ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 4 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE
Www.bankinhausanovels.com.ng
Aziza na da shekara biyar aka yi mata Kani mai suna Nasir, a lokacin ne ma aka haifi Muhammad Kani na biyu ga Hameed. Sannan sai
a shekarar Allah Ya bama Maryam haihuwa, ya bata da namiji, ta yiwa Mustapha takwara, wato Ya Abban ki. Sannan kuma a wannan dai shekarar Murja matar Alh. Aminu dan wajen ‘Haj. Saude itama ta haifi da namiji mai suna Sameer. : – In taKaita miki a shekarar nan dai sai da – kusan duk yaran. mu suka haihu, a Kalla cikin shekaru biyu sai da muka yi jikoki sun kai bakwai, kuma duk maza, mata biyu.
Amma bayan shekara daya sai da muka rasa mutum uku, cikin su na farko Kabir wanda yake bin Hameed, sai Nasir Kanin Aziza, sai kuma Fiddausi ‘yar wajen Hajara. Shekarun Aziza goma a duniya lokacin Allah Ya dauki ran Alh. Nasir, rasuwar da har yanzu bamu mayar da gurbinta ba, tsayawa baki labarin irin tashin hankalin da muka shiga ba zai yiwu ba, domin kowa yasan mun yi rashin babban bango.
Ya je wata Umra ne cikin Azumi yana dawowa da sati biyu Allah Ya aiko masa da ciwon ajali, wani zazzafan ciwon ciki ne ya
kwantar da shi, kwana biyu Allah Ya amshi abinsa.
Babu wanda bai ji mutuwar nan ba cikin Zuri‘ar, to amma babu yadda za muyi dole muka haKura muka dauki dangana da ta zamo mana dole, domin kowa dan haka ne. Bayan sadakar uku haka dangi suka hada mu suka shiga yi mana nasiha mu da yaran mu akan mu hada kanmu domin wannan shi ne _ babban burin dan ‘uwansu, da wasu maganganu da suka dinga fada mana wanda mu kanmu bamu sansu ba, suka ce duk shi ne ya basu wasiyya idan ta Allah ta kasance gare shi to sai ‘su sanar mana. Nan dai muka Kara yin kuka da jin
irin abubuwan da ya so ganin munyi. Tafiya ta soma tafiya babu wata matsala, * domin manyan da suke tare damu suna dora mu akan hanya, haka aka ci gaba da gudanar da rayuwa tamkar mai gidan yana nan, sai dai abin da ba za a rasa ba, Haka manyan yaranmu suka tsare mana mutuncin mu, babu abninda muka nema muka rasa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Lokacin da aka zo rabon gado al’amarin ba Karamin bamu mamaki yayi ba na jin irin tarin dukiya da kadarorin da ya mutu ya bari, sai a sannan Zuri’a ta Kara tabbatarwa cewa Alh. Nasir ba Karamin miloniya bane, tsayawa na fada miki irin tarin dukiyar da kowa ya samu bata lokaci ne.
Abin godiyar Allah Zumuncin mu haka ya ci gaba da dorewa ko da yaushe, sai dai abu daya ne ya soma bamu tangarda akai, shi ne Hameed. DOmin sam baya ji, tsabar gata da shagwaba da yake samu yasa ya fara kawo matsala, sai yanzu ne aka fara gano cewa yawan gatan da yake samu ne yasa ya dawo baya jin tsoron kowa.
Hameed ya fara bawa kowa matsala da ya fara abu anyi masa fada sai ya hau yin fushi da mutum.ko ma waye, ganin yawan fadan da Abban ku yake masa akan rashin jinsa yasa ya bar gidan ya koma gaban mahaifansa, nan suka gyara masa daki ya koma abinsa. Shiru kwana biyu Hameed ya daina shigowa gidan, Amminsa da kanta ta zo gidan Www.bankinhausanovels.com.ng
wai ta zo bikon danta. Lokacin suna zaune a falo ita da Haj. Asiya wato mahaifiyar sa ta ce. Yaya na biyo sawun dana, kwana biyu naji shi dif, ke kuma ba ki dawo min da abina ba, ko nima har dani a cikin laifin? Don naga da ya fice bai Kara waiwayo ni ba”,
Hmm! Ai kin san halin dan naki da taurin kai da kafiya, tun jiya nake cewa ya koma yana ce min wai shi takura masa ake yi”Yaya takura kuma? Kin san halin Abban. su dai, nasan akan yawon nan da ya fara ne suke samun takun saKa””To ai shima bai kama ta yana yi masa haka ba, nawa Hameed din yake da za ana matsa masa kamar wani mace?” Muryar da suka ji ta doki kunnen su nan take suka juya suka ga Alh. Jafar ne yake maganar; kai tsaye yanayin fuskar su ta sauya. Kallon junan su suka yi jin irin furucin da yayi, ko, da yake Aisha ce kawai ta fi nuna namakin sabanin ita Haj. Asiya. Aisha kar ki damu, Hamecd ya same ni ‘da kansa ya ce ya gaji da zaman can ya dawo nan ‘ya dan huta don ya buKaci can ya dawo, don haka ina son a bashi wannan damar domin da an shi ne daya nema muka bar shi ya dawo
hannur ku, amma tunda yanzu ga abin da yake so sai ku barshi yayi, da fatan ba zaku damu ba . tunda yanzu ya fara girma bana tunanin za a hana shi samun ‘yancin sa ba”. – . Aisha taji kalaman nasa sun yi mata wani iri, don bata taba zaton wannan Www.bankinhausanovels.com.ng furucin daga . bakin babban yaya ba. . Ta ce, “Shi kenan yaya Jafar, zamu bar shi mu gani ko kwana biyu zai huce”. “A’a ku barshi dai kawai, bana yin tunanin ma zai koma ma gaba daya”Gabanta ya fadi ta ce, “Yaya na ga kamar cikin bacin rai kake, ko ya fada maka anyi masa wani abu ne da ya bata maka rai?” Girgiza kai yayi yace, “Ko kadan kada ki
Sama kanki damuwa, shi ne dai ya buKaci haka, ni kuma nake son nayi masa abin da yake so “Shi kenan Yaya, babu laifi tunda ka ga hakan ya fi kuma mu ba zamu yi fishi da shi ba, ” .° muna nan muna jiran dawowar sa nasan da ba Zai fushi da iyayensa ba”. Tana gama fadin haka ta mike cikin sanyin jiki.
Hajia Asiya ce ta rako ta har bakin get din – gidan, tace. ” Aisha kada ki nuna damuwar ki, naga kamar ranki bai so ba, ni na rasa me yasa Daddy ya fada miki wannan maganar, amma don Allah ki nuna komai ba komai ba, wannan sirrin mu ni da ke ba tun yau ba yake son Hameed ya dawo hannunsa, nayi-nayi ya fada min dalili amma yaki, dole na rabu da shi tunda haka ya faru ki bar shi mu zuba masa ido, nasan halin Hameed, muna nan zaune zai ce zai koma gidan su.
Ran Aisha yayi fari domin jin kalaman da Haj. Asiya ta yi mata, bata san lokacin da ta saki murmushi ba, ta ce. “Yaya na gode sosai, insha Allahu nima ~zan bar wannan maganar cikin rai na, babu wanda zan tonawa ita”.Nan dai suka yi sallama cikin dadin rai, amma dai cikin ran Aisha ta tafi a was-wasi na cewa to mene ne dalilin da yasa yaya Babba yake son Hameed ya bar gurinmu ya dawo hannunsa bayan irin tarin zumuncin da suke yi da dan uwansa, domin kaf cikin DANGIN JUNAn ba sa taba yin abu kansu tsaye ba tare da sun yi shawara da shi ba tsabar girman da suka bashi, haka kuma ya samo asali ne gurin mahaifinsu.To amma mai zai,sa a fara samun Baraka a gurinsa yana matsayin shi ne babba cikin (family)? Dole ne ta boye wannan matsalar, ba zata Www.bankinhausanovels.com.ng bayyanawa kowa ba, domin ta hango so da Kaunar dansa a idanunsa wanda take tunanin matuKar za a nuna ja akan abin da yake so to tabbas wata matsala na iya faruwa. Don haka duk ma mai zai faru ba zata taba bari Mustapha ya fuskanci komai ba cikin wannan lamarin, domin zai iya yin wani tunani da zai zo ya cutar_ da ZURI’Ar su, saboda haka ita kuma ba zata bari hakan ya faru ba cikin yardar Allah. Aziza ta shiga nuna damuwar ta ganin kwana biyu ba ta ganin Ya Hameed dinta, domin kwana biyu ba sa taba, ‘yar tsamar da suke yi da juna.
Kai tsaye gurin mahaifinta ta nufa ta ce, “Abba wai me yasa Ya Hameed ya Ki dawowa ne? Na je gidan Daddy na ce masa ya dawo ya Ki, wallahi nima zan koma can kuma idan na tafi ba zan taba dawowa ba sai ranar da ya dawo . Sannan zan dawo”.
Murmushi yayi ya ce, ““Ammi na kenan, to ya zan yi da yayanki? Baya jin magana, na san fushi yayi da ni amma na san zai huce, amma idan kinga.za ki koma can to bi shi, nasan idan ya ganki wata Kila ya yarda ya biyo ki ku dawo gida tare”. Haba! Nan Aziza ta shiga murna da tsalle wai-za ta koma gidan Daddy gurin Ya Hameed dinta. Da gudu ta nufi dakin Amminta ta na fada mata abin da Abba yace Www.bankinhausanovels.com.ng
Itama mura ta nuna domin dai tasan irin shaKuwar da ke tsakanin Hameed da Aziza ta tabbata daya ba zai iya rayuwa ba tare da dan uwansa ba, dole ta san duk inda daya yaje sai dayan ya bishi. Nan da nan ta kwashi kayanta bai fi kala uku ba ta juya ta fice da gudu tana murna.Mustapha da. Aisha suka bita’ da kallo suna mata dariya, domin ganin irin murnar da take yi. Mustapha yace “Aisha zan so naga Kaunar nan da yaran nan suke wa junan su ta . dore har zuwe girman su, domin sai na hada auren su cikin yardar Allah, saboda na yarda da Kaunar da suke wa junan su”Murmushi tayi tace “Allah Ya nuna mana hakan, da kuwa an Karfafa zumunci domin wannan shi ne burin Alh. Abbas kuma insha Allahu sai mun cika masa burinsa wanda yana kwance cikin Kabarinsa rahma zata na zuwar masa domin ZURI’A DAYA za su hadu su yi ta yada Zuri‘u cikin yardar Allah”.
“Allah Ya amsa wannan fata naki, Ya hada kan ZURI’A dinmu ta zamo DAYA, yadda babu inda baraka za ta zo mana”Amcen”. Ta fada cikin farin ciki.
Ya Hamee! Ya Hameed!! Ya Hameed!!! Kana ina ne ina ta kwada maka kira ka Ki ka amsa, Aziza ce fa”.
Da sauri ya fito daga shiryayyen dakinsa daga shi dogon wando da farar singilet a jikinsa, don Kwanjinsa ya fara fitowa na matasan samari,
Lokacin shekarun sa sha shida. Farin ciki ne ya bayyana a fuskar su lokaicin da suka ga juna ware hannu ya yi ta zo ta fada jikinsa ya wani runtse ido na jin dadi, daga nan sai ya saketa, ta ce.
“Ya Hamcecd (guess what)?” Ya runtse ido ya bude, ya ce, “(No idea)” Murmushi tayi ta ce, “Baka ga me yake hannuna ba? To nima na gudo daga gida na biyo ka gidan Daddy, nima ba zan koma ba sai lokacin da zaka koma sai mu koma tare”. Tsalle ya yi ya riKe hannunta, ya ce, “Yauwa Aziza na, wallahi dama_ kullum tunaninki nake yi, sai naji kamar naje na sato ki ki dawo gidan Daddy mu zauna da ke, amma sai ina jin tsoron Abba kamar ba zai barni ba. Kin san Abba yana da fada da tsawa, ni kuma bana son fada shi yasa na dawo nan, da na fadawa Daddy ya cé na dawo ba zan koma ba”,
“Nima ba zan koma ba, a nan zamu yi ta zama ni da kai tunda Abba yana maka fada da tsawa, kuma ni bana son naga an yiwa Ya Hameed na tsawa da fada”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Murya suka ji ance, “Yauwa yaran Daddy, ku shirya ku zo mu fita abinmu aje.a siyowa Aziza komai sabo, ba zata yi amfani da kayanta na gidan Abbanta ba, daki itama za a gyara mata _ irin na yayanta Hameed”. – Juyowa tayi cikin farin ciki da ta gane wane yake maganar, Daddy dinsu ne. Da sauri ta je ta rungume Daddy, ta dce. ’ . “Yauwa Daddy na, kaima baka so na koma ko?”Cikin murmushi ya ce, “Eh Ammi na”. ‘Nan Haj. Asiya ta Karaso gurin cikin fara’a ta ce. “Aziza wato kema kin biyo yayanki kun yiwa Ammi da Abba yaji ko?” “Eh Mami ba zamu koma ba tunda Abba yana yiwa Ya Hameed dina tsawa da fada, shi kuma baya so, ya ce ba zai koma ba, anan zamu yi ta zama tare ko Ya Hameed?”’
Daga mata kai yayi yana ta murmushi ‘ alamar hakane.“Mami ina ne dakina da za a gyara min na kwana? Amma fa ni kadai ba zan ke kwana da – su Muhammad ba tunda ni ce babba irin Ya Hameed”. Dariya suka saka gaba dayan su, Daddy ya ce.
“Gaskiyar ki Ammi na, dole ne a baki daki a shirya miki shi sosai har sai ya fi na yayanki kyau”. Murna da tsalle ta shiga yi tana cewa. “Yeeeh! Daki na zai zama (very beutiful) ya fi na Ya Hameed”,
Ta shiga yi masa gwalo, nan da nan ya kufula domin dama sun saba da hakan dama – kwana biyu ba su taba ba. Abinka da Aziza dama gata gwanar tsiwa
da tsokana shi kuma Hameed da bi sanin ya fara girma haka ya biye mata suna ta guje-guje a cikin falon, iyayen na musu dariya. Nan dai .ta samu ta buya jikin Daddy donsu, babu yadda zai yi dole ya rabu da ita yana cewa zan kama ki ne za ki gane kuren ki”. Haka dai rayuwar su ta ci gaba da gudana, tuni Aziza zamanta ya koma gidan su Hameed, – kowa ya yi farin ciki da hakan. Sai dai ni ce kawai da naji raina bai so ba, ba don komai ba sai irin sake da nake hangowa a cikin gidan – domin kaf cikin Zuri’ar mu babu gidan da Turanci ya ratsa da boko irin gidan Alh. Jafar; domin ganin yadda naga suke rayuwar su na sake. Sam ba ya tsawatar wa yara, yaro sai abin da ya ga dama shi zai yi ba kuma wanda ya isa . yahana shi.Www.bankinhausanovels.com.ng
Na so na nuna cewa Aziza ta dawo gida, amma gudun kada na haifar da wata matsala cikin ZURI’A sai na ja baki na nayi shiru, domin dana ce wani abu za a iya canza min abin da nake nufi. Hakan yasa na yi wata hikima nayi shiru, sai dai abu daya nasa cikin raina zan saka idanu akan rayuwai aziza a cikin gidan, domn ban so ta tana mace ta taso da tarbiyyar taurin kai. Haka, na yi wata hikima da wayo da dabara, nakan shiga gidajen sauran yaranmu ba don komai ba sai don kada su gano cewa gidan – Jafar kadai nake zuwa ayi tunanin da bana zuwa sai da jikata ta koma gidan sannan na tsiri zuwa, sai na mayar da abin cikin hikima yadda babu wani da zai zarge ni da wani tunani, yau naje ‘ gidan wannan gobe naje gidan wancan, hakan _yasa na fara janyo Aziza jiki na. . A duk ranar da naje gidan nasu nakan ganin abinda raina baya min dadi, domin sai ina ganin Hameed na yawan jan Aziza jikinsa, wata
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG