SADAUKIN SADAUKAI CHAPTER 2 by Nura Muhammad
Www.bankinhausanovels.com.ng
Yayinda suka qaraso se aljani DURFAN yalura da gimbiya SAFRAH data doki kan maridi yake mutuwa. nanfa shima yabude shafin sabuwar barna. da maridan suka lura da wannan saisuka fara tsalle suna dirowa akan aljanun suna latsesu.
ita kuwa gimbiya kashesu kawai takeyi ba sassauci. takashe kusan 200. saida suka wuni sunayi yaqi sannan sukaci galaba akan maridan. sauran maridan duk suka gudu suna ihu suka 6oye dikda yawansu baiwuce kimanin 26 ba.
Nanfa saisuka cigabada tafiya. kusan sa’a biyar sannan suka isa bakin baqin daji nabiyu inda komai nacikinsa bakine harta bishiyoyin. saisuka lura sauran aljanun basu wuce guda 130 ba sakamakon sauran duksun mutu awajan maridan nan.
Aljani DURFAN ne yace mutsaya anan domin muhuta domin damunshiga nan xamu tararda aljanu wa’inda baku ta6a ganin irinsuba, su ake kirada “jinnul uyum” sunkasance bakake kuma munanan aljanu, zamu zauna anan yake shugabata sai gobe da maraice mushiga domin ba’a shiga da rana.
Haka suka Yanke shawarar kwana ana kafin washe gari sucigaba da tafiya.
A6angaren sarki DAWWAM da boka ‘balbalin bala’i’ kuwa da sarki yakoma sai bokan yake sanar dashi cewa yanxu yakamata yayi saurin xuwa DARUL AHBAB cikin BABUL AHBAB yaje yadauko TAKOBIN MUTUWA domin yanxu gimbiya SAFRAH qarfin tsafinta yaqaru yafi nashi domin taje inda bawani aljanindayata6a zuwa yadawo darai.
saiya dauko wata takarda medaukeda hatumin hanya yabashi sannan yagayamai wasu dajika uku daxasu wuce kafin sukai DARUL AHBAB. dajin farko dajin wasu gagaruman macixaine.
na2 dajin wani katon dodone wato DODO WASWAS,
daji na uku dajin wani Gawurtaccen zaki ne wanda girmansa yakai na sadaukan aljanunsa 5.
cikin tsananin mamaki yacemai yanxu yarka takusa cimma aljani MARKAHUL NAR. Toyakamata kuyi sauri domin wannan aljanin yanada matukar sauri da zafin nama fiyeda dukkanin wani aljani aduniyarnan awannan zamanin.
alokacin da boka balbalinbala’i yagama fadin haka saiyayi shuru nayan daqiqu wanda yasa sarki DAWWAM Yadaka masa tsawa wanda yajawo qasa tai girgiza. cikin tsananin kaduwa da razana boka balbalinbala’i yadago kai yace ya shugabana kasani koka mulki takobin MUTUWA to sadauki SHAHYAT zema wahalar kashewa domin akwai wani hatimi ahannunsa wanda duk inda yafiskanta atake wajen yake qonewa. kasani takobin baxaiyi tasiri ajikinsaba sai kaje kanemo wata KIBIYA wadda kecan kulle acikin taskar KIBRIYAN wadda ita wannan taskar tana qasan kogin nil.
saiya dauko wata sandar tsafi ja~ja~jur yabawa sarki DAWWAM sannan yacemai kasani wannan sandar xata zama haske gareka alokacin daka shiga duhu kushirya kutafi.
nantake aljanun sukayi sahu kaikace yaqin duniya zasu. cikin salo irin na hatsabibancin sarki DAWWAM saiya tsaya agabansu. nantake saiwani bakin hayaqi yabayyana yaxagayesu saisuka bace kamar bawanda yata6a wanxuwa awajan Battt.
ABANGAREN GIMBIYA SAFRAH KUWA.
itakuwa gimbiya SAFRAH da aljani Durfan sunyanke hukuncin yada xango suhuta domin tinkarar bakin dajin aljanun dayake gabansu.
dasuka xaunane aljani DURFAN yalura dawata daftareriyar yanka a fiffikensa wadda taja harya tsage. ahaka aka dimkemai yasa magani itama gimbiya SAFRAH akwai qananun yanka ajikinta sukuwa sauran aljanun kowannensu yagalabaita.
saida sukai kwana2 suna magani sannan suka warke sukayi yunqurin shiga baqin dajin domin tinkarar bakaken dodannun aljanin dake ciki kimanin dubu hudu, wa’inda aka ajiye domin gadin kejin da aka ajiye aljanin markahulnar….
Abangaren sarki DAWWAM kuwa, tunise tsala gudu sukeyi domin xuwa DARUL AHBAB. Can daga nesa saisukaga wani daji wanda tsayin bishiyunsa hargajimare suna ta6owa. saisuka tsaya domin sun tabbatar nanne daji macizan nan da boka ‘balbalin bala’i’ yagaya musu. saisuka sauka sannan yayi siddabasunsa saiga wata shirgegiyar tsuntsuwa tasauko wadda sbd tsananin firgita ga aljanun saida suka tarwatse domin girmanta kokanta ba’agani se kadankadan.
tana sauka tayi girgiza wadda seda guguwa me qarfi tatashi.
cikin wata murya mara dadin sauraro me matuqar razanarwa tsuntsuwarnan tace ‘amsawarka ya shugabana’ sarki DAWWAM yace yakai bawana kasani cewa zamu shiga cikin dajinnanne na macizai, to inada bukatar katsaya kacece mutanena karinka dauke macixannan kana kaiwa yan uwanka harsubiyoka sutaimakemu.
cikin fargaba tsuntsunnan yaja da baya amma SARKI DAWWAM yadakamai tsawa wadda saida qasa tayi girgiza. sannan tsuntsun yadurqusa qasa yace ya shugabana kasani banida ikon shiga dajinnan nikadai saidai muje garinmu dakai mu roqi yan uwana suxo sutaimakemu. sarki DAWWAM yakamuda mamakin dajinnan saboda har babban bayinsa nabiyu daga mayaqansa wanda ke iya tada gari shikadai amma.yakasa shiga.
saiyacewa tsuntsun to daukemu muje. sarki yasa manyan dakarunsa 50 tare dashi sukahau bayan tsuntsun sannan tsuntsun yayi wata kururuwa yadaga fiffike farat yalulaqa sama kamar bedau komai abayansaba ya6ace 6at acikin sararin samaniya.
Alokacin da tsuntsun yakada fiffike yatashi duksauran aljanun naqasa saida suka fadi domin tsananin qarfin iskar.
tsuntsun yana gudune cikin wani nau’in axababbe kuma sihirtaccen gudu domin adaqiqa daya yakanyi tafiyar shekara. cikin daqiqa 100 segasu acikin wani babban birni wanda basu ta6a gani irinsaba naban al’ajabi {koda ni kaina duk yawan duniyar danasha amma bantaba ganin irinsaba} da isarsu se afadar sarki inda sarkin tsuntsayen yake.
ABANGAREN GIMBIYA SAFRAH KUWA.
sunmiqe kenan zasunufi dajin baqaren aljanu saisukaji guguwa abayansu. suna waigawa cikin mamaki saiga wani shirgegen aljani mematuqar tsoratarwa. bakowa baneshi face BOKA KIRYAN. duka sauran aljanun saisuka zube aqasa sunamai gaisuwa. ita kuwa SAFRAH tana tsaye seboka KIRYAN dakansa yadurqusa yaimata gaisuwa sannan tadakamai tsawa tace ‘meya kawoka nan bayan munyi dakai saimun dauko aljani MARKAHULNAR sannan zamu dawo gareka?’ cikin biyayya BOKA KIRYAN yaqara durkusawa sannan yace “yake shugabata kisani cewa naxonanne bada komaiba saidaidan insaku ahanya domin dajinnan yafi dajin baya nasifu sau dubu.
kisani dukduniya ayanxu ba aljanun dasukakai wa’innan bakaken aljanun juriya darashin imani. kisani muddin kuka shiga ahaka to mutuwa xata bakunceku. gimbiya SAFRAH tadakawa boka KIRYAN tsawa domin taga yana shirin sagarmata dagwiwa.
nanfatacemai karka qara ambatarmin rashin nasara domin inka kara sainasaka akurkukun shardas. cikin firgita datashin hankali BOKA KIRYAN yayi wata qara domin yasan cewa bawanda akesawa akurkukum shardas saiwanda aka yankemai hukuncin kisa domin ayanxu haka iyayensa naciki. sai BOKA KIRYAN yaduqusa yace natuba yake shugabata.
gimbiya SAFRAH tace menene yakawoka kuma dawani taimako katawo. sai BOKA KIRYAN yaqara durqusawa sannan yace.
BOKA KIRYAN yace yake shugabata kisani aljanunnan qarfin damtse ko tsafi baya tasiri akansu face dabara. dukkan qarfi da tsafi baxaiyi tasiri akansuba saida dabara kuma basajin duka ako ina face a idanunsu. indai kika bugi idansu to nantake xakiga yafadi matacce.
sai yakara dacewa gawasu dakarun aljanunan natawo miki dasu guda 200, sune xasu tayaki kiyaqe wa’incan daxamu tunkara yanxu. saiya ambaci wasu kalmomi saiga wasu aljanu matsakaita atsawo sunbayyana jikinsu kamar wuta irinsu akekira da JINNUL NARII.
Saisuka shirya suka shiga dajin. dajin gwanin ban sha’awa domin ga itatuwa da kayan marmari daban daban. sunyi tafiya takusan sa’a biyu inda suka gamu dawani wawakeken rami. bahanyar wucewa. cikin rashin sani gimbiya SAFRAH tadaga fiffikenta domin tatashi ta tsallake ramin. tashinta keda wuya kofara tafiya batayiba sai dajin yafara girgiza nantake bishiyu suka fara rikida dajin yayi bakikkiri kamar duhun dare.
cikin qanqanin lokaci dajin yacanja dukkan bishiyun suka rikida suka koma aljanu. aljanun sunkasance manya dogaye ga jajayen ido. duk girman aljanin daya yakai girman gimbiya SAFRAH sau biyu xuwa uku. farat saisuka afkamusu.
aljanun sunkasance masu tsananin gudu da zafin nama domin cikin qanqanun lokaci sukafarawa dakarun boka kiryan dauki daidai. aqalla sunkashe kusan 20 sannan aljani boka kiryan yayi tsalle sannan yasoki idon guda daya da takobinsa a cikin tsakiyar idonsa. aifa aljanin yakurma wani uban iwu wanda seda qasa tayi girgiza sauran aljanun sukai kamar xasu kurumce sbd tsananin qarfin qarar. nantake aljanin yafadi matacce.
al’amarin yayi matukar bawa sauran aljanun mamaki domin atariyi bawanda yata6a gwabxawa dasu yakashe daya daga cikinsu ballema har agane lagwansu. cikin zafin nama boka KIRYAN yakemusu dauki daidai wanda hakan yayi matukar tunxurasu sai dukansu suka fadawa BOKA KIRYAN dan halakashi……
cikin xafin nama BOKA KIRYAN yakemusu dauki daidai wanda hakan yayi matuqar tayar musu dahankali harsuka fado kansa suduka dan halakashi. tabbas aljani KIRYAN yayi musu barna domin yakan kashe kusan fiyeda 50 a dakika biyar. cikin tsananin fishi wani shirgegen katon aljani nadaban yaruqo BOKA KIRYAN sannan yafyadashi aqasa wanda nantake BOKA KIRYAN yafadi sumamme. cikin tashin hankali GIMBIYA SAFRAH takale BOKA KIRYA wanda atinaninta yamutu. ⁸ 08108488607