SHU’UMIN NAMIJI CHAPTER 13 BY FATYMA SARDAUNA

SHU’UMIN NAMIJI CHAPTER 13 BY FATYMA SARDAUNA

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

Yana zaune acikin falon, taturo ƙofa tashigo bakinta ɗauke da sallama, cike da mamaki yake kallonta. “Bakije gidan Ƙawartaki bane?” ya tambayeta yana me tsareta da kyawawan idanunsa.

Murmushi tayi haɗe da ƙarasowa cikin falon, zama tayi gaf dashi, haɗe da ɗaukan hanunsa ta ɗaura akan cinyarta.   “Naje nasamu batanan, kuma dama banaso nabarka kai kaɗai agida, shiyasa na dawo” tafaɗi haka tana me ƙara faɗaɗa murmushinta.

Kansa yajinjina haɗe da ɗaukan goran ruwan dake  aje a gabansa, yakai bakinsa,  kallonsa take tanaso tafaɗa masa abun dake cikin ranta, amma kuma tsoro takeji saboda batasan taya zai ɗauki maganar ba.

Matsewa kawai tayi haɗe da sanya hanunta ta saƙalo hanunsa,  fuskarsa takafe da ido kana tace “Yau nahaɗu da Zahrah”

Da sauri ya ɗago kansa ya kalleta, cike da tsananin mamaki yace “Wace Zahrah?”

“Zahrah wacce kasani, wacce kuma tunaninta ke maƙale acikin zuciyarka, babu dare babu rana” ta bashi amsa.

“A ina kikasanta, har kikasan cewa itace Zahrah’n danake tunani akowani lokaci?” yajefomata tambaya yana me kafeta da idanunsa.

“Duk wanda yasanka dole zaisan Zahrah, mussamman ma ace wanda yake kusanci dakai, ko kamanta cewa har yanzu akwai hotonta acikin ɗakinka?”

Miƙewa yayi daga zaunen dayake haɗe da cusa hannayensa cikin aljihun wandonsa.

“Zahrah ɗaya na sani a rayuwata, kuma tajima da mutuwa, saboda haka ni bansan wata Zahrah ba” yanakaiwa nan azancensa yasakai yawuce cikin bedroom ɗinsa, ko waiwayenta baiyi ba.

Mamakine ya bayyana ƙarara akan fuskar Afrah, sakamakon jin kalaman Zaid da tayi,  “Dare safe rana, bashida wani aiki sai tunaninta, tasha jinsa yana kuka a toilet, dukkuma akan Zahrah ɗinne, amma wai kuma yau da bakinsa yake cewa Zahrah ta mutu, anya kuwa Zaid yana lafiya?” Afrah ke magana da zuciyarta.

Murmushi tayi asakamakon tunawa da wani abu da tayi, tashi tayi tanufi ɗakin da Zaid yashiga.

Yana zaune agefen gadonsa hanunsa, riƙe da wani littafi da kuma biro,  da’alama nazartan littafin yake, amma kuma idanunsa cike suke da ƙwalla, yanajin motsin shigowar Afrah, yayi sauri ya rufe littafin, ransa a ɓace, ya juyo gareta.

“Mekikazo ɗauka? Bana faɗa miki cewa bakoda yaushe ne, nake da buƙatarki ba, please get out!” yaƙare maganar yana meyi mata nuni da ƙofar fita daga cikin ɗakin.

Ajiyar zuciya ta sauƙe haɗe da takowa zuwa garesa, tana zuwa gabansa ta durƙusa haɗe da zube guiwowinta a ƙasa.

“Kagafarceni idan abun dana faɗa maka akan Zahrah ya ɓata maka rai, banyi haka donna ɓata maka ba, saidai kuma zanfaɗa maka koda zaka tsaneni ne,  wallahi bazaka taɓa yin rayuwar farinciki ba, harsai kasamu Zahrah ka ƙara neman yafiyarta,  nasan cewa kana da buƙatar Zahrah akusa dakai, fiye da yanda kake da buƙatar ko wace mace a duniya,  amma kuma ƙaddara babu yanda bata juyawa bawa, dan Allah kayarda dani, akwai abunda zanyi wanda zaisa kusamu jituwa a tsakaninka da Zahrah, harma da mijinta”

STORY CONTINUES BELOW

Kallonta yayi da jajayen idanunsa haɗe da tashi, kawai yawuce cikin bathroom.

“Afrah bazata taɓa ganewa bane, shi kaɗai yasan irin zogi da kuma ciwon da zuciyarsa keyi masa, aduk sanda aka ambato masa sunan Zahrah,  a yanzu so yake yasa aransa cewa, babu wata Zahrah, domin wacce yasani tajima da mutuwa, wanda yake gani a yanzu, wata Zahrah’nce daban kuma ta wani ce”  tsaida zancen zucin nasa yayi,  haɗe da cire rigar dake  jikinsa, direct gaban shower ya nufa, tsayawa yayi haɗe da sanya hanunsa  ɗaya, ya dafa jikin bango, ruwane keta dukan kansa dakuma bayansa, sauda dama idan yana acikin ƙunci, tsayawa yake gaban shower ruwa yaita dukansa, dahaka yake ɗan samun relief.

*** ***

Kwance take akan kujera, sanye take da wani dogon sket, wanda yake a tsuke daga sama har ƙasansa,   sket ɗin  irin roba ɗinnnan ne,  rigarta kuwa wata ƴar vest ce marar nauyi, fara ƙal da ita, tunda ta samu cikin nan, bata rabo dajin zafi, hakan yasanya bata cika zama da kaya masu nauyi ba,  wayartace rike a hanunta, kunnenta kuwa sanye suke duka da airpiece, waƙar film ɗin Sanam Teri Kasam takeji, harwani lumshe ido take, saboda tanason waƙoƙin film ɗin sosai,   sweet ne abakinta tana ɗan tsotsa, gudun tara yawu, dayake bata ƙure volume ɗin waƙarba, hakan yasanya tajiyo bugun ƙofar da akeyi mata,   da mamaki take kallon ƙofar falon, ita dai tasan batayi da kowa cewa yau zaizo wajenta ba, kuma yanzu ba lokacin dawowan Doctor bane, batajin zata iya tashi dan haka saita bawa me knocking door ɗin damar shigowa kai tsaye.

Da sallama ɗauke a bakinta, tashigo cikin falon.  Kallon kallo suka shigayiwa juna ita da Zahrah,  ita tana kallon Zahrah ne fuska ɗauke da murmushi, yayinda  Zahrah kuwa ke ƙare mata kallo, saboda batasanta ba ma ita kwata kwata.

“Da dai anbani izinin shigowa, aida sai na shigo” takatse Zahrah daga kallon da take mata, ta hanyar faɗan haka.

Murmushi Zahrah tayi haɗe da tashi zaune tace “Bismillah, shigo”

Ƙarasowa tayi tsakiyar falon, haɗe da zama akan kujera.

“Sannu da gida” tace tana murmushi.

“Yauwa sannunki da zuwa” Zahrah tafaɗi haka itama tana murmushi.    Miƙewa tayi da niyar takawo mata ruwa da lemo, da sauri tace. “A’a barshima basai kinkawomin komai ba, daga gida nake banajin ƙishi”

Kallonta kawai Zahrah tayi kana ta koma kan kujera ta zauna, cike da ƙosawa Zahrah tace.  “Baiwar Allah Bangane wace ke ba fa”

Murmushi takumayi akaro na barkatai.   “Sunana Afrah, dama nasan baki sanniba, amma ni nasanki, kiyi haƙuri bansaniba ko hakan danayi yaɓata miki rai, jiya naganki a hotel kinacin abinci keda wani, wanda nake kyautata zaton cewa mijinki ne, tunda naganki, naji kin kwantamin arai, kuma wallahi da zuciya ɗaya nake sonki, please idan bazan takuraki ba, inaso muzama ƙawayen juna”

Murmushi Zahrah tayi me sauti, haɗe da cewa “Nagode ƙwarai da ƙauna, amma kuma inaganin kamar akwai matsala, idan har muka fara ƙawance yanzu, dududu fa yau nafara ganinki, kinga dole kafun abota musan halin juna” inji cewar Zahrah.

“Da alamu bakida wata matsala nima kuma haka, kuma insha Allah bazakiyi danasanin ƙawancen mu ba”   taƙara da cewa “Akan hanya nake, watarana zanyi miki zuwa na musamman amma kafun nan,please samin number’n wayarki” miƙawa Zahrah wayarta da ta cirota cikin jaka tayi.

Babu musu Zahrah ta amshi wayar tasanya mata number’nta aciki, kana ta miƙa mata abarta.

Murmushi tayi haɗe da miƙewa tsaye, “nagode sosai” tace kana ta nufi hanyar fita daga cikin falon, Zahrah na ganin ficewarta ta sauƙe ajiyar zuciya, haɗe da komawa ta kwanta, aranta tana addu’an neman tsari daga sharrin mugayen mutane, da kuma aljanu….

*** *** ***

Gaba ɗaya yau tatashi jikinta arikice, ganin haka yasa Dr.Sadeeq hana kansa zuwa office, yazauna tare da ita, yanata amsar shagwaɓanta, zuwa yanzu sosai shagwaɓanta yafi na da, tun da tasamu cikin wani sakalci da taɓara ya tsiro mata,  shikuwa doctor biye mata yake, hakan yasa gaba ɗaya yanzu tazama wata, shagwaɓaɓɓiya da ita sai kace ƴar shekara 4.

Kwance take akan sofa yayinda kanta ke ɗaure bisa cinyarsa, minti irin me tsinkenan ne abakinta, tana tsotsa a hankali, yayinda shikuwa ke shafa sumar kanta a hankali.

_______

STORY CONTINUES BELOW

Mamakine ya matuƙar kashesa, ganin unguwa da kuma inda Afrah ta kawosa, ɗago idanunsa yayi ya watsamata su, “Inane nan?” yatambayeta still idanunsa na kanta.

Murmushi tayi masa haɗe da cewa “Unguwar su ƙawartawa da nake gaya maka ne, kuma ganan ma gidan nata” taƙare maganar tanayi masa nuni da gidan dake gefensu,   bugawar zuciyarsa ne ya ƙara tsananta,  take yaji kansa nayi masa wani irin sarawa.

“Kimaidani gida Afrah, tunkafun ranki ya ɓaci!” cikin yanayi na ɓacin rai yake maganar.

Dama tasan za ayi haka,  hanunta ta ɗaura akan nasa cikin son ta rarrasheshi tace “Kayi haƙuri Dear, bazamu wuce 30 minute ba, nasan kasan gidan, kakuma san wacece acikin gidan, banyi haka donna ɓata maka ba, nayi hakane don kawai kasamu salama, ƙwarai nasan idan harta yafema kuma ayau idan kuka ga juna, tabbas komai zai wuce, duk da nasan sai ahankali, amma kuma dukanku zaku samu sassauci….”

“Kimaidani gida nace kona ɓaɓɓala ƙashinki gida biyu anan wajen!!” amatuƙar hasale yaƙare maganar.

Saida ta tsorita domin bata tsammaci wannan tsawan daga gareshi ba.  

“Fita” yace da ita murya a dake.

Sumi sumi ta fice acikin motar, dan ta fuskanci sam babu alamar wasa a tattare dashi. Fita shima yayi daga cikin motar ya koma wajen zaman driver domin dama a wajen mai zaman banza yake dazama, itakuma tana wajen zaman driver.

Yana shiga yatada motar, kallon  Afrah yayi fuska babu walwala, da sauri ta buɗe motar tashiga, da ƙarfi yaja motar sukabar ƙofar gidan.

Suna zuwa gida, ya wuce ɗakinsa kai tsaye, itama Afrah tayi nata ɗakin,  sam bataso haka yakasance ba, taso ace  abun da ta ƙudurta aranta shine ya faru.

Kayansa yashiga haɗawa acikin trolly ɗinsa, saida yatabbatar ya haɗa duk wani abun da yake buƙata,  dama kuma jiya aka kawo masa visa’n su.

Tana tsaye agaban mirror daga ita sai wata ƴar fingilan riga, kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kansa,  akwatinta ya ciro acikin drawer, kallonta yayi itaɗinma kallonsa take.

“Kishirya kayanki, 6 pm zamu tashi gobe insha Allah” yanakaiwa nan azancensa yasakai yafice daga cikin ɗakin.

Mamakine yakama Afrah,  “dama ya shirya musu tafiya shine baisanar da’ita ba?” tambayar da tayiwa kanta kenan,  ganin bata da wani wadataccen lokaci yasanya, tashiga shirya kayanta acikin trolly’n, da ya fito mata dashi. 

Zama yayi akan gado haɗe da jawo diary ɗinsa ya buɗe, abun rubutu ya ɗauka yaɗanyi rubutu, kaɗan kana ya rufe diary’nnasa ya  tura acikin wata ƴar ƙaramar jaka.

Washe gari

Kamar yanda ya faɗa ƙarfe 6 dai dai jirginsu ya ɗaga zuwa ƙasar America, a wannan karon baya tunanin zai waiwayo Nigeria, so yake ya koma America da zama gaba ɗaya,  wannan shine ƙudurinsa, sai dai idan Afrah tace zatazo  Nigeria bazai hanata ba, shikam dai yasa aransa cewa bazai zoba, saidai ko wani babban dalili, me ƙarfi.

***   *** ***

Abuja University Gwagwalada.

Yau suke bikin kammala degree ɗinsu, saboda haka gaba ɗayansu sunacikin farinciki.   Kowannensu yasha adonsa cikin shiga ta burgewa gwanin ban sha’awa.

Tsaye take ajikin wata bishiya tana waya,  sanye take da baƙar tie abaya gown ajikinta, wacce daga hanunta zuwa ƙasanta aka mamayeta da ado na flowers masu kyaun gaske.   Da babban mayafi tayi amfani wajen rufe jikinta, sai dai kuma duk da haka, saida cikinta ya bayyana kansa, sosai taƙara haske da kuma kyau, sai wani ɗaukar ido take, daganinta kaga me ciki, wacce take cikin jin daɗin,  yanzu watannin cikinta huɗu kenan amma kuma tuni ya bayyana kansa, ita kanta har mamakin girman cikin nata take, don watanninsa basukai ace girmansa yakai  har  haka ba.

“Zakizo mu kammala pictures ɗinne kokuma zaki tsaya soyewa”   Husnah dake tahowa ga Zahrah tafaɗi haka da ɗan ƙarfi. tayanda Zahrah’n zata jita.

Murmushi Zahrah tayi haɗe da kashe wayar, kana ta juyo da kallonta ga Husnah.

“Kinsan banagajiya da jin muryarsa ne, amma muje mukammala agurguje, saboda gida nakeson nakoma gaba ɗaya jina nake agajiye” Zahrah ta  faɗi haka tana ɗan yamutsa fuskarta.

Murmushi Husnah tayi haɗe da cewa “Nima sauri nake saboda yau Man ɗina zai turo magabatansa gidanmu, kuma ayau za’a sa mana ranan aurenmu, nasankuma baza asa ranan da yawa ba, just ba zai wuce 1 month ba”

Dariya Zahrah tayi haɗe da cewa “Lallai Husnah aure kikeso sosai, ji yanda lokaci ɗaya kika falle.”1

Dariya sosai Husnah tayi haɗi da cewa “Laifine dan mace irina taso aure? nakai aure, nakuma cika mace me lafiya, kinga kuwa dole naso aure, ke nifa wallahi gaba ɗaya yanzu rayuwata, a daddafe nakeyinta, na ƙosa najini a ƙirjin mutumin, nima yakasheni da irin nasa salon” cikin yanayi na shauƙi ta ƙare zancen.

Dariya dukansu sukayi  kana suka tafa.

Basu tsaya an kammala bikin dasu ba, kowaccensu ta nufi gida.Kwance take akan gado, hanunta riƙe da littafin hausa, tana karantawa,  sanye take da doguwar riga irin bubu gown ɗinnan, zuwa yanzu cikinta ya ƙara girma, har tsoro girman ke bata, ga yawan motsin da takeji acikin cikin nata.

Yajima a tsaye yana kallonta,  sosai cikin ya ƙara mata kyau, gashi cikin ya bayyana kansa acikin rigar dake jikinta.

“Ƴan mata na!” yaƙira sunanta cikin wata murya me sanyi.

Da sauri ta dawo da kallonta garesa, murmushi tasakar masa, haɗe da tasowa daga kan gadon, da ɗan gudu gudu, tafaɗa cikin jikinsa ta rungumesa.

Hannuwansa yasanya duka biyu shima ya rungumeta,  kiss ya manna mata akan wuyanta, haɗe da lumshe idanunsa, yana me shaƙan ƙamshin jikinta, sosai ƙamshin nata keyi masa daɗi.

“Nayi kewarki madam ɗina me ciki” yafaɗi haka yana me shafa cikin dake jinkinta.

Ashagwaɓe tace “Nima nayi kewarka sosai fa dear!”

“Dagaske kinyi kewata? keda ma kika hanani abun daɗina, two days fa kenan yau baki bani zumana ba!” cikin yanayi na ɗan karya murya yafaɗi haka, lokaci guda yana me marerece idanunsa.

Ɗan ƙaramin bakinta taturo gaba, cike da shagwaɓa tace “To bakaineba saikanamin da ƙarfi, kuma Allah Hubby yanzu  idan kajima kanayi sainaji kamar zan amar da kayan cikina, gashi tsoro nakeji idan kana fidda wannan sautin numfashin, kamarfa zaka sume haka kake”

Sake marerece fuska yayi haɗe da kwantar da kanta akan wuyansa, hanunsa ya ɗaura akan cikinta.”Babyn Mama kaine kake wahalar min da mata ko? kuma kaine kake hanawa abani abun daɗi na ko? please my boy kabari yau abani ko kaɗanne, kuma ae balaifina bane, banasanin ma inayin kamar zan shiɗe, kuma ma ae daɗin kine yake da yawa ko Baby boy ɗina?”  yatambayi yaron cikin?

Dariya ne yakamata ganin yana magana da cikin,  “Kai Hubby ina ma zaijika, ko saninka fa baiyi ba, ni kaɗai ya sani” ta ƙare maganar tana dariya.

“Wayace miki baisanniba, lallai kam idan bai sanniba ae kuma shikenan magana ta ƙare, taya ma za’ace baisan wanda ke yawan aika masa gaisuwa ba? dan ma dai kwana biu….”

“Shiii! Ina roasted fish ɗina, da nace katahomin dashi?” taje fo masa tambayar ta hanyar katsesa daga maganan da yakeyi.

“Nakawo miki yana falo..”

Bata tsaya jin sauran zancenba, ta wuce falo cikin sauri.

Zama tayi akan sofa tashiga cin roasted fish ɗinta, sosai taji daɗin kifin, domin kuwa da ɗuminsa aka kawo mata, gashi yaji onion sauce. saida taci sosai kana ta ɗaura da lemon exotic.

Shikuwa tana fita acikin ɗakin, direct bathroom ya nufa, wanka yayi, domin dama agajiye yake sosai, kasancewar daga office ya dawo.

Fitowarsa daga cikin bathroom ɗin yayi daidai da shigowarta cikin ɗakin. Kallonsa tayi haɗe da sakar masa murmushi, shima murmushin yayi mata, kana yanufi gaban dressing mirror don kimtsa kansa.  Doguwar riganta ta cire kana ta faɗa toilet.

Lokacin da tafito ɗaure da wani ɗan ƙaramin towel ajikinta, shikuma yana zaune akan gado, yana sipping fresh milk, a hankali.   Kallon santala santalan cinyoyinta yayi, haɗe da haɗiye wani yawu, sosae yake missing matar tasa, musamman ma daddaɗan ɗumin dake cikin jikinta, wanda idan yajisa yake sanyasa cikin nishaɗi da kuma nutsuwa.  Kasa haƙuri yayi alokacin da ta juya masa baya, mai take shafawa ajikinta, yayinda towel ɗin yaɗan zame daga kan ƙirjinta, har tsayayyun breast ɗinta suka ɗan bayyana kansu

STORY CONTINUES BELOW

Rungumeta yayi ta baya, haɗe da ɗaura kansa bisa wuyanta.  Hancinsa yashiga gogawa akan wuyannata yana  me busa mata numfashinsa me ɗan ɗumi akan fatarta, take taji tsikar jikinta na tashi,  ɗago idanunta tayi ta kalleshi, shima idanunsa ya jefa acikin nata, wani irin kallo me matuƙar kashe jiki, yake jifanta dashi, bazata iya ɗauke idanunta, daga cikin nasa idanunba, haƙiƙa kyawun idanunsa, na matuƙar ɗaukar hankalinta,  lumshe idanunta tayi, haɗe da sauƙe wani irin numfashi, sake jawota jikinsa yayi haɗe da  ɗaura duka hannayensa, akan ƙugunta,  matso da fuskarsa yayi daf da tata, har hancinsu na gogan najuna, still idanunta a rufe suke bata iya kuma buɗesu ba,  ɗaura bakinsa yayi akan nata bakin, a hankali ya shiga tsotsan leɓenta na ƙasa,  yayinda itama  ke tsotson lip ɗinsa na sama,  numfashi suka shiga sauƙewa a tare, harshenta yakama yana sha a hankali, yayinda yasanya hanunsa, ya warware towel ɗin dake ɗaure ajikinta, hakan yabawa towel ɗin daman faɗuwa ƙasa,  ahankali yake shafa bayanta, zuwa gefe da gefen cikinta,  sauƙar numfashinta ya tsananta, saboda sosai takejin daɗin abun da yakeyi mata.  Harsaida tasamu kusan ɗaukewar numfashi, alokacin daya soma murza breast ɗinta, yanayin yanda yake mata ya matuƙar shiɗar da ita, ashe bashine kaɗai yayi missing ɗinta ba itama tayi kewarsa sosae. Hanu tasa ta zame rigar dake jikinsa,  wani irin ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya suka sauƙe alokaci guda, sakamakon haɗuwar fatar jikinsu waje ɗaya,sosai hakan yasake basu wani shauƙi. Kasa jure yanda take goga masa tausassun breast ɗinta akan chest ɗinsa yayi, ɗagata yayi caɗak suka nufi kan bed. 

Kwantar da ita yayi flat haɗe da bin ko ina najikinta da kiss, har izuwa kan breast ɗinta.   Sosai yashiɗar da ita, yayinda shikuma ya zauce,  ba abun dake tashi acikin ɗakin, sai sautin numfashinsu, dake fita a hankali….. Yau love fa yakawo wuta, domin kuwa gaba ɗaya Doctor ya manta, da kansa da kowa nasa, Zahrah’nsa tabasa zuma wanda samunsa ke da matuƙar wahala, musamman kuma daya kasance wannan zuman natane ita kaɗai, Allah yabata, sauran kuwa kowacce da irin tatabaiwar,   sosai yau doctor ya tara mata gajiya, sai kukan shagwaɓa kawai takeyi masa, dakansa yayi mata wanka, bayan yayi nasa, kana ya naɗota a towel kamar wata ƴar baby, kwanatar da ita yayi akan gado, bayan yasanja bedsheet ɗin, domin wancan ya ɓaci da sperm ɗin Me daɗinsa,  shi har mamakin yawan ruwa irinnata yake.  Kwanciya yayi shima akan gadon kana yajawota jikinsa, luf tayi acikin jikinsa, tana me fesa masa iskan numfashinta, acikin ƙirjinsa.    Bayanta yake shafawa a hankali, yana me sauƙe ajiyar zuciya akai akai.    Ƙamshin turarensa dake tasowa yana shiga cikin hancinta, shine abun da ke neman hautsina mata ƙwaƙwalwa, domin kuwa, yana mata yanayi da wani ƙamshi  wanda har abadan duniya bazata taɓa, mantawa da ƙamshin da kuma mai ƙamshin ba,  take bugun zuciyarta ya tsananta, haka nan taji zuciyarta naneman karyewa,  bazatace ta manta dashiba, domin kuwa aduk kwanan duniya yana maƙale acan ƙasar zuciyarta. “To tayama za’ayi ta manta dashi?” tambayar da tayiwa kanta kenan, lumshe idanunta tayi, alokacin da ta tuno da haɗuwarsu ta ƙarshe, alokacin daya kusanto zuwa gareta yana me neman yafiyarta, bazata taɓa mantawa da wannan ranan ba, kamar yanda bazata taɓa mantawa da ranan daya fyaɗeta ba,  wani murmushine ya kuɓuce mata, batare da ta shiryawa hakan ba,  azuciyarta tace “Lallai Zaid yayimini babban Illa, wanda har nakoma ga mahaliccina tabonsa bazaigoge ba, yayimin fyaɗe sannan kuma ya koyamin soyayyarsa” batasan da cewa hawaye sun fito daga cikin idanuntaba, saida taji ɗuminsu nabin kan kumatunta, da sauri tasanya hanu ta share gudun kada doctor ya gani. Ashe ta makaro domin kuwa  idanunsa na kanta.  Sake matseta yayi acikin ƙirjinsa, haɗe da kai bakinsa, kan nata yashiga tsotsa a hankali,  ganin haka yasa takama harshensa tana tsotsa, kamar tasamu sweet,  sosai takejin daɗi idan tana sucking tongue ɗinsa, har wani suga suga takeji akan harshen,  wata ƙila hakan yana da nasaba, da yawan shan sweet da yakeyi, zaiyi wuya kaga bakinsa shiru babu sweet aciki, hakan ajininsa yake. (Kamar dai sweet and big bro ɗina, i miss you yayana😰)     bedaina kissing ɗinta ba harsai dayaji sauƙar numfashinta, nafita slowly, alaman tayi bacci kenan, mintuna kaɗan shima bacci ya ɗaukesa….

*** *** ***

America.

Tunda sukaje America take ta fama da rashin lafiya, gaba ɗaya ta zafge ta rame sosai, ga Zaid daya sata agaba, kullum saiyayi sex da ita sama da sau biyu.  Yanzuma durƙushe take aƙasan tiles tanata kwarara amai,  ko kyakkyawan motsi takasa yi.

Shigowarsa gidan kenan, sosai yaƙara kyau da haske,  ƙaƙarin amanta daya keji ne yasanya sa nufar ɗakinta da sauri.  Tagama aman amma takasa tashi daga wajen domin gaba ɗaya jikinta yayi laushi.

Jawota yayi jikinsa ya ɗaurta akan cinyarsa, cike da kulawa yake shafa bayanta, sannu yaketa yi mata, don ko ba afaɗaba, kowa yaganta yasan tanashan jiki. Shida kansa ya gyara wajen, kana ya buɗe drawer’nta ya ɗauko mata mayafi,  hanunta yakama suka fita daga cikin ɗakin, direct asibiti ya nufa da’ita.

STORY CONTINUES BELOW

Gwaje gwaje aka mata, kana akace su ɗan jira akawo musu result, babu jimawa kuwa, saiga result ɗinsu yafito.  Bayan doctor James yaduba result ɗinne, yasaki murmushi haɗe da duban Zaid, cikin harshen turanci  yace “Congratulation friend matarka tana ɗauke da ciki, na 9 weeks!”

Kamar sauƙan aradu haka Zaid yaji kalaman Dr.James acikin kunnuwansa, da sauri ya kallo Afrah wacce itama take cike da mamakin abun da Dr.James ɗin yafaɗa.

“Cikifa kace Doctor?matana tana ɗauke da cikina?” yatambaya cike da tsananin mamaki.

“Eh mana, ai bazanma wasa ba, dagaske matarka tana ɗauke da ciki, shiyasa take ta amai babu ƙaƙƙautawa” duk cikin harshen turanci irin nasu na America suke maganan. 

Bazai taɓa misalta irin daɗin da yajiba, hakanan ya tsinci kansa da sakin murmushi, tashi yayi ya rungume Afrah, jiyake kamar ya ciro cikin aJikinta, yadawo dashi jikinsa, gani yake kamar zaifi kula da cikin.   Agurguje yayi duk wani cike cike da zaiyi sukabar asibitin.  suna isa cikin gida yayi parking motar, amaimakon yabarta tayi tafiya da ƙafanta, saiya ɗagata caɗak, wai yana gudun kada cikin ya jijjiga.  Akan kujeran falo ya direta haɗe da zama daɓas agabanta, hannayenta yakamo duka biyu, cike da farinciki yace.  “Nagode Afrah, nagode miki sosai, kin bani farincikin dana rasa,  haƙiƙa Allah ne yadubeni yadawomin da farincikina ta hanyarki,  please Afrah, kikulamin da ƴata dake cikin cikinki kinji, daga kan naira ɗaya har 100m zan iya mallakamiki, matuƙar zaki kulamin da ƴata dake cikinki, inasonta inasonta fiye da komai aduniya, Allah ne yadawomin da abuna, dama tawace bata kowa ba, please ki kulamin da cikin dake jikinki, namiki alƙawari zanbaki duk wani abu dakikeso”

Mamakine yakusan kashe Afrah, sam bata fahimci me kalamansa suke nufi ba, yace dama tasace bata kowa ba to wakenan? tambayar da take matuƙar so tasamu me amsa mata kenan.  Ganin ya kafeta da idanunsa ne yasanya tasaki murmushi haɗe dacewa “Nima inason na haifamaka ɗa ko ƴa, kuma insha Allah Zan kula da cikin nan sosai, fiye ma da yanda zan kula da kaina, amma me yasa kaketa cewa ƴa, bamusan fa menene ba macece ko namiji Allahu a’alam”

Murmushi Zaid yayi haɗe da miƙewa tsaye “Mace zaki haifa insha Allahu, wannan bayin kaina ko yin wani bane, yin Allah ne, shiya hanani, yanzu kuma shiya bani, saboda haka bazan gajiya dayi masa godiya ba” yana kaiwa nan azancensa yawuce ɗakinsa.   Haryanzu dai ita bata fahimci ina kalamansa suka dosa ba, kwanciya tayi akan kujera, minti kaɗan bacci ɓarawo yayi gaba da ita.

Shikuwa yana shiga cikin ɗakinsa, ɗan ƙaramin drawer ɗinsa ya buɗe wanda ciki yake aje diary’nsa, ɗauko diary,n yayi yasoma rubutu, yana kammalawa ya buɗe shafin farko na diary’n nasa, take wani hoto wanda ke ɗauke da kyakkyawar fuskarta ya bayyana, tayi kyau ƙwarai acikin hoton, gaɗan ƙaramin bakinta nan yasha lipstick, murmushi yayi alokacin daya kai hanu yashafi kan kumatunta,   ahankali yace “Nasani dama zaki dawo gareni, kobata hanyar zama tawa ba, amma tabbas zaki dawo gareni, gashi kuma kindawo ta hanyar dayafi dacewa,  nan bada jimawa ba zakizo amatsayin tawa ta har abada, duk wuya duk tsanani ke ɗin zaki kasance tawace, nine wanda bakida kamarshi acikin duniya, nine mutum guda ɗaya wanda zai kasance me matuƙar mahimmanci a wajenki, nine wanda bazaki taɓa samun irina ba har abada, ni ɗayane nake da wannan matsayin agareki, bayanni babu wani”   wasu irin hawayene masu zafi suka gangaro daga cikin idanunsa, da sauri yarufe diary’n kana ya shiga toilet donyin wanka, jinsa yake acikin matsanancin farinciki, lallai Allah yamasa kyauta, wacce zata kasance mafi soyuwa agareshi.

(Wayaga Zaid da ƴa ko ɗa😜)

***

Wani irin kulawa na sadidan Zaid ke bawa Afrah, kome takeso adunia shiyake yi mata,  zuwa yanzu harmamakinsa takeyi, irin yanda yake nunamata tsananin ƙauna,  wani lokaci har kuka takeyi, itama tana matuƙar son cikin sosai, amma yanda Zaid ke ƙaunar cikin ba’a magana, tasani badon komai yake nuna mata wannan ƙaunarba saidon cikin dake jikinta,   haka take rainon cikinta cike da ƙaunar abun dake cikinsa, wani lokaci tana mamakin yanda Zaid keta faɗan wasu irin maganganu wanda suke matuƙar ɗaure mata kai, daga zaran yataɓa cikin sai yafara cewa “Babyna kina lafiya ko, na ƙosa kidawo gareni, inakewarki sosai, kizo muyi rayuwarmu wacce bamuyita ba da, muyi rayuwa cikin farinciki, inasonki sosai babyna!” abun dayake faɗa kenan, hakan kuwa mamaki yake bata sosai, duk kuwa yanda taso fassara kalaman nasa, bata iyawa, hakanan take haƙura kawai ta share. Cikin nada wata huɗu Zaid ya ware wani ɗaki dake cikin bedroom ɗinsa, saida yacika ɗakin tam da kayan wasan yara, babu abun da babu nawasan yara acikin ɗakin,   acewarsa ɗakin babynsa ne, itadai Afrah idanu kawai tazuba masa, saboda taga soyayyar dayakeyiwa abun dake cikinta naneman zautar dashi.

STORY CONTINUES BELOW

*** *** ***

Nigeria.

Masha Allah cikin Zahrah ya ƙara girma sosai domin kuwa yanzu yana wata na bakwai ne, sosai cikin yayi turtsetse dashi,  zuwa yanzu batasanya wani kaya sai dogin ruguna, irin masu faɗin nan.

Tana zaune atsakiyar falon, yayinda ta tusa wani tray wanda ke ɗauke da kayan fruit agaba, gefe kuwa plate ɗin dambun nama ne wanda yaji albasa, sai kuma ɗan wake wanda yaji cabbage da cocumber ga tomatoes, yasha mai da yaji, wai duk wannan tulin kayan ciye ciyen Zahrah so take taci kowanne acikinsu.  

Auntie Raliya ce tafito daga kitchine hanunta ɗauke da  wani cup wanda cikinsa ke ɗauke da wani zuma, me magani aciki.

“Manya anata fama kenan” Inji cewar Auntie Raliya.

“Wallahi Auntie ni duk na rasa ma da wanne zan fara, inaga ɗanwakena kawai zanci sauran kuma nabari saina koma gida” Zahrah tafaɗi haka ga Auntie Raliya tana me jawo plate ɗin ɗanwaken ta.

Dariya Auntie Raliya tayi haɗe da zama kusa da Zahrah’n  “Gaskia Bro bai iya ajiyaba, wannan wani irin ɗa ne haka yasa miki acikin cikinki, yaro ne zance ko yarinya, sai shegen ci”

Dariya Zahrah tayi sosai haɗe da kallon Auntie Raliya cikin dariya tace “Wallahi kuwa Auntie, dubeni fa yanda nayi ƙatuwa, nayi muni, shikuma duk kwanan duniya ƙara kyau yake, gaskia ni bazan yarda ba, auntie wayo kawai yamin”

Dariya Auntie Raliya tayi haɗe da miƙowa Zahrah kofin dake riƙe a hanunta.   “Ungo amsa kishanye duka”

Zaro idanu Zahrah tayi, haɗe da kallon Auntie Raliya’n “Auntie kamar tsumi ne fa, acikin cup ɗin?”

“Ba kama bane, tsumine me kyau na mata, wanda yake matuƙar wujijjiga oga, amsa kisha banason gardama” Auntie Raliya tace tana ƙoƙarin kai kofin bakin Zahrah.

Kwaɓe fuska Zahrah tayi, haɗe da ɗan marerece ido. “Wallahi Auntie tsoro nake insha wani tsumi, a yanzun, kinsan kuwa yanda nake fama, doctor fa shiɗewa yake, nasha wannan kuma ae shikenan sumar dashi kikeso nayi”

Dariya sosai Auntie Raliya tayi, haɗe da ɗaukan tsuminta ta shanye  “Shikenan to idan kin haihu na miki haɗi na musamman, matar doctor, ashe ba abanza ba, gaba ɗaya ƙanina ya sukurkuce akanki, wato kinsan me kikeyi masa” cewar Auntie Raliya.

Dariya Zahrah tayi haɗe da cigaba da cin ɗanwakenta, sai kaɗa kai take wai ɗan waken yayi daɗi, itakuwa Auntie Raliya saiyi mata hira take,  sosai suka seta ita da ƴan uwan mijinta,  ƙauna sadidan take samu daga wajen Hajiya,  yayinda Auntie Raliya ma ke nuna mata so, sun saba sosai da Auntie Raliyan, harjinta take kamar ƴar uwarta tajini, don babu abun da take ɓoyewa Auntie Raliyan, dayake Auntie Raliyan ma irin wayayyun matan nanne, basu da nuƙu nuƙu, baruwanta dawani abu waishi surukanta, ta ɗauki Zahrah’nne kamar ƴar ƙaramar ƙanwarta, don har sirrin yanda ake kama me gida a hanu take faɗa mata..

Sunsha hira sosai da Auntie Raliya, sai bayan sallan Isha doctor Sadeeq yazo ya ɗauketa suka koma gida.  Washe gari kuwa, tun 7 am tatafi gidansu amarya Husnah, don yau za’ayi kamunta, kuma itace best friend, don ma ciki yayi mata cikas. 

Anyi kamu cikin kwanciyar hankali, yayinda kamun ya ƙawatar sosai, anyi ɓarin naira sosai baga gidansu ango ba baga gidan su amarya ba, naira tayi kuka don ankasheta a wannan ranan, kayan da amarya tasanya ma kaɗai kuɗinsu baƙaramin yawane dasu ba. Zahrah bata bar gidansu Amarya ba sai bayan magrib kusan 9 pm,  haka ta koma gida agajiye. Washe gari kuma,  aka rangaɗa walima, shima sosai yaƙayatar don anyi musu wa’azi me ratsa jiki,  ranan friday kuma aka ɗaura auren Husnah da angonta,  sosai dai akasha shagalin bikin Husnah, inda Zahrah tataka rawar gani sosai, wajen ganin tabawa ƙawartata kyauta, wacce zata burgeta. Ranan da aka kai Husnah ɗakin mijinta sosai Zahrah tayita mata tsiya, ita kuwa Husnah ko ajikinta, cewa ma tayi “Mijinta baifi ƙarfinta ba, bata wani jin tsoro, tsaf zata iya ɗauke buƙatarsa”…..

***

Yana zaune akan kujera ita kuma tana zaune aƙasa, wani irin ciwo takejin cikinta nayi mata, tun ɗazu yake ankare da ita, amma dai baice da ita komaiba, ganin dayayi tana murƙususu waje ɗaya ne yasanya sa cewa “Baby yadai, akwai damuwa ne?”  murmushin dole ta ƙaƙalo haɗe da dubansa ta mererece fuska. “Samad marata kemin ciwo da cikina” tafaɗi haka tana me cije laɓɓanta.

“Subahanallah to kodai naƙira Bro nafaɗa masa ne?” yatambayeta cike da damuwa.

Da sauri ta girgiza masa kae haɗe da cewa “A’a  dan Allah Samad karka ƙirasa, banaso yatashi hankalinsa”

Murmushi kawai Samad yayi haɗe da cewa “Babe ƴar daɗi miji”

Harara ta aika masa haɗe da murguɗa masa baki tace “Eh ɗin”

Murmushi yakumayi yaci gaba da cin abincinsa, itakuwa sake matsewa tayi tana mejin ciwon naƙara ƙaruwa.   (Kodai Babe haihuwa zatayine ? Chaiii wayaga Zahrah a Labour room🏃‍♀🏃‍♀)Har ya ƙare cin abincin tana nan zaune sai rumtse ido da cije baki take,  ƙirjinta ne yasoma bugawa akai akai, sakamakon tunawa da tayi cewa akwai aiki  babba agabanta.  Miƙewa tayi daga zaunen da take, ahankali take taka ƙafanta data ɗan kumbura, harta shige cikin ɗakinta.  Da kallo yabita har ta ɓacewa ganinsa, murmushi kawai yayi shima  kana ya ɗauki wayarsa yafice daga cikin falon.

Tana shiga cikin ɗaki direct ta wuce bathroom wanka tayi da ruwan zafi, kana ta zo ta ɗauki magungunanta tasha.    wata ƴar ƙaramar riga tasanya ajikinta, kana tabi lafiyar gado ta kwanta, minti shida tsakani bacci ya ɗauketa.+

Kwanciya yayi luf abayanta bayan yacire rigar dake jikinsa,  hanunsa yasanya ya ɓalle mata aninayen dake  jere  a gaban rigarta,  lumshe kyawawan idanunsa yayi haɗe da sanya hanu ya shafi breast ɗinta.  Saida ya sauƙe ajiyar zuciya me ƙarfi, kana ya sake rungumeta ajikinsa, kansa ya ɗaura akan wuyanta, haɗe da sanya harshensa, yashiga lasan fatar wuyanta, yayinda hanunsa ke kan breast ɗinta, yana murzawa a hankali. Kamar acikin mafarki takejin abun da yakeyi mata,ahankali ta buɗe idanunta, batakai ga kallonsa ba, daddaɗan ƙamshin turarensa, ya sanar da ita cewa shine, sake narke jikinta tayi acikin nasa,  jin alamun cewa tafarka ne, yasanyasa juyo da ita suka zama suna fuskantar juna.  Kallonsa tayi da idanunta, da suke cike da magagin bacci, murmushi tasakarmasa haɗe da sanya hanu ta shafi lallausan sajen fuskarsa.   Idanunsa da suke cike da  tarin sha’awarta ya watsa mata haɗe da matso da fuskarsa daf da tata, har numfashinsu na gauraya dana juna,  yanayin irin yanda yake kallonta ne, yasanya taji gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, wani irin ƙaunarsa me sanyi taji tana shiga cikin jikinta.  Ranƙofowa yayi haɗe da yi mata rumfa da ƙirjinsa,  baikai gayin romancing ɗinta ba, amma gaba ɗaya kallon daya keyi mata, ya gama kashe mata jiki,  ahankali ta lumshe idanunta, sosai ƙamshinsa keyi mata daɗi.   Kansa ya cusa acikin ƙirjinta dake tashin ƙamshi, ahankali yake goga mata lallausan sajensa akan breast ɗinta.  Sake lumshe idanunta tayi, haɗe da sanya hanunta, a bayansa ahankali take shafawa, tana fidda wani irin numfashi.  Slowly yake kissing ɗinta, tundaga ƙirjinta har zuwa kan bakinta, da kaɗan kaɗan yake tsotson pink lips ɗinta, yana me lumshe idanunsa, da suka koma kalar ja,     baitaɓa mata irin wannan kissing ɗin me rikita tunani ba sai yau, sosai takejinta cikin wani irin yanayi na musamman,  ajiyar zuciya me ƙarfi ta sauƙe, haɗe da buɗe bakinta,  kamar zatace dashi wani abu, amma kuma babu wata kalma da zata iya fitowa daga bakinta, saboda gaba ɗaya ya shiɗar da ita. Ya ruɗata da salonsa,   harshensa ya tura acikin bakinta, haɗe da soma kaɗa mata shi acikin bakin nata.  Hanunsa yasanya ya zare ƴar rigan dake jikinta.  ƙasa yayi da kansa yana sucking ɗinta,  kamar kullum daya fara sucking ɗinta take saka masa kuka ta kuma shiɗe masa, yau ma hakance takasance, ganin numfashinta nashirin ƙwace mata ne, yasa ta janye kansa, haɗe da mirginawa gefe tana sauƙe wani irin numfashi,  ji take kanta na juya mata,  ga wani irin sha’awarsa dake fusgarta. Sake kwanciya yayi a bayanta, haɗe da cusa kansa cikin tulin gashin kanta.   Numfashi shima yake fitarwa akai akai, burinsa ɗaya shine yaji wannan ɗumin nata, me zautar masa da tunani.

Juyowa tayi gareshi haɗe da hayewa saman ƙirjinsa, hanu tasanya tana shafa gashin kansa, yayinda taɗaura bakinta akan ƙirjinsa, tana sakar masa wasu irin kiss dake tada masa da tsikar jiki,    lumshe idanunsa yayi yana me karɓan saƙonta, dama akunne yake matuƙa, gashi yanzu tana ƙara kunnasa.   Ganin da yayi cewa zata haukatasa da yawa ne, yasanya sa dawo da ita ƙasansa yazamana shine a samanta.   Kallon da yayi mata ne ya ƙara kashe mata jiki,  haɗe bakinsu yayi waje ɗaya,  lokacin da ɗumin jikinta ya ratsashi saida ya sauƙe wata ajiyar zuciya me ƙarfin gaske, take kuma ya fara manta awacce duniya yake, atare suke kissing ɗin juna, cike da wani irin so,   sun matuƙar zautuwa, kowannensu yatafi wata duniyar ta daban, amma duk da haka bakinsu yana cikin na juna……….

STORY CONTINUES BELOW

*** *** ***

Bayan Wata Biyu.😜

Yanzu cikinta yana wata tara harda sati biyu, amma haihuwa shiru, zuwa yanzu ko tashi bata iyawa sai antaimaka mata, cikinta yayi wani irin girma, hakannema yasa Hajiya da kanta taje ta ɗaukota, ta dawo gidanta da zama, bahaka Dr.Sadeeq yasoba amma babu yanda ya iya, dolensa ya haƙura, kuma sosae yake kewar matartasa, wai donma yanasamu suna keɓewa, idan dare tayi, har hotel suke zuwa.

Kwance take akan doguwar kujeran dake falon Hajiya,  green Apple ne riƙe a hanunta, ita bata ciba ita bata ajiye ba.  Tun daran jiya take fama da wani irin ciwon mara dana baya,  amma babu wanda ta faɗawa, gudun kada su tashi hankalinsu,  yanzu kam abun yasoma fin ƙarfinta, don ciwon kamar zai zautar da ita haka takeji, zamowa tayi ƙasa daga kan kujeran da take,  haɗe da durƙushewa aƙasan tiles, hanu tasanya takama gefe da gefen cikinta, tare da sakin wani ƙaran azaba, lokaci guda taji wani irin ciwo  yataso mata gadan gadan.  Fitowar Hajiya daga ɗaki, yayi daidai da shigowan Doctor Sadeeq cikin falon.  Dukansu da sauri sukayi kanta. 

“Innalillahi Hajiya, dama bata da lafiya ne?” Dr. Yatambayi Hajiya a  matuƙar ruɗe.  Kafun Hajiya takai ga cewa wani abu Zahrah ta fashe da kuka haɗe da faɗawa jikin Doctor ta ƙanƙameshi ƙam,  gaba ɗaya ya ruɗe yarasa inda zai tsoma kansa, shima rungumeta yayi tuni idanunsa sun kawo ƙwalla.

Hajiya ce tafito daga ɗakin Zahrah’n hanunta ɗauke da Hijab, ita tasawa Zahrah’n hijab ɗin, kana tace doctor Sadeeq ɗin ya ɗauki Zahrah su wuce asibiti.  Jikinsa na rawa haka ya ɗaga ta ca ɗak yasata a mota, Hajiya tashiga motar ta riƙeta, shikuma yaja suka nufi asibiti, gudu yake dasu kamar zaitashi sama, kanaganinsa kaga wanda baya cikin hayyacinsa,  bayaso wani abu na wahala yasamu matarsa ko kaɗan, da ace zai yiwu to daya karɓa mata naƙudan, don baya ƙaunar ganinta cikin wahala da azaba har haka.

Suna shiga cikin asibitin direct aka wuce da Zahrah labour room.  Wasu likitoti ne guda uku mata akanta,  babu abun da take sai salati da cije baki, ita kaɗai tasan me takeji,  ganin bazai iya jurewa ba, yasanya sa faɗawa cikin labour room ɗin, dayake dama asibitinsu ya kawota, yanazuwa gaban gadon, ya kama hanunta,  buɗe wahalallun idanunta tayi ta kalleshi,  atare wasu hawaye masu zafi suka fito daga cikin idanunsu,  matsanancin tausayinta yakeji, fiye da tunanin me tunani,  Hanunsa dake saman nata, takama ta matse, haɗe da girgiza masa kanta, cikin wata irin murya me ɗauke da tsananin ciwo tace.

“Kayafemin idan na mutu dan Allah!”

Kai ya girgiza mata da sauri haɗe da cewa. “Bazaki mutu ba Zahrah, zamu rayudake acikin duniyarnan insha Allah, zaki raini abun da zaki haifa ɗa hanunki, insha Allah!!” cike da tsananin rauni ya faɗi haka, sosai zuciyarsa ta karye,  bata sake ce dashi komaiba, kawai ta ɗauke idanunta akansa, cigaba tayi da nishi haɗe da karanto addu’a, Doctor na riƙe da hanunta, yana tofa mata addu’a, haɗe da shafa kanta, ƙwalla ne kawai suke fita daga idanunsa. Wani irin yunƙuri haɗe da nishi tayi sai ga kukan jariri ya cika ɗakin.  Laƙwas haka tayi akan gadon, lokaci guda komai nata ya tsaya, motsi da numfashinta, duk suka ɗauke, kumatunta yasoma bubbugawa yana ƙiran sunanta, hawaye kuwa akan fuskarsa wani na koran wani kamar an buɗe famfo.

Wata daga cikin likitoti matanne ta ɗauki yaron, takaishi wajen da ake aje jariri, kallon Dr.Sadeeq da yake hawaye tayi, tace

“Haba Sir, wannan fa ba wani abun damuwa bane kasani, yanzu zata farfaɗo insha Allah”

Hankalinsa ma baya wajenta balle yaji me take cewa,  shigaba ɗaya ma basirarsa toshewa tayi, amaimakon yabata taimakon dayasan zai dawo da ita hayyacinta, saiya tsaya yana ƙiran sunanta, yana kuma jijjigata.   Likitance tashiga bata taimako,  wani ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya Zahrah ta sauƙe,  alaman ta farfaɗo, bayan kamar mintuna uku ta shiga buɗe idanunta a hankali,  dashi tafara tozali ya tusata a gaba, sai kuka yake, hanunta ta miƙa masa, da sauri yataho yakama hanun,  kissing ɗinta yayi akan goshinta, haɗe da  rungumeta, atare suka shiga sauƙe ajiyar zuciya akai akai, sun kusan 8 minute ahaka, kafun taɗan janye jikinta daga nasa, murya a sanyaye tace “Ina Hajiya?”  “Tana waje” yabata amasa a taƙaice, yana me binta da kallo me ɗauke da tsananin ƙauna, haɗe da tausayi me ruguza zuciya.  1

STORY CONTINUES BELOW

Wata daga cikin likitotinne tace “Sir yakamata a kimtsata, sai mukaita ɗakin hutu”

Juyowa yayi ya kalli likitan haɗe da cewa.  “Babu buƙatar ɗaya daga cikinku sai ta kimtsata, nida kaina zan kimtsa abata”

“Sir tana buƙatar ɗinkifa, saboda ta ƙaru” likitan takuma faɗan haka.

Da sauri ya kalli Zahrah, take hawayen dake cike acikin idanunsa, suka gangaro kan ƙuncinsa, wani sabon tausayinta ne yasake kamasa, “Ina sam bazai iya mata ɗinki ba, bazai taɓa koda kwatantawa bane ma, dakansa da hanunsa ya huda Zahrah’nsa? wannan abun bamai yiwuwa bane” yafaɗi haka acikin ransa. Baice da likitotin komai ba, sai matsawa dayayi kusa da Zahrah, yasake sumbatarta akaro na biyu, wata allura ya ɗauko yayi mata a hanunta, tayanda yasan bazataji zafiba,   kallonta yayi still hawaye yake, daƙyar ya iya jan ƙafansa yafice daga cikin ɗakin, abun mamaki kota kan jaririn baibiba, tun dama yafaɗo dunia bai kulasaba, yanata rabin ransa Zahrah. 

Likitotinnan ne suka ɗinke ta tsab, saidai bata wani ji zafi sosai ba, domin alluran da Doctor yayi mata, allurace me ƙarfi dake hana jin zafi, suna gama ɗinketa, wata acikin likitotin takamata suka wuce bathroom,  likitance ta haɗa mata ruwa tayi wanka, tana fitowa likitan tabata wata riga wacce takarɓo awajen Hajiya tasanya, miƙo mata jaririn likitan tayi, hanunta na rawa haka ta karɓi jaririn ɗan nata, tana karɓansa taji wani irin sanyi ya ratsa zuciyarta, fuskar Dr.Sadeeq ta kalla sak akan fuskar yaron nata, lokaci ɗaya taji wani irin so da ƙaunarsa sun cika mata zuciya, tana fitowa acikin labour room ɗin, Hajiya da Dr.Sadeeq sukayo kanta, daga ita har jaririn Hajiya ta haɗasu ta rungume, sai ga ƙwallan farinciki na zuba daga idon Hajiya, amsar yaron tayi daga hanun Zahrah haɗe da sanya sa acikin ƙirjinsa ta rungumesa, sosai takejin ƙaunar jikan nata, musamman dataga yana kama da ubansa, sai dai duk da haka akwai kamannin Zahrah a tattare dashi.    Dr.Sadeeq kuwa ko kunyan Hajiya dake tsaye baiyiba yaje ya rungume matarsa, kyakkyawan kiss ya sauƙe mata akan ƙuncinta, haɗe da ɗaura kansa akan kafaɗanta.  

Saurin tureshi tayi daga jikinta, ta haye gado ta kwanta, tana sauƙe numfashi, kawar da kanta gefe tayi, wasu irin siraran hawayene suka gangaro daga cikin idanunta, ita kaɗai tasan menene yasata wannan hawayen.  Mintuna kaɗan bacci ɓarawo ya ɗauketa, dagani kuma kasan tanajin daɗin baccin.

Alokacin da Doctor yakarɓi jaririn ahanun Hajiya, kafesa yayi da manyan idanunsa, wani irin ƙaunar ɗan nasa ne ke fusgarsa, sosai yaron ke kama dashi, rungume ɗan yayi acikin ƙirjinsa, sai kawai ga hawaye nafita daga cikin idanunsa, kallonsa ya maida ga Zahrah wacce take bacci,  wutar sonta ne ke ƙara ruruwa acikin zuciyarsa, lallai Zahrah tana da babban matsayi agareshi, ta basa farinciki me ɗorewa, tahaifa masa ɗa, tayi masa komai a duniyarnan, baisan damene zai saka mata ba.      

Hajiya dakanta ta ƙira Inna tasanar mata maganan haihuwan, dama tuni Aunty Raliya kam ta tsofe a asibitin,  koda su Inna sukaji cewa Zahrah ta haihu, ba ƙaramin farinciki sukayi ba, sunji daɗi sunyi murna sosai,  ita da Baffa duka suka rankayo zuwa asibitin. 

Ba ita tafarkaba sai bayan azahar,   bathroom ɗin ɗakin da take ciki ta shiga, haɗe da sake tsabtace jikinta, tana fitowa kuwa tasamu Doctor ya karɓo musu takardan sallama.  Gaba ɗaya likitotin asibitin babu wanda baitaya Dr.Sadeeq murnan samun  ƙaruwan da yayi ba,  har ɗaki suke zuwa su duba Zahrah, sukuma tayasu murna.

Hanyar da Hajiya taga  ya miƙa ne yasanyata cewa.

“Wai ina zaka damu ne Sadeeq?”

Da compidence ɗinsa ya juyo gareta haɗe da cewa. “Gidana mana Hajiya”

“Gidanka? to ba gidanka zamuba, gidana zamuyi, hauka kake  na ɗauki yarinya da ɗanyen jiki, na baka? wama zai tsaya ya kula da ita? maza juya akalar motarnan” Hajiya tafaɗi haka babu alamar wasa akan fuskarta.

Sam bahaka yasoba, amma babu yanda zaiyi, shikenan shi baza abarsa yaji ɗumin matarsa dana ɗansaba, haka yata ƙunƙuni acikin ransa shi kaɗai, har suka isa gidan Hajiya.

1

Abinci mai rai da lafiya Hajiya ta kawowa Zahrah, ga kuma gasashshen nama,  bayan taci abincin Hajiya dakanta, tasakeyi mata wanka.

Zama tayi agaban mirror tashafe jikinta da manta me daɗin ƙamshi,  powder tashafa afuskarta, bata tsaya nanba harda janbaki tashafawa laɓɓanta, ga kuma kwalli da ta sanyawa cikin idanunta, mascara ta ɗauko ta zizira akan eye lashes ɗinta, take fuskarta taƙarayin kyau. Wani riga da sket na material me tsada tasanya ajikinta, take takoma ƴar baby  kamar yanda take da, dogon gashinta ta kanannaɗe a bayanta, haɗe da hayewa gado, zataci gaba da bacci,   miƙo mata yaron Inna tayi haɗe da cewa “Wani kwanciya kuma zakiyi bayan baki bawa yaron nono ba?”1

Shagwaɓe fuska Zahrah tayi haɗe da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba,  da ƙyar ta iya ciro nonon nata ta kai bakin yaron,  yana kamawa ta runtse idanunta da ƙarfi, saboda wani zafi da taji, haka dai ta ɗan daure, shikuwa yaron sai zuƙeta yake,  gajiya tayi dajin zafin ta cire nonon abakinsa, kwantar dashi tayi, itama kana ta kwanta agefensa, baccin gajiya ne ya kuma ɗaukarta…

Idan dai hartaji sauƙan numfashinsa akan wuyanta, to yazame mata dole ne farkawa daga baccin da take, yanzu ma sauƙan numfashin nasa taji adai dai saitin kunnenta, a hankali take ware idanunta harta sauƙesu akansa. Murmushi yasakar mata haɗe da ɗaura kansa akan ƙirjinta.

“INA SONKI!!!” yafaɗa murya a sanyaye….Tafaɗa tana me lumshe idanunta. Iskan bakinsa ya hura mata akan fuskarta, haɗe da sake rungumeta, ɗayan hanunsa yasanya ya shafi kan jaririn nasa, dake ta bacci. Murmushi Zahrah tayi ganin yanda Dr.Sadeeq ya kafe yaron nasa da ido. Hajiya da Inna ne suka shigo cikin ɗakin atare, da sauri Zahrah ta janye jikinta daga na doctor, shima a kunyace ya sauƙa daga kan gadon yana sosa kai.+

“Hmmm Allah yashirya, Inna kina gani ko, wai da ahakan yakeso na basa ita” inji cewar Hajiya.1

Murmushi kawai Inna tayi batace komai ba. ( Su Inna anzama nitsaljin🤣) Kallon Doctor Hajiya tayi haɗe da cewa “Zo muje inason magana dakai” babu musu yabi bayanta suka fice daga cikin ɗakin.

Zama tayi akan kujera haɗe da maida hankalinta garesa.

“Me dame kake shiryawa sunan nanne? sannan kuma da wani suna kayiwa yaron huɗu ba?”

Murmushi ya ɗanyi haɗe da cewa “Ai nagama shirina tuntuni Hajiya, dama lokaci kawai muke jira, sannan kuma dama tuntuni sunan babanta nake son sawa yaron, dashi kuma nayi masa huɗu ba”

Hajiya tace “Masha Allah, To Allah Ubangiji ya rayasa, hakan da kayi kuma ka kyauta, tashi kaje dama maganan da zamuyi kenan”

Miƙewa yayi haɗe da yi mata sallama yafice daga cikin falon.

Lokacin da Husnah tazo ganin Baby kusan haukacewa tayi, sai santin yaron take wai yayi mata kyau sosai, komai nasa irin na babansa, ga idanunsa kyawawa, itadai Zahrah dariyanta kawai take, saboda itama Husnan tana ɗauke da ɗan ƙaramin ciki.

Akwatuna guda biyu Dr.Sadeeq ya kawo wa Zahrah, ɗaya nata ɗaya na baby’nsa wai kayan barka, kayane masu kyau da tsadar gaske sosai ya kashe kuɗi, wai ahakanma wasu kayan nanan zuwa.

Kulawa Zahrah take samu a wajen Hajiya sosai, idan kaganta ma kamar ba itace ta haihu ba, sosai jikinta ya murje, tasakeyin fresh, hasken fatarta ma sosai ya ƙaru, komai nata ya cika, taƙara kyau akan nada, shikansa Dr.Sadeeq idan yaganta, ko son ɗauke idanunsa akanta bayayi, saboda yanzu tasake zama wata mace ta musamman, duk inda ta zauna kuwa ƙamshi take rabawa.

Ranar suna yaro yaci sunan baban Zahrah wato Adam, za’ana ƙiransa da (Asad) lokacin da labarin sunan da aka sawa yaro yazo kunnen Zahrah sosai taji daɗi, wani irin farinciki taji acikin ranta, girman Doctor kuwa ya ƙaru acikin idanunta, ta tabbatar cewa shiɗin mai so da ƙaunarta ne.

Da sassafe meyi mata meckup tazo ta tsantsara mata ado, sosai fuskarta tasha kwalliya, wani haɗaɗɗen lace orange and milk colour tasanya ajikinta, wanda yaji ɗinkin riga da sket irin 12 piecess ɗin nan, sosai kayan sukayi mata kyau, domin sunja kuɗi wajen sayansu da ɗinkasu, kowa yaga Zahrah da babynta saiyace masha Allah. Saboda sunsha kyau sosai. Hidima sosai akayi tundaga kan abinci da abun sha, har izuwa abubuwan da za’a rabawa baƙi, akwati guda biyu Hajiya tayiwa Zahrah da ɗanta, haka Baffa ma akwati yayi mata Inna ma zagewa tayi tayiwa Zahrah akwati shaƙe da kaya, Auntie Raliya ma akwati ta mata, sosai Zahrah tasha kaya, har rasa inda zata sa kayan tayi, ana cikin haka saiga kayan Dr.Sadeeq sun iso, akwatuna huɗu, biyu natane shaƙe da kaya, sauran biyun kuwa na yarontane, bata gama mamakin irin dukiyar da Dr.Sadeeq yakashe mata ba, saiga Aunty Raliya tana rangaɗa guɗa, hanunta riƙe da key, danƙawa Zahrah key ɗin tayi ahanunta, haɗe da cewa “Ungo amsa kyautace ta musamman daga mijinki, ya baki kyautar gidansa dake cikin asokoro” mamakine ya kusan kashe Zahrah2

STORY CONTINUES BELOW

“Gida kuma Aunty?” ta tambayi aunty Raliya don tayi tunanin ko kunnuwanta ne basu jiye mata da kyau ba.

“Ƙwarai kuwa gida, saima kinga gidan, don gidane me tsananin kyawun gaske, yafa kashe kuɗi sosai wajen ƙawata gidan” Inji cewar Aunty Raliya.

“A’a Aunty gaskiya nikam banaso, wani irin kyautane haka? hidimar da Doctor yakeyi dani tayi yawa, daga haihuwata zuwa yau yakashe kuɗi yafi 3 million fa Auntie, yanzu kuma yace yabani kyautar gida suku tum, inajin tausayinsa Aunti banason nazama rauni acikin arzikinsa” Zahrah tafaɗi haka da iyaka gaskiyarta.

Murmushi Auntie Raliya tayi haɗe da sanya hanu ta dafa duka kafaɗun Zahrah.

“Kada ki damu Zahrah, shi ɗinfa mijinki ne, kuma kome zaimiki aduniyarnan bazai biyaki ba, kamar yanda kema bazaki iya biyansa duk abun daya miki ba, saboda haka babu wani abun damuwa don yamiki wannan kyautar, kin cancanci hakanne agareshi, don haka amshi makullin gidanki, ke dai kawai kiyi masa godiya, irin wacce ta dace” Aunty Raliya ta faɗi haka tana me damƙawa Zahrah makullin gidan ahanunta.

Kuka Zahrah ta fashe dashi tana jin ƙarin ƙaunar mijinnata na huda mata zuciya, lallai yazama dole agareta taƙara ƙaimi wajen kyautata masa.

Yamma nayi aka haɗa walima me rai da lafiya, bayan malama tazo tagabatar da wa’azine akayi ciye ciye, aka kuma sha drinks, duk wanda yazo sunan kuwa babu wanda baisamu kyaututtuka ba, abun sai dai ace Alhamdulillah, kafun magriba tuni mutane sun watse, gida ya saura daga Hajiya sai Zahrah da kuma Aunty Raliya.

Wanka tasakeyi ta tsantsara ado cikin wani irin meterial me kyau da tsada, wanda yana cikin kayan da Doctor ya ɗinka mata don fitan suna, doguwar riga akayi mata wanda ya matuƙar kama jikinta sosai, dogon gashinta dayasha saloon ta kanannaɗe atsakiyar kanta, ba abun dake fita ajikinta sai ƙamshin humra dana body spray.

Zama tayi akan gado haɗe da ɗaukan wayarta tashiga kan whatsapp, yaronta kuwa tuni dama yana wajen su Hajiya dake zaune a falo suna hira, Sadiya me aikin Hajiya ce tashigo cikin ɗakin haɗe da sanarwa Zahrah cewa wai tayi baƙo yana falo.

Jitayi gabanta yaɗan faɗi, amma saita dake tace da Sadiyan tace da baƙon tana zuwa.

Mayafi ta ɗauka ta yafa ajikinta, kana ta zura flat shoe ɗinta, tafice daga cikin ɗakin.

Su Hajiya tasamu zaune afalon, sai kuma wani, wanda bata ma taɓa ganin fuskarsa ba. Kafun takai ga gaishesa, shiya ɗago mata gaisuwa, amsawa tayi tana ɗan murmushi, gyara tsayuwansa yayi haɗe da cewa..

“Saƙone dama akabani nakawo miki, yana waje, idan ba damuwa muje saiki gani”

Kallon tsoro tashiga yi masa, saboda batasansa ba balle tasan wanene ya aikosa.

“Badamuwa, Raliya rakata sai kuje kuga saƙon ko”

Hajiya tafaɗi haka, don ta lura da tarin tsoron daya bayyana akan fuskar Zahrah’n.

Hakan kuwa akayi tare suka fita da Aunty Raliya.

A compound ɗin gidan suka tsaya gaban wata haɗaɗɗiyar mota ƙirar mercedes maroon colour, mutuminne ya bubbuɗe ƙofofin motar, take kayan dake shaƙe acikin motar suka bayyana, ɗan makulli ya miƙowa Zahrah haɗe da cewa

“Ranki ya daɗe gashi ni nacika umarnin da aka bani, wannan kyautace daga megida na, yace na ce miki Allah ya raya”2

Mamaki haɗe da al’ajabi ne suka kama Zahrah da Aunty Raliya.

“Kyauta daga me gidanka kuma? wayeshi to?” Zahrah tayi masa duka waƴannan tambayoyin cike da son jin amsa, haɗi da kuma mamaki, gani take kamar mutumin baida cikakken hankali.

Murmushi kawai ɗan aiken yayi haɗe da sake miƙo mata makullin motar yace

“Kiyi haƙuri bai bani damar sanar miki dashi ɗin kowaye ba, amma yace dan Allah ki karɓa”

Ta buɗe baki zatayi magana kenan motar Dr.Sadeeq ta kutso kai cikin gidan.

Kasa cewa komai tayi har Dr.Sadeeq yafito daga cikin motarsa, ya ƙaraso garesu, kallonsa Zahrah tayi shima kallonta yakeyi.

“Hajiya ga makullin ni zan wuce” wannan mutumin yafaɗi haka, yana sake miƙa mata ɗan makulli.

“Ko ma waye ya aikoka, kace masa banaso, don bana buƙata” tafaɗi haka tare da juyawa daniyar komawa inda ta fito.

“Zahrah!”

Sunanta da Dr.Sadeeq yaƙirane yasanyata tsayawa cak haɗe da juyowa tana kallonsa.

“Zoki amsa, ki kuma yi masa godiya” Dr.Sadeeq yafaɗi haka, yana me karantar yanayinta.

Cike da mamaki tace “Amma…”

“Banaso kice komai ki amsa kawai nace” yakatseta daga maganar da take ƙoƙarin yi.

Jiki asanyaye ta karɓi makullin motar.

Ciki ciki tace “Kace nagode”

“To” kawai ɗan aiken yace kana ya juya yafice daga cikin gidan.1

“Wai meke faruwa ne, waye ya aikosa?” Aunty Raliya ta tambayi doctor, don ta lura kamar yana da masaniya akan wanda ya aiko motar da cikinta ke shaƙe da kaya.

Murmushi Doctor yayi haɗe da cewa “wani aminina ne dake zaune a Dubai, shine dana gaya masa ta haihu yayi mata wannan kyautar”

Dafe ƙirji Aunty Raliya tayi tare da cewa

“Lallai wannan koma wayeshi yanaji da naira, wannan motarfa zatakai 4million inma bata fi ba, ga kuma kayan dake cikinta, wanda suma kaɗai sun haura 1m, me kenan yake nufi?”1

“Babu wani abun da yake nufi Aunty, haka dama shi yake kyautarsa, muje ciki ko” yaƙare maganar yana kallon Zahrah wacce ta daskare a wajen.

Cike da mamakin kyautar abokin Doctor ɗin Aunty Raliya taja ƙafanta takoma falon Hajiya, Zahrah ma jikinta a sanyaye tabi bayanta, shima falon yanufa, yanda yaga tana tafiya asanyaye ne yasanyasa yin murmushi kawai.

Bata tsaya a falon ba direct ɗakin dayake masauƙinta ta wuce, tsayawa tayi a gaban mirror zuciyarta cike da tarin tambayoyi kala kala, sam bataji zuciyarta ta aminta da kyautar nan da’akayi mata ba, kwata kwata batama yarda cewa wai abokin Doctor bane ya bata. Tana acikin tunanin, yaturo ƙofar ɗakin yashigo bakinsa ɗauke da sallama.

Amsa masa sallaman nasa tayi haɗe da zuba masa idanunta, dagani kai kasan tambayoyine cike a bakinta.

takowa yayi ya ƙaraso daf da ita, hanunsa yasanya ya jawota jikinsa, saida yashaƙi daddaɗan ƙamshin dake fita ajikinta, ya sauƙe ajiyar zuciya, kana yace.

“Kinyi kyau sosai”

Murmushi ta ƙaƙalo haɗe da cewa. “Nagode”

Cikinsa yashafa tare da cewa. “Yunwa nakeji sosai, nayi missing sweet cook ɗinki, please ko zaki kawomin abinci?”

“Meyasa kake barin kanka da yunwa? kasan banaso, yanzu me zakaci na kawo ma?” tatambayeshi cike da kulawa.

“Koma me idan kika kawomin ni mai iya ci ne” yafaɗi haka yana me zama a bakin gado.

Harta kusa fita daga cikin ɗakin sai kuma ta tsaya cak, haɗe da juyowa, idanunsu yafaɗa cikin na juna, domin dama shima kallonta yake.

“Waye ne yaturomin da mota? Nasan kasan ko waye, domin zuciyata tafaɗamin cewa, ba abokinka bane ya turo, kamar yanda kafaɗa a baya” tambayar da tayi masa kenan, cike da burin samun amsa agareshi.

“Baki yarda da abun dana faɗa ba kenan?” ya tambayeta yana me ƙara tsareta da manyan idanunsa.

Murya a sanyaye tace “Kayi haƙuri, bawai ina nufin kamin ƙarya bane, kawai dai naji zuciyata ce bata gamsu da amsar da ka bayar ga Aunty Raliya ba”

Murmushi yayi haɗe da cewa “Zuciyarki tafaɗa miki gaskiya, domin kuwa ba abokina bane yaturo kamar yanda na faɗa a baya”

Waro idanunta tayi, duk da zuciyarta ta raya mata cewa ba abokinnasa bane, amma kuma duk da haka bata tsammaci jin haka daga bakinsa ba.

“Waye?” tatambaya murya na rawa.

“ZAID” yabata amsa ataƙaice…ZAID!” ta maimaita sunan abakinta cike da tsananin mamaki.+

Yanda yaga jikinta na ɓari shine abun daya basa mamaki, zallan tsoro ya hango kwance akan fuskarta, yayinda cikin idanunta kuwa, suka bayyana soyayyar dake kwance acikinsu, wato soyayyar ZAID, shi yasani ba tun yauba, bakuma zai yaudari kansa ba, yasani ƙwarai Zahrah na son Zaid, so ba irin na wasaba, so matsananci, amma kuma babu yanda zaiyi, dayana da iko to daya cire mata son Zaid acikin zuciyarta, amma wannan banasa bane, na Allah Ne, yasan Zahrah tana sonsa, amma soyayyar da takewa Zaid ta dabance, da ace zai iya, to daya danne zuciyarsa, ya miƙata ga Zaid, yasan hakan zai samarmusu da farinciki, ita da Zaid, amma kuma yasan koda yayi hakan to ba mafita bane, domin ayanzu yasan dole idan baya tare da Zahrah tayi kewarsa, yana sane da cewa yakafa mata tutar son sa, wanda bazata ankara da hakan ba, har sai randa yazama baya tare da’ita, baya fatan wata ƙaddara ta rabasu, amma yasani ko mai daren daɗewa sai sun rabu, saboda akwai mutuwa, koshi ko ita, watarana ɗaya dole zai bar ɗaya, yau idan baya raye, baya fata Zahrah ta auri wani namiji idan ba Zaid ba, tunaninsa yayi nisa, baisan da cewa ta ƙaraso inda yake ba, saida yaga ta zube a gabansa, tana kuka, cikin muryar kukan takecewa.

“Kada kamin haka doctor, wallahi ni banason duk wata kyauta da zatafito daga garesa, namantasa acikin rayuwata, banaso kuma nasake tunasa, kamayar masa da kyautarsa, bana buƙata farincikin da kake bani kaɗai ya isheni”

Tunda tafara maganan yake kallonta, ajiyar zuciya yayi, haɗe da kamo hannayenta, cikin murya me sanyi yace. “Kinsani bakyau maida hanun kyauta baya, meyasa to zakiyi haka? mekike tunani akan Zaid?” ɗan dakatawa da maganar yayi, tare dayin wani murmushi, kana ya miƙe tsaye, daga zaunen da yake.

“Kyautace kawai ya miki, ai atunanina hakan ba wai yana nufin wani abubane, bazan tilasta miki ba, amma nasan abundake cikin zuciyarki, don gashi har a idanunki sun nuna, so ba ƙarya bane Zahrah, haka kuma ba laifi bane, don zuciya na dakon so, wannan ma wata ƙaddarace, wanda babu wani wanda ya isa ya kauce mata” yanakai ƙarshen zancen nasa yanufi hanyar fita daga ɗakin.

Da sauri taje ta faɗa jikinsa, kuka take sosai, durƙusawa tayi haɗe da zube guiwowinta a ƙasa, kana ta riƙe rigarsa, kanta tashiga girgizawa, tana kuka tace. “A da na sosa fiye da yanda naso kaina, amma ayanzu baya acikin zuciyata kamar yanda kake tunani, Inasonka da duka zuciyata, bana fatan wata ƙaddara tazo wacce zata rabani dakai, kabani farinciki, kajiyar dani daɗi, kashayar dani zuman soyayyarka, bazan iya watsa maka ƙasa idanunka ba, kai mijinane wanda bayan kai bani da wani tamkarka, nasan kai ɗin me sonane, amma meyasa kayi haka? mai yasa kai da kanka, zaka amince da na karɓi kyautar wanda yazama silar rugujewar rayuwata?”

Durƙusawa yayi agabanta, haɗe da sanya hanunsa ya share mata hawayen dake gudu akan fuskarta, cike da kulawa yace. “Banason kukanki Zahrah, keɗin wata babban jigo kuma mahaɗi ne acikin rayuwata, nasan Zaid ya cutar da rayuwarki, amma kuma hakan bazai hana ki amshi kyautarsa ba, ayanzu kowa yasan cewa ke matatace, saboda haka Zaid bazaiyi miki kyauta da wata manufa ba, kuma kafun ya miki kyautar saida ya tambayi amincewata tukunna, nakuma amince masa, nayarda da Zaid Zahrah, nasan idan duka mutanen duniya zasu taru su cutar dake, to Zaid bazaiyi hakan ba, haka kuma idan ni zan iya cutar dake, to ina tabbatar miki idan Zaid yasan da hakan, to bazai bari na cutar dake ba, Zaid ɗin da kikasani ada bashine wanda yake a yanzu ba, kada kiyi tunanin wai ko zanji haushi akan kyautar da Zaid yayi miki, niba jahili bane Zahrah, haka kuma halina ya banbanta da na wasu mazan, ni mutum ne me saurin fahimta, sannan kuma abune mawuyaci nayiwa wani na mummunan zato, agurin wasu mazan, hakan zai iya zama matsala, amma a wajena hakan ba komai bane, tunda nasan cewa keɗin tawace ni kaɗai, bakuma wai don bana kishinki bane yasa hakan tafaru ba a’a, ni kalan nawa kishin ba irin na wasu bane, inakishinki sosai, sai dai kuma kome acikin nutsuwa nakeyinsa, ke kinsan inasonki ina kuma kishinki ” yaƙare maganar yana me lakace mata dogon hancinta.

STORY CONTINUES BELOW

Kukane yakuma ƙwace mata sai kawai tafaɗa jikinsa, ta rungumesa ƙam, shima rungumeta yayi yana shafa bayanta ahankali, haɗe da hura mata iskan bakinsa, acikin kunnenta.

Saida tayi kukanta sosai, kafun ta soma sauƙe ajiyar zuciya, cikin murya me sanyi tace.

“Kai na da banne Mijina, irinka basu da yawa acikin duniya, haƙiƙa nafi kowacce mace sa’a dana sameka, dakai kaɗai zan rayu har izuwa mutuwa ta, kaima ka rayu dani ni kaɗai kaji, bazan iya jure ganinka da wata mace ba bayanni, Ina maka son da bansan iyakarsa ba!”

Murmushinsa dake ƙara masa kyau yayi, haɗe da sanya iskan bakinsa ya hura mata fuska.

“Dake kaɗai Zan rayu Zahrah na, ni nakine ke kaɗai, amma idan kina kukan nan fa, dole zan ɗan yi ƙasa da idanuna, na hango wata, saina kawota ko wanke wanke ne tanayi mana ko, idan dare yayi kuma sai ina raba muku kwana ko…”

Bata bari yakai ƙarshen zancen nasa ba, ta muntsine sa aciki, saida yasaki wata ƴar ƙaramar ƙara, cike da shagwaɓa tace “Wallahi nidai babu ruwana dakai, idan dai har kace zakamin kishiya!”

Dariya yayi sosai haɗe da cusa kansa acikin ƙirjinta. “Ni na isa ma nayiwa ƴar sakalalliyar matata kishiya, amma bandai saniba wataƙila idan naga kin tsofe na miki!” yanzuma cikin zolaya yayi maganar.

Hannayenta tasanya acikin gashin kansa, tashiga ya mutsawa, hadda kai masa cizo a wuyansa. Sai da tayi masa buji buji da kayan jikinsa kafun ta ƙyalesa, gashin kansa ma gaba ɗaya ta hargitsa masa shi. Koda ta kawo masa abinci tare sukaci, yana kwance ajikinta itakuma tana bashi abincin abaki, ahaka har ya ƙoshi.

Kallonta yayi da idanunsa, dake tsumata kana yace “Namatsu abani ke Baby na, wallahi ina kewar ɗumin ki sosai, amma Hajiya gaba ɗaya ta kanenaye min ke, waidole saikinyi arba’in, Babyna kice tabarmu mu koma gidanmu kinji!” cikin yanayi na shagawaɓa ya faɗi haka.

Murmushi Zahrah tayi, haɗe da sanya hanu ta shafi kumatun sa, cike da ƙaunarsa tace “Kayi haƙuri Hubby, nima ina kewar sucking ɗinka, kuma ai bawai bazan dawo bane zan dawo fa” tafaɗi hakane don kawai ta kwantar masa da hankali.

Ya buɗe baki zaiyi magana kenan muryar Hajiya ta karaɗe kunnuwansu, inda take cewa.

“To iyayen rashin kunya, saika tashi katafi dare na ƙarayi, ke kuma miji daɗi, ga yaronki nan, abincinsa yakeso ki basa.” kunyar Hajiya ne yakama Zahrah, haka ta amshi yaron kanta a ƙasa.

Doctor kuwa turawa Hajiya baki yayi, haɗe da cewa “Hajiya zantafi, amma kiɗanyi haƙuri ba yanzu ba mana”

Baki Hajiya ta sake tana kallonsa. “Sannu marar ta ido, wallahi saika tafi yanzu kuwa” Hajiya tafaɗi haka tana me kama hanunsa, haka yanaji yana gani ta fitar dashi daga ɗakin, Zahrah kam dariya taketa yi masa. Bayan ta shayar da yaron natane, tashiga toilet tayi wanka, doguwar rigan bacci tasanya, kana ta ɗauko diary’nta, rubutu tayi aciki, ta mayar dashi ma’ajinsa. Kwanciya tayi luf akan gado, cike da tunani kala kala bacci ya ɗauketa….

*** *** ***

Yau kwanansu 50 cif cif agidan Hajiya, sunƙara kwanaki 10 akan kwanakin gama wankansu, idan kaga Zahrah bazakace ita bace, sosai taƙara cika da kyau, fatarta ta ƙara haske, komai nata yasake cika, gwanin sha’awa, yau ne zata koma gidanta, tuni Dr.Sadeeq ya sanja mata kayan furnitures ɗinta, komai yasanya mata sabo, Hajiya kuwa tun tuni taketa ɗirka mata magunguna, haka Aunty Raliya ma ta dage sai bata wasu magunguna masu ƙarfi take, ita kuwa sha take abunta, wanda taji yanada bauri ne kawai take ajiyewa bata sha.

Wanka ta tsantsara cikin wata jar atamfa Super Exclusive, wacce taji ɗinkin riga da sket, sosai kayan ya amshi jikinta, zama tayi da kanta, ta tsantsarawa fuskarta kwalliya, sai gashi kuwa kyawunta ya ƙara bayyana, dogon gashinta dayasha gyara ta tubke da ribbon haɗe da kafa ɗaurin ɗan kwalinta me kyau, wani red ɗin takalmi tasanya aƙafanta me tsinin gaske, ɗan ƙaramin mayafi ja ta ɗauka ta rufe jikinta dashi, babu abun dake fita ajikinta, sai daddaɗan ƙamshi.

STORY CONTINUES BELOW

Yana tsaye ajikin motarsa dake fake a compound ɗin gidan, yaga fitowarta, kusan suman tsaye yayi. “Tabbas Zahrah me kyauce, tahaɗu tako ina, kullum ƙara kyau da cika take, lallai kuwa da yayi saken barin Zahrah, tabbas da yazama soko, marar rabo, samun mace kamar Zahrah, babban sa’ane daya samu a rayuwarsa” yafaɗi haka acikin zuciyarsa, yana hangame da baki wajen kallonta, baisan ma taƙaraso garesa ba, saida yaji ni’imtaccen ƙamshinta na ratsa cikin hancinsa.

Murmushinta me kyau tayi masa haɗe da kashe masa idanunta ɗaya. “Ya dai kwalliyar tayi maka ne” tafaɗi haka tana me juya masa bayanta. Alaman yaganta da kyau.

Yawu ya haɗiye, alokacin da idanunsa suka sauƙa akan hips ɗinta, baigama dawowa hayyacinsa ba, yakuma jefa idanunsa akan ƙirjinta, jikinsa na rawa ya jawota ya rungumeta.

Wani irin ajiyar zuciya suka sauƙe atare.

“I really Miss you Babyy!!” yafaɗi haka akasalance.

“Miss you too dear!” itama ta mayar masa da amsa cikin muryar raɗa.

Hajiya dake kallonsu ta window tasaki murmushi haɗe da komawa cikin falonta ta zauna, aranta tanayi musu fatan shiriya.

Saida suka biya ta JABI lAKE sukayi sayayya tukun kafun daga nan suka wuce gida.

Wanka ta sakeyi ta shirya kanta cikin wata irin fitinanniyar sleeping gown, wacce ta bayyana komai na surarta bata ɓoye komai ba, rigar doguwace har kusan ƙafa, amma kuma duk da haka itaɗin kamar babu take, kasancewarta shara shara. dogon gashinta ta sake a bayanta, haɗe da shafe jikinta da shu’umar Humra, wani sweet Lip Gloss tashafa akan leɓenta.

Yana zaune a falo yana danna laptop ɗinsa, ƙamshinta ne yafara kawo masa ziyara, lokacin daya sauƙe idanunsa, akanta sai da yaji wani irin shock ajikinsa, da sauri ya miƙe ya ƙarasa gareta. buɗe hannayensa yayi daniyar rungumeta, da sauri ta matsa gefe, tanayi masa dariya, haɗe da yin wata irin tsayuwa, wacce takusa zautar dashi.

Lumshe idanunsa yayi tare da sanya hanunsa ya jawota jikinsa. Ƙam ya rungumeta, sai gashi yana sauƙe ajiyar zuciya akai akai. Kallon juna suka shiga yi idanun ko wannensu ɗauke da tsananin sha’awar ɗan uwansa. Jikinsa na rawa ya kama lip ɗinta na ƙasa, yana tsotsa ahankali, jiyake kamar yanashan honey. da kanta ta zame rigar dake jikinta, ta faɗi ƙasa, take surarta ya bayyana, hmmm ba yau yafara ganinta ba, amma kuma ya zautu ƙwarai daganin surar jikinta, jiyake kamar ma baitaɓa kusantarta ba, sosai yayi missing ɗinta. Jikinsa na rawa ya ɗauketa suka wuce bedroom, tuni dama Asad yayi bacci, dama shi haka yake sam baida ƙiriniya, daya ƙoshi sai bacci, bakuma zai tashiba sai dai idan yanajin yunwa.

A yau ɗin ne suka sake tabbatar da cewa sunyi kewar juna, musamman ma Doctor Sadeeq da kusan cinyeta ne kawai baiyi ba, gaba ɗaya ya zauce, ya susuce, wasu maganganu yake wanda ita kanta batasan me yake cewa ba, saboda sun lula wata duniya ta musamman, wacce sukayi nisa acikinta basaji basa gani, kansu kawai suka sani. Aranan nan wata zuma suka shayar da junansu, wanda bazasu taɓa mantawa ba. Wannan ranan takasance rana ta biyu masu muhimmanci a garesu.1

*** *** ***

Bayan wata 6……..

America

Zufa ne keta ketowa ta goshinsa, gaba ɗaya baya cikin nutsuwarsa, kai komo yaketayi agaban labour room ɗin sama da 1 hour kenan yana abu ɗaya, jiyake kamar yasanya hanu akansa yaita ƙwala ihu. Ɗaya daga cikin Nurse ɗin dake kanta na fitowa ya nufi wajenta, da sauri idanunsa sunkaɗa sunyi jajur dasu. Murmushi Nurse ɗin tayi masa haɗe da cewa “Ina tayaka murna, matarka ta haihu, kasamu baby girl” wani irin sanyin daɗi yaji acikin ƙirjinsa, baisan lokacin dayayi sujja don nuna godiyarsa ga Allah ba.1

Ana kaita ɗakin hutu, wata nurse tace yashigo ya karɓi babynsa, lokacin daya sanya hannayensa ya amshi babyn, wani irin kukane ya ƙwace masa, alokacin da idanunsa suka sauƙa akan kyakkyawar fuskarta kuwa, bugun zuciyarsa ne ya ƙaru, saboda kokaɗan yarinyar bata kama da mahaifiyarta, durƙushewa yayi aƙasa, riƙe da yarinyar tasa yana kuka, hakan kuwa sosai yabawa likitotin mamaki.

Bakomaine yasa sa yake kuka haka ba, face tsananin danasani na rayuwar da yayi abaya da yake. yakasance mazinaci, mashayin giya. “Yanzu idan ƴarsa mafi soyuwa agaresa, tataso taji labarin abun da ya aikata a baya, wani irin kunya zaiji? mezaice da’ita idan ta tambayesa, meyasa yazamo haka?” tambayar da yayiwa kansa kenan, amma kuma baida amsa, baida kuma me amsa masa.

Rungumeta ya sakeyi tsam, acikin ƙirjinsa, ahankali yace.

“Kindawo gareni Zahrah, Allah yadawomin dake, Inasonki Inasonki, inamiki so na musamman Allah ya albarkaceki ƴata!!!” kiss ya manna mata akan goshinta, kana yazuba mata idanu, bazaiyi mamakin kamannin daya gani akan fuskar ƴartasa ba, saboda yasan ba aja da ikon Allah, kuma hakan ma wata rahamace da Allah yayi masa, Allah ya hanasa Zahrah alokacin dayaso, yanzu yakuma basa Zahrah alokacin dayaso, hancinta bakinta duka kalan nasa ne, amma kuma idanunta tamkar idanun Zahrah aka ciro aka sanya mata, kallon farko da yarinyar tayi masa, saida yaji tsikar jikinsa ya tashi, saboda gani yayi tamkar Zahrah ce dakanta agabansa. yana rungume da yarinyar ya ƙarasa gaban Afrah dake kwance akan gado tana kallonsu, ranƙwafowa yayi ya manna mata kiss akan goshinta, hanu yasa yashafi kumatunta, haɗe da cewa “Nagode ƙwarai Afrah, Allah ya miki albarka, bazan manta da wannan ƙoƙarin da kikamin ba, Inasonki”

Karo na farko kenan arayuwarta da taji kalmar nan tafito daga bakinsa akanta, “Inasonki” ta maimaita kalmar abakinta cike da mamakinsa.

Kansa yajinjina mata haɗe da sakin murmushi.

“Ki kwanta ki huta, nasan kinsha wahala sosai” yafaɗi haka yana shafa kanta.

Lumshe idanunta kawai tayi saiga hawaye nabin kan fuskarta. Hanu ta miƙa masa ya bata yarinyar, ba iya mamaki ba hadda tsoro saida ya bayyana akan fuskar Afrah, sakamakon ganin fuskar yarinyar ɗago kanta tayi ta kalleshi da sauri.

Kamar yasan me take tunani, murmushi yayi mata haɗe da ɗaura hanunsa akan kafaɗanta. “Kada kidamu, Allah ne yayi ikonsa, Allah ne yadubeni yayimini rahama, sannan kuma ko da ace kowa zaiyi mamakin kamannin yarinyar ni bazanyi ba, saboda wacce take kama da ita, jinin jikinane, sannan kuma Allah yana da ikon yin komai”

Ajiyar zuciya kawai Afrah ta sauƙe haɗe da kafe yarinyar nata da ido, tabbas da badan taji ƙauna irinta uwa da ƴa akan yarinyarba, to tabbas da tace ba itace ta haifi yarinyar ba, Zahrah ce, shine aka sanja mata, aka ɗauki nata aka kaita wani gun, itakuma aka kawo mata wannar, a matsayin ƴarta. Rungume ƴar tata tayi, tanajin ƙaunarta aranta.

***

Suna komawa gida Zaid yayiwa Afrah kyautar zuƙeƙiyar mota, tare da kuɗi Naira Million 3 duk na murnan ta haifa masa baby ne, washe gari kuwa suka tarkato suka dawo Nigeria, abisa takurawan Mom ɗinsa. amma da anyi suna yace zasu koma. Aranan da aka haifa masa Zahrah aranan ya mallaka mata babban kamfaninsa na ƙera takalma, dake Italy, aranan kuma akasanjawa kamfanin suna zuwa sunan yarinyar, saɓanin da dayake sunan Zaid.

Tunda aka haifi Zahrah Zaid baibari kowa ya ɗauketa ba, inbanda uwarta, nan ma nono kaɗai take bata, idan yaɗauketa yashiga ɗakinsa da ita, kulle ƙofar yake da key gudun kada wani ya damesa, komai na duniya shiyake mata, wani irin so da ƙaunar yarinyar yake ji, wanda baitaɓa jin irin saba, akullum kallon Zahrah kawai yakeyiwa yarinyar. Irin soyayyar dayake yiwa yarinyar shike tsorita kowa.

Ranan suna kamar yanda ya alƙawartawa kansa cewa idan ya haifi ƴa mace sunan Zahrah zaisawa yarinyar, hakance takasance domin kuwa sunan nata yasaka, wato FATIMA ZAHRAH, koda Afrah taji sunan da ƴartata taci sai kawai tayi murmushi, ko kaɗan batayi fushi da faruwar hakan ba, saboda tasan albarkacin Zahrah itama zata samu soyayya ta musamman daga wajen Zaid ɗin, haka kuma albarkacin Zahrah ƴarta itama zata samu gagarumar soyayya daga wajen ubanta.

Nairori sunyi kuka a wannan rana, sosai Zaid yayi ɓarin kuɗi tundaga randa aka haifeta kawo yau dayake suna, dukiya kawai yake ɓararwa, tun abun nabawa Mom ɗinsa da Afrah mamaki, har suka daina mamaki, saboda zuwa yanzu sunsan soyayyar da Zaid keyiwa ƴarsa Zahrah ta wuce gaban kwatance, harta bacci akan ƙirjinsa takeyi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *