KWASAR GANIMA CHAPTER 5 BY FAUZIYYAH D. SULAIMAN
Www.bankinhausanovels.com.ng
Wa Aka F1 Cuta?
SAMARI ne, matasa ’yan bana bakwai, ke ta hira cikin nishadi a majalisar su mai suna Sa’idawa. A’isha ta zo ta wuce ba tare da ta dubi inda su ke ba. Bala ne ya fara jan tsaki ya na fadin: “Wannan banzar yarinyar ta fiye girman kan tsiya, ita kuma ba diyar kowa ba ya dillalin kashi!”’ Ila ya amshe: “‘Ashe ba ni kadai na ke jin haushin ta ba. Wallahi da da akwai hanyar da zan yi maganin ta da sai na yi.” Lawan da ke zaune daga gefe ya na busa taba ya ce, “Amman kun ba ni kunya; wannan ’yar yarinyar za ku zauna ta na raina muku hankali kullum sai kunyi maganar ta in dai za ta wuce. Wallahi ban sa kai na ba, da tuni na yi maganin ta.” Kai Malam, saurarara! Wannan ba irin wadanda ka saba yaudara ba ne. Wannan shegen taurin kan tsiya ne da ita; idan za ka kwana ka na magana ko kallo ba ka ishe ta ba,”” Mudi ya amshe zancen. Lawan ya kufula ya ce, “Au, haka ka ce? To nawa ka sanya? Ni kuma wallahi zan gwada maka ba ta isa komai ba!” Mudi ya ce, “A’a, babu batun kudi, sai dai mu nada ka sarkin majalisa, ko ba haka ba Www.bankinhausanovels.com.ng abokai na? Shi ne zai zama sarkin majalisar mu ta Sa’idinawa, kuma majalisar mayaudara kamar yanda ake ce mana.” Da wannan shawara su ka watse.
***
Da Lawan ya tashi bin A’ isha sai ya bi ta makarantar da ta ke karatu, ta ’yan mata. Sa’ilin da ya tare ta ta tsorata, domin dai ba ta taba tsayawa da saurayi
ba, don baban ta ya hana ta. Sai dai irin shigar sa ta kamala da lafazin sa mai cike da laushi da tarbiyya ya sanya ta tsaya duk da yake dai ba ta saki jiki ba _ yasami yadda ya ke so. Tun daga wannan rana ya fara samun shiga, amma ta hana shi zuwa gidan su don kada baban ta ya gan shi don ya dage sai ta yi
karatu mai zurfi ta zama lauya ko ’ yar jarida.
Cikin KanKanin lokaci Lawan ya saye zuciyar A’ isha da yaudara har ta kai idan aka tura ta makaranta sai ya dauke ta su tafi shagon sa. Tsawon lokagj su na haka, rannan kwatsam sai ga ciki a jikin A’isha. Hankalin ta da na iyayen ta ya yi matuKar tashi. Baban ta kamar ya kashe ta don bakin ciki Daga Karshe su ka matsa mata da ta sanar da su wanda ya yi mata. Ta ce, “Lawan ne.”
Don haka su ka sanya a nemo masu Lawan din. Amman da ya zo sai ya bada wa idanuwan sa toka ya ce sharri ta yi masa.
Malam ‘Daha, mahaifin A’ isha, ya kwantar da murya ya ce, “Ka ga dana, abin bai kai na zafi ba, tunda dai ta kai ga haka ai sai mu hadu mu rufa wa juna asiri ka aure ta kawai.” Kamar an tsikara masa allura, Lawan ya tashi ya dinga tijara da rashin mutunci, ya fice. *Ko da ya isa majalisar tasu sai su ka sanya ihu su na fadin: “Sai Sarki wallahi!”
Ya zauna ya na dariya, ya na ba su labarin yadda aka yi. Can yace, “Kai, ya dace ma na nuna wa tsohon nan shi Karamin Kwaro ne. Kara zan kai su, nace sun yi mini Kazafi shi da diyar sa. Ka ga ai na huta, ko?”
Su ka kuma saka ihu, su na dariya. Sa’ilin da Malam ‘Daha ya sami takardar sammaci daga kotu ran sa ya kuma baci, amma haka su ka halarta ranar da aka sanya za a fara shari’ar. Mai karanto Kara ya karanto Kara, sannan aka kirawo Malam ‘Daha da diyar a kan ko za su kare kan su a kan wannan zargi. A’ isha dai ta tabbatar da lallai Lawan ne. Daga Www.bankinhausanovels.com.ng Karshe alKali ya ce ta kawo shaidu, idan kuwa ba haka ba za a yi masu haddi ita da mahaifin ta. Daga Karshe dai da babu shaidu aka yanke masu hukuncin Kazafi. Lawan ya dinga kallon abokan sa ya na dariya don ya yi nasara. Malam Daha ya roKi arziKin a ba shi dama zai yi wata magana. Alkali ya ba shi. Ya yi gyaran murya, sannan ya fara fadin: “Da farko na so mu kashe mu binne mu da yaron nan, amman tunda ta kai mu ga haka ni zan fada maku dalili na na hana yarinyar kula kowa na ce har sai ta yi ilimi mai zurfi sannan zan samar mata miji daidai ita. Ba kuma wani abu ba ne illa lokacin da ta ke da shekara shida a duniya ta yi wani ciwo da aka ce sai an Kara mata jini. Wani dan’uwa na ya ba da nashi bayan an gama tantancewa. Ashe shi a lokacin ya na shan magani ne, shi ya sa ciwon bai nuna ba. Sai da aka yi shekara da haka sannan ciwon ya bayyana a jikin ta. Mun sha wahala har Allah ya raya ta. Wanda ta sami ciwon ta sanadin sa shi tuni ya mutu ma. To shi ne mu ka ci gaba da karbar mata magani da zummar idan ta mallaki hankali sosai sai na zabar mata mijin a irin masu lalurar ta. To…” “Kai Malam, wai A’ishan ka ke nufi ta na da Kanjamu?” Lawan ya katse Malam ‘Daha. Shi kuma ya ce, “Ya wuce wai; ga sakamakon ta na cutar mai karya garkuwar jikin ma.”
Lawan ya dora hannu a ka, ya na fadin: “Wayyo Allah, na shiga uku! Amman yarinyar nan kin cuce ni! Shi kenan kin goga mini Kanjamau…!” Gaba daya kallo ya koma kan sa, don har ya suma ma.
Wanda Ya KiJI…
SU na tafe cikin mota ita da maigidan ta su na ta hira har su ka iso
daidai Gidan Murtala. Mijin ya tsayar da motar ya ce, “‘Salama sai ki
Karasa a motar A-Daidaita-Sahu domin kin san zan shiga Gidan Murtala na kai wadannan takardun. Idan kun gama sunan sai ki yi kira na, na zo na dauke ku.” Ya dube ta da kulawa ya na ci gaba da fadin: “Nawa ne zai isheki ku hau A-Daidaita-Sahun? Kin san ba na son hawa babur. Ya kai ku har Kofar gidan saboda rana da kuma mama na” — ya na nufin diyar sa da ke hannun ta. Ta gyara zama ta ce, “Dubu daya ya isa ya kai mu har Kofar gidan, darling.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Bai tsaya wata-wata ba, ya zaro kudin ya mika mata. Ta bude motar ta fita, rungune da yarinya, tana daga masa hannu. Ya karkata motar tasa ya shige cikin harabar Gidan Murtala din. Sai da ta ga shigar sa sannan ta yi gaba da sauri. Wani mai motar A-Daidaita-Sahu ya tsaya a gefen ta. Ta ce masa, ““Nawa za ka kai ni Dorayi daidai masallaci?”’ Ya yi dan jim, sannan ya ce, “Hajiya, za ki ba da dari biyu…”’ “Dari biyu fa ka ce! A’a, na fasa. Je ka…”
“To nawa za ki bayar, Hajiya?”’ “A’a, ka je, na fasa kawai”’ Ya ja motar sa ya yi gaba, yana KunKunin bata masa lokaci da ta yi. Ta tsaida wani mai babur, ta ce, ‘“Dorayi. Nawa za ka kai ni?”’ “Ki ba da dari, Hajiya.” ““A’a, zan ba ka tamanin dai.” “To, hau mu je.””Ta kwaye zanin ta haye kan babur din. Ta rungume diyar tata a tsakiya. Ta ja gyalen ta, ta rufe fuskar ta don kada wai ta hadu da idon sani ya gaya wa mijin ta cewata hau babur. Mai babur din ya zambada da gudu; dama irin ’yan ‘a rufta’ din nan ne. Lokacin da su ka isa Sabuwar Kofa, wata mota ta fito daga Kofar za ta
tsallaka ta shiga cikin Hukumar Firamare, ita ma ta shararo da gudu. Ganin babu mota da ta taho, ba zato ba tsammani babur din nan ya daki motar da Karfi. Gaba daya su ka yi tsalle su ka zube a titi. Mama ce kawai ta fada can gefen badala. A take a nan wata mota ta bi ta kan dan acabar, ita kuwa Salama ta sami karaya a cinya. Da taimakon jama’a aka dawo da ita gefen hanya, tana kuka cikin azaba. Aka tafi a gaya wa ’yan sanda. Maigidan ta ya fito da wuri, ya biyo ta titin, sai ya ga gosulo ya yi yawa. Dole ya tsai da motar sa. Jin yadda ake ba da labarin hadarin ya sanya yaji ya kamata ya leKa shi ma ya gani, musamman da ya ji ana ta tsine wa matar tunda da ma ana ta gargadin mata kan su daina hawa babur. Yana lekawa kuwa ya hango matar sa, kan ta babu dankwali balle gyale, tana tarusa kuka. Ga Mama an ba ta ta riKe da hannu daya. Ya rafka salati, ya na fadin, “Salama, haka za ki yi mini? Sai da na ba ki kudin da na san sun haura kudin motar fa don kada ki hau babur, amman ki ka yi mini haka! To ai wanda ya Ki ji ba ya Ki gani ba. Na sake ki saki uku! Kuma mu je na kai ki asibiti, ’yan’uwan ki sa je su yi jinyar ki.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Wayo Mara Wayo
la’asar sakaliya. A kishingide ya ke, idon sa a lumshe, ya na lazimi. Can, sai ya ji Karar babur, don haka ya bude ido da sauri. Sai ya ga wasu mutum biyu sun tsaya. Wanda aka goyo ya yi magana da mai jan babur din, sannan ya nufo wurin Malam Ahmadu, wanda ya tashi zaune sosai, ya jingina da bango.
Ya na isowa, ya durKusa har Kasa ya gaishe shi.
Malam ya mika masa hannu su ka gaisa sosai. Sannan ya ce ga wuri ya zauna, ya nuna masa kusa da shi.
Mutumin ya zauna a ladabce, kan saa Kasa. Can, cikin murya mai cike da ladabi, ya fara magana.
““Malam, zuwa na yi ka yi mani wani taimako don girman Allah domin na san ku mutanen Allah ne, masu taimako bayin sa.” Malam ya gyara zama, ya ce, “Ina jin ka, bawan Allah. Allah ya sa taimakon ba zai fi Karfi na ba.” A zaton sa, kila kudi mutumin zai tambaya. Mutumin ya gyara zama, ya ce, ““Wallahi wata yarinya na ke nema, to da yake ni iyaye na ba a nan jahar su ke ba sai ake neman a hana ni duk da yake wani kawu na ya je. Sai na ce ai kai ma dan’uwan mu ne domin na san ba za ka Ki taimaka mani ba bisa raya sunnar Ma’aiki. Shi ne na zo neman alfarmar mu tafi da kai ka sanya baki a maganar, domin dai duk wanda ya taimaka aka raya sunna, na san yana da lada mai dama.”
Malam ya yi dan jim, sa’annan ya ce, “Haka ne. Amman ina fatan idan na taimaka maka za ka riKe musu diya da amana. Sannan kuma ina son sanin inda ka ke da ainihin garin ku.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Bakon ya gaya wa Malam inda ya ke da zama da garin su. Sa’annan ya koma wurin wanda su ke tare a babur, su ka yi magana, daga nan su ka taho tare.
Na farkon ya dubi wanda su ka taho din, ya ce, “‘Bari mu je da Malam mu dawo; ka zaunaa nan.” Su ka hau babur, su ka tafi. Mutumin ya na ci gaba da bai wa Malam labari YA na zaune a Kofar gida bisa tabarma da ya shimfida kan dakali da a kan auren nasa. Ya ce yarinyar ta na son sa Kwarai, domin mutum shida ya kasa. Iyayen ne su ke son su hana shi domin sun hango wani wanda ya fi shi maiko. Sai da su ka je unguwar Dorayi sannan ya sauke Malam a Kofar wani gida, ya ce ya zauna ya jira shi ya je ya dauko kawun nasa ya dawo. Ya Kara da cewa nan ne Kofar gidan su wacce ya ke so din. Malam ya samu wani gungume, ya zauna zaman jira. Amma har aka yi sallar magariba mutumin nan bai dawo ba. Da Malam ya gaji da jira, sai ya tsayar da wani babur din ya koma gida. Ya na zuwa, ya tarar da wanda ya zo tare da wancan na farin, har ya yi alwala ya yi sallah. Haushi ya fara dibar Malam. Ya ce, “Kai, ina dan’uwan naka? Na gaji da jiran sa bai zo ba, na taho!” Cikin mamaki, mutumin ya ce, “Dan’uwa na kuma? Ai ni ban san shi ba! Ba yace kai kawun sa bane?” Malam ya ce ko daya. Ya shiga tafa hannu, ya na gaya masa abin da ya hada su dazu dazu. Nan fa mai babur ya tibire a kan bai yarda ba, ya ce shi kawai a fito masa da babur din sa. Ya ce lallai wata Kullalliya ce aka shirya don a raba shi da hanyar Www.bankinhausanovels.com.ng neman abincin sa. Abu kamar wasa, rigima ta yi tsamari har ofishin ’yan sanda. Malam Ahmad ya dinga tafka rantsuwar cewa bai san mutumin nan ba, amma babu wanda ya ko bada masa Kasa. Ba tare da bata lokaci ba, aka tura shi bayan kanta.
In ran sa ya yi dubu, ya baci. Ya na Kyata, ya na cewa: “Lallai wannan mutumin ya na da wayo, sai dai wayon nasa mara wayo ne. Ina roKon Allah Ya yi gaggawar bi mani hakKi na!” Bayan minti talatin, ’yan sanda su ka tura shi sel. Anan ya kwana.
*
Hankalin iyalan sa duk ya tashi, amma ya ce kada su damu, Allah Ya na sane da shi. Ya na zaune kan benci, ya duKar da kai, ya yi tagumi. Matar sa da wani dan sa sun zo tun kafin Karfe 7; a lokacin aka fito da shi daga sel, inda bai runtsa ba har wayewar gari.
Da mai babur ya zo wajen Karfe 10, *yan sanda su ka matsa wa Malam Ahmadu lallai sai ya fadi sunan mutumin da ya dauke shi a babur su ka tafi,
llahi bai fa san shi ba, kuma bai taba ganin sa ba. Wani dan sanda da ya kufula ya daga kulki zai Kwala masa, hayaniyar jama’a ta dakatar da shi.Sai ga mutane riKe da kwalar wani mutum. Aka tambaye su abin da ya faru, su ka ce, “Yara ya kade har guda uku ya tsere, aka bi shi. Da Kyar aka kama shi.”
‘Daga kan da Malam Ahmadu zai yi sai ya ga ashe mutumin da ya danfare su din nan ne. Ko kafin ya kai ga cewa wani abu, mai babur ya riga shi yace wa shugaban *yan sandan: “Yallabai, ai wannan shi ne wanda ya gudu da babur din namu.” Mutumin ya daga kai su ka hada ido da mai babur. Haba, ai sai ya Kara firgicewa. Malam ya yi murmushi, ya ce, “Ai shi wayo, in dai mara wayo ne, ba ya zuwa ko’ina!”