BA SONTA BAKE BA TAUSAYI BE CHAPTER 13

“Ki dena damuwa insha Allahu ni zan taimaka miki, Amman ina son dan Allah dan Annabi (s.a.w) kada ki nuna ni na taimake ki sanin halin mijinki ze iya ta kakkiya har gidana ya cimin zarafi ina zamana ƙalau”

Talatu ta faɗawa hassana wadda take sharewa ummul hawayen ta dake zuba kamar famfo.
Sallamar sadiya ita ta hana hassana magana da sauri ta miƙe ta ɗauko ƙatuwar silva ta karɓi kwakin ta juye ta bawa sadiya tace taje ta jiƙa musu sannan ta ɓalli magani ta bawa ihsan bakin ta yaƙi rufuwa da godiyar data kema talatu.
Sadiya ta zuba suga cikin kwakin tare da cokula tazo gaban hassana taja hannun ummul akan tazo suci.
Share hawaye ummul tayi tare da tashi taje ta ɗauko kofi ta ɗibi kwakin tare da ƙarasawa gaban hassana ta kamo hannun ta.
Muryar ta a tausashe tace mata.
“Bamu kici rabona ni naƙoshi ki daure ki dinga tsakurar abin ci koya ne kina ci, idan kika faɗi kika mutu yaya zamuyi da rayuwar mu”
Cak talatu tayi tana kallon madarar ƙaunar ƴar da uwar lallai ƴa mace rahma ce ga al’ummah.
Amman ga waɗanda basu san darajara haihuwa ba se su dinga dangana haihuwar ƴaƴa mata da bala’i musamman irin su malam habu kaiba mai kuɗi ba amman ka ɗauki tsanar duniya ka ɗorawa ƴaƴa mata, Domin takurar sa ma ga matan nasa yana da nasibi da haihuwar matan da sukai masa.
Murmushi hassana tayi tare da amsar kwakin.
Sannan tace.
“Kingan ta talatu wallahi idan ban shaba itama bazata shaba wanann jin ƙai na ummi na rasa irin son data mini”
Murmushi talatu tai.
“Sekina mata addu’a daga sharrin mutum domin naga alamun gidan nan ba ƙaunarku ake ba kar aje ai amfani da ƙaunar data ke miki a tarwatsa mata rayuwa musamman idan aka hango zata ji ƙanki”
Murmushi hassana tayi.
Bata ce komai ba domin ita bata yadda tai maganar hadiza agaban kowa duk abin da take mata dannewa take bata magana.
Cikin son ta katse wannan maganar tace.
“To ina jinki talatu wani taimako zaki min muna magana sadiya ta shigo zanyi magana kuma haɗin kwaki ya ɗauke min hankali”
Gyara zama talatu tai tare da cewa.
“Kin ganni nan ban yarda zuciyata ta mutu akan se lallai namiji ya tallafa mini ba bahaushe yace idan dama taƙi se abi ta hagu! hassana yanzu fa sekai da gaske bare ke mai ƴaƴa mata nan da shekaru kaɗan zakiji maganar aure dan haka kibar bacci kibar ƙullah gyaɗa tashi xaki ki zama mace mai kamar maza kiyi sana’ar da zata baki cida sha harma da, Kuɗin makarantar yaranki Ki cire tsoron malam habu kizo mu haɗa kai na sama miki gidan aikin dazaki tawo dana dare acan ke zakici na rana ga kuma albashin ki”
Talatu ta faɗawa hassana cike da bata ƙarfin gwiwa.
Ƙifta idanu hassana ta shiga yi wannan shine ga ƙoshi ga kwanan yunwa.
Kafin kuma tace.
“Ai talatu baze yuwu ba maganar nan kamar ƙanzon kurege ce kin san tashin hankalin baban su baze yarda na fita aikatau ba”
Tafaɗa cikin sanyin ta.
“Haba hassana ke kamar ba mace ba ai bazaki ce masa aikatau zaki ba cewa zaki abincin ƴan makaranta zaki dinga dafawa ana baki albashi”
Tiryan tiryan talatu tagama tsarawa hassana yadda zata gayawa baba wanda duk ta gamsu taiwa talatu godiya taraka ta har soro kana ita ta dawo cikin gida.
Malam habu bai dawo gida ba se sha ɗayan dare tabarma ya shinfiɗa a tsakar gida gefen shi ƙullin tsire ne yake ci seya haske tsakar gidan da fitila yadda bazaka ga mai yake ciba hassana tayi sallama can gefen sa ta zauna gidan tsitt alamar mutan gidan sunyi bacci.
Haɗe rai yayi tare da ce mata.
“Lafiya dai uwar sadiya kika zo kika tsayamin akai na saƙeƙe”
Mayar da tsinin daya tokaro mata tayi tare da cewa.
“Allah nagode masa daya sa dai ƴaƴan naka ne babu damuwa dan ka dangana ni da uwarsu”
Tafaɗi maganar a ɗan fusace domin ta fuskanci magana ya gasa mata.
“Dariya ya sheƙe da ita tare da ƙara ɗauko tsiren shi ya wulla cikin bakin shi.
“Ada nai farin cikin auren ki sabida ina kwaɗayin samun ɗa namiji daga gareki domin ko banza ya dinga taimakona wajan aiki to ƙarin bala’in kema seki kaita jero mata waɗanda babu abin da suka sani se ci da sha se kawo ƙarar gidan miji”
Yafaɗa cikin fushi.
“Malam kenan ina guje maka ranar da zakai kukan farin cikin haihuwar ƴa mace ranar zakai kukan kunya ne bana wani abu ba, sannan kuma maganar aure jaraba ce kawai irin taku ta maza kai baka ƙoshi ba baka wadata gidan kaba baka da yadda zakai da mata biyu ka tashi kai aure kuma kaine kake da ƙwan haihuwar mata bani ba domin ni bazan wa kaina ciki ba, tun farko inda nabi maganar abokan aikin ka da bazan aure kaba amman ni ina yadda da kaddarata ƙaddarar ƴaƴana ita ke zaune dani agidan nan tsananin rabo ne yasa na aure ka amman rabona da jin daɗin gidan ka tun ranar da ummi tai kwana arba’in aduniya”
Tafaɗa tana mai zubar da hawaye.
Ai seya hauro ya dinga surfa bala’i yana ɗaga muryar da har maƙota sesun jisu.
“Hassana ni kike gayawa haka? yaushe kika sha miyar birni har kikai kilewar mayar min da magana hassana?”
Ya kuma kiran sunanta yana yowa kanta kamar ze daketa.
Nan da nan zuciyar fulanin ta motsa mata ta juya harshe sabida hausarta bata fita tar tar.
Magana take mayar mai da zafi wadda ta bawa malam habu tsananin mamaki koda yake daman mai haƙuri bai iya faɗa ba.
Ganin faɗan nasu yaƙi ƙarewa yasa hadiza ta fito tana janye hassana wadda take furta.
“Malam ka sake ni nikuma bazan bar gidan ba sabida ƴaƴana zanyi zaman su mai za’ai da ƙaddararran auren ka”
Da ƙyar hadiza takai hassana ɗaki tare da bata haƙuri amman itama mamakin taurin zuciyar hassana take domin idan ita ce bazata iya gayawa malam ɗin haka ba.
A daren ranar babu wanda ya rintsa a tsakanin malam da hassana, shi tsananin mamakin ta ya hanashi bacci ita kuma nadamar abin da taiwa mijinta uban ƴaƴanta ya hana ta bacci.
Sabida haka asubar fari ta lallaɓa zuwa tsakar gida lokacin yana alwala ze fita ta rissuna ta gaishe shi bai amsa mata ba dan haka ta cigaba da bashi haƙuri tana share hawayen ta.
Taga ɗan sassauci saman fuskar shi dan haka hankalinta yaɗan kwanta ta koma ɗaki ta tashi su ummul akan suje suyi alwala suyi sallah.
Tun wajan shidda kausar ta sanya kukan yunwa cikin faɗa hassana tace.
“Dan uban ki bani da abinci ko babu zan baki?”
Buɗar bakin kausar se cewa tayi.
“Eh Bamu ki bani babun naci”
Sautin dariya taji daga tsakar gida wadda hadiza take yinta da iya ƙarfinta tana faman sakin habaici tana cewa ƴaƴanta suzo suci abinci.
Kafin taga malam akan ta yana muzurai.
“To hassana naji dukkan batun ki najiya dan haka daga yau babu ni babu ƴaƴanki babu sabuluna bare omo abinci ma na dena baku gaki ga ƴaƴan naki nan kiyi zaman su”
Fuwwwww ya fice yabar mata ɗakin.
Hannunta ta ɗaga sama hawaye na zuba tace.
“Ya Allah ka kawo mani mafita”
Ta shafa gudar hamsin data yage ta bawa ummul tace taje ta siyo koko wanda kausar da ihsan zasu sha…………….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *