ITA CE QADDARATA CHAPTER 14

ITA CE QADDARATA CHAPTER 14 W

ashegari wajen k’arfe 12 na rana suka had’a kayansu, Ya biya kud’in kwanakin da sukayi a hotel suka koma Hausawa.+ “Noor sai kinyi hak’uri da sabuwar rayuwar da zamu fara anan, kinga bamu da kowa nan sai Allah bamu San kowa ba, sana’ar provisions ce zan fara har muga abunda Allah zai yi, amma na miki alk’awari zan rik’e ki amana, zanyi iyakacin k’ok’arina wajen ganin na faranta miki kuma na kula dake” Murmushi tayi tace “Allah ya baka iko, Allah kuma ya bamu zaman lafiya” “Ameen my angel” Tashi yayi Yace “zan fita shago” “Allah ya Bada Sa’a” “Ameen”, Ya fice Ta bishi da kallo tana murmushi sonshi na k’ara shigarta. Gidan ta share ta goge ko’ina, Ta Shiga kitchen ta d’aura abinchi, Jollof d’in Taliya da kifi, Gidan ya game gaba d’aya da k’amshin girkinta, Da ta dahu tasa a kula, ta ajiye, Wanka tayi tasa wata atamfa lemon green d’inkin doguwar Riga, Tayi kyau sosai tana ta rambad’a k’amshi, ta zauna shiru tana tunanin yadda rayuwarsu zata kasance da Imran har ta fara tausayinshi dan bai Saba wahala ba. Sallamarshi ta katse mata tunani, Da murmushi d’auke a fuskarta ta amsa mai sallamar, Kusa da ita ya zauna, k’amshin turarenta nata dukan mai hanci, Ya shafi fuskarta Yace “kinyi kyau my angel”, Kunya ta kamata ta sunkuyar da kanta k’asa tace “bari na kawo ma abinchi”. Har ta mik’e ya jawo hannunta ta fad’o kan cinyarshi, “Zauna ban gaji da kallonki ba, ko bani kika ma kwalliyar ba”, Wata kunyar ta sake kamata bata bashi amsa ba sai k’ok’arin sauka daga cinyarshi da take, ya sake matseta Yace “anan nake so ki zauna, nifah mijinki ne dan haka ki cire wata kunya gefe”. Hannunta ya Kama yana murzawa a hankali, har lokacin bata ce komai ba, Kissing hannun yayi, Yace “I Luv ur fingers they are so cute”, Noor wani shock taji ta kasa ko da k’wakk’waran motsi, “Jeki d’auko abinchin muci tare”. Mik’ewa tayi jiki a sanyaye ta nufi kitchen, kular abinchi ta d’auko da plate,spoon da ruwa, Ta zuba abinchin ya sauka daga kan kujera, Yana ci yana bata a baki har sai da suka cinye wanda ta zuba a plate d’in tas. “My angel kin iya girki sosai” Tana murmushi tace “Thank you”, “Sai yanzu aka ga damar yi min magana” Bata ce komai ba tashi ta kwashe kwanukan, Yace “ni zan koma shago ki kular mun da kanki”, “Toh ina so zan Shiga mak’ota mu gaisa” “Amma kar ki dade” Ta gyada kanta sama alamar toh Hijabinta tasa, ta Shiga gidajen dake compound d’in, Gidan dake kusa dasu itama Amarya ce sunanta Ameerah, satinta biyu da tarewa, da kad’an ta girmi Noor, sunyi hira sosai Noor taji dad’in haduwa da ita, itama taji dad’in had’uwa da Noor, Da zata tafi ta bata turare Mai bala’in k’amshi ta rakota tace sai tazo. Imran bai shigo gida ba sai k’arfe tara, Noor har ta gama abincin dare tayi wanka tasa doguwar riga ta bacci ta fesa turaren da Ameerah ta bata, Tana d’aki kwancen kan katifa, Ya shigo k’amshin turarenta ya dakar mai hanci, sai jinshi tayi ya rungumota ta baya, a kunne ya rad’a mata “You scent nice I Luv you so much” Ya Fara kissing d’in wuyanta, bata hana shi ba, runtse idonta kawai tayi, tana jin dad’in hakan, ba tare da ta juyo ba, Ya Kai minti biyu yana kissing d’inta har fuskarta, A kunne ya rad’a mata ki had’a mun ruwan wanka, jikinta duk ya mutu ya sakar mata kasala, ta mik’e ta nufi kitchen, Imran ma wata irin kasala yake ji yaso ace ya zarce but duk da haka ya rage wani abu da yake ji a kanta, lumshe ido yayi sonta na k’ara shigarshi. Yayi wanka yasa kayan abinchi, ya kwanta kusa da ita dan har tayi bacci, Ya d’aura kanta kan k’irjinshi, a haka sukayi bacci. Da asuba ta farka ta ganta kwance kan k’irjinshi, murmushi tayi tace “I Luv u soo much Imran”, Ta mik’e kenan taji mararta ta masifar murd’awa, ta durk’ushe anan k’asa tana murk’uk’usa tana kuka da fad’in sunan Allah, Sautin kukanta yasa Imran farkawa a firgice, Yayi kanta ya rik’ota ya rungumeta yana tambayarta ” Me ya sameki?” , Kasa magana tayi sai mararta da take rik’ewa, Cike da tashin hankali Ya kwantar da ita kan katifa, Ya fita kamar mahaukaci, Mijin Ameerah ne ya ganshi Yace “lafiya na ganka haka?”, “Wallahi matata ce bata da lafiya, Dan Allah ka taimaka ka kaimu asibiti da motarka”, Yana ta zufa “Muje in dubata nima Doctor ne” “Alhamdulillah, muje toh” Noor nata mirgina a k’asa, Imran ya d’agota yana hawaye, Dr ya duddubata yaje ya d’auko allura ya mata, Yana mata bacci ya d’auketa, Ya kalli Imran Yace “Matarka na fama da matsalar ciwon mara, wanda wasu matan keyi idan zasuyi al’ada toh ita abun ya had’e mata hadda k’arfin sha’awa da take dashi, da za’a samu ko sau d’aya ne to zata samu sauki sosai, Amarya ce hala?” “Eh Doctor” “Ok Allah ya bata lafiya” “Ameen Ameen” Maganguna ya mik’o mishi Yace “Inda ta farka taci abinchi sai ka bata tasha, ta kiyaye shan maganin kan lokaci” “In shaa Allah, nagode sosai Dr” “Nawa ne kud’in maganin” “A’ah kar ka damu da wannan” Imran ya mishi godiya sosai, Ya rakashi ya dawo, Kanta ya d’aura kan cinyarshi yana shafa mata marar a hankali, tausayinta duk ya cikashi. Awarta biyu tana bacci kan cinyarshi, ko motsi baya son yi dan kar ta tashi, ido kawai ya zuba yana kallonta, A ranshi yana cewa ya d’auki alk’awarin zai kula da ita da k’arfinshi da lafiyarshi, He will always be by her side nomatter the situation, Tana farkawa suka had’a ido da Imran, Murmushi ta mishi shima ya mayarta.+ Tashi tayi zaune “Ya jikin naki?” “Da sauk’i” ta bashi amsa “Bari na had’a miki ruwaan wanka” Da ya had’a ruwan, d’aukarta yayi ya kaita har toilet, Yace “Zaki iya cire kayan ko in cire miki” Da sauri tace “zan iya” Tsayawa yayi yana jiran ta cire ya mata wankan. “Ya dai?” “Kai nake jira ka fita” “Bakya so in miki wankan?” “Zan iya da kaina” Ba musu Yace “okay”, Ya fice. Restaurant yaje ya siyo mata takeaway na chips da k’wai, ko da ya dawo har ta fito daga wankan ta shirya, Plate ya d’auko ya juye chips d’in, ya had’a mata tea kakkaura yaji madara da Milo, A baki ya rik’a bata, Spoon biyar yana bata bai ci ko sau d’aya, Na shidan da zai bata tace “kai ba zaka ci bane?” Yayi murmushi Yace “naci nawa kina bacci”, “Uhmm shine baka jirani mun ci tare ba” “Am sorry my angel, yunwa nake ji sosai” “Da ka tasheni ai” “Bana so na tasheki kina bacci, kanki yayi ciwo” “Uhmm nima sai na rama” “My angel rigima” Ya cigaba da bata har sai da tace ta k’oshi, Ya bata tea d’in ta sha tare da magungunanta, Sauran chips d’in da ta rage ya zauna a kitchen yaci dan muguwar yunwa yake ji, idan dai ita taci, ko da shi bai ci ba, bai damu ba, D’akin ya koma ya jawota jikinshi ya rungume yana shafa gashin kanta a hankali, sun dad’e a haka ba mai cewa kowa komai, Noor tace ” ba zaka shago bane?” “idan na tafi shago wa zai kular mun dake?” “Ai naji sauk’i” “Uhmm.. Korata dai kike” “A,ah fah na isa na koreka, bana so ne kana wasa da aikinka” “ok kula da matata shine wasa da aikina” Dariya tayi tace “toh zauna” “Bazan zauna ba nayi fushi sai na tafi, sai ki zauna ke kad’ai tunda haka kike so”, Noor dariya tayi a ranta tace “ba zan iya da rigimar Imran ba” Fita yayi shi a dole yayi fushi, Pillow ta jawo ta rungume tana murmushi a ranta tana cewa “Ashe lokaci zai zo da Imran zai zama nawa, Allah nagode ma da ka bani Imran a matsayin mijina”. Naseer yana ta jiran kiran Imran shiru, da yaga sabuwar number an kirashi zai d’auka Imran ne, har ya fidda rai yana addu’ar Allah yasa lafiya, Kano babban gari balle yaje nemanshi, Imran bai kyauta mai ba amma yasan duk daren dad’ewa watarana dole ya dawo gida, Yayi missing Imran sosai bashi da aboki kamar shi. Hajiya kullum bata da aiki sai kuka ita dai Imran, Alhaji na k’ok’arin kwantar mata da hankali yace mata Imran zai dawo, su Ihsan ma kullum cikin lallashinta suke amma inaa bata fasa ba, Khairat tayi kuka kamar ranta zai fita but duk da haka bata cire ran auran Imran ba, komai daren d’ad’ewa sai ta aure shi. Yazeed ungulu ta koma gidanta na tsamiya ya koma halinshi na bin mata da zuwa club, yanzu har shaye-shaye yake, ba kullum yake kwana gida ba, Alhaji bai fasa sana’ar caca ba, kud’inshi sai k’ara habb’aka suke, Mahaifin Noor shima dukiyarshi sai k’aruwa take ta hanyar caca, Yama manta yana da wata ‘Ya Noor, sai cin duniyarsu suke da tsinke shi da mummy da ‘ya’yanta. Ranar da tayi wankan tsarki, tana zaune kan sallaya, ta idar da sallar la’asar, Imran ya shigo ganinta kan sallaya yasa shi jin wani sanyi a zuciyarshi dama ya k’osa tayi wanka, Kan gado ya zauna yana jiranta, Ta gama addu’o’inta sannan ta juya gareshi tace “Sannu da zuwa” “Yawwa my angel, ina zaune shago naji ke kad’ai nake son gani” Dariya tayi Yace “Ganin kyakkyawar fuskarki yasa naji sanyi a raina” Ya taso ya k’araso inda take, Kiss ya mata agoshi “Ina sonki my angel kece farin cikina” Ya kamo hannunta ya had’a da nashi “kimun alk’awari ba zaki tab’a barina ba” “Ina tare dakai duk wuya duk runtsi, I will never leave ur side, I will always Luv u ” Rungumeta yayi dan d’ad’in furucinta, Yana rad’a mata sweet words a kunne, Ya saketa yana shafa fuskarta “Zan koma shago amma ki sani kina zuciyata har inje in dawo” “Nima kana tawa” Ya mata peck a kumatu, Ya juya fuskarshi Yace, “Nima kimun” Kunya taji ta kasa yi “Kimun mana ko kina so nayi fushi” Da sauri da girgiza kanta “Oya am waiting” Ta rufe idonta tai mishi peck Ta ruga da gudu cikin toilet, Dariya yayi ya girgiza kai “Yau d’in nan zan cire miki kunyar nan” Wajen k’arfe tara ta gama abinchin dare, tayi wanka tasa kayan bacci, bayan ta feshi jikinta da turaruka masu bala’in k’amshi, Ta kwanta kenan taja bargo, Imran yai sallama ya shigo, amsa mishi sallamar tayi daga kwance, “Har kin kwanta my angel” “Na gaji ne na kwanta in d’an huta” “Ok sannu ko inzo in miki tausa” “A’ah na hutar da kai, kaima nasan ka gaji” “Ba wata gajiya” “Toh ni dai na hutar da kai” “Toh ni sai na miki, bari nazo” Ledar dake hannunshi ya ajiye, Ya Shiga toilet ya watsa ruwa ya fito, jallabiya yasa ya fesa turaruka masu k’amshi, Tashi tayi ta d’auko abinchi da zob’o mai sanyi. Yana bata a baki tana bashi, sai zuba santi yake ita dai tana ta murmushi dan ta gane santi yake, Da suka gama ta kwashe kwanukan ta wanke. Ledar ya bud’e, kaza ce k’atuwa guda d’aya sai k’amshi take, “My angel ga kazar ki ta amare da baki ci ba” Tana dariya tace “kazar amarya sai yau, na yafe” “Baki isa ba kuwa” “Toh shikenan zamu gani” Ya marairaice murya “Haba my sweet angel kar muyi haka dake, zo kici” Ganin yadda ya marairace yasa tazo, Kan cinyarshi ya d’aurata yana bata kazar kamar wata Baby, “Kai baka ji toh” ta fad’a a shagwab’e “Kina so inci” “Eh” ta bashi amsa tare da d’aga kanta sama “Ta bakinki nake so” Ta tsaya tana mai kallon ban gane ba, D’aga mata gira yayi alamar Yes, Ya yago kazar wajen tsoka Yasa mata a baki “Tsotsewa zakiyi kar ki tauna” Tsotsewar tayi, ya bud’e baki Yace “Samun, da bakinki Zaki Samun” Naman ta turo daga bakinta ta sa Mai, “Uhmmm….wow its taste delicious saboda ya fito daga bakin ki” Noor mamakin salon soyayyar Imran take, “What are you thinking of?” Ya katse mata tunani “A haka Zaki cigaba da bani har sai na k’oshi” Noor ba musu idan ya sa mata nama, Ta tsotse ta sa mishi a baki, Suna ta haka tare da k’ara jin so da k’aunar junansu. Sai da Yace “Ya k’oshi” ta daina bashi “Mik’e k’afa in miki tausa” “No ka barshi na hutar dakai, kai dai zaka mik’e k’afa in maka” “Naji Zaki mun amma sai na miki”+ Mik’e k’afa tayi dan bata so su cigaba da musu, Tausa ya fara mata a hankali har kan cinyarta, Noor har lumshe ido take saboda dad’in tausar, Ba tausa kad’ai ya tsaya ba, Romancing d’inta ya fara, sai da su duka suka fita hayyacinsu, Ya d’auketa sai kan katifa, Noor tasha kuka tana rok’on Imran amma ina bai saurara mata ba, Rungume yake da ita tana mishi kukan shagwab’a, Sonta yake ji na ratsa dukkan sassan jikinshi, matsayinta ya k’aru a zuciyarshi, Yana ma Allah godiya da ya bashi Noor a matsayin mata, Farin cikin da ya tsinci kanshi a yau ba zai misaltu ba. Ruwan zafi ya had’a ya mata wanka, bayan yasa ta zauna cikin ruwan zafi, Ya shafa mata mai yasa mata Kaya, Ta Saki jiki dashi a cewarta zance kunya ya k’are tunda ba daren da jemage bai gani ba, Ranar ko bakin k’ofa Imran bai fita ba, Yana manne da Noor yana tarairayarta, ita kuwa sai langab’ewa take tana zabga mishi shagwab’a, Kwance take kan cinyarshi yana shafa kanshi ganta “My angel yau dai shagwab’a kike ji” Ta tab’e baki tace “Toh ba kai bane uhmm” Ya shafi fuskarta “Am sorry darling hak’k’ina na karb’a, anjima ma zaki bari na karb’a koh?” ya wani langab’ar da kai kamar k’aramin Yaro, “Tabb hu’um lallai ma” “Haba babyna” “Ni ka daina mun maganar bana so” Ta k’arsa maganar kamar zata yi kuka “An daina gimbiya” Wata hirar ya d’auko, suna ta hirarsu ta masoya Haka suka cigaba da rayuwarsu cikin so, k’auna da kulawar juna, Kowannensu bashi da buri da ya wuce ya faranta ma d’aya, Imran kullum cikin yin abunda zai faranta ma Noor raina yake, itama haka duk abunda zai faranta mai rai shi takeyi. Sun Saba sosaii da Ameerah, itace k’awar shawarta, duk wasu maganin mata da na gyaran jiki Ameerah ce ke bata, shiyasa duk lokacin da Imran ya kusanci Noor sai yaji kamar yau ya fara saninta, Noor ta tsare tsarki da Magarya( Magarya nada matuk’ar amfani tana wanke duk wani datti na gaban mace, tana hana warin gaba) kuma bata tsarki da ruwan sanyi dan yana lalata mace. Yau da gobe, kudi’n da Naseer yaba Imran sun k’are, Cinikin da yayi a shago da kud’in suke cefane, Nama ba kullum suke sawa a miya ba, Noor bata tab’a nuna ta damu ba, kullum k’arfafa ma Imran gwiwa take kan Neman halal d’inshi, da kwantar mai da hankali watarana sai labari. A radio Imran yaji ana sanarwa, Makarantar CENT LOUIS za’a yi jarabawa duk Wanda yaci za’a bashi scholarship hatta books bazai siya ba duk school d’in ce zata bashi, Yana shigowa gida ya sanar da Noor, Tayi murmushi tace “Banda abunka ina ni ina cin wannan jarabawa” “Jarabawa Sa’a ce sai kiga kinci” “Ni dai abar zancen nan dan nasan ba ci zanyi ba” “Me yasa kike saurin given-up, never give up in life, Duk yadda kike son yin Karatu, baki da buri da ya wuce kiyi Karatu but you can’t fight for yourself, Noor try, I will support you 100% wajen ganin kin cimma burinki , kar kiyi turning d’ina down” Shiru tayi na seconds tana nazarin maganganun Imran tabbas gaskiya ya fad’a, bata da wani buri da ya wuce tayi Karatu ta zama Lawyer Mai kare hak’k’in al’umma, “Na yarda, Allah ubangiji yai mana jagora” “Ameen my angel haka nake son ji” Yai mata peck a kumatu, itama ta mayar masa. Da k’yar ya samu ya had’a dubu biyun da ya siyan mata form na scholarship d’in makarantar, Ya cika yayi submitting, Jarabawar Maths, English da government ne zatayi, Yan science kuma suyi Maths English da chemistry, Mutum uku da suka fi kowa marks su za’a ba scholarship, Imran ya dage kullum yana ma Noor lesson, Da ya koya mata nan da nan ta d’auka, Idan yana shago tai ta practising. Ana washegari jarabawar daga Noor har Imran basuyi bacci ba, Sallar dare suka kwana yi suna rok’on Allah, Washegari tunda safe Imran ya kaita har makarantar, Gabanta nata fad’uwa ta shiga exam hall. Jarabawar ta mata sauk’i sosai, Ta fito tana ta far’a, Imran na waje na jiranta, ya tambayeta “Ya Jarabawar?” “Tayi sauk’i, Alhamdulillah” “Allah ya Bada Sa’a, yasa result yayi kyau” “Ameen” Kwana biyu da yin jarabawar, Result ya fito, Noor tafi kowa marks, Farin ciki wajen Imran da Noor ba’a gama hadda kukan dad’i Noor tayi. An bata uniform da books, hadda sock da sandal duk su suka bata, SS3 aka kaita maimaikon ss2, Ranar da zata Fara zuwa Imran ya mata nasiha sosai, Yace ba ruwanta da kowa, abunda ya kaita shi kad’ai zatayi ta dawo, Shi ke kaita a keke napep yana d’aukota, Sai ta tuna lokacin da yake kaita a had’add’iyar motarshi, motoci gasu nan sai wacce ya zab’a, hadda k’walla tayi na tausayin Imran, Rayuwa kenan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *