AUREN KWANGILA BOOK 3 CHAPTER 4 BY SUMAYYAH ABDULKADIR
Www.bankinhausanovels.com.ng
shikansa yana jin kunyar bata takardar sakin a hannunta. Saboda shi ma ya san ko giyar wake ya sha ba zai iya fuskantarta ido cikin ido ya ba ta wannan takardar sakin ba, duk da abu ne da ta kwana da sanin kasancewarsa, to amma akwai Www.bankinhausanovels.com.ng KARAMCI da KYAUTATAWA a cikin zamansu, wanda ba zai taba gogewa daga tarihin rayuwarsa ba, kuma ba zai gushe yana kallon Hafsatu da su ba. Da sassarfa ya isa ga motarsu ya bude ya shige ya maida kofar ya rufe, ya kwantar da kai a kan sitiyarin ya kai hannu ya dafe kirjinsa daidai saitin da ke azabtar da shi. “ME NA AIKATA???” Yake fadi a fili.
*********
Da rarrafe Hafsat ta rarrafa ta isa ga Dr. Bashar kafin ta karaso ya taso ya cimmata, ya sanya ta tsakiyar hannayensa ya rungume. Yanayin da Hafsat ta samu kanta a wannan lokacin ba ta taba tsintar kanta a kololuwar dadin irinsa ba. A tsaye suke tsakiyar taron nan kusan minti goma kafin Dada ta mike ta rabo ta da uban ta kamo hannunta.
War hadosabajo’am Hafsatu (Zo nan kawata Hafsatu)”. In ji tsohuwa Dada.
“Sobirawo na malla launirawo? (Kawalli ce ko kishiya ce ?)’ Daada ta sake fadi tana hawaye.
Duk da Hafsat ba ta san me ta ke fadi ba ta isa gare ta, ta rungume ta don ta fahimci ita ce mahaifiya ga Habiban, wato Kaka a gare ta.
Malam Hashim Babbah ya share nasa hawayen ya shiga baiwa kowa baki. Ya ce, “Alhamdulillahi, Alhamdulillahi, Alhadulillahi” har sau uku. Www.bankinhausanovels.com.ng
Sannan ya cigaba da cewa “Allah bai yi lamunin za mu sake ganawa da Habiba ba, amma bai barmu da kewarta mai yawa ba tunda ta ajiye Hafsu. Zuciyoyinmu yanzu sun samu nutsuwa daga taraddadin da kullum suke ciki. Baiwar Allah!” Ya dubi Hajiya Maryam.
“Alkhairinki ya bi ki har ‘ya’ya da jikokinki. Ba mu da kalaman da za mu furta godiya a gare ki. Muna rokon Ubangiji Ya fi mu godewa. Ba sai kin fadi irin rikon da ki ka yi wa yarinyar nan ba, ido ba mudu ba amma ya san kima, kowa ya dube ta ya san ta fi karfin komai na rayuwa. Allah ya zama gatanku ke da mijinki da zuri’ arku bakidaya”’Kowa ya amsa da, “Amin-amin”.Hafsatu matso kusa da ni, ko ba kya aure da tsoho? Dube ni sosai, gemuna bai gama kodewa ba”.Murmushi ta yi ta matsa kusa da shi. Ya kama hannayenta biyu ya rike cikin nasa. Adda Hafsatu babar Hajiya maryam ta ce da shi.
“Anya takwara tana auren nan da kai Malam? Dubi sardidin mijinta a gefe, gara ka rike Yadanka kada ka yi ba-wan-ba-kanin”’. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ido ya koma ga inda Adda Hafsatu ta nuna, kowa na son ganin wane ne mijin dalleliyar baturiya Hafsat? Wayam! Babu kowa, babu wanda ya ankara da fitarsa saboda a lokacin sun rude da koke-koke.
Modibbo ya fiddo ido cikin mamaki ya tambayi Adda Hafsatu, “Ba dai Barrister abokin Kawu Sagir ba?”
“Shi kuwa. Jiya aurensu shekara guda da watanni uku”. Aunty Luba ta ba da amsa.
“Kuma Da yake a gare su, shi ne babba dansu’”’. Aunty Mariya ta kara bayani.
“Allahu akbar! Allahu Akbar!!” Abinda Malam Babba da iyalinsa ke fadi kenan cikin jinjina halin GIRMA da karamci irin na Hajiya Maryam da mijinta tsohon Ambassador Hamza Atiku. Daddy ya ciro waya yana kiran Abdul’azeez. Yana dagawa ya ce da shi, “Ina ka tafi? Ka shigo yanzun nan”. Ba tare da ya saurari amsa daga gare shi ba ya kashe wayarsa ya maida aljihu.
Falon ya rikice da tofin albarka da fatan alkhairi ga Hajiya Maryam Hamza Atiku. Sai da kowa ya gaji ya bari sannan ta gyara zama, ta ce.
“Na yi zama da Habiba zama na amana, domin ta so yarana ta kaunace su, ta kula da su tsakani da Allah, musamman Abdul’azeez na hannun damanta. A kan idonsa aka haifi Hafsat a asibiti can Jeddah. A tasowarsu kuma sai na fahimci yana shiri da uwa ba ya shiri da ‘yarta, tun a wannan lokacin nake nazarinsu na fahimci sam ba sa ga maciji. Ni kuma na sa a raina tun a lokacin Abdul’ azeez ba shi da mata sai Suhaana. Mun yi musu aure ba tare da son ran kowannensu ba, su suka san yadda sukai suka shirya kansu”’.
Kalaman da ya tsinta kenan a shigowarsa falon wadanda suka kara tsinka masa zuciya. Wata juwa-juwa ya ji tana kwasarshi tana neman fyada shi da kasa jin kowa a falon na kiran sunansa cike da kauna da tsananinbegensa a zukata da fuskokinsu, “Angon Hansatu!”.“Shine mijin nata?” Wasu cikinsu suka ce“Abdul’azeez na Hafsu. Allah ya yi albarka!”. Kowanne da abin da yake cewa na nuna kauna da kulawa a gare shi.
Kusa da mahaifinsa ya lallaba ya zauna, amma sai Malam Babba ya ce ya taso ya zo kusa da shi. Da rarrafe ya yi hakan, sabida gwiwoyinsa sun kasa daukar sa. Malam ya yafito Addah da hannayensa. Cikin matsananciyar kunya ta tashi daga kusa da Dada ta tafi ta zube a gabansa. Hannun Abdul’azeez ya dauka ya sanya cikin na Hafsat ya cure wuri guda. Daga Abdul’azeez har Hafsat bugun zuciyarsu ya tsananta a wannan lokacin, sun kuma kasa duban junansu idanun kowannensu na kan kyawawan yatsun da Malam Hashim ya cure ya dunkule wuri Www.bankinhausanovels.com.ng guda,siraran zobunan danyen ‘gold’ na hannunta guda biyu sun kawata yatsun. Yatsun kawai suke kallo sarke cikin najunansu da tunanuka masu nauyi a zukatansu. Abdul’azeez na ji a ransa sallama yake yi da Hafsat, sallama irin ta SAI WATARANA…… Hafsat na tunani a zuciyarta, mene ne muhimmin aibunta da Abdul’azeez ya kasa sonta??? In a da rashin asali ne, yanzu fa? Zai dubi Allah da girman UWA ya kaunace ta su ci gaba da kyakkyawar rayuwarsu ko kuwa? Ko kuwa zai rufe ido a karo na biyu ya zabi Mu’azatu a kan su su biyu ita da mahaifiyarsa? Yau ta tsayar da zuciyarta wuri guda ta fahimci kauna ce sak! Mai lullube da ‘soyayya’ ta ke yi wa mijinta Abdul’azeez Dakata ba wani abu daban ba. Ba za ta taba sonsa da abin Allah wadai ba. Fushin iyaye kuwa abin Allah wadai ne, tana rokon Allah ko ba zai so ta ba ya ci gaba da zama da ita don tsira daga fushin UWA-MAHAIFIYA, ta amince ya auro Mu’azatu ya karo cikin gidan za ta zauna lafiya da ita, koda kuwa bazai iya adalci a tsakanin su ba zata jure ta zauna. Ta sa a ranta muddin ta samu damar kebewa da shi kafin barinsu Jimeta za ta shawarce shi a kan wannan hangen na zuciyarta. Za ta iya jure komai ban da rayuwarta. Ya cika mata dukkan burirrikanta. Ya kawo dawwamammen farin ciki da kwanciyar hankali gare ta. Za ta so shi da makamancin hakan shi ma (Allah sarki Hafsat).
Kawunansu Malam Babba ya kama ya shiga kwararo musu addu’a. A karshe ya ce, “Miji ake baiwa amanar matarshi, amma ni Hashim Babba Jimeta, ke Hafsu na baima amanar jikana Abdul’azeez, ki kula min da shi, ki rike shi amana, Allah ya yi muku albarka bakidaya’”’.
Abdul’azeez ji ya yi idanunsa sun cicciko da kwalla. A haka ya dago su ya kalli Hafsat wadda kanta ke sunkuye, mayafinta ya zame ta baya. Manyan kitson kanta sai kyalli suke suna daukar idonsa. Da a ce bai yi azarbabin kuskuren sanya takardar nan a jakarta ba ya bari sai za su koma Kano ya bata hannu da hannu kamar yadda zuciyarsa ta shawarce shi da farko, da yayyagawa zai yi yanzu ba wanda ya ji ba wanda ya gani, ya yi fatali da wasu alkawurruka da ya san ya daukarwa Mu’azatu tunda ita ba Allah ba ce. In ya so ya yi kaffara ya ci gaba da zama da Hafsat har karshen rayuwarsa. Www.bankinhausanovels.com.ng
An ce ana barin halas ko don kunya! Ya tabbata zai iya mantawa da Mu’azatu cikin rayuwarsa, amma ba zai taba iya mantawa da Hafsat ba. Al’amarinsa da ita ya fi gaban a kira shi ‘soyayya’ irin tashi da Mu’azatu. Wani al’amari ne daban beyond his expectations. Wasu igiyoyi ‘ ties’ sun bi sun daddaure zuciyarsa tamau sun hanashi sukuni da jin dadin rayuwar ko ta yaya, daga jiya zuwa yau da bai kwana wuri guda da Hafsat ba.
Ya tabbata za su ci gaba da bibiyarsa suna kassara shi har karshen rayuwarsa in bai yi gaggawa ya gyara kuskurensa ba.
Kamar an ce da Hafsat dago. A hankali ta cira idonta suka sauka cikin na Abdul’azeez. Sababbin al’amura masu ban mamaki ta gani a cikinsu wadanda bata taba gani ba. Ji ta yi ba za ta iya jure kallon tsakiyar idanunsa ba domin sosai ta fahimci yana cikin wani hali da ta kasa ganewa. Sunkuyar da kanta ta yi ta zame hannunta daga cikin nasa ta koma jikin Dada ta zauna. A kusa da Malam ya ci gaba da zama ya kasa tashi. Don ya san muddin ya mike kafafunsa ba za su iya daukar nauyin gangar jikinsa ba. Ya tafka gundumemen kuskure wanda bai san ya ya zai yi ya gyara shi ba.
Hotunansu da Habiba a Jeddah Mammah ta fiddo kala-kala a ke ta gani. Duk cikin bakar abaya ta ke irin ta matan Saudiyya amma fuskarta a waje ta ke ta dage himar din sama dauke da murmushi mai keta zuciya da hakorin makkah na gwal a bakinta, yawanci duk tare ta ke da su Isma’el a wuraren wasan yarababu Abdul’azeez yana Nigeria a lokacin. Addu’o’i na musamman aka yi aka rufe taron, sannan jama’ar gidan suka shiga fiddo da garar abinci kala-kala wanda aka tanada musamman dominsu. Rago guda aka kyafe aka gashe musu ko daddatsa shi ba’a yi ba. Abinciccikan na fulanin Jimeta ne irin su tuwon Alabo ( nyiri gurka )da miyar kubewa, tuwon masara da miyar yakuwa da gyada wato ( hako lauto ), tuwon dawa da miyar zogale ( hako kabije) tuwon shinkafa da miyar karkashi ( hako gubudo). A fannin abin sha kunu ne guda uku; ga kunun shinkafa ( garibasise ), kunun gyada ( gari biriji), kunun tsamiya ( garijabberi ) sannan ga soyayyar rama ( sa’ande ). Kowa yaci abincin nan da matukar marmari yayi hani’an hade da gasashshen naman rago. Www.bankinhausanovels.com.ng
Har dare suna gidan sai magriba maza suka fita sallah, suma matan suka yi a cikin gida. Bayan sallar isha’i suka yi sallama da kowa za su wuce masauki. Mammah ta dubi Hafsat wadda ita ma ta mike tana son ta bi su saboda rashin sabo, ta ce ta zauna da Dada, gobe kafin su wuce Kano za su biyo su yi sallama, kuma ta sanya wayarta a Caji za ta kira ta anjima.
Ta zura hannu cikin jakartatana lalubo wayar, sai ta ji farar takardar cikin ambulan. Zaro ta ta yi ta juya ta a hannunta ganin an rubuta sunanta
‘HAFSAT? a jikin ambulan din. Sai dai abu daya ya ja hankalinta, ‘handwriting’ din Abdul’azeez ne wanda ya riga ya zauna a memory din ta sabida yawan duba takardunsa data ke yi in ya bari a falo. Ta maida ita inda ta dauko ta don ta ga bai kamata ta bude agaban Mammah ba batasan ko menene a ciki ba. Mammah ta ce. “Wasikar mene ne wannan kamar rubutun mijinki?”
Cikin jin kunya irin nata ta sunkuyar da kai, ta ce, “Ina jin shi ya saka”.
Mammah bata ce komai ba ta yi musu sallama ta bi bayan su Adda Hafsatu, Suhaanah ta koma dakin Dada rike da jakarta.
Har karfe goma sha daya na dare Hafsat da kakarta Dada ba su kwanta ba. Hira suke yi tana ba ta labarin rayuwar mahaifiyarta. Da duk abin da ya kamata ta sani na zuri’arsu. Ita kuma Hafsat na ba ta nata labarin rayuwar a gidan tsohon Ambasada Hamza Atiku har zuwa aurenta.
Dada ta ce, “A duniya da ma akwai sauran mutane irin wadannan? Alherinsu ya bi su har ‘ya’ ya da jikoki
A cikin labaran da ta ke baiwa Dada ba ta taba kuskuren cewa Daddy bai karbe ta a baya ba, ta riga ta shafe wannan daga tarihin rayuwarta, ko Daddy bai yi ‘repenting’ kuskurensa ba ba za ta gushe tana mai yi masa uzuri ba da kallonsa matsayin uban da ya haife ta. Www.bankinhausanovels.com.ng
Suna shirin kwanciya tana kakkabe gadon bonon Dada da gefen zaninta don ta kwanta,
Dada ta shimfida sallaya za ta dasa sallar daren
da ta ke cinye rabin dare tana yi sannan ta kwanta. Ta bawa Dada baya tana ta kakkabe gadon, ta ji muryar Dada na zolayarta.
“Tun ganina da shi na farko na ji ya kwanta min a zuciya kamar autana Nuru. Da Hajiya Mairamu ta sani ta barki kin bi mijinki kun yi kwanan sallama, tunda za ki kwana biyu a nan a kai ki ki ga sauran dangi da ba ki gani ba, kuma Babanki ya ce za ku je Numan ya kai ki wajen nashi ‘yan uwan”’.
Murmushi ta yi ba tare da ta juyo ba, a ranta ta ce, “Ma’aurata na hakika su suka damu da juna har in za su rabu na wani dan lokaci su damu da su yi sallama da juna ban da mu Dada! Mu namu auren suna ne kawai”’.
Ta shiga tunanin ita yaushe rabon ma ta kwana daki daya da Abdul’azeez Dakata? Tun wani zamani can da suke cikin zama na aminci kafin ya rikide mata ya canza kamar wahainiya, har gobe in za a kashe ta ba ta san ina Abdul’azeez ya sa gaba a aurenta ba. Idan ta yi kokarin fassarawa sai ya rikide ya canja wanda ya nuna shi kansa ba shi da ‘direction’. Tunowa ta yi da takardar dazu da ta ciro a jakarta har Mammah ta gani, ta yi mamakin yaushe ya sa takardar a jakarta ba ta sani ba? Ta kuma cika da dokin son ganin me takardar ta kunsa? Don haka da ta gama gyaran gadon, kayan barci ta sanya ta jona wayarta a caji, sannan ta dauko takardar ta bi lafiyar gadon audugar kakarta, ta rufe rabin jikinta da bargon Dadan ta bude takardar ta soma karantawa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ga abin da Abdul’azeez Dakata ya rubuta wa matarsa Hafsat-Suhaana.
‘A zaman da muka yi na tsawon watanni goma sha biyar, in na ce akwai wata rana da ki ka bata min ko kika yi min abin da raina ba ya so ba bisa kuskure ba, na zalunce ki. Ta nawa bangaren ne akwai babban ‘gibi’ da ya sa ni kasa ci gaba da zama da ke Hafsah, amma ba don ba ki cancanci a so ki ba, ko a ci gaba da zaman aure da ke ba. You are a darling (ke abar so ce) ga duk wanda Allah ya yi wa alfarmar samunki a matsayin mahadin rayuwa. Rauni na guda daya ne; INA SON MU’AZATU! Na yi duk iya tunanina don nema wa aurenmu mafita na rasa Hafsat don shinge ne (barrier) a gare ni ga samun Mu’azatu, amma ba don ina kin ki ba. A bisa hakan, da wasu dalilai da dama na yanke igiyar aurenmu guda daya kamar yadda muka yi YARJEJENIYA. Allah ya ba mu mafita ta alkhairi ni da ke bakidaya.
Sa-hannu
ESQ Abdul’ azeez Dakata.
A hankali Hafsat ta lumshe idanunta, zuciyarta ta yi wani irin bugu sau uku; fat-fat-fat, a jere a lokaci daya. Ta shaki iska don ta fesar amma iskar ta makale ta ki fitowa daga huhunta. Kokawa ta shiga yi da numfashinta daga huhu zuwa makogaro amma iskar ta ki fita wanda hakan ya maida ita ‘unconscious’ na lokaci mai tsawo. Sai numfarfashi ta ke ta baka kamar mai ciwon ‘asthma’ da ta samu ‘attack’. Dada ta yi sallama kenan daga sallar da ta idar ta ji numfarfashin Hafsa kamar na fitar rai. Da sauri ta yaye mayafinta ta wurgar ta yo kanta. Bakinta ta sanya cikin bakinta ta shiga ba ta taimakon farko irin wanda ake badawa mouth-tomouth idan numfashi ya yi gardama.
Sun dauki mintuna biyar a haka kafin ta ji numfashin Hafsan na daidaita. Dago ta ta yi ta kwantar a kan kirjinta ta rungume ta. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ko da Hafsat ta samu kanta runtse idanunta ta yi hawaye suka soma sauka wani na bin wani. A ganinta bai kamata sakin ya fitar da ita hayyacinta har haka ba tunda akalla ta san da wanzuwarsa. Lokacin karbarsa ne ba ta sani ba. Ya zo mata ne awkwardly (bagatatan) kamar fadowar aradu. Abdul’azeez ya shammace ta, ya kuma tafi da dukkan farin cikin da ta ke ciki a yau wanda shi ne silarsa. Bai kamata ta ce ya karya zuciyarta ba, amma ya karya din. Rokon Allah ta ke ya sa mafarki ta ke yi, ire-iren mafarkanta na ranakun KWANGILA sun cika Abdul’azeez ya sake ta. Ta farka ta ganshi yana shirin (office) a gefenta ko yana kumbing kanshi yana feso mata ruwan jikakkiyar sumar sa a fuska, amma ta yi duk wani kokari da za ta iya don ta farka daga mafarkin yau, wasu hujjoji masu yawa sun tabbatar mata na yau reality ne.
Hujja ta farko jinta jikin dattijwwa Dadanta, tana shafa kwantaccen gashin kanta tana tambayarta, “shin tana da ciwon asthma ?” Da hausarta da ba ta fita sosai, amma kwarai ta ke gane duk abin da ta ke fada. “Ba ni da asthma Dada, amma ina da nimoniya (pneumonia)”. Ta amsa cikin dusashshiyyar murya.
“Amma abin da ki ka yi dazu, ya fi kama da na mai ciwon asthma”.
Hannu ta kai tana share hawayen da ke yin ambaliya suna bulbulowa daga idanunta.
“In ma ba ni da ‘Asthma’ Abdul’azeez ya saka mini”. Abinda ta fadi kenan cikin zuciyarta.
Baccin da ba su yi ba ke nan, sai da aka yi kiran ‘assalatu’ a kunnuwansu. Hafsat ta ga kuka da ciwon zuciya ba za su kare ta da komai ba tunda dai (he finally made his decision) ba ya bukatarta cikin rayuwarsa, bai boye ba ya gaya mata, ya kamata ta bude zuciyarta ta rungumi kaddararta da hannu bibbiyu…Ta karbi rayuwar a yadda tazo mata.
Ko wani bai fada mata ba ta fahimci zuciyarta ta dade da kamuwa da so da kaunar Abdul’azeez… to idan so cuta ne ya kamata hakuri ya zamo maganin cutar nan tunda an ce babu cutar da ba ta da magani a duniya. Www.bankinhausanovels.com.ng
Da wannan tunanin Hafsat ta kwarara zuciyarta, ta karbi butar da Dada ta cika mata da ruwa ta zaga ta kuma dauro alwala. Kafin ta yi sallah sai da ta tabbatar ta yi wa takardar sakinta kyakkyawan boyo, ta yi alkawarin kame bakinta ba dai wani ya ji wannan maganar daga bakinta ba, shi da ya aikata ya yi musu bayani in sun nemi ba’asin rashin dawowarta. Ta zo Jimeta kenan! Ita da Abuja sai da ziyara, ziyarar ma daga shekara sai shekara.
Ta dauki rayuwar da ta yi da Abdul’azeez Dakata ta sanya cikin wani kundi (littafi) mai dadin karantawa. A yau ta kawo karshen karatun
wannan KUNDI wato littafi ta rufe shi ta adana cikin tsohon akwatin karfe ta tura karkashin gado tare da duk wani al’amari da ya shafe shi. Tana tausayin kanta da sabon sunan da al’umma za ta laka mata na bazawara (before the age of 20), amma ta fi tausaya wa Mammah.Wadda ta dauki duk wani buri ta dora a kan aurenta da danta. Dan da a wurinta ba nata ba ne, ita ce ‘yarta. Idan kalaman Abdul’azeez sun so su yi mata ciwo sai ta yi maza ta kawo uzuri… iyakar gaskiyarsa ya fada… ya fadi zahirin abin da ke zuciyarsa ne. Yana daga cikin halayensa da ta ke so; fadar gaskiya komai dacinta… “Bata da abubuwan da Mu’ azatu ke da su, shi ya sa ya kasa ba ta gurbin matar aure!!!” Www.bankinhausanovels.com.ng
Sallah ta ke, amma kuka ta ke yi, hawayenta na bilbila a cikin sujjadarta. Rokon Allah ta ke ya ba ta juriya ta karbi sabuwar rayuwar nan da ta zo mata!!!
***
Da dai a ce ba daki daya ya kwana da kakansa Baffa Atiku ba da Allah kadai ya san irin halin da zai kasance. To Baffan kamar ya gane yana cikin wani hali, ya kasa ya tsare ya hana shi tunanin komai. Idan Allah ya yi maka alfarmar rayuwa da kakanninka, to ka gode masa duk girmanka. Suna da wani ‘feeling’ a kan jikokinsu da son farin cikinsu wani lokacin fiye da iyayen da suka haife su. Bai titsiye shi a kan sai ya gaya masa damuwarsa ba, amma ya lura ana ta kiransa a waya ba ya dauka, karshe ma da aka ci gaba da kiran wayar ya kashe ta bakidaya ya sanya ta a caji. Baffa bai bar kunnuwansa sun huta ba sai da bacci ya soma fizgarsa. Wani azababben barci da babu komai sai mafarkin Hafsat-Suhaanah, da halin da ta ke ciki a daidai wannan lokacin domin ya tabbata zuwa yanzu kyakkyawan sakonsa ya isa gare ta.
Kowa ya kalle shi a washegari sai ya tambaye shi ko ba shi da lafiya ne? Musamman Daddy wanda ya fi kowa shiga damuwar halin da ya ga Abdul’ azeez din a ciki. Ya zabge ya fyade a dare daya kamarwanda ya yi wata yana jinya, ya ce in ya san bashi da lafiya ba zai iya tuki ba su je ‘Airport’ su hau jirgi ragowar su taho a mota, ya ce zai iya, kuma lafiyarshi kalau bacci ne bai samu ba. Wani irin kallo Daddy ke binsa da shi na rashin yarda. Www.bankinhausanovels.com.ng
Demsawo suka nufo suka yi sallama da kowa na gidan, Mammah ta ce da Hafsat tunda hutu bai kare ba ta yi zamanta sai hutu ya kare Abdul’azeez ya zo ya taho da ita. A karshe ta ce, ta je yana dakin Malam su yi sallama. Ta yi sallama da Dada da matan su Yaya Tijjani, da sauran kannen Habiba da basu koma gidajensu ba tun jiya, an hada musu tsarabar Jimeta rankatakaf! Yara suka yi ta kwasa suna kaiwa mota. Mammah ta fita ta shiga mota suna jiran Abdul’azeez.
Kusa da dakin Malam dakin Nuru ne autan Dada, yana makarantar da yake koyarwa a lokacin da yake ranar aiki ce juma’a da safe. Hafsat ta tafi don cika umarnin Mammah, amma sai ta ratse ta shige dakin Nuru ta rufe har da saka sakata. Ba ta son ganinsa, ba ta son wata alaka ko ta
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG