BATUUL
CHAPTER 17
Sulalewa kasa tayi wasu hawaye masu d’umi na bin kuncinta bayan tayi recover daga shock din da ta tafi na kusan minti goma, ta kai minti ashirin xaune nan gun ta kasa motsi, so take kawai taji wani yace mata a mafarki take jin duk abin nan da ya faru a while a ago, kuka ta fashe da da karfi, wanda hakan ya tabbatar mata ba mafarki takeyi ba, komai a zahiri yake faruwa, ba gizo kunnenta ke mata, sai a lokacin taji zuciyanta na bugawa kamar mai shirin fitowa, a hankali ta shiga girgiza kai tana tariyo duk abinda ya faru kanta, yanzu duk wannan abinda Abu ya fad’a mata duk gaske ne, Batuul matar Abu ce, ji tayi zuciyarta na shirin fitowa don wani irin bugu yakeyi da ya tsorata ta, a hankali ta kai hannu kan fuskarta ta shafo hawayen dake ta kwaranya ba tareda ta shirya fitowansu ba, maganganun Abuturrab ne ya rik’a dawowa a hankali yana mata yawo kwakwalwarta “kika kuskura ki sake tab’ata ko kika yi gigin k’iranta da karuwa sai na hallaka ki wllh, don matsayinta d’aya yake da naki a gidan nan, “Let me tell you what you don’t know jiddah, kamar yadda kike matata a gidan nan, toh haka Batuul ma take matata ta sunna, snn cikin dake jikinta ba na kowa bane, nawane” wani irin ihu ta saki tana toshe kunnuwanta ta fad’a k’asa tana rik’e da kanta tana birgima kamar wata yarinya, gaba d’aya ta fita hayyacinta sai ihu takeyi, abunka da farar fata har ta canja kamanni tayi jajir, tun ranar da ta fara ganin Batuul a gun graduation d’insu har aka sashi yin pictures da ita kawae ke tariyo mata, ranan dinner d’insu da ya d’aukota a motarshi, ranan da ya dawo mata da Batuul gida wai karatu tazoyi har yau da ya bud’i baki yake ce mata Batuul matarsace kuma shi keda cikin jikinta, wani abune taji ya tokare mata mak’oshi ta rintse ido ta bud’e jikinta ya dau rawa, wani kara ta kuma saki tace “Inaaaa, Bazai yiwu ba wlhy, zakuyi dana sanin rainamin hankali da kukayi daga ku har iyayenku, bakusan wacece Ajiddeh ba, Aliyu sai na sa kayi dana sanin cin amanata da kayi wlhy, ita kuma tsinanniyar nan wlhy na rantse sai ta d’and’ani azaba da zata gwammace gara ta mutu da ita snn in aikata Lahira da ita da shegen dake cikinta, wlhy sai nasa na Lahira ya fiki jin dad’i, da haka ta mik’e ta haura sama da k’yar dan ji take zuciyarta kamar zata fito ga wani mugun jiri da take gani, tunda take bata taba shiga tashin hankali da rudani irin na lokacin ba.
+
Shi kam yana haurawa sama, kan gadon d’akin da yake kwana ciki yanzu ya kwantar da Batuul da kanta yake a d’aure, gaba d’aya jiri ke damunta, idonta taf da hawaye, k’ok’arin rage mata kayan jikinta ya shiga yi, dukda bata jin k’arfin jikinta hakan bai hanata rik’e rigan ba, lumsassun idanunshi ya sauk’e kan fuskarta yace “stay still or I slap you”, ture hannunshi tayi daga jikinta tace “Ni ka bari sanyi nakeji”, mik’ewa yayi yaje ya kaso ACn d’akin ya dawo ya zauna kan gadon, kallonshi kawai Batuul keyi har saida yayi noticing d’in kallon ya d’age girarshi d’aya yace “Anything”, d’auke kanta tayi daga kallonshi ta rintse ido, gaba d’aya maganganun da Ajiddeh ta fad’a mata ke dawo mata yanzu, “In kana tunanin ni xa ayi ma wasa da hankali kayi karya Aliyu, don zaman karuwan nan ya k’are gidan nan, Munafuka algunguma, ashe karuwanci kike yi dama, toh yau Allah ya toni asirinki, iskanci ba a gidana za ayishi ba dan ban gada ba, a tafi can inda aka saba aci gaba dayi, Dan ni dai kam ban zama da mai cikin shege a gidana, k’arshen karuwanci dai yau ya k’are gidana, aje gaba aci gaba daga inda aka tsaya”, idonta taf da hawaye take kallonshi, a hankali ta bud’e baki tace “I don’t get abinda matar ka ke cewa, waye mai ciki a gidan?” jin tambayar da ta mishi yasashi juyowa yana kallonta, had’e rai yayi yace “wane cikin? were you eavesdropping?”, had’e rai tayi itama ta harareshi tace “Ba ina wajen ba naji ta fad’a”, had’e rai ya sakeyi yace “look! Lie down and sleep, bana son shirme”, daga haka ya Shiga k’ok’arin kwantar da ita, ture hannayenshi ta shiga yi tana kokarin saukowa kan gadon tace “I have classes today, ni zan shirya in tafi” ta fad’a tana k’ok’arin sauk’a daga kan gadon, jiri ne ya d’ebeta tayi baya zata koma yayi sauri ya jawota jikinshi yana mata wani irin kallo yace “ina miki wasa ko, I will slap you if you dare move an inche daga nan”, da k’arfi ta shiga janye jikinta daga nashi tace “Nikam ka kyaleni, I told you school zanje, av missed a lot”, har lokacin yana rik’e da ita yace “You are going no where,” kuka ta fashe mishi da tace “nikam sai naje, kuma zan fad’awa Ammah baka barin ina xuwa makaranta”, kallon fuskarta yakeyi yanda hawaye ke kwaranya daya na bin d’aya har cikin ranshi yakejin kukan da takeyi, ji yakeyi kamar zaiyi affecting abinda ke cikinta, yace “not just today, daga yau baki sake fita ko ina, and dare going anywhere kiga abinda zan miki”, birkice mishi tayi tana kuka ta shiga dukan k’irjinshi tana turashi ya saketa tace “I knew it dama you are always against my happiness and you will surely stop it someday, gashi yanzu ka fara da hanani zuwa school, why? What have I done to you to deserve all this, why why why me?”, rintse ido yayi dan ji yakeyi ko improper motsi tayi wani abun zai sami babyn cikin dake jikinta, a hankali ya bud’e lumsassun idanunshi da har sun fara canja kala, shoulders d’inta yayi gripping firmly yana kallon face d’inta da ya jik’e da hawaye da d’an k’aramin lips d’inta da ya sake rinewa saboda kukan da takeyi, cikin husky voice d’inshi in a serious tone yace mata “Fatima you are carrying my baby, I can’t risk losing my child, zaki koma school bayan kin haifa min babyna”, ya sassauta muryanshi ya kamo fuskanta yace “I promise you zaki koma school kinji Fatima, for now kiyi hakuri I need to take care of my child and in kina zuwa school you will b stressed har yayi affecting babyna kuma bazan samu time d’in kula da Babyna ba, kinji”, ya fad’a yana d’an kad’a kanshi yana son yayi convincing d’inta, tsit tayi tana kallonsa da mamaki fuskarta, baby kuma, which baby is he referring to, kamar yasan tunanin da take a hankali yace “Yea our baby!” Wani matsanancin kuka ta fashe da, wato ita ce me cikin da Ajiddeh ke nufi, jawota yayi ya shiga lallashinta, wani haushin shi kawae ta dinga ji a lokacin, kenan wannan aman da take tayi da bacci duk cikin ne ya jawo mata, ita da anytime sooner or later take tunanin zai maidata gida shine wai itace harda haihuwa, d’an k’aramin tsaki yaja daga ciki jim kamar ana d’ada tunxurata, yarinyar nan na birkita mishi kwakwalwa ba kadan ba, ko shirmen da Ajiddeh ta gama yi mishi bai d’aga mishi hankali ba kamar yadda kukanta ke yi ynxu, duk wani motsi nata yanzu a ranshi yakeji, rungumota yayi jikinshi sosai a kunnenta yace “Batuuul mana, its okay tell me, duk mey kikeso zanyi miki shi, I promise”, har ranta taji yadda ya k’ira sunan nata, this is his first time calling her Batuul, shi baima san ya fad’i ba, a hankali ya sassauta rik’on ya d’ago hab’arta yana kallon fuskanta yace “kinji?”, bata bashi amsa sai tambayar da ta jefo mishi tana shessheka tace “zaka maidani gidan Aunty in na baka babyn ka toh?”, ya kai 2mins yana kallonta jin mey tace, it caught him off guard, lumshe ido yayi ya bud’e sannan yace “will that make you happy?”, kai ta gyad’a mishi, yace “Fine, but for the time being xakiyi duk abinda nace, babu arguments, zaki barni in kula da Babyna dake kanki, you will do everything as I say, and then we will b best of friends, babu tsiwa kuma”, da sauri ta shiga gyad’a mishi kai tace “na yadda, kuma dama ai can ni bana tsiwa”, yace “That’s my girl, I will do that for you”, murmushi ne yayi escaping lips d’inta ta dunk’ule hannunta tare da miko mishi tace “Deal?”, shima murmushin yayi ya miqo nashi hannun yace “Deal”, janyota jikinshi yayi daga haka ya shiga kissing lips d’inta da suke tempting d’insa passionately
Ajiddeh na shiga d’aki ta shiga k’iran Aunty Jainaba dake airport waya, kamar zatayi hauka haka ta riqa ji a ranta, abunda kawai zai kawar mata da damuwarta take nema, wani zuciyar ke raya mata kawai ta tashi taje ta shak’e Batuul d’in har sai ta bar numfashi snn ta saketa inma yaso itama a kashetan, har wayan ya gama ringing ya katse ba a d’auka ba, jefar da wayan tayi zataje yin abinda zuciyarta ke raya mata har wani rawa jikinta yake, tana kaiwa bakin k’ofa taji wayar na ringing, komawa tayi ta d’auka, Aunty Jainaba na d’auka, cikin rawan murya tace “What time jirginku zai tashi?”, jin yadda muryan Ajiddeh yake yasa tace “Ke Ajiddeh, shafa min, ya aka yi da xancen cikin?”, har a mak’oshinta taji ambaton cikin da Jainaba tayi bata ansa mata ba saima cemata da tayi “ki dawo ki fasa tafiyar yau, gobe zamu tafi tare”, da sauri Jainaba tace “keh kuwa mai ya faru da zaki taho gobe, ki fad’amin an tabbatar muku cikin ne da ita?”, ta fashe sa kuka ta xube kasa kamar yarinya tace “na shiga uku Anty, wayyo ni, matarsa ce, cikin jikinta nashine”, Jainaba batasan lokacin da ta miqe ba daga zaunen da take tace “Kinada hankali kuwa?, kinsan mey kike cewa ma?, banason shirme, wannan bak’ar yarinyarce matarshi?, kamar xata shide don kuka tace “haka yace min Anty kuma baya karya, he was so serious, har marina yayi antyy” Jainaba na huci xufa na karyo mata tace “rabu da d’an abu kazan uba, karya yakeyi munafiki, asirinta kawai yakeson rufewa, amma duk sai sunci ubansu, ina komawa gida za a san yadda za ayi, ki kwantar da hankalinki zamuyi maganinsu, karya ma wllh yake maki, kar ma ki bi ta Kansu, ki maidasu kamar bakisan suna nan ba”, haka tayi ta convincing Ajiddeh tana kwantar mata da hankali, ita ko sai kuka take sosae ta daura hannu a ka, har ta d’an ban tausayi.
Kwantar da ita yayi jikinshi yana shafa gashin kanta, a hankali yace “Mey zakici”, tace “Ni ban sani ba, Ice cream zan sha”, yace “And what?”, tace “toh da Burger da lasagne da …..”, yace “da cream rolls da pizza da Tacos da sandwich da…..”, ta d’ago kanta ta marairaice fuska tace “Ni bance ba”, yayi dariya yace “But Babyna yace ai”, tayi shiru ta koma ta kwanta jin ya ambaci Babynshi, ya d’agota yace “muje tare?”, ta tab’e baki tace “No am not going, Farida yanzu zata dawo”, sai lokacin ya tuna da zancen Farida na gidan yace “Ohhh yeah, don’t mention our deal to anyone kinji?” ta gyad’a mishi kai, ya kwantar da ita ya mik’e yace “Not even Farida”, tace “toh”, da haka yayi pecking d’inta yace “Be right back, ki kula min da Babyna”, zumb’uro mishi baki tayi batace komai ba, murmushi yayi ya juya ya fita yana jin wani irin feeling da bai tab’a experiencing ba a kanta, sae da ya fita ya tuna da wata Ajiddeh nan fa hankalinsa ya fara tashi, juyawa yayi ya koma ya sa ma kofar dakin da Batuul take key sannan ya nufi d’akin da yasan Ajiddehn take, dai dai nan ta fito daga d’akin, kallonta yayi ya d’auke kanshi kamar bai ganta ba, ita ko takowa takeyi inda yake sai dai fa hawaye ne kawai ke bin kuncinta.Har ranshi ya dinga jin wani tausayin Ajiddeh, Sam ba ta haka yaso tasan wacece Batuul ba, yaso ya zaunar da ita yayi mata bayani yadda zata fahimta snn ya lallab’ata har ta hak’ura, shi kam yama rasa ya akayi taji zancen cikin nan dan yasan bata shigo office d’in doctor ba, toh ko lab’e takeyi har ta jiyo abunda suke fad’i, kafad’a ya d’aga alamar ita ta sani inma laben tayi, gashi gaba d’aya bayason ganin hawayen idonta dan its making him feel guilty, ji yakeyi kamar yaci amanarta da bai sanar da ita tun da wuri ba, Ajiddeh kam tsayawa kallonsa tayi ganin ya ki ce mata komai Sae ma barin wajen da yayi, zuciyanta ne taji kamar ya fito tsabar bugawan da yakeyi, shikenan yanzu ta sake tabbatar da gaskiyan al’amarin, lallai Batuul matarsa ce tunda har ya iya wuceta tana hawaye ba tare da yace mata komai ba, so take kawai taji wani ya tado ta daga wannan mugun mafarkin da takeyi amma ina bata samu hakan ba dan ba mafarki bane take, ji tayi k’afafuwanta na rawa baza su iya d’aukanta ba, da k’yar ta juya tabi bayanshi itama, zaune ta taddashi bakin gado ya dafe kanshi, zuwa tayi ta tsaya mishi aka kamar wacce ta hadi’yi tab’arya, a hankali ya d’ago kanshi yana kallonta, goge hawayen fuskarta ta shiga yi tana kallonsa a k’ek’ashe, duk wani so da tasan tana yiwa Aliyu yau ji tayi ya koma tsana lkci daya, kyan da take gani yanayi mata yau duk babushi sai tsanarsa da takeji kamar ta shakeshi, da k’yar ta iya bud’e bakinta tanajin wani abu tokare a mak’oshinta tace “Ka sallameni, ka bani takardata zan tafi gidanmu”, kallonta yayi da kyau jin abinda take fad’i, hannayensa ya mik’ar zai kamo nata dasu ya zaunar da ita gefenshi tayi maza ta janye hannayenta tana mishi wani matsiyacin kallo tace “kar ka kuskura kayi gigin tab’ani, ni ba mazinaciya bace bare ka goga min najasar dake tattare dakai”, ido ya rintse jin abinda Ajiddeh ke fad’a mishi, yasan koma dai menene shi yayi causing da tun farko bai sanar da ita ba, hannunta ya fizgo a karo na biyu ya zaunar da ita gefenshi, idonshi dake rikitata ya zuba mata tanajin yadda sonshi da ta dad’e tana dako da kuma tsanarshi da ya shigeta lokaci d’aya ke kokawa cikin zuciyarta, ta fashe da kuka tayi saurin d”auke idonta daga nashi dan har cikin ranta takejin kallon na piercing through her, k’ok’arin danne d’aya b’angaren zuciyarta dake son rinjiyarta akanshi tayi cikin dakewar murya ta sake ce mishi “nace maka bana auren, free me from this hell so called marriage, ai ba kaine kad’ai namiji ba a duniyan, kaje kuci gaba da zaman da kukeyi, ni dai saken….”, bai bari ta k’arasa ba ya d’aura yatsunshi biyu kan lips d’inta, gaba d’aya pulses d’inta saida sukayi responding to abinda takeji gameda Aliyu amma yanzu ba shine gabanta ba, ji take komai zata iyayi kan Aliyu yanzu dan tuni tausayinshi ya fita daga ranta tun daga lokacin da ya bud’i baki ya fad’i mata matsayin Batuul, ko da rabasu da ransu ne ji takeyi zata iya a daidai wannan lokacin, matso da ita yayi kusa da shi yana kallon yadda hawaye ke zirya a fuskarta, hannu yasa ya shafe mata hawayen, kamar yayi electrocuting d’inta haka takeji jin hannunshi kan fuskarta, rintse ido tayi tana jin sabon al’amarin dake faruwa da ita a yanzu, a hankali yave “Ajiddeh open your eyes and look at me”, Kin budewa tayi sai kukan da take har da shessheka, ya kuma maimaita abinda yace a karo na uku, a hankali ta bud’e rinannun idanunta ta sauk’e kanshi, cikin sanyin murya yana murxa hannunta dake cikin nasa yace “Everything happened so fast, naso fad’a miki tun farko but I don’t know wat draw me aback from telling you, I….”, yaja wani dogon numfashi snn yaci gaba a hankali “Just take it as our fate wife, kaddarar muce tazo da haka, bamu isa tsallake ta ba, Duk da ba haka naso ki San wacece Batuul ba, I wanted calming you, in nutsar dake da sanin who she is but yadda kikayi approaching d’inta was so stupid”, ta fashe da matsanancin kuka jin abinda yake ce mata, wato dai this is real ba mafarki take ba, turasa tayi kamar mahaukaciya tace “abinda yafi stupid ma duk zaka fad’i tunda kaci amanata, ka cuce ni, ka yaudareni Aliyu, I won’t forgive you for this”, bai dakatar da Ita ba har saida tayi shiru yace “Hear me out Ajiddeh, its been over a year tunda mukayi aure, ban tab’a ce miki inason ki haifa min baby ba despite inaso amma nasan Allah ke badawa at d right time shiyasa ban tab’a bothering d’inki ba, get this Batuul is my wife and tana d’auke da d’ana a cikinta,” kamar ya watsa mata mai mey zafi cikin ranta haka ta rik’a ji jin ya ambaci shegen dake cikin Batuul da d’anshi, shikenan tata ta sameta tana zaune wata can xata Haifa masa d’a ba Ita ba, matsowa yayi kusa da ita yaci gaba “I can’t risk anything happening to my baby, Inaso ta haifamin abinda ke cikinta ko wane iri, am destined to auren Batuul, babu mai iya gujewa Destiny, there is nothing more for me to say saidai am sorry for hiding the truth from you all this while, nayi hakan ne dan kada in tada miki hankali a lokacin, I was waiting for d right to let you know of everything amma Allah yayi sai yanzu zaki sani, I promise you myself being married to Batuul bazai canza komai gameda Son da nake miki ba Ajiddeh, ki kwantar da hankalinki ki d’auketa as a sister, kinga yarinyace sosai, help in all ways you can, in kikayi min haka nasan son da kike min dagaske ne, I want to have that Baby Ajiddeh”, ya k’arashe maganan tareda cupping fuskanta a tafin hannunshi, a hankali ta janye fuskarta daga rikon da yayi mata tace “Ka gama?”, ta tambaya tana kallonshi a k’ek’ashe, shi da kanshi yasan he have wronged her ta kowanne b’angaren, babu matar da mijinta zaiyi aure ba tareda saninta ba har sai matar ma nada ciki snn ta Sani kuma ta yadda hankali kwance, bazai biyewa duk wani shirme da zatayi mishi ba yanzun dan yasan ranta ya gama b’aci, ta ja wani arnen tsaki tace “kai duk zamanka duniya ka tab’aji ance familyn mu mun zauna da kishiya?, toh ko tarar da ita mukayi sai ta bar mana gidan bare kuma har har tazo ita ta sameni in zauna da ita, bamai yiwuwa bane wlhy, gidanmu zan tafi, in ka tashi ka aiko min takaddar sallama ta dan ban zama da munafiki, ita waccan shegiyar da tayo shege daga waje kake ikirarin matarkace sai kayi zaman da ita amma badai ni ba” ta k’arashe tareda mik’ewa zata tafi, da sauri yasa hannu ya fizgota ta fad’o kanshi, idanun nan nashi da bata son gani su ya zuba mata, kallon da yake mata yasa ta d’auke kanta da sauri, hannu yasa ya juyo da fuskanta yace “babu saki a tsarina, nace miki am sorry for everything, ki fad’i min duk abunda kike so zan baki shi amma babu cikinku wacce ta isa tasa na rabu da d’aya, and mind you, don’t try anything stupid dan duk lokacin da kikayi gigin barin gidan nan bada Sanina ba, you ain’t gonna like it”, kwace kanta tayi daga rikon da yayi mata ta fashe da kuka tace “munafiki mey xakayi da ya wuce wanda kamin, ai wlhy ka janyowa kanka, kwanciyar hankali ma ka rasa at this very minute, mugu kawai, sai meye in baka sakeni ba, ai ba kai kad’ai keyin auren ba, gidanka kuma sai na bar maka shi kaci uwar da zakaci da kaida karuwar taka”, rintse ido yayi dan bayason losing cool d’inshi, amma yarinyar nan na d’aga mishi hankali har cikin ransa yake jin dacin sunan da take k’iran Batuul da, mik’ewa yayi bayan ya bud’e idonshi ya tashi ya bud’e side drawer d’in d’akin ya fiddo makulli yayi waje, dan yasan zamanshi d’akin zaisa yayi abinda bashi da niyya, yana fita yaja k’ofan ya kulle ta baya ya bar makullin daga jiki
2
Yana fita ya waiga ya kalli d’akin Batuul, da hanzari ya sauk’a ya fad’a mota ya tada ya d’au hanyan Inda zaije siyowa Batuul abinda take buk’ata, cikin 15mins ya siyo komai ya dawo mota dan hankalinshi sam bai kwanta ba barin Batuul da Ajiddeh da yayi a gida tare su kad’ai dukda ya rufe musu k’ofa su biyun duka, yana parking a gida ya fito ya d’ebo wasu daga cikin ledojin yayi sama dasu, d’akin Ajiddeh ya bud’e ya lek’a yaga babu kowa cikinshi, da mamaki ya k’arasa shiga jin motsinta a toilet yasashi sauk’e ajiyar zuciya ya ajiye ledojin dake hannunshi ya fita ya sake rufe k’ofan ta baya yayi d’akin Batuul, a kwance ya tadda ta kan gadon, ajiyar zuciya ya sauk’e ganin she is fine, wani irin feeling yakeji sauk’e idonshi da yayi a kanta, duk wannan stress da damuwar da ya kwaso gun Ajiddeh ji yayi duk ta b’ace mishi, idonta a kanshi har ya k’araso cikin d’akin, kwanciya yayi bakin gadon snn yasa hannu ya jawota jikinshi, ido ta wara zata b’ara mishi baki yayi saurin d’aura d’an yatsanshi kan lips d’inta yana kallon Idonta, da sauri ta rintse su hakan da tayi yasashi yin murmushi, y’ar crop top d’in dake jikinta yasa hannunshi ciki ya d’aura hannunshi kan cikinta, da sauri ta bud’e idonta jin inda ya d’aura hannunshi, hannu tasa zata ture nashi hannun ya rik’o hannun nata da d’ayan nashi, a hankali yayi brushing lips d’inta da yasa gasp escaping lips d’inta, ta shiga k’ok’arin turashi, dariya yayi yace “Hey Babyna keh missing d’ina, am just checking on him”, baki ta zumb’uro mishi ta d’auke kanta tace “Ina abincin da zanci? yunwa fa nakeji”, ta k’ara turo baki ta juya mishi baya, da hanzari ya mik’e yace “Damn, I was checking ko Babyna na lafiya that I forgot kinajin yunwa, sorry let’s get going”, jin har ya manta da yunwar da takeji yasa hawayen dake idonta silalowa, shi dai kawae ta haifa masa yaro, hannunta ya kamo yace “muje”, tace “ni baxanje ba, ba babynka yasa ka manta inajin yunwa ba, ka bashi abincin yaci ni baxan ci ba”, ta koma ta kwanta, dariya ta bashi ya mik’e cak ya d’auketa, ihu ta fara mishi ya sauk’eta tana cewa “Ka sauk’eni Yaa Abu, ina zaka kaini”, daidai neck pulse d’inta ya rank’wafo har tana jiyo numfashinshi da ke kalar mint na bugun fatar jikinta yace “Babyna zanje inyi feeding, just stay still before in jefar dake downstairs”, aikam kamar cewa yayi taci gaba haka ta dinga wuntsila k’afa, bai bi ta kanta ba ya ya bud’e k’ofa ya fito, har saida ya bud’e mota sannan ya sata ciki ya zaga ya shiga, tana zama idonta ya fad’a kan ledojin, da sauri ta janyo ta shiga bud’ewa ta ciro ice cream d’in ta shiga sha, zama yayi da murmushin da baisan sanda yayishi ba shimfid’e a fuskanshi yana kallonta, a hankali ta juyo da lumsassun idanunta ta sauk’e kanshi, ganin kallonta yakeyi yasa ta d’an tsuke fuska ta mik’a mishi robar tace mishi “you want some?”, murmushi yayi ya d’auke kanshi yace “No, kisha kayanki”, ta tab’e baki itama taci gaba da shan abinta, saida ya tada motar ya fara tafiya snn ya juyo ya kalleta ganin yanda ta dage sai shan ice cream d’in takeyi yace “bad manner”, da sauri ta kalleshi jin abinda yace mata ta zumb’uro baki tace “mey nayi?”, mirror dake gefenta ya jawo mata ta kalli fuskanta, dariya ta fashe da ganin abinda ke fuskanta, ice cream d’in ne gaba d’aya gefen fuskanta, ta kalleshi ganin baya dariya itama ta tsaida nata tace “toh ai sune basu saka tissue ciki ba”, daidai nan yayi parking k’ofar d’aya gidan nashi, robar ice cream d’in nata ya jawo ya d’auki cokalin dake ciki ya shiga goga mata a lips d’inta, tsuke fuska tayi tace “you messed my face” tasa hannu zata goge yayi maza ya rik’o hannunta ya d’age mata girarshi yace “No you look cute”, ta zumb’uro baki tace “ba yanzun nan kace min bad manner bane”, yace “No ai yayi miki kyau”, ta sake jawo mirror tana kallon kanta ta fashe da dariya tace “kamar moustaches d’in santa ko?” shikam kallonta ya tsaya yi ganin dariyar da takeyi ya k’ira Sunanta a hankali, juyawa tayi ta kalleshi jin mey zaice, taji yace “You are cute”, kallonshi takeyi ta kasa d”auke idonta kanshi, a hankali yayi leaning ya shiga kissing d’inta har saida ya lashe duk cream d’in da ya bata mata fuska, daga nan ya d’auketa cak yayi waje da ita.
2
Suna barin gidan motar su Farida ya shigo gidan, saida tacewa David “Thank you” snn ta shigo gida, tun daga parlour take kwalawa Batuul k’ira taji shiru, kitchen ta lek’a taga bata nan, sama ta haura d’akin Batuul d’in nanma bata nan sai wayarta dake ajiye kan gado, tana fitowa d’akin taji ana bubbuga k’ofar d’akin Abu da k’arfi kamar ana shirin b’allashi, a tsorace ta k’arasa k’ofar d’akin, ganin mukullin a jiki yasa jikinta na b’ari ta kama ta bud’eshi, da k’yar ta iya sa hannu ta tura k’ofan, da mamaki ta tsaya kallon wacce ke cikin d’akin tana dukan k’ofar, wani dogon tsaki ta ja ta juya xata bar wajen, Ajiddeh da dama jira take ta fixgota da karfi tana huci tace “Uwar ki kike ma tsaki bani ba,”Wani matsiyacin kallo Farida ke bin Ajiddeh da ta tsaya tana hararanta taja tsaki tace “ke wllh kika sake gaya min maganar banxa baxa kiji da dad’i ba, ko ce miki akayi nice na rufe miki d’akin” juyawa tayi xata bar wajen ta ji Ajiddeh ta kuma damk’ota tayo cikin d’akin da ita, taga taga Farida tayi kamar zata fad’i tayi saurin regaining balance d’inta ta tsaya tana kallon Ajiddeh da mamaki tace “ke anya kanki daya kuwa, ko dai kina da tabin hankali ne” a fusace Ajiddeh tayo kanta, idon nan ya k’ank’ance dan jaraba tace “ke uwarki ke da tabin hankali ba ni ba, ni sa’ar uwarkice y’ar iskar mai kama da tsuntsaye da shegun dogayen k’afafuwanki, toh yanzun nan zanci ubanki shegiya munafuka, har ni za a ciwa mutunci a ci amanata, ku da munafukar uwar taku har kun isa ku wulakantani, ai sai nayi muku abinda duk baku zata ba, yadda kuka tozartani sai nasa kunyi kuka da idanunku, matsiyata munafukai, nafi k’arfin wulak’ancinku matsiyatan banza da wofi…..”, tsabar frustration ma ta rasa tak’amai mai abinda zata fad’i sai huci take kamar karya, Farida dai kallonta ta tsaya yi baki bude dan ta tabbata yanzu cikin biyun nan da akwai d’aya inma dai tab’in hankali ko Kuma shigar aljanu, tana gyada kai tace “lallai ya Abuu na cikin masifa, ina ga tun farko bai san kina da tabin hankali ba ya auro ki, tun da ba ni na daura maki ba baxan maki addu’ar samun sauki ba sai dai ince Allah ya dauwamar da ke a haka” daga haka tayi gaba abinta ta wuce ta, cikin d’aga murya Ajiddeh tace “Uwarki ce mara hankali, Ehh Bilkisu ba, ita ce mara hankalin dan uwar….”, bata k’arasa ba taji wani lafiyayyen mari har guda biyu da ya gigitata kan fuskarta, hawaye cike a idonta take kallon Farida zata tabbatar daga inda marin ya isota, Farida na huci tace “kika sake kika kuma zagina bama iyayena ba sai na zubar miki da rub’ab’b’un hak’oranki wllh, kazama kawai jahila wawiya wacce batada wayo, in shi da ya ajiyeki kin zageshi ya k’yaleki wlhy ni sai na lakad’a miki duka a cikin gidan nan kuma na daki banza tunda ke bakida hankali, kucaka dake har kin isa ki zagar min iyaye, toh koh Yaa Abun da kanshi in yana nan kika aikata haka bai hukunta ki ba toh ni a gabanshi zanyi wanda yafi haka ma, kuma aure an aura mishi d’in, keh har wata matace da za a k’ira da sunan mata in banda tsawo da kika sa a gaba kamar bishiyar dabino, in banda kaddara mey ma ya had’a Yaa Abu da auran irinki, bakida aiki sai kici ki kwanta, toh ko zaki rabe biyune dan takaici BATUUL matar Yaa Abu ce ta har abadan kuma mutu ka raba aurensu, sai dai in zaki mutu da takaici ki mutu, shasha kawai”, ta watsa mata wani irin kallo ta juya taci gaba da tafiyarta, Ajiddeh dake tsaye kamar statue ji tayi zuciyarta na neman rabewa tsabar bakin cikin da ya taru ya mata yawa, wai har Farida ce zata mareta,wani irin k’arfi ne taji yazo mata, tsalle ta daka ta cakumo Farida da har ta kai k’ofa tayi baya da ita, Rai b’ace Faridan ke kallonta tace “ke wllh darajar auren Yayana dake kanki kike ci wlhy da kuma tarbiyar da aka min a gida inba haka ba yanzun nan sai na nuna miki k’aramin hauka kikeyi jahila kawai, cika ni”, ta turata ta juya zata tafi Ajiddeh tayi wani kukan kura ta kuma cakumo Farida tace “Dan uwarki yau zakiga k’arshen rashin hankali” gaba d’aya ran Farida ya gama b’aci da wannan rashin hankalin na Ajiddeh, in ba tayi dagaske ba baza ta shafa mata lafiya ba, matsowa tayi dab da ita ta ta k’ara mata wasu lafiyayyun marin da suka fi na d’azu girgizata, a harzuk’e ta shiga dukanta ta ko ina kamar ta kama y’arta, Ajiddeh kam baki ya rufuwa sai ihu take tana cewa “dan uwarki dani kike , sai kin barmin gida tunda ba na ubanki bane shegiya gantalalla”, sai da farida ta likid’eta iya son ranta ta nanata da k’asa, banda ihu da tsine tsine babu abinda Ajiddeh keyi bakinta na jini, Farida na huci tace “dama a cike nake dake, gobe ki kuma zagar min iyaye kuma ke in gidan na naki uban ne sai ki koreni”, daga haka ta fice daga d’akin, Ajiddeh in banda kuka ta kasa yin komai, ko tashi ta sake cakumo Faridar bata sake yunk’urin yi ba.
4
Abuturrab Bai direta a ko ina ba sai kan gado bayan sun shigo ya haura sama da ita, ita kam sai kallonshi takeyi idanunta na lumshewa dan bacci takeji, fita yayi ya dawo da ledan abincin dake mota, da mamaki ya tsaya kallonta ganin har ta fara bacci, k’arasowa yayi ciki ya ajiye ledan abincin daga k’asa ya hau kan gadon ya d’agota, a hankali ta bud’e lumsassun idanunta ta kalleshi, sulalewa tayi da muryar bacci tace “bacci zanyi” ta koma zata kwanta yayi saurin rik’ota yace “Eat before you sleep”, ta zumb’uro mishi baki tace “Na k’oshi ni, bana jin yunwa”, tanayi tana lumshe ido, had’e rai yayi yace “cmon kin tashi kinci anbinci kokuwa?, da kikaci mene d’inne kika k’oshi?”, bata bud’e ido ba ta bashi amsa tace “ba nasha ice cream ba”, d’an tsaki yaja ya d’agota ya d’aurata kan cinyarshi ya janyo ledan ya shiga d’ebo abincin yana bata a baki, da k’yar ya samu taci kad’an tace mishi ta koshi, badan ya so ba ya bar bata abincin hakanan, kayan jikinta ya shiga k’ok’arin cire mata, da sauri ta tashi zaune ta wara ido tana kallon abinda yake son yi, kallonta shima d’in yakeyi yace “Meye, har kin gama baccin?” ta gyara zamanta tace “bafa bacci nakeji ba dama”, bai kulata ba yaci gaba da cire mata kayan snn yace “wanka zanyi miki, yau duk bakiyi wanka ba, I want my baby to stay clean”, ta tsuke baki jin yace babynshi tace “ni banyin wankan kuma sai anjima” baibi ta kanta ba ya cire duka kayan dake jikinta sai nonnokewa takeyi wai ita kunya ya rage daga ita sai inner wears ya janyo towel ya d’aura mata, cak ya d’auketa yayi hanyan toilet da ita, sai da yaje bakin toilet ganin dagaske yake tayi maza ta sauk’o daga jikinshi, har cikin ranshi yaji wannan wuntsilawar da tayi yayi saurin rik’ota ya had’e rai yace “kinada hankali kuwa, bakisan da Babyna a jikinki ba, I will slap you next time you try this shit”, zumb’uro mishi baki tayi tace “Toh zanyi wankan da kaina nace”, tsaki yaja ya kamo hannunta suka shiga toilet d’in, tana nan tsaye har lokacin yana rik’e da hannunta d’aya ya had’a mata ruwan wanka a bathtub, ya juyo zai cire mata towel d’in tayi maza ta riqe da k’arfi tayi raurau da ido tace “Dan Allah mana Yaa Abu, zanyi da kaina nace”, kallonta kawai yakeyi ganin yadda tayi maganan har idonta ya cicciko ya janye hannunshi a hankali yana kallonta yace “be careful”, ajiyar zuciya ta sauk’e ya janye mata curtain d’in yaje ya zauna daga gefe yana jiran ta gama bata fi 8mins ta fito daga cikin abin wankan d’aure da towel d’inta, da sauri ya mik’e ya d’auketa cak yayi waje da ita, kan vanity chair ya ajiyeta, itakam sai mamakinshi takeyi gaba d’aya ganin ya janyo wani d’an box ya fidda hand dryer a ciki, wai Yaa Abu ke yin duka wad’annan abubuwan, wani part d’in zuciyarta kam dad’in abinda ya ke mata ta dinga ji, a hankali ya shiga drying gashin kamar mai tsoron tab’awa, itakam Batuul har wani lumshe ido takeyi dan jin dad’i, sai da ya gama drying ya d’auko man gashinshi ya shiga shafa mata su yayi parking mata gashinta, dariya yadda yayi parking gashin ya bata, murmushin shima yayi, yana gamawa ya shafa mata nashi man jikin ya fesa mata cool turarukanshi, tana zaune ya bud’e wardrobe d’inshi ya fiddo wata shirt d’insa blue mai dogon hannu da boxer d’inshi shima blue and black sabbi duka ya mik’a mata, shi da kanshi mamakin kanshi yakeyi kan abinda yake aikatawa, he never tot he will b doing abubuwan nan for a lady, wara mishi ido tayi tace “Na meye?” Yace “Wear them, ko kinada kayan da zaki sa ne a nan?”, da sauri ta kad’a mishi kai tace “Yeah akwai su a wancan d’akin”, shi sam yama manta dasu baki d’aya, yace “Yeah I know, I want you to wear these”, ta marairaice mishi zatayi magana ya rik’ota zai janye mata towel d’in ta fasa ihu ta riqe tace “Ai zan saka”, mik’a mata yayi ta karb’a a sanyaye tace “toh nikam ka rufe idonka”, dariya ta bashi yace “in karb’a in saka miki kenan?”, da sauri ta girgiza mishi kai, da murmushi a fuskanshi yace “Then wear them”, kamar zatayi kuka ta shiga b’are boxer daga cikin leda, shi ya karb’a ya bud’e mata su ya mik’o, da sauri ta juya zatayi toilet a guje yayi maza ya fizgota, had’e rai yayi yace “ban hanaki tsalle ba”, ta marairaice tace “toh bazan sake ba”, ganin ya tsareta da ido ta fara saka kayan shiko sai mugun smirking yakeyi, baisan lokacin da ya furta “Wow” ba bayan ta gama saka kayan, itakam kasa d’ago kanta tayi ganin y’ar rigar iya cinya, takowa yayi yazo gabanta ya d’ago hab’arta yana kallonta, daidai fuskarta ya sunkuyo yace “You look cute”, itakam kasa d’agowa tayi ta kalleshi sai ji tayi ya d’agata yayi gado da ita, a jikinshi ya kwantar da ita ya warware gashin da ya tufke da kanshi ya shiga kwantar mata da gashinta, a hankali ya rad’a mata a kunne “kiyi baccinki”, kamar ya sani kuwa bacci ne ke fizgarta, kamin yace komai har tayi bacci a jikinshi, ido ya tsura mata yana kallon tiny figure d’inta dake kwance, ita komai nata k’arami ne, a hankali ya sako hannunshi ta cikin rigarta yana shafa cikinta da yake a shafe tareda lumshe ido yana jin wani exceptional feeling na daban da bai tab’a experiencing ba, da sauri ya d’an d’age rigar yana kallon flat tummy d’inta, wai wannan cikin ne yanzu mutum xai fito a ciki, murmushine yayi escaping lips d’inshi, a hankali ya d’aura lips d’inshi kan cikin nata yayi kissing yace “Fatima can’t wait to see our baby, I will love her till my last breath”, da sauri ya d’ago kanshi jin yace her, wa yace mishi mace zata haifa, kai ya kad’a yana murmushi yace “I want a baby girl Fatima, just like you”, ya kalli Face d’in Batuul dake kwance tana baccinta peacefully ya d’aura yatsunshi kan face d’in nata yace “Including your cute lips Baby”, Batuul dai baccinta takeyi bata ma san mey yakeyi ba, a hankali ya gyara zamanshi ya gyara mata kwanciyarta dan taji dad’in Baccin nata, wayanshi ne yaji ya fara ringing amma sabida baccin da ta fara yanzu baya son ya katse mata shi, k’iran na katsewa wani na shigowa, haka aka dingayi mishi har wajen missed calls 8, ganin anqi dena k’iran yasashi jan d’an tsaki ya kwantar da Batuul a hankali ya mik’e ya isa gaban vanity table d’in ya d’auki wayan
A bangaren Ajiddeh kuwa kuka ta dinga risga kamar an aiko mata lbrn mutuwa, ganin kukan ba taimakonta zaiyi ba ta d’auko waya ta shiga neman layin Aliyu, har ya gama ringing bai d’auka ba, bata dena k’iran ba har saida taji an d’auka snn ta fashe mishi da wani matsanancin kuka tareda sakin wani razananne k’ara da ya sashi rintse ido, kuka takeyi sosai ta shiga koro mishi jawabin k’arya da gaskiyan abinda ya had’ata da Farida kuma yazo ya fita da Farida inba haka ba zata bar mishi gidanshi, shi yasan Farida bataji amma bai tab’a kawowa har zata iya yiwa Ajiddeh duka ba, ce mata yayi gashi nan zuwa, kan gadon ya koma yana tunanin barin Batuul ita kad’ai a gidan, gaban desk top d’inshi yaje yayi activating CCTV snn yayi securing gidan, pecking d”inta yayi snn ya fita ya bar gidan, cikin minti kad’an ya isa gida, kai tsaye d’akin Ajiddeh ya isa ya tarar da ita xaune kan gado sai kuka takeyi duk bakinta ya kumbura, nan taci gaba da shirgo mishi k’arya da gaskiya, ba karamin baci ransa yayi ba ya shiga rarrashinta, ganin yadda ranshi ke b’ace ta fara murnan zai yiwa Farida koran kare a gidan, da murna ta biyo bayanshi, k’ofan d’akin Batuul ya tura, Farida na kwance kan gado tana playing Word Crush a wayar Batuul, mik’ewa tayi xaune tana kallonsu duk da yanda gabanta ke faduwa ganin yanayin fuskanshi hakan bai hanata daure fuska ba, ta mike tsaye tace “Yaa Abu tun d’azu fa na dawo ina ta nemanku, ina Besty na take itama bata nan”, ta shiga lek’a bayanshi ko zata hango Batuul, sai lokacin ma Ajiddeh tasan Batuul bata gidan ashe, fizgota yayi yace “in the next 5 mins ki tabbatar kin gama tattara kayanki you are going back home”, ganin murmushi shimfid’e fuskan Ajiddeh ta had’a rai tayi kamar bataji mey yace ba tace “Yaa Abu kace ta bamu waje zanyi maka magana, bana son gayyar sa ido”, wani tsawa yayi mata yace “Ba magana na miki ba?”, had’e rai tayi tace “Toh Yaaa Abu mana, nifa hutuna bai k’are ba kuma ni ba wajenku nazo….”, wani tsawan da ya daka mata yasa ta razana ta kasa k’arasa maganan, tace “Yaa Abu ni gun Batuul Ammah ta siyamin ticket nazo fa”, gnin yana yiwowa kanta yasa ta fasa ihu ta isa wardrobe ta shiga had’a y’an kayanta, Ajiddeh duk da tana murna amma ba haka taso ba, taso ya rama mata dukan da Farida tayi mata yayi mata korar kare, suna tsaye Farida ta shiga had’a kayanta tana hawaye har ta gama tazo ta tsaya gabanshi tace “Toh ina Batuul d’in, mu jira ta dawo sai in tafi”, bai kulata ba ya kamo hannunta ya shiga janta har suka sauk’o k’asa, Ajiddeh kam hakan ba k’aramin dad’i yayi mata ba dan dama so take a barta daga ita sai Batuul a gidan, har k’asa ta biyosu tana yiwa Farida habaici, itakam ko kallo bata isheta ba, suna shiga mota ya tada suka tafi.