AUREN KWANGILA BOOK 2 CHAPTER 8 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

AUREN KWANGILA BOOK 2 CHAPTER 8 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA 

Abdul’azeez dan uwanta ne kamar Isma’el tunda Mammah ce ta haife shi, ba za ta taba son wani mummunan abu ya faru da shi ba ko rashin lafiya. A haka lokacin sallar azahar ya yi mata, da ma tana da alwala ta matsa wajen ibadarta ta tada sallah.
Samun kanta ta yi a cikin sujjadarta tana yi wa Abdul’azeez addu’a har da hawayenta, a kan ko ma me ye ke damunshi, Allah ya sa ya zo masa da sauki. Da ta idar tana so ta fito falo ta ga halin da yake ciki, amma ta kasa. Zama ta yi ta hada kai da gwiwa sai a lokacin ta tuna da wayarta, ko Mammah za ta kira ta gaya mata ya dawo a cikin wani irin yanayi ba lokacin da ya saba dawowa ba? Wata zuciyar ta ce. “Akul! Ki je ki tabbatar da abin da ya same shi din tukunna, yanzu haka ma ya bar gidan”’.
Mikewa ta yi cikin sanda kamar marar gaskiya ta bude kofa ta fito falon. Yana nan yadda ta barshi awanni uku da suka wuce, ko juyawa bai

ZAMU TASHI 

yiba. Ya yi rub-da-ciki a kan hannayensa. Is touching him a crime ? (Taba shi zai zama laifi?) Ta tambayi kanta. Ba ta sani ba! Don haka ta je ta tsaya a kansa tana tunanin abin yi. Lokacin sallah ya yi”. Ta fada muryarta na karkarwa.
Ko motsi bai yi ba, sai ta tsugunna ta kai hannunta kan goshinsa. Zafi rau! Ta taba wuyansa shi ma kamar garwashi don zafi. Kawai sai ta durkushe a wurin ta sanya kuka. Da kyar ya cira kansa daga kwancen ya bude idanunsa da suka kankance suka yi jawur yana kallonta. Ta dago fuskarta suka yi wa juna kuri da ido. “Wane taimako zan iya ba ka?”


Abinda ta iya tambayarsa kawai kenan cikin kuka da karkarwar murya. Duk halin da yake ciki sai da ya yi murmushi, “she’s very soft-hearted”. Ya fada a ransa. “Ki duba lokar jikin gadona akwai paracetamol ki dauko min”. “Dakin a bude yake?”
Ya lumshe ido tare da daga kai, shi bai ma taba rufe kofar dakinsa ba wai don zai fita, ashe ba ta taba shiga ba? Mikewa ta yi da hanzarinta har tana tuntube zuwa dakin. A tsayin rayuwarta ba ta taba ganin dakin barci mai ban sha’awa irin wannan ba. Yafi nata tsaruwa ninkin ba ninkin. Ko kuma idonta ne ya ga hakan? Bazata iya cewa ba. (English Www.bankinhausanovels.com.ng Bedroom ) komai fari da ruwan toka (white and ash), hatta labulayen. Ba ta wannan ta ke ba, ‘drower’ din ta nufa kai tsaye ta debo kwayar maganin ta fito. Kicin ta koma ta samo gorar ruwa mara sanyi ta dawo. Taimaka mishi ta yi ya tashi zaune, ta sa mai kwayar maganin a hannunsa ya watsa su a baki ta kafa mai robar ruwan a bakinsa. Komawa ya yi zai kwanta ta rike masa hannu, dan dago ido ya yi da kyar ya dube ta da idanun tambaya. Kada ka kwanta a nan, ka koma daki”’“Ba zan iya ba”. Ya ce da ita a wahalce. “T’ll help”. Ta ba shi amsa. Ciwo ya ci karfinsa, amma a ransa ta ba shi dariya sosai. Dube ta ‘yar ficika da ita, ko ta ya ya za ta iya daga kato irinsa? Da zai iya doguwar magana da ya tambaye ta hakan. “Ki bari in kwanta kadan for some minutes tunda na sha magani, zan koma”. Ba ta ce komai ba ta koma ta zauna a gabansa, Zuciyarta a jagule. Ya maida idonsa ya rufe sai bacci. Www.bankinhausanovels.com.ng
Da ta ji yana sauke numfashi irin na bacci, sai ta samu kwanciyar hankali, ta koma daki ta yi sallar la’asar. Kicin ta koma ta hado duk abin da ta soya a kan ‘tray’ ta dafa shayi baki da lipton din ‘tetley tea’, ta zuba kayan kamshi su kaninfari, cinnamon da citta kadan ta tace da ‘yar seive ta dura a tea flask ta dauko ta dawo falon da su, ta ajiye a gefensa. Baccinsa ya yi nisa sosai, don haka sai ta koma daki ta kwanta tana ci gaba da yi masa addu’ ar samun sauki. Cikin dan barcin da ya soma fisgarta ta ji kamar ana kiran sunanta. Ta bude ido sosai, daga falo ne Abdul’ azeez ke kiranta. Da sauri ta fito, ya tashi yana zaune dafe da kansa da hannun damansa.
Zama ta yi a gefensa ta hau zuba masa shayi ta zuba zuma, ta juya ta mika masa. Bai yi musu ba ya karba ya soma sipping a hankali. Tana kokarin zuba agada da chips ya ce. “Bar wannan. Ba ni farfesun kawai”.
Ta zuba a dan bowl na tangaran ta tura gabansa. Tana so ta ce ya cire suit din mana saboda sai zufa yake yi amma ta yi shiru, kada ta wuce makadi da rawa. Kafafunsa ya mika mata bayan ya ajiye bowl din a gefe ba don ya gama ba.“Cire min”.
Dago ido ta yi cikin wata irin siga ta kalle shi. Kwayar idanunsu suka sarke da na juna. Ta ya ya za ta iya kama kafafunsa ta cire masa takalmi da safa? Aikin ya so ya yi mata tsauri. Shi kuma ba da wata manufa ya fadi hakan ba, zazzabin jikinsa ya sauka ne, zafi yake ji yanzun sosai. Ganin umarninsa ya jefa ta a gajeren tunani sai ya fara kokarin cirewa da kansa. Sorry, you can go (za ki iya tafiya)”. Ya fada da sanyin murya.
Sai ta ji ba dadi, mene ne a cikin cire safa da takalmi da ta kasa? Bashi da lafiya shine dalili. Bayan wannan ba wani abu. Mikewa ta yi kamar wadda kwai ya fashewa a ciki ta nufi daki zuciyarta babu dadi.
Da ya cire takalman ci gaba ya yi da shan farfesun kadan-kadan. Girkinta yana da _wani sinadarin dandano irin na Mammansa. Ya fahimci hakan tun sanda yake cin abincinta, lokacin da tana amarya. Ganin cin abincin nata da yake yi zai haifar da wani ‘bond’ na daban a tsakaninsu shi ya sa ya daina, ba don ba ya so ba. Auren da ba mai dorewa ba bai kamata ya bari ya yi tasiri mai yawa a zuciyarsa ba.
A nan ya bar bow! da spoon din da ya sha farfesun ya tattara shirginsa ya koma daki. Bai kara fitowa ba, wanka ya yi, sannan ya yi sallolin azahar da la’asar da ke kansa, ya bi lafiyar gadonsa ya kwanta bayan ya kashe wayoyinsa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Tufka da warwara ya kwanta yana yi, na yadda rayuwarsu ta gaba za ta kasance tsakaninshi da ita.

******

Ta ci abincin dare ta yi shirin kwanciya, amma anya za ta iya barcin nan mijinta na gefe ba shi da lafiya? “Ki daina kiranshi mijinki fa, mijin Mu’ azatu dai” . Wata zuciyar ta gyara mata. Har yanzu hotonta da ya kafa musu a falo yana nan. Ta shafa wa kanta lafiya ne ta daina kallon bangaren da hoton yake.
“Abdul’azeez bai cancanci ki tausaya masa ba, saboda ba sonki yake ba, ko yau din ma da ya kula ki don ba shi da yadda zai yi ne, ba shi da mai taimaka masa. Manta da shi ki yi barcinki”.
Amma abin mamaki ta kasa bin wannan shawarar ta zuciya mai gaskiya. “Ko ba ya sona Dan Mommah ne, duk wani jininta amana ne a gare ni, ba za ta ga Da nata ba lafiya ta kauda kai ba. Ni ma ba so nake ya so ni ba, amma tunda ya fara kyautata min, dole in kyautata masa ko da ba zai gode ba”.
Saukowa ta yi daga gadon ta bude wardrove dinta, ta dauko wadataccen mayafi ta lulluba a jikinta. Kicin ta nufa ta gasa masa karamar kazar
gidan gona data yiwa hadin kayan kamshi dana dandano sosai, ta yayyanka akan faranti ta hada da gwangwanin maltina ta kinkima a kan ‘tray’ ta yi dakin nasa. Tsayawa ta yi a bakin kofar ta yi sallama, kirjinta na dukan uku-uku. Tana jin sautin muryarsa kasa-kasa kamar yana waya, “Come in”.
Ya fada yadda za ta jiyo, ya ci gaba da wayarsa.
Murda kofar ta yi ta shiga, sanyin A.C har ya yi yawa, kamshin turaren da yake yawan amfani da shi ( creed-aventus ) ya gauraye da sanyi da kamshin A.Cn ya bada wani atmosphere mai dadi da sanyaya zuciya. Karasawa ta yi ta janyo wani dan teburin gilashi karami ta dora tray din hannunta, ta matso da shi gabansa. Sannan ta kashe AC din dakin kada ta illata ta. Shi bai ma lura da kashewar data yi ba. Wayarsa ya ci gaba da yi bai ce mata komai ba. Cikin hirarsa ta ji yana fadin, “I?ve never lost a case, but I lose it today Mu’ azatu . (Ban taba faduwa a shari’ah ba amma na fadi yau Mu’azatu). Yanzu haka a kwance nake ba ni da lafiya tun safe…..”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Tsaki ta yi ta juya za ta fice, tsakin da bata san lokacin da ya subuce mata ba, sai jin hannunta ta yi cikin na Abdul’azeez, ya riko hannunta ta baya.
Kasa juyowa ta yi, zuciyarta na wani irin tafasa, ita ba ta taba ganin irin wannan masifar ba, Mu’ azatu dai! Komai Mu’azatu! Tana jin ranar da suka yi aure sai ya maida ita cikinsa don so da kauna. “To ke ina ruwanki???” Wani bangare na zuciyarta ya tambaya da question marks har guda uku.. Zuciyarta ta bada amsa nan take. “Ni ma mace ce, ko da ba’a sona ina da zuciya irin ta ‘ya’ ya mata wadda Allah ya sanya kishi a cikin ta tunda muna tare, watakila har zuwa ranar da za mu rabu….. Watakila ranar ne zan daina damuwa da lamarinta”’ .
Ba ta ankara ba ta ji hawaye sun shimfido mata masu gudu da dumi akan kundukukinta. Sauri ta yi ta kai daya hannun ta share su. Bacin ranta na ninkuwa, ya rike mata hannu ya hana ta tafiya kuma bai fasa wayarsa ba. Kalaman da ake fada a cikin wayar ba ta taba jin irin su ba. Idan ta fizge hannunta ya ce ta yi masa rashin kunya. Sun yi a kalla mintuna biyar a haka, sannan ya yi sallama da Mu’ azatu i missed you Habeeb Qalby…”missed you more habeebty…”
Ya jefa wayar kan gado ya juyo ta suka yi facing juna. Duk da babu hawaye a kan kundukukinta ta share su tsaf da daya hannunta, idanunta sun yi jazur kuma ya gane kuka ta ke yi. Kukan farin mutum ba ya buya, gabadaya fuskarta ta kada ta yi jazur. “Ban san abin da yake yawan sanya ki kuka ba. Fitar hawaye abu ne mai matukar sauki a wurinki na fahimta, c’mmon zo mu zauna ki gaya min, ni ne nake sa ki kuka? Ko kuwa kina yi kawai don ki ji dadi ne?”
Janyo ta yayi ya zaunar a kusa da shi, jikinsu na gugar na juna. Shiru ta yi masa kamar ba da ita yake magana ba. Ko ransa ya baci, to wannan karon bai nuna ba, ya yi appreciating kulawar da ta nuna masa a yau, a lokacin da yake tsananin bukatar hakan. Ya tuno kukan da ta rika yi ganinsa cikin halin rashin Www.bankinhausanovels.com.ng lafiya, wannan ya nuna yana da wani matsayi ko ya ya ne a zuciyarta, wanda bai san a wane rukuni yake ba tsakanin na miji da na dan uwa. Kusa da ita ya jawo table din da ta dora masa abinci. “Lets eat, mu ci tare. Na tabbata ke ma ba ki ci ba”. Girgiza kai ta yi ranta a jagule, Ni ba na jin yunwa”Space din cikina zai ishemu mu biyu, ki ci. I assure you cikina zai shigo”. Murmushi ta yi ta sunkuyar da kanta, ko ba komai yayi nasara ya fiddo murmushi akan sirriyar fatar bakinta. ‘“‘ How could this be possible ? (Ta yaya hakan zai yiwu?)” Ta fada cikin raunin murya.
“A duniyar ‘yan uwantaka everthing is possible Hafsah, just eat, muna ci muna hira”.
Dauke kai ta yi cikin mamakinsa, da ma haka yake? Haka yake Hafsat, in ki ka yi la’akari da yadda yake tadi da Mu’azatunsa ke yake yi wa ( horrow-face ), ke da ba ya so, baya so ya ga kin yi farin ciki a rayuwa. Ta saci kallonsa ta gefen idonta, cin kazarsa yake da fork a tsanake. Sajen fuskarsa ya kwanta a kan kyakkyawar fuskarsa sai sheki yake kamar gashin kansa. Ta yi rayuwa a cikin larabawa da turawa ba ta taba ganin wanda saje ya yi wa kyau irin Abdul’azeez ba, hancinsa gwanin kyau, idonsa abin sha’awa, bakinsa….. dole wannan Mu’ azatun ta nace masa tunda ta san ya fi ta komai.
Ba ta ankara ba ya juyo sai idonsa cikin nata, ya kama kwayar idonta red-handed tana yi masa kallon kurillah na babu gaira babu dalili, kallo mai zurfi mai cike da magana, wadda bakinta ba zai iya furtawa ba. Da sauri ta sunkuyar da kanta, shi ma ya shiga kallonta. Kafin ya yi murmushi ya juya ya ci gaba da cin abincin. Tunda ta ce ba za ta ci ba, bai takura ta ba. Karamin firjin cikin dakin ya mike ya nufa, gwangwanin coca-cola ya dauko ya dawo gefenta ya sake zama. Maltina data kawo masa ya ture gefe. (He’s a Coca-Cola addict ). Budewa ya yi ya sha sosai, ya rike ragowar a hannunsa. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Hafsat me ya sa sanya ki kuka?” Ya tambaya ( in subdued ). Shiru ta yi ba ta ba shi amsa ba, to ta ce masa me? Abubuwa da yawa suna sanya ta kuka. Tana da tausayi, tana da raunin zuciya, ba ta son ji ko ganin al’amarin Mu’ azatu, shi kuma yana yi mata abubuwa da gayya tunda ya fahimci ba ta so din. Don haka yi masa shirun shi ne abu mafi alkhairi a gare ta. Barin zancen ya yi don ya yarda ba za ta amsa ba. Wani sabon zancen ya kawo har mamakin kansa yake yi. Tana basar da shi, tana komai amma kamar dole sai an yi hirar? So yake ya debe mata damuwar da ya ganta a ciki bayan kuma shi ne sanadinta.
“Who thought you how to take care of a patient? (Wa ya koyar da ke kula da maras lafiya?)”
Girgiza kai ta yi, kafin ta amsa_ cikin kankanuwar murya, “Nobody !” Wato babu kowa.
Abdul’ azeez ya dube ta na ‘yan sakanni, Sagir da ‘yarsa na kara fado masa a rai, hatta yadda ta ke basarwa haka Sagir ke basarwa in yana bada amsa. Ajiyar zuciya ya yi yana lissafi cikin zuciyarsa.
“Hafsah”. Ya kira ta da bayyanannen sauti. Dagowa ta yi a hankali ta dube shi, ya fi kowa iya kiran Hafsah, yana da wani irin taushin murya da dole in yana magana ka saurare shi, balle kuma in a kotu ne, jerarrun kalaman bakinsa na da daukar hankali cikin kowanne harshe yake yinsu tsakanin Hausa da Turanci. Yana da lafuzza nasa na kansa masu sanya mai saurarensa nutsuwa. Sosai ta ji wata irin Www.bankinhausanovels.com.ng nutsuwa ta shige ta, ta bashi dukkan hankalinta don da alama magana mai ma’ana yake so su yi ba wasan da yake ta janta da shi tun dazu ba, don kokarin sa na son gusar da bacin ranta. “Kafin a yi mana aure mun zauna, mun yi maganganu masu yawa ko? Wadanda suka shafi rayuwar auren da za mu yi, da lokacin da za mu yi (terminating) auren. Na fada miki cikin zamanmu babu takura, babu munanawa juna, babu zalunci. Kowa zai yi zaman kansa ne ya ci gashin kansa. Sannan ya cika alkawarin da ya daukarwa dan uwansa. Don haka yanzu da ki ka yi waya hankalina ya gaza kwanciya, don haka nake kara rokonki ki rike amanar da ke tsakaninmu ki san abin da za ki dinga gaya wa Mammah da su Isma’el. Ta fannina ina nan ina ta kokarin cika alkawurra na, wane alkawari ne on your side ? Sake gaya min don in tabbatar ba ki manta ba”. Ga mamakin Hafsat, ba ta farin ciki da zuwan ranar rabuwar nan yanzu. Amma ta fahimci rabuwar ita ce babban abin da ya sa gaba a yanzu, tunda ga shi yana kara jaddada mata. Kara sunkuyar da kai ta yi, ta soma karanto masa alkawuran wadanda suke kwance luf a cikin kanta.
“Mun rabu ne ba don ba ma son juna ba, sai don kowannenmu ya kasa jure hali da dabi’un dan uwansa. Haka kaddara ta tanadar mana Mommah”Www.bankinhausanovels.com.ng
Kwanciyar sautinta yake bi da tasa zuciyar. Alokacin da ta ke furta kalaman. Ta fade su ne cikin kwantaccen sauti kamar da Mammah din ta ke magana.Je ki kwanta Hafsat, na gode da kulawarki ta yau. Allah ya ba mu alkhairi’’.
Cikin nutsuwa ta mike ta bar dakin, ba tare da ta sake waiwayowa ba. Insha Allahu, daga rana irin ta yau za ta koya wa zuciyarta jarumta, ta daina hango komai sai ranar rabuwa. Bacin ran da ta ke sa wa kanta a kan Mu’azatu aikin banza ne Abdul’ azeez bai fa san tana yi ba. Ya yi nisaa kan Mu’azatu, nisan da ko uwar da ta haife shi ba ta isa tabuka komai a kai ba balle wata ita Hafsat da bai dauke ta cikakkiyar mutum ba, face wani tsani da zai bi ya taka ya kai ga cikar burinsa. Don haka barcinta ta yi cikin nutsuwa har da munshari. Washegari da ta yi sallar asubah bata koma gado ba, kicin ta fada ta shirya masa ‘break fast’ mai rai da motsi. Ko kafin karfe bakwai ta shirya komai tsaf a cikin ‘food basket’ don ta dade da sanin ba ya karya kumallo a gida sai ya je office. Daki ta koma ta yi wanka, doguwar riga ta saka kirar Dammam ruwan dorawa. Ta sharce kanta ta kame da katon bound shima (yellow). Turarrukanta ta feshe jikinta da su, sannan ta fito falo. A tsakiyar falon ta tadda shi yana shirya wasu takardu a ‘briefcase’ dinsa.
“Morning Suhaanah!”. Ya fada ba tare da ya dago ya dube ta ba, yana ci gaba da abin da yake yi. Gefensa ta karasa ta russuna tana gaishe shi. Yaya jikin naka Yaya Azeez?” Wannan karon ne ya juyo ya dube ta, ta yi wani irin kyau da (fresh) kamar jinsin Somali. Hannun damanshi ya mika mata, Gara mu yi irin wannan gaisuwar za ta fi gamsarwa”’Kunya ta ji sosai ta sunne fuskarta cikin tafukanta tana WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG murmushi. Tun a Brussels Mommah ta hana ni yin hannu da maza”’Idanunsa biyu ya fiddo mata,
“Kuma ta ce har mijin da ta daura miki aure da shi?”
Mikewa ta yi, ta nufi daki da gudunta ta rufe kofa. Ba ta taba jin kunyar Da namiji a rayuwarta irin ta yau ba. Kamar wani abu daban ya bukaci su yi ba gaisuwa ba. Ana fadin kalmar ‘Miji’ sosai a cikin magana ba tare da mace ta ji komai a kai ba. To amma gare ta yadda ya fada din da tune din da ya yi amfani wajen fadin ya zo mata da sabon salo, ga wani irin ‘launi’ da kwayar idanunsa ta bayar na rikida a sanda yake fadin maganar kamar ba Yayansu Azeez ba. Wani kwayan mutum guda daya da ta ke wa fassarori masu yawa a baya tun daga shekarunta na kuruciya har girma zuwa yanzu da dangantakar AURE ya hada su zama karkashin inuwa daya. Kullum kuma daga sanin da ta yi masa zuwa yau sake rikida yake yana fitar da sababbin halaye da kamanni masu ban mamaki, na yau daban da na gobe, da ke sanyawa ta rasa gane inda ya sa gaba.
Wato gaskiya ne da aka ce, kada ka yi judging halin mutum sai ka zauna da shi. Idan ka ce za ka yi hukunci da fassarar zuciyarka a kan mutum, za ka fadi gaibu kuma Ubangiji subhana ya hana amfani da zato, domin zunubi ne. Zaman tare shi kadai yake proving who that person is (wane ne wannan mutum din). Abdul’azeez kishiyar yadda ta dauke shi yake a bangarori da dama, barshi dai da ra’ayin rikau irin nasa, ta kira shi odd, ta kira shi stranger , ta kira shi weird ….amma ashe mutum ne mai matukar kirki, kuma mai sanin yakamata. Masanin sirrin zamantakewa. Kokari yake daga jiya zuwa yau ya Sa ta sake da shi ta daina wannan dari-darin da ta ke yi da shi. Sai dai ya manta cewa, duk wani abu da aka san yana da karshe to ba za’a zira jiki a cikinsa ba. In yau sun yi musabaha gobe kuma sai Yayan musabaha ko Babanta??? Jingine ta ke da kofa idanunta a rufe tana wannan tunanin. Ta tuno da abincin da ta shirya

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *