kuma san daga waye bane.
Bata damu da ta duba sauran kayan dake cikin kwalin ba, ta tattara shi ta ɓoye acikin kayanta.
Zama tayi dirshan akan katifa tana mai da numfashi akai akai, sosai abun yabata mamaki, tabbas ko ma waye ne wanda yake bibiyarta ta tabbata yayi mata farin sani, amma kuma rainin hankalin yayi yawa, dole zataimawa tufkar hanci. Abun da ta ƙudurta kenan acikin zuciyarta domin iskancin yasoma isarta.
Ƙarfe 6:30 na yammaci Dr Sadeeq yayi wa gidansu Zahrah tsinke, bayan yasha adon sa cikin riga da wando na shadda ƴar bugu mai kyau. Zama yayi acikin motarsa yana mai jiran fitowar Zahrah, domin kuwa yamata waya yasanar da’ita cewa gashi nan, a ƙofar gidansu.
Kafeta da idanu yayi domin kuwa bakaɗan ba tayi masa kyau, cikin shigar doguwar rigan dake jikinta, lallai Zahrah ƙarshe ce wajen haɗuwa dakuma kyau.
Fuskarta ɗauke da murmushi Zahrah ta ƙaraso wajen da motar tasa take fake. Tsayawa tayi ajikin motar, batare da ta buɗe tashiga ba. Ganin haka yasa Dr Sadeeq buɗe murfin motar yafito.
“Yau kuma aji ake jamin ne?” ya tambayeta cikin yanayin tsokana.
Ɗan guntun murmushi tayi haɗe da juya idanunta. “Eh mana, ko bankai naja aji bane?” itama ta tambayesa cikin yanayi na shauƙi.
“Murmushi yayi haɗe da ɗage giransa sama “Kin isa har kinma wuce, ko bakisan cewa keɗin tamusamman bace?”
Hararan wasa Zahrah ta wurgamai haɗe da kawar da kanta gefe, batare da tace dashi komai ba. Haka take al’adar ta ne, bakoda wani lokaci take bada amsar tambaya ba, domin a cewarta shiru ma magana ne.
“Kona zagayo na buɗe miki murfin motar ne gimbiyata, saboda naga kamar bazaki iya ba ?” yafaɗi hakan cike da kulawa.
“A’a ba buƙatar hakan, ni dakaina ma zan iya” taƙare maganar tana mai buɗe murfin motar, haɗe da shiga tayi mawa kanta mazauni.
Shima komawa yayi cikin motar ya zauna. Bayan ya ɗaura duka idanunsa a kanta.
“Kinyi kyau sosai, fiye da ko yaushe” yafaɗi haka yanamai kashe idanunsa.
Ɗanguntun murmushi Zahrah tayi “Nagode” tace dashi ataƙaice
Jinjina kansa yayi azuciyarsa kuwa cewa yayi “Lallai Zahrah tana da aji, duk da ta rasa Virginity ɗinta hakan baisanya ta zama wata sakaka da’ita ba, yanason mace wacce ta’iya takunta, wacce bata sakar baki tayita dariya like mental problem, wasu matan da zaran kace dasu sunyi kyau tofa take zasu wage baki suita ƙyaƙyata dariya, babu wani ɗan jan aji ba komai. nima shaida ce irin su Sister Munubiya idan kace dasu sunyi kyau ae har kyautan kuɗi zasu baka tsabar daɗi🤣”
STORY CONTINUES BELOW
Sake gyara zamansa yayi haɗe da dawo da nutsuwarsa zuwa gareta.
“Zaki’iya zama dani a ko wani irin hali Zahrah?”
Ya jefomata tambayar da bata tsammaci jinsa ba.
Cikin yanayin mamaki Zahrah ta dawo da kallonta garesa, haɗe da cewa “Banfahimci maikake nufi ba”
“Inanufin zaki iya rayuwa dani ako wani irin hali na tsinci kaina? sannan zaki iya yarda na haɗaku ku biyu na aura?” yakuma maimaita tambayar tasa.
Dummm haka Zahrah taji ƙirjinta ya buga, idan da badon kada yace ta rainasa ba, to tabbas da zatace dashi yasake maimaita maganar da yayi. Domin idan kunnuwanta sunjiye mata dai dai, to kuwa bata da amsar da zata basa, domin koda ta basa amsa zata iya faɗuwa, saboda balallai ta bashi amsa dai dai da abun da ya tambaya ba.
Idanunsa duka ya tsura mata, amsa kawai yakeson ji daga bakinta.
Kasa ce dashi komai tayi, domin kuwa haryanzu bata gama haɗa amsar da zata basa ba.
“Nasani dama ba lallaine ki amince ba, Hajiya na ta amince da aurena dake, amma kuma kamar yanda nafaɗamiki a baya, tun tuni akwai zaɓin da tayimin, takuma umarceni da na aureku duka biyu, shin zaki iya aurena a haka, zaki iya zama da wata a matsayin kishiyar ki?” yafaɗi hakan cike da zaƙuwan son jin amsa daga gareta.
Jikinta ne gaba ɗaya yayi sanyi, take taji zuciyarta ta karaya, batasan ya’ake zama da kishiya ba, haryanzu ita yarinyace, bakomai tasani na game da al’amarin duniya ba, tanaji a labarai irin illan da kishiyoyi suke mawa junansu saboda kishi, amma ita yanzu ba wannan bane a gabanta, makomarta na gaba take tunawa, shinya zata kasance?” ta tambayi zuciyarta…
“Kinyi shiru kice wani abu mana zahrah ko zuciyata zata daina bugawan da takeyi” Dr yafaɗi hakan cikin yanayin damuwa.
“Bazan taɓa ƙin aurenka ba, sai dai idan har kaine kace kafasa aurena, sai dai kuma inajin tsoro, bansan mene zai kasance dani gaba ba, dan Allah kada soyayyar matarka ta ruɗeka, ka wulaƙantani, banda wani madogari sai ALLAH sai kuma kai” taƙare maganar cikin rawar murya, yayinda idanunta sukayi rau rau dasu, alamar zasu zubda ƙwalla.1
Ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauƙe, haɗe da sakin ɗan taƙaitaccen murmushi. “Har abada kada kitaɓa tunanin zan wulaƙantaki Zahrah, inasonki da gaske bada wasa ba, namiki alƙwari zan kamanta adalci a tsakaninku, bazan juya miki bayaba insha Allah!” Doctor Sadeeq ya faɗi haka cike da lallashi.
Tuni idanun Zahrah suncika da ƙwalla, amma idan ta tuno cewa bata da zaɓi sai taji gwamma kawai ta daure zuciyarta, haka ta ta ƙaddaran take.
“Kada kiyi kuka kinji My Princess, ina tare dake ako wani lokaci, zankuma share miki dukkanin hawayenki nan bada jimawa ba namiki alƙawari”
Saurin maida hawayenta tayi haɗe da ƙaƙalo murmushin dole ta’aza akan fuskarta, wan nan damuwarta ne ita kaɗai, baikamata ace tabari Dr Sadeeq yagane ba, lallai tun yanzu yakamata ta zama mai juriya.
“Baffa yana gida kuwa?” Dr. Sadeeq ya tambaya.
Wasa da yatsun hanunta tashiga yi, haɗe da kaɗa masa kai alamar “Eh”
Kai yajinjina haɗi da cewa “Yanaga duk jikinki yayi sanyi? banace kada kisa damuwa a ranki ba” cikin kulawa yayi maganar.
Cike da shagwaɓa Zahrah ta langwaɓar da kanta gefe haɗe da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba, “Nibansa damuwa a raina ba” tace haka cikin sanyayewar jiki.
Wani irin kallo maiɗauke da ma’anoni masu yawa Dr.Sadeeq yashiga yi mata, ji yake tamkar yajawota jikinsa ya rungumeta tsam acikin ƙirjinsa, saboda ako da yaushe idan yana tare da’ita wani irin feeling yakeji a jikinsa.
STORY CONTINUES BELOW
“Kije kimin sallama da Baffa inaso zamuyi magana”
“To” kawai tace dashi haɗi da buɗe murfin motar tafita. Dakallo kawai ya bita harta shige gida.
Tana shiga cikin gida ta iske Baffa yana ƙoƙarin fitowa daga ɗakinsa.
“Zahrah har kindawo? badai likitan yatafi ba?” Baffa yajeromata tambayoyi alokaci ɗaya.
“A’a baitafi ba Baffa, shine ma yace nace ma yana son magana dakai” Zahrah tafaɗi haka ga Baffa cikin girmamawa.
“To Allah yasa lafiya, yanzu kuwa zanje na sa mesa” ya faɗi maganar yana mai nufar hanyar fita daga gidan.
Zahrah kuwa ɗakinta takoma.
Sosai maganar Dr.Sadeeq yataɓa mata zuciya, bakomai take hangomawa kanta ba, sai yanda makomarta zai kasance acikin gidansa, tabbas ta tabbatar wacce zai aura, ba irin ta bane, tasan tana da galihu, saɓanin ita da take ko oho, sannan kuma dole zata ga banbanci daga ƴan uwansa, haka ma Dr.Sadeeq ɗin dole zai banbantasu, saboda waccar zai sameta a budurwa, saɓanin ita da zai sameta ba’a budurwa ba, kukane yaƙwace mata mai sauti, cusa kanta cikin cinyoyinta tayi tashiga rera kukanta, har abada cutar da Zaid yayi mata bazai taɓa gushewa ba…..
“Alhmdlh masha Allah! haƙiƙa naji daɗin wannan magana taka Likita, lallai kacika mutumin kirki kuma mutumin ƙwarai, Allah yasaka ma da gidan Aljanna, kuma idan dai Zahrah ce kada kaji komai natabbatar itama tana ƙaunarka, saboda haka nabaka izini ka turo magabatanka, don mu tsaida magana,kuma maganar bayarwa nabaka Zahrah!” Baffa yafaɗi haka cikin farinciki, duk da kuwa cewa dama tun abaya yasan cewa Dr.Sadeeq yanason Zahrah, amma sake tabbatar masa da Dr. ɗin yayi yanzu, yasanyashi jin daɗi, domin shima yanzu burinsa shine ya inganta farincikin marainiyar Allah wato Zahrah..
Farinciki ne sosai yakama Dr.Sadeeq, yaji daɗin aminta dashi da Baffa yayi.
“Nagode da wannan dama da kabani Baffa, Allah yajiƙan magabata” Dr Sadeeq yafaɗa cike da girmamawa.
“Mune da godiya Likita, ai mu ba’abun da zamuce maka saidai fatan alkhairi” Baffa yafaɗa shima cikin jin daɗi, domin yasan Zahrah na auren Dr.Sadeeq wahalanta yaƙare da yardan Allah,saboda yana da tabbacin cewa Dr.Sadeeq zai bata kyakkyawan kulawa, duk da kuwa cewa Dr.Sadeeq ɗin yasanar dashi cewa ba Zahrah ita kaɗai zai auraba, yasanar dashi komai, kuma Baffa yayi na’am da hakan, saboda shi baimaga wani aibu acikin hakan ba, ai namiji mijin mace huɗu ne.
(Nima nace wannan gaskia ne, sbd haka duk me mace ɗaya ya ƙara😜😂)1
Cike da farinciki Baffa da Likita sukayi sallama, yayinda Baffa yakoma cikin gida, ya kumace da Dr.Sadeeq zai turo masa Zahrah suyi sallama.
Tanajin Muryan Baffa a tsakar gida, tayi saurin share hawayenta, haɗe da miƙewa tsaye, domin har Baffa yafara ƙwaɗa mata ƙira.
Fuska cike da fari’a Baffa yace “Likita ke yake jira, zai tafi”
Sumi sumi haka Zahrah ta fice yayinda tabar Baffa yana gayamawa Inna abun da ya wakana tsakaninsa da Likita.
Tun fitowarta yake ta zabga murmushi, kallo ɗaya zakai mawa fuskarsa ka gane cewa yanacikin farinciki.
“Kitayani murna My Princess saura ƴan kwanaki ƙalilan na mallake ki!” Dr Sadeeq yafaɗi haka cike da shauƙi.
Kunyane yakama Zahrah, don haka ta sanya duka hannayenta biyu ta rufe fuskarta, bayan ta ƙaƙalo murmushi ta aza akan fuskar ta..
“Baffa yabani daman naturo magabatana don asa mana ranan aure, kuma insha Allah, gobe magabatana zasu zo, za’asa ranan aurenmu nan bada jimawa ba, so sai ki shirya domin kin kusa zama amaryata!” yanayin yanda ya ƙare maganar kaɗai ya isa taɓa zuciya..
Kunyane yasake kama Zahrah, har batasan sanda murmushi mai sauti ya kufce mata ba, gaba ɗaya ta lura Dr.Sadeeq ya ƙosa da ayi aurensu bata kumasan dalilinsa nayin hakan ba..
STORY CONTINUES BELOW
“Kinyi shiru kodai bakya farinciki ne my princess?” yatambaya.
Ɗan satan kallonsa tayi haɗe da sakarmasa murmushi mai tsayawa a zuciya.
Ƙaran wayarsane ta katsesa daga kallonta da kuma zancen zucin da yakeyi. Ajiyar zuciya ya sauƙe ganin wacce take ƙiran nasa, maida wayar tasa cikin aljihu yayi batare daya ɗaga ƙiran ba.
“Dare yayi Zahrah kishiga gida, zamuyi waya, kikulamin da kanki ” yafaɗi hakan yana me ƙoƙarin shiga cikin motarsa.
Murmushin dole Zahrah tayi haɗe da yi masa saida safe, tajuya ta nufi cikin gida, hakanan taji wani iri a zuciyarta duk da batasan me yasa baiɗaga ƙiran da ake mai ba, amma tana da yaƙinin cewa matar da zai aura tare da itane ta ƙirasa. Saurin kawar da tunanin tayi aranta, domin tuna hakan ma bashida amfani a gareta.
Washe Gari….
Kamar yanda Dr.Sadeeq yafaɗa hakanne ya kasance da da dare bayan sallan magriba Baffa Amadu shida amininsa suka zo gidansu Zahrah don tambayan aurenta, balaifi Baffa yayi musu tarba mai kyau, sunkuma ji daɗin hakan, duk da sun lura cewa suɗin basuda wani ƙarfi, ma’ana arziki…
Magana ta fahimta akayi tsakanin Baffa da kuma Baffa Amadu, a taƙaice dai Baffa yabasu auren Zahrah, yayinda sukuma suka ɗau alƙawarin cewa a cikin satin za’akawo kayan tambaya dakuma na lefe, daga nan sai asa ranan aure, amma basason auren ya ɗau lokaci, saboda rana ɗaya suke so ayi dana Salima.. Da to kawai Baffa ya amsa musu domin shi baida wani abun cewa banda hakan, sai dai a ƙasan zuciyarsa tunani yake taya zai samu kuɗin da zaiyi mawa Zahrah kayan ɗaki, domin dai bayanda za’ayi ace anyi aure ba kayan ɗaki… Haka dai sukayi sallama cike da mutun ta juna…
Baffa ne Zaune akan tabarma ya yi jigum bakomai ke damunsa ba, kamar sha’anin auren Zahrah, Allah yasani ko abincin da za’aci abikin bai tanada ba, balle wata uwa uba kayan ɗakin da za akaita dashi..
“Wai tunanin mekakeyine haka tun ɗazu?” Inna dake zaune gefensa ta jefo masa tambaya.
“Ba dole nayi tunani ba Salame, kinga dai yau iyayen yaron nan Sadeeq suka zo, kuma da duk kan alama basa so aja auren nan yakai wani lokaci, kin kuma san halin dai da muke ciki na rashin kuɗi”
“Yo dama akan wannan kake ɗaga hankalinka? hmm Malam kenan to ai ni banga abun ɗaga hankali anan ba, ca nake shi Sadeeq ɗin yasan duk halin da muke ciki, kuma shi yakawo kansa yace ya na so, bawai mu makai masa dole ba, saboda haka malam ka kwantar da hankalinka, Zahrah ya nema kuma Zahrah’n zamu bashi” Inna tafaɗi haka da’iyaka gaskiyarta…
Kallon Inna kawai Baffa yayi haɗe da girgiza kansa, yasan ma koda yayi ƙoƙarin fahimtar da’ita to fa bazata fahimta ba.
***
“What? Mom cewa fa kikayi wai bani kaɗai Sadeeq zai aura ba, anya kuwa Mom kinji abun da Hajiya Habiba tafaɗamiki da kyau?” Salima tatambayi mahaifiyarta Hajiya Furaira cike da mamakin jin abun da mahaifiyarta tace da’ita..
“Abun da na faɗa miki shi naji daga bakin Hajiya Habiba, Salima kicire Sadeeq a ranki, domin kuwa aurenki dashi bazai taɓa yiyuwa ba, da raina dakuma hankalina bazan taɓa bari ƴata taje kan kishiya ba!” Hajiya Furaira tafaɗi haka cikin ɓacin rai..
Kuka ne ya ƙwacemawa Salima cikin muryan kuka ta soma cewa “Wani irin cin amana ne wannan mom, sai da maganar aurena dashi ta kankama sannan wata banzar magana zata ɓullo, wallahi bazan haƙura da shi ba, bakuma zan taɓa zama da wata a matsayin kishiyata ba, dole ne Sadeeq ya aureni ni ɗaya batare da wata ba, bazan iya jure rashin saba Mom, dan Allah kiyi wani abu” Salima ta ƙare maganar cikin shaɓe shaɓe da hawaye.
“Mekikeso nayi Salima? so kike naje na basu haƙuri akan su sa Sadeeq ya aureki ke kaɗai? ko ko sokike na zubar miki da ƙima daƙuma ƴancinki? Hajiya Habiba ƴar uwatace kuma ƙawata, bantaɓa tunanin haka daga gareta ba, amma bakomai, zanyi maganin abun, kuma ni banzauna da kishiya ba, ƴa tama bazata zuana da kishiya ba, wannan alƙawarine na ɗaukar mawa kaina” still cikin ɓacin rai Hajiya Furaira take maganan…
STORY CONTINUES BELOW
Cikin matsanancin ɓacin rai Salima ta juya ta koma ɗakinta, ji takeyi zuciyarta na tafarfasa, kamar ita ace ta haɗa miji da wata, sam bazai yi wuba, lallai ko da mahaifiyarta bazatayi wani abu ba yakamata ace ita tayi, wayarta da mayafinta ta ɗauka, a fusace ta fice daga ɗakin nata, tana son Sadeeq tun ba yau ba, zata kuma iyayin komai akan sa.
Ɓangaren Dr Sadeeq kuwa tuni yasoma haɗa mawa Zahrah kayan lefe, sosai yake iya ƙoƙarin sa wajen ganin yasanya duk wani abu da yasan zai burge Zahrah.
Ɓangaren Hajiyarsa da Aunty Raliya kuwa, sam basu wani damu da auren ba, hakanne ma yasa suka tura masa aniyarsa, su dai sunfi bada ƙarfi wajen ganin Salima tasamu abun da take so, yayinda Hajiya Furaira ta kafe kan cewa ƴarta bazata auri Sadeeq ba matuƙar ba’a fasa aurensa da Zahrah ba, ranta bai ƙara ɓaci ba ma, sai da taji labarin cewa Zahrah ƴar talakawa ne, sannan kuma bata da wani galihu, ai take ranta yaƙara ɓaci, tace sam bata amince ba, yayinda Salima kuwa ta kafe akan cewa lallai sai ta ruguza auren da Dr.Sadeeq yake nema bayan nata.
Gaba ɗaya Zahrah ta ruɗe, zuwa yanzu wanda yake turo mata saƙo ya uzurawa rayuwarta, a yanda ta fahimta shine duk inda tayi yana biye da’ita, wani babban tashin hankali daya kunnu mata shine, sabbin saƙonnin da yafara turo mata a cikin wayarta, tagama iya hasashenta ko zata gano a ina yasamu number’n ta amma takasa samun daman sanin inda yasamu number’nta, gaba ɗaya yanzu salon saƙonnin nasa sun sauya salo, domin kuwa yanzu saƙon kalamai yaƙe turo mata masu daɗi, wanda kuma duk rabin saƙon yaba kyawunta yake, babban abun daya ƙara ruɗata shine irin maƙudan kuɗaɗen dayake turomata ta waya. sannan kuma idan ta gwada ƙiran number’n da yake turo mata saƙo dashi, bata samu domin da zaran taƙira wayan za’ace mata a kashe wayar take, hakan yasa tafara tunanin cewa kodai gamo tayi…
Ɗan ƙara wayarta tayi alamar shigowar saƙo, take taji gabanta yafaɗi, zuwa yanzu har tsoro take taji wayarta tayi ƙara, domin kuwa tasan idan har wayanta tayi ƙara to ko ƙiran Dr.Sadeeq ko kuma saƙon mutumin da batasan shiba…
Number’n nan ce dai, da aka saba turo mata saƙo dashi, yauma saƙonne aka kuma turowa..
_Tunaninki ya hanani sukuni My Zahrah, ina fatan dai kina lafiya, ina kuma fatan zuwa yanzu kindaina tsoro da kuma mummunan tunanin da kikeyi akaina, kina da kyau My Zahrah, komai naki me kyau da burgewa ne._
Abun da saƙon ya ƙunsa kenan.
Zahrah ta karanta saƙon nan yafi sau biyar, kwata kwata ta kasa fahimtar abun da saƙon yake nufi.
Saurin yin Deleting saƙon tayi haɗe dayin switch off ɗin wayar tata, bazata taɓa yarda wan nan mai saƙon ya haukata mata tunanin ta ba, yazama dole a gareta ta sanja layi.. Kwanciya tayi lamo tana mai addu’an Allah yasa bacci ya ɗauketa. domin bacci ne kaɗai zai kawo mata sauƙi a zuciyarta.
Zaune suke dukansu a ɗan madai dai cin tsakar gidan nasu, domin dama idan dare yayi sukan zauna a tsakar gida su ɗan taɓa hira, haka al’adarsu take..
Wani yarone yashigo cikin gidan bakinsa ɗauke da sallama, haɗa baki sukayi wajen amsa masa sallaman.
“Wai ana sallama da mai gidan nan” yaron yafaɗa.
“To kace inazuwa” Baffa yafaɗi haka yana ƙoƙarin miƙewa tsaye.
Kusan tare suka fita shida yaron sai da Baffa yaji wani irin faɗuwar gaba sakamakon wasu irin danƙara danƙaran motoci guda biyu da yagani fake a ƙofar gidansa.
Ja Baffa yayi ya tsaya turus yana me mamakin ganin waƴan nan rantsatstsun motocin a ƙofar gidansa, “Allah yasa da alkhairi suka zo” Baffa yafaɗi haka a cikin zuciyarsa.
Buɗe murfin motar Alhaji Ma’aruf yayi haɗe da sako ƙafarsa waje.
Sake waro idanu Baffa yayi haɗe da kafe Alhaji Ma’aruf dake ƙoƙarin fitowa daga cikin mota da ido.
Fuska cike da annuri Alhaji Ma’aruf ya ƙaraso wajen Baffa, haɗe da miƙa masa hanu alamar su gaisa.
Cikin ɗari ɗari Baffa ya ɗago hanunsa haɗe da miƙamawa Alhaji Ma’aruf suka gaisa.
“Inafatan kaine ma mallakin wannan gida, kuma Baffa ga Zahrah?” Alhaji Ma’aruf ya tambaya.
Saida Baffa yaji zuciyarsa tayi tsalle sakamakon jin an ambaci Zahrah, Allah yasa ba wani abun Zahrah tajawo musu ba.
“Eh nine ranka ya daɗe, Allah yasa lafiya?” cikin dar ɗar Baffa yafaɗi hakan.
Murmushi irin nasu na manya Alhaji Ma’aruf yayi haɗe da kallon Baffa…”Nazo da magana mai mahimmanci, inaga zaifi kyautuwa kabiyoni cikin mota mu tattauna, don maganar bata tsaye bace”
Kallon Alhaji Ma’aruf Baffa yashiga yi, haɗe da excort ɗin da suke bayan Alhaji’n, tabbas Alhaji Ma’aruf baiyi masa kama da irin mugayen mutanen nan ba, domin daga ka gansa zaka fahimci cewa dattijon arziki ne, hakanne yasa Baffa bai musa masa ba, yabisa zuwa mota..
Acikin mota kuwa bayan sun sake gaisawa, Alhaji Ma’aruf yayi gyaran murya haɗe da cewa…
“Sunana Alhaji Ma’aruf, kasancewar dare ne yasanya ka kasa shaida fuskata, domin ni ba ɓoyayyen mutum bane. Nazo gare ka ne domin nemawa ɗana Auren Ƴar Wajenka Zahrah, ina fatan bazaka watsa mini ƙasa a ido ba”…….Shirune yashiga tsakanin Baffa dakuma Alhaji Ma’aruf, bakomai ne kuma yasa hakan ba face nazari da Baffa yashigayi, lallai wannan abu da mamaki yake, neman aure mace ɗaya duk alokaci guda.+
“Naji kayi shiru, Allah yasa dai ba wata matsala bace ta faru” Alhaji Ma’aruf ya faɗa, domin ko kaɗan baya fatan wani abun da zai zo ya gifta har ya katsewa Zaid cikar burinsa..
Gyara zama Baffa yayi haɗe da sauƙe ajiyar zuciya..
“A gaskiya Alhaji bazan ɓoyemaka ba, yanzu haka na bada auren Zahrah ga wani, wanda kuma tariga da ta aminta dashi, sai dai bazan yi saurin yanke hukunci ba, idan har Zahrah ta aminta dashi ɗan wajen naka, shikenan, saboda ni bazan mata dole ba, duk wanda takawo tace shitake so, to shi zan aura mata, amma kuma a iya sanina babu wani wanda yake zuwa wajenta, bayan likita’n dana bashi aurenta, sai dai kuma bansan shi ɗan wajen naka a ina yaganta har yaji yanada burin aurenta ba”
Ɗan jim Alhaji Ma’aruf yayi haɗe da sauƙe ajiyar zuciya. Lallai yakamata yayi duk abun da zaiyi, domin shikansa yanaso Zaid yayi aure, amma kuma yasan cewa nema cikin nema haramunne, tunda gashi har shi Baffan yarinyar ya ri ga daya shaida masa cewa yabada auren yarinyar ga wani, yazama dole suyi haƙuri kenan.
“Naji maganarka Malam Hayatu, nakuma gamsu, amma bayar da aurenta ga wani, ae bashi yake nufin anɗaura aurenta ba, koda yaushe ra’ayin mutane yana iya sanjawa, saboda haka zanbaka dama kayi tunani mai kyau” Alhaji Ma’aruf yafaɗi haka bayan yaciro wasu maƙudan kuɗi a cikin aljihun rigarsa ya ɗauramawa Baffa akan cinyarsa..
Ware idanu Baffa yayi sakamakon ganin maƙudan kuɗin da Alhaji Ma’aruf yaɗaura masa akan cinyarsa, badai yana nufin duk nasa bane.
Murmushi irin na manya Alhaji Ma’aruf yayi haɗe da cewa “Kada kadamu bawai nabaka kuɗinnan bane,don ka bawa ɗana auren ƴarka ba, nabaka ne kawai saboda shi meyin alkhairi ako da yaushe baya rasawa”
Cikin sanyin jiki Baffa yayi masa godiya haɗe da buɗe murfin motar yafita, zuciyarsa cike da ɗunbin mamaki…
Baffa na fita daga motar Alhaji Ma’aruf yamawa driver’nsa umarni akan cewa su tafi, aikuwa ba ɓata lokaci drivern yatada mota..
Saida suka ɓacewa ganinsa kafun Baffa ya iya ɗauke idanunsa daga kansu, kuɗin dake hanunsa yashiga juyawa, “Lallai wannan mutumi yanada ihsani, amma kuma yazo da babbar magana, da ace yanada dama to da a yanzu yabawa ɗan Alhaji Ma’aruf ɗin auren Zahrah, to saidai kuma yanzu ya saduda, sakamakon wa’azi mai tsoratarwa dayaji akan cutar da maraya, da kuma irin azabar da za’amawa mai cutar da maraya, tundaga wannan lokacin yaƙudurta aransa cewa bazai sake cutar da Zahrah ba, yanzu ma dolensa zai bata zaɓi, domin ita zatayi zaman auren ba shiba…
Yanashiga gida Inna da takasa zaune takasa tsaye, ta ƙaraso wajensa da sauri tana me cewa “Lafiya naga ka jima, har nafara jin tsoro naɗauka irin mutanen nan ne masu garkuwa da mutane suka kamaka, domin na leƙa naga wasu fankama fankaman motoci a waje”
STORY CONTINUES BELOW
Harara Baffa ya wurgamata, haɗe da jan tsuka “Bazaki taɓa sanja halinki ba ko Salame, wato ke dai koda yaushe kai da kuma idanunki sunaga ƙofar gida, kullum cikin leƙe kike, wato dai har dare ma yanzu leƙe kikeyi, Allah ya kyauta” yafaɗi haka yana mai nufar hanyar ɗakinsa…
Fuska Inna ta ɓata haɗe da kafe aljihunsa da idanu, domin kuwa tuni idanunta sun ƙyallaro mata tudun da aljihunnasa yayi, ƙwafa tayi haɗe da rufa masa baya, koma mene sai
taje taganema idanunta, idan ma abuncine aci da’ita..
Sake gwalo idanu Inna tayi, ganin kuɗin da Baffa ya’aje akan gadonsa, “Malam kace farar fita kayi, a shema baƙin arziki ne, nayi musu mummunar fahimta, ae irinsu muke fatan suta zuwa” washe da baki ta ƙare maganar…
“Akwai matsala Salame, amma jeki ƙiramin Zahrah” Baffa yafaɗa bayan yayimawa kansa mazauni, a bakin gadonsa.
“Yanzu kuwa” Inna tafaɗa tana me fita daga ɗakin..
Zahrah ce zaune akan gadonta, game take bugawa a cikin wayarta, da’alama dai game ɗin yayi mata daɗi, domin kuwa ita kaɗai sai murmushi take.
Inna ce tashigo cikin ɗakin haɗe sa shaida mata ƙiran da Baffa keyi mata, haka nan taji gabanta yafaɗi. Tare suka fito da Inna, dukansu suka ɗunguma zuwa ɗakin Baffa’n…
Gyara zama Baffa yayi haɗe da maida kallonsa ga Zahrah, wacce ta duƙar da kanta ƙasa.
“Bayan Likita akwai wani wanda kikasan yanasonki, ko kuma kika basa dama ya turo magabatansa wajena?” Baffa yatambayeta cike da kulawa.
“A’A Baffa bana mu’amala da kowa sai likita, bankuma bawa kowa izinin zuwa wajenka ba” tafaɗi haka cike da girmamawa, duk da kuwa cewa kanta ya ɗaure da jin tambayar da Baffa’n yayi mata…
Kai Baffa yajinjina haɗe da cewa “Ƙiran da akai min ɗazu wani ne yazo nemawa ɗansa aurenki, shine nayi tunanin ko kinsan da zuwansa”
Wani irin bugawa Zahrah taji ƙirjinta yayi, har batasan sanda ta ɗago da idanunta ta kalli Baffa ba.
Baffane yacigaba da cewa “Bansan ko su ɗin suwaye bane, amma ban ɓoyemusu komai ba, nasanar dasu cewa nabada aurenki ga wani, amma mahaifin yaron yace yabani lokaci nayi tunani, saboda hakane ma naƙiraki domin ni bazan miki dole ba, zanbaki dama ne ki zaɓi wanda kikeso”
Take idanun Zahrah suka kawo ƙwalla, sakamakon jin wani baƙon al’amari dayake shirin kunno kansa cikin rayuwarta.
“Kinyi shiru, ki kwantar da hankalinki bazan miki dole ba Zahrah, kema kina da ƴan ci, zan kuma baki ƴancin ki, sai dai abun da nakeson sani shine wanene yaron nasa, saboda bai yiwuwa a haɗaki aure da wanda bamusani ba, amma idan ke kinsan sa shikenan ba damuwa”
“Bansan saba Baffa, kuma ma koda nasansa bazan aminta dashi ba, saboda idan nayi haka ban yi mawa Dr.Sadeeq adalci ba” Zahrah tafaɗi haka cikin sanyayewar murya…
“Adalci, kaji shirmen banza don Allah Malam, wani adalcine yarage miki, wanda yawuce ki kai kanki cikin arziki kicisa yanda yakamata, saidai ko inkuma baƙin ciki kike mana”
Inna ta tsomo bakinta cikin maganar batare da angayyaceta ba…
“Tashi kije Zahrah, idan suka sake zuwa zan sanar dasu cewa hakan da sukeso bazai yi wuba” Baffa yafaɗa, yana mai wurgamawa Inna harara..
Cikin rashin ƙwarin jiki haɗe da ɗaurewar kai Zahrah tabar ɗakin.. Haushin Zahrah da Baffa ne yacika zuciyar Inna, amma ganin yanda Baffa yahaɗe fuska bai bata damar yin ƙorafi ba yasanya itama tafice daga ɗakin tana me ƙananan maganganunta wanda ita kaɗai tasan metake cewa..
Zama Zahrah tayi jigum haɗe da zurfafa tunanin ta, ba’abun dake bata mamaki da ɗaure mata kai, kamar neman aurenta da Baffa yace anzo anyi, “To waye zai zo neman aurenta batare da saninta ba? batare da ta kuma sanshiba, lallai koma waye baisan meyafaru da’ita ba, domin tasan daya sani, da baiyi gigin turo magabatansa nema masa aurenta ba” Haka dai tayita saƙawa da kuncewa har bacci ya ɗauketa……
STORY CONTINUES BELOW
Cike da tsananin mamaki Zaid yake kallon mahaifinsa, sakamakon ji da yayi mahaifin nasa nacewa “Wai anbada auren Zahrah’nsa ga wani” ” Anya kuwa gidan su Zahrah Dad ɗinsa yaje? kodai yayi mistake ne yaje wani gidan amadadin nasu Zahrah?” duk wannan tambayar kansa ya mawa.
“Inaga zaifi kyautuwa kanemi wata My Son, domin kafasan nema cikin nema haramunne” Alhaji Ma’aruf ya faɗa yana me kallon ɗan nasa.
“Inaga ba gidansu kaje ba Dad,
domin ni nasan Zahrah tawace, baza’a bawa wani ita ba bayanni” Zaid yafaɗi haka bayan yayi sipping holandia milk ɗin dake aje cikin glass cup ɗin dake gabansa.
Kallon mamaki Alhaji Ma’aruf, yashiga yi mawa Zaid, sakamakon jin abun daya faɗa.
Baisan me yake shirin faruwa da ɗansa ba, amma tabbas ya hango wata irin soyayya acikin idanun Zaid ɗin me matuƙar zafi, wanda Zaid shikansa baisan da’ita ba…
“Akwai matan aure dayawa Zaid, zaifi kyau ka zaɓi wata, koda a cikin ƴan uwankane” Alhaji Ma’aruf yafaɗi haka cikin lallashi.
Murmushi kawai Zaid yayi haɗe da kallon mahaifin nasa…
“Kai mahaifinane saboda haka bana iya ɓoye maka komai, a gaskiya banjin zan iya zama da wata daban, idan ba Zahrah ba, zanyi komai da kaina kawai” yafaɗi haka yana me miƙewa tsaye… Da kallo kawai Alhaji Ma’aruf yabi sa dashi har ya fice daga cikin falon nasa. Ajiyar zuciya yayi haɗe da cewa “wataƙila idan kuɗi na magani, to zasu maya Zaid, ta hanyar samo masa auren Zahrah”
(hmm bakomai ake nema a samu ba, bakuma komai kuɗi yake iya saya ba)
Kai kawo Zaid yashigayi a tsakiyar tankamemen aljannar duniyar falonsa, gaba ɗaƴa yarasa me yake masa daɗi, shin maganar da Dad ɗinsa ya faɗa masa cewa anbada Zahrah, gaskiya ne kokuwa Dad ɗinnasa ne yayi mistake wajen gano gidan su Zahrah, dudduniya babu wani mahaluƙi daya isa yimasa shamaki da muradinsa, lallai lokaci yayi daya kamata ya bayyana kansa gareta, baidamu da yanda zata ɗaukesa ba, shidai burinsa kawai shine ya mallaketa amatsayin matarsa, lallai yanzune zai gudanar da babban takunsa, sannan kuma yazama dole yagano bayanshi wayake bibiyan Zahrah, har ake yunƙurin aura masa ita, dole yagano wannan, domin yayi imani cewa Zahrah tasa ce…
***
Fitowarsu daga lecture kenan, wayarta tayi ƙara alamar shigowar saƙo,, ko kaɗan batayi mamaki ba, domin zuwa yanzu tasaba da saƙonnin da’ake turo mata batakuma san waye yake mata hakan ba.
Ajiyar zuciya ta sauƙe bayan ta gama karanta saƙon, yau madai kalamaine masu tsayawa a zuciya, ɓoyayyen mutumin nata ƴarubuta mata, sai dai kuma duk sanda ya turo mata da saƙo, idan takaranta kalaman sukan tsaya mata arai suna kuma yawan yi mata yawo a ƙwaƙwalwarta, koda sau ɗaya ne bata taɓa tunanin mayar masa da amsa ba, amma hakanan taji yau tanason tambayarsa ko shiɗin waye.
“Waye kai?” Abun da tarubuta tatura masa kenan.
Zaid dake kwance cikin wata luntsumemiyar kujera yana sipping wine yaji wayarsa tayi ƙara alamar shigowar saƙo, ɗaga wayartasa yayi yaduba, murmushinsa me kyau yayi bayan yagama karanta tambayar nata..
“Kinason ganina?” shima yamayar mata da tambaya, tahanyar tura mata saƙo.
Zahrah na karanta saƙon tasoma typing kamar haka….”Mezai hana idan zaka bayyana kanka” tana gama rubutawa tayi sending..
“Kishirya ranan friday 8:00 pm zankawomiki ziyara, ina fatan zakiji daɗin ganina, sannan zan taho miki da kyakkyawan surprise” yana tabbatar da cewa saƙon ya isa zuwa wayarta, yayi switch off na wayarsa, sake gyara kwanciyansa yayi ajikin kujeran, haɗe da lumshe idanunsa, jiyake mararsa tana yi masa ciwo, kusan kwana uku kenan da yake fama da wannan ciwon maran, hakan kuma yasamo asali ne da wata irin sha’awa da ta damesa, sai alokacinne ma yake tuna cewa yajima baiyi sex ba, lallai akwai abun da yake damunsa, Zaid ɗin da baya iya kwana ɗaya baiyi sex da mace ba, wai shine yanzu yake iya kwanaki batare da yayi sex ba, shida mace ɗayama bata isan sa, amma sai gashi, yau ɗayan ma, yakasa nutsuwa yakusanceta, lallai yanzu kam yayarda da cewa akwai abun dake damun jiki da zuciyarsa….
Ɗan jim Zahrah tayi bayan tagama karanta saƙon nasa, idan bata mantaba yau Tuesday kenan saura kwana biyu jumma’a tayi, lallai tanaso taga wanene wannan wanda yaɗau lokaci yan ɓata tunaninta, ta wani ɓangare na zuciyarta kuwa, ji takeyi tamkar akwai wani gagarumin abu dazai faru da’ita, yayinda idan ta tuna aurenta da Dr.Sadeeq saitaji ta zama wani iri da’ita, bakuma aurenta da Dr. ɗinne bataso ba, a’a kawai dai tanaji ajikinta kamar basu dace da juna ba ita dashi…
Dariya sosai Salima tashiga yi, sakamakon labarin da ƙawarta kuma aminiyarta Laura tabata yanzun. Wani irin daɗi taji haɗe da sanyi acikin zuciyarta, gaba ɗaya labarin Zahrah Laura ta kwashe ta sanar da Salima, wanda Laura ta samo asalin labarin Zahrah ne daga bakin wata Asma da take unguwarsu Zahrah’n kuma har school ɗinsu ɗayama da Zahrah..
“Dama akan sauran wani Doctor yake wulaƙantani hadda jamin aji, hmm lallai kuwa bazanyi kishi da mai aji bama ballentana marar aji” Salima ta faɗi haka cike da kunfar baki…
“Ae magana taƙare Salima, kamar yanda na faɗamiki, tashi kawai zamuyi muje hargidansu, muci mata mutunci mukuma gargaɗeta da tafita hanyar Doctor Sadeeq” Laura tafaɗi haka cike da son zuga Salima.
“Gaskiya ne nima ina bayan maganarki Laura” wata wacce take zaune gefen Laura ta faɗi haka, tana me taɓe baki..
Kallonta Salima tayi haɗe da cewa “Shiyasa nake sonki ƙawata, bakida wasa, wajen sawa ayi rashin mutumci, idan kinshirya muje gidan nasu yanzu, domin akan Doctor sai inda ƙarfina ya ƙare” Salima tafaɗi haka tana maitashi daga zaunen da take.
Motar Salima suka shiga su duka ukun yayinda Laura ke tuƙasu, domin itace jagoran tafiyan kasancewa har gidansu Zahrah ta sani, saboda tasa Asma ta nuna mata….
Zahrah ce zaune a tsakar gida bisa kan tabarma, kwanon abincine aje a gabanta, gaba ɗaya ta kasa tsayawa taci abincin yanda yakamata domin kuwa yau Thursday gobe ne kuma haɗuwarsu da mutumin dayake ɓoye mata kansa, duka nutsuwarta baya gareta, hakanan takejin babu alkhairi a haɗuwarta da mutumin…
Wani irin bangaja da aka mawa ƙofar gidansu shiyasanyata ɗago kanta takai kallonta zuwaga ƙofar gidan nasu..
Wasu tsalan tsalan ƴan mata su uku ta gani, tsaye ko wacce ta kafa makeken glass akan idonta, yayinda suke taunar cingam cike da iyawa haɗi da salo……Baki da hanci Zahrah ta sake tana kallon waƴan nan ƴan matan da suke tsaye suna me yimawa cikin gidannasu kallon wulaƙanci haɗe da ƙyama..+
Cire glass ɗin dake idanunta Salima tayi, haɗe da watsamawa Zahrah wani irin kallo mai ɗauke da mugun tsana, cike da ƙyama ta furzar da yawu, haɗe da kallon Laura “Itace wan nan?” Salima ta tambaya tana me nuna Zahrah da hanunta cike da taƙama.
“Eh itace ƴar matsiyata” Laura ta faɗa tana yanatsina fuska.
“Lafiya kuwa bayin Allah? su waye ku? Zahrah ko kinsan sune?” Inna da fitowarta a ɗaki kenan ta tambaya, Tana me mamakin ganinsu haɗi da aljabi.
“Ba alkhairi bane ya kawomu, saboda baku kai matsayin da zamuzo muku da alkhairi ba, sunana Salima, nazone domin najawa wannan matsiyaciya kuma karuwar ƴar taku kunne, koda wasa Doctor Sadeeq basa’an aurenta bane, saboda yawuce ajin macen da taraba mutuncinta a titi” takawa taci gaba da yi cikin isa harta ƙarasa gaban Zahrah, da ta kasa ko motsi… “Banzo danna cutar dake ba, amma tabbas idan kika sake nakuma dawowa cikin gidan nan to zanyi miki babban illa, rabuwa dashi zai fi miki, idan kuma kika ƙi, hmmmm zakisan cewa bakin rijiya bawajen wasan makaho bane, bake kaɗaiba, hatta tsohon da yake riƙe dake sai ya ɗanɗana” Salima tana kai ƙarshen zancen nata tamaida glass ɗin ta dake riƙe a hanunta, haɗe da kallon su Laura “Muje” tace dasu, babu musu kuwa suka rufa mata baya, suna tafiya suna kareraya…
Tamkar statue haka Zahrah tayi ƙasaƙe tana kallonsu, harsuka fice daga cikin gidan.
Sallallami Inna tashiga yi haɗe da tafa hannuwanta duka biyu, “Lallai kuwa wa ƴan nan ƴan iska masu jajayen fuskar suncika marassa ta’ido, rashin kunya har cikin gida” Inna tafaɗi haka cike da mamaki.
Kai kawai Zahrah ta girgiza, haɗe da jawo kwanon abincinta ta ci gaba da ci, batare da ta tankawa Inna da take ta ɓaɓatu ba,, sai dai kuma sosai maganganun Salima suka daki zuciyarta, har wani ɗaci takeji a cikin maƙoshinta.. Tura abincin takeyi amma jinsa take tamkar maɗacin dayafi kowanne ɗaci, har wani zafi takeji a ƙirjinta. Tana gama cin abincin, ta kora da ruwa, haɗe da tashi kai tsaye tanufi ɗakinta.
“Karuwa” sunan da Salima taƙirata dashi yafiye mata komai ciwo, tunda take a duniya ba’a taɓa ƙiranta da sunan karuwa ba, sai a yau ɗin, wasu irin zafafan hawayene taji sunshiga gangarowa daga cikin idanunta, durƙushewa tayi a ƙasa haɗe da soma rusa kuka, filla filla kalaman da Salima ta faɗa mata suke dawowa cikin kanta, koda wasa bata taɓa tunanin za’afaɗi kalma na ɓatanci masu muni irin haka akan ta ba.
“Kacuceni Zaid, Kacuceni, me yasa ka aikata haka agareni, shin koda sau ɗaya ne bakayi tunanin yanda rayuwata zata kasance ba, bazan taɓa yafe maka ba Zaid har kuwa nakoma ga mahaliccina” cikin kuka ta ƙare maganar, domin kuwa sai yau tasake tabbatar da cewa Zaid ya cuceta, takuma ƙara jin matsanancin zafi dakuma ciwo akan fyaɗen da Zaid yayi mata.. Abu kamar wasa haka Zahrah tayita kuka tamkar ranta zai fita, sai gashi cikin mintuna ƙalilan ciwon kai yakawomata ziyara, wanda har sai da yakaita ga kwanciya.. Ƙiran Dr.Sadeeq ne yashigo cikin wayarta amma tanaji tana gani takasa picking call ɗin har wayan ta tsinke, taƙi ɗaga wayan ne kuma don bataso yafahimci cewa tana cikin damuwa. Wani ƙiran nasa ne kuma yasake shigowa, still dai har wayan ta katse, Zahrah bata ɗauka ba, domin har yanzu bata dawo cikin nutsuwarta ba.. Ƙira na uku ne yakuma shigowa cikin wayarta ta, ƙoƙari tayi wajen ɓoye damuwarta haɗe da ɗaukan wayar ta kara akan kunnenta..
STORY CONTINUES BELOW
Ajiyar zuciya Dr.Sadeeq yasauƙe sakamakon ji dayayi ta ɗaga wayan.
“Wani irin laifi me girma na’aikata haka da aka ƙi amasa wayata?” Dr.Sadeeq yatambaya.
Cikin sanyin murya Zahrah tace dashi “Bana kusa ne shiyasa”
Wata ajiyar zuciya yakuma sauƙewa cike da kulawa yace “Naji muryarki ta sauya ina fata dai kina halin lafiya?” cikin kulawa ya ƙare maganar.
“Lafiya ƙalau” tabasa amasa a taƙaice.
“Yakamata nazo muyi magana domin inaso nasan irin shirye shiryen da zakiyi, idan lokacin auren mu ya gabato, kinsan yakamata ace anfarayin komai akan lokaci, yanzu ina tuƙi ne idan na tsaya zanƙiraki”
“To” kawai ta’iya cewa dashi, har ya katse ƙiran.
Tanacire wayar akan kunnenta saƙo yashigo cikin wayar.
“Nakan ji wani iri a jikina idan har kina cikin wani irin yanayi, ki daina sa kanki a damuwa, saboda zaki iya cutar da zuciyarki, nikuma bazan so haka ba, saboda kece muradina” abun da saƙon yaƙunsa kenan..
Tsuka Zahrah tayi bayan tagama karanta saƙon, haɗe da kashe wayarta ta baki ɗaya, jira take kawai Allah yakaita gobe taga wayane yake raina mata hankali haka, daga goben kuma zata takamawa komaye birki, domin kuwa ko ma wayene bazai taɓa burgeta ba, zuwa yanzu babu wani ɗa Namiji da zaiyi tasiri acikin zuciyarta.
Zaid ne kwance akan makeken gadonsa wanda yasha bedsheet na alfarma, kwanciyar nan yayi irin wanda ba kyau, wato rufda ciki, wata doguwar takarda ne riƙe a hanunsa, wanda take ƙunshe da duk wani abu daya ƙunshi Dr.Sadeeq daga kan sunansa aikinsa har zuwa mazauninsa, dakuma a halinsa, kyakkyawan bincike Zaid yasa a kayi masa akan Doctor ɗin, saboda a cewarsa babu wanda ya’isa ya shiga huruminsa, saboda Zahrah tasace shi kaɗai, saboda haka dole ne zaitakawa Dr.Sadeeq birki..
Murmushine ya bayyana akan fuskarsa bayan yasanya duka hanunsa biyu ya shafi sajen dake kwance akan fuskarsa,, shi kansa yaƙosa gobe tayi yaga Zahrah’n sa, duk da kuwa cewa yana biye da duk wani shiga da ficenta, amma kwata kwata baya gajiyawa da ganinta, sam baisan meke damunsa ba, zuwa yanzu yafara kokonto dakuma tunani anya ba wannan abun da yakeji shi ake ƙira soyayya ba kuwa? Idan kuwa harda gaske abun nan da yakeji a game da Zahrah shi ake ƙira soyayya, to tabbas yakamu da so matsananci, sai dai kuma bayida ikon tabbatarwa kansa cewa so yake, hakanne ma ya hanasa gane wanni hali yake ciki, ko da wasa bai taɓa tunanin cewa Zahrah zata ƙisa ba, saboda haka ako da yaushe cikin ƙarawa kansa ƙwarin guiwa yake….
FRIDAY
Rana bata ƙarya, ranan yau ta kasance Friday kuma yaune Ɓoyayyen mutumin ta yayi mata alƙawarin baiyana kansa gareta, sai dai kuma baƙon al’amarin da ta wayi gari dashi yasoma tsinkar mata da zuciya, haɗe da sanyayewar jiki, domin kuwa yau ta tashi tana me jin faɗuwar gaba, haɗe da bugawan zuciya da akai akai, hakan kuwa baƙaramin tsoro yajefata ciki ba, saboda bata taɓa mantawa irin wannan faɗuwar gaban ta dinga ji a ranan da mummunar ƙaddaranta zata rusketa,, sai dai kuma babu abun da yagagari Allah, don haka ta shiga yin addu’o’i acikin zuciyarta, saboda ta samu salama..
Ƙarfe Uku na yammaci de de suka fito a lecture’n ƙarshe da suke dashi na wannan ranan, gaba ɗaya sukuku haka ta wuni a cikin school ɗin, Husnah tayi tambayan har ta gaji, akan ta faɗa mata meke damunta amma tace ba komai, to me zatace mata? ita kanta batasan meyake damunta ba.
Su Husnah ne suka kawota har ƙofar gida, saboda yanzu Dr.Sadeeq aiki yamasa yawa sosai, ga aikin office ga kuma hidiman hada hadan biki, gaba ɗaya baya samun isashshen lokaci, hakan yasa idan sun tashi a school take shiga motar da ake zuwa ɗaukar Husnah su sauƙeta a gida…
Tun azaure take ta kwaɗa sallama harta shigo cikin gidan nasu, amma babu wanda ya amsa mata, hakan yasa ta tabbatar cewa bakowa acikin gidan, har ɗaki ta leƙa amma babu Inna babu alamarta, saboda haka kai tsaye ta wuce ɗakinta. Zama tayi jigum tamkar wacce aka mawa mutuwa, fargaban haɗuwa da ɓoyayyen mutumin nan take, hakanan takeji dama bata nemi ganinsa ba, saboda gaba ɗaya jikinta yagaya mata babu alkhairi a haɗuwarsu, sai dai kuma babu yanda ta’iya tunda ya tabbatar mata da cewa yau ɗin zaizo, ganin da tayi tunani na shirin damunta, yasa ta ɗauko alƙur’ani mai girma tasoma karantawa, saboda hakan yana sauƙar da salama sosai acikin zuciyar wanda yake cikin ƙunci da fargaba….
STORY CONTINUES BELOW
Tana kai sujjadar ƙarshe ta sallan isha tafashe da wani irin kuka me tsuma zuciya, hakan yafarune kuma saboda ta kasa control ɗin kanta, sosai faɗuwar gaban da takeji yake tsanan ta aduk bayan wasu mintuna.. Cikin kuka tasamu ta sallame sallan isha ɗin, bayan ta gama faɗawa ALLAH buƙatunta, tana me kuma neman sauƙi a garesa, idanunta da suke cike da hawaye ta ɗaga haɗe da maida kallon ta ga yagalgalellen agogon bangon dake ɗakin nata, ƙarfe bakwai da arba’in, saura mintunan da basufi Ashirin ba yaƙaraso kenan, domin ƙarfe takwas yace mata zai zo…
Bugawan da agogo yayi 8:00 pm, yayi dai dai da bugawar zuciyar Zahrah, har saida taji cikinta yabada wani sauti. Kallon agogo takumayi akaro na barkatai, bazata iya tantance me takeji ajikinta ba, tsoro ne kokuma ruɗewa ne, takasa banbancewa.
Idanun Zahrah nakan agogo har ƙarfe takwas da minti biyar, ko ƙyafta idanun ta batayi ba, azahiri agogon take kallo, amma a baɗini ba da idanunta take kallo ba, da ƙwaƙwalwarta take gani, kallon agogon kawai take amma bata fahimta saboda tunaninta ba a kansa yake ba.
Saƙone yashigo cikin wayarta, wanda yayi dai dai da kusan ɗaukewar numfashinta.
“Inaƙofar gidan ku” bakinta na rawa haka takaranta saƙon saikace wanda aka turomata saƙon ranar mutuwarta.
Takai kusan minti huɗu tana sake maimaita karanta saƙon, sai kace wanda aka yo saƙon da wani harshe bana hausa ba, idan kaga yanda take karanta saƙon zakai tunanin bata iya hausa bane, kokuma bata gane abun da saƙon yake nufi ba, bakomai yasa hakan ba kuma face tsoro da taji ya daki zuciyar ta, yayinda gabanta yatsananta faɗuwa, tabbas wannan faɗuwar gaban bana haka kawai bane, lallai dole akwai abun da zai faru da ita, amma kuma yazama dole taje taga wanda yake turomata saƙonni, hanunta na rawa haka ta ɗau hijib ɗinta ta sanya, da ƙyar take iya jan ƙafanta ta fita daga ɗakin…
Inna ta iske zaune a tsakar gida, tana jin radio, “Inada baƙo a waje Inna” Zahrah tafaɗa cikin wata irin murya me rauni. Yanayin yanda Inna taji muryan Zahrah yasanya ta ɗago da kanta ta kalle ta, “Lafiyanki kuwa, meke damunki?” Inna tatambaya cike da mamakin yanda taga jikin Zahrah a sanyaye.
“Babu komai Inna” Zahrah tafaɗi haka tana me nufar hanyar ƙofar fita daga gidan..
Kasancewar akwai wadataccen haske a ƙofar gidan nasu na ƙoyayen wuta wanda maƙotansu suka kukkuna hakan yasa wajen baida duhu, zaka iya hango duk wanda ke tsaye dakuma wanda ke tsugunne, kai harma wanda ke kwance zaka iya ganinsa.
Bugun zuciyarta ne yaƙaru yayinda ƙafofinta suka soma yi mata nauyi, wani mutumi tagani tsaye ajikin wata mota da ta amsa sunanta mota, sai dai kuma yajuya baya, saboda haka bayansa kawai take iya hangowa, sanye yake da wandon jeans black dakuma black ɗin riga sannan kuma akwai hula irin fosin kaf ɗin nan akansa. A hankali take taka ƙafafunta dasuka mata nauyi tanufi inda yake tsaye, yayinda ta sanya hanunta ta cikin hijab ɗinta ta dafe ƙirjinta da takejinsa kamar zai daka tsalle yafito waje..
Abu na farko daya fara hargitsa mata ƙwakwalwa bayan ta isa gareshi shine fitinannen ƙamshin turarensa wanda har gaban abada bazata taɓa manta wan nan ƙamshin ba, wani irin killer smile Zaid yayi bayan yatabbatar da cewa ta karaso gab dashi, fuskarsa ɗauke da murmushi ya juyo zuwa gareta, haɗe da sanya hanunsa ya cire hular dake kansa, take kyakkyawar fuskarsa ta bayyana, wacce take ɗauke da murmushi.
Jikinta ne yaɗauki rawa yayinda idanunta suka ƙara buɗewa take numfashinta yasoma ƙoƙarin ƙwacewa, zuciyarta tashiga duka, ƙafafunta suka ƙage waje ɗaya, yayinda hawaye suka dinga fitowa daga idanunta tamkar anyi ambaliyan su.
Kallon yanda jikinta yake rawa Zaid yayi haɗe da dawo da kallonsa kan fuskarta jefa idanunsa yayi cikin nata. “ZAHRAH!” yaƙira sunanta da wata irin murya me sanyi, sakamakon ganin da yayi kamar cewa bata cikin hayyacinta…
“ZAHRAH” yasake ƙiran sunanta, de de lokacin ne kuma numfashin ta yashiga gudu yana neman ƙwace mata, aikuwa kasa fusgo numfashin nata tayi, lokaci ɗaya numfashinta yayi nasaran fita daga jikinta, take ta yanki jiki tafaɗi warwas a ƙasa, cikin mugun tashin hankali Zaid yayi kanta, haɗe da sanya hannayensa duka biyu ya ɗagota zuwa jikinsa, sunanta yashiga ƙira cikin tashin hankali dakuma ruɗewa, a matuƙar firgice ya sanyata acikin motarsa haɗe da shiga cikin motar da wani irin gudun gaske Zaid yafigi motar ya cillata kan titi… Gaba ɗaya ya ruɗe wani irin gudu yake shararawa baburuwansa da wanda ke gabansa ko bayansa, gaba ɗaya ya ruɗe sunan Zahrah kawai yake ambata, Allah yasa ba zuciyarta ta haɗiya ba..
STORY CONTINUES BELOW
Matsanancin gudun da Zaid yakeyi har ya wuce hankali, da wani irin gudu yashigo cikin asibitin yayin da ya ɗauko Zahrah caɗak a hanunsa tamkar wata ƴar tsana, haka yashigo da’ita cikin asibitin, ganin haka yasa Doctors sukayo kansa da sauri, hankalinsa a matuƙar tashe ya miƙa ta ga doctors sukayi emergency da’ita kai tsaye.. Taimakon gaggawa likitoci suka shiga bawa Zahrah domin kuwa bako maine ya haifar mata da ɗaukewar numfashin ba, face razana dakuma tsananin firgita haɗi da tsoro da suka rusketa alokaci guda, sannan yanayin yanda zuciyarta ke bugawa, yawuce mizani, idan har zuciyar tata tacigaba da bugawa da sauri sauri haka, tofa lalllai rayuwar Zahrah tana cikin haɗari…
(Niko nace idan Zaid yakashe mana Zahrah zamuci …. ko fans😂)1
Iya ruɗewa Zaid ya ruɗe yakasa koda zamane, damuwarsa ɗaya shine Doctors ɗin da suke kan Zahrah, su sanar dashi meke faruwa, lallai idan har Zahrah tasamu wani matsala, to bazai taɓa yafewa kansa ba, sannan kuma babu uban da ya’isa yazauna lafiya, matuƙar likitocin nan suka kasa shawo kan matsalan Zahrah..
Kusan minti talatin likitocin nan sukayi suna ƙoƙarin shawo kan numfashin Zahrah, cikin ikon Allah kuwa sun samu komai yayi dai dai sai dai dole tana buƙatar hutu kodan zuciyarta ta samu salama…
Suna fitowa Zaid yayi kansu, gaba ɗaya idanunsa sun kaɗa sunyi jajur dasu.
Kallonsa ɗaya daga cikin manyan likitocin dasuke kan Zahrah yayi haɗe da dafa kafaɗunsa, “Ka kwantar da hankalinka, komai yayi dai dai, yanzu biyoni office ɗina”
Ba musu balle girman kai Zaid ya bi bayan liikitan.
Kasa zama akan kujeran da Dr ɗin yabasa yayi, babban damuwarsa shine yasan wani hali Zahrah take ciki.
“Nace ka kwantar da hankalinka, kazauna saimuyi magana ko” likitan yafaɗa yana me nuna masa kujera..
“Kaga Doctor bazamane yadameni ba, babban damuwana shine nasan wani hali take ciki” Zaid yafaɗi haka cikin damuwa..
“Zan faɗama ko wani hali take ciki, amma dole sai ka zauna”
Badon Zaid yasoba haka yazauna akan kujera haɗe da sanya duka hanunsa ya dafe kansa.
“Bawani babban abubane yake damunta, akwai abun da yafirgita ta ne, kuma dama anasamun irin haka, sau da dama firgici da tsoro, yakansa mutum yasamu ɗaukewar numfashi naɗan wasu daƙiƙu, amma idan tadawo hayyacinta komai zaidawo dai dai, sai dai kuma tana buƙatar hutu sosai, saboda haka bayau zaku samu sallama ba, dole sai kunjira zuwa gobe da safe, saboda yanzu haka akwai alluran damuka mata kuma suna sa bacci sosai”
Ajiyar zuciya me ƙarfi Zaid ya sauƙe, saboda jin bayanan Doctor da yayi, sun sauƙar masa da nutsuwa “Amma dole sai anan zamu kwana? me zai hana kabani ita mutafi gida, idan yaso saitayi baccinta acan” Zaid yafaɗi haka fuskarsa ɗauke da damuwa.
Murmushi Doctor yayi haɗe da cewa “Hakan bazai samu ba, saboda zata iya farkawa da kowani lokaci, bamu kuma san a wani hali zata tsinci kanta ba, bayan ta farka, saboda haka zamanku anan ɗin zaifi amfani” Doctor yafaɗi haka cike dason gamsar da Zaid.
Kai kawai Zaid yajinjina haɗe da kallon Doctor “Zan’iya ganinta kuwa? sannan kuma inaso akaita ɗaki na musamman konawane kuɗin ɗakin zan biya”
“Wannan ba’abun damuwa bane, zamu kaita ɗaki na musamman sannan kuma zaka iya ganinta, bana ƙira nurse sai a sanja mata ɗaki daganan saikaje ka ganta ko” Dr yafaɗi haka bayan yakara waya akan kunnensa. Cikin mintuna ƙalilan aka sanjawa Zahrah ɗaki inda aka kaita ɗaki na musamman.
Zaid ne tsaye akanta yana me ƙare mata kallo, karo na farko kenan daya farajin wani irin matsanancin tausayin ta acikin zuciyarsa, haɗe da wani shauƙi mai fisgar zuciya. A hankali yaƙaraso dab da gadon nataz haɗe da ranƙwafo da kansa dakuma ƙirjinsa zuwa gaf da’ita, lumshe idanunsa yayi haɗi da kai bakinsa gefen kumatunta ya yi mata kiss, haɗe da sa hanu yashafi gefen fuskarta, “I’m sorry Zahrah!” yafaɗi haka acikin maƙoshinsa. Karo na farko kenan a rayuwarsa daya soma bawa wata mace haƙuri.. Zama yayi a bakin gadon, haɗe da kama hanunta na dama yasanya acikin nasa hanun, a hankali yake murza hanunta haɗe da lumshe idanunsa.
Abu kamar wasa hankalin Inna ne yasoma tashi ganin Zahrah ta kwashe sama da awa ɗaya, a waje batare da ta shigo gida ba, gashi ta leƙa waje bataga ko da me kamannin Zahrah bane, kasa zama inna tayi gaba ɗaya hankalinta a tashe yake, Baffa ne yashigo cikin gidan bakinsa ɗauke da sallama, ko amsa sallaman nasa Inna batayi ba tayo kansa tana cewa “Yau wa Malam gwamma da ka dawo, ko ka haɗu da Zahrah a waje kuwa?”
“Zahrah kuma, ina Zahrah’n take?” Baffa yatambaya cike da mamaki.
Nan Inna tashaida masa cewa tunɗazu tafita bata dawo ba,bayan tasanar mata cewa wani ne yaƙira ta a waje.
Take hankalin Baffa yatashi, domin kuwa Zahrah bata taɓa irin haka ba, har maƙota ya aika ko taje amma aka ce masa bata zoba, take Baffa da Inna suka zuba tagumi, sun marasa ta ina zasu fara, Inna cema takawo shawara akan cewa aƙira Doctor Sadeeq koshine yazo ya ɗauketa, aikuwa Baffa yayi na’am take yadannawa number’n Dr.Sadeeq ƙira, bugu biyu Dr.Sadeeq yaɗaga wayan,, shima bakaɗan ba hankalinsa yatashi jin dayayi cewa wai su Baffa basuga Zahrah ba, ae take yashiga motarsa yataho gidansu Zahrah’n duk da cewa dare yayi…
Kallon agogon hanunsa Zaid yayi a karo na barkatai, ƙarfe 10 na dare kenan, ajiyar zuciya ya sauƙe akaro na uku, haɗe da furzar da iska a bakinsa, kallonsa yakuma mayarwa ga Zahrah, wacce take ta sharan bacci, hakanan yatsinci kansa da sakin murmushi mai sauti, komai na Zahrah me kyaune, tafiyin kyau ma idan tana bacci.
Zama yayi akan wata kujera dake kusa da gadon haɗe da jingina bayansa da jikin bango, lumshe idanunsa yayi tare da cije laɓɓansa sai yanzu ƴake tunanin ya makomarsa zai kasance idan Zahrah tafarfaɗo, domin kuwa ya hango muguwar tsanarsa acikin idanunta.Lokaci ɗaya hankalin Dr.Sadeeq yayi wani irin mummunan tashi, take ƙwaƙwalwar kansa tashiga charge, a iya tsawon sanin da ya yi mawa Zahrah, ita ba mace bace meson fitar dare, balle har tayi nisa da gida, sai dai kuma abun mamaki gashi yau annemeta an rasa, bayan ko ɗazu suna tare a waya shida ita, baikuma ji wani sauyi a tattare da’ita ba, sai dai kawai muryarta da yaji cikin sanyi. “To ina Zahrah taje?”
Yayi mawa kansa tambayar da bayi da amsa.. “Kodai Zahrah tayi hakane don batason aurena da’ita?” yakuma tambayar kansa, sai da zuciyarsa ta buga, shi kansa yatambayi kansa abun daya faɗar masa da gaba, kai amma Zahrah bazatayi haka ba, saboda ita da kanta ta tabbatar masa cewa ta amince da auren sa, saboda haka bazata bar gida saboda batason auren sa ba..
Kallonsa yamaida ga Inna wacce tayi tsuru tsuru da ido tamkar wata munafuka…”Da tazo fita bakiga wani alaman damuwa ko tashin hankali akan fuskarta ba?” Dr yatambaya cike da kulawa.+
“Ƙwarai kuwa da damuwa tafita, saboda kwana biyun nan gaba ɗaya da damuwa take wuni sakamakon waƴansu tsinannun ƴan mata da suka zo, acewar ɗaya daga cikin su wai ita zaka aura Samira take ko Salma oho, haka nan suka zo hargida suka zagemu kaf, tamkar ma zasu mana luguden duka, to tundaga tafiyarsu dai take fama da ƙuncin rai har kawo yau, Allah dai yasa ma basune sukai mata wani abun ba” Inna tafaɗi haka cike da jimami..
Cike da mamaki Dr.Sadeeq yace “What Salima tazo har gidan nan taci muku mutunci?”
“Ƙwarai kuwa ashe dagaske kasanta, tabbas haka tace sunanta wai Salima, ita da waƴansu masu ƙoƙaƙƙun fuska, kamar an gasa nama”
Hanu Dr.Sadeeq yasanya yadafe kansa, lallai idan de har Salima bata ji kunyar zuwa ta zagar masa abar sonsa ba, to tabbas shima bazaiji kunyar zuwa har gidansu yaci mata mutumci ba, Uwa mahaifiyarsa kaɗai ze iya ɗagawa ƙafa akan Zahrah, amma duk wacce tace zata ci mutumcin Zahrah tofa shima zaici nata mutuncin, lallai yakamata ne yafara nemo inda Zahrah take kafun yasan matakin da zai ɗauka akan Salima. Sake dialing number’n Zahrah yayi amma still ce masa ake wai wayar akashe take, tun ɗazu yake ƙiran wayar anacemasa akashe wayarta ta take.. Tunanin ƙiran abokinsa inspector Adam ne ya faɗo masa, saboda yalura lamarin dole sai anshigo da hukuma ciki, tunkan suyi sake lokaci ya ƙure musu. Nan yashiga dialing Number’n inspector Adam amma har wayar ta katse bai ɗauka ba, sake ƙira yayi amma still bai ɗauki wayar ba, tsuka Dr.Sadeeq yayi haɗe da maida wayarsa cikin aljihunsa….
Asibiti
Sai yanzu tunanin halin da iyayen Zahrah zasu shiga yafaɗo masa arai, tabbas yakamata ne yasanar dasu halin da ake ciki, wayarsa yaɗauka haɗe da soma rubuta saƙo, domin bayason wayar da zaiyi yatashi Zahrah a baccin da takeyi, saboda haka gwamma yatura saƙo,a ganinsa hakan zaifi… wata number yaturawa saƙon, batare da yajira amsar da wanda yaturawa saƙon zai basa ba, ya maida wayarsa cikin aljihu…..
Dr.Sadeq ne yadubi Baffa dake a halin damuwa. “Banaje nasanarmawa ƴan sanda, akwai abokina inspector, inaga kawai gwamma naje gidansa na sanar dashi abunda ke faruwa, ina ga zaifi akan tsayuwan damuke” yafaɗi maganar yana me duba agogon dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa, ƙarfe sha ɗaya na dare kenan agogon sa yanuna masa..
STORY CONTINUES BELOW
Sallaman da sukaji ana kwaɗawa a ƙofar gidan ne yaɗauki hankalinsu, ae ba shiri Baffa da Dr. Sadeeq suka ɗunguma zuwa ƙofar gidan, Inna ma ba’a barta a baya ba ta rufa musu baya.
Wani mutumi me shigar cute baƙaƙe suka gani tsaye a bakin ƙofar gidan, yayinda yarufe idanunsa da tabarau, da ganinsa dai zaka gane irin body guard ɗin nan ne.
“Waye kai?” Dr.Sadeeq yatambaya yana me ƙaremasa kallo.
“Saƙo aka bani nasanar daku cewa Zahrah bata da lafiya, yanzu haka tana asibiti..” baikai ga idar da zancen nasa ba, Dr.Sadeeq yace “Meyasameta sannan kuma a wani asibiti take?” duka tambayar yayisune alokaci ɗaya, kuma
cikin ruɗewa..
“Zaku iya biyoni muje” Body guard ɗin nan yafaɗa yana me nufar wajen da motar da yazo da ita ke fake.
Kallon su Baffa Dr.Sadeeq yayi haɗe da cewa su shigo motarsa subi bayan body guard ɗin, hakan kuwa akayi motar Dr.suka shiga yayinda Dr.yashiga bin bayan motar body guard ɗin. Gaba ɗaya ba acikin nutsuwarsa yake driving ɗin ba. Fargabane cike a zuciyarsa, bayi da wani buri da yawuce yaga Zahrah, yakuma ji meke damunta, har aka kawota asibiti batare da sanin su Baffa ba..
Suna shiga cikin asbitin wannan body guard ɗin ya kalli Dr.Sadeeq haɗe da cewa ya biyosa ciki, su Inna kuwa su jirasa, da su Inna sunso ƙi, amma sai Dr. Sadeeq yace su yarda su jirasu anan ɗin, badon su Inna sun so ba, suka tsaya daga waje… Suna shiga cikin wani corridor guard ɗin yaciro wayarsa, haɗe da karawa akan kunnensa.
“Oga na faɗa musu sunma biyoni, yanzu haka munatare da wani inazaton ɗan uwanta ne, iyayenta kuma suna waje” Abunda Body guard ɗin yafaɗa kenan cike da girmamawa.
Tsuka Zaid yayi sakamakon jin abunda guard ɗin nasa ya ce, shirmen banza, cewa yayi yafaɗamusu bawai ya taho masa dasu ba, to yanzu dayakawosu ina zai sasu, wata tsukan yakuma yi, haɗe da sakai yafice daga cikin ɗakin bayan ya sake rufe Zahrah da bargo..
Cakume kwalan guard ɗin nan Dr.Sadeeq yayi cike da ɓacin rai yace “Bamason iskancin banza kace tana asibiti bata da lafiya, gashi munzo kuma kana ƙoƙarin raina mana hankali, wlh idan wani abu yasameta saina ɗaureka” Cikin ɓacin rai Dr.Sadeeq yafaɗi maganan domin kuwa yulura guard ɗin nema yake ya raina masa hankali….
“Idan har ka’iya ɗauresa, to tabbas zan iya yarda na ƙiraka da suna jarumi !!” muryar Zaid takaraɗe wajen, wanda yake ƙarasowa garesu cikin takunsa na isa..
Kallon Kallo aka shigayi tsakanin Zaid dakuma Dr.Sadeeq, wanda kowannensu da irin manufar tasa kallon.
Sama da 5 minute Zaid da Dr.Sadeeq suka ɗauka suna kallon juna, Zaid nayimawa Dr.Sadeeq kallon tsana, yayinda Dr.Sadeeq kuma kemawa Zaid kallon tuhuma, haɗe da son sanin koshi waye…
Kallon guard ɗin nan Zaid yayi haɗe da taɓe bakinsa cike da isa yanuna Dr.Sadeeq haɗi da cewa “Wan nan kuma waye?” yayi tambayar cike da rainin hankali, yana me ɗage kai sama bayan yajefawa Dr.Sadeeq wani irin kallo..
“Hmm ba buƙatar kasan koni ɗin waye, kai de zaifi kyau kasanardani ko kai waye, amma shishshigi baikamace kaba, saboda bakayi kama da me kula da lafiya ba, kafi kama da masu shiga inda ba’a buƙatarsu” Dr.Sadeeq yafaɗi haka shima yana me ɗauke kansa daga kan Zaid.
Murmushi Zaid yayi haɗe da kallon Dr.Sadeeq daga sama har ƙasa. Kansa kawai ya girgiza “Lallai bana buƙatar kowa, kasan yanda zakayi dasu” Zaid yafaɗi haka ga Guard ɗinsa, haɗe da juyawa yanufi ɗakin da aka kwantar da Zahrah, lokacinsa bana me aikin duba lafiya bane, lokacinsa muhimmine kuma sai me mahimmanci yake bawa…
Hasala Dr.Sadeeq yayi lokaci ɗaya yaji zuciyarsa tana masa zafi, yana da sauƙi amma watarana abu kaɗan ke ɓata masa rai, a zuciye ya juya yafice daga cikin asibitin.. Su Inna dake tsaye a harabar asibitin suna ganinsa sukayo kansa da sauri suna tambayarsa ko Zahrah tana lafiya?
STORY CONTINUES BELOW
Kasa amsa musu yayi saima cewa da yayi, su shiga mota su yasauƙesu a gida… Bayanda suka iya haka suka shiga cikin motar jiki a sanyaye, saboda sunga gaba ɗaya fuskar Dr.Sadeeq ɗin ɓacin raine shumfuɗe akanta, kenan akwai abun dake faruwa.. Da wani irin gudu yaja motar suka fice daga haraban asibitin…
Gyara zama Baffa yayi haɗe da kallon Dr.Sadeeq wanda da’alama tunaninsa baya jikinsa.
“Meyake faruwa ne Likita? kashiga kakuma fito da ɓacin rai, ina Zahrah’n takene me yasameta?” cikin damuwa Baffa yayi tambayar domin shi gaba ɗaya kansa ya kulle.
Daure zuciyarsa yayi haɗe da cewa “Tana nan lafiya, gobe da safe zamu zo mu ɗauketa”
Ajiyar zuciya Baffa yasauƙe me ƙarfi yagodewa Allah da ba wani abun bane yasamu Zahrah, to amma ae da anbarsu sun ganta…
A ƙofar gida Dr.Sadeeq ya sauƙesu haɗe dayi musu saida safe yaja motarsa yayi gaba..
Suna shiga gida Inna ta kalli Baffa haɗe da cewa “Anya kuwa Malam bakaganin cewa akwai matsala?”
“Bawai gani nakeba, tabbas ma nasan akwai matsala Salame, sai dai fatana ɗaya shine Allah yatsare Zahrah, amma tunda Likita yace gobe da safe zamu koma asibitin, saimu jira zuwa goben idan Allah yakaimu”
“To Allah yakaimu” Inna tafaɗa jiki a sanyaye… Da “Ameen” kawai Baffa ya amsa.
Kamar yanda Zaid ya kwana a zaune, haka Dr.Sadeeq yakwana juyi, gaba ɗaya kansa ya kulle, yarasa meke faruwa, baisan waye wannan gayen ba, amma tabbas yaji tsanarsa fiye da misali, amma babban abun tambayar shine me yasamu Zahrah har aka kawota asibiti? sannan kuma meke tsakaninta da wannan mutumin? tambayar dayake buƙatar a amsa masa kenan, amma babu wanda zai amsa masa, tambayar da ta kuma hanasa bacci kenan…
Ƙarfe bakwai na safe Zaid yasa aka turo masa nurses guda biyu, suka zo dankula da Zahrah, saboda yana buƙatar yaje gida yayi wanka…..
Tamkar amafarki haka fyaɗen da yayi mata yasake dawowa cikin idanu da ƙwaƙwalwarta, wani irin nishi tayi haɗe da sakin ƙara mai sauti, lokaci guda kuma ta ware idanunta da suka cika tab da ƙwalla, da sauri nurses ɗin nan sukayo kanta.
Kallon Nurses ɗin tashiga yi, haɗe da soma ƙaremawa ɗakin da take ciki kallo, tabbas idan ƙwaƙwalwarta bata juye ba, zata iya cewa nan ɗakin asibiti ne sannan kuma waƴan nan dake tsaye a gabanta nurses ne.
“Barkanki da tashi, me kike buƙata yanzu a kawomiki?” ɗaya daga cikin nurses ɗin nan ta tambayi Zahrah cike da kulawa…
“Idanunta dasuke zubar da ruwan hawaye, ta ɗaga ta kalli nurse ɗin haɗe da girgiza kanta alamar batason komai.
Hanun nurse ɗin takamo duka biyu haɗe da fashewa da wani irin kuka me ciwo, da’alama wani abu takeson faɗawa nurse ɗin.. Dai dai lokacin aka turo ƙofar ɗakin aka shigo, Zaid ne yasha adonsa sai zuba ƙamshi yake.
Tsayawa yayi cak daga bakin ƙofar sakamakon ganin yanda Zahrah take kuka..
“Me kukayi mata?” yajefawa nurses ɗin tambaya cikin yanayi na rashin yarda dasu.
“Bamuyi mata komai ba,ranka ya daɗe tashinta kenan tasoma rusa kuka” su duka biyu suka haɗa baki wajen faɗan maganar…
Tamkar wanda aka zuba mata narkakken dalma haka taji sauƙan kalamansa acikin kunnuwanta, rumtse jajayen idanunta tayi, ji takeyi tamkar zuciyarta zata faso ƙirjinta ta fito.
A hankali Zaid yasoma takawa zuwa gare ta.
“Zahrah” yaƙira sunanta dai dai lokacin daya ƙarasa kusa da’ita.. Tunkafun yagama rufe bakinsa yaji sauƙan wani irin gigitaccen mari akan ƙuncinsa, kafun ƙwaƙwalwarsa tagama tantance masa abun dake faruwa, yakumajin sauƙar wani marin aɗaya ɓangaren hagu na kumatunsa..
STORY CONTINUES BELOW
Kasa koda motsawa yayi saima hangame bakinsa da yayi haɗe da zaro idanu yana kallonta,, Gaba ɗaya marukan nan Zahrah ce ta shararawa Zaid akan fuskarsa..
Yanayin yanda idanunta sukayi ja kace barkono ko attarugu aka watsa mata a ciki.
“Kazone ka sake cutar dani? to gani kacutar dani, gani nace ka cutar dani!!” tafaɗi haka da wani irin tsawa..
Cikin matsanancin kuka Zahrah tasanya hannayenta duka biyu tashiga dukan sa, tako ina Zahrah ke kai masa duka tana kuka, ganin hanu bazai wadarta ba yasanya ta sanya bakinta, tashiga cizonsa a ƙirjinsa, hakama bai mata ba saida ta ɗauki wani ƙarfe dake kusa da’ita tashiga kwaɗa masa a jikinsa tana kuka me tsuma zuciya… Haka Zaid ya tsaya tamkar gunki Zahrah na cizo da yaƙushinsa, gakuma dukan da take kai masa, amma yakasa yi mata komai, yakuma kasa koda motsa hanunsa ne.. dai dai lokacin su Dr.Sadeeq suka shigo cikin ɗakin, turus suma sukayi sakamakon ganin abunda ke faruwa.
“Kasheni zaifi maka sauƙi aduniyar nan, akan ace kabarni da raina, natsaneka, dan Allah ka kasheni!!” Abun da Zahrah ke faɗa kenan tana kuka. Kowa a wajen tsayawa yayi yana kallon ikon Allah, bakomai ke tashi a ɗakin ba face kukan Zahrah, tun tana dukansa da’iya ƙarfinta har ƙarfin nata yasoma ƙarewa a hankali ta sulale zuwa ƙasa, saboda kuka har shiɗewa take…
“Zahrah” Dr.Sadeeq yaƙira sunanta, cikin wata irin murya.. Jin muryan Dr akunnenta yasa taɗago kanta, tana ganinsa tsaye tatashi a guje haɗe da nufar inda yake da sauri tafaɗa cikin jikinsa haɗi da rungumesa ƙa ƙam,wani sabon kukan kuma ta sanya, haɗe da soma buga kanta akan ƙirjinsa..
Duka hannayensa shima yasanya ya rungumeta..
“Wayeshi?” Dr. Sadeeq yayi mata tambayar acikin kunnen ta..
“Shine wanda yaruguzamin rayuwata, shine yarabani da budurcina, shine yayi sanadiyar lalacewar farinciki na!!” Zahrah ta bashi amsa cikin matsanancin kuka, muryarta ko fita batayi da kyau tsabar kuka…
Iya kaɗuwa Dr.Sadeeq ya kaɗu dajin cewa wai wanda yayiwa Zahrah fyaɗe ne tsaye a gabansa, kallon tsana Dr.Sadeeq yashiga yi mawa Zaid..
Zaid kuwa tuni idanunsa sun rune sun zama jajur dasu, jikinsa har rawa yake, koda sau ɗayane baiji zafin duka dakuma marin da Zahrah tayi masa ba, babban abun da yayi masa zafi, shine yanda Zahrah taje jikin wani ta lafe. Tun da yake a rayuwarsa baitaɓa jin abun da yaji a yau ba… Takowa yashiga yi harzuwa inda suke tsaye ita da Dr.Sadeeq, hanunsa yaɗaga domin ya ciro Zahrah daga jikin Dr.Sadeeq. Da sauri Dr.Sadeeq ya tura Zahrah bayansa, haɗe da damƙe hanun Zaid wanda yakawo daniyar taɓa Zahrah..
“Babban kuskuren da zakayi a rayuwarka shine kayarda hanunka yasake taɓa jikinta, kayi na farko yakuma isheka, saboda haka ka kiyaye! ” Dr.Sadeeq yafaɗi haka cikin matsanancin ɓacin rai…
Hanun Zahrah yakama haɗe da janta suka fice daga cikin ɗakin, da sauri su Inna ma suka rufa musu baya, saurin dafe saitin zuciyarsa Zaid yayi, wanda yakeji tamkar zatayi tsalle ta fito waje.. Jingina bayansa yayi da bango haɗe da lumshe idanunsa.. Zafi yakeji a ƙirji dakuma zuciyarsa, take wani irin ciwon kai da zazzaɓi me zafi suka sauƙar masa alokaci guda..
Dr.Sadeeq dakansa yasanya Zahrah a mota, wacce har yanzu kuka take, ataƙaice dai tsabar kuka numfashinta har ɗaukewa yake…. Saboda tsabar gudun da Dr.Sadeeq keyi cikin mintuna ƙalilan suka isa gida, kowa acikinsu yana cikin tashin hankali. Inna ce takama Zahrah takaita ɗakinta. Bayan minti kaɗan Inna tafito daga ɗakin Zahrah da sauri. “Likita temaka numfashinta yana shirin ɗaukewa, taƙi daina kukan” Inna tafaɗa a ruɗe.
Dr.Sadeeq yana shiga ɗakin yace inna tabasa ruwa, aikuwa mintuna kaɗan Inna takawomasa ruwa, cewa yayi Inna taɗan basu wuri bamusu Inna tafita a ɗakin…1
ɗago Zahrah Dr.Sadeeq yayi haɗe da kai kofin ruwan bakinta, sosai tasha ruwan, take ta soma sauƙe ajiyar zuciya, amma still hawaye na gangara akan fuskarta..
Idanunta dasukayi luhu luhu saboda kuka ta ɗago dasu takalli Dr.Sadeeq, saikuma tasake fashewa da kuka, haɗi da faɗawa cikin jikinsa tarungumesa ƙam, hanunsa duka biyu yasanya shima ya rungumeta, a hankali ya shiga hura mata kunnen ta, saboda hakan zai sa taɗan samu relief, koba komai kukan nata zai tsagaita. Har tsakiyar kansa yakejin kukanta.
Tsawon mintuna 15 yakai yana hura mata kunne, a hankali tasoma rage sautin kukan nata, bayan kamar mintuna 5 yajita shiru, sai sauƙar numfashinta da yake ji akan ƙirjinsa akai akai..
Yana duba fuskarta yaga tayi bacci, hawayene yaji suncika masa idanu, tabbas Zahrah taga ƙaddara a rayuwarta, wani irin tausayinta yakeji me tsanani, tabbas idan ya aureta zai yi iya ƙoƙarinsa wajen ganin ya mantar da ita duk wani damuwa da tshin hankalin da ta tsinci kanta ciki, zai kuma yi iyaka ƙoƙarinsa wajen ganin yabata farinciki me ɗorewa.
A hankali ya kwantar da’ita, haɗe da sanya hanu ya gyara mata dogon gashinta da ya rufe mata fuska. Yajima yana kallonta kafun daga bisani ya tashi yafita daga cikin ɗakin…
Zaune yasamu Baffa da Inna a tsakar gidan sunyi jigum. Yana fita suka tsaresa da ido da’alama bakinsu ɗauke yake da tarin tambayoyi..
Ajiyar zuciya ya yi haɗe da cewa “Tasamu bacci, kada ayi wani abu da zai tasheta, ni zan wuce office anjima zandawo”
Har bakin motarsa Baffa yarakasa bayan sun tattauna wata magana me mahimmanci….
Zaid ne zaune a cikin falon sa dake guest hause ɗinsa, kallo ɗaya zakai masa kafahimci cewa yana cikin tashin hankali, kwalaben giyane zube a gabansa, guda uku daga cikin kwalaben duk ya shanye giyan dake a
cikinsu, ba abun dake gigita masa tunani da ƙwaƙwalwa kamar yanda Zahrah ta nunamasa tsana a fili ƙarara, kallonsa yakai ga hanunsa na dama wanda yake fidda jini, bakomai yajawo hakan ba face ƙarfen da Zahrah ta kwaɗa masa akan hanun,, runtse idanunsa dasuka kaɗa sukai jajur yayi, haɗe da cije laɓɓansa, wani irin zafi yakeji acikin zuciyarsa a duk sanda idanunsa suka hasko masa lokacin da Zahrah taje ta faɗa ƙirjin Dr.Sadeeq, jiyake kamar ya kurma ihu, ko zai samu salama acikin zuciyarsa…. Ahankali yamiƙe tsaye haɗe da nufar ɗakinsa, Da ƙyar yake iya tafiya, saboda abuge yake mankas, kai tsaye ɗan ƙaramin drowern dake kusa da gadonsa yanufa, wani tablet yaɗauko haɗe da ɓarewa kusan guda takwas ya watsa a bakinsa, haɗi da korawa da ruwan swan… Faɗawa kan gado yayi yana me rumtse idanunsa, “Natsaneka” shine kalmar da tafi ɗaga masa hankali aduk cikin kalaman da Zahrah ta faɗa masa. itace kuma kalmar da takeyi masa yawo acikin kansa, cikin wani irin yanayi Zaid yatashi tsaye haɗe da nufar wajen da yake aje kayan shafansa, watsi yashigayi da duk wani abu dake kan dressing mirror ɗin nasa, lokaci ɗaya yayi buji buji da ɗakinsa, yayinda ya fasa gaba ɗaya kwalaben turarensa, har sai da wasu kwalaben suka yankesa a hanu da ƙafarsa, amma don tsabar baƙin kishi ko zafi baiji ba, idanunsa Zahrah kawai suke hangomasa kwance a ƙirjin Dr.Sadeeq. Lokaci ɗaya yaji wani irin juwa ta ɗebesa, harsai da yariƙe bango, a daddafe yaƙa risa kan gadonsa ya kwanta, ji yayi kansa yasoma juyawa, yayinda idanunsa suka soma rufewa, yasoma ganin komai bibbiyu, cikin mintuna ƙalilan idanunsa suka rufe ruf…..Ba’itace ta farka ba sai wajen ƙarfe ɗaya na rana..+
A hankali take ware manya manyan idanunta da suka kaɗa suka zama jajur dasu, ba tun yanzu ta farka ba, kawai dai Allah ne be bata daman buɗe idanun nata ba sai yanzu. Tun farkawarta kuwa take cikin tsanani da kuma mamakin mutum mai taurin zuciya irin Zaid, lallai shiɗin yacika ɗan iska kuma shu’umi, duk da irin girman laifin da ya aika ta mata, hakan baisanya yaji ɗar ko kuma shakkan tunkarar ta ba, lallai shiɗin acikin ƴan iska ma daban yake,, haka nan taji gaba ɗaya zuciyarta ta ƙeƙashe takuma bushe, lallai tunda ya nuna mata shiɗin babban ɗan iska ne yakamata ace itama ta nuna masa iyakar iskancinsa, tunda har baiji kunyar tako ƙafa yazo gareta ba, to tabbas itama yakamata tacire kunya, wajen ganin ta koya masa hankali… Sai dai kuma kome zatayi bazata huce ba, saboda iyaka kuma maƙurar cuta Zaid yayi mata, ya mata illa dakuma tabon da bazata taɓa mantawa ba, harta koma ga mahaliccinta kuwa, Zaid ne ya surka mata farincikinta da wani irin mummunan baƙin duhu, ya katse mata jin daɗi da kuma walwalanta, ya lalata mata rayuwa a rana ɗaya, ya ruguza duk wani buri da fatanta, ya gwada mata ƙarfi ya amshi budurcinta cikin yanayi na tozarci, me yafi wan nan ciwo a rayuwar ƴa mace? tasan ƙiyayya amma kuma zafin ƙiyayyar da takeyi mawa Zaid na daban ne, tabbas idan da kisan kai yana da kyau a addinance to haƙiƙa ba abun da zai hanata kashe Zaid san nan kuma itama ta kashe kanta, saboda ƙuncin da ya mamaye zuciyarta ba’irin ƙuncin nan bane da yake fita, lallai ƙuncin zuciyarta dawwa memme ne, sai dai kawai ta roƙi Allah daya sassauta mata…..
Hawayen da suka fito daga cikin idanunta suka gangaro ta gefen kumatunta ta sanya hanu ta share haɗe da miƙewa zaune, babu amfanin ɓata hawayenta wajen fiddasu, yanzu lokaci yayi da shine yakamata yayi kuka ba ita ba. Kayan jikinta tashiga cirewa, haɗe da ɗaura zani akan ƙirjinta kana ta sanya lufaya….
Tana fitowa daga cikin ɗakin nata, Inna ta kalleta haɗe da cewa.
“Yauwa Zahrah kintashi ko? ya ƙarfin jikin naki de?” alokaci ɗaya Inna tajero mata duka waƴan nan tambayoyin..
“Eh Inna na tashi, ko zan samu ruwan zafi inaso nayi wanka ne, gaba ɗaya banajin daɗin jikina, gashi ina so naje gidan su Husnah” tafaɗi maganar tana me ɗan rumtse idanun ta, saboda wani juwa da taji yana ƙoƙarin ɗibanta..
“Kinkuwa ci sa’a yanzu na ɗaura ruwan abincin rana, gashi can inaga yama tafasa saiki ɗiba, amma idan kin ɗiba ki ƙaramin ruwa acikin tukunyar” Inna tafaɗi haka tana meyi mata nuni da tukunyar abincin dake ɗaure kan murhu…
Sosai taji daɗin jikinta sakamakon wanka da ruwan zafi da tayi, bayan ta idar da Sallan Azahar ne, tayi mawa kanta mazauni akan katifarta haɗe da ɗaukan jakar kayan kwalliyanta, mai kawai tashafa sai kwalli da ta zizara a cikin idanunta, ko powder bata shafa ba…
Doguwar rigar atamfa irin me sauƙin kuɗin nan tasanya ajikinta, haɗih da ɗaura hijab akan kayan nata mai kalar blue, yakumayi shige da atamfarta saboda shima atamfar kalan blue ne dashi (shuɗi). Me kyau de me kyaune ko a yaya kuwa, duk da batayi kwalliya ba kuma fuskarta a kumbure take saboda kuka, amma hakan bai hana kyawun fuskarta bayyana ba….
STORY CONTINUES BELOW
Kallon Inna dake ƙoƙarin sauƙe tukunyar abinci Zahrah tayi, tana me gyara zaman lufayar jikinta tace.
“Inna ni zan je gidansu Husnah, zuwa yamma zandawo insha Allah”
“Wani irin maganar zuwa gidansu Husnah kuma Zahrah? inace ɗazu ɗazun nan muka dawo dake daga asibiti, har kin yi sauƙin da zaki soma fita yawo?”
(Su Inna anfara soyayya da Zahrah fans, lol)
“Kada ki damu Inna yazama dole ne naje, amma bazan jima ba zandawo, dan Allah kada ki hanani zuwa Inna!” Zahrah ta faɗi haka cikin yanayi na nuna zaƙuwa.
“Shikenan tunda kin matsa, ai de kya tsaya kici abinci, idan yaso saiki tafi”
“A’a Inna banajin yunwa yanzu, idan nadawo zanci” takai ƙarshen zancen nata tana me nufar hanyar fita daga cikin gidan. Da kallo kawai Inna tabita harta fice daga gidan…
Tsayawa tayi tana kallonsa cike da mamaki, yayinda shima kallon nata yake cikin yanayi na mamaki…
Giransa ɗaya ya ɗage haɗe dayin murmushi…. “Ashe ma kinyi sauƙi, dana sani da ban bar aikin da nakeyi nazo duba kiba ae” Dr.Sadeeq yafaɗi haka yana me takowa zuwa wajen da take tsaye.
Kunyarsa ne taji yakamata, sakamakon abun da yafaru ɗazu a tsakaninsu, wato rungumarsa da tayi, wanda tasan hakan ba abu bane me kyau haramunne, mace ko namiji su taɓa mutumin da ba muharrami’n su ba, duk da cewa ba’acikin hayyacin ta ta rungumeshi ba, amma tabbas hakan bai dace ba…
“Yade naga kina wani sunkuyar dakai kamar amaryar da aka kaita ɗakin mijinta” Dr.Sadeeq ƴafaɗi haka cike da zolaya.
Sai alokacin ta’iya ɗago kanta ta aika masa da
hararan wasa,,,,, ” Yaushe kazo? kuma me yasa ka tsaya anan baka shiga cikin gida ba?”
“Ummm banjima da zuwa ba, dama inaso amin sallama dake ne, kinga bai dace ace koda yaushe ina shiga cikin gidanku kai tsaye ba, amma sai kuma naga kamar keɗin sauri kike zaki unguwa ko?”
Yaƙare maganar yana me leƙa fuskarta wanda ta sunkuyar da ita ƙasa.
Wasa da yatsun hanunta tashiga yi, haɗe da sanya haƙorinta na sama taɗan datse leɓenta na ƙasa..
“Yajikin naki?” yatambayeta don yaga bata daniyar basa amsan abun da yatambaya.
“Dasauƙi, dama ni lafiyata ƙalau” tabasa amsa a ta ƙaice..
“Eh hakane kuma dama kinsan wani lokacin, idan lafiya tayi mawa mutum yawa, takan iya sawa ya kwanta a gadon asibiti”
Saurin kallonsa tayi sakamakon jin abun da yace, “Lafiyan?” ta tambaya cike da mamaki.
“Eh itafa lafiyan, to baga example akan ki ba” yanayin yanda yayi maganar kaɗai ya’isa ya tabbatar maka cewa zolaya ne kawai ke damunsa..
“Hmm” kawai Zahrah tace haɗi da ɗan satan kallonsa, aikuwa karab suka haɗa idanu, saurin ɗauke nata idon tayi.
Hmm yalura sarai kunyarsa takeji, kuma shiɗin ma kusan hakanne, kawai de dauriya dakuma shariya yafita, shiyasa ya share abun, amma shikansa yasan cewa ya aikata ba dai dai ba, saboda da ta rungumesa baikamata ace yabiye mata ba, kamata yayi ace ya ɓanɓareta daga jikinsa, sai de kuma babu yanda ya’iya saboda alokacin tana cikin halin buƙatar taimako, kum san nan shi be rungumeta don yaji daɗi ba.
“Inazakije ne haka, da rana tsaka?” yajefo mata tambaya…..
“Gidan su Husnah zani” ta basa amsa a taƙaice, saboda ba da kowani lokaci tacika son dogon magana ba…
“Shikenan muje saina kaiki, domin kinsan samun abun hawa zaimiki wahala, saboda rana tayi sosai”
Kallonsa tayi naɗan sakanni, kafun ta rausayar da kanta gefe cikin yanayi na shagwaɓa tace “Dama kabarni, koda ƙafana ai zan iya zuwa, idan har bansamu abun hawa ba, balle ma nasan zan samu”
STORY CONTINUES BELOW
“Da gaske zaki iya takawa da ƙafa daga nan har gidansu Husnah? to shikenan tunda zaki iya, zaimafi kyau ki taka da ƙafan, saboda kisamu ki ɗan rage wan nan ƙiban dakika haɗa, gaba ɗaya duk yasa kin yi muni, kin zama wata super mama dake” yafaɗi haka yana me ƙare mata kallo.
Waro idanu Zahrah tayi haɗi da soma kallon kanta, wai tayi ƙiba, takuma zama super mama.
Take idanunta suka yi raurau dasu, yayinda ruwan hawaye ya soma cika cikin su, “ashe da gaske tayi ƙiba bata sani ba? gashi harya fara goranta mata, to me yasa ita bataganin ƙibanta?” tatambayi kanta…
Dariya Dr.Sadeeq yasanya domin kuwa yalura tayarda da maganarsa, shikuwa wasa yake mata, bawai dagaske tayi ƙiban bane, gashi har tana ƙoƙarin yin kuka, shikam ya lura gaba ɗaya kuka baya bata wahalar yi, hawayenta a maƙale suke, mintuna kaɗan saikaga sun tsiyayo”
“Kintsorata ne dan nace kinyi ƙiba? hmmm nan gaba kaɗan zakiyi bindiga ki fashe saboda tsabar ƙiba”
Sake waro manya manyan idanunta tayi zuwa yanzu kam har ƙwallan cikin idanunta sun gangaro akan fuskarta….
“Au kinfiso ki kumbura ki fashe ɗin kenan?” yatambayeta yana me danne dariyar da ta taso masa…
Kai ta girgiza masa alaman “A’a”
“To kinaso na faɗamiki me zakiyi wanda zaisa bazaki fashe ba?”
Dasauri ta ƙaɗa kai alamar tanaso yafaɗa mata…
“Yauwa ƴar gari ashe de kema bakyaso ki fashe, to abu ɗaya zakiyi wanda shizai hanaki fashewa, kinga de ni likita ne ko? nakumayi zurfi cikin karatun likitanci, saboda tsabar zurfin da nayi ina karatune ma yasanya nagano cewa idan mutum yacika matsantawa kansa da damuwa da kuma yawan koke koke to yakan iya kumbura kamar de yanda kikayi yanzu, daga nan kuma bayan kamar 1 week shikenan sai dai yayi bindiga yafashe fush, shikenan kuma sai de wani bashi ba, kinaso haka ta faru dake?” yafaɗi haka yana me zura mata manya manyan idanunsa.
“A’a” tabashi amsa cikin murya me sanyi, domin kuwa a haƙiƙanin gaskiya ta yarda da kalamansa, ko kaɗan bata gano cewa shiya shirya abunsa ba. take fargaba ya ɗarsu a zuciyarta….
Wata irin dariyane takama Dr.Sadeeq amma kuma ba halin yasaki dariyar tasa, dolensa ya danne ta matuƙar yanaso Zahrah ta gamsu da bayanan sa hundred percent,,, lallai yau yaƙara tabbatarwa kansa cewa Zahrah yarinyace kuma yarinta na damunta, amma inbanda haka ta’ina ta taɓa jin ance mutum ya yayi bindiga yakuma fashe da ransa.
Gyara tsayuwarsa yayi haɗe da cewa “To yanzu de zaɓi ya rage gareki Yarinya, ko ki daina kuka ko kuma ki fashe, saboda haka zaki biyoni muje ne ko kuwa a’a nayi tafiyata?”
“Zanbika” tafaɗa cikin muryar tsoro saboda gaba ɗaya kalaman likita sun rikitata…
Murmushin gefen baki Dr.Sadeeq yayi haɗe da juyawa yanufi wajen motarsa, yana me danne dariyarsa…
Zahrah kuwa tamkar wacce ƙwai yafashewa haka ta bi bayansa.
Saida suka hau titi kafun yajuyo da kallonsa gareta, gani yayi tayi jigum da’ita, da’alama tunani takeyi….
“Amma nace miki yawan sakai a damuwa shike sa mutum ya fashe ko? hala don ba ɓangaren likitanci kike karanta ba shiyasa bakisan da hakan ba”
Kallonsa tayi haɗe da ƙwaɓe fuska, cikin murya me sanyi tace “Ni ae yanzu bawai a damuwa nake ba, kawai de ina kallon hanya ne” ….
Kansa ya jinjina haɗe da cewa tayi masa kwatancen gidansu Husnah’n domin shi basani yayi ba….
A dai dai ƙofar gidan su Husnah ya tsaida motar tasa, haɗe da dawo da kallonsa ga Zahrah wacce ke ƙoƙarin buɗe murfin motar tayi ficewarta…
“Da yaushe zaki koma gida?”
STORY CONTINUES BELOW
Ɗan jim tayi kana tace “Ko zuwa bayan la’asar ma, irin ƙarfe biyar ɗin nan haka” yanayin yanda taƙai ƙarshen zancen nata tana me juya kyawawan idanunta, shi ya shagaltar dashi har ya tsaida idanunsa akan ta, sosai takeyi masa kyau idan tana juya idanunta, ya kuma lura cewa hakan al’adarta ne, idan hartana magana, to takan juya idanunta masu kyawun gani, musamman idan maganar tazo ƙarshe..
“Ya de?” Zahrah ta tambayeshi sakamakon ganin da tayi yakafeta da idanunsa..
“Babu, kikulamin da kanki kinji, zan zo na ɗaukeki idan 5 ɗin tayi, inafata babu wata matsala?” yatambayeta cike da nuna kulawa.
Murmushinta me kyau tayi masa haɗe da cewa
“Babu wata matsala”
Yana kallonta tabuɗe ƙaramar ƙofar dake jikin gate ɗin gidan su Husnah tashige… Yana tabbatar da shigewarta yayiwa motarsa key haɗe dayin reverse yaɗauki hanyar asibitinsu, saboda dama aiki yabaro yazo gareta, to yazaiyi tunda tazama wani ɓangare na jikinsa…
Da matuƙar farinciki Husnah ta rungume Zahrah tana mejin daɗin ziyarar bazata da Zahrah’n takawo mata, saboda bata faɗa mata zata zoba. Bayan Zahrah ta gaisa da Momyn Husnah ne, suka rankaya zuwa ɗakin Husna’n,,, ba ɓata lokaci Husnah ta cikawa Zahrah gabanta da kayan ciye ciye dasu drinks.
“Naji daɗin zuwanki sosai ƙawata, kamar kuwa kinsan ina kewarki, jiyafa har mafarkin ki nayi, da safe naƙira wayarki kuma najita switch off, ina fata dai kina lafiya?”
Hijabin dake jikinta ta cire haɗe da cewa “Lafiya amma ba sosai ba”
Da sauri Husnah ta dawo da kallonta ga Zahrah
“Meyafaru dear?” Husnah tatambaya cike da kulawa.
Kallon Husnah Zahrah tayi na tsawon minti guda….
“Babuƙatar tuna abun da yafaru Husnah, saboda kinsan inada raunin zuciya, tuna abun zai iya sake jefani cikin wani hali”
Damuwane ya bayyana ƙarara akan fuskar Husnah haƙiƙa tamkar ƴar uwa ta jini take kallon Zahrah saboda haka duk wata damuwa ta Zahrah damuwar tace itama.
“Zaki iya ɓoyewa kowa damuwarki amma bandani Zahrah, sai de kuma babu amfanin takuraki akan cewa lallai sai kin sanar dani, saboda bansan wani hali zaki samu kanki aciki ba bayan kin faɗamin”
Dafa kaɗan Husnah Zahrah tayi haɗi da daure zuciyarta…
“Nasake haɗuwa da…. da….wanda ya yimin fya…….” kasa ƙarasawa tayi saikawai tafashe da kuka.
Ko bata ƙarasaba Husnah tafahimci me Zahrah take nufi.
Cike da tashin hankali Husnah tasoma salati…
Sake jawo Zahrah jikinta tayi haɗi da rungumeta….”Ki daina kuka, yanzu ba lokacin kuka bane Zahrah, kinmaci abinci kuwa ?” Husnah ta tambayi Zahrah cikin kulawa…
“Banajin yunwa Husnah!” Zahrah tafaɗi haka cikin shaƙewar murya, wani yunwa zataji ita da take cikin bala’in sake ganin Zaid…
“Kinsan de ba kyau zama da yunwa ko, kinga yau ni namayi abincin dakaina, bana zuba mana muci tare, kuma dan Allah kada kicemin a’a”
Babu yanda Zahrah ta’iya dole tabiyewa Husnah taci abinci, gaba ɗaya Husnah se zuba take tamkar kurna, takasa yin shiru koda na minti biyu ne, tayi hakanne kuma saboda ta gusarwa da Zahrah da muwarta, daga ƙarshe de har game, Husnah ta jona musu a tv suka buga, sosai kuma hakan ya ɗebewa Zahrah kewa….
Tare sukayi sallan la’asar daga nan kuma Husnah ta ɗebi Zahrah, suka tafi shoprite, dangin su ice cream da chocolate suka jida, daga nan sukayo gida.
Kamar yanda yafaɗa ƙarfe biyar da minti ɗaya dai dai ya ƙaraso ƙofar gidansu Husnah.. Ƙiran Zahrah yayi a waya ya tabbatar mata cewa yana ƙofar gidan su Husnah….
STORY CONTINUES BELOW
Zahrah na ajiye wayarta Husnah ta kalleta haɗe da kashe mata ido ɗaya.
“Ƙawata tazama ƴar soyayya, sosai yanayin soyayyarku da Man ɗin nan yake kasheni, kinfasan gayen naki ya haɗu over, da badan ke bace danayi snatching ɗin sa!” cike da zolaya Husnah ta faɗi maganar…
Dariya suka sanya su dukansu, haɗe da rungume juna.
Har bakin motar Dr.Sadeeq Husnah ta raka Zahrah, bayan Momyn Husnah ta cikawa Zahrah leda da dangin su turare dakuma kayan shafa hadda kyautar wani haɗaɗɗen leshi, sosai Zahrah tayi godia, hakan kuma yana ɗaya daga cikin abubuwan daya sanya bata son zuwa gidansu Husnah, saboda idan dai tazo tofa sai mahaifiyar Husnah tayi ɗawainiya da’ita wajen bata kyautan kayayyaki masu kyau da tsada…
Harsaida Husnah taga tashin motar su Zahrah kafun takoma cikin gida…
“Kinsamo abun daɗi shine kokimin tayi ko?” Dr.Sadeeq yafaɗi haka ga Zahrah wacce ta ɗaura ledan sayayyar da sukayi a shoprite ita da Husnah akan cinyarta…
“Murmushi me sauti tayi haɗe da cewa “Ba’abun daɗi bane, kayan shafa ne”
“Um um ni banyarda ba, kitaimaka kiban ko chocolate ɗaya ne, naci yunwa nakeji, yau duk banci abinci ba” yaƙare maganar yana me shagwaɓe fuska, sai kace wani ƙaramin yaro…
Dariya Zahrah tayi haɗe da satar kallonsa “wai ma ya’akayi yasan cewa acikin ledar hanunta akwai chocolate?” ta tambayi kanta.
“Kina mamakin ya’akayi nasan cewa a ledarki akwai chocolate ko?, ai ba abun mamaki bane, tunda nasan shiɗin favorite ɗin ki ne” yafaɗi haka cikin yanayin shauƙi, amma still idanunsa naga titi..
Buɗe ledar tayi taciro wani chocolate mai kyau da daɗi kusan yafi kowanne ma daɗi acikin sauran chocolate ɗin da ta saya, ta miƙa masa haɗi da cewa “Ga wan nan amma bazan iya baka kyautarsa duka ba, saboda haka kaci rabi kabarmin rabi”
Saurin kallonta yayi fuskar sa ɗauke da murmushi… ” Naƙi wayon, idan har kinaso na karɓa saide kibani kyautansa duka”
Turo ɗan ƙaramin bakinta tayi gaba, haɗe da noƙe kai alamar hakan bazai yiwuba, kallon bakin nata yayi, harsai da yaji tsikar jikinsa ƴa zuba, hmmm lallai idan ya auri Zahrah, zai tsotse wan nan ɗan ƙaramin bakin nata ne yanda ya kamata🙈…
“Kici chocolate ɗinki ke kaɗai nikam na gode” yafaɗi haka a taƙaice domin dama wasa yake mata baci zaiyi ba, shi da yake fama da ciwon ciki idan yaci chocolate kuma yake nan?
Lokacin da suka iso gida biyar da rabi har ta gota… kallon Zahrah Dr.Sadeeq yayi haɗe da ɗan nisawa.
“Nagama haɗa miki kayan lefe da kuma sauran abun da suka dace, wace rana kikeso a kawo?”
Saurin ɗaga idanu tayi ta kallesa jin abun da yace.
Idanunsa ɗaya ya kashe mata, wanda yasanya taji gabanta yafaɗi, saboda a wajen mutum ɗaya ta saba ganin irin wan nan kashe idon, kuma shi hakan yazame masa al’adarsa ne, bakowa bane kuma face ZAID.
“Zamuyi waya” Zahrah tafaɗi haka don son kawar da tambayar tasa, saboda a yanzu bata da amsar da zata basa..
Ajiyar zuciya ya sauƙe haɗe da dafa steering motar da duka hannayensa biyu. “Shikenan idan kin nutsu zan ƙiraki” yafaɗi haka cikin sanyin murya..
Murmushi tayi masa irin me tsayawa a rai ɗin nan, kana tabuɗe murfin motar tayi ficewarta, sai de batare da yasani ba, ta aje masa wan nan chocolate ɗin…
Bayan kamar 2 minute da shiganta cikin gida yaja motarsa shima yayi tafiyarsa…
*ZAID*
Tunda yasha wan nan ƙwayoyin baisan inda kansa yake ba harsai ƙarfe uku na yammaci,, ko da ya buɗe idanunsa ji yayi duniyar na juya masa, amma haka adaddafe ya shiga bathroom yayi wanka haɗe da ɗauro alwala, sai yanzu zaiyi sallan Azahar don tsabar asara, gashi har la’asar ma takawo kai….
Yana idar da sallan azahar ya miƙe daga kan sallaya haɗe da zura slipper ɗinsa yafice daga ɗakin… Kai tsaye masallacin jikin gidansu yanufa don gudanar da sallan la’asar wanda ake ƙira yanzu.. Ko a cikin masallacin mutane sai mamakin ganinsa suke saboda abune mawuyaci ka gansa a masallacin da wan nan time ɗin, yafi yawan zuwa sallan isha ko asuba, amma banda azahar da la’asar saboda a wan nan lokacin ma kwata kwata baya gida, sai de yayi sallah a wani wajen. Baidamu da kallon da mutane suke masa ba, yana idar da sallan sa yatashi yayi shigewarsa cikin gida…
Tsab yagama shirya kansa cikin ƙananan kaya, riga da wando na blue jeans wanda suka matuƙar amsar jikinsa. Ba abun da yake sai tashin ƙamshi.
Zama yayi abakin gadonsa haɗe da sanya hanunsa duka biyu ya dafe kansa dake yi masa ciwo kaɗan kaɗan,, wani irin sabon al’amari yakeji a cikin zuciyarsa, baisan da wani suna ze ƙira abun ba, amma tabbas jiyake zuciyarsa na azalzalarsa akan Zahrah, san nan yanajin cewa itace muradinsa, saurin buɗe idanunsa da ke lumshe yayi sakamakon hasko masa marukan da Zahrah ta sharara masa akan fuskarsa da sukayi, hanunsa yakai kan ƙuncinsa ya shafa haɗe da sakin murmushi, tunda yake a a rayuwarsa wata mace banda mahaifiyarsa bata taɓa kai hanunta jikinsa da sunan duka ba ballan tana har akai ga mari, sai gashi yau, Zahrah ta shararamasa lafiyayyun maruka harguda biyu akan fuskarsa, takuma haɗa masa hadda duka, amma ko kaɗan baiji zafin abun ba, anya kuwa shine? kodai an musanyashine bai sani ba? meke damun ƙwaƙwalwa da zuciyarsa ne? shine Zaid kuwa? Yajerowa kansa waƴan nan tambayoyin….