AUREN KWANGILA BOOK 3 CHAPTER 1 BY SUMAYYAH ABDULKADIR
Www.bankinhausanovels.com.ng
Karbi ki sha, ba kyau kwana da yunwa, daga ni har ke ba mu yi ‘dinner’ ba”.
Ba musu ta karba ta kwankwade, don yayi gaskiya yunwa take ji, ya kara mata ta shanye ta ba shi kofin ta haye can karshen gadon ta rufa da zanin atamfarta. Zama ya yi a farkon gadon yana shan madarar a hankali. Dauki duvet din ki rufa ke daya, na bar miki’Ta kuwa janye ta kudundune a cikinsa. Shi ina zai iya rufa da wani quilt bayan zai kwana cikin zafi babu AC sabida ita? Dama tsokanar ta yakeyi. Sai da ya gama abin da zai yi, ya yi addu’a, sannan ya yi (light off) ya kwanta.
Shi ya tashe ta da asubah suka yi sallah jam’i tare. Cikin sauri ya yi wanka ya shirya cikin farar shaddah kal ‘yar ciki da babban riga sun sha aiki da zare ruwan kasa , ya kafa hula zanna-bukar ruwan kasa ya daura agogon ‘rolex’ a damtsen hannunsa duk Hafsat na kwance tana kallonsa.
A JIMETA
Jirgin ‘Arik’ ya sauke Abdul’azeez da Sagir a_ Jihar Adamawa (Yola), Karon Abdul’azeez na farko da zuwa Adamawa a rayuwarsa. Kai shi a jihohin Nigeria bakidaya zai iya kirga wadanda kafarsa ta _ taka, wadanda_ karatu ya_ kai _ shi (Ibadan, Lagos), sai ko mahaifar iyayensa (Kanon Dabo) sai kuma yau da ya_ taka _ “kafarsa a
Adamawa a dalilai guda biyu. Na farko abokinsa Sagir wanda yake abokantaka da shi da zuciya biyu kyakkyawan tsammaninsa na cewa yana da alaka da Hafsat da kuma aiki da ya hada su wuri guda. A yau kuma ya zo Adamawa ne don amsa gayyatar
Sagir da ya yi masa na daurin auren dan Yayarshi Modibbo da kuma son yin kyakkyawan bincike a kan Sagir da ahalinsa don tabbatar da wannan zargi da zuciyarsa ta riga ta mika wuya da shi. Www.bankinhausanovels.com.ng
Daga filin jirgin saman (Yola Airport) shatar taxi suka yi (drop) har garin JIMETA kofar gidan iyayen Sagir da ke unguwar DEMSAWO.
Demsawo unguwa ce mai tsohon tarihi a Jimeta. Babban gida ne irin na ‘extended family’ (gidan Gandu) wanda ya tuna masa da nasa gidan kakannin da ke Kano. Tun isowarsu wajejen karfe goma na safe suka tadda jama’a sun fara taruwa a kofar gidan wanda dakali guda biyu suka sanya shi a tsakiya. Karfe goma sha daya na safe za a tafi gidan su yarinyar inda za a daura auren, nan gidan su Sagir shi ne wurin haduwa (meeting point).
Sai yi musu barka da zuwa ‘yan uwan Sagir ke
yi har suka samu damar shiga cikin gidan. Wuce wannan lungu, shiga wannan sashe har suka tadda bangaren iyayen Sagir wanda ke can karshen gidan. Abdul’azeez zai iya rantsewa ya ga fuskoki na mata da maza masu yanayin zubin halitta ko kamanni na fuska da matarsa Hafsat sun kai guda goma. Tazbihi kawai yake yi wa ALLAH Sarkin ‘kaga halitta wanda ya halicci wannan ‘family’ ya kuma sanya kamanceceniya mai tsanani a tsakaninsu da Hafsat wadda idan har ba ta jini ba ce, to hakika imaninsa ya karu da Ubangijinsa.Mai yin halitta yadda ya so a tsakanin al’ummar Annabinsa Muhammadu (SAW). Al’amarin ya kara rikirkita shi a lokacin da suka kuke ga isowa kuryar gidan zuwa dakin dattijuwar da ake ta kira da ‘Daada’ a bakin manya da yara.
“Daada adon nderna (Dada kina ciki)?” Sagir ya tambaya a kofar dakin, yana mai zura rabin jikinsa ciki. Mido nder Sagir, yottu nder (ina ciki Sagiru, karaso ciki)”Bismillah Barrister mu shiga daga ciki’
Ya gusa ya bai wa Abdul’azeez hanya. Tare suka shiga dakin suka zazzauna a kan tabarmar kaba da ke shimfide, suka fara gaida Daadan, wadda ko kusa Hausa ba ta zauna a kan harshenta ba.
“Shi ne abokina da nake gaya miki Barrister Abdul’ azeez Dakata’”’Jabbama-jabbama Abdul’azeez, Allah ya kara albarka a gare ku da iyalanku, barka da zuwa garin Jimeta”Www.bankinhausanovels.com.ng
In ji dattijuwa Daada, cikin tattausar muryarta mai cike da nutsuwa. Irin dattijan nan ne da yawan ibada da kula da sallah ya sanya musu kamala, dattaku da nutsuwa ta musamman a rayuwar girmansu. Abdul’ azeez dago ido ya yi yana kallon Daada, wannan karon zuciyarsa neman hantsilowa waje ta yi. Hakika ba’a mutuwa a dawo, kuma har da shi aka binne Habibah a birnin Jeddah, idan kuma aka hada shekarun Habiba a sanda ta ke raye tare da su zuwa yanzu shekaru goma sha takwas ko kusa ba za ta yi shekarun wannan dattijuwar ba. Ba don haka ba da ya ce Habiba ce ba mutuwa ta yi ba, Nigeria ta dawo. Hatta wata tawwadar Allah da ke gefen hancin Habiba ga ta nan a gefen hancin Maman Sageer. Bai gama farfadowa daga tunanin da ya lula ba ya lura da wani ‘enlargment’ na wani hoto a gabas maso kudu na dakin, wanda ya gama warware duk wani tunani da zargi da ya saura masa.
Wani farin Dattijo ne tare da Daada, da ‘ya’ya maza da mata sun kai goma har da Sagir tun bai wuce shekaru sha takwas ba, a cikin jerin matan ga wadda zai iya kira ‘HABIBAH’ ko daga barcin mutuwa aka taso shi Habiba ce wannan.
Jikinsa har rawa yake yi, yana kallon Sagir da Dada na magana yana kallon hoton. Kafin ya sauke idonsa an cika gabansu da akusan abinci kala-kala. Muryar Sagir ya tsinkaya a_ tsakar kansa, “Tunanin me ka ke haka ina ta magana ba ka jina? Mu ci abinci maza mu tafi lokaci na tafiya Abdul’ azeez”’.
A hankali ya sauke idonsa a kan Sagir ya sake daga su ya kalli hoton sannan ya kalli mahaifiyar Sagir. Tunani ya yi gara ya bar komai a cikinsa kada ya bata musu rana, bayan suna da abin farin cikin da suka shirya yi. Wannan tunanin ya sa shi daidaita fuskarsa ya maido hankalinsa ga Sagir, wanda ya ciko kofi da farin kunun gyada mai kyawun gani a ido ya miko masa, ya kuma dauki ‘plate’ ya cika musu da wainar shinkafa da kuli (maasa) ya sanya a tsakiyarsu suka fara ci. Dada na tambayarsa ko yaransa nawa? Murmushi ya yi. “Dada auren nawa ko shekara bai yi ba”To Allah ya kawo masu albarka”’.
Amin Dada”.Sosai ya ji dadin abincin nan, don ya jima bai ci irinsa ba. Kuma basu karya ba suka fito. Da suka gama Dadan ta miko masa kwanon sha cike da sabuwar madarar shanu mai dumi. Ya karba ya sha sosai, da doki mai yawa. A lokacin angon ya shigo wanda Sagir ya kira da suna Modibbo, ya sha manyan kaya sai kamshin turare yake. Sai Abdul’azeez ya kara tsinkewa, tsinkewar da bai yi a baya ba na zaton da dangin Hafsat ya ke tare. Yanzun ne ya karasa mika wuya. Www.bankinhausanovels.com.ng
Wannan saurayin bafillace wanda alamu sun nuna ya samu ilmin boko mai zurfi bai bar komi na Habibar da ya sani ba. Mika musu hannu ya yi suka yi musabaha, ya ce da kawun nashi, wato Sagir ya tashi su wuce unguwar su amaryar inda za a daura auren.
Bayan an daura aure sun dawo aka yi liyafar cin abinci a wani babban falo da ke gidan na mahaifin su Sagir. Su’isu ne ‘family’ din gidan maza zallah. Ko abokan ango ba su da yawa, daga nan jama’a suka soma watsewa.
Booking dinsu na komawa Abuja na karfe biyar na yammacin ranar ne, don haka cikin gidan Sagir ya ja shi suka koma. A lokacin mahaifin su Sagir da suke kira da Malam Babbah ya dawo yana shigifarsa wadda ke kusa da dakin Dada, can Sagir ya ja shi suka gaisa da Malam. Ya gabatar da shi a matsayin amininsa a wajen aiki.
Malam Babba malami ne na sosai, malamin Alkur’ani masanin addini wanda gwamnatin jihar ta Adamawa ta san da zamansa, ta ke kuma damawa da shi a kan al’amuran da suka shafi addini a jihar. Kamalarsa da kwarjininsa a bayyane suke na malaman kwarai ma’abota dimbin ilimi. Sosai yake jan Abdul’azeez a jiki don ya sake su yi hira, kasancewar Abdul’azeez bai saba shiga irin wadannan wuraren ba sosai yake nuna bakunta, ga kuma nauyin da zuciyarsa ta yi. Amma duk da haka ya saki jiki da Malam Babba sun yi hirar iyayensa da kakanninsa da ke Kano.
Ba karamin dadi Abdul’azeez ya ji ba lokacin da Sagir ya ce su koma dakin Dada su yi mata sallama, su yi haramar wucewa ‘airport’. On warti na (kun dawo)?” Dada ta tambaya.
“Ai tun dazu muka shigo muna tare da Malam Babba”. Sagir ya ba ta amsa cikin fulatanci shima. Wasu abubuwa cikin jarka ta turo gaban Abdul’azeez. “Ga man shanu da kindirmo ka kaiwa maidakinka. Ga kuma masa sabuwa an yi muku ita ma ka tafida ita, na lura kana sonta sosai”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Murmushi ya yi, ya ja jarkokin gabansa yana godiya, Sagir na taya shi. Idonsa ya mayar kan hoton nan da ke kafe ya ci gaba da kallonsa. Har Dada ta lura ya kurawa bangare guda ido, ta juya don ganin abin da yake kallo. “Kana kallon ‘yan uwanka ne?” Ta fada da hausarta mai rauni, fulatanci shine harshen da ya kama harshenbakinta, tsilli-tsilli take jefa hausar wadda ma dalilin Abdul’ azeez din take yin ta.
Mikewa ya yi ya isa ga hoton ya bambaro shi daga bangon ya dawo ya zauna kusa da Dada da shi a hannunsa. “Dada yanzu duk ke ki ka haife su?”
Murmushi ta yi, amma saboda alkunya irin ta Fulani sai ba ta ce masa komai ba. Sagir ya matso kusa da shi ya soma yi masa bayanin jama’ar cikin hoton.
“Wannan shi ne babban yayanmu Yaya Tijjani, wannan Yaya Yusha’u, wannan kuma Yaya Habiba… sai Maiwada, Sa’ade, Fusam, Haladu, ni Sagir da autan Dada Nuru. Duka mu tara ne ‘ya’yan cikin Dadanmu”.
Yatsansa (ibham) ya dora a kan fuskar Habibah ya ki daukewa, har Sagir ya lura ya ki dauke yatsansa daga kan fuskar ta. Kamar yana bukatar karin bayani a kanta, amma bai furta hakan da bakinsa ba. Sagir ya kara matsowa kusa da shi sosai.
Ita wannan da ka ke gani a yanzu ba ma tare
da ita. Ita ce Yaya Habiba mahaifiyar Modibbo da aka daura wa aure yau. Mun rabu da ita shekaru. goma sha tara kenan, har gobe zukatanmu cikin taraddadi suke da tarin alhini. A duk halin da muke ciki farin cikinmu ragagge ne a dalilin rashinta, da rashin sanin wane hali ta ke ciki tunda kuwa ba mutuwa ta yi ba, bacewa ta yi sama ko kasa muka rasa ta. Sai bayan shekaru masu yawa da muka tsananta addu’a komai ya bayyana gare mu na sanadin barinta gida, labarin mai tsaho ne Abdul’azeez. Sannan ba mai dadin ji ba. Kuma mai taba zuciya.
Mun yi duk wani nema na duniya har gobe babu Yaya Habiba babu labarinta. Musabbabin fara ciwon hawan jinin Dada kenan, wanda ta ke fama da shi har gobe. Malam kuwa a duk istikharar da zai yi a kan Habiba ya ce ba ya ganin komai sai duhu , Allah ya rufe masa komai, mun kasa sanin komai a kanta. Tun muna cikin tashin hankali har a hankali muka soma sabawa da rashin Yaya Habiba. A yanzu sai dai mu tuno ta mu yi mata addu’a,
amma mun saba da rashinta, shekaru goma sha tara ba kwana tara ba ne. A yau babban danta Ridhwan (Modibbo) ya yi aure, kaninsa Abdurrahman na ajin karshe a jami’a, sai autanta Imaamu yana aji uku a FUTY, to ka ji’. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ajiyar zuciya mai nauyi Abdul’azeez ya sauke, a lokacin da Sagir ya saka aya na takaitaccen labarin da yake ba shi. Ya tambayeshi ina mijnta? Sagir ya ce “Yana nan a raye. Da ka kula da wani farin mutum mai hula ruwan kasa da farar shadda
a wurin daurin auren nan yanata gaisawa da jama’a shine mahaifin su Modibbo. Malami ne a tsangayar harshen turanci a FUTY. Duk wanda ya kwana ya tashi a Federal University of Technology Yola, ya san da zaman Farfesa Bashar Maijama’a sabida rubuce-rubucensa a kan koyar da harshen turanci a jami’ar FUTY. Abdul’azeez na son sake tambayarsa ko me suka gano sanadin barin Habiban gida bayan watanni da batan nata?Sai shesshekar kukan Dada suka ji, wadda tun sanda Sagir ya fara bada labarin ta soma kuka. Duk cikin ‘ya’yana ta fi kowannensu taimaka mini, kafin a yi mata aure ban san shiga madafi don yin girki ba, data tafi gidan miji ma bata fasa dafowa ta kawomin ba, ta fi dukkansu kyautayi a gare ni. Zuciyarta mai kyau ce, mai kaunar UWA, mai nufin alkhairi ga kowa. Samun mace mai kyautayi da jin kan UWA kamarta a wannan zamanin abu ne mai wuya. Ta so mijinta da zuciya daya, ta zauna da shi tsakani da Allah tun ba shi da komai. Rana daya Hajara ta raba su, ta shiga tsakaninta da ‘ya’yanta. Ta bar su sun girma babu dumin Uwa. Ta raba ni da nagartacciyar diyata! Ba zan taba yafewa Hajara ba har duniya ta nade……”. Ta ci gaba da kuka sosai mai taba zuciyar duk mai imani.
“Ki ba ni watanni hudu Dada, as a lawyer (a matsayina na lauya) na yi alkawarin binciko miki labarin “‘yarki Habiba, domin kamar na santa, kamar na taba ganinta a wani wuri”’Abdul’ azeez ya samu kansa da fada ba tareda ya shirya kalaman akan harshensa ba, sun fito ne kai tsaye ba tareda karbar umarni daga zuciyarsa ba sakamakon tausayin wannan UWA mai tsananin begen diyarta. Daga Sagir har Dada zabura suka yi suka mike tsaye. Hannu dafe da kirji, baki a bude. “Da gaske Abdul’ azeez?”
Suka hada baki wajen fadar hakan. Gyada kansa yayi cikin tabbatar musu da sahihancin furucin sa. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Tun ranar da na fara ganinka zuciyata ta gaya min kana da alaka da Habiban da na sani. Rokona daya mu bar zancen nan a matsayin sirri a tsakaninmu zuwa dawowata. Na yi muku alkawarin da kafata zan dawo da cikakken bayani a kan Habiba, da shaidu kwarara’”’Da ya zo nan, ya kuma tuna Habiban ba ta duniya sai ya ji kwalla ta cika masa idanu.
“Kabar ni in gaya wa Malam na samu wanda ya taba ce min ya ga Habiba bayan shekaru sha tara kafin mu tadda kushewa ko na ji dadi a zuciyata”. Dada ta fada tana kukan farin ciki.
“Za ki iya gaya wa Malam, amma daga shi babu kari har in dawo. Bana so ku kasance cikin zullumi har tsayin wannan lokacin ne shi ya sa”.
“Zullumi ko kwanciyar hankali? A kalla dai mun san tana nan ba mutuwa ta yi ba……”.
Sai ya kauda ido, ya share ambaliyar hawayen da suka cika masa ido da yatsun hannunsa.
Karfe biyar daidai na yamma jirginsu ya taso daga Adamawa zuwa FCT Abuja.
**********
Hafsat ta ji dadin tsarabar kindirmo, man shanu, masa da kuli da Abdul’azeez ya kawo mata daga Jimeta. Sosai ta ci ta koshi ta sanya ragowar a firji za ta dinga dumama musu a microwave har ta kare, nonon ma da man shanun duk a (fridge) ta adana su.
Washegarin ranar ya kai ta ta baiwa Mammah hakurin fushin da ta ke yi da ita, ta ce ita ba fushi ta yi ba, tana so ne ta yi hankali da kawayen zamani, Nigeria ba Brussels ba ce ta kama kanta, ta rungume mijinta ta fita sabgar kowacce tarkacen kawa in ba haka ba za su kai ta su baro. Www.bankinhausanovels.com.ng
Hafsat dai hakuri ta ke bayarwa a kan laifin da ba nata ba. Ita da Abdul’azeez yanzu wani_ irin kyakkyawan zama ne a tsakaninsu. Kowanne gani yake ba mai kirki a duniya irin dan uwansa. Ya wadata ta da duk wani abu da dan Adam ke bukata na abinci da suttura da na amfani. Bai kara (attempting) neman komai daga gare ta ba, ganin iyayenta da kakanninta da irin gidan da ta fito da ya yi, ya kara mata kima da martaba a idanunsa. Ya yarda Hafsat ba gangar da zai ci amfaninta ya yar da kwaurenta ba ce. Gara ya maida ita ga iyayenta da ‘yan uwanta cikin mutuncinta, ta samu miji na gari mai nagartattun halaye irin nata ta aura. In yaso ya zame mata bango abin jingina a duk sanda ta bukaci hakan. Don haka soyayyarsa da Mu’azatu ta kara karfi a wannan dan tsukin wadda saura kadan ta kammala (Lawschool) dinta.
Jarrabawar su Hafsat ta fito, ta kwaso points masu yawa har (300). Ba da jimawa baya samar mata gurbi a ‘NILE’ jami’ar nan mai zaman kanta dake birnin tarayyah, Abuja.
Duk wani shige da fice da dalibi zai yi don zama cikakken dan makaranta Hafsat tare da Abdul’ azeez suka yi shi. Ta zama cikakkiyar dalibar ‘Nile University’ a tsangayar ilimi da koyarwa (education) inda za ta gwanance a fannin koyar da ilimin halicce haliccen duniya Geography (Education/Geography).
Ba sa kwana a daki daya, Abdul’azeez ya haramtawa kansa wannan. Kullum kuma shi yake kai ta makaranta da kansa sannan ya wuce office . Don haka basa bata lokaci da safe suna fita da wuri, in ta riga shi tashi ya tura direban office dinsu ya maida ta gida, in sun tashi lokaci daya shi zai biya ya dauke ta su tafi gida. Wannan ma ya taka wata rawa ta www.bankinhausanovels.com.ng musamman wajen sanya shakuwa mai tsananin karfi a tsakaninsu.
**********
Sosai Hafsat ke jin dadin abin da ta ke karanta. Darasin (Geography) da ma na cikin darussan da ta ke so tun a sakandire. Shi ma Abdul’azeez ganin ta samu AJi a darasin ya sanya shi zabar mata shi, sannan halayenta za su yi kyau da na malamin makaranta saboda tana da hakuri, sanyin rai da juriya. Hafsat na jin dadin karatunta a NILE fiye da tsammani, ta yi kawa wata mutuniyar Zamfara mai suna Mami, aiki ne ya kawo mijinta Abubakar Sadik Abuja, Mami za ta girme mata
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG