Lokacin da ya isa gidan Hajiyan bayan ya gama yin parking a wajen da aka tanaza don adana motoci,sai ya dakata bai fito ba yana ansa call,lokacin ne kuma Bilya me gadi ya iso tare da zubewa yana kwasan gaisuwa,hannu kawai A.Maleek da har lokacin ke amsa waya ya ɗaga masa,hakan ya ankarar da Bilya cewa uban gidan nasa amsa waya yake,sai ya tashi ya bar wajen,da ido A.Maleek ya bishi tausayin dattijon na sake ratsa shi,lokacin daya kammala ansa call ɗin sai ya fito yana kulle motan ya fara takawa zuwa cikin gidan,tafiya yake cikin takunsa me cike da nutsuwa da zafin jini,kallo ɗaya za kaiwa fuskansa da ba ma’abocin fara’a sosai ba kasan cewa miskili ne na gaske,lokacin da yaiwa falon gidan tsinke bakinsa ɗauke da sallama,dai-dai lokacin ne Hajiya Aysha ta fito daga wani corridor,hannunta riƙe da waya da wani Cup,amsa sallaman nasa tayi hancinta na cigaba da shaƙo qamshin turaren RALPH LAUREN,ta ƙariso cikin falon a lokacin da A.Maleek ɗin yaiwa kansa mausaki a cikin kujeran 2 Seater,kusa da kujeran da ya zauna nan Hajiya ta zauna itama,domin indai har zatai zaman falo to wannan kujeran dake daura da inda A.Maleek yake nan ne wajen zamanta,shiyasa ma yaima kansa mazauni anan ɗin,idanunta fes akansa yake lokacin da take aje wayanta da Cup ɗin da ke hannunta,A.Maleek yayi saurin zamowa daga kan kujeran ya zube a ƙasan Carpet yana kwasan gaisuwa,Hajiya Aysha da idanunta ke kansa ta saki lallausan murmushi tana amsa gaisuwan tilon ɗan nata namiji,kafin ta ɗaura da faɗin “Ina ka baro Suhailan da ka sanyata kuka tunda farin safiya,har da ruɗata da cewa zakai mata kishiya duk awani dalilin?”
A.Maleek da ya cigaba da zama daga ƙasa ba tare da ya koma bisa kujeran ba,ya ɗaga manyan idanunsa da ya gada wajen Hajiyan yana faɗin “Hajiya har yanzu dai na lura baki daina ma Suhailah kallon ƙaramar yarinya ba,kullum cikin goya mata baya kike bakya son laifinta sam,wallahi Hajiya Suhailah bata jin maganata,sam ba ta ma ɗauki aure da wani muhimmanci ba,amma a yau ina son warware miki irin zaman da muke ko zaki daina goya mata baya.”
Ya dakata da maganan yana kallon Hajiya,wacce ta nutsu tana sauraransa kafin ta gyaɗa kai tana faɗin “Ina jinka sanar dani menene ke faruwa da rayuwan auren naku?”
A.Maleek yai ƙasa da kansa kafin ya fara da faɗin “Hajiya Suhailah bata kula dani,duk wani aiki da kika san macen ƙwarai xata tsaya taiwa mijinta Suhailah bata min,ban isa ince ina son abu ka za ta tashi ta girka min da kanta ba sai dai mai aiki,gyaran ɗakina sai ta bushi iska take yi,shima ina ga a wata baifi tayi sau biyu ba,ni ne da kaina idan na shigo gari zan zage ingyara komi idan ina son ganin ɗakin yadda nake buƙatansa,sannan babban matsalata da ita rashin son haihuwa,Hajiya Suhailah ita da kanta ta kai kanta asibiti ta fara amsan Pills na tsarin iyali ba tare da sani na ba,a cewanta tana tsaka da karatu akai bikinmu baxata taɓa yadda ta ɗauki ciki ba,yanzu bikin mu shekaru biyar kenan ta gama karatun tayi Service amma bata daina amsan alluran hana ɗaukan ciki ba,na ɓoye miki gaskiyan magana cewa babu abinda muke yi ne,sabida na ga idanunki ya rufe a nuna mata soyayya,sam baki son laifinta san……”
“Dakata Abdul-Maleek kana so kace min ita Suhailan da kanta ne ta yanke ma kanta yin tsarin iyali ba tare da izininka ba ma, yaushe Suhailah tayi buɗewan ido har haka,ina tarbiyan dana bata ?”
Hajiya Aysha ta katse A.Maleek a fusace,tare da jero masa waɗannan tambayoyin,fuskanta gaba ɗaya na rinewa da zallan ɓacin rai,hakan yasa A.Maleek dubanta yana cigaba da faɗin “Nima abinda na jima ina tambayan kaina kenan Hajiya,ina ga qawaye ƴan duniya tayi da suke son sauketa akan turban da kika ɗaurata akai tun farko,to ni a gaskiya na gaji da halayyan Suhailah kuma bazan iya zama da macen da bazata haihu dani ba sai dai ƙaryan nuna min soyayyah,shiyasa nace a yau zan fayyace miki watakila ke idan kika zaunar da ita kikai mata faɗa zata ji naki,ta canza banzayen halayyan data fara koya,shiyasa na shigo da maganan sake aure kuma am very serious idan har bata sauya ba zan tabbatar mata da cewa ni ba zata maida ni sakarai ba,koma ta canza ɗin ina ji ajikina akwai abinda zai faru nan ba da jimawa ba.”
A hankali A.Maleek ya zayyanewa Hajiyan nasa irin mafarkan da yake a ƴan kwanakinnan,da wata wacce sam ba’a nuna masa zahirinta illah idanunta masu haske da ake nuna masa a mafarkin,sai hannayenta da take miƙo masa tana kuka alamun neman taimako,amma da zaran yakai hannunsa don kamo nata yake farkawa daga mafarkin ,Hajiya Aysha bayan gama saurarensa tai shiru tare da shiga tarin nazari,matsalan Suhailah da mafarkin da A.Maleek ɗin ke yi suka taru suka kulle kanta,har ta rasa wani tunani ma zatayi sai zuwa wani lokaci ta numfasa,batai masa magana ba sai wayanta da ta ɗauka ta shiga neman layin Suhailah,bugu biyu ta ɗaga Hajiya bata jira komi ba ta furta “Ma za yanzu kizo nan gida ki sameni.”
Daga haka ta kashe wayanta zuciyanta na cigaba da ɗaukan zafi akan lamarin Suhailah,tabbas tana ganin a wannan karon dole ta ɓata ran Suhailan don ko kaɗan bazata lamunci irin wannan sakarcin ba,sannan bata tunanin idan har Suhailah ta cigaba da nuna rashin son haihuwa da gudan jininta to tabbas ita da kanta ma zata nemo masa wata macen ya aura ko bai so ba,zaman awa ɗaya sukai suna cigaba da tattauna matsalolin Suhailah,kafin motar Suhailah ta iso gidan Hajiyan,ta shigo wurjanjan don tunda taji kiran da Hajiyan ke mata tasan ba lafiya ba,A.Maleek ya gama kwancewa Hajiyan komi,hakan yasa ta shigo jikinta a sanyaye tana faman raba ido,kallo ɗaya A.Maleek yai mata ya ɗauke kai yana sake haɗe fuskansa tsaf babu alamun wargi,kusa da Hajiya ta je ta zauna tamkar zata shige jikinta,amma sai Hajiyan ta shiga ture ta tana jifanta da wani mugun kallo take faɗin “Dallah! Matsa ki bani waje ashe ke ɗin sakaryace mara hankali Suhailah,irin tarbiyan dana baki kenan,ko ni haka kika taso kika ga inama marigayi rashin albarka da rashin biyayya? Maxa sanar dani gidan uban da kika kwaso dukkanin halayyan da Maleek ya sanar dani,har kinyi buɗewan idon da zaki tsarama kanki rayuwa Suhailah,a gidan ubanwa kika taɓa ganin inda Haihuwa ya hana karatu? Har da zaki je ki cuci kanki ki fara tsarin iyali alhali ko haihuwan fari baki taɓa yi ba.”
Inda Hajiya Aysha ke shiga ba tanan take fita ba,taiwa Suhailah tas wacce zuwa lokacin kuka sosai takeyi,cike da tarin nadaman Planing ɗin da tai tayi abaya,da gaske takewa Maleek ta daina shan pills ɗin da takeyi,kusan shekara guda kenan rabonta da shan komi amma ciki yaƙi samuwa,shi kuma ya kasa yadda ta daina ɗin abinda yasa suke ta samun saɓani dashi kenan,jikin Hajiyan ta koma tana cigaba da kuka sosai,Hajiyan ta sake ture kanta daga jikinta,don da gaske haushin Suhailan me zafi take ji,cikin muryan kuka Suhailah ke faɗin “Don girman Allah Hajiya kuyi haƙury ke da Yah Maleek,wallahi zan gyara duk halayyan da baya so,amma bazan iya ganinsa da wata mace ba bayan ina raye,wallahi Hajiya na daɗe da daina tsarin iyali shekara guda kenan,Allah ne bai kawo rabon ba shi kuma ya kasa yadda na daina.”
“Ta ya za’ai dama ya yadda kin daina ɗin,tunda lokacin da kika faro ba da yawunsa kika fara ba,Allah yasa ba illah kikai wa kanki da kanki ba,inko har wani matsalan kika janyowa kanki,kinga maganan kice baki son ganin mijinki da wata mace ma bai taso ba,don ni da kaina zan masa wani auren don bazan zuba ido banga ƙwansa a duniya ba,alhali shi kaɗai na mallaka ɗa namiji da Allah ya bar min ya rayu,tunda ke shashashace baki san inda kanki ke miki ciwo ba,in banda ke ɗin sakaryace har wani tsoron haihuwa zakiyi don kina boko bayan gani a raye,ki gayamin wani wahalan raino zaki sani inda kin haihun alhali kinsan kuna dani a raye,to kisawa ranki zama da kishiya nan ba jimawa ba matuƙar ya tasaki agaba kuka je wajen likita aka tabbatar alluran da kikai ne ya janyo miki wani matsalan.”
Hajiya Aysha ta ƙare maganan cikin fusata tana ji tamkar tun a yanzu ɗin ta rufe Sunailan da duka,Suhailah da kalaman Hajiyan ke sake kiɗima zuciyanta idan ana shigo da zancen Maleek ɗin zai iya sake aure,ta sake rushewa da kuka so take ta je ga Maleek ɗin ko shi zai tsaya ya saurareta,amma kallo ɗaya tai masa taga yadda shi ɗinma ya sake ɗinke fuska yana jifanta da wannan shu’umin kallon nasa me ɗaga hankali,ai sai ta kifa kanta jikin kujera tana cigaba da rasgan kuka,yayin da Hajiya ta cigaba da rufeta da faɗa daga baya ta koma nasiha,hakan yasa Maleek zame jikinsa yai sallama da Hajiyan ya bar gidan,zuciyansa fes don baiyi tunanin Hajiyan zata iya rufe ido taci zarafin Suhailan har haka ba,idan yana tuna irin son Suhailan da yake rufe idanun Hajiyan,sabida kawai Suhailan ta fito daga tsatson jinin qanwanta da suka fito ciki guda,ta rasu ta barwa Hajiyan Suhailan tun tana da shekaru biyar a duniya,tuƙi yake yi yana fata da addu’an Allah sa dukkanin faɗa da nasihan Hajiyan suyi tasiri a zuciyan Suhailah har ta gyara ɗabi’unta da baya so,wayansa da yake ruri ya kalla ganin sunan abokinsa Naseer ne yasa shi ɗaga wayan yana sanar da Naseer ɗin inda zasu haɗu.
Tunda TAIMIYYAH ta tashi take ta tunanin ta yadda zata tsiri yiwa Yah Sadeeq ɗin girkin da ya buƙata,ba tare da Iya ta gane don shi tayi ba,bare har ta rufe ta da faɗa,dubara ne ya faɗo mata lokacin da ta kammala shirinta cikin wata rigan atamfa da akaiwa ɗinkin free gown da yai matuƙar yi mata kyau,ɗankwalin kayan ta ɗaura tana bin jikinta da turarenta me sanyi da daɗin qamshi,agogo ta kalla taga lokacin ɗaura lunch ɗinsu yayi,hakan yasa ta fita da ƙwarin guiwanta zuwa falo,kaman yadda tai tunani Iyan na hakince cikin kujera,ta tasa TV agaba tana kallon wa’azin da ake haskawa a tashar Manara,TAIMIYYAH ta cigaba da takowa cikin irin tafiyanta da sai da taimakon dafe guiwan ƙafanta me laluran take iya tafiya,ta iso kusa da Iya tana faɗin “Iya yau kuma me Ladi zata girka ne ko dai in amshi girkin tunda nayi sarai sosai,sai in dafa mana ko Rice and Stew ne,ke me son wake sai a dafa miki waken daban.”
Ta ƙare maganan tana ɗauke idanunta daga kan Iya,ita kuma Iyan sai ta zubawa TAIMIYYAH ido tana jin ƙaunarta na sake zama a zuciyanta,rashin son jikin TAIMIYYAN da jajircewanta wajen iya sarrafa nau’in girke-girke na tsananin birgeta,don haka bata kawo komi ba ta gyaɗa kai cike da gamsuwa take faɗin “Hakan ma yayi TAIMI na indai zaki iya sai ki shiga Kitchen ku haɗu da Ladin kuyi girkin,amma ni ina son a dafa raguwan Kazan nan da ke cikin Freezer,ayi farfesun ta kawai ki ɗan saka dankalin turawa irin yadda kike mana yai daɗinnan a zuba kayan qamshi yaji sosai kinji ko.”
TAIMIYYAH ta gyaɗa kai lokacin da take miƙewa,ta dubi Iya tana faɗin “To Iya duk za’ayi yadda kike so bari inje inga me Ladin take yi.”
Daga haka TAIMIYYAH ta nufi Kitchen ɗin nasu,zuciyanta fes kaman ƙanƙara don ta san ta gama da shafin rigiman Yah Sadeeq ɗin,itace tayi komi Ladi kawai blanding kayan miya tai mata,sai ganyen Salad da ta sata yanka musu don TAIMIYYAH bata son cin abinci babu ganye,shiyasa basa rabo da aje kayan Salad ko na Coleslow,bayan kammala abincin TAIMIYYAH ta kwashe su a kulolin da suka saba zuba abinci Ladi na ɗauka tana fita dasu zuwa falon Iya,tana jerawa a ɓangaren da suke cin abinci,sam bata wani wahal da kanta ɗibarwa Yah Sadeeq ɗin daban ba,don tana da tabbacin nan Sasan nasu zai yi masauki yaci abincin,Zoɓon da ta tsaya kammalawa sawa Flavour ta ƙarisa haɗawa ta miƙawa Ladi tasa shi cikin ƙaramin fridge,ita kuma ta juya tabar Kitchen ɗin zuwa ɗakinta don yin sallan Zuhur ganin time yaja,lokacin da ta idar memakon ta fita falo taci abinci sai tayi kwanciyanta a gado,ta ɗauki wayanta tare da kunna Data ta hau online,shiga nan fita can har ta ɗauki lokaci ba tare da ta damu ba,sai da taji Iya na ƙwalla mata kira sannan ta fito,a tsaye ta samu Iya riƙe da wani leda a hannu,fitowan TAIMIYYAN yasa Iya maida dubanta gareta tana faɗin “Maza ɗakko Hijab ki zo ki miƙawa Zuwaira wannan saƙon,turaren wuta ne aka aiko min na ɗibar musu,ki kuma sanar mata yau bana buƙatan abincin daren su,Ladi zata tuƙa min tuwan dawa ne zuwa anjima.”
TAIMIYYAH ta gyaɗa kai tana faɗin “To Iya bari in ɗakko Hijab ɗin.”
Daga haka ta koma ɗaki ta sanyo Hijab ɗin sallanta ta fito,ledan da kwalban turaren wutan yake ta ɗauka tai waje,tana takawa a hankali har ta isa sasan Baba Sanin……..✍🏻
Ɗansabo ce
DOMIN KARANTA CI GABA DANNA👇