AUREN KWANGILA BOOK 3 CHAPTER 5 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

 AUREN KWANGILA BOOK 3 CHAPTER 5 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

Demsawo suka nufo suka yi sallama da kowa na gidan, Mammah ta ce da Hafsat tunda hutu bai kare ba ta yi zamanta sai hutu ya kare Abdul’azeez ya zo ya taho da ita. A karshe ta ce, ta je yana dakin Malam su yi sallama. Ta yi sallama da Dada da matan su Yaya Tijjani, da sauran kannen Habiba da basu koma gidajensu ba tun jiya, an hada musu tsarabar Jimeta rankatakaf! Yara suka yi ta kwasa suna kaiwa mota. Mammah ta fita ta shiga mota suna jiran Abdul’azeez.
Kusa da dakin Malam dakin Nuru ne autan Dada, yana makarantar da yake koyarwa a lokacin da yake ranar aiki ce juma’a da safe. Hafsat ta tafi don cika umarnin Mammah, amma sai ta ratse ta shige dakin Nuru ta rufe har da saka sakata. Ba ta son ganinsa, ba ta son wata alaka ko ta

gaisuwa ce ta sake shiga tsakaninsu. Me ya saura a tsakaninsu? Babu for now! Sai ‘yan uwantakar musulunci da zumuncin haihuwarsa da Maryam Dakata ta yi ya riga ya hada. Da ta san haka zafin saki yake a zuciyar diya mace da ba ta yarda da wannan

yarjejeniyar ba. Da ta san haka zafin so yake, da ba ta yarda ko kusa Abdul’azeez ya shiga rayuwarta ba. A sanda suke tare, * the feeling is So sweet’ a yanzu da rabuwa ta zo, ‘ it’s painful, very painful’ . Zuciya ta yi duhu, babu komai cikinta sai kunci mai azabtar da ruhi. Hawaye ke zuba daga idanunta suna sauka a kan tafukan hannayenta. Www.bankinhausanovels.com.ng
Abdul’azeez Dakata zaune a dakin Malam Babba, Mammah ta ce da shi, ga Hafsat nan zuwa. Ji ya yi kamar ta dauke masa wani nannauyan dutse da ya danne zuciyarsa. Kokari zai yi ya karbe takardar daga hannunta tun wani bai ji ba bai gani ba, ya yi ‘ repenting’ . Ya san Hafsat na da sanyin zuciya, sannan tana girmamashi, tana yawan yi masa uzuri, kalamai kadan za su wanke wannan gundumemen laifin nasa (kamar yadda yake tsammani). Daga shekaranjiya zuwa yau ya nutsu ya tantance aya da tsakuwa, ya yarda rayuwarsa ba za ta taba komawa daidai ba, ba tare da dawowar Hafsat cikinta ba. He can do without Mu’ azatu, but he cannot do without Hafsat , wannan wani abu ne da ya yarda da shi daga jiya zuwa yau kadai ganin yadda rayuwar ta birkice shi (upside-down) ta maida shi wani birkitacce susutacce. Rokon Allah yake ya sa Hafsat ba ta yi zancen wasikar nan da Mammah ba. Kai ba ta yi ba… babu wani canji a tare da Mamman har ta shiga mota”’Don haka ya ci gaba da taraddadin jiran fitowar Hafsat ya maida hannun agogo baya. Amma har ya kwashe mintuna talatin a zaune babu Hafsat balle kamshin sanyayyan turarenta. Www.bankinhausanovels.com.ng
Hankalinsa ya soma tashi ne lokacin da Daddy da Mammah suka shiga kiran wayoyinsa da ke aljihun rigarsa, da fari kamar ba zai amsa ba amma suka ci gaba da kiran. Dole ya amsawa Daddy. Har yanzu sallamar ba ta kare ba ne Yayansu? Akwai tafiya fa a gabanmu rana tana yi”.
“Ga ni nan Daddy”. Kawai ya ce a sanyaye. Ya tabbata Hafsat ba za ta fito ba kenan. Da za ta fito da tsawon mintuna talatin din da ya share a zaune sun isa su fito da ita, daga dai cikin gida zuwa dakin Mallam. Wannan ma shaida ce mai tabbatar masa da cewa Hafsat ta karbi sakonsa;(And she acts accordingly).
Cikin sagewar gwiwa da debe tsammani ya fito daga gidan Malam Hashim Babbah Jimeta, ya ja motar da iyayensa da kakanninsa ke ciki, suka soma fita daga shiyyar Demsawo. Tafiya sannusannu har suka hau titi dodar suka bar garin Jimeta. Ji yake tamkar ya bar wani bari na gangar jikinsa cikin Jimeta, barin da bai san yadda zai yi ya dawo da shi jikinsa ba. Anya bai tafka kuskure ba? Ta yaya ya tabbatar rabuwa da Hafsat shi ne babban tsanin da zai samo masa Mu’azatu daga wajen mahaifiyarsa? Anya hakan ba shi ne kuskure ba maimakon ya zamo MAFITA a gare shi? Da wadannan tunanukan masu nauyi Abdul’azeez yake tuki yana wuce dazuzzuka da
bishiyoyi, garuruwa da kauyuka yana mai jin tamkar karshen rayuwarsa ya zo! Da wacce kalma zai kare kansa ranar da Mammah ta karbi sakin da ya yi wa Hafsat don ya samu Mu’ azatu???

********

Sai da ta ji tashin motocinsu sannan ta koma cikin gida. Dada ta tambaye ta sun tafi? Ta ce sun kama hanya. Kwananta uku ba inda ba a kai ta ba gidajen ‘yan uwa da dangi. Ranar da ta cika sati gidan Yayanta Modibbo ta wuni a Use-Demsawo tare da matarshi Kaltum. Washegari kuma gidan mahaifinta wanda ke cikin gidajen malamai na jami’ar Yola. Matarshi Aunty Kubra ma’aikaciyar gwamnati ce a hukumar haraji ta jiha, mace ce da ta san ciwon kanta, ta ke kuma rungume da su Imamu da zuciya daya. Www.bankinhausanovels.com.ng
Cikin sati daya da Hafsat ta yi a gidan mahaifinta Dr. Bashar tare da shi da ‘yan uwanta na ciki daya Imamu da Abdurrahman tunda Modibbo da suke kira Hamma Modibbo yana nasa gidan, Modibboma’aikacin (Immigration Office) ne. Sabo mai tsanani ya shiga tsakaninsu musamman Imamu, wanda ke karatunsa a (American University Yola) a kan tsimi da tanadi. Shikuma Abdurrahman yana aiki da gidan wayar Etisalat. Rayuwar gidan abar koyi ce domin kowanne na da abun yi, sun fahimci juna kuma ilmi ya ratsa kowa. Tsakanin Imamu da Abdurrahman da Dr. Bashar din kansa har rige-rige ake wajen farantawa Hafsat da suke kira (GAAJI) wato
‘auta’ da harshen fulatanci. Wannan ya taimaka kwarai wajen mantar da ita Abdul’azeez da duniyarsa.
A karshen satin Daddy ya shirya musu tafiya zuwa ‘NUMAN’ ainahin asalinsa don su kai Hafsat ta ga sauran ‘yan uwansa tunda iyaye babu sun kare.
A motar Dacta Bashar kirar ‘Sienna’ suka yi tafiyar har Hamma Modibbo da maidakinsa Kaltum. Ita da Kaltum na kujerar can baya, Abdurrahman, Modibbo da Imamu na kujerar gabansu, Daddy ke tukin motar, Aunty Kubra na gefensa. Tafiya ce mai dadi da sanya nishadi a gare su, suna tafe suna hira har suka isa garin Numan. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Yan uwan haihuwar Dacta Bashar su uku ne ke raye, Baffa Sa’adu, Malam Zakari da Surajo duk tare suke da iyalinsu a can Numan kowanne na da kwakkwarar sana’arsa. Su Malam Zakari sun ga ‘yar dan uwansu sun kuma ji duk abin da ya faru da Habiba. Addu’a kan Habiba ta sha ta kamar yadda Hajiya Maryam ta sha tofin albarka da fatan alkhairi. Bayan dawowarsu daga Numan da kwana daya Dada ta aiko Nuru ya zo ya dawo mata da Hafsat ta yi shirin komawa gidan mijinta, Mammah ta yi mata waya cewa hutun su Hafsat ya kare za su koma makaranta ranar litinin kwana uku masu zuwa.
Tun barin su Mammah Jimeta Hafsat ba ta kara kunna wayarta ba. A ganinta wayar ba ta da sauran amfani a gare ta. Ba ta da sauran alaka da
wanda ya mallaka mata wayar amfanin me zata yi mata? Mammah kuwa da Baba Azumi in ta samu nutsuwa za ta dinga kiransu ko ta wayar Dada ne tana gaishe su.
Da ta dawo Demsawo ta tadda sakon Mammah daga bakin Dada, rasa me za ta ce ta yi. Ta fito fili ta ce da Dada ba ita ba Abuja, mijinta ya sake ta ko me? Kwata-kwata ba ta son tuna cewa ‘an sake ta’ kalmar tana yi mata maqaqi a zuciya. Wa za ta gaya wa tsakanin Malam, Mammah da Daada ba tare da hankalinsa ya tashi ba? Ko dai shiru za ta yi ta koma Abujan ta ci gaba da zama gidan Mammah ta cigaba da zuwa makaranta tunda ba za ta iya barin karatunta ba? To amma Yayan Haleem ya sake ki, kuma ki koma ki ci gaba da zama gidan mahaifinsa? Alhalin ba rasa muhallin zama ki ka yi ba? Wata zuciyar ta ce.
“Haba Hafsatu? Kada ki zam-makaho warke ka karya sandarka! Har abada ba ki da gidan da ya fi na su Abdul’azeez din in har duniya da halacci da amana. Koma gaban Mammah ki ci gaba da karatunki in har za ta barki, ki kuma cika alkawarinki na taimaka wa Abdul’azeez ya cimma burinsa…… Wani hanin ga Allah baiwa ne!”.
Da wannan shawarar Hafsat ta soma shiri kamar yadda Dada ke ta yi mata itama don komawa Abuja. Sai dai irin hakukuwa da sauyoyin da Dada ke damawa kala-kala tana ba ta, ta ce ta shanye a kan idanunta kasa gane kansu ta yi. Da ta tambaye ta ko magungunan me ta ke bata? Cewa ta yi na gyaran aure ne. Bakinta ta ja ta yi shiru ta ci gaba da shirya ‘yan kayan da ta zo da su wadanda duk sun ji jiki saboda maimaita su da ta yi ta yi tana wankewa kasancewar ba ta debo kaya da yawa ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ana i-gobe Hafsat za ta koma Abuja, Mammah ta kira ta a wayar Dada, ko gaisawa ba su yi ba ta soma yi mata fadan rashin amfani da wayarta da ta ke yi. Hakuri ta yi ta ba ta, ta gaya mata sun yi tafiya zuwa Numan kuma tun zuwanta ba ta zama. Ziyarce-ziyarcen dangi ake raka ta nesa da kusa. Mammah ta karbi uzurinta, ta kuma gaya mata goben jirgi za ta hawo ta dawo. Abdul’azeez ba ya kasar, ya je America ‘graduation convocation’ na Isma’el daga jami’ar Harvard, daga can za su wuce na Usman a Brussels sai nan da sati biyu za su dawo shi da Isma’el da Usman din. Don haka nan Asokoro za ta taho in ya dawo sai su koma gidan nasu.
Wata ajiyar zuciya Hafsat ta yi cikin sanyin murya irin nata ta ce, “Toh Mommah, sai Allah ya kawo ni lafiya. A gaida Baba Azumi da Daddy”.
“Za su ji, ki gaida Dada da Malam da duk mutanen gidan”. Da wannan suka yi sallama.
Washegari Dr. Bashar da kansa da Imamu suka kai Hafsat da kayanta filin jirgin saman Yola, jirgin ‘Azman’ ta bi zuwa Abuja. Babanta ne ya biya kudin tikitin duk da Mammah ta aiko mata
da kudi ta account dinta, ita a wajenta har gobe nauyin Hafsat yana wuyansu ba abin da ya canza.

*********

Ta sauka a Abuja da misalin karfe shidda na yamma, a reception suka hadu da Salisu direban gidansu ya zo daukanta. Ya karbi kayanta ya sanya a ‘boot’ ya bude mata murfin motar ta shiga ta zauna ya rufe suka nufo Asokoro.
Suna shigowa tangamemen get din gidan ta hango Mammah a kofar shiga babban falo tana jiran isowar su. Ta kara kyau, kullum kamar ana kara mata kuruciya, za ka rantse ba ta haifi Haleem ba balle uwa-uba Abdul’azeez. Wasu zafafan hawaye na tausayin Hajiya Maryam da ita kanta suka cicciko idanunta. Ta san tana son aurenta da dukkan zuciya da ruhinta, amma ta yi amanna Mammah ta fi ta son wannan auren da dorewarsa. To ya za su yi? Tunda wanda ke da iko da igiyoyin auren ya tsittsinka su? Ba ya sonta! Ba ya bukatar hada rayuwa da ita, dole ita da Mammah su dau dangana su hakurkurtar da zukantansu. Allah ya sa hakan ya zama alkhairi ga rayuwar kowannensu. Ta sa gefen mayafinta a fakaice ta share hawayenta. Www.bankinhausanovels.com.ng
Mammah na tsaye aka fito da kayanta na ‘boot’ ta kasa jiranta ta karaso inda ta ke ta tako ta iso jikin motar ta bude mata kofa. Salisu ya roke ta ta bar masa kayan zai shiga da su. Ta kama hannun Hafsat abinda ta lura da shi jikin Hafsat a matukar sanyaye yake tamkar wadda aka yiwa duka. Idanunta sun kode da alamun ta jima bata sanya musu kwalli ba. Kai in ba ta yi kuskure ba, za ta iya cewa Hafsat ta rame. Ta dai bar komai a cikinta Hafsat din ta samu ta huta. Dakinta na ‘yammatanci aka shigar da komai
nata, a can ta yi wanka ta yi sallah kuma har can Baba Azumi ta kai mata abincinta ba su ce ta zo ta ci a ‘dining’ ba kamar yadda yake a al’adar gidan duk don ta samu nutsuwa.
Ta nemi wata doguwar riga mara nauyi cikin kayanta ta sanya, ta zauna da zummar ta ci abincin, amma duk yadda ta kai da kokarin ganin ta ci din abin ya faskara. Zuciyarta ta yi nisa wajen tunanin yadda za ta nunawa Mammah takardar sakinta! Haka ta saka abincin a gabanta tana kallo kwata-kwata hankalinta ba ya jikinta. Sau biyu Mammah na shigowa jin shirun nata ya yi yawa tana ganinta cikin wannan halin. Azumi ma shigowarta biyu, har suka fita ba ta san sun shigo ba balle fitarsu.
Mammah dakinta ta koma ta yi shiru, daga bisani ta yi kiran Baba Azumi, ta shigo ta zauna gefen uwargijiyarta a kan ‘center carpet’, Mammah na gefen gadonta. Ba ki fahimci Adda na cikin damuwa ba?” Azumi ta gyara zama ta ce, “Ni kuwa na fahimci hakan. Har magana na yi mata sau uku ba ta san ina yi ba’.To a ganinki me ke damunta? Ko a da Hafsat da ta san ba ta da kowa sai mu ba ta sanya kanta cikin damuwa ba sai yanzu?” “Ba kya tunanin tafiyar mijin ce?” Inji Baba Azumi.
“Ba ta magana da shi a waya. Ya gaya min rabon da ya yi magana da ita tun a Jimeta. Ta kashe wayarta kwata-kwata tsayin kwanakin nan
data yi acan. Da na yi mata fadan kashe wayar cewa ta yi ba ta samun zama, kuma ta je kauye. Shin a wannan zamanin duk inda ka je za ka kasa yin mu’amala da waya? Balle ka kasa magana da mijin aurenka tsayin sati biyu?” Duk sai suka yi shiru. Daga bisani Azumi ta ce Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ina tunanin matsala ce suka samu a tsakaninsu”.
Mammah ta runtse ido kadan ba ta ce komai ba, amma ta yarda da abin da ta ce din.
“Ki zuba musu ido Maman Haleem, kada ki tambaya, kada ki bi ba’asi. Tsakanin mace da miji sai Allah. Sanda za su shirya kansu ba za ki sani ba”.
Zuciyar Hajiya Maryam babu dadi, ta ce, “Haka ne”. Amma can a karkashin zuciyarta tana jin ba dadi, sanin cewa auren Abdul’azeez da Suhaana ba normal auren so ba ne. Sai dai ya taho da nasara fiye da yadda ta tsammatar masa. Tana tsoron duk wata matsala da ka iya tasowa a cikinsa. “Ya Rabbi Sallim!”
Ta furta a fili bayan fitar Azumi daga dakinta.

*****

Kwanan Hafsat biyu kenan da dawowa daga Jimeta. Mammah na lure da ita, ba abin da ya canza cikin yanayin da ta dawo da shi, sannan ko sau daya ba ta ga ta jona wayarta a caji ba balle ta kunna. Washegarin ranar suka koma makaranta. Hafsat ta sani, amma ko alama ba ta yi wa
Mammah zancen ba. Ji ta yi karatun kansa ya fita a ranta, duk wani buri da ta ci masa ya zagwanye. Ashe karatu ba shi ne farin cikin rayuwa ba? Ashe akwai abin da ‘yamace ta fi bukata a rayuwarta fiye da karatun boko? Ashe ba abin da ya fi muni ga rayuwar diya mace fiye da ‘sakin’ da ada ta ke ganin ba komai ba ne? Ashe tsakanin zuciyarta da Abdul’azeez ‘soyayyah’ ce kuma ‘kauna’ ce mai tsananin da zuciyarta ta kasa karbar rabuwa da shi da sauki??? Www.bankinhausanovels.com.ng
Duka a bandaki (toilet) ta ke wannan tunanin, ta shiga da zummar wanka, amma sai ta bige da zama a kan (soak-away) ta shiga shesshekar kuka, kukan da a baya ba ta yi ba tun ganin takardar sakinta. Koyaushe cikin mutane ta ke a Jimeta ko gaban kakanninta, suna yi mata hirarrakin uwarta da ke debe mata kaso 80% na tunanin Abdul’azeez da karewar ‘KWANGILARsu’. Yanzu ne komai ya rufto mata take jin kanta cikin wata irin kewa mara misaltuwa. Tamkar ta rasa komai na jin dadin duniya, tamkar ta rasa komai data taba mallaka a rayuwarta.Zamanta cikin gidansu da kasancewarta kusa da wadda ta fi kowa kusanci da shi a duniya ya maido komai sabo kuma danye a zuciyarta, ya maido mata komai baya na rayuwarda ta yi da shi ta shekara da watanni. Yadda shekarar ta kasance dalla-dalla a kan tafin hannunta……. Daga rayuwar DUHU zuwa rayuwa mai HASKE kafin ta karkare ta koma DUHU dudum a halin yanzu kenan da wannan rayuwar ta duhu da haske ta kare bakidaya. Sai dai duk ta inda zuciyarta ta karkata don baiwa Abdul’ azeez laifi Hafsat ta ki karba, zuciyar mai so da kaunar Abdul’azeez kare shi ta ke yi. A bisa dalili da dama da hujjojinta kwarara! Www.bankinhausanovels.com.ng
Muhimmi cikin hujjojinta shine;Abdul’azeez bai taba yaudararta da cewa za su dore da rayuwar aurensu ba! Bai taba yaudararta da kalmar ‘SO’ ba. Zuciyarta ce ta zarme zuwa ga son abinda yafi karfinta…. ta zamo out of her control ta jefa ta cikin matsananciyar soyayya da kaunar Abdul’azeez din data ke da tabbacin baya son ta. Ba ta yarda da hakan ba sai yau da suka rabu, auren kwangilar ya kare! A yau ta yarda cewa ta dauki lokaci mai tsawo cikin soyayyar Abdul’azeez Dakata ba tare da saninta ba. Wani kwantaccen so mai bin jiki da jijiya. Ba ta fahimci hakan ba sai a kurarren lokaci, lokacin da ya zamo haramiyarta…!!!
Fuskarta ta sanya cikin tafukanta ta dinga kuka wanda ke fitowa tun daga karkashin zuciyarta.
Shigowar Hajiya Maryam na uku kenan dakin tana komawa ta fita da sauri, saboda zuciyarta da ta kasa jure sauraron irin kukan da Hafsat din ke yi. Ta koma dakinta jikinta har rawa yake yi. Babu wanda zai tada hankalin Hafsat, ya jefa ta cikin wannan halin in ba mijinta Abdul’ azeez ba, tunda wa ta ke da shi bayan iyayenta da su in ba shi ba? Babu wanda zai bata mata rai a Jimeta! Zuciyarta na son daukar waya ta kira shi, wata zuciyar na hana ta.So ta ke ta ce da shi “ da ka bata min ran marainiyar Allah Addah ‘yar amana ta, gara ni ka bata nawa ran”. Ta tuna shawarar da Baba Azumi ta bata; “ Kada ta shiga, kada tatambaya, kada ta bi ba’asi” . Baba Azumi ba ‘yar aiki ce kawai agareta ba yanzu, uwa ce a gareta, kuma wanda ya riga ka kwana dole ya riga ka tashi. Www.bankinhausanovels.com.ng
Bataso ta yarda da kaso mafi rinjaye na zuciyarta da ke cewa, “Abdul’azeez ba ya son Hafsat har yanzu……. damuwar Hafsat kenan’”’. Shigowar Daddy dakin nata yana tambayar wasu mukullansa ya sa ta farfadowa daga zazzafan tunanin da ta fada, wanda zuwa yanzu ya fara tafarfasa zuciyarta. Dagowa ta yi a hankali ta dube shi idanunta jazir. Da sauri Dr. Hamza ya karasa shigowa dakin, “Lafiya Maryama? Me ya faru? Mutuwa aka yi?” Ya kama dukkan hannayenta biyu ya rike cikin nasa. Ganin yadda hankalinsa ya tashi da ganin yanayinta ya sa ta nemo wa kanta murmushi wanda bai wuce iya fatar bakinta ba.
Bai kamata ta ce masa komai ba, tunda itama ba ta san me ke faruwa din ba. Ga shi Baba Azumi ta ce ta ba su lokaci, watakila da ya dawo sun koma gidansu komai zai wuce, ko harshe da hakori ai ana sabawa. Ita da ta yi auren soyayya da Prof. Hamza wane irin bacin rai ne bai jefa ta a ciki ba, kuma ta jure sun zauna a haka har aka zo gejin da bacin ran nata shi ne abu na karshe da yake guje mawa?
“Hafsat ce ba ta jin dadi”. Ta fada a hankali yadda zai kwantar da hankalinsa.
Ya ce, “Ai sai ku je asibiti a duba ta, ba ki zauna kina tagumi da jan ido ba”.
Ya dauki mukullayensa a kan lokar gadonta, ya juya. Har ya kai bakin kofa ya kama marikin kofar sai ya juyo da murmushi a kan fuskarsa.
“Ko amarya zan samu ne kwanan nan aka gaya min indirectly ?”

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *