ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 10 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE
Www.bankinhausanovels.com.ng
Haka yayi ya gaji ya koma ya dawo, haka
ya yi tsawon ranar shi ba abinda yaje ya fadawa wani cikin ‘yan uwansa ba abin da yake gudu ya zo ya faru, domin dole ne sai sun so jin dalilin sa na yin hakan, shi kuma ba zai iya fadawa kowa ba.
Haj. Asiya tana kallon su babu abin da ta ce da su sai tsananin mamakin irin Kaunar da yake nunawa Hameed kamar ransa, wanda hakan ne ya janyo ya fada cikin wannan halakar. Don tabbas ta san Alh. Jafar yana: matukar son Hameed fiye da komai a cikin rayuwar sa, ta san zai iya aikata komai akan sa, don ya ga ya bashi farin ciki.
Sai dai kuma a yanzu yanda ake da wuya ya bawa Hameed farin cikin da yake so, domin farin cikin sa a yanzu shi ne ya bar shi ya fada cewa shi ne ya yiwa Aziza wannan aika-aikar. Amma ina! ba zai taba barin haka ya fsaru ba. Sai misalin sallar isha taje ta yiwa Hameed magana akan ya bude dakin, da yaji
muryar ta ne da sauri ya bude don ya ji dadi, don ko ba komai zai samu .wata nutsuwar domin rashin wata nutsuwar har da rashin kulawar da yake samu gurinta, hakan ma ya sake sa shi cikin wani azabar.
Lokacin da ya bude ta ganshi sai da itama hankalin ta ya tashi, abinka da tsakanin da da ~ mahaifi. Gani tayi ya yi mugun fadawa cikin kwana daya da wuni daya babu ci babu sha, nan — take taji Kwalla ta ciko idanunta, tayi sauri ta kau da kai don kadaya gata tausaya masa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Da sauri ta juya zaya bar gurin, ya yi saurin riKo hannunta, duk da ba shi da Kwarin jiki sosai amma ya yi KoKari ya yi mata wani rikon tsauri. .
Cikin kuka ya ce, “Mom me yasa ba kya tausaya min? Ki taimaka min na fita cikin Kuncin da nake ciki duk da kuwa nasan ba zan taba samun wani farin ciki da sukun ba tun dana riga na yiwa rayuwar Aziza na illa, na san haka zan Kare rayuwa ta.
Mom da kina bani kulawa duk da na san ban cancanta a bani ita ba amma Momi idan kika duba nayi nadama, kuma a shirye nake da a
zartar min da kowane irin hukunci ko da na kisa ne domin bai kamata a barni haka ba. Mom sai yanzu na gane cewa ke kadai ‘ .. ki ke Kaunata ba Daddy ba, domin kece ki keso a hukunta ni shi baya so. Ganin halin da Aziza take ciki a (hospital) yasa na Kara tsanar kaina da fitar da ran idan ta mutu a haka ba zan taba samun rahamar Allah ba, domin ban ce ta yafe min ba. Don haka na yanke shawarar ko da Daddy zai kashe ni sai na tona asirin kaina don na samu nutsuwa. Don haka Mom ki yafe min, ki kuma ci gaba da nemar min gafara gurin allah, wallahi na tuba, kuma nayi nadama, ba zan sake ba”. Hawaye ne sosai suka gangaro a fuskarta, ~ ta sa hannu ta goge da dayan hannun, ta juyo ta kalli Hameed ta Kara tausaya masa, ta ce.“Hameed, me yasaka yiwa ‘yar uwarka haka?™ Shima cikin kuka ya ce, “Momee wallahi ‘ sharrin zuciya ne da shaidan, amma don Allah ki yafe min ko don wannan hawayen da na sa ki, (Please) mom na san ina cikin fushin Ubangiji”. Www.bankinhausanovels.com.ng
bawa Aziza sauki. Sai dai ba zamu so ta tuno bin da ya faru a baya ba, don gudun tonuwar asirin mu. Hameed, kada kaji ina fadar haka kana ganin kama ina farin ciki da abin da ya faru da ” Azizan ka, ko kadan wallahi duk loakcin da na zauna na tuno da halin da take ciki sai na ji ba * dadi, amma idan na tuno kai ne ka aikata hakan . Sai gwiwoyi na suyi sanyi, domin babu abin da. zan iya yi akai Hada idanu. suka yi da mahaifiyar sa, ya ga bacin rai sosai a tare da ita, har ya yi niyyar _ yin magana ta sa hannu ta dakatar da shi ta ce. Ban yarda da cewa kana tausayin ‘yar dan _” uwanka ba dandai har da gaske tausayin kake yi me yasa ba zaka tona asirin wanda ya yi laifin ba? Don kawai son zuciya irin taka da rashin son zumuncin Allah, kasan abin yana KarKashin ka amma ka Ki ka bayyana. — SO Ni dai zan dibar muku lokaci daga kai har _ shi, matuKar ba ku bayyana ba to ni zan bayyana ko kuma shi Allah da Kansa Ya bata lafiya ta fada da kanta tunda komai a Hannun sa yake Zai iya yin komai cikin KanKanin lokaci”. . Www.bankinhausanovels.com.ng
Hameed, kana da wannan tunanin da kuma tsoron Ubangijin ka amma har kaje ka yi wannan mugun aikin? Hameed ba zan yi maka baki ba ko wani mugun kalami, jin furucin ka yau yasa na yafe maka amma dai dole ka bayyanawa iyayen ka ko me zai faru ya faru. Idan ka ci gaba da Istigfari da KasKantar da kai Allah Zai iya yafe maka naka laifin kai da shi, domin Yana son ganin bawan sa mai nuna nadama da neman tuba na gaskiya. Amma ba Zai iya yafe maka hakKin Aziza ba, wannan sai kai da ita”.
Ji ya yi wani sanyi da farin ciki sun tsirga masa, ya yi sauri ya rungume mahaifiyar sa yana kuka yana cewa ya gode, kuma ta saka ido zai yi mata abin da take so. A wannan halin Alh. Jafar ya shigo cikin gidan, yana ganin hameed wani farin ciki mara misaltuwa ya ratsa masa zuciya, ya ji kamar an * masa albishir da gidan aljannah. Da sauri ya zo ya rungume shi, ya ce.
“Haba, me yasa ka cika taurin kai ne? Ne ce ka cire damuwa insha Allah komai zai zo cikin sauqi, mu ci gaba da yin addu’a
Allah Ya Cikin zafin rai ya ce, “Asiya na fuskanta yanzu duk abin da ya zo bakin ki kina rufe ido ki fada min ko? To kije ki fadawa duk wanda za ki fadawa.
Ciwo na Allah ne, idan Allah Baiga damar dawo mata da tunaninta ba babu mai iyawa, domin da asirin Hameed ya tonu na gwarmace Aziza taji sauki ba tare da tunaninta ya dawo ba, domin idan Allah ya bata lafiya a shirye nake ni da Hameed mu shiga cikin rayuwar ta mu kawo mata dukkan farin ciki a rayuwar ta, domin shi ne zai aure ta don ya wanke dukkan laifin da ya yi mata”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Cikin mamaki ta ce, “Jafar kai ne da kanka kake irin wannan maganar kamar ta yara don kawai son danka ya rufe.maka idanu? To lallai ka ke yi da gaske, domin wata rana kana tare da daukar jin kunya”.
Tana gama fadin haka ta juya ta bar su a gurin.
Bayan ya bita da kallo ta wuce, sannan ya dawo da hankalin sa kan Hameed, ya dube shi sOsai ya ga yadda ya koma cikin kwana daya da. wuni daya, domin dazun bai gama lura da —
yanayin sa ba, ganinsa ya rude yasa murna ta ‘ mantar da shi.
Hameed, kaga kuwa yadda ka koma cikin kwana daya kawai? Haba my boy, me yasa ka cika kafiya da taurin kai? Me yasa ba ka tausaya min ne? Kaga halin da nake ciki tunda abin nan ya faru har yanzu nima bana cikin walwala domin na san kaima ba ka ciki. Hameed ka saki ranka don Allah ka dawo cikin walwalar ka kamar yadda kake can da”.
Murmushi Hameed ya yi na takaici wanda daga ka gani ka san ba cikin dadi aka yi shi ba, anyi ne kawai, ya ce. “Daddy walwala ta fa ka ce? Daddy tuni na manta wannan cikin rayuwa ta, Daddy na san
tunda na taso kake bani farin ciki dai-dai da rana daya ba ka taba bari na rasa wani-farin ciki ba indai daga gare ka ne, to (why) yanzu ka hana ni samun sa a yanzu bayan yanzu ne nake buKatar sa? Daddy tsawon kwana ki kana hana ni duk abin da nake so, ina ta bin umarnin ka don kada na bata maka wanda kai da kanka ka hana ni zuwa asibiti gurin Aziza duk da kuwa zan iya zuwa a
sace baka sani ba, amma duk nayi don kai ma na baka irin farin cikin da ka jima kana bani”.
“Hameed ban taba hana ka wani farin ciki ba har yanzu, ka fada min wanne farin ciki na hana ka samu a yanzu?” Ajiyar zucitya Hameed yayi ya ce.
Daddy farin ciki daya nake so na ga na samu, idan kayi min haka to Daddy zan san cewa kai mai son farin ciki na ne.
Ba komai nake so ba illa ka barni naje a hukunta ni, ma’ana zan je kotun Musulunci a yi min bulala domin a fitar da hakKin Allah a kaina, daga nan sai na je gurin su Abba na fada musu cewa ni ne na aikatawa Aziza wannan danyen aikin”.Www.bankinhausanovels.com.ng
Cikin huci da masifa-ya ce, “hameed baka da hankali ne? Kana son tube min rigar mutunci na a cikin ‘yan uwana bayan duk irin zafin da nake yi akan wannan faruwar al’amarin daga baya su ji cewa daga gindina abin yake me kake tunanin za su dauke ni? To kuwa indai wannan shi ne farin cikin naka to sai dai ka ce tunda nake ban taba baka shi ba,
Abu daya zan yardar maka, shi ne kaje duk inda za a fitar maka da haqqin Allah, ma’ana ayi maka bulala. Na yarda da wannan don kada ka yi tunanin bana tsoron gamuwa da Allah, amma ni dai ba zan yarda ‘yan uwana su san cewa kai ne ka aikata wannan rashin imanin ba”Shi kenan Daddy, zan yi abin da ka ce zan je a yi min bulalar”.
Runtse idanu Alh. Jafar ya yi, ya ce, “Hameed ban son kaje a taba lafiyar ka, kaje kayi ta Istigfari Allah Zai yafe maka”.
“Daddy nutsuwa nake son na samu . farko, matuKar aka yi min bulalar nan zan fi zaton samun rahama tunda Allah ne Ya fada Kansa. Na sani idan na duKufa da Istigfari Allah Ya dubi zuciya ta zai iya yafe min, agama tunda ga yadda Ya ce mu bi dole ne mu bi hakan.
Daddy a yadda nake ji.matuKar aka ce kashe ni za ayi idan na yi haka zan kubuta Allah har da cewa Aziza ta yafe min, ta yarda a kashe ni”.
“Hameed ka yi min shiru, bana son jin zancen mutuwa! Ba haka Allah Ya ce ba, saurayi da bai taba aure ba bulala dari, idan me aure ne kuma a jefe shi har sai ya mutu. Haka itama mace idan bata da aure bulala dari, idan mai aure ce a jefe ta, sai dai idan tana da ciki shi ne za a bari ta haihu ta gama shayarwa daga nan sai a jefe ta. Don haka kai ba kisa za a yi maka ba, bulala ce.
Tunda kana so kaje ni ba zan iya kai ka ba, amma bana so ka yi a garin nan domin ba zan jure ganin ka cikin jinya ba”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Cikin farin ciki mai hade da kuka ya ce, . “Daddy na gode, zan yi duk abin da ka ce, sai dai ina neman wata alfarma a gurinka, kafin wannan
Ina so muje da kai a matsayin ka na mahaifi na domin mu yi koyi da Sahabin Manzon Allah (S.A.W), Umar (R.A) da hannunsa ya kai dansa
‘aka hukunta shi, don haka nima zan yi farin ciki a ce mahaifina ne da kansa ya kai ni aka fitar da hakKin Allah akai na”
Hawaye ne suka zubo a idanun Alh. Jafar domin tausayin dansa da yaji ya kama shi, tabbas ya yarda cewa sharrin shaidan ne da rudin zuciya suka debe shi ya afka wannan ta’asar, . gashi da kansa yake neman ayi masa hukuncin da Allah Ya tanadar wa mai irin laifin sa. Saka hannu ya yi ya goge hawayen, ya ce. “Hameed naji zan kai ka da hannu na, to amma ka dan bani lokaci kadan ina wani shiryeshirye ne”. . . Murmushi ya yi ya zo ya rungume ‘ mahaifin sa yana masa godiya da ya amshi buKatar sa. Alh. Jafar ne da kansa ya je ya hado masa kayan abinci, ya saka shi a gaba yana bashi a baki kamar wani Karamin yaro, haka ya soma ci sosai domin rabon sa da cin abinci har ya manta, – sai dai ruwa kawai yake ta’ammali da shi. Haj. Asiya tana can daga nesa tana hangen irin so da Kaunar da Alh. Jafar yake nunawa dansa kamar shi kadai Allah Ya mallaka masa a duniya. Ta yi Kwafa ta bar gurin, domin tana labe duk taji abin da suka yi magana akai, ta yiwa Allah godiya tare da cewa Allah Yasa ya aikata abin da ya ce zai yi. Watannin Aziza biyu a kwance da sati biyu, sai dai muce sauKi yana gurin Allah, domin dai har kawo wannan lokacin tana cikin doguwar
suma (Coma), abin da likita dai ya fada mana shi ne tana raye dai har yanzu, kuma cikin kowane lokaci zata iya farkawa. Mu dai kawai muna jinsa ne kawai, tabbas ba don na’urorin da muke gani suna amfani a jikinta ba da sai muce ta jima da mutuwa bai son gaya mana ne. Abban ki duk ya Kare ya kasa yin komai, jinya ta mata ce amma da shi ake yi, ya daina zuwa wurin aiki sam, ya yi baki duk ya rame domin yadda yake nunawa idan Aziza ta cika wata uku bata dawo cikin hayyacin ta ba zai shirya fita da ita Kasar waje, haka likitocin suka shiga bashi haKuri akan ya dan Kara hakuri. Www.bankinhausanovels.com.ng
A lokacin babu wadda muke tausayawa kamar ki, kullum sai kin yi kuka ke dai Aunty ki Aziza za ki wajen ta, a lokacin da ki ka ganta kwance cikin na‘urori duk sai kika tsorata kike ta yin kuka wai ke a tashe ta ku tafi gida. Lokacin babu wanda bai zubar miki da hawaye ba don tausayin ki, haka dai muka ci gaba da rayuwa cikin jiran tsammani.
Da yake Allah maji roKon bawansa ne, Gagara misali, wata rana na shiga bandaki Ammin ku ta fita waje don yin rakiyar ‘yan dubiya da suka zo, Abban ku yana can masallaci _ kamar yadda ya saba yana karatun AlKur’ani. : Ina fitowa sai kawai na iske Aziza zaune kan gadon gsibiti ita kadai garau da ita sai dube_ dube take, cikin murna da doki na ce. – “Aziza na.Na fada cikin Karaji da doki, sannan na daga hannu sama na fara yiwa Allah godiya. Abin mamaki Aziza bata juyo ba bare ta . Lura da abinda nake yi, ita dai hankalin ta gaba daya yana kan Www.bankinhausanovels.com.ng robar igiyoyin da suke. jone jikinta su tabi da kallo tana mamakin yadda aka maKala matasu. Da sauri na zo gabanta na riKe hannayen ta, hawaye na zubo min na ce. “Aziza ba ki ganni-bane? Granny dinki ce – fa?” ~ Wani irin kallo na rashin’ fahimta ta bini da shi kamar tana so ta yi tunani, sai ta kasa, nan dai Allah Yataimaka tace. “Wace ke?” ‘ Murmushi nayi mai hade da kuka, na sake damKe hannuwan ta nace.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG