RIKICIN KAUNA CHAPTER 1 BY MARYAM SALISU MAI DALA

Tafidal Tafidal Kaka dake uwar daki take

kiransa ta yinkura ta fito tace “Kaico dai

Tafida nace kaiconka, ka rasa wacce zaka tsaya ka dinga biyewa kana tsokana sai kanwar bayanka Nana, kuma abin kunyar wai tayi banza da kai amma kaki yi mata shiru.”

Nanar ce ta katse kakan da jan ruwan da take a rijiya ta ce “Kaka ni banga mazubin na ki ba na iddasa zuba nawa.

Kaka ta fito sosai tana nuna mata fanteka da zata zuba mata yayin da ta ci gaba da fadan, shi kuwa Tafidan sai ‘yar dariya yake yi.

Da°u abokin Tafida ya ce “Ai kaka ko da kika ji Nana na yiwa Tafida banza idan ta- tashi kwara guda ta ishi Tafida idan ta fado ta wuceta barshi da mita.”

Kaka ta ce “To ai mai da shi tayi bi can shi yasa bata fiya kulashin ba, amma Tafida bai kyalewa. Nana ta ce, “Shi kenan kaka?”

Ta ce, “Shi kenan don ma ko kin cika wani abin kuma Tafida zai kwashe shine ya yi wanka, shi ko ba kokarin janyowa ba.

Da’u ya ce “A’a Kaka kin ji ko! A gaban Nana don ta kirashi rago.” Kaka ta harare su duka ta ce “Nanar bata sanshi ba ne kuma su wanene ku dukan idan ba ragwayen ba daga kai har shi din akwai me iya hude kunya hudu a yini guda.”

Da’u ya kwashe da dariya don yadda kakan take kallonsu a raine, Tafida kuwa yana dan shafa kansa yana “yar dariya ya ce “A bamu a gani mana in an ga ba mu yi ba ba a bamu ba ne.”

Kaka ta ce “Kai tafi can da dai tsokanar Nana ce da kune a gaba.” Ta juya tana yiwa Nana sannu, sanda Nanar ke maida mata ruwan gefen tana kare mata shi saboda akuyoyi ta ce “Sannu ke dai Nana.” Ta dubi su Tafida ta ce “Ku ko Allah ya kyauta mukun.” Ta yi wucewarta daki.

Nana kuwa ta kama ruwanta suna kallonta ta janyo wata butar alwalar Kaka ta tintsira daga cilin nata na boliti duka ko magana bata yi musun ba ta nannade gugar ta maidawa kaka inda take ajiyewa ta ajiye a hankali don kada Kakan ta jiyo.

Da’u yake cewa “To ke ma dai Nana kiyi kokari ki gyara tsayuwar Ra dink a baki duk sanda zaki fado Ra sai sautin ya fito ‘Ra, kinga ba Tafida ba ko wa ki na fada sai ya maimaita da sunan tsokana.” Ko kallonsu bata yi ba ta kama ruwan ta ta dora aka har Da’u na yin sauri da hannu wai ya tare kar ya fadi, amma shima yana daga zaunen.

Tafida ya ce “Kyale ta har na share bakin dariya don tana faduwa zanyi.”

Da’u ya yi ‘yar dariya “A haba.”

Nana kuwa ta dauki butar da ta cika ta matsa kusa da Tafida ta dan gwarar ta ce “Idan ka ga ma surutun sai ka shiga ka watsa don kwana biyun da baka yi wanka ba nasan jikinka ne yake cizon ka kake ta maiko, shi yasa bakinka ma kansa yaqi zama shiru.” Tana idda fadin kuwa tayi ficewarta.

Da’u kuwa har kusan kasa ya kai yana dariya,

Tafida ya diro daga kan dan tudun da yake yana dan hade fuska “Ni din ne na kwana biyu ban wanka ba!” Kafin ma ya Karasa magana tuni Nana ta ida shiga gidan su, sai dai daga murya da ya. dinga don ta jiyo shi, ta jiyo shin kuwa ta sauke ruwanta a rumfar girkinsu da ke tsakar gidan tai shigewarta daki, yana hango sanda ta yi shigewar tata. Makota ne katangarsu daya, abinka da ginin Kasa yawan dukan ruwan sama ya sa ita ma katangar ta zaizaye don muddin kana tsakar gidan su Tafida ka yi yinkuri sosai zaka hango tsakar gida. Malam Mado babansu Nana, amma ba ko ina din ake hanga ba illa kofar dakin su Nana da

Hmmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *