RAI BIYU CHAPTER 6

RAI BIYU





CHAPTER 6



Haƙiƙa akwai ƙurciya a rayuwar Habiba, yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa ta aikata abunda ta aikata, wanda take tunanin kamar mafitane, sai gashi ya zame mana matsala, yanzu kuma tana ganin kamar guduwa ta bar gida shi ma mafita ne, ni ko nasan duk yarinyar da ta gudu ta bar iyayenta lallai tana tare da na sani da kaico a rayuwarta.
Ba zan bari ƴar’uwata ta aiwatar da wannan ƙudirin nata ba, ko da kuwa haka yana nufi salwantar rayuwar mahaifiyata ne, ba zan bari ta sake aikata wani kuskuren ba. Ƙoƙari nake na tsayarda kuka ta yadda zan ƙarfafa mata guiwa da rarrashi amman hawayen da ke min zuba sun ƙi bani haɗin kai.
Idan har ban yi ƙarfin halin shiga tsakaninta da wannan kuɗirin nata ba, lallai zamu iya rasata wanda na san hakan zai iya sama sadiyar rasa Inna.
Hannayenta na saki na share hawayena ina kallonta, cike da ƙarfin hali na ce +

“Babu inda zaki je Habiba, irin wannan tunanin na ki ne yaja miki kika jefa mu cikin wannan halin, yanzu kuma zaki sake aikata irinsa? Kina tunanin aikata wannan abun shine mafita? Ba zai canja komai ba, sai dai ma ya ƙara ɓata ran Inna har ta kasa yafe miki, mu kuma ki ja mana ɓacin suna, haka kike so?” 2

Ta girgiza kai alamar a’a, muryarta a shake ta ce.

“Ta ce ta yi nadamar haihuwata ni ce ajalinta, ba zata yafe min ba”

Hannu na kai na sake riƙe hannayenta.

“Zata yafe miki Habiba, ni ma uwace na san halin da Inna take ciki, akwai zafi idan wani abu ya samu ɗanka musamman mace, idan wani abu ya sami Noor bana iya yafewa kaina, bana iya controlling kaina bana iya juriya, kin san saboda me? Saboda Ina ƙaunar Noor, a duk faɗin duniya babu wacce zata gwadawa ɗa so kamar uwarsa, duk abunda Inna ta yi miki saboda tana ƙaunarki ne ke kanki kin san Inna tana son ki, karki yarda ki gudu idan har kika gudu babu ni babu ke har abada!” 1

“Ba zan gudu ba, ba zan je ko’ina ba na miki alƙawari, ko da kuwa Inna zata yanka ni ne”

Ya faɗa cikin kuka. Sai na zaunar da ita ina share mata hawayenta, tare da yi mata wasu kalaman da zasu ƙarfafa mata guiwa.
Ban bar ɗakinba sai da na tabbatar kuka da take ya tsagaita, sannan na fito na shiga ɗakin Inna.
Gurin da barta a nan na sameta sai wannan karon tana daga kwance ne, gurin da fuskarta take ya jiƙe da ruwan hawaye kamar an zuba ruwa a gurin. Daga inda na ke tsaye na soma mata magana ciki da ƙarfin hali.

“Habiba ta aikata abunda ta aikata ne saboda tana tunanin kamar hakan shine mafita, ta aikata abunda ta aikata saboda Baba da ke da kuma mu duka, kin yarda da ƙaddarar da ta samu Baba har kika riƙa bani haƙuri, shin miyasa ba zaki yarda da wannan ƙaddararba…?”

Tashi tayi zaune ta kalleni a tsawace ta amsa min

“Saboda ita ta kai kanta”

Na matsa kusa da ita

“Akwai ƙurciya da tare da ni balle kuma Habiba, hankalinta da tunaninta be kai inda kike tunaniba, babu banbanci tsakanin wannan ƙaddarar da kuma wacan dukansu ƙadarori ne, babu wanda ya dace ya nunawa Habiba soyayya a yanzu fiye ke, babu wanda zai mata magana hankalinta ya kwanta fiye da ke”

“Habiba ta ɗauko wata rayuwa wacce bata gidan nan ba, sam wannan ba tarbiyarmu ba ce”

“Wannan kaɗai ya isa ya tabbatar miki da cewar ƙaddarace, ashe ko haka ya isa yasa ki rumgumeta ki nuna mata kina tare da ita”

Ajiyar zuciya ta sauke kana ta kalleni

“Kina da ƙarfin zuciya Nawwara, haƙiƙa Muhammad Noor ya yi sa’ar uwa” 2

“Ƙarfi guiwata taki ce Inna, kin rigani zama uwa kin fini sanin komai a rayuwa”

Wani dogon numfashi taja ta sauke tana cige baki ta ce.

“Wani lokacin kaina ya kan kulle har na yi tunani ba dai-dai, Allah ya kan jarrabi bawa da abubuwa da dama har bawa ya ga kamar Allah baya sonshi” 1

“Zamu jarrabeku da yunwa da tauyewar ƴaƴan ittatuwa da rayukan da dokiyoyi, ka yi bushara ga masu haƙuri (Masu jure waɗannan jarabce-jarabce) Waɗanda idan masifa ta samesu sai su ce (Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un) Mu ɗaga gurin Allah muka fito kuma a gare za a maida mu, kyakkawar yabo ya tabbata agaresu daga Ubangijinsu, haka Allah ya faɗa a ciki alƙur’ane mai girma, akwai kuma inda Allah yake cewa ‘Ko wane tsanani yana tare da sauƙi har ya sake maimaitawa Haƙika ko wane tsanani yana tare da sauƙi, sai kuma ya ce Fasbir sabaran jaamila wato ya kai Annabi ka yi haƙuri haƙuri mai kyau, Allah yana tare da masu a haƙuri. Inna duka waɗannan Allah ne ya faɗa. 2

STORY CONTINUES BELOW


Kin tuna lokacin da na yi aure? Na fuskanci wulaƙanci da ƙalubale kala-kala a gidan aurena, har na fito na haifi Noor cikin baƙinciki da damuwa, na sake wani auren har na fara jindaɗi sai Allah ya karɓe abunsa, na sake dawowa cikin wannan wahalar, sa’anina da wanɗanda muka yi makaranta tare da su, duk sun zama manyan mutane har basa son abota da ni, ni kuma ina nan, amman hakan be taɓa saka ni na yi tunanin ko Allah baya so na ne ba ko da sau ɗaya, da ace Allah ya yi ni kafira da zan yarda Allah baya so na saboda komai na tara a duniyarnan zan mutu na bar shi naje ƙiyama na shiga wuta, amman kin ga yanzu zan iya sha wahala a nan idan har na aikata aiki na ƙwarai ina zuwa ƙiyama kai tsaye aljannah zan wuce, kuma kin ga can ba a mutuwa ba a baƙinciki balle tsufa. 1

Ki rumgume ƙaddarar nan Inna, karki yi Habiba abunda zai ƙara mata baƙinciki, ta ce min zata gudu ta bar gidan nan saboda kar ta zama silar ajalinki”

Da sauri Inna ta miƙe tsaye da sauri hankalinta a tashe.

“Ina take?”

“Tana ɗakinmu”

Da gudu ta nufi ɗakin, ni kuma na rufa mata baya. Ko da muka shiga ɗakin sai muka samu babu kowa a cikinsa, daga ni har Inna sai da gabanmu ya faɗi, Inna ta juyo ta kalleni nima na kalleta.

“Habiba”

Na kira sunanta da ƙarfi, sai ta amsa min daga bayan gambu da take ɓoye, a zatonta Inna zata faɗa mata wata maganar marar daɗi ne ko kuma ta daketa hakan yasa ta ɓuya a nan. Da sauri Inna ta duba gurin domin ta fini kusa da shi sai ga Habiba a tsaye tana hawaye jikinta na rawa tana jiran sakamakon Inna.

“Zo nan ƴata na yafe miki duniya da lahira, Allah ya yi miki albarka, ya isar miki”

Inna ta faɗa tana miƙa hannu taja Habiba jikinta ta rumgume, sai suka fashe da kuka, sai nima na fara nawa kukan da daga inda na ke tsaye, a raina kuma ina ta godiyar Allah.
2

*** *** ***

Haka muka wuni a cikin gidan kamar waɗanda akayi wa mutuwa, Sakina da Jamila ma sun lura da haka su kansu basa wani sakewa saboda ganin kamar muna cikin damuwa, Noor ne kawai yake ta sha’aninsa shi kan be ma damuba.
Washe gari kasa zuwa aiki na yi saboda na tashi jikina da kuma zuciyata babu daɗi, duk yadda Inna ta so naje sai na ƙi, su Sakina kawai suka je makaranta, mu kuma muna gida shiru-shiru babu wani motsin kirki da ɗayanmu ke yi, misalin ƙarfe ɗaya da rabi Bilal ya kirani ina ɗauka sai ya fara tambaya miyasa ban je aiki ba, ni kuma na amsa masa da cewar babu komai, sai dai ban yarda ba yana ganin kamar ɗan ya ganni babu hijabi jiya ne yasa na yi fushi.

Jikin Habiba ya ƙara tsanani da yamma, har na ke bada shawarar mu kaita asibiti sai Inna ta ƙi saboda aganin asiri mu zai tonu.

“Idan mukaje asibiti zasu faɗa mana ciki ne, wanda nasan nan da nan za a ji a unguwar nan, ya kike so acewa Yakumbo da kuma mutane babban gida? Da wane ido zamu kallesu, yanzu zasu ce dan margayi ba shi da rai ne na ƙyale Habiba ta aikata wannan abun ni zasu ɗorawa laifi”

“Da ido da muke kallonsu Inna, tun bayan da aka gama amsar gaisuwa kin saki ganin ƙafar wani a gidan nan? Ba mu da nisa da su amman basu taɓa ɗauko ƙafa suce bari su leƙo mu suga ya muke ba, kowa harkar gabansa yake”

Ta yi shiru kamar ba komai kamar mai tunani can kuma ta kalleni

“Ni da wai na ce ko zubar da cikin zamu yi?” 2

Gabana ya faɗi, naji maganar kamar saukar aradu.

“A’a Inna idan muka je zubar da cikin ai dole za’aji”

“Ba asibiti ba wai gida”

“Taya zamu zubar da ciki gida?” 2

“Ƴan kayan ɗacin nan da ake badawa mana, tun da kin ga yanzu be yi ƙwari ba kuma a iya busa masa rai ba, idan har be zube ba sai mu ƙyaleta”

Na kasa cewa komai saboda na lura ranta ya kwaɗaitu da a zubar da cikin, duk da ina ganin zubar da cikin yana daga cikin alamomin rashin yarda da ƙaddara. Tausayin Habiba ne ya kamani sai na ji ina ma nice ba ita ba, hawaye suka zubo min sai na yi saurin tashi tsaye ina faɗin.

“Bari naje na siyo mata maganin zazzaɓi”

Inna ta amsa min da tau cikin yanayin damuwa, ɗaki na nufa na ɗauko Hijabina ina kallon Habiba take kwance malala kamar lakka.
Kamar na fasa kuka haka na fito ɗaga ɗakinmu bayan na ɗauko ƴan canjina na fita zuwa siyo mata magani, har na isa tunanin maganar Inna nake, ta yadda zan yi na hanata kawai na ke nema.

Bayan mum gaisa da mai shagon maganin sai na miƙa masa ɗari biyu na ce ya haɗa min maganin zazzafi kala-kala. Ya haɗa min kusa kala takwas cikin har da na malaria da na ciwon kai da na zafin jiki, ya ɗora min a saman gilashin da suke ɗora magani ni kuma na karbi leda na saka ina jiran canji.

Sai kawai na ga Mustapha cikin shagon kamar an jefoshi, matsawa yayi kusa da ni sosai yana min magana ta yadda babu wanda zai ji

“Ki yi haƙuri da abunda ya faru ranar nan, Wallahi ba da ke nake ba da mai Napep ɗin daya ɗauko ki na ke” 2

Ji na yi kamar ace akwai wuƙa kusa da ni na daɓa masa a ƙirji, wani ɗogon tsaki naja wanda ya jawo hankalin duk wanda ke shagon zuwa garemu, na ɗauki canjina na fice zuciyata na bugawa kamar zata fito saboda ɓacin rai.’Ba a banza ya baki haƙuri ba, taya zai baki haƙuri mutumen da ba ya ganin kowa da mutuncin, ba dake yake ba kika mareshi sai kuma yanzu ya zo ya baki haƙuri, lallai akwai abunda yake nufi da ke’ 2

Shine abunda na ke ta saƙawa a zuciyata, a zahiri kuma sai nan nemin tsarin Allah akansa.

“Allah ka min tsari da sherinsa”

Har na iso gida ina ta saƙe-saƙen abubuwa biyu a raina, maganar zubar da cikin Habiba da kuma haƙurin da Mustapha ya ba ni. Na samu kaina da faɗuwar gaba sakamakon hango Bilal da na yi a tsaye ƙofar gidanmu, cikin rashin kuzari na ƙarasa daman can babu kuzarin a tare da ni. Lokacin da na ƙarasa kusa da ƙofar gidanmu sai na tsaya dai-dai inda yake tsaye ina masa sallama.

“Assalamu alaikum”

A maimakon ya amsa min sai kawai ya ɗaga idonsa dake ƙasa ya kalleni.

“Miya hana ki zuwa aiki yau?”

Ajiyar zuciya na fara saukewa sannan na haɗe yawun da ke bakina na fara magana a daƙishe.

“Bana jindaɗi ne”

“Miyasa baki kira kin sanar min ba?”

Yanzu kan bansan mi zan ƙara ce masa ba, shirun da na yi ne ya bashi damar fassara ni da abunda yake hasashe.

“Saboda kin yi zaton na ganki ko? Wallahi Nawancy ban ganki babu Hijab ba, lokacin sa kike aikinki ina can ina nawa aikin, ba zan miki alƙawari ba amman zan yi ƙoƙari na kawar da idona daga kallonki idan kina aiki”

“Wallahi ba saboda haka ba ne Bilal, kawai akwai abunda ya ke damuna”

“Ko zan iya sanin minene?”

“Sanin ba shi da amfani, barin wannan sirrin a cikina zai fi min amfani”

Magana nake kamar zan fara kuka saboda damuwar da ke raina. Shi kansa ya fahimci haka saboda be saba ganina cikin irin wannan yanayin ba.

“Allah ya yaye miki damuwarki Nawancy, Allah ya zama gatanki, ƴa shiga dukan lamarinki ya tsareki daga dukan sheri, ya jiɓɓanci lamarinki, kada Allah ya barki da kanki” 2

“Amin”

Na amsa hawaye na bin fuskata. Ya lumshe ido ya buɗe.

“Ki shiga ciki, ni zan wuce, daman na rubuta wasiƙa a gurin aiki amadadakin cewar baki da lafiya”

“Zan shigo gobe”

Na faɗa ina share hawayen idona.

“Karki dakurawa kan ki, and if you need someone to talk to i’m here”

“Thank you Bilal you have encouraged me every time, Without you I don’t think I could ever be fine”

Na faɗa kuka na cin ƙarfina sosai. Har ga Allah ina jindaɗin zama da Bilal yana ƙarfafan min guiwa, yana damuwa da damuwata ko kaɗan baya son ganin ɓacin raina.

“Get some rest”

Na gyaɗa masa kai sannan na shiga cikin gida ina jin kamar na rafke na faɗi. Ɗakinmu na nufa jiki babu ƙwari, sai na samu Habiba a zaune tare da Inna kwanon ruwa na gaban Habiba jiƙe da magani. Na zauna nima ina buɗe ledar maganin.

“Gashi ya ce wannan uku zaki sha, wannan kuma biyu biyu sai wannan shi ma uku”

Na faɗa mata yadda ya rubuta a jikin kwalin maganin, sauran kuma duka na ɗiba ne, wasu biyu wasu huɗu.

“Tau ki bari har a jima ki sha, yanzu na jiƙa mata tagargade da gishiri ta sha”

Cewar Inna ni kuma na kalleta cike da mamaki.

STORY CONTINUES BELOW


“Tagargade da gishiri kuma Inna?”

“Ee yana yanke mara, wai ko za a samu cikin ya zube”

Wani dogon numfashi naja na sauke, na san ko na yi magana ba lallai ne Inna ta fahimta ba, idan har kuma nasa ta bar cikin a can gaba wani abun ƴa faru zata ɗora laifin a kaina.

“Bani maganin na sha ko zan samu sauƙin zazzaɓin nan”

Habiba ta faɗa tana miƙo min hannu. Tashi na yi na ɗebo mata ruwa na miƙa mata maganin ta sha, sannan na je na yi alwala har na yi sallah tunani ne a raina.
A tare da ita muka kwana a ɗakin, duk bayan minti biyu zuwa uku Inna sai ya miƙa mata tagargaden ta sha, haka ta kwana wulle-wulle sai abun ya zame mata biyu ga zazzaɓi ga ciwon ciki. Ita ke ciwon amman ni na kwana kuka ina jin zafin ciwon kamar a jikina ya ke, can kusan asuba Allah ya bata sauƙi har ta samu bachi.

Ni kuma na tashi da ciwon kai na yi alwala na yi sallah, ina zaune saman carpet ɗin ina karatun ƙur’ane har rana ta soma huduwa. Tashi na yi cikin ƙanƙanen lokaci na shirya na aika Sakina ta siyo kunu suka sha domin ni ko ruwa bana iya kaiwa a bakina.
Haka na kama hanya zuwa gurin aiki ba tare da na saka komai a cikina ba, duk kuwa da kasancewar ana cewa fita ba a karya ba bashi da kyau. Har na isa gurin aikin jina nake kamar ba ni ba, sai nake jin kamar ba ni nake motsa jikina ba, wata ƙila saboda nauyin da na tashi yana min yau ne. As usual sai da nayi duk abunda ya dace tun daga kan rubuta suna da time na yi komai sannan na shiga cikin kamfanin na soma aikina.

Ina daf da ƙarewa a ɗaki na ƙarshe, Amina ta shigo tana min magana kaɗan-kaɗan.

“Ƙawata ana kiranki, wai kin yi mopping da ruwa da yawa, matar nan sai masifa take”

“Wacece?”

“Wata mai’aiki a nan ce amman ita babba ce dan har office tana da shi”

Ba musu na bita muka tafi inda ta ce ana kirana ɗin wato a ɗakin dana fara mopping, abun mamaki sai na samu Zinatu tsaye a ɗakin tana sanye da suit da baƙin gilashi hannunta riƙe da wani ƙaramin akwati. 2

“Nawwara ke kika yi mopping ɗin gurin nan?”

Na ɗaga mata kai alamar Ee.

“Amman fisabilillahi haka ake mopping? Wai miyasa idan zaku yi abu baku yinsa tsakani da Allah, yanzu idan gidanku ne haka zaki yi, aikin nan fa biyanku za’ayi amman kuka abu da kissa kamar kyauta kuke yinsa haka sam be dace ba, yau da safen nan meeting zamu yi da manyan mutane yanzu idan suka shigo suka duba yadda kamfanin nan yake ai sai kuja mana ɓacin suna”

Yadda ta runtse ido take min masifa kamar bata san wacece ni ba, tabbas na bar ruwa saboda ga gurin nan har yanzu be bushe ba, sai dai ba da gangan na yi haka ba, na yi mopping ɗin ne a lokacin da hankalina baya gurin, sai dai ban jidaɗin yadda take ɗaga min murya ba kamar wata uwata.

“Ki yi haƙuri zan kiyaye a gaba”

Na faɗa abunda yake har a zuciyata shine, ƙawata sai dai a nan kuma ita ce babba a gurin aikina, kuma dole ne na bita idan har ina son cigaba da aikin.

“Better” 2

Ta furta tana ƙoƙorin juyawa sai ga wani mutun ya shigo shima cikin shigar suit sai dai na shi blue ne tsaɓanin nata da suke baƙaƙe. Har ya buɗe baki ya yi magana sai kuma ya fasa sakamakon idonsa da suka sauka a kaina. Bakinsa a sake yake kallona fuskaraa na nuna alamun mamaki, hakan yasa kunya ta rufe ni domin tun da na shigo kamfanin a yau ban samu kaina da jin kunyar tufafin da ke jikina saboda damuwata ta mantar da ni komai.
Sai dai kallon da yake min ya ya karantar da ni da akwai wani abu, wata ƙila ya daba ganina da Hijabi yau kuma ya gan ni babu Hijabi ko kuma dai yana mamakin yadda na ke aikin ne, tau tsaya ma wai ni ina na san shi balle na yi tunanin haka ni dai fuskarsa bata min kama da wanda na sani ba, wata ƙila dai shi ya sanni ne kai sai ka ce wata ƴar film ko mawaƙiya. 2

Ni kaɗai na ke ta tsaƙe-tsaƙe na domin kuwa Zinatu ta daɗe da ficewa ɗakin, yanzu daga ni sai shi ne sai kuma Amina.

“Newcomer?”

Ya tambaya ni kuma sai na gyaɗa masa kai.

“Your Name?”

Ya sake tambaya.

“Nawwara”

Ya rausayar da kansa sannan ya sake kallon na from head to toe sai ya juya ya fice.

“Shine mai kamfanin?”

Ma tambayi Amina bayan ya fice, sai ta zaro ido.

“Tab mai kamfanin zai tsaya tambayar sunanki, ai yana zuwa gurin nan zai ɗaukeki mari sai kin manta hanyar garinku” 2

“Saboda me?”

“Saboda wannan kuskuren da kika yi”

Na taɓe baki.

“Ni kan ba zan yarda ya wulaƙanta ni ba, saboda kawai ina aiki ƙarƙashinsa”

“Aiko idan baki ɗauki wulaƙanci ba, baki shirya aiki a kamfanin nan ba, amman na ga mutumen kamar ya san ki”

“Ni ban ma taɓa ganinsa sai yau, da alama shima a nan yake aiki ko?”

“Shi ma babba ne a kamfanin nan, kuma ance suna shiri da mai kamfanin sosai wai amininsa ne, ko meeting ne idan be samu damar zuwa ba shi yake turawa”

Haka muka fito tana ta labarta abubuwa da dama akan kamfanin da kuma ma’aikatan gurin cikin har da Zinatu da take ita sabuwar zuwa, sai dai ita ta rigani zuwa da wata huɗu, yadda take ta yabon kirki da kuma halin Zinatu har sai da abun ya ban tsoro wata ƙila duk wannan mugun halin nata mu take yi ma shi mu da muke tsofin ƙawayenta.
Komawa na yi ɗakin na gyara sannan na dawo na cigaba da aikina, bayan na gama na fito na nufi gurin da ake rubuta suna na rubuta duk abunda ya kamata ina kamawa sai ɗaya daga cikin mutanen da suke reception ɗin ya miƙa min wata farar takarda, ya bani wani file wai na saka hannu, bayan na yi karɓa na nufo gurin da na aje Hijabi na ɗauka na saka sannan na kama hanyar fita daga kamfanin ina warware takardar.

Naira ɗari biyar ce a ciki sai kuma sunan Bilal a jikin wata ƙaramar takarda, na san ya yi haka ne saboda na nuna masa bana son na ganni babu Hijabi. Ƙasaitaccen murmushi ne ya bayyana a fuskata murmushin da na manta rabon da na yi irinsa. Ƙamarar takardar mai sunansa na ɗauka na jeta a bakina na taune zuciyata cike da shauƙi Bilal.

Wannan shauƙin shi ya kawar min da komai na damuwata har na isa gida. Da sallama na shiga Jamila da Noor suka amsa min domin sune a tsakar gida, Inna tana ɗaki tare da Habiba. 2

“Miya hana ku zuwa makaranta?”

“Noor ne ya ce ba zai je ba”

Cewar Jamila kamin Noor ya karɓe mata.

“A’a Wallahi ita ta fara cewa ba zata je ba, Anti Sakina ce kawai ta tafi”

“Daman haka kuke so, idan bana a cikin gidan nan babu mai matsa muku kuje makaranta”

Da faɗan na shiga ɗakinmu, sai na samu Habiba ita kaɗai kwance ƙasa ƙafafunta lulluɓe da ƙaton kuma tsohon Bedsheet ɗin Inna.

“Habiba”

Na kira sunanta a hankali, sai ta ɗago ta kalleni amman da dukan alamu kamar bata cikin hayyacinta, domin alamu sun nuna hakan. Hannu na kai na buɗe bedsheet ɗin dake rufe da ƙafafunta sai ga jini a gurin kamar an juye jalkar manja, ba shiri na saki bedsheet ɗin na yi baya-baya dafe da baki ido a waje, zuciya mugun bugawa kamar an ce min ga mutuwata nan kusa da ni.!
6

WHAT DO YOU EXPECT NEXT?Na yi saurin rufe bakina idona cike da hawaye na nufi waje da gudu, ɗakin Inna na shiga ban sameta a ciki ba, ina fitowa waje Inna na fitowa daga banɗaki tana riƙe da buta. Kallo ɗaya ta yi min ta ɗauke kai ta nufi ɗakinmu, ni kuma na rufa mata baya hankalina a tashe. +

“Inna kin ga halin da take ciki kuwa?”

Ya gyaɗa min kai.

“Ko minti talati ba ki yi da fita ba, ta fara zubar jini ina jin cikin ne yake zubewa”

Tsugunawa na yi a gurin na dafe kai ina hawaye.

“Inna bata cikin hayyacinta”

“Dole ne zata yi haka saboda wannan ne na farko kuma kinga yarinya ce, amman zata warke zata dawo lafiya ƙalau”

“Inna dan Allah mu kaita asibiti”

Na faɗa ina fashewa da kuka, sai ta ce

“Babu inda zamu je Nawwara, zata warke”

Ta janye bargon ta soma gyara mata jiki ni ko ina duƙe a gurin ina aikin kuka. Haka muka wuni muka kwana babu wani canji sai ma ƙari, tun ina ganin tausayinsa har zuciyata ta fara raya min wasu abubuwa marasa kyau. Ita kanta Inna ta soma tsorata ganin mun kwana da ita a haka babu wani canji, ni ko na kasa zuwa aiki saboda ina ganin kamar idan na je na barta zan dawo na tarar ta mutu, ina jin kamar idan ina kusa da ita babu abunda zai sameta.
Can da yamma abun ya fara zuwa da sauƙi da har ina maganar ko Inna bata so sai na ɗauke ta na kaita asibiti saboda gudun kunya ba zan bar ƴar’uwata ta mutu ba.

Jikin nata babu ƙarfi amman hankalinta ya dawo, har ma ta ɗan jiro hannunta kaɗan ta ɗora saman nawa, kasancewar ina zaune ne kusa da ita saman tabarma. Numfashi take wahalce gaba ɗaya idanuwanta sun canja kamar wata tsohuwa.

“Sannu Habiba”

Na faɗa cikin muryar kuka ina mai tausayin ƴar’uwata, sai ta yi min murmushi hawaye ya fito daga gefen idonta.

“Ina Inna?”

Ta tambaya daker cikin muryarta na marar lafiya.

“Taje maƙota zata samo miki lafiya dubu”

Ta yi shiru tana lumshe ido, hakan yasa na tashi na ɗebo mata ruwa, na ɗan ɗaga kanta na kai mata kofin a baki, ba laifi ta sha da yawa kamar zata haɗe kofin har mamaki na yi na ce.

“Na ƙaro miki?”

Sai ta girgiza kai alamar a’a, sai ta rufe idonta tana numfashi a hankali. Ganin haka yasa na miƙe tsaye domin naje na kira Inna sai na ji ta kira sunana.

“Nawwara…”

Sai na koma na zauna ina kallonta.

“Na’am”

Na amsa ina kallon idonta dake rufe.

“Ance mace data mutu gurin haihuwa ana kyautata mata zaton samun aljanna saboda ta yi shahada, tau idan kuma mace ta muru gurin zubar da cikin banza fa?”

Ji nayi kamar jiri ya ɗibeni, hawaye uku-uku ya soma sauko min, ta farkon ido da kuma tsakiya, sai kuma ta gefen ido. Me Habiba take nufi ne? Wannan wace irin tambaya ce take min haka? Bakina a sake nake kallon yadda take numfashi. Ina haka Inna ta shigo, da fari gabanta ya faɗi ganin hadda hawaye suke min zuba sai dai ganin Habiba ta buɗe ido yasa ta ɗanji sanyi har ma da yin murmushi ta zauna kusa da ita tana nuna mata kulawa irin ta ƴa da uwa. Ta tsorata lokacin da takai hannu ta gwale idon Habiba, ya yi ɗorawa kamar marar jini, sai ta kalleni.

“Kamar bata da jini”

Kai kawai na iya gyaɗawa mata, sai ta miƙe tsaye da sauri tana kiran Sakina.

“Sakina zo ki siyo mata maltina da madara ta sha kamin muje asibiti”

Da gudu ta shiga ɗaki ta ɗauko kuɗi ta bada a siyo mata maltina uku da madara ta bata, sai kuma ta dawo ta zauna kusa da ita tana kuka.

“Na yi wauta Habiba yanzu zan kai ki asibiti, ban ɗauka abun har ya kai haka ba, kin zubar da jini da yawa” 2

A wahalce Habiba ta soma magana.

“Karki kai ni asibiti Inna, ko kin kaini mutuwa zan yi, kuma mutane zasu ji, na barku da damuwa, ƙara baki je ɗin ba domin Wallahi mutiwa zan yi-”

Na yi saurin kai hannu na rufe mata baki, sai ta lumshe ido, Inna ta tashi a firgice ta fita daga gidan tana kuka, kamar jira take na janye hannuna daga bakinta sai ta ce. 2

“Nawwara zan tafi na barki ke kaɗai…”

Na sake rufe mata baki ina kuka. Sai ga Inna ta shigo.

“Riƙata ga Napep can na na tsayar zamu kaita asibiti”

Kamar waɗanda suka ɗauki takarda haka muka ɗaga Habiba, jikinta ya yi sanyi sosai ƙwayar idonta baƙar ta ɓata ɓat sai farin kawai kake gani. Cikin hanzari muka saka mata wasu tufafin muka saka mata Hijabi muka ɗauketa sai gurin mai Napep.
Muna shirin shiga Napep ɗin Sakina ta dawo daga siyen madara da maltuna, tsabar hankalin Inna ya ɗauku bata ko iya karɓa ba muka kama hanyar asibitin uduth dake gawon nama, duk da da kasancewar mun san asibitin ta kuɗi ce.
Gudu sosai mai napep ɗin ke yi amman kasancewar tsakanin unguwarmu da asibitin uduth akwai ƴar tazara sai da tafiyar ta yi mana nisa. Muna isa bakin gate ɗin asibitin, Habiba ta sauke wani irin ajiyar zuciya ta kwanto da kanta dake jikina zuwa jikin Inna, rai ya yi halinsa ƴar’uwata ta amsa kiran mahaliccinta…!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *