TAWA TA SAMENI CHAPTER 23 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

TAWA TA SAMENI CHAPTER 23 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

text ya shigo min na bude sai naga show message i love you forever na duba. Yauma kamar kullum zai kai kusan sati biyu kullum sai an min wannan short msg na rasa waye?amma ina ganin Adams ne sai ya wani boye no naja tsaki ya karata nidai ba zan nuna mishi nasan yana yi ba ina yan fadace fadace na sai call ya shigo na duba sai naga yaynmu ne da sauri na dauka hello ki samenj dakin Kabir,hijabi na saka na fito falo mama yaynmu na kirana zai aikeni,to tace min Na fita zaune kan kujera na sameshi da remote a hannu
gani na fada ina Dubanshi sai naga ya daure fuska dan haka sai nima na shiga taitayina cikin dakewa da
miskilanci na shi yace zauna,na zauna ya dubeni da
farko ina maki murnar daidaitawa da mahaifinki da
fatan ki zama mai mishi biyayya ya cigaba da cewa naji batun Adam’s da kuma na gyara papers dinki kin zabga

karya kince kina son shi ya harareni
makaryaciyar banza innaso in miki gata ki samu krt ko da Degree ne ynxu kuma baki son krt ko?nayi shiru ya daka min tsawa bakya jina?bakina na rawa na ce ina son krt mana yace karya ne da kina son krt da kin tsaya kan ra’ayina na sonki yi krt amma sai kika ki kika dauki son aure kika dora a ranki to muddin kikayi aure


ba wani krt da zakiyi lokacin kiyi kuka da kanki ba da niba,na dube shi ai Adam’s yace zan ci gaba da krtna ya harareni wannan ra’ayin shi ne ina sonki san cewa ba dole bane Adams ya zama mijinki,don ba shi zuciyarki take so ba,haushi ya kamani nace ina sonshi yayanmu ya fusata zan mareki fa,karya na maki Www.bankinhausanovels.com.ng kenan?gara ma ki fito ki fadi wa wanda kike so ko zai taimaka miki da sauri na dubeshi yace shiii yi min shiru kin san siyasa na karanta ko?ya cigaba in ina son bararda Adams a wajen su Alhj a guna abu mai sauki ne sai dai ba halina bane yanzu zan fada miki sirrin zuciyarki,kin kamu da ciwon son wanda kike so tun shekarun baya sai dai baki da tabbacin ko yana sonki dalilin shi ne kika kamu da ciwon zuciya dan kin kasa neman shawara ko mafita kar ki min musu kuma kar kiyi mamaki mutane da dama suna zaton na karanci halayyar dan Adam ne saboda yanda Allah yayi min baiwar saurin fahimtar mutane kin yarda ko har yanzu kina nan kina nan kan cewa ba haka bane?wata zuciyar tace min ki fada mishi gsky wata kuma tace kar ki bada kai,sai nace ni fa ba wanda na taba so ni Adams kawai nake so,ya zuba min Www.bankinhausanovels.com.ng
ido ranshi in yayi dubu ya bace shi in ban dama yana
ganin zubar da girma ne yace yana son yarin
yar nan da dai ta yarda da abinda yace to sai ya nuna mata cewa zai taimaka ya aureta dan dai shi ba zai taba cewa yana sonta ba ta raina shi,to ita kuma ga shegen taurin kai ynxu yaya zaiyi kenan?kai shi ai daya san inda ake ajiye so da ya cire inda nata yake ya yar ya huta ya mike tsaye yana dubana sannan yace na zone nayi sallama dake don gobe kamar yanzu muna hanya duk yanda kika ga dama kiyi sai dai zan fada miki wani abu komai ya biyo baya kiyi kuka da kanki zan maimaita miki kiyi kuka da kanki yace kina iya tashi ki tafi sannan in kina bukatar taimako ko na menene kina iya nemana ta waya jikina babu karfi na mike a raina na raya bari na mishi kallon karshe dan haka sai na dube
ashe shima ni yake kallo na juya daidai kofar fita na
kuma juyowa na dubeshi sannan na fita,gidansu Amira
na nufa tana kwance tama aikin karanta littafi kanta na dafa ina kuka tayi jifa da littafin hannunta ta juyo Ify Iman?me ya faru?cikin kuka nace shi kenan mun rabu tace dawa?nace da yayanmu,sannu kan hankali na zayyane mata komai ta ce kash! Kinyi wauta dakin sani kince mishi kina sonshi menene?ba zan iya ba Amira tunda shifa ba sona ya keyi ba cewa fa yayi wanda nake son zai taimaka min gara na hakura sam ya ma ki nuna cewa shi nake so da kyar Amira ta lallasheni sannan na dawo gida.
Kwana biyu duk na rame na fita hayyacina saukin tama naje gidan Babana kamar yanda Alhj yayi alkawari gata dai na duniya ba irin wanda ban gani ba har kasuwa yaje dani can naga yaya Abubkr da yaya Ibrahim don ynxu sun kyaleni,kyauta dai na sameta gurin abokan babana yace yaya Ibrahim ya dawo dani gida ya maida ni Anty Fati sai huci take yi niko ko kallonta banyi ba Anty Maijidda itace matar da babana ya sake aura itama yar cikin kano ce shekara biyu kenan da auran,itama dai shiru ba haihuwa tana da kirki sosai kuma ta nuna tana sona har kitso tayi min dan haka sai nake gurinta,da babana ya dawo kuma sai na koma Www.bankinhausanovels.com.ng
gurin shi tare muke cin abinci muyi hira ya kan
tambaye ni me nafi so ko kuma me na ke so ya sai
min?na dinga mishi lissafi ranar da zan dawo sai da
muka shiga kasuwa dashi siyayya har ta banza kuma
daga kan sutura kayan shafe shafe turarurruka da
takalma su Jamila da Sagir kai har su Mami sai da nayi
musu tasu tsarabar,Mama da Alhj turare na sai musu
sai kace daga wani gari na dawo da ya kawo ni gida
kamar kar mu rabu nace zan kuma zuwa ai ya kara
bani wata wayar yace shi kadai zai dinga kirana ya
samin layin glo ya zuba min no dinshi da ta tsohuwa
kakata yace na kira nace zai kawo ni na kwana biyu
nace babana na tafi ka gaida Anty Maijidda ta bani
tirare tace na ba Mama yace shine baki fadamin ba?
nace ita tace kar na fada maka yace to zan mata
godiya ki ce ina gaida Habiba har na kai bakin kofa sai
yace kin manta da tsarabarki nace lah na mance na
dawo ya kwaso min, duk wani motsina idonshi yana
kaina kai Babana na sona matukar so..
Kwanaki suna_ shudewa,Lokaci na_ kara wucewa mun
gama Diploma a Comp, sannan munyi jarabawa sai dai
jiran abin da zai biyo baya Adams yana kirana a waya
duk da bani sonshi a raina ina dan sauraranshi yaynmu kam bai taba kirana ba sonshi dai yana nan makale a raina ,Alhj da Babana sunyi bincike akan Adams ashe ma mahaifin shi abokin Alhaji Adamu garko ne me gidan Babana dan haka basu sha wata wahala ba wurin bincike sun shirya magana tasu ta manya sannan sunce sai sunji ta bakin Adams sun kira shi sun mishi bayani yayi murna sannan sun bukaci ya fadi daidai lokacin da yake son a sa bikin yace su bashi kwana biyu zai sanar dasu, a son Alhj ayi bikinmu rana daya dasu Mami da Sa’a da Bilki,to amma da kyar hakan zata samu. Yau laraba zaune nake gonar kawu kabiru kanin mama Www.bankinhausanovels.com.ng
a kauye gefena Jimmala ce kanwar yaya Ibrahim tunda naje kauye kullum sai naje gona kota dangin mama ko ta dangin babana,daga inda nake ina hangen kawuna yana bawa masara ruwa wayata ta soma ringn Adams ne na sani dan haka sai na dauka gami da sallama yar gidana na jima ina nemanki ban same ki ba?nace matsalar ntwk ne yace to ya gari?nace gari na hannunku mutanen England yayi dariya,to yaya?na me? na zancen mu mana kinsan yau ne na yanke musu zan sanar dasu date din daya kamata a sa fa,na dan yatsina baki nace kai yaushe kake so,nafi so asa watan goma kin ga yanzu muna watan hudu nan da wata shida kenan ko?nace to hakan ma yayi daidai, su Mami zasu rigamu dan su saura wata biyu yace insha Allah dani za’ayi bikinsu Mami,Amira fa?nace ita sai tayi HND tukunna yace Ok! to duk yanda sukayi zan kiraki nace kai yaushe zaka zo yace sai bikin su mami zamu zo tare da yaynku ne,gabana ya fadi sam bana son tuna shi dan yaynmu shi kadai nake so so mai tsanani rabona da ganin shi tun bankwanan nan da mukayi yace kina jina?nace ina jinka Adams wai dan Allah kuna shiri da yaynmu?yace sosai ma dashine muka sa date din bikinmu gabana ya fadi nace haba yace Allah gaske ne fa nace suna Ify yace kalau shine ma ya tsaida date don nace nan da four month yace gara six din,nace Allah ya kaimu yace amin…
Adams kan abin motsa jiki yaynmu ne ya hada zufa
tamkar mai tukin mota yanata faman yi can ya dubi
agogon dake manne jikin bangon dakin karfe takwas na
safe ya jawo tawul ya soma share gumin da ke zubo
mishi sannan yasa baki ya kira Mimi,Mimi ta shigo da
sauri gani ya dubeta ina shayin wai yaushe ne zaki koyi
yanda ake kula da miji ne?kin san kawo shayin nan
aikin ki ne daidai wannan lokacin amma kullum sai nace ki kawo?to za kije ki kawo din koko?kin tsaya min akai,ta juya shi kuma ya ja tsaki sannan ya sauka daga kan abin motsa jikin ya hau kan wata kujera a gefe ya zauna yaci gaba da share zufar,ta shigo rike da kofin tangaran babba da karami,ta ja wani dan tebur ta tura mishi ta juya ba tare da magana ba ya bita da kallo sannan ya girgiza kai sam Mimi bata dace dashi ba ta kowanne fanni sannan yana son a inganta mishi ciki dan kowa ya san yan kwallo da cin abinci,ya kurbi ruwan na lipton mai hade da wasu ganyayyaki can sam Sai yaji komai ya ishe shi ya kwana biyu kenan baya cin wani abin kirki tunda Adams yazo mishi da zancen Www.bankinhausanovels.com.ng
sa ranar shi da Iman ya kuma nemi shawarar sa ya
bashi shawara ya bari sai nan da watan goma ne dan
yana son ya nemi mafita sam ba zai bari adams
ya auri yarinyar da yake masifar so ba,so mai tsanani sannan yasan tana sonshi taurin kaine yasa taki fadi to shima yayi alkawarin sai ya aureta muddin yana numfashi a doron kasa,yayi lissafi Mimi tana da ciki wata biyu zata haihu watan sha daya yana son sai mimi ta haihu
sannan ayi bikin nashi ,amma ba zai yiwu ba,ya danyi
shiru na wani dan lokaci sannan yace na san abinyi ya
mike tsaye ya fita bayi ya shiga a cikin dakin shi ya
hada ruwa yayi wanka a gagauce ya shirya cikin JC
blue da ratsin fari ya daura takalmi mimi ta shigo kana Www.bankinhausanovels.com.ng
da bako,ya dubeta wanene?ta dan tsina baki ko Adams yake ne oho?haushi ya kama shi me yasa yarinyar nan batada kunya ne yanxu?amma zaiyi maganainta yace fita anan banza kawai ni zaki cewa baki san Adams ba? ta fita tana yin kuna kunai na gaji da wulakancinka komai kace sai an maka ni ko gsky ko a gidanmu ban kauda tsinke bare wani girki ina dan wanda zan iya kai kuma kana ganin kasa wata yana jiyota sai dai bai san me take fada ba yace zaki gane kuskurenki. Ya sami Adams zaune shima da shiga irin ta Maska Adams ya dubeahi kace ka shirya Maska ya zauna sai dai ban karya ba,haba baka karya ba kai da kake da iyali ma,Maska yace kasan bata da Ify gata dama da son jiki sam bata son aiki Adams yace sai hakuri nidai Allah
yasa nayi dace in har ka dace ka sameta din to Adams
kar kayi shakka zaka sami yanda_ kake so,Adams ya ce ya kake cewa in har na sameta?kana ma shakka
kenan?kar ka manta fa har na biya sadaki an sa mana rana kuma kaine ma ka tsaida min har na sanar da manya,Maska yayi wani murmushi Adams ya kalleshi

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *