AUREN KWANGILA BOOK 3 CHAPTER 2 BY SUMAYYAH ABDULKADIR
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ba sa kwana a daki daya, Abdul’azeez ya haramtawa kansa wannan. Kullum kuma shi yake kai ta makaranta da kansa sannan ya wuce office . Don haka basa bata lokaci da safe suna fita da wuri, in ta riga shi tashi ya tura direban office dinsu ya maida ta gida, in sun tashi lokaci daya shi zai biya ya dauke ta su tafi gida. Wannan ma ya taka wata rawa ta www.bankinhausanovels.com.ng musamman wajen sanya shakuwa mai tsananin karfi a tsakaninsu.
**********
Sosai Hafsat ke jin dadin abin da ta ke karanta. Darasin (Geography) da ma na cikin darussan da ta ke so tun a sakandire. Shi ma Abdul’azeez ganin ta samu AJi a darasin ya sanya shi zabar mata shi, sannan halayenta za su yi kyau da na malamin makaranta saboda tana da hakuri, sanyin rai da juriya. Hafsat na jin dadin karatunta a NILE fiye da tsammani, ta yi kawa wata mutuniyar Zamfara mai suna Mami, aiki ne ya kawo mijinta Abubakar Sadik Abuja, Mami za ta girme mata
da wajen shekaru hudu don shekarunta ashirin da biyu. Komai na Hafsat da yanayin shigarta na kamala da tsantseni na burge Mami wadda ainahin sunanta Rabi’a Sada. Mijin Mami ma’aikacin Etisalat ne, duk ajinsu babu wanda Rabi’a ta ga ya kamata ta yi abota da shi sai Hafsat Dakata, ko don ta amfana da ita saboda cikin dan lokaci hazakarta ta (good foundation) din da ta samu ta fito fili, kowa ya fahimci ‘talented’ ce. Daga ‘assignment’ har ‘test’ ita ce zakaran gwajin dafi. Ita dai Hafsat ba ta zura jiki a kawancensu da Mami sosai, saboda yadda
Mammah ta tsoratar da ita a kan kawayen Abuja, amma yadda Mamin ke nace mata ya sa dole ta ke kula ta, amma a abin da ya shafi harkar karatu kadai. Ba ta taba yarda wata magana bayan ta karatu ta hada su ba. Har ga shi watanni sun gangara suna shirin fara jarrabawar (first semister) wanda ya zo daidai da kammala Www.bankinhausanovels.com.ng (Law-school) din Mu’azatu wadda ta shafe watanni goma a jihar Yola.
*******
Yau a kan idon Mami da mijinta Abubakar Abdul’azeez ya dauki Hafsat, da ta bude motar ta shiga ta zauna, sunkuyawa yayi ta saman kanta yana gyara mata sarkar wuyanta da ta harde cikin gashin kanta ta baya,gashin yake zarewa daga cikin sarkar a hankalihannayensa zagaye da ita. Yayin da kanta ke kusa da kafadunsa. Sosai Mami ta saki baki da hanci da ido daga nesa ta ke kallonsu da mamaki, don ba ta taba sanin Hafsat na da aure ba ganinta yarinya karama danya shataf. ‘Couple’ din sun zauna mata a zuciya sun kasa bacewa, sai zancensu ta ke yi wa mijinta a hanya. Ba ta taba ganin matar da ta dace da miji irin Hafsat Dakata ba, har kishi ya sike Sadik ya ce. Wallahi zai ajiye ta a gefen titi, ina ruawanta da kallon mijin kawarta har ta ke yaba shi a gabansa sabida jahilci?” Sosai Mami ta kama kanta don ta san halinsa sarai zai iya ajiye ta a titin a kan kishinsa, amma ta sa a ranta za ta tirke Hafsat sai ta ba ta labarin rayuwarta da inda ta hadu da wannan ‘handsome’ da ta dade ba ta ga namiji mai tarin abubuwan da ya mallaka ba. Duk da itama ta san ba abune mai sauki samun hakan daga Hafsat din ba yadda take ji da class dinnan da zata tsaya tana wani bata labarin rayuwarta ko na mijinta. Amma ance a rashin tayi akan bar arha. Zata gwada sa’ arta. A washegari da ta turke Hafsat da tambaya, nan da nan tayi fuska, ta ce ita ba mijinta ba ne,
Yayanta ne. Amma irin Yaya a dangi ko irin family friends din nan ko?” Saboda ita dai ta ga abin da ta gani wanda ya sanya ta shakka a kan zancen Hafsat. Murmushi Hafsat ta yi har kuncin nan ya lotsa ciki sosai. Murmushin da Mami ta kara dorawa a sikeli.
“Ke me ye damuwarki Mami a kan hakan? Daga ganin mutum ba ki san ko wane ne ba sai ki ce mijina ne? To babu ko daya”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Mami ta ajiye biron hannunta tana murmushi ta ke kallon Hafsat. “Ni na ga abin da ya sa na tambaya ko kin ki gaya min Hafsat, a sanda ya bude miki murfin mota ki ka shiga ki ka zauna, ya sunkuya yana gyara miki sarkar wuyanki. Akwai wani babban al’amari cikin kwayar idanunsa a kanki. In kin sani kina boye min ne ban ga laifinki ba, don na dade da sanin kawance na da ke bai dadaki da kasa ba. In kuma ba ki sani ba, ina mai sanar da ke wannan. Idan kuma da gaske Yayanki ne kamar yadda kika dage i’m telling you wannan Yayancin will turn to something very special nan ba da dadewa ba”. Bin labban Mami Sada ta yi da kallo, a lokacin da ta ke furta kalamanta. A ranta tana mamakin me ta gani da ya sa ta fadar hakan?Ko jiya Abdul’azeez kwana ya yi da wadda yake so a kan waya, tsakaninta da shi ya kai ta makaranta ya dauko ta, ta dafa masa abinci ya ci. Ba ta da sauran buri a kan Abdul’azeez yanzu, ta dade da yi wa zuciyarta fada, kuma zuciyar ta dade da shiga taitayinta. Ba ta sanya mata komai sai tunanin tahowar ranar karewar KWANGILA wadda ta tabbata tana tafe nan bada jimawa ba. Bai gaya mata ba, amma tana lissafe da watanni, kuma ta ji yana fadin zai tafi Lagos (call to Bar Ceremony) din masoyiyarsa, ba ita ya gayawa ba, abokinsa Abdallah ta ji yana gayawa a waya.
Ga mamakin Mami gani ta yi idanun Hafsat sun cicciko da wata zazzafar kwallah. Ta kuma dade da barin jihar da suke ciki, ta lula wata jihar daban ta tunani mai zurfi. Wannan ya tabbatar mata akwai wani al’amari mai girma tsakanin Hafsat da handsome din da ta kira Yayanta kamar yadda ta ke ikirari. Amma tunda Hafsat mutum ce da ba ta son a yi mata shisshigi cikin (personal life) dinta zai fi kyau ta kyale ta. “Ni dai shawarata ita ce, duk runtsi kada ki bari ya kubuce miki, nasan mijinki ne ba saurayi ba,
irin wadannan daban ne Hafsat, alamu sun nuna yana daga cikin mazan da matan waje ba za su kyale wa matansu na gida kadai ba. In wannan ce matsalarki Hafsat ki cire kunya da kawaici ki damke mijinki da hannu bibbiyu, in ba haka ba za ki sha mamaki cikin garinnan”Sosai Hafsat ta yi mamakin yadda Mami ta gane Abdul’azeez mijinta ne. Maganganunta kuma kamar ta san me take ciki a rayuwarta da shi din. Bata ce komai ba sai binta da kallo. Www.bankinhausanovels.com.ng
A wannan ranar direban office dinsu ya sa ya maida ita gida sabida ayyuka da suka yi masa yawa. Don haka a hanyarsu ta dawowa ta kifa kanta jikin murfin motar ta yi kukanta mai isarta ta koshi. Kukan tausayin kanta… kukan rashin sanin mene ne aibunta da Abdul’azeez ya kasa sonta har duniya ta fara gane tana da matsala makamanciyar wannan a tare da shi? Aibubbuka da yawa Hafsat. Babban cikinsu ‘rasin asali’, don haka ki ci gaba da yi masa uzuri kamar yadda ki ka faro, watarana sai labari’. In ji zuciyarta.
**********
Sai da ya bari Hafsat ta kammala jarrabawar karshen zango da ta ke zanawa sannan ya je gida a wata ranar lahadi tunda ba ranar aiki ba ce, ya tabbatar Daddy yana gida a lokacin Isma’el ya koma America, Haleem da Usman ne kawai ya rage ba su koma inda suka fito ba. Ya samu Mammah da Azumi uwar goyon Suhaana wadda a yanzu za a iya ce mata kaka a gare su, ya ce ya zo ne da muhimmiyar magana, yana bukatar su zauna a falo dukkanninsu.
Mammah ta je ta fito da Daddy ya same su a falon har Haleem. Barrister da sanyin safiyar nan, ya aka yi?” Murmushi ya yi ya sadda kansa kasa. Har gobe Dr. Hamza bai bar jan ‘ya’yansa a jiki ba duk da dukkanninsu a yanzu babu wanda bai isa a yi masa aure ba banda Haleem, shi ma da a kauye ne ba irin rayuwarsu ba, da tuni ya jima da yin auren. Www.bankinhausanovels.com.ng
Sai da kowa ya nutsu ya ba shi hankalinsa, sannan ya fara ba su labari tiryan-tiryan tun hirar da yayi da Habiba aranar da al’amarin zai faru, da bincike da ya soma a boye akan garin Jimeta, haduwarsa da Barrister Sagir Hashim Jimeta. Yadda ya rika nace masa duk da kasancewarshi ba mai son harka da jama’a ba, sai dalilin kamanninshi da Suhaana. Yadda suka zama abokai na jiki a watannin da suka gabata da yadda har yake zuwa gidansa cin abincin dare duk don ya shiga jikinsa, ya tabbatar da abin da yake son tabbatarwa. Gayyatarshi daurin auren dan Yayarshi da Sagir yayi, da abin da ya faru zuwansu Jimeta ya kwashe duk ya gaya musu. Mammah da Baba Azumi sai kabbara suke yi zukatansu fal farin ciki. Dr. Hamza Atiku sunkuyar da kai ya yi yana tuna tarin wautar da ya yi a baya, yana kara istigfari cikin zuciyarsa.
Ka yi maganar da Addah?” Mammah ta tambaya.
Girgiza kai ya yi, “Ban taba yi mata zancen ba har bayan da na tabbatar, saboda bana son abin da zai dagula karatunta”’. Masha Allahu”. In ji Mammah.
“Tafiya Jimeta ta same mu, tunda ai ta kare jarrabawar ko?” “Ta gama jiya”’.
“Bari in yi wa mutanen Kano waya su shirya don gabadayanmu za a yi wannan tafiya”.
Kan ka ce me ye wannan Mammah ta hau bugawa su Adda Hafsatu waya, su Luba, Mariya, Furera da Murja, har Aunty Zuwaira da ke nan Abuja ba ta bari ba. Matar Uncle Idris da matar Ibrahima da sauransu. Cewa su yi shiri za su tafi Yola an gano iyayen Addarta. Tsofaffin hotunansu da suka sha yi da Habiba a Jeddah ta hau bincikowa, Abdul’azeez ma yana da wasu daga ciki, ya sanya a aljihu ya tafi da su har Jimeta da zummar in bukatar hakan ta taso ya fiddo su, to kuma da ya canza shawarar rashin tada maganar a lokacin daurin auren ya dawo da abinsa ya boye inda Hafsat ba za ta gani ba.
Shiri sosai wannan family ke yi na tafiya Jimeta (Yola North), wanda za su yi kwanaki uku masu zuwa. Mammah ta kasa bari har zuwa karshen mako don haka ta sanya tafiyar ranar Laraba, masu aiki su dauki uzuri. Www.bankinhausanovels.com.ng
Washegari a ofis dinsu ya tadda Sagir yana rubutu cikin wasu ‘files’. Gaisawa suka yi kamar yadda suka saba, tun kafin ya yi magana Sagir ya riga shi, ya gaya masa Dada ta ce a yi masa tuni kan maganar nan ko tana da rabon ganin ‘yarta a sauran numfashinta. Ta fara kasa jurewa jiran.
Sadda kai Abdul’azeez ya yi yana jin wani iri a zuciyarsa. Daga bisani ya ce da Sagir, abin da ya kawo shi kenan. Iyayensa sun yi shirin tafiya Jimeta a kan maganar Habiba ranar Larabar nan ya sanar da su Dada. Iyayenka???” Sagir ya tambaya cikin mamaki. Daga masa kai Abdul’azeez ya yi da siririn murmushi a fatar bakinsa, ya ce, “Dogon labari ne Sagir, amma a gidanmu Yayarka ta zauna. Sauran bayani sai mun isa can”, Daskarewa Sagir ya yi a zaune, yana tazbihi yana kadaita Allah.
**********
A falo ya tadda Hafsat, ta yi daidai da takardu irin na zane manya-manyan nan tana zana World Atlas . Wani assignment ne na cikin hutu (holiday assignment) aka basu akan wani kwas ‘ map analysis’ . Zane ta ke yi na kwallon duniya world map ta maida hankalinta kacokam kan abinda ta ke yi. Idan ka kalle ta a zuciyar ka abinda zaka fara cewa shine; ( A Geographer withdetermination and enthusiasm). Ko shigowar motarsa ba ta ji ba balle takun sawunsa. Tsayawa ya yi a bakin kofar shigowa falon ya jingina da kofar hannunshi na hagu na dogare da kofar dayan na cikin aljihun wandonsa. Langabar da kansa ya yi gefe yana kallonta. Watanni goma sha biyar kenan cif da aurensu, wanda ya yi daidai da SHEKARA DAYA da watanni uku.
Abubuwa da yawa sun faru cikin wadannan watanni goma sha biyar din wadanda ba za su Www.bankinhausanovels.com.ng
taba shafewa daga kwakwalwarsa ba! Masu dadi da marassa dadi, na ban dariya dana ban haushi. A cikin wadannan watanni, Mu’azatu ta gama LLB tayi karatu a ‘Law-school’ ta gama ta fito a matsayin cikakkiyar lauya daidai da burinsa na matar da zai aura. Ya zauna da Hafsat-Suhaana cikin wadannan watanni zama wanda aka tsara yadda zai kasance tun farko, amma abin mamaki ya rikide ya Jirkice zuwa ba yadda aka tsara shi ba. Ya zo da abubuwa masu yawa beyond his mere or casual assumption… ..
Awata rana irin ta yau daidai wannan lokacin yana rungume da Mu’azatu a ofis dinsa yana daukar mata alkawurran da ba’a so musulmi ya dauka saboda ba shi ke iko da rayuwarsa ba. Gabadaya rayuwarmu rubutacciya ce tun haihuwarmu a Allon Lauhul-Mahfuz . Manzon Rahma (S.A.W) ya ce, yana daga cikin alamomin munafuki in ya yi alkawari sai ya saba , in aka amince masa Sai ya yi ha’inci , idan ya yi zance sai ya yi karya (Bukhari).
Ya yi wa Mu’azatu alkawari, in ya saba sunansa MUNAFIKI. Ya yi wa Mu’azatu zance tun daga karkashin zuciyarsa, in ya canza shi ya yi KARYA . Mu’ azatu ta amince masa, in ya zabi Hafsat ya barta ya yi HA’INCI . Ta rabu da kowanne Da namiji saboda shi. Shekaru ukku kenan cif tana dakon soyayyarsa mai wahala a zuci. Lokaci ya zo da zai aiwatar da kalaman bakinsa yana so ko ba ya so. To amma anya babu babban kuskure a cikin al’amarin nan? Yaya rayuwar Hafsat za ta kasance in ya rabu da ita? Karatunta zai dore? Mammah za ta barta ta ci gaba da makaranta babu aure? Zuciyarsa wadda har yau ba ta baiwa Hafsat matsugunni guda daya a cikinta ba ta ce da shi.
“Tun farko ba ka yi wa Hafsat alkawarin rayuwa mai dorewa da ita ba, kuma ta san wannan. Abu daya ka ke yi wa shi ne SABO! Ba mutuwa ake yi wa kuka ba ‘sabo ne’, da sannu zai gushe tamkar ba a yi shi ba. Babu mai mara maka baya ka auri Mu’azatu kana tare da Hafsat. Matsayin da Hafsat ke da shi babu soyayyah sai emotion. Wani irin ‘emotion’ na can karkashin zuciya. Wanda a kullum yake da nauyi kamar ansababban dutse an danne shi. Zuciya mugun nama.. ta ci gaba da angiza shi da cewa… Mu’azatu na jiranka Abdul’azeez da tarin soyayyah mara algus….. za ku shimfida rayuwa mai ma’ana irin wadda ka ke buri….. soyayyah irin wadda ka ke mafarki… yadda ta yi maka tanadin kanta tsawon shekarun nan ta tsayar da soyayyarta a kanka kai kadai, ta cancanci ka watsar da komai ka cika alkawarin da ka daukar mata… sai ka rabu da Hafsat ne za su dubi al’amarinka da Mu’ azatu da idanun basira. Www.bankinhausanovels.com.ng
Hafsat duk wasu alkawururruka da ka daukar mata a yau Allah ya nufa ka cika mata su. Abu daya ya rage ka damka ta a hannun MAHAIFINTA, wanda in Allah ya so Ya yarda wannan ya zama tarihi. Zuciyar ta ci gaba da qawata masa komai na Mu’azatu ya fi na Hafsat sau dubun dubata. Hafsat har gobe kamata ya yi a ce tana gaban iyayenta suna ci gaba da rainonta… yadda ka shirya rayuwa da matarka ta aure da tarin bukatar gangar jiki da zuciya,me Hafsat za ta iya dauka a ciki? Wane martanin soyayya kake tunanin samu daga gare ta? Mu’azatun dai! Ita ce daidai da rayuwarka, wadda za ta zage ta nuna maka soyayya dakwanji, da jiki da zuciya.
********
kyakkyawar rayuwar da zai shimfida da Mu’ azatu in ya same ta. Bangaren kyakkyawan tunani ya toshe, idan ma akwai, to son cika alkawarin da ya dauka ya rinjayi komai… A ganinsa in ya cika wannan alkawarin ne zai kubuta daga sahun munafukai, makaryata, maha’intakuma rayuwarsa ta zauna lafiya. Duk sanda zuciyarsa ta kawo masalaha ga rayuwar ita Hafsat din, daya zuciyar sai ta hambare. Da hujjarta na cewa, ‘ ita ‘yar gata ce yanzu… mai iyaye, ‘yan uwa da kakanni babu abin da zai dame ta don ta rabu da kai … Mammah kuwa in za ta yi adalci ai ka yi mata biyayya, lokaci ya zo da za ta karbi naka zabin ta ba ka ‘yancin da Ubangiji ya ce ta baka. A zaman da ka yi da ‘yarta ba ka taba cutar da ita ba… ba ka taba bata mata ba sai ko bisa ajizanci irin na dan adam, ko ka yi kuskuren ma kana kokarin gano kuskurenka da kanka ka yi ‘repenting’. Idan ba a gode maka ba a rikon da ka yi wa Hafsat, to a kalla ba za a yi maka tofin Allah tsine ba……!!!” Www.bankinhausanovels.com.ng
Da wannan kwarin gwiwar Abdul’azeez Hamza Atiku ya dauke ido daga kallon Hafsat, ya karasa shiga cikin falon. A lokacin ne Hafsat ta ankara da shigowarsa. Wani irin dadi ta ji a ranta domin sosai ta yi kewarsa a gidan tun fitarsa. Rashin abin yi ne ya sanya ta yin assignment din kuma map din ya yi kyau sosai kamar ba ita ta yi ba. Ga mamakinsa ya kasa hada ido da Suhaanah a yau, kai tsaye ya nufi dakinsa ba tare da ya ce da ita komai ba.
Hafsat ta yi dan jimm! Me ke damun Yayanta Abdul’azeez? Ko wani ne ya bato masa rai a waje? Mikewa ta yi da niyyar binshi dakin, amma sai ta dakata. Sun dade da daina shiga dakin junansu. Sannan a lokacin da miji yake cikin fushi matarsa nesa-nesa ya kamata ta yi da shi. Damuwarta shi ne, ta shirya masa abinci mai rai da motsi da za ta so ya ci kafin ya shiga barci. Amma haka ta hakura ta soma tattara kayan zanenta don barin wajen.
A wannan daren mai cike da rudani ga Abdul’azeez Dakata daga shi har Hafsat kowanne ya kasa barci. Cikin sulusin dare ya samu takarda ya yi rubutu ya ninke ya adana a lokar gefen gadonsa. Wata irin ajiyar zuciya ya saki ya maida kansa ya jingina a kan filo. Amma ga mamakinsa ya kasa runtsawa. Ya rasa takamaiman abu guda da kwakwalwarsa za ta kama, gabadaya ta hargitse, ta cukwikwiye, duk kuwa da ya yanke hukuncin da zuciyarsa ta fi amincewa da shi din. Kamata yayi ace ya samu (peace of mind) bayan zartas da hukuncin amma kamar ya kara hargitsa kwakwalwar sa fiye da baya.
Hafsat kuma damuwarta me ke damun Abdul’azeez ne? Ba ta taba ganinsa cikin wannan yanayin ba. Ko ba ya jin yin magana zai gaya mata ba ya son magana ta yi harkarta ta kyale shi. Amma a yau ko alfarmar hakan ta kasa samu balle ta ga kwayar idanunsa. Ga shi da alama yana cikin rudani irin wanda ba ta taba ganinsa a ciki ba. Ta samu kanta da mikewa ta dauro alwala Www.bankinhausanovels.com.ng
ta dasa sallar nafila cikin daren. Addu’a ta ke ko mene ne matsalar Abdul’azeez Allah Ya ba shi kyakkyawar mafita, Ya iya masa abin da ba zai iya ba, Ya shige masa a gaba a kan al’amuransa (Allah sarki Hafsat).
*******
Wani barci ne mai nauyi ya sure ta gabanin asubahi, bayan ta idar da sallar asubah. Ba ita ta farka ba sai wayewar gari tangararan. Lokacin tuni Abdul’azeez ya tsufa a ‘office’. Takaicin kanta ne mai tsanani ya kamata. Haka ta mike ta yi wanka ta shiga kicin don sama wa cikinta abin da zai ci.
Abdul’azeez bai dawo gidan ba har ta yi shirin barci, gidansu ya tafi a can ya ci abinci. Hatta Mammah ta lura cikin damuwa yake, amma da bai furta ba sai ta kyale shi. Yana gidan har karfe goma, Mammah ke tambayarsa ko ya gaya wa Hafsat maganar tafiyarsu Yola? Ya ce, abubuwa sun masa yawa, ya manta. Amma da ya koma zai gaya mata. Fada sosai Mammah ta hau yi masa na ba ya daukan abubuwan kowa da muhimmanci sai nasa. Hakuri ya ba ta ya kuma tabbatar mata yau zai gaya mata.
Da ya dawo ta dade da shigewa daki ta kashe wuta ta kwanta. Ko ta yi barci ko ba ta yi ba, ba zai iya cewa ba. ‘Text’ ya yi mata a ciki ya ce ta shirya kayanta da na bukata wanda zai yi mata sati biyu za su tafi jihar Adamawa jibi dukkansu, har su Mammah.
Washegari tana kunna waya abin da ta fara gani
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG