AUREN KWANGILA BOOK 3 CHAPTER 8 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

AUREN KWANGILA BOOK 3 CHAPTER 8 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

                   Www.bankinhausanovels.com.ng 


tattare zani suka fara hawa dutsen nan kamar kadangaru daya na zamowa daya na tallafo ta har suka iso bakin wani dogon kogo na rarakakken dutse, Mu’azatu takalmi, dankwali da mayafi duk a hannu saboda wahala, har hawaye ta ke yi. Zuwanta wannan wajen na biyu kenan bayan Regina ta ce in ka zo sau daya ba ka kara dawowa bukatarka ta gama biya. Www.bankinhausanovels.com.ng
Haduwarta ta farko da Abdul’azeez Dakata a ofishin mahaifinta ta fara sonsa kamar ta ciro rai ta ba shi. Ba irin kyautata masa da ba ta yi ba don ya so ta, bata taba tunanin neman soyayyarsa ta wata hanya bayan kyautatawa ba. Amma sai ya bada mata kasa a ido, ta hanyar nuna mata shi babu wannan a gabansa, yana da abin da ya kawo shi ‘Law School’ ta yi hakuri ya ci gaba da bata

girman da yake ba ta na kasancewar ta ‘yar malaminsa. Duk wasu dabarunta sun kare, ta kasa canza wannan murdadden lauyan data fahimci ba abinda ke canza masa wani irin ra’ayin rikau irin nasa. Regina abokiyar karatunta ce wadda ta fito daga jihar Benue. Hira ta yi hira a tsakaninsu irin ta shaqiqan aminairannan sai ta ke gaya mata yadda ta samu kanta a kan Abdul’azeez da raddin sa gare ta, da kuma matsanancin halin data ke ciki akan hakan. Ba da wata manufa ta fadawa

Regina ba sai don ta rage radadin dake ranta, irin wanda dan adam ke samu idan ya raba damuwarsa da wani nasa. Wani sakaran kallo Regina ta yi mata ta ce. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ke wa ya gaya miki yanzu ana tarar namiji haka zikau, a ce ana sonsa ba tare da an tabbatar an kama shi a hannu ba?”
Mu’ azatu ta ce, ita ba za ta iya biye-biyen malamai ba, saboda in aka fara ba’a dainawa, ta ga Mamanta na yi amma ita ta hane ta, ta sha ce da ita“ adashi ne wanda ba’a dauka ”. Regina ta ce, “Ina da inda zan kai ki a yi miki aiki a kansa, in aka je sau daya babu komawa, kuma aikinsa na har kabari ne (har wanda aka yi wa ya mutu). Idan kuma na ce ki kara komawa kada ki kara kallon inda nake”. (Mafarin zuwan Mu’azatu Rufa’i wajen boka Chiwonzhu a Kaduna-South, kauyen Kufana). Www.bankinhausanovels.com.ng
A kan idonsu ya kamo tunkiya ya kalli kudu ya farke mata ciki, zuciyar tunkiyar ya tsigo tana yararin jini ya dora ta a kan wani kasko ya zuba hayaki a kai ta hau tiriri har sai da jinin jikinta ya
kone. Bata zuciyar ya yi a tafin hannunta ya ce ta gutsire ta sau goma sha biyu, duk gutsira daya ta ambaci sunansa har ta cinye. Duk kyankyamin da Mu’azatu ke ji haka ta cinye danyar zuciyar tunkiyar nan. Ya hada ta da wani garin magani ya ce a ciyar da shi a abinci tsayin kwana talatin ba tsallakewa. Wanda ta nufa da wannan asiri ba zai taba samun nutsuwa da kwanciyar hankali ba har sai ya aure ta. Zai iya ja da kowa a kanta, in yace kowa yana nufin kowa_har sai ya aure ta.
Wannan shi ne makasudin Mu’ azatu na fara ciyar da Abdul’azeez abincin gidansu, daidai da rana daya ba ta taba kuskurewa ba, har zuwa cikar wa’adin da boka ya debar mata.
Dawowarsu a yau tsibirin boka Chiwonzhu ga su a gabansa, tun shigowarsu yake dawurwura a kansu yana zagaye su. Yana bugun kan Mu’azatu da wani gashi yana wasu maganganu da ba sa fahinta kafin ya yi zaman ‘yan bori a gabansu. Idan ya yi hakan, yana jira ka fadi abin da ya kawo ka ne, ya gama duba matsalolinka.
“Ya daina damuwa da ni, ya ki zuwa mu yi aure, ya daina kirana, ya daina amsa nawa kiran. Nema yake ya fasa aurena daga dukkan alamu”. Kakansa ya lalata komai yarinya!”. Gabadaya suka dago a firgice suka dube shi. “Wani farin dattijo mai farin gemanya, mai tarin shekaru rututu. Yana can Arewacin Najeriya yana karya duk wani sammu da ke jikinsu ba tare da su kansu sun sani ba!!!’’Idanun Mu’azatu suka firfito cikin tashin hanKali. “Yanzu ba wani taimako da za ka yi min ya
aure ni?” Ta fada cikin son kecewa da kuka.
“Ko mun yi Zai sake lalatawa, amma akwai aiki guda daya wanda ba yadda zai yi da shi sai dai daga gare ki amincewar take”.Www.bankinhausanovels.com.ng
“Fadi ko mene ne wallahi zan iya in dai ba zan rasa Abdul’ azeez ba’. Mu’ azatu ta fada tana kuka tare da zubewa a gaban Chiwonzhu.
“Zai iya zama mai tsauri a gare ki, amma ina tabbatar miki kamar yankar wuka yake. Kuma ba a jikin jikansa zai zauna ba balle ya karya, a jikinki zai zauna har gaban abada.In ba ni ba babu mai iya karya shi’. Rokonsa Mu’ azatu ta shiga yi ya yi mata wannan aikin, ko nawa ne za ta biya. Ita dai burinta ta auri Abdul’ azeez ko ta halin kaka. Chiwonzhu ya ce, “Aikin ba ya bukatar ko sisinki. Magani ne zan shafa a jikina in sadu da ke, idan ba a yi auren nan cikin sati biyu ba, kada ki kara dawowa inda nake”’
A hankali Mu’azatu ta soma ja da baya, Regina ta soma harararta, “Me ye a ciki? Ba kanki aka soma ba, na kwanta da shi ya fi sau goma, me ya ragu a jikina?” Girgiza kai Mu’azatu ta shiga yi tana kara ja da baya, “ I’m a virgin Regina, al’adarshi ba daya ta ke da tamu ba. Idan na je masa babu budurci ba zan taba yin daraja a idonsa ba…”.
“Kuma aka ce miki haka za mu kyale shi bayan an yi auren?” Kamar ta ce da ita, “An zo gurin, maganar Mamana ta tabbata; in aka fara binsu ba za a daina ba. Nikuma ba zan iya jura ba, ko zuwa wajen nan kadai bala’i ne balle hada jiki da wannan kazamin mutumin”. Shi dai boka wasu harkokinsa ya shiga yi a cikin kogon ya manta da su ita da kawarta suna ta jayayya. Da suka fara isarsa ya ce, idan ba ta amince ba su tattara su bar gabansa. Mu’azatu ta wawuri jakarta ta mike kan su ce me ye wannan har ta kai kofar kogon. Chiwonzhu ya dube ta cikin takaici, “Ki sa a ranki ke da wannan mutumin har abada! Ba zai taba aurenki ba. Kina iya gwada wani bayan ni, don ki tabbatar da abin da na fada’”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Da kuka wiwi Mu’azatu ta fito daga kogon Chiwonzhu, ta soma kokarin saukowa daga dutsen, ga rashin nutsuwa ga tashin hankalin abin da ya fada. Santsin dutsen da ta ke kokarin bi a hankali ya kwashi sassalkar kafarta ta yo suuuufa tun daga sama har kasa ta fadi a kan kwankwasonta.
Wata azababbiyar kara ta saki Regina na kallonta daga saman dutsen ta yi tsaki ta ci gaba da saukowa a hankali har ta sauko tsaf, ta kama ta ta mikar tana zuba ihu a haka suka karasa motarsu. Regina ta watsa ta kujerar baya ta tuka motar suka tafi.
Kwananta uku tana jinyar Mu’azatu wadda ko zama ba ta iya yi sai kwanciya, amma Regina don mugunta ta ki kai ta asibiti. Kwana ta ke kuka tana gaya mata pelvic-girdle dinta (kashin kugu) ya karye. Da ta gaji ta tattara ta ta sa a jirgin Lagos ta koma gida.
A wheel-chair ma’aikatan jirgin suka turo
Mu’ azatu zuwa reception . Nan ta fiddo waya ta kira Babanta ya turo a dauke ta tana filin jirgi ta karye. Da kansa ya zo cikin tashin hankali har da Mamanta suka kwashe ta sai wani babban asibitin kashi. Likitoci suka duba ta sosai, nan suka gayawa Babanta ta samu tsagewar kashi a kashin kugunta za a yi mata aiki. Ya yi addu’a kada abin ya taba lakarta (spine). Hankalin Attorney General ya yi mummunan tashi, Mamanta sai kuka. Bayan an yi aikin an fiddo ta Babanta da Mamanta suka sanya ta a gaba ta gaya musu inda ta je ba da saninsu ba kwana hudu ta karye. Tana kuka cikin zafin ciwo ta gaya musu tun zuwansu na farko wajen Chiwonzhu da Regina a kan Abdul’azeez har kawo na wannan karon da abin da ya rikitata har ta sulmiyo. Ran Attorney ya yi mummunan baci, idanunsa ya yi jazir ya ce. “Wato duk tsawon lokacin nan ‘charming’ din Www.bankinhausanovels.com.ng Abdul’azeez ki ka yi don ya so ki? Na raine ki kan ki zamo mai son kanki ki zama heartless Mu’ azatu? Ina ki ka kai darajar da Allah ya yi miki ta diya mace? Shin daga kan Abdul’azeez aka ce maza sun kare a duniya? Mene ne farin cikinki na zama da wanda ki ka san ba don Allah yake sonki ba? Kina tsammanin akwai abin da ba kararre ba a wannan duniyar? Mu’azatu kin san azabar da ki ka gana wa zuciyarsa tsayin wannan lokacin? Kin san ya ya zuciyar tunkiya ta ke? Haka ake nufin ki maida zuciyar mijin aurenki. To ina batun samun aljannan kuma tunda kin maida zuciyarsa ta tunkiya? Yau da kin ba wa bokan nan kanki da na yi tirr da haihuwar ki. Afuwar da zan miki kenan tunda ki ka tsira da wannan hankalin. Kin san halin da ki ka jefa zu
ciyarsa tsayin wannan lokacin Mu’ azatu?
Gaskiya na ga iyayensa na yin baya-baya da maganar aurenki, ashe su suka san abin da suke gani daga gare shi a kanki. To bari ki ji in gaya miki aure zan yi miki karshen watan nan. Ba irin maneman da Allah bai baki ba kina wulakanta su kike tsaye nacin wanda baya son ki. Jinina yafi karfin irin wannan auren. Ko a waya ki ka kara kiran Abdul’azeez ban yafe miki ba duniya da lahira!”
Kuka Mu’azatu ta sa, “Daddy kada ka yi min haka, wallahi tun kafin hakan yana sona, tun kafin in je Kadunan muke tare”.
Mamanta ta kai hannu ta buge bakinta. “Ban ce kada ki taba bin bokaye ba a rayuwarki? Ban gaya miki adashin da babu dauka ba ne? Ban gaya miki in aka fara ba’a dainawa ba? Kin biyewa arnan kawayenki kafirai wadanda su basu san Allah shi ke sawa Yake hanawa ba? To wallahi ni ma na fada ko shi ya saura namiji a duniya ba za ki aure shi ba! Abin da ba ki sani ba ma iyayensa sun dade da yi masa aure, jiya wata kawar Mamansa ta gaya min mun hadu a wajen conference , ke ya mayar sakarai, shashasha”. Kuka Mu’azatu ke yi har ta ji babu dadi,
“Mummy na sani fa! Ya yi min alkawarin zai sake ta in na gama ‘law-school’ mu yi aure”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ga mamakinta daga uwar har uban sai suka bushe da dariya, “ So he is playing with your senses duk da asirin naki? Ya dauke ki mai kwakwalwar ‘yar tsana. Tunda ki ke kin taba jin wannan almarar?” In ji Maman. Attorney ficewa ya yi don takaici bai kara dawowa asibitin ba har bayan kwana biyu. Shi
kadai ya san me yake shirya mata. Akwai wani ‘Grand Khadi’ abokinsa tun na karatu, dansa Barrister Muntada ya dade yana son Mu’ azatu ba ta ma sani ba. Yana aiki a ‘court of appeal’ ta jihar Lagos. Mahaifinsa ya biyo ta kan Daddynta yana nema wa dan nasa izinin a bashi dama ya fara nemanta. Attorney ya ce ya dakata saboda akwai maganar wani student dinsa a yanzu a hannunsu, amma bai san me Allah zai zaba mata ba. A lokacin ya fadi hakan ne ganin tsohon Ambassador Hamza na yin baya-baya da zancen. To a ranar da ya bar asibitin bai kwanta ba sai da ya nemi Grand Khadi Akilu Lawal ya ce ya baiwa Muntada Mu’azatu, ko yaushe suka shirya su fito. Alkalan sun shirya komai a tsakaninsu ba tare da Attorney ya kara bi ta kan Mu’azatu ba a wannan lokacin, don ya fara tunanin bayan buguwar tata a kwankwaso kanta ma ya bugu ta fara fita daga seti a kan Abdul’azeez. Wannan kenan.

********

Kwanan Hajiya maryam biyar a asibitin ‘DIFF’ sannan ne aka samu jikinta ya sauka taji sauki sosai likita ya ba su sallama tare da ka’idojinsa cikin buhu, hatta abincinta ya canza shi ya mayar da shi zuwa na masu lalurar hawan jini. Duka jama’ar gidan Dr. Ya hana su zuwa tun zuwansu na farko ya ce hutu ta ke bukata, don ranar da suka zo sai da jininta ya kara hawa. Hafsat ce kawai tare da ita, ita ma ba wata hira suke ba don mafiya yawan lokuta ma tana barci. Www.bankinhausanovels.com.ng
Shi kadai ya san cikin yanayin da ya kwana a wannan rana, zai iya rantsuwa cewa idanunsa ba su runtsa ba. Yana da tabbacin Mammah za ta yi fushi duk ranar da ya karar da auren kwangilarsa amma bai yi zaton al’amarin zai yi girman da har zai taba lafiyarta ba. Their Mum is always healthy and vibrant, always busy taking care of them and their Dad, yau bakin cikinsa ya jaza mata cuta ya kwantar da ita a kan kafafunta. Ba ta sani ba, ya fi ta shiga damuwar abin da ya aikata. Ya runtse ido ya aikata ne don ya tserar da kansa daga tozarta alkawari.
“Zan yi repenting Mammah… Ki ba ni dama! One last chance!” Ya fada a fili ya fi sau shurin masaki.
Washegari har ofishin Ahmad ya tadda shi, kallo daya ESQ Ahmad Kutama ya yi masa ya tabbatar al’amarin bai tafi yadda suka so ba.
“Be a man”. Abin da ya fara ce da shi kenan.
“Komai ya cabe Ahmad,yadda bazan iya gyara shi ba. Mammah ta ji. She’s now on admission . Na tabbata ni ne sanadi’”’.
Ga mamakin Ahmad sai ga hawaye sun sauko a fuskar Abdul’azeez shar-shar! Hannunsa Abdul’azeez ya kama ya ce, “ What will I do now? In Mu’azatu ce na fasa aurenta, ba ni da wani sauran buri a kanta. I need my wife back, and my Mum’s forgiveness”.
Ahmad ya jinjina kai kafin ya ce “Daga yau ka daina jayayya da iyaye, ka kasance mai godiya da abin da Allah ya baka ko baka sonshi komai kankantarsa, ka daina zurfafawa a soyayya ko kiyayya, komai mai iya canzawa ne a duniya
banda mulkin Allah da ikonSa a kanmu. Ba duka abin da muka kallafawa rai muna so bane alkhairi a garemu. Wasu alkahairan na rayuwar mu a lullube suke bamu san dasu ba amma Ubangijin da ya halicce mu ya yi mana tanadinsu in munyi hakuri mun bi iyayenmu zasu tadda mu har inda muke. Mu daina cewa lallai sai mun mallaki abinda muke so ko ta halin kaka. Mu roki Allah zabinsa ba zabin zuciyarmu ba. Abdul’azeez ina mai fada maka da babbar murya ka yi kuskure! Ba Mamanka kawai ka sabawa ba har da Ubangijin da ya halicce ka. Aure ba abin wasa ba ne, umarni ne na Ubangiji. Amma ka yi shi ba da tsarkakkiyar niyya ba, duk auren da aka yi shi babu ikhlasi kuma aka kayyade masa wa’adi bai inganta ba a shari’ah. Bana tunanin ko ka rufe zancen nan ka karbe takardarka daga hannun Hafsat ka ci gaba da zama da ita auren ku ya gyaru duk da dai ni ba malami bane. Ka kwashe fiyeda shekara ba ka sauke hakkin aure da Allah ya rataya a wuyanka ba, wanda shi ne gundarin auren. Wasu malaman ma sun ce watanni uku babu saduwa tsakanin ma’ aurata kuma babu hujja ta rashin lafiya ko tafiya, auren ya lalace. Www.bankinhausanovels.com.ng
Don haka sanin da iyayenku suka yi ina ganin shi ne daidai. Su zasu nemi yadda zasu gyara muku auren idan sun huce. Ka roki Allah gafarar wannan zunubin da tuba nasuuhan. In aka ce tuba nasuuhan wato a yi shi da niyyar ba za a sake
maimaita laifin ba. A yanzu kam, ai kada ma ka doshe su da bukatar su maida maka Hafsat, hakan zai zamo
tamkar zubawa wuta fetur ne. Suna kan tsinin fushinsu, kuskure ne ka riga ka tafka, sun maka zabin da suke ganin shi ne daidai da rayuwarka da ra’ayin su ka ce ba su iya ba, kai ne ka iya. Saboda sun tsaya maka kayi karatun zamani har kana ganin ka fisu sanin zamanin. Sai ka jure duk wani punishment da za ka fuskanta daga gare su, ka kwantar da kai kawai ka amshi laifinka da hannu bibbiyu, duk wani bayani da zaka yi musu bazai gamsar dasu ba a yanzu, amma ga wata shawara… ka nemi hadin kan matarka’’.
A sanyaye Abdul’azeez ya dago, cikin ransa yarda yake da duk kalaman da ke fita bakin Ahmad, ya ce. “Kutama, Suhaana ta yanke duk wani communication gap da ke tsakaninmu. Daga ranar da muka rabu ba ta kara amfani da wayarta ba. Ina jin kunya in je gidanmu in ce zan ganta, ban da nan din kuma ban san inda zan ganta ba, ba ta zuwa ko’ina Ahmad, ko da makaranta”’.
Dariya Ahmad ya yiya ce “Haba Abdul’ azeez kaman ba namiji ba? Kada ka bada maza, mazan ma mafiya hikima da sarrafa fasaha (lauyoyi). Kai za ka nemo hanyoyin communicating da ita. Kada ka manta weakness din mata daya ne ( soyayyah ). Balle kai dinnan ( brainlliant and handsome hunk Abdul’azeez) wanda na tabbata Hafsat ta dade da macewa akan ka. Ka fi Romeo iya soyayyah, ka fi (William Shakespeare) iya sarrafa harshe wallahi za ka sha mamaki. Sai da ya sa Abdul’azeez murmushin da bai shirya ba amma bai ce masa komai ba. Damuwar dake cin sa a zuci ta hana shi bawa zancen nasa muhimmanci.

********

Tunda suka dawo gida daga asibiti Hafsa ke hidima da Mammah, ta hana ta yin komai na gidan, girki ita ke yi, nasu daban na Mammah daban. Baba Azumi na taya ta da gyaran gida da tsabtarsa, wanke-wanke da shara. Ga Isma’el na debe mata kewa da hirarrakin budurwarsa da yake matukar so Wasila, in ya je zance ya dawo duk hirar da aka yi a kunnenta za ta kare. Duk da ba’a gama hirar ba tareda sunyi fada ba saboda wasan kanin miji irin na Isma’el mai ban takaici. Su ba yara ba ne daga shi har Usman, ganinta a gida da halin da Mammah ke ciki lokacin da suka dawo ya fahimtar da su abin da ya faru ba tare da kowa ya zaunar da su ya gaya musu ba. A zuciyar Isma’el bai yi mamaki ba in ya tuno abin da ya faru tsakaninsa da Yayan nasa kafin auren. Ya tuno Www.bankinhausanovels.com.ng zuwansu na farko gidan nasu, da yadda aka yi kan hoton budurwar falo wadda ya tabbata budurwar Abdul’azeez ce don ya tuna inda ya ganta bai fada bane a lokacin saboda Mammah. Ranar ‘ call tothe bar ceremoney’ ne na Yayan nasu. Ita ce ta kawo musu abinci. Ba tun yau ba ya san Yayansa is very selective and ideal a kan macen aure. Amma bai ga inda wadannan halaye suka yi proving kansu a gare shi ba in dai a Mu’ azatu ya kare. Ko ta ina ba su daidaita ba, tarbiyyah, al’adu, dabi’u da halayya. Daga ganinta girman kudu ce, kuma sakakka, ba kunya ba kamun kai, ba al’adun Malam Bahaushe ko daya a tare da ita. Da ya kalle ta sosai ma sai ya ga kamar ba bahaushiya bace. Suhaanah kuwa ai matar manya ce ko shi ba zai gaya mata komai ba banda zurfin ilmi wanda in yayi hakuri nata na tafe yanzu take nemansa. Sun samu labarin ganin dan
gin Suhaanah da aka yi kafin dawowarsu. An ce fadan da babu ruwanka dadin kallo gare shi. A kwayar idon Yayansa ya ga al’amari mai girma a kan Suhaanah ranar da ya sanya ta gaba da tsokana a gidansu. Don haka ya san ko ma mene ne wannan ba shi ne karshen auren Yaya Azeez da Hafsat-Suhaanah ba. Shi Usman dama dan ba ruwana ne, bai kawo komai a ransa ba kuma bai tambaya ba, shi ya ma dauka zaman da ta ke yi a gidan din jinyar Mammah ta ke yi.
Yau kwanansu biyar da dawowa daga asibiti Hajiya Maryam ta dan fara sakin ranta, har suna hira da ita. A daren ranar ta shiga ta tadda Hafsatun a dakinta tana shirin bacci. Irin zaman da ta yi a Www.bankinhausanovels.com.ng gefen gadonta da yanayin fuskarta ya tabbatar mata muhimmiyar magana ta kawo ta. Barin komai ta yi ta zo ta zauna a gefen kafafunta. Hajiya Maryam ta daga ido ta dube ta, kullum kara ramewa ta ke a tsaye kamar kudin guzuri. Ta juyar da kai cikin takaici ta ce, “Zuwa na yi mu yi magana Addah”Kanta ta sunkuyar tana sauraronta. Kina da iddarshi a kanki?” Dagowa ta yi ta dubi Mammah cikin rashin fahimtar Hausarta, har gobe Hausa mai tsauri na yi wa Hafsat wuyar ganewa. Hajiya Maryam ta fahimce ta sai ta maida bayanin nata gwari-gwari. “Na ce ya taba kwanciya da ke?”

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
Kasa ta kara yi da kanta kamar tace da kasar ta hadiyeta ta huta, kunya, daburcewa da kidimewa babu wanda babuwannan lokacin a tareda ita. How could she say to his mother something like that (ta ya ya za ta iya fadawa mahaifiyarsa wani abu kamar wannan)? Da za ta iya da ta ce da ita,

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *