BA SONTA NAKE BA CHAPTER 6 F
Farouq yayi kusan minti goma yana kallon Zara wadda batada niyyar matsawa daga wurin da take.+ Wata zuciya ce tace yayi tafiyar shi ya barta a nan yayinda dayar ta bashi haquri akan ya qarasa wurinta. Tsaki yayi ya ja motar har zuwa inda take, kashe mishi ido daya tayi tana murmushi ta zagaya ta shiga. Kallon shi tayi tace “wow, Ya Farouq kayi kyau dayawa, I am jealous” da sauri ya juyo ya kalli fuskarta wadda ta nuna she is serious about what she said. Tsaki yayi sannan ya ja suka tafi. Suna tafe a kan hanya ne Zara tace “Ya Farouq ya jikin Anty Ruqayya?” yace “da sauqi” daga nan basu qara yi ma juna Magana ba har suka isa event hall din. PEACHVINE MARQUEE EVENT CENTRE Bayan Farouq ya faka motar shi ne suka fito inda take qoqarin gyara rigarta wadda take jan qasa. Tuni Farouq ya kama hanyar shiga hall din yayinda ya barta a baya tana tahowa ahankali saboda dogon takalmin da ta sa. Ganin yayi mata nisa ne yasa tace “Ya Farouq please wait for me” juyowa yayi ya hango ta a bayan shi tana tahowa da qyar. Tsaki yayi a ranshi yace “I wonder why mutum zai sa abinda zai dinga bashi wahala” A lokacin da ta qaraso daf da shi ashe akwai steps din da tayi missing sai ji tayi ta tafi zata fadi. Ihu tayi yayinda ta ji Farouq ya riqo ta. idanuwan ta a rufe tana kyarma tace “thank you big brother, da na fadi kuwa sai na karye” Farouq cikin bacin rai yace “open your eyes and move ko in jefar da ke a nan wurin, crazy girl. Kina tafe ba kya kallon gaban ki” Zara dai murmushi tayi tare da riqe hannun shi gam suka cigaba da tafiya yayinda tace “toh ai Ya Farouq takalmin da na sa ne dogo” Yace “kinsan bazaki iya tafiya da shi ba wa yace ki sa shi?” Zara dai tana jin dadin hirar tasu tace “toh ai idan ban sa shi ba riga na zai ja qasa sossai” A lokacin har sun shigo hall din suna Magana basu san mutane suna kallon su ba yayinda mai gabatarwa yake ta kirarin babban abokin ango da babbar qawar amarya sun shigo. Har yanzu Zara tana nan riqe da hannun shi inda yace mata “you look beautiful though” Da sauri Zara ta kalle shi cikin mamaki tace “Ya Farouq??” ya kalle ta yace “what??” ji yayi ta rungume shi tare da fadin “thank you so much, I love you” Tuni mutane suka fara daukar su hotuna yayinda ake ta yaba how cute they look together. Mukhtar da Hafsat dai kallon juna suka yi suna dariya yayinda Mamy da ke zaune tare da su Mom ta dafe kai tace “yau na shiga uku da yaran nan” Mom tana dariya tace “ai wadannan aure kawai yakamata ku hada su” Mamy tana dariya tace “ai dole”. Mai gabatarwa ne ya matso kusa da su yace “barka da zuwa Farouq da Zara yara a gidan CBN Governor Alhaji Al-Hussain Umar Jimeta” Zara ce ta dan matsa baya da sauri tana waige waige tare da kallon Farouq tace “i am sorry” sannan ta wuce wurin qawayen su yayinda ya girgiza kai a ranshi yace “she will be the death of me soon”. Mai gabatarwa ne ya kira babban abokin ango don ya bada tarihin ango sannan ya kira babbar qawar amarya don ta bada tarihin amarya. bayan Farouq da Zara sun fito sun bada tarihin ne mai gabatarwa yace “Allah ya nuna mana ranar naku bikin” zaro idanuwa Farouq yayi yayinda Zara ta fashe da dariya. STORY CONTINUES BELOW Gaba daya hall din kuwa akayi ihun “ameen”. Hafsat da Mukhtar dai babu abinda suke yi banda kwasar dariya har Mukhtar yana fadin “yau zan sha qorafi wurin abokina, Allah yasa kar yayi tunanin da ni aka hada baki da MC” Hafsat ta dinga dariya. Taro yayi taro yayinda aka ci aka sha. Zara wadda take bala’in son rawa haka ta zage ta dinga rawa a cikin mutane yayinda Farouq yake kallonta yana hararar ta a ranshi yace “yarinyar nan tana da matsala a qwalwa I am sure” daga nan ya kauda kan shi. Wayar shi ce tayi ringing ya duba ya ga sunan Ruqayya. Miqewa yayi ya koma can wani wuri kusa da exit ya zauna sannan ya amsa. Cikin bacin rai tace “Honey wai me kake yi da yarinyar nan? Yanzu na ga wani post a instagram tayi hugging dinka” katse ta yayi yace “hey relax, it’s nothing. I will explain when I get home” Cikin muryar kuka tace “amma Honey…” dafe kai yayi ya katse ta tare da fadin “sai na dawo, take care” sannan ya kashe. Kafin ya tashi ne ya ji an ce “Ya Farouq ina wuni” dago kai yayi ya ga qanwar Anty wato Saima. Murmushi yayi yace “Saima how are you? Yaushe kika zo?” tayi murmushi tare da zama kusa da shi tace “jiya muka zo tare da su Safa, so how have you been? Meyasa baka zuwa France kamar da??” Yace “kin san dama mid-year holidays ne nake zuwa yi a France when I was in Germany, tunda na dawo Nigeria kuma my schedule is always tight amma ina nan zuwa in rama cin da kika yi mun the last time ai” dariya tayi tace “dagaske Ya Farouq na fi ka iyawa, ka san kuwa anyi sabon Mortal Kombat?” yace “haba?” sai ta zaro wayarta tace “dagaske, bari in nuna maka” Wannan abu da ake yi duk akan idon Zara yayinda ta tsaya cikin mamaki tana kallon yadda Farouq da Saima suke ta hira har yana murmushi. Bata rai tayi a ranta tace “wato Ya Farouq yana shiri da Saima sossai ni shine baya shiri da ni” gani tayi Saima tana nuna mishi wani abu a wayarta wanda har karba yayi sannan ta ga ya kalle ta yana mata Magana. Zara dai bata san lokacin da ta miqe ta nufi wurinsu ba. Ganin ta yayi tsaye a kanshi tana kallon Saima tace “Hajiya, Safa tana ta neman ki ashe kina nan?” Saima ta kalli Zara tana murmushi tace “ina nan tare da Ya Farouq tun dazu ai” Miqewa tayi ta kalli Farouq tace “Ya Farouq zamu sake bugawa and I am going to win insha Allah” Murmushi yayi yace “all the best” Zara dai wadda ta zama confused sai kallon shi tayi tace “Ya Farouq maganar me kuke yi?” Ya miqe tare da fadin “its none of your business little one” nan suka bar ta tana ta jin haushi. A yanzu ta tabbatar ita kadai ce Farouq baya so a dangin su kaf. Zama tayi a wurin yayinda zuciyarta take ta tafasa. Daga inda take zaune ta hango shi tare da Saima da su Marwa suna ta hira har yana dariya. Tsaki tayi ta kauda kai. Wayar ta ce tayi ringing ta duba. Mahmood ne yake sanar da ita isowar shi. Aikuwa nan da nan ta miqe ta fita suka shigo tare. Tunda Farouq ya hango Zara tare da Mahmood ya miqe ya bar hall din. Ya rasa dalilin da yasa yake jin haushin gayen. Zara kuwa bata lura da lokacin da ya bar hall din ba. MUKHTAR ABUBAKAR MANSION A gajiye suka dawo yayinda suka zube suna ta hirar Dinner din da akayi. Hafsat ce ta koma kusa da Zara tace “toh Juliet, bani labarin abinda kika yi a hall dazu” Zara tayi murmushi tace “hmmm, kin san abinda Ya Farouq yace mun? wai nayi kyau” Hafsat ta zaro ido tace “da gaske bestie?” tace “wallahi, ban san lokacin da nayi hugging dinshi ba” Hafsat ta fashe da dariya tace “hmmm, something is going on somewhere” Zara tana murmushi tace “nothing is going on”. STORY CONTINUES BELOW Saima ce ta shigo dakin tace “Yauwa Zara dama ke nake nema, dan bani lambar wayar Ya Farouq please” cikin mamaki Zara tace “what??? Me zakiyi da lambar shi?” Cikin mamaki Saima tace “me ya ruwanki da abinda zanyi da shi?? are you jealous??” Zara ta bata rai tana hararar ta yayinda Saima ta matsa kusa da ita ta zauna tace “yi haquri Hajiya, na san Ya farouq no go area ne besides ni bazan iya kishi da ke ba” Zara tayi murmushi tace “matar shi tana can gida, ni babu ruwana” Kira mata lambar tayi wanda yasa suka kalleta cikin mamaki. Saima tace “you mean kin haddace lambar shi??” Zara ta Harare ta tace “toh lambar tana da wahala ne?” Saima ta miqe tana dariya tace “ko kadan gimbiya” yayinda Hafsat take dariya. Bayan Saima tayi godiya ta fita daga dakin ne Zara tayi tsaki tace “wannan Saiman bata jin Magana wallahi, yanzu meye nata da son lambar wayar Ya Farouq kuma?” Hafsat dai tana kallon ikon Allah tana dariya. ************* Washegari bayan sallan isha’I ne su Zara suka shirya Hafsat domin tarbar angon ta. Suna nan zaune a dakinta ne suka ji shigowar ango da abokanen shi. Wayar Zara ce tayi ringing inda ta ga sunan Mukhtar. Ta amsa cikin tsokana tace “Ya Muky ka dai san ba yau zan tafi ba ko?” dariya yayi yace “wallahi baki isa ba, yanzu ma zaku tafi ku bani wuri” dariya tayi tace toh bari dai mu fito ku sallame mu tukun”. Zara ta kashe wayar sannan ta kalli sauran qawayen su tace “oya babes ku zo mu je mu yi sealing final deal din mu” Hafsat tayi dariya yayinda ta gyara gyalenta wanda ta rufe fuskar ta da shi. Mukhtar ne zaune a falon qasa tare da abokanen shi yayinda suke ta tsokanan shi. ‘yan matan ne suka sauko suka gaishe su. Zara ta kalli Farouq wanda shima ita yake kallo ta kashe mishi ido daya sannan suka zazzauna. Zara ce tace “toh gamu mun zo” Daya daga cikin abokanen angon ne mai suna Aminu yace “nawa zamu bada hajiya?” Zara ta juya ta kalli ‘yan matan inda suka hada kai suka dan yi wasu maganganu sannan ta juyo tace “eh toh don kada mu bata muku lokaci ku kawo miliyan daya kawai, deal??” bata Ankara ba ta ji muryar farouq yace “deal” Juyawa tayi ta kalle shi cikin shagwaba tace “wallahi Ya Farouq da nasan kai zaka amsa da miliyan biyar nace” gaba daya suka fashe da dariya yayinda Farouq ya dalla mata harara. Bayan sauran abokanen sunyi addu’o’I tare da fatan alkhairi ne suka tafi tare da sauran ‘yan matan yayinda aka bar Farouq, Zara, saima, Safa da Marwa wadanda Farouq din zai mayar da su gida. Zara ta koma wurin Hafsat don tayi mata ban kwana, aikuwa Hafsat dai tana ganin cewa qawarta zata tafi sai ta fashe da kuka. Anan itama Zara sai ta fashe da kuka. Mukhtar ne da Farouq suka shigo dakin suna kallon ikon Allah. Farouq ne yace “meye haka?” Zara ta dago tana kallon shi yayinda Hafsat ta boye fuskar ta a cikin gyalen ta. Mukhtar ne ya fashe da dariya tare da fadin “abokina please take your crazy sister away, duk ta bi zata tada ma baby na hankali” Farouq ya kalli Zara yace “oya wuce mu tafi” Zara ta qara rungume qawarta tace “Allah ya bada zaman lafiya bestie, i am going to miss you” ta sauka daga kan gadon yayinda Farouq ya dafa kafadar abokin shi yace “abokina Allah ya bada zaman lafiya, take care of her and safe journey” Mukhtar yayi murmushi yace “thank you our soon to-be daddy, ka gaida Ruqayya” Maganar Mukhtar ce tasa Zara waigowa da sauri tace “what??!! Ban gane soon to-be Daddy ba” Mukhtar yayi murmushi yace “Yayan naki bai fada miki Ruqayya is expecting ba?” hankalin Zara yayi mugun tashi yayinda jikin ta yayi mugun sanyi. Zara dai bata sake yin Magana ba sai gani suka yi ta kama hanyar fita daga dakin, bata ankara ba ta ji ta buga kanta a bango wanda ya sa tayi ihu, dawowa baya tayi zata fadi yayinda Farouq ya riqe ta cikin hanzari. Tuni Hafsat ta yaye gyalen ta yayin da ta miqe ta yo kan Zara wadda take hannun Farouq. Goshinta ne yake jini yayinda Farouq ya zaro hankici daga aljihun shi yana gogewa. Farouq ya kalli Mukhtar da Hafsat wadanda suke cikin damuwa yace “relax, I will take care of her” yace ma Mukhtar “please ka sa driver dinka ya kai su Safa gida” Haka suka sauko yayinda Hafsat da Mukhtar suke ta yi ma Zara sannu. Zara dai gaba daya banda Farouq da ya bata support da ko tafiya ma bazata iya yi ba, gaba daya zuciyar ta sai tafasa take yi. Ganin goshin Zara duk jini ne yasa hankalin su Safa ya tashi. Mukhtar ne yake yi musu bayani yayinda Farouq ya wuce da ita. Ko da ya sa ta a mota suka kama hanyar asibiti fashewa tayi da kuka sossai kamar wadda aka yi ma mutuwa. Farouq dai ko kallonta bai yi ba domin kuwa shi kanshi ya zama confused akan abinda ya faru. CENTRAL HOSPITAL Zaune take akan daya daga cikin kujerun ofis dinshi inda yake dressing din ciwonta. Daya daga cikin Nurses dinshi da take wurin tana riqe da kayan aiki ta so tayi treating Zara amma ya hana. Bayan ya kammala ne ya ba Zara PCM ta sha sannan ya sallami Nurse din tare da bata umurnin ta hada ma Zara magunguna. Zama yayi akan kujerar da ke kusa da ita ya sa mata ido. Itama shi take kallo yayinda take ta ajiyar zuciya. “Aren’t you happy cewa zan zama daddy? Is that why you hit your head?” Abinda ta ji ya tambaye ta kenan. Kanta ta kifa akan tebir ta fashe da kuka. Miqewa yayi ya nufi fridge dinshi ya bude ya dauko goran ruwa ya bude yana sha. Gaba daya ya rasa gane abinda yake faruwa, a ran shi ne yace “could she be…” da sauri yace “No.. not possible” Ya koma ya zauna kusa da ita yace “idan baki daina kuka ba I will slap you” da sauri ta dago kanta tana share hawaye. Yana kallonta yace “talk to me, what is it” ajiyar zuciya tayi tace “I am gonna miss my friend” Zaro idanuwa yayi tare da bata rai kamar ba abinda ya so ta fada kenan ba. Tsaki yayi yace “you are very stupid, mutuwa tayi? Ko wani gari aka kaita? She is just going away for two weeks…” bai qarasa maganar shi ba yace “common tashi mu je in kai ki gida before I lose my patience” da sauri Zara ta miqe suka fita. Nurse din da tayi assisting dinshi wurin dressing ciwon Zara ce ta nufo su tare da miqa ma Zara ledan magunguna tayi mata fatan Allah ya qara sauqi. *********** A kan hanya gaba dayan su zuciyoyin su a hargitse suke. A bangaren Zara ranta a bace yake jin cewa Ruqayya tana da ciki zata haifo ma Farouq baby. A bangaren Farouq kuwa disappointment ya cika shi. Ya rasa dalilin da yasa bai so reason dinta na shiga damuwa ba… ************ Wani ikon Allah tun daga ranar da Zara ta ji cewa Ruqayya tana da ciki ne ta rage walwala. Gaba daya bata so ta ji an kira sunan Ruqayya balle Farouq. Ita kanta ta rasa dalilin da yasa ran ta yake baci a game da cikin Ruqayya. Mamy ta kula da yadda Zara ta koma shiru shiru, komai cikin sanyi take yin shi ba kamar da ba. Ko da ta tambayeta abinda yake damunta sai cewa tayi karatu take yi a dalilin an kusa fara tests. Gashi su safa da suke dan debe mata kewa sun koma France dukda ma Saima tana yawan bata haushi akan maganganun Farouq da take yawan yi. A kullum idan ta je makaranta zaka gan ta zaune ita kadai tayi shiru. Qawarta Hafsat ta tafi London Honeymoon tare da mijinta Mukhtar. Mahmood ne kadai yakan debe mata kewa tare da mantar da ita damuwar da tasa a ranta. Dayake dai Mahmood ya iya zantukan bada dariya haka yake zama yayi ta sa ta dariya. A duk lokacin da Zara take cikin damuwa idan dai Mahmood yana kusa toh fa sai ya mantar da ita komai, wannan ne yasa yake qara shiga ranta. Idan ta dawo gida kuwa idan ba wurin cin abinci ba Mamy bata ganin ta. Mamy bata sa komai a ranta ba domin kuwa duk lokacin da zata shiga dakin Zara tana ganin ta da litattafai a gaban ta. Asali kuwa Zara tana qoqarin yin karatu ne don saboda ta manta da abinda yake damunta. A yanzu haka rabonta da ganin Farouq tun ranar da ya dawo da ita gida, idan ma ya zo gidan boyewa take yi. Kwata kwata bata son ganin shi dukda kuwa tayi missing dinshi sossai. Wasa wasa dai hatta hotunan da take aika mishi ta daina, kiran waya da text message wanda take takura mishi da su ta daina. Shi kan shi Farouq dukda ba wani damuwa yayi da Zara ba a da, a yanzu ya kula cewa Zara ta fita harkar shi a cikin ‘yan kwanakin nan. Hakan kuwa baiyi mishi dadi ba domin kuwa dai yau da gobe ya fara sabawa da shiriritar ta. Ko da ya tambayi Mamy ta fada mishi cewar karatu ta sa a gaba sai ya qyale tunda dai she is doing fine shikenan. Bayan sati biyu da tafiyar su Hafsat ne suka dawo. Murna a wurin Zara abin ba’a cewa komai. MUKHTAR ABUBAKAR MANSION Washegarin ranar da su Hafsat suka dawo kuwa tun da safe Zara ta nufi gidan, a lokacin da ta isa kuwa Mukhtar ya tafi ofis domin kuwa ana ta neman shi tun suna London. Ko da Zara tayi sallama gidan cikin murna Hafsat ta rungume qawarta. Zara dai zaro idanuwa take yi tana kallon qawarta wadda tayi kyau tayi haske sannan har qiba ta yi. Zara tace “babes, kin ga yadda kika canza kuwa? Me Ya Mukhtar yake baki ne haka?” Hafsat tayi murmushi tace “bazaki gane ba bestie, sweetlove is the best thing that has ever happened to me” Zara tayi murmushi tace “I am happy for you” Hafsat ta dan kalli Zara cikin mamaki tace “kinyi ciwo ne bestie shine baki fada mun ba?” STORY CONTINUES BELOW Zara tayi murmushi tace “nope banyi ciwo ba, me kika gani?” Hafsat ta janyo Zara suka nufi dakinta, bayan sun zauna bisa gado ne Hafsat tace “kunyi fada da Ya Farouq ne?” Daure fuska tayi tace “No” Hafsat tayi murmushi tace “you are lying to me babes” wani irin kallo Hafsat tayi ma Zara tace “wait, ba dai tun lokacin da kika gano Anty Ruqy na dauke da cikin shi ba?” aikuwa kamar dama jira take kawai sai ta kwanta akan cinyar Hafsat ta fara kuka. Hafsat cikin mamaki tace “Zara like seriously? Sannan ki ce ba son Ya Farouq kike ba?” Cikin kuka Zara tace “ni ba sonshi nake ba, ni kawai na fi so in zama closest to him, she has taken him away from me bestie” Hafsat dai shiru tayi tana mamakin halin qawarta. Zara ta cigaba da fadin “kin ga gaba daya babu ruwan shi da ni kuma, I am sure ya ma manta da ni. I am his sister for crying out loud. Mamy da Ya Farouq are important people in my life amma shi Ya Farouq ya qi gane hakan, he always push me aside… why?” Hafsat dai tuni jikinta yayi sanyi inda ta rungume qawarta tana shafa kanta. Da qyar ta lallashi Zara ta daina kuka sannan tace “look bestie, I understand cewa you care a lot about him but ina so ki gane wani abu, Ya Farouq is married to Anty Ruqy. Kin sani cewa yau da gobe dama dole ne zata haifo mishi baby, whats wrong with that? Stop saying ya manta da ke, I am very sure ya Farouq bazai taba mantawa da ke ba, so please calm down” Cikin tsokana tace “wai ban tambaye ki ba, ina Mahmood ne?” Zara ta dan yi murmushi tace “yau ke kike tambayar shi bayan nasan ba sonshi kike tare da ni ba?” Hafsat tayi murmushi tace “toh ai banda choice than to like him tunda bestie dina tace idan ba shi ba sai rijiya, yaushe ne bikin naku?” Tashi tayi zaune tace “what?? Ba yanzu ba babes, ni fa sai na gama masters dina zanyi aure” Hafsat tayi murmushi tace “toh babes, tashi mu je kicin ki taya ni hada lunch, amma fa ki bi ahankali kada ki qone ko ki yanke hannu ki ja mun sharri” Zara ta fashe dariya. AL-HUSSAIN MANSION Mamy ce zaune a daya daga cikin kujerun qaramin falon ta yayinda Ruqayya take kwance bisa cinyar ta . Farouq ne zaune nesa da su yayinda suke hira. A yau Farouq da Ruqayya sun zo gidan don gaida Mamy. Sun dade suna hira ne Zara ta shigo gidan. Bata kula da motar Farouq ba a tsakar gidan domin kuwa gidan cike yake da motoci dama. Bayan ta gama amsa gaisuwar ma’aikatan gidan kamar kullum ta wuce cikin gidan. Sashen Mamy ta nufa inda ta ga babu kowa a babban falonta don haka ne ta kama hanyar qaramin falo. Tana gab da shiga ne ta ji muryar Ruqayya, nan da nan gaban ta ya fadi. Ajiyar zuciya tayi sannan ta dan leqa falon ta hango Ruqayya kwance kan cinyar Mamy, tsaki tayi ta juya abinta. A lokacin da ta leqo Farouq ya hangota wanda yayi mamaki matuqa yadda ta juya ba tare da ta shigo ba. Miqewa yayi yace “ina zuwa” ya fita. A lokacin da Farouq ya fita tuni Zara ta haye sama, bin ta yayi a baya har saman. Ta sa hannu zata bude qofar dakinta ne ta ji yace “hey” runtse idanuwan ta tayi sannan ta bude. Jiki a sanyaye ta juyo ba tare da ta kalli fuskar shi ba tace “ina wuni Ya Farouq” bai amsa ba ya cigaba da kallonta. STORY CONTINUES BELOW Zara kuwa tana nan tsaye ta kasa kallon shi sannan ta kasa shiga dakin nata. Idanuwan ta ne suka ciko da hawaye yayinda take ta ajiyar zuciya. Gani yayi kawai ta rugo a guje ta rungume shi wanda ya sa ya zaro ido cike da mamaki. Farouq dai bai ture ta ba sannan kuma bai riqe ta ba, hannuwan shi a kan iska yayinda yake jin kukan Zara har cikin ran shi. Ji yayi tace “I missed you Ya Farouq”. Ajiyar zuciya yayi ya banbare ta daga jikin shi tare da dafa kafadarta da hannun shi biyu ya duqo daidai saitin fuskar ta yana kallonta yace “I have been around ai, ban je ko ina ba” Zara tana kallon shi tana kuka tace “I.. I know but…” Katse ta yayi tare da fadin “ssshhh” Ya kamo hannun ta suka koma falonta suka zauna. Farouq yana kallonta yace “what happened to you na ga kin rame, were you ill?” Girgiza kai tayi alaman a’a tana goge fuskar ta. ji tayi yace “ni ne??” Da sauri ta kalle shi yayinda ta kasa Magana. Ya girgiza kan shi yace “Na ga kwana biyu ma kin daina turo mun progress report, no pictures…” Kafin ya qarasa maganar shi ne tace “Ya Farouq??” yace “what??” murmushi tayi tace “dagaske dama kana karantawa?” girgiza mata kai yayi alamar eh. Gani yayi tayi murmushi tace “can I see your phone?” Cikin rashin fahimtar abinda zata yi da wayar shi ya fiddo ya miqa mata ta karba. Yana kallonta ta bude gallery din shi ta fara dubawa. Cikin mamaki yace “what the hell, bincike kike yi mun?” tana dubawa ne tace “sorry big brother…” gani yayi ta zaro idanuwa tace “Ya Farouq ashe baka deleting hotunan da nake aiko maka?” Dafe kai yayi ya miqa mata hannu alamar ta bashi wayar shi sannan yace “mantawa nake yi, bani inyi deleting” da sauri ta boye wayar tayi kneel down tace “don Allah kayi haquri kada ka yi” Bata rai yayi yace “akan me? Memory dina ya cika, so I need space” Zara ta zaro wayar ta duba memory dinshi tace “wallahi Ya Farouq kana da space sossai, ko rabi fa bai kai ba. please don’t delete my pictures” Wayar shi ce tayi ringing Zara ta duba ta ga sunan Ruqayya. Bata rai tayi tana kallon wayar yayinda yake jira ta miqa mishi wayar. Ganin ta kusa tsinkewa ne yace “my phone” ajiyar zuciya tayi ta miqa mishi. Ko da ta miqa mishi wayar ta riga ta tsinke don haka ne ya kira Ruqayyar yayinda yake kallon Zara wadda yanayinta ya canza. Ko da Ruqayya ta amsa wayar cikin shagwaba tace “Honey kana ina ne ban gan ka ba?” gyaran murya yayi yace “ina sama tare da Zara” Ruqayya shiru tayi tana mamakin yadda Farouq baya ko denying wasu abubuwa a game da Zara. Ji yayi tace “ina zuwa” yace “okay”. Ruqayya ce ta hauro sashen Zara ranta a bace, tana shigowa falon ne Zara ta dago kai ta kalli fuskar ta sannan ta kalli cikin ta. ji tayi gaba daya ran ta ya baci. Ganin alamun bacin rai ne a tattare da Zara yasa Ruqayya tayi murmushi tare da fadin “ashe kana nan tare da gimbiya” yayinda ta tafi kusa da shi ta zauna tare da kwanciya jikin shi tace “Honey babynka yana wahalar da ni” Zara dai ji tayi kamar ta hadiye rai a wurin saboda baqin ciki. Ajiyar zuciya kawai take yi tare da matse yatsun hannuwan ta. Farouq wanda ya saci kallon fuskar Zara ya lura da jikinta har rawa yake yi yace “I think mu tafi gida ki huta kawai” Zara ta miqe tare da kallon Ruqayya tace “bamu gaisa ba Anty Ruqy, ina wuni” Ruqayya ta Harare ta tace “lafiya” daga nan Zara ta kalli Farouq tace “Ya Farouq bari in je inyi karatu ina da test gobe” Gani yayi idanuwan Zara sunyi ja, dan murmushi yayi yace “Okay dear, all the best” Jin ya kirata da dear yasa ta dan zaro idanuwa cikin mamaki yayinda ran Ruqayya ya baci har ta miqe tace “Honey mu tafi” ya miqe suka fita. Zara tana shiga daki ta ji wayar ta tayi qara alaman text message tana dubawa ta ga message ne daga Farouq kamar haka: “don’t you ever miss me again!!” Zaro idanuwa tayi yayinda ta qara karanta message din kawai sai ta fashe da dariya tayi replying din shi kamar haka: “I wont only if I see you everyday big brother, deal??” nan da nan ta ga reply dinshi kamar haka: “deal”. ************* Wani ikon Allah tun daga wannan ranar Zara ta koma yadda take da, abinda take so ta samu, Farouq ya fara kula ta ba kamar da ba. Babu laifi Farouq ya fara replying text messages dinta sannan idan ta kira shi a waya ya kan dauka amma fa baya dadewa domin kuwa surutunta yana damun shi sossai. Hotunan nata ma a yanzu idan ta tura mishi har complementing yana yi. Hatta Mamy ta lura Farouq ya dan fara shiri da Zara ba kamar da ba. wannan abu yayi mata dadi sossai. Hafsat dai a kullum mamaki Zara take bata, batada labarin da ya wuce na Farouq da na Mamy. Mahmood din da take ikirarin tana so ko maganar shi bata yi kamar yadda take maganar Farouq. ************ CENTRAL HOSPITAL Zaune yake a ofis dinshi yana waya da Dr Klose wanda yake qasar Germany.+ Suna tataunawa ne akan wani surgery wanda Dr Klose din zai shiga yayinda yake neman qarin bayani a wurin Farouq. Yana wayar ne ya ga ta shigo ofis din riqe da litattafai a hannunta. Ko da ya kalli fuskar ta sai gani yayi tana kallon shi tana murmushi. Zagayawa tayi kusa da shi ta tsaya tare da ajiye litattafan a gaban shi. Girgiza kai yayi yayinda ya cigaba da Magana a wayar, bayan yayi sallama da Dr klose ne ya kashe wayar sannan ya dago kai ya kalle ta yace “meye na tsaya mun a kai?” murmushi tayi tace “yi haquri Ya Farouq, I wanted to make sure ba da wata kake Magana a wayar ba” hararar ta yayi yace “I will slap you” dariya tayi tace “sorry big brother” Litattafan da ta ajiye a gaban shi ne ya bude yace “yaushe ne test din?” tace “qarfe sha biyu ne” ya kalli agogo ya ga qarfe goma da rabi sannan ya kalle ta yace “I have only thirty minutes, janyo kujera ki zauna” Zara ta zagaya don dauko kujerar yayinda ya sa mata ido. Ji yayi tace “oouch” tare da duqewa ta riqe qafarta. Da sauri ya miqe ya zagaya don ganin abinda ya faru. Dago kai tayi ta kalle shi ta fashe da dariya tace “sorry Ya Farouq bazan iya daukar kujerar ba, tayi nauyi. Please help me” cikin mamaki ya kalli Zara a ranshi yace “she is definately crazy” Tsaki yayi ya dauko kujerar ya ajiye mata ta zauna sannan suka fara. Zara dai wani test suke da shi na maths, course din yana da bala’in wahala sannan idan mutum yayi failing course din carry over zai samu. Kusan sati daya kenan tana roqon Farouq ya koya mata sai yau da za’a yi test din ne yace ta zo. Wani ikon Allah cikin minti talatin Farouq ya koya mata wadanda bata iya ba har tana fadin “ashe ma babu wahala shine muke ta tsoro” Murmushi yayi yace “idan kika yi failing course dinnan I will deal with you” Dariya tayi tace “toh ai bazaka sani ba ko nayi failing” yace “I know your HOD, zan samu feedback daga wurin shi” Zara ta zaro ido tace “dagaske kasan Prof?? ashe ma idan nayi failing zaka iya yi mishi Magana ya…” Miqewa yayi yana daukan wasu files ran shi a bace yace “don’t you try that nonsense” miqewa tayi ta bi shi tace “I wont big brother, wasa nake” ya girgiza kai tare da fadin “all the best, we will talk later” tace “okay Sir, thank you soo much. You are the best”. Yace “i know” sannan yayi mata murmushi ya fita. AL-HUSSAIN MANSION Mamy da Abba zaune a sashen shi suna kallon labaru daddare yayinda suke hirar abinda yake faruwa a qasar Nigeria. Farouq ne yayi sallama ya shigo, da ganin fuskar shi kasan a gajiye yake. Bayan ya gaida iayayen nashi ne ya koma kusa da Mamy ya zauna inda ta kalle shi tace “you look tired my Prince” yace “Wallahi Mamy wani complication aka samu a wani surgery da nayi, we almost lost the patient” Abba yace “Allah sarki, I am glad you were able to save a life” murmushi yayi yace “thank you Sir” Mamy tace “ya jikin Ruqayya fa?” yace “da sauqi Mamy” daga nan kuma suka cigaba da hira. STORY CONTINUES BELOW Farouq ya dauki wayar shi ya tura ma Zara text message kamar haka: “kin ce in zo, gani na zo ban gan ki ba” A lokacin Zara tana kitchen ta ji wayar ta tayi qara. Ko da ta duba murmushi tayi ta tura mishi reply kamar haka: “sorry Sir, gani nan zuwa” Larai ta kira ta hada mata komai a kan dinning sannan ta ruga a guje zuwa sashen Abba. Tana shiga falon Abba ta nufi wurin Farouq ta zauna daf da shi cikin rada tace “Ya Farouq ya aiki? You look tired, what happened?” Shima cikin rada yace “I had a rough day. If not because you asked me to come da yanzu ina gida” Murmushi tayi tace “mu je in baka wani abu” Abba da Mamy ne suka kalli juna suna murmushi yayinda Abba yayi gyaran murya yace “meye ne ake fadi da ba’a so mu ji?” Murmushi suka yi yayinda Zara tace “ba komai Abba, kawai wani abu ne zan nuna ma Ya Farouq” ta miqe tare da janyo hannun shi tace “mu je big brother” Farouq ya miqe yace ma iyayen shi “I will just be back”. Bayan sun fita ne Mamy da Abba suka yi murmushi har Mamy tana fadin “Allah ka nuna mun wannan rana” Abba yayi dariya yace “ameen” Zara tana tafe yayinda farouq yake biye da ita har suka isa wurin dinning din. Tsayawa yayi yana kallonta cikin mamaki yace “yanzu kina nufin saboda abinci ne yasa kika hana ni zuwa gida?” Da sauri ta matsa kusa da shi cikin shagwaba tace “yi haquri Ya farouq, I just want to thank you for helping me with my test today ne” Zama yayi ya kalleta yace “hurry up and serve me before I change my mind” Nan da nan ta bude inda ya hango wani butter milk pie wanda tayi garnishing da straw berries da grapes. 3 Kallonta yayi cike da mamaki yace “who made this?” cikin shagwaba tace “ni ce Ya Farouq, nasan dai kana son desert with little sugar, please kada kace bazaka ci ba” Hannunta ta dago ta nuna mishi tace “ka ga inda na qone” ta sake nuna mishi wani wuri tace “ka ga da nan ma” girgiza kai yayi yace “ eyaah.. sorry amma dai yanzu idan kika qara bata lokaci zanyi serving kaina by myself” Dariya tayi tace “sorry Sir” bayan ta zuba mishi ne sannan ta zuba ma kanta ta zauna. Gani tayi ya sa fork yana ta cinye fruits din da tayi garnishing din butter milk pie din. Ta sani sarai Farouq yana matuqar qaunar fruits don haka ba abin mamaki bane. Da sauri ta qwace fork din daga hannun shi tace “haba Ya Farouq not like this” cikin rashin fahimta yace “toh how?” STORY CONTINUES BELOW Gani yayi ta sa fork ta yanko pie din sannan ta hada da straw berry ta dago ta kai saitin bakin shi. Murmushi yayi ya karbi fork din yace “lafiya na lau, ki bari idan banda lafiya sai ki bani da kanki” Murmushi tayi tace “bana so kayi rashin lafiya but I definitely will love to feed you someday” Dariya ta bashi sossai. Haka dai suna ci tana ta bashi labarin test din da suka yi wanda ita ta fara gamawa tayi submitting. Zara dai surutu take yi amma kwata kwata ma baya jin ta domin kuwa ba qaramin dadi desert din yayi mishi ba. Gaba daya sai da ya cinye shi tas sannan ya kalle ta yace “i really enjoyed this, tanx alot” tayi murmushi tace “anything for you big brother”. Tare suka koma Falon Abba inda suka dan taba hira sannan yayi musu sallama. Har motar shi Zara ta raka shi wanda tayi ta jan shi da hira kala kala. Wasu hirarrakin ma baya ganewa. Shi dai kawai idanuwa yake zuba mata. Da qyar ta sallame shi ya tafi gida. Farouq dai ko da ya je gida bai bi ta kan abinci ba domin kuwa dama ba son irin abincin da ake bashi yake yi ba. BAYAN WATA DAYA AL-HUSSAIN MANSION Abba ne zaune a falon shi tare da Mamy da Zara. Farouq ne yayi sallama wanda dama shi ake jira domin kuwa Abba ya kira shi akan idan ya kammala abinda yake yi ya zo. Bayan ya gaida iyayen shi ne ya zauna yayinda Zara take ta kallon shi har sai da yayi mata alamar “what??” Da hannu. Murmushi tayi mishi tare da kashe mishi ido wanda shima yayi murmushin tare da girgiza kai. Abba ne yayi gyaran murya yace “Farouq dama na kira ka ne don in sanar da kai ina da wani convention da zan halarta a London jibi, tare da Mamy zamu tafi don muna so muyi visiting din Sadiq daga nan” Zara ce tace “Abba tare zamu je??” murmushi yayi yace “no princess, ba kun kusa fara examz ba kika ce?” a sanyaye tace “eh Abba” Ya kalli Farouq yace “shiyasa na kira ka don in sanar da kai, Zara zata zauna a gidan ka har sai mun dawo saboda bazamu tafi mu bar ta a cikin gidan nan ita kadai ba, ina ganin bazamu wuce wata daya ba” Farouq ne ya kalli fuskar Zara wadda hankalin ta ya tashi sannan ya kalli Abba yace “its Okay Abba” Ji sukayi Zara tace “Abba ni bazan je gidan Ya Farouq ba” cikin mamaki dukkan su suka kalle ta yayinda ta murtuke fuska. Mamy tace “why princess?” ta kalli Farouq tace “ni fa Anty Ruqy ba wani sona take yi ba” Abba da Mamy suka fashe da dariya yayinda Farouq ya dauki wayar shi ya tura mata message kamar haka: “kin tabbata ba tsoron ta kike ji ba?” Wayar ta da tayi qara ne ta duba ta karanta message din. Da sauri ta kalle shi yayinda ya bata rai kamar ba shi ya aika mata message din ba. Daddy ne yace “haba princess, ya zaki ce Ruqayya bata sonki? Me kika yi mata da zata tsane ki? Gidan Farouq zaki zauna and bana so in ji wata Magana kuma” Cikin damuwa tace “toh Abba” anan dai suka cigaba da labarin tafiyar nasu yayinda Zara tayi shiru tana sauraron su. Farouq ya fahimci lallai Zara bata son zuwa gidan shi. shi kanshi ya san cewa ba qaramin matsala za’a samu ba domin kuwa kamar yadda ta fada cewar Ruqayya bata sonta tabbas haka ne. abinda dai ya sani shine zai yi qoqarin ganin cewa ya kauda rigima a tsakanin su. Shin zai iya????? 🙄 Bayan Farouq yayi sallama da iyayen shi ne ya miqe ya fita. Wayar zara ce tayi qara alamar text message. Ko da ta duba miqewa tayi ta fita yayinda ta same shi a waje. Zaune yake a cikin motar shi yayinda qafar shi daya take waje. Ko da ta iso wurin shi kallonta yayi yace “me yasa kike tunanin Ruqayya bata son ki?” Cikin shagwaba tace “nima ban sani ba, qila saboda kai ne” murmushi yayi yace “ni babu ruwana” Zara tace “Ya Farouq kullum fa harara ta take” yace “kema ai kullum hararar ta kike yi, na sha ganin ki ai” Shiru tayi tana turo baki yayinda ya sa qafar shi a cikin mota yace “ki shirya kayan ki, you are coming with me tomorrow” bai jira jin abinda zata ce ba ya rufo qofar shi sannan ya tada motar shi yayi tafiyar shi. Zara ta koma dakinta ta kira Hafsat a waya ta fadi mata abinda ya faru. Me kuwa Hafsat zata yi banda dariya. Zara wadda ran ta yake a bace tace “dariya ma kike yi mun?” Hafsat tace “sorry babes, meye abin damuwa anan? Ba dama nema kike ki taka mata birki ba? this is your chance” Zara tace “ni fa tsoron ta nake babes” Hafsat ta fashe da dariya tace “you are funny my friend, kar ki bani kunya mana. Dadin abin ma yanzu kuna shiri da Ya Farouq, I am sure he will watch your back” Haka dai Hafsat ta cigaba da lallashin ta har suka yi sallama. Ko da Hafsat ta ba Mukhtar labari ya sha dariya har yana fadin “ashe akwai drama a gidan abokina”. FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION Zaune suke a kan dinning inda suke breakfast. Ruqayya ce tace “Honey anjima zan je in dubo Hajjaju. Kwana biyu ban je ba saboda rashin lafiya da nayi. Girgiza kai yayi yace “no problem, amma driver zai kai ki ko?” murmushi tayi tace “No, zan iya tuqawa ai. I am much better yanzu” Shiru ya danyi sannan yayi gyaran murya yace “uhm na manta ban fada miki ba, Mamy da Abba zasu yi tafiya so idan kina dawowa daga gidan Hajjaju zaki iya zuwa kiyi musu sallama” tace “toh Honey” Farouq ya cigaba da fadin “while they are away Zara zata dawo nan gidan…” Tun kafin ya qarasa maganar shi ta miqe cikin tashin hankali tace “what??? Gaskiya ba dai gidan nan ba, ka sani sarai Zara bata jin Magana kuma ma…” Dakatar da ita yayi yace “I am not asking you for permission I am simply telling you” Ya miqe yayi mata kiss a goshi yace “sai na dawo, take care” ya fita abinshi. Ruqayya dai haka ta tsaya tana kallon shi cikin tashin hankali da bacin rai har ya fita. Dafe kai tayi ta fashe da kuka tace “wallahi baku isa ba, ni za’a kawo ma ‘yar iskar yarinyar nan ta zauna mun a cikin gida?” Da gudu ta ruga sashen ta don shiryawa. A yau dinnan dole ne su koma gidan boka cika aiki. Asali ma dalilin da yasa basu je ba bayan Hajjaju ta dawo daga Dubai saboda samun cikin nan nata ne da dan zazzabin da ta dinga yi kwana biyu sannan ta kula Farouq yana nuna damuwa akanta ba kamar da ba. A yau ko da rarrafe ne sai ta je wurin boka cika aiki domin bazata amince da zaman Zara a gidanta ba. ************