BATUUL CHAPTER 25 KARSHE

BATUUL 
CHAPTER 25 KARSHE

*………SEVEN MONTHS LEAP*
    
      Tsaye take a kitchen da yamma tana soya wainar fulawa, wayarta da tayi k’ara ta duba, ganin mai k’iran yasa ta sakin wani k’ayattacen murmushi, da wannan sunyi waya a yau kad’ai yafi sau goma sha biyar, har face time sunyi amma yanzu ma k’iranshi ke sake shigowa, hannunta ta goge da napkin snn ta d’auki wayar tasa a kunnenta, tana d’agawa taji yace “Glitter ki dena bari yayi ta ringing before you pick”, murmushi tayi tace ” Amore aiki nakeyi before ka bugo”, ido ya wara kamar yana gabanta tareda dafa goshinshi yana tafiya yace “Ya Allah, aikin mey kikeyi?, ba nace bana so ba?”, ji tayi maganarshi na kusantota, a hankali ta juya inda take jiyo muryan, k’ara ta saki tareda yar da wayan zata gudu ganinshi jingine bakin k’ofa yayi tucking hannunshi d’aya cikin aljihun wandonshi yana kallonta, da hanzari ya k’araso wajenta ya janyota jikinshi ya rungume, sosai ya matseta jikinshi sabida yanda ta tsorata, shi da kanshi saida ya tsorata ganin irin gudun da ta saka kamar wani abin zai sameta ita da cikin da ya bayyana a jikinta, a hankali ya dinga patting bayanta yana karanta mata ayatul kursiyu cikin kunne, a hankali ta dinga sauk’e ajiyar zuciya, muryarta na rawa kamar mai kuka tace “Amore you scared me”, saida yaji ta nutsu snn ya rad’a mata a kunne “am sorry Glitter, I didn’t mean, I just wanted surprising you”, sake shigewa jikinshi tayi tace “You just did ai”, dariya yayi tareda d’agota daga jikinshi “I just remembered, aikin mey kikeyi glitter?”, ya tsareta da ido, sunkuyar da kai tayi tareda turo d’an bakinta, cikeda sanyin murya tace “Kagani ko wainar fulawa nake ta son inci kuma bansan ya zanyi ba, kai kuma baka nan shinefa na shiga kitchen ina dafawa, bama dayawa bane muje in nuna maka”, tasan babu abinda zatayi ya b’ata mishi rai, koda zai b’aci kallonta na sashi manta komai, bare yanda take mishi magana yanzu, d’an k’aramin bakin nata ya kama yace “wayo zaki min ko, shine harda pouting min lips d’inki?” Da sauri ta girgiza mishi kai tana mirmushi tace “dagaske nake”, ya mik’ar da ita shima ya mik’e yace “ba nace ki dinga bari zanyi miki ba, sai kin bawa babyna wahala?”, juyowa tayi ta fuskanceshi ta tallabo fuskanshi da duka hannayenta biyu tayi pecking duka tace “ai kam bana so ka wahala, kuma fa “, ya sakar mata hararan  wasa yace “meye shi wainar fulawan da ya saki kin jin maganata?, muje in gani”, raurau tayi da ido tace “Amore banqi jin maganan ka bafa?”, ta fad’a tana tsaye inda take, juyawa yayi ya kamo hannunta yace “its been long I see these tears, bana son ganinsu yanzu ma”, baki ta zumb’uro mishi tace “toh ka yadda ban qi jin maganan ka ba?” Ya had’e rai yace “Muje dai in gani”, ya riqo hannunta suka k’arasa gaban stove d’in, yatsina fuska yayi yace “wannan Ne?”, a hankali ta gyad’a mishi kai, stool ya janyo mata ta zauna akai snn ya ciri apron d’in dake rataye ya d’aura, cikin watanni ya koyi abubuwa da bai tab’a tunanin yinsu ba, sauran paste d’in da ya rage ya shiga soyawa a pan d’in, tana daga zaune tana kallonshi, tasan ko zata kwana tana cewa ya barta tayi da kanta ba yadda zai ba, a hankali ta bud’e baki tace “Amore”, volume d’in stove d’in ya rage yana kallonta yana jiran jin mey zatace, kamar mai jin tsoro tace “Amore fushi kakeyi har yanxu ko?”, gabanta ya dawo yana janyo d’aya stool d’in stool d’in ya zauan yana lakuce mata hanci yace “cute face d’innan naki zai bari inyi fushi dake ne?, ko nayi fushi idona na fad’awa d’an lips d’innan nake hucewa”, kai ta girgiza mishi dan ita ba abinda take nufi ba kenan, amma tunda bai gane ba sai tace “koh nayi laifi baza ka min fad’a ba?”, yace “zan miki fad’a but ban iya fushi dake, you are too cute da son da nake miki bazai barni in iya fushi dake ba, nasan in nayi fushi dake nima zan ji jiki,”, tace “Yaa Abu itama kayi mata fad’a mana kaji, fushin nan da kake yi da ita ba tareda tasan makomarta ba yana wahalar da ita, Kayi hak’uri ka yafe mata, kayi mata fad’an amma kayi hak’uri ka janye fushin nan da kakeyi mata plsss”, take far’ar dake fuskanshi ya b’ace, hannunta dake cikin nashi ya janye tareda mik’ewa zai bar wajen, da sauri ta riqo mishi hannu tana girgiza mishi kai idonta tab da hawaye, d’an siririn tsaki yaja yana girgiza mata kai dan bayason hawayen nan su zubi yace “Glitter I thought we were done with that, ba nace bana son zancen nan ba”, tace “Allah ni har raina na yafe mata, wlhy son da take maka ya sata aikata abinda duk tayi, Amore tayi hak’uri sosai, batareda da ka sani ba kayi auren nan, mey kake so tayi?, she was angry, she was feeling betrayed, tunaninta duka kaci amanarta ne”, wani irin rik’o da yayiwa hannunta saida ya tsorata ta, with stern masculine voice d’inshi yace “shine take so ta kashe min, akwai wani abu da yakeda hujjan kisa a duniya?, in kin mutu me zatacewa Allah?, because she was feeling betrayed sai ta nemi yin kisa?”, kai kawai Batuul ke girgiza mishi tana hawaye, tana son ya fahimci kishi babu abinda baya sawa indai kana son maishi, ba kishi saida so, hab’arta ya d’ago yace “Look at me”, a hankali ta d’ago idonta ta kalleshi, yace “goge hawayen”, babu musu tasa hannu tana goge hawayen, hannu yasa yana goge mata sauran hawayen yace “This should be the last time we will talk about this kinaji?”, a hankali ta kad’a mishi kai, yace “Look at me and talk”, a hankali tace “toh, am sorry kaji?”, ido ya lumshe ya bud’e yace “tashi muje kici wainar taki”, ya d’agata ya sauk’ar kan kujera snn yayi mata plating wainar, Fridge ta bud’e ta ciro jug d’in zob’on da ta had’a, kallon jug d’in yayi snn ya kalleta yana langab’ar mata da kai, tayi murmushi tace “inasone fa insha, tun safe nake kwad’ayinshi”, baice komai ba ya sa hannu ya karb’i Jug d’in daga hannunta, flask d’in dake ajiye kan island d’in yaga ta d’auka, ido ya wara yace “again?”, this time ita ta langab’ar da kan, da sanyin murya tace “kunun kane nayi maka”, kai kawai ya jinjina ya d’au flask d’inma, palo yaje ya baje mata komai snn ya koma ya d’auko cups d’in, ganin yanda ta baje tana cin wainar fulawan har dariya ta bashi, d’agowa tayi tana kallonshi da tsukakken bakinta da yaji duk yabi ya dameta, ruwa ya mik’o mata yana dariya yace “dole ne cin yajin?”, bakinta ta sake tsukewa tace “yafi dad’i da yaji”, zama yayi yana janye plate d’in gabanta yace “nidai kar a koyawa babyna cin yaji”, raurau tayi da ido tace “toh buh lemme have my plate back”, kai ya girgiza mata yana juye yajin a d’aya plate d’in da babu komi, marairaicewa tayi tace “Da yajin fa yafi dad’i”, kai ya girgiza mata yace “am not taking the risk, ga wannan na rage miki”, ya mik’a mata plate d’in da d’an kad’an ciki, karb’a tayi ta zumb’uro mishi baki tana cin abinta, zama yayi yana shan kununshi bayan ya gama yace ta rakashi pool d’in dake bayan gidan, tare sukaje tana zaune ya shiga ya gama wankanshi dan ya hanata koda k’arasawa wajen bare ta shiga pool d’in, bayan sunyi sallahn magrib suka fita tare tafiya asibiti dan EDD d’inta ya kusa, snn akayi reffering d’insu asibitinsu na Nigeria dan Ammah tace Lallai Lallai su dawo tunda ta kusa haihuwa, a waje suka ci abincin dare snn ya biya dasu Trotters, waje ya samar mata ta zauna, da kanshi ya dinga zagayawa yana kwaso kayan baby da maternity clothes tunda ga kan coats, jumpers, leggings, shauls, towels, Baby bathing sets, craddles, ds duk saida ya tanada kuma duk designers, daga M&S sai Ck, duk in ya d’auko sai ya kawo mata ta gani tukunna kuma yawanci na mata yake kwasa ko kuma unisex, tun tana ganin yawansu tana cewa ya bari in ta haihu lafiya a siya sauran yana qi har tayi shiru ta zubawa sarautar Allah ido, da tayi mishi maganan yayi mata addu’a kawai, ba lallai ta haihu da lafiya ba, had’e rai kawai yakeyi yace mata shi tana dena fad’an haka, shiru kawai takeyii dan batason ranshi yana b’aci, sai wajen sha d’ayan dare ya gama siyayyan nashi yasa akayi packaging wasu aka tura Nigeria saura ya barsu a nan, kamar ba kud’i yake zubawa ba haka suka dawo gida, washegari ma da daddare suka sake fita ya sake kafa wata sabuwar siyayya, ana gobe zasu dawo Nigeria suna zaune parlour tana jikinshi yace “Glitter?”, d’agowa tayi ta kalleshi yace “Kina da sunan da kike so a sawa Babyn?”, kallonshi ta tsaya yi snn ta girgiza mishi kai a hankali tace “A ah, duk wanda ka saka ma zaimin”, kitson da shi ya kama mata yake warwarewa yace “you sure?”, kai ta kad’a mishi, a hankali ya sunkuya yayi pecking goshinta “I love you”, murmushinta mai kyau tayi tace “I love you more”, tara ya kashe musu wuta ya taimaka mata suka haura sama, baccin su sukayi peacefully cikeda shak’uwa, washe gari suka shirya suka tafi Nigeria, babu yadda Abu baiyi Ammah ta barshi su sauka gidansu ba tace sam bata San zancen ba, a gidansu zata zauna, tun a waya yace “Ammah Al’ada nefa duka wannan, ya za a raba miji da matarsa bayan ba fad’in Allah bane, tun lokacin ta balbale shi da masifa, badan yaso ba suka sauk’a a gidan Ammah akan bayan kwana biyu zai kaita, ana gobe zai kaita gidan Aunty tana zaune kan gadon tana shan cream in chicken soup, shi kuma yana gaban desk top yace “Glitter yanxu kema yadda zakiyi a d’aukemin keh har tsawon wata da wani abu?, I can’t even imagine a day without you, nasan in keh kika fad’awa Ammah zata yadda”,  murmushi tayi tace “Amore you know I will miss you more ko, with every passing second?, its a tradition, yanzu zaka ga ya wuce”, pouting bakinshi yayi yace “Shikenan”, ta bud’e baki kenan zatayi magana taji wani suka ta bayanta, ido ta rintse tana ambaton sunan Allah, plate d’in dake hannunta ta ajiye ta a hankali tana k’ok’arin mik’ar da k’afanta, lip d’inta na k’asa ta cije tana cewa “Yasalam”, juyowa yayi ya kalleta, da hanzari ya sauk’o yana d’agata yace “Glitter mene, cikinki ne?”, ido ta rintse tana riqe mishi hannu tace “Yaa Abu bayana”, duk ya gama rikicewa yama rasa ya zaiyi, d’agota yayi yana yi mata sannu zai fita da ita, kamin su fita Ammah ta shigo d’akin kawowa Batuul kunu, da sauri ta ajiye abinda ke hannuta ta k’araso tana “Subhanallah, Bitti ciown ne?”, Batuul da ta kasa magana Ammah ta k’araso ta riqe tace “Aliyu d’auko key, I think its delivery, duk ya gama rikicewa ya d’auko key snn ya ciccib’i Batuul dake ta cije lips sbd azabar zafi, a parking lot suka had’u da Farida ta dawo daga school tana parking mota, da gudu ta k’arasa wajensu tana tambayansu, ganin babu mai bata amsa ta koma motan ta bi bayansu, suna zuwa asibitin aka karb’e cikin gaggawa akayi Labour room da ita Binsu yayi a baya zuwa d’akin da aka shigar da Batuul d’in, daidai bakin k’ofa wata nurse tace “We are sorry Sir, but you can’t get in”, wani irin kallo ya jefeta dashi da yake mata nuni da bakida hankali ko, da sauri ta sauk’e idonta k’asa tana cewa “am sorry sir”, hannu yasa ya matsar da ita gefe ya tura k’ofar shiga d’akin, kan gado ya tarar da Batuul kwance har an bata maternity wear, sun fito da duk wani abu da ake buk’ata, da sauri ya k’arasa gadon da take kwancen, ido kawai ta rintse tana ambaton sunan Allah dan yau hawayen ma nemanshi take ta rasa, dukda azabar da take sha hakan bai hanata jin d’umin hannunshi cikin nata ba, a wahalce ta bud’e idanunta ta sauk’e cikin nashi, ido ya lumshe ya bud’e, bayason ganin wannan yanayi da take ciki, a hankali tace “Yaa Abu Aunty”, kamar wacce ta watsa ruwa haka sweat duk ya jik’ata, hannunta dake cikin nashi ya riqe ya kai bakinshi tareda kissing yace “You will be fine Babyna, we will make it together, am here kinji?”, ido ta lumshe tana kad’a kai cikeda azaba tace “inaso inga Aunty, plss call her for me kaji Yaa Abu, inaso in ganta”, ta fad’a tana sake cije leb’e, gaba d’aya ta gama rikitashi, shima so yake kawai yaga hawaye ya zubo mishi ko zaiji dad’i da wannan irin ciwon da yake jimata, daidai fuskarta ya sunkuyo yace “Glitter you will b okay, Aunty will be here anytime,Ammah zata fad’awa Aunty, am upright sure, she will b here shortly, sannu kinji?”, daidai lokacin da doctor da nurses d’in suka k’araso cikin shirin aikinsu, ganin Abu zaune Doctor yasa yace “Good Afternoon Mr Kyaree, we are sorry but we need you to stay outside to carry out our work efficiently”, fiyeda kallon da yayiwa Nurse d’in d’azu yayiwa Doctor dukda sabon dake tsakaninsu amma yau mantawa yayi da hakan, gaba d’aya ranshi ya gama b’aci, matarshi in such a pain maimakon yayi attending to her yake kawo masa shirmen banza wai ya fita, a fusace yace “Get yourself composed Doctor and attend to my wife, She is my wife, we are in this together, I ain’t moving an inch from here”, ya sake maimatawa sternly snn yace “And if anything happens to her?, am gonna shut d whole hospital down, you will all pay for it”, yayi maganan idonshi na kad’awa, “Damn it, Doctorrr”, ya fad’a kamar zai make doctor, ganin dagaske yake kuma zai b’ata musu lokaci yasa kawai suka fad’a aikinsu cikeda k’warewa, duk wani kuka na Batuul yau nemanshi tayi ta rasa, Addu’o’in da Abu keyi yana tofa mata duk wanda ta kama shi takeyi, da taji azaba lokacin take tuna Aunty, take zata fara Rabbir Ham huma kama rabbayani Sagira, duk wani motsi da Batuul zatayi har cikin ranshi Abu ke jinshi, sosai ya tausaya mata ganin irin wahalan da take sha, a lokacin ya sake ganin kima da daraja irin ta mata had’e da tausayinsu, in basu ba wazai iya enduring irin wannan ciwon, addu’a yayiwa duk wata mace wacce aka haifa da wacce ta haifa, a hankali ya fara tofa mata “wa tilka hujjatuna atainaha Ibraheema ata qaumihi, narfa’u darajatin man nasha, inna rabbaka hakeemun aleem”, a zuci ta dunga maimaita aabinda taji yana fad’i, a hankali taji ciwon na raguwa, ba a cika one hour ba ta sumb’ulo y’ar Babynta k’arama mai kyau itama, Hamdala Abu yayi yana kai hannu zai tab’a Babyn Doctor yace Mishi “No pls, not now”, yatsina fuska yayi ya janye hannunshi, tareda shi suka taimaka aka gyara aka kimtsa Batuul da Baby, bayan an fito da Babyn yana zaune bakin gadon da Batuul ke kwance yana mata sannu suka mik’o musu Babyn, da Bismillah yasa hannu ya karb’eta daga wajen nurse, gaba d’aya komai na jikinta farine, babu komai nata a waje sai d’an k’aramin face d’inta, wani irin k’auna da nutsuwa da baisan daga inda yake sauk’o mishi ba yakeji jin d’umin Babyn jikinshi, murmushi ne ya kufce Mishi ganin komai na fuskan Babyn irin nashi, lips d’inta ne Kad’ai irin na Batuul hatta heart shape d’in bottom lip d’in nata irin na Batuul ne, a hankali ya matso da Babyn kusa da Fuskan Batuul yace “Fatima our child, our Baby, kyautar da Allah yayi mana Fatima, look at her please, she is too cute for me”, murmushi kawai Batuul tayi dan bata jin k’arfin jikin nata sosai, daidai kunnen Babyn ya sunkuya tareda k’ira mata Sallah, ya karanto “inni sammaituha (A’eesha) wa inni u’ixuha bika wa xurriyatiha minash shaaid’anir rajim” yayi mata addu’o’i sosai tareda yi mata Hud’uba da Suna A’eesha, Dabinon Ajwan da dama yana cikin kayansu yasa aka mik’o mishi da ruwan Zamzam ya tauna ya d’iga mata tareda ruwan Zamzam d’in, kamar wacce tasan abinda akeyi ta yatsina fuskarta tana lashe baki, dariya yayi ya sunkuya yayi kissing goshinta snn ya matsa jikin Batuul d’in yace “Glitter?”, a hankali ta d’ago lumsassun idanunta ta dubeshi, yace “kin bani kyautar da duk duniya babu mai bani irinta, you have given me the best gift I would ever ask off, I will forever be grateful, Allah ya barmin keh Glitter kici gaba da bani wasu Babies d’in, just tell me anything you want, ko meye shi indai akwai shi a nan duniyan, I promise to get it for you, you have given me the best gift of life, I promise you, just ask me duk abinda kikeso zanyi miki shi, just tell me jinni”, a hankali ta bud’e idanunta da suke a lumshe, kallonshi takeyi da murmudhi d’auke kan fuskarta tana tunanin abinda takeson cewan, tasan duk murna ne ya cikashi amma da wuya ta samu abinda takeson, a hankali ta bud’e baki tace “You Promise?”, kallonta yayi for seconds kamin ya kad’a mata kai, zai yi magana doctors da nurses d’in suka zo za a canja mata d’aki, tana kwanace suka turata zuwa wani d’akin, badan ta saba da ireirensu ba da zatace d’aki ne kawai ba na asibiti sbd girma da kuma kyansu, saida Nurses d’in suka gama duk wani necessary abu da ya kamata suyi mata itada Babyn snn suka kwantar da Babyn gaban Batuul suka fita suna mata sannu, kallonsu yayi with so much adoration yana yiwa Allah godiya da kyautan nan da Allah yayi mishi, Batuul is one part of him da baya tunanin zai iya rayuwa babu ita, hannunshi yasa ya kamo na Batuul d’in yana d’an murzawa a hankali yace “Fatima you are the best thing that ever happened to me kinsan da haka ko?”, a hankali ta kad’a mishi kai yaci “I know I love, ban san amfanin kud’ina ba if I can’t give you abinda kike nema, komeye shi kike so indai bai sab’awa addini back just mention the anything, zanyi miki shi Glitter”, ya fad’a yana sassauta muryarshi tareda sak’ale yatsunsu waje d’aya, a hankali ta bud’e baki tace “Yaa Abu ka dawo Ajiddeh gidanka, zamanta haka ya isa batareda sanin makomarta ba, banasone ka shiga hakkinta, na fad’a maka nikam na yafe mata wlhy, nobody is above mistake, kuma everything happens for a reason, maybe for us to realise each others worth, how much we mean to each other, Yaa Abu plssssss”, ta k’arasa maganan tana lumshe ido , shi kad’ai yasan irin impact d’in da Batuul ta yiwa rayuwanshi, mesa baza ta fad’i wani abin ba sai wannan, har ga Allah ko jiya da Abui ya sake mishi zancen Ajiddeh  ce mishi yayi zai rabu da ita, zai sallameta, duk da ya yafe mata shima amma ya kasa samun wajen da zai ajiye abinda ta aikata ya manta dashi, baya tunanin zai iya d’aukan wani abin da zai sami family d’inshi ya qyale maishi nan gaba, amma its about Batuul yanzu, she is worth more than that, He can sacrifice that atom of happiness da ya rage mishi for her to be happy, tana son ya maida Ajiddeh d’akinta, kuma alk’awari yayi mata akan ta fad’i abinda takeso, how can he just deny her , a hankali ya sauk’ar da idonshi kan fuskan Batuul ya shafi gefen fuskarta da d’aya hannun nashi yace “will that make you happy?”, kai ta kad’a mishi, murmushi yayi mata yace “Anything for you Fatima, just know I will always love you”, murmushin ta mishi amma jin yanayin da yake  sab’ule hannunshi cikin nata yasa murmushin dake fuskarta bajewa, duk da rashin k’arfin da takeji hakan bai hanata damqe hannunshi ba, kallonta yayi, ganin hawaye idonta yasashi zama da wuri yana girgiza mata kai, cikin siririyar muryarta tace “Are you sad, angry about what I requested for?, ka bari na fasa if you are not okay with …..”, bai bari ta k’arasa ba ya d’aura dogayen yatsunshi kan lips d’inta yace “Shhhh, am happy with whatever that makes you happy, okay?”, kai ta kad’a mishi yayi murmushi yace “Good girl, get some rest”, ya fad’a yana d’aga mata girarshi d’aya, murmushin tayi mishi itama tareda lumshe ido, ido ya tsura musu itada y’ar Babyn dake gabanshi yana kallonsu yana dad’a yiwa Allah godiya da ya bashi wad’annan precious kyautan a rayuwanshi, yana nan zaune yana kallonsu aka turo k’ofar d’akin, Abui ne sai Ammah, Farida sai Sadiq, lokacin doctors suka sanar dasu da Batuul ta sauk’a lafiya zasu iya shiga su kanta, tsabar murna Farida har rawa jikinta keyi sbd d’okin zuwa taga niece d’inta, y’ar yayanta y’ar Bestyn ta that turn out to be a sister, Abui ne ya fara d’aukan Babyn da murmushi a fuskanshi yana tuna lokacin da ya fara riqe Abu for the first, yace “This is how I held Aliyu , kamar jiya fa gashi yanzu Allah ya bani tsawon rai nayi witnessing haihuwar y’arshi, Allah yayi muku albarka baki d’ayanku”, ya fad’a tareda kissing goshin yarinyar, duk suka amsa da “Amin”, Ammah ce ta karb’eta daga hannun hannun Abui murmushi d’auke fuskanta snn ta kalli Batuul dake kwance tana bacci tace “Allasarki Bitti, yadda kukaga wannan jaririyar haka Fatima take lokacin da aka haifota, tun ranan Allah ya dasa min sonta a raina kamar ni na haifeta, ashe itace zata fara samar min jika, Allah ya k’ara miki lafiya ya d’ayyiba miki zuri’a”, duk suka amsa da Amin, Abu ya dubi Ammah yace “Ammah an fad’awa su Aunty? Tun d’azu take nemanta”, ya fad’a yana kallon Batuul, Ammah tayi murmushi jin Batuul nata Neman Aunty tasan zafin haihuwar yasa ta neman Aunty, tace “Dama ana shiga da ita na fad’a musu toh bayan doctor ya fad’a mana sauk’arta lafiya nayi maza na sanar dasu, da yake ma can d’in za a kaita basai sunzo nan d’in ba ai”, ya d’an tsuke baki yace “Ammah har yanzu wai zancen kaitan na nan?, wlhy hankalina zaifi kwanciya in ina kusa dasu, zan kula dasu Sosai In sha Allah, Plssss Ammah”, ya k’arashe maganan kamar mai shirin yin kuka, dariya ma yaso ya bawa Ammah amma ta dake tace “Kai nifa ban cike da shirme kana jina, ba al’ada bace da zaka wani ce kafison a bar maka su?, toh ba kanka za a dena ba, gidansu ne sai ta tafi yin wanka”, badan yaso ba ya hak’ura ya miqe tareda yin sallama dasu, Farida da batasan me ke faruwa ba duk hankalinta na kan jaririyar kamar zata maidata ciki ya duba yace “Farida let her be plssss, bacci takeyi”, kallonshi tayi da murmushi a fuskanta tace “nifa nasan da ni take Kama, bari ta tashi zaku gane abinda nake fad’a muku”, kai kawai ya kad’a yace “Naji ai ke zakiyi rainaonta but for now barta ta huta, bata ma saba da iskan duniyar ba bare wahalar cikinta”, cikeda murna Farida jin yace ita zata yi raino ta matsa da baya da sauri tace “Ai na ma matsan, Allah ya raya mana Babyn mu, Sunan waye za a saka mata?”, har ya fara tafiya kamar ya fad’a mata ko sunan wa yarinyar zataci ya fasa, Abui ne kad’ai yasan meye sunan jaririyar, yayi murna sosai ya sa musu albarka su dukkansu, tareda fatan Allah ya k’ara had’a Kansu, Sallama yayi da Ammah da Farida ya fice daga d’akin, Kai tsaye gidan Aunty ya, yasa akayi mata magana dan bata parlour ko kince, kamar kullum cikin shigarta ta alfarma da gayu ta sauk’o, ganin Abu ne yasa ta d’an fad’ad’a murmushin dake fuskarta, yana hangota ya sauk’o daga kan kujeran tareda d’an duk’awa ya gaidata, wani kunyan Aunty yakeji yau na daban, ta amsa mishi snn ta mishi barkan k’aruwan da ya samu tareda addu’o’i, murmushi kawai yakeyi yanajin dad’in addu’ar da take musu, tasa aka kawo mishi refreshments, ruwan kawai ya bud’e bai kai ga sha ba ya fad’a mata abinda ke tafe dashi, might murmishi Aunty tayi, ita da kanta taji tausayin Batuul, tasan wahalan haihuwan da ta sha ya sa take son ganinta, da murmushinta tace “Kaima Aliyu sai ka biyewa shirmenta Batuul kaima, me zuwan nawa ma zai mata in banda shirme irin na Batuul, addu’a kawai zamuyi mata da fatan sauk’a lafiya kuma Alhamdulillah Allah ya amsa mana addu’a, sai kuma yanzu muce Allah ya k’ara musu lafiya ita da abinda ta haifa”, kanshi a k’asa yace “Aunty ayi hak’urin dai muje in ta farkan ta ganki dan tun d’azu take ambatonki, she will be to wake up to you by her side”, Murmushi kawai Aunty tayi tace “Tohh shikenan bara insa a shirya mata abubuwan da na sa akayi mata sai insa Baa Liman ya kaini in tq gannin hankalinta ya kwanta na dawo”, Sam Abu yaqi yadda saidai Aunty ta bishi, badan taso ba ta haqura suka tafi, a asibiti da kanshi ya bud’e mata k’ofa tareda samo ma’aikata su shiga da kayayyakin dake baya, har lokacin Batuul bacci takeyi, har mamakin yawan mutanen dake d’akin yayi, sai barka suke mishi da Allah ya raya, gaisawa yayi dasu snn yayi musu sallama ya fita, yana fita ya qira Massa akan zaizo ya sameshi zai rakashi, kai tsaye gidan ya wuce, Abu ke tuk’a motar Massa na daga gefe yana taya Abun murnar k’aruwa, sai shak’iyanci yake mishi, ganin yaqi kulashi yace “Wai kai inama zamune haka?”, Abu ya shafe fuska yace “Gidansu Hauwa zani, I promised Batuul to take her back”, Massa ya wara ido yace “Amma kai duniyanci duk ka iyashi, are you telling me all these while tana gidansu da aurenka kuma kanta?”, Tsaki yaja yace “Kaga ni karka dameni, she caused everything, and I can do it bitter and better than what I did, am talking about Fatima, she is my reality, I can’t risk anything da zai cutar da ita, and taking back Ajiddeh is a compromise, she told me she dd be happy, so please spare all these naggings”, Kafad’arshi Massa ya dafa yace “You are a man, you can take whatever, kawai Addu’a zakayi Allah ya shige maka gaba”, a sanyaye ya amsa da “Amin”, shi gaba d’ayanshi baisan ta ina zai fara ba, seven months amma bai tab’a waiwayarta ba sai Yanzu, har yazo k’ofar gidansu Ajiddeh yana sak’e sak’e a ranshi, masi gadi da sauran ma’aikatan dake bakinta da murna suka dinga gaidashi dan sun sashi da kyauata da yi musu alheri, saida yayi parking yasa a duba mishi ko Dad na gidan, in yana nan ayi masa iso dashi, hakan kuwa akayi akace musu yana daga garden, can wani yayi musu jagora suka isa, yana zaune kan d’aya daga cikin kujeraun dake k’ark’ashin hut d’in wajen da ruwa gabanshi, da mamaki Dad ke kallon su har suka k’araso wajenshi, a ladabce suka gaida Dad, da fara’a ya amsa musu kamar wani abu bai shiga tsakaninshi da y’arshi ba, har saida Abu yaji kunya ganin yanda Dad ke janshi a jiki, shiru ne ya biyo baya kqmin Abu yayi k’arfin hali a sanyaye  yace “Dad munzo mu bada hak’uri kan abinda ya faru, kuskurene da muka aikata bisa son zuciya, nazo in koma da Hauwa d’akinta, Allah ya have mana baki d’ayanmu” Dad da ya k’ura mishi ido ya cire glass d’in dake idonshi yana kad’a kai yace “Aliyu tun lokacin da Hauwa tazo min da zancen kai zata aura nasan tayi sa’an miji, nayi murna sosai dan nasan zaka kula da ita iya gwargwado, tun kana k’arami lokacin Ina aiki k’ark’ashin mahaifinka nasan kai yaro ne mai dattako, Aliyu ta fad’amin duk abinda ya faru tsakaninku da ita saidai kunyar mahaifinka da nakeji bazai barni inje baku hak’uri, nasan sunyi muku kuskuren da bai canci wannan yafiya ba, saidai duba da irin gidan da ka fito yasa bazanyi mamaki ba, ina mai sake baka hak’uri kan abinda suka aikata muku,, maganar kkmawar Hauwa kuma Aliyu tunda ka tako da k’afarka bazan iya hanaka ba, amma tunda hakane inason duk wani kuskure da zata sake maka ka hukuntata fiyeda yanda zanyi dan in har ta yadda ta sake takowa gidan nan da sunan tayi maka laifi toh saidai ta nemi wani uban ba ni ba kuma”, daidai Abu zai amsa wata mata ta k’araso da babbar rigan a hannunta, bata lura da mutannen dake wajen ba ta k’arso tana cewa “Daddy nikam baka gama karanta Jaridan ba, you are getting late fa”, sai lokacin ta lura da su Abu, dukda face d’in Abu looks familiar but ta kasa tuna inda ta sanshi, Dad yayi musu introducing juna kan itace sabuwar matar da ya aura 4months back sunanta Kulthum,  su kuma ya nuna Abu yace “wannan shine mijin Hauwa Aliyu, wannan kuma d’an uwanshi ne Mustapha”, sai lokacin ta tuna inda ta sanshi, duk d’akin Ajiddeh hotunan shine hatta gaban wayarta hotunanshine, da murmushi suka gaisa, Dad ya karb’i riganshi yace “Sai su shiga daga ciki, ni inada meeting, yanda kukayi duk ka sanar dani Aliyu”, ya Amsa mishi da Insha Allah da yi mishi fatan a dawo lafiya, a d’akinta Aunty Kulthum ta tarar da ita kwance duk ta rame tayi duhu, kamar ba ita bace ba wannan Ajiddeh sarkin gayu da d’osana lipstick ba, gashin nan ma da yake shan gyara duk ya kad’e, wutan d’akin Aunty Kulthum ta kunna tana mai k’iran sunan Ajiddeh Kai tsaye Aunty Kulthum closet d’inta ta nufa ta bud’e tana cewa “Ajiddeh ki tashi Allah maji rokon bayinsa ya amsa mana addu’armu, Allah gafarur rahim ya dubi niyyarki ta tuba kuma yaji kukanku, maza tashi ki shiryaki baqinki na guest parlour suna jiranki”, kamar ba da ita akayi zancen ba ko juyowa batayi ba saima rintse ido da tayi tana maida k’afafunta k’ark’ashin duvet, Aunty Kulthum tafi kowa sanin matsalarta mesa zatazo ta dameta da surutun tayi baqo, ita ba kowa tayi da yaxo wajenta ba, koma wacece saidai ta tafi dan batajin tanada kuzarin da zai iya mik’ar da ita daga wannan kwanciyar, ita kanta ma ciwo yake mata, juyowa Aunty Kulthum tayi bayan ta ciro wani lace cikin closet d’in tace “Kehhh ashe haka Aliyun nake had’add’e, dole mana ki rikice kanshi irin wannan gayun haka da had’uwa, ai hotuna ma basa mishi adalci indai shine wannan”, idanunta da ta rintse sbd sarawa da kanta keyi ta bud’esu a hankali daidai inda tasan zasu sauk’a kan d’aya daga cikin enlargements d’in Abutturab dake d’akin tanason sake ganin ko da wani sabon canji ne jikin hoton da sai yau Aunty kulthum d’in ke gani, dubawa tayi sosai bata ga wani sabon abun jiki ba, ganin Ajiddeh batada niyyan tashi ta k’araso bakin gadon ta zauna tareda yaye duvet d’in tace “Au inata magana kin barni ina zuba bazaki tashi ba, Aliyun naki nefa yazo gidan nan har yaga Daddynku kamin ya fita, yanzu haka yana guest parlour side d’innan shine ana ki tashi ki shirya kina kwance ke sarkin son jiki ko?, toh kwanta nan ki jawa kanki salalan tsiya”, wani iri Ajiddeh ke jiyo magnar da Autyn nata keyi, yaushe ne Aliyu zaizo gidan nan, saidai in a mafarkanta da ta saba ko kuma in yazo kawo mata takardar sakinta, zumbur ta mik’e kamar wacce aka tsikara tunanin saki da tayi, hawayen taf idonta take kallon Aunty tana girgiza kai tace “Aunty Kulthum wlhy na yadda inyi ta zama da aurenshi koda bazai sake waiwayata ba amma kar ya sakeni, nashiga halin da ban tab’a shiga ba duk tsawon rayuwata, Allah ne ya jarabceni da son Aliyu, da inada yadda zanyi da tuni na cire na huta, son shine ya sani butulcewa Allah har ya kaini ga cutar wani, wlhy zan zauna da aurenshi koda bazai sake kallona ba a nan duniyan amma inason kasancewa matarsa a rayuwar da zamuyi nan gaba, yana bani takardata Dad zai aurar dani ga duk wanda yaga dama ina gama idda kamar yanda yayiwa Yaa Zee, nasan nima cemin zai yi in nemi wani uban idan har yayi min wani auren na kuskura na kashe, kuma na tabbata auren wani ne zai zame mini ajali, Dan Allaah Aunty kije ki bashi hak’uri ya koma da takardarsa, alfarmar da kad’ai zaimin kenan duk da nasan ban cancanci ayi min alfarma ba, ya barni da rad’ad’in da nake kwana in tashi dashi, kinji Aunty”, sosai Aunty Kulthum ta tausaya mata ganin yanda ta gama rud’ewa har wani rawa jikinta keyi ta rungumota tace “Hauwa bana tunanin takardarki yazo kawo miki, ga dukkan alamu salama(Peace) yake nema ba akasin shi ba kuma inma hakance ta faru haka Allah ya qaddara miki, haka Allah yayi ke ba matarsa bace, hak’ura zakiyi ki rungumi kaddara, ki sa a ranki Dan Allah kika tuba badan ki samu kyakyawan sakayya ta hanyar samun Aliyu ba”, girgiza kai takeyi tana hawaye jin maganganun Aunty Kulthum ta d’ago daga jikinta tace “Aunty so kike ki kwantar min da hankali ko?, so kike kawai inji dad’i, ni nasan wasa kike min”, hannayenta duka biyun Aunty Kulthum ta riqo cikin nata tace “Hauwa tun ranar da na fara ganinki Allah ya samin sonki dukda bansan wacece ke d’inba amma na karanci damuwa k’arara a fuskarki, ban d’aukeki a matsayin y’ar miji saidai kallon k’anwa da nakeyi miki kullum, kullum fatana shine inyi abinda zai faranta ran Daddyn ku kamar yadda nima ya faranta min, ya cika min burina da nayi niyyan na mik’a azzaluman da suka cucemu nida y’ay’ana ga hukuma, ya sani cikin farin ciki har nake ganin nafi kowa sa’a, bazan so ganin jininshi cikin k’unci ba, Allah ma muna mishi laifi yana yafe mana, kisa Allah a ranki ki tashi ki shirya kije ki samesu, daga gani yaron d’an babban gidane yanada dattako da mutunci, kiyi fatan Allah ya zab’a miki duk abinda yafi alheri, ke dai ki tuna duk abinda zakiyi da Allah na nan, kinji?” jiki a sanyaye Ajiddeh ke jin duk wani abu da Aunty Kulthum ke fad’a mata, maza Aunty Kulthum ta sata ta shirya cikin lace mai kyau, ta sata ta gyara fuskarta tayi kyan gani, wardrobe d’inta ta bud’e ta ciro mata hijab d’aya cikin hijaban da ta d’inka mata, kallon Aunty Kulthum kawai takeyi har ta gama zira Hijabin, Aunty Kulthum tayi murmushi tace “Masha Allah, kinyi kyau abinki kamar amarya”, d’ago ido ajiddeh tayi tana kallonta, Aunty Kulthum taci gaba “Ahap na manta, ashe amarya kike yau tunda za a wajen ango”, sunkuyar da kai tayi dan jin kunyar maganar, turaruka ta feshe ta dashi snn tace mata ta k’arasa wajensu, in banda bugu babu abinda k’irjin Ajiddeh keyi, duk wata addu’a da ta kama ma sub’uce mata yakeyi, ta dad’e tsaye wajen kamin tayi shahada ta d’age labulen kanta a k’asa, Abutturab dake zaune duk yacika sbd yana son gano halin da Batuul da Babynshi ke ciki duk ya gaji da jira ya mik’e zai fita kenan ta sako kai, dafarko bai gane ko wacece ma saida yaji Massa yace “Madugu Uban tafiya ai sai ka dawo tunda gata nan gimbiyar taka da kasa hak’urin ta k’araso zaka bita nan ta shigo”, dukda gabanta na fad’uwa maganganun Massa sun sa taji dad’i har ta samu k’warin gwiwa sake d’aga k’afa ta k’araso cikin d’akin, jin maganar Massa yasashu juyowa yana k’arewa halittan dake tsaye gabanshi kallo, ya rasa gane me ke bashi mamaki, hijabin da ya gani har k’asa jikin Ajiddeh ko kuma yanda ta koma, Idanunta a k’asa ta kasa d’agowa ta dubesu kuma ta kasa tsayuwa, shi d’inma kallonta yakeyi har saida yaji Muryan Massa yace “ina laifin kace ta zauna sai kaji dad’in kallon nata, amma ka barta tsaye duk k’afarta tayi tsami?”, duk da tasan Massa nada barkwanci amma na yau Sam bata jinshi, wani irin relief kawai taji ganin ba kawo mata takardarta sukazo yi ba , wani kallo Abutturab ya jefawa Massa kamin ya samu waje ya zauna, ganin bashida niyyan cewa Ajiddeh ta zauna yasa yace “Uwar gida shine aka guje mu bamusan laifin da mukayi ba,  toh nidai bari in baku waje dan wannan kallon da angon naki kemin zai iya sa hannu ya makeni, kema in na fitan sai kiji dad’in zaman tunda kin qi ki zaunan”, ya fad’a yana mik’ewa tareda exiting d’akin, cikin masculine husky voice d’inshi da take muradin ji ko da yaushe taji yace “tsayuwar ke miki dad’i ne da baza ki zauna ba?”, jiki a sanyaye hawaye taf idonta ta samu waje ta zauna a gefen kujeran daga k’asa, kallonta kawai yake kamar ba ita bace Ajiddeh da ya sani, sarkin gayu da kwalliya, fuskarta da kullum cike yake da rigima yau duk babu hakan, saima wata nutsuwa da sanyin dake shimfid’e kan fuskar, har wani dogon hijab ta zira abunda bai tab’a ganinta dashi, ko guntune bare yau har k’asa, ko a da in ya matsa mata da tayi Sallah wata riga take zirawa tayi Sallarta da ita sab’anin yau da ta sanya hijab, cikeda nutsuwa yayi maganarsa yace “kinyi laifi amma shine baki iya bada hak’uri ba ko?”, hawayen da ya taru mata ne ya shiga silalowa ta d’ago y’an fici ficin idanunta da suka rine ta kallleshi, sai yanzu ta kalleshi for the first time tun d’azu, har wani d’an haske ya k’ara da kyau, janye idonta tayi daga kanshi tana jin nauyinshi da kunyan abinda ta aikata, cikin siriyar muryarta dake cike da kuka tace “I know I was never a good wife, I wasn’t a good daughter Inlaw, duk abinda nayi doesn’t deserve a second chance, komai nayi nayishi ne sabida son da nake maka, na manta da Allah na nan, na manta shike biyawa bayinshi bukatunsu na alheri, na manta sai da yardarshi abu zai faru, sai da izinin zaka sami abu, na manta da ba komai mutum ke so zai samu ya zame mishi alheri ba, wani hanin ga Allah baiwa ne, son da nake maka yasa na butulcewa ubangijina duk da ya bani komai na rayuwa, nasan I don’t deserve your love, Aliyu nasan zuciyarka tsarkakkiyace, fushinka da alhakinka ya kamani, badan halina ba kayi hak’uri ka yafemin, av learnt a lot, na koyi darussa da dama da a ada nake ganin bazan iya yinsu ba, zanje in har gida ince Fatima ta yafemin, Ammah ma zanje ince musu su yafe min, I promise you am not repeating such a mistake, In sha Allah baza ka sake facing problem dan ni ba, everything happens for a reason, kuskurena happened for me to change to a better person, av changed for the good, forgive me plss”, ta k’arashe maganan cikin matsanancin kuka da nuna tayi nadamar abinda ta aikatan gaba d’aya abinma mamaki yake bashi, wai Ajiddeh ce ke magana haka a nutse, gaba d’aya jikinshi sanyi yayi, da yaso yi mata fad’a sosai ya nuna mata kurenta kan abinda ta aikata amma gaba d’aya sai yaji tausayinta ya cikashi, a hankali yaji yace “Hauwa”, gaba d’aya jikinta saida ya amsa k’iran da Abutturab d’in yayi mata, kamar yaune ta fara jin sunanta daga bakinshi, a hankali ta d’ago rinannun idanunta jin ya sake ambaton sunanta ta sauk’e kanshi, hannunshi d’aya ya mik’a mata alamun tazo ta zauna daga gefenshi, in banda bugawa babu abinda zuciyanta keyi, batayi musu ba ta tashi ta isa kujeran dake gefenshi ta zauna a d’arare, hannunshi d’aya yasa ya kamo d’ayan hannun nata, rawa kawai hannun keyi har saida ya sake sa d’ayan hannun nashi ya rik’e mata hannun duka biyu, a hankali kukan nata ya fara sassautawa, saida yaga rawan jikin nata ya dena tukunna ya d’ago hab’arta da hannunshi d’aya yana k’arewa fuskarta kallo yace “I need not say a lot Hauwa, idona ya gama ganemin komai akanki yanzu, I can clearly see the better changes in you, ina fad’amiki hakan ne bawai dan inason kisan how worthy and valuable Fatima is to me ba, nasan tun kamin wannan lokacin kinsan ya take a wajena, am telling you this dan ke kisan worth d’inta, am here because of her, tamin kuka, tamin magiya duk dan in maidaki tun bata san mey kika aikata ba har bayan ta sani hakan bai hanata yimin magiyar in yafe miki ba”, hawayen da take ta k’ok’arin maidawa kar su zubo suka shiga zarya, kuka takeyi na nadaman abinda tayiwa Batuul d’in, ta cutar da ita amma ita da alheri take binta, yaci gaba “babu amfanin maida abinda ya wuce, Marrying her was never her choice, I married her tun bataso but sbd iyayenta, she obeyed them, she sacrificed her happiness for them to be happy and satisfied with her, it was never her fault, keh kinsan I had no intention of keeping a second wife, but yaya zanyi, you caused everything, you made me fall into it, bani kad’ai ba, har parents d’ina saida ya shafa, I can’t say no to them, I had to do it a lokacin da suke so inyi d’in, everything happened so fast, I know you will be furious in har kika ji zancen, dukda ban san ya zanyi ba a lokacin nasan babu yadda za ayi in rabu da Batuul, badan ma su Ammah ba sai dan she had been a part of me tun kamin in san da zancen ita zan aura, I wanted telling you a lokacin, I couldn’t get how, ban taba sawa a kaina ta haka zaki san matsayin Batuul ba a wajena, am sorry for everything”, kukanta ta tsananta tana nadamar duk wani mugun abu da tayi tun kamin zuwaan Batuul gidan har lokacin da tasan matsayinta, murya cikeda kuka tace “Ni zance kuyi hak’uri, wacece ni da zan hana abinda Alllah ya hallata, na d’auka komai nakeso zan samu at my own disposal, nayi watsi da rahamar da Allah yayi min naqi bin umarninsa ai dole inga ba daidai ba”, sam ya kasa yarda da Ajiddeh ce gabanshi yau take maganan masu hankali, ajiyar zuciya ta Sauk’e tace “How is she?”, girarshi d’aya ya d’age alamar tambayn wa kenan?, a hankali ta furta “Batuul”, wani wide smile ta gani shimfid’e kan fuskarshi jin ta ambaci sunan Batuul, tun d’azu yake son yaje ya sake ganinsu itada Babynshi, itama murmushin tayi ganin yanda murmushin yayi mishi kyau yace “She gave birth today, yanzu hakaR tana asibiti, I came to fulfill her promise”, ido Ajiddeh ta wara tana dad’a widening smile d’inta tace “Aliyu dagaske?, yaushe ta haihu?, Ya Allah mey ta samu?, plss muje in ganta kaji?, plsss” murmushi yayi yana mik’ewa yace “d’azu, su nake son zuwa in duba, we will talk ltr”, kamin tayi magana har yayi gaba kamar wanda ake turawa, har yaje bakin k’ofa ya tuna da Mum, juyowa yayi suka kusa cin karo yayi maza ya rik’ota, ko bata fad’a ba response d’in da jikinta keyi ya isar ya nuna mishi tayi missing d’inshi, murmushi yayi a hankali yayi leaning yayi kissing d’inta, saida ya saketa yana maida numfashi yace “Zaki sani yin abin kunya gidan surukai ko”, murmushi tayi tareda lumshe ido tana godewa Allah da ya dawo mata da Aliyu tace “kaima ai gidankune”, yace “Mum fa?”, take murmushin dake fuskanta ya b’ace, a sanyaye tace “Its been seven months tunda Mum ta kwanta ciwo, ka tuna lokacin da nake ta k’iranka baka picking, I tot I dd lose her, inaso ko sau d’aya ka ganta ka yafe mata itama kai da su Fatima but duk inda nabi bana samun nasara”, hannun ta dake hannunshi ya damqe yace “Tana gidane har yanzu?”, ta kad’a kai tace “Yeah tana side d’inta”, ya jawota gabanshi yace “Muje in dubata before I go”, ba musu ta bishi a baya har side d’in Mum, saida ta fara shiga kamin ta fito tace ya shiga shima, Mum zaune cikin wheelchair duk ta rame kamar ba ita ba, tana ganin Abutturab hawaye ya fara zaryo mata, akan cutar da wannan bawan Allah taga ishara, gata nan zaune babu abinda zata iya yiwa kanta saidai ayi mata dashi, tana ji tana gani, har k’asa ya tsuguna ya gaida ta cikeda girmamawa, sosai ta nemi da su yafe mata su dukkansu tace kuma har gida zatazo ta samu su Batuul su yafe mata, Abutturab kam kasa cewa komai yayi, wai wannan itace Mum da last time da ya ganta tana ta bambamin anyi y’arta sharri baza ta yadda ba yau itace zaune haka bata iyawa kanta komai, dama in baka godewa Rahamar Allah ba ai ka godewa azabarsa, tun da lafiyarka baka more shi ba gashi yanzu kana nema ma babu hali, mik’ewa yayi bayan sun gaisa ya fad’awa Mum abinda ya kawoshi snn yayi sallama da ita akan anytime suka gama shirya Ajiddeh sai ayi mishi magana, murna fal ran Mum ta dinga mishi godiya, har mota Ajiddeh ta rakashi kamar kar ya tafi ta dinga ji, so yake kawai ya ganshi kusa da Batuul, a mota ya tarar da Massa yana jiranshi, sallama sukayi suka wuce, a hanya Massa ke fad’a mishi Ammah ta kirashi akan anyi discharging Batuul, da sauri ya ciro wayarsa cikin aljihu, missed calls ya gani nasu Ammah da sauran mutane kasancewar wayan na silent, number Batuul kawai yayi dialling dukda baiga missed call d’inta ba, bugu biyu ta d’aga, cikin siririyar muryarta tace “Hello”, ajiyar zuciya ya sauk’e yace “Glitterrr”, jin yanda yaja sunan nata tasan something is wrong, kamin tace wani abu yace “Glitter sun tafi min da ku ko?”, murmusshi tayi kaman yana gabanta a hnakali tace “All thanks to Aunty, tace da nan da can d’in duk d’aya ne, duk care d’in da zata bani Ammah will give me better, taqi a tafi dani gidanta, I know you will be happy shiyasa banyi insisting ba”, wani irin dogon ajiyan zuciya ya sauk’e yana fad’in “Alhamdulillah, Glitter! Allah ya k’arawa Aunty tsawon rai, lafiya da Imani, Aunty is the best kin sani ko”, sosai Addu’ar tayi mata dad’i tace “Amin Yaa Abu”, yace “Twinkle fa?, bacci take ko?”, d’an yatsina fuska tayi dan bata gane wa yake nufi ba tace “Waye kenan?”, yace “Glitter mana, bayan ke akwai wanda zan tambaya at this right moment bayan Babyna?”, kai ta kad’a tana dariya tace “Ohhh sunan da ka saka mata kenan?”, yace “Yeah, she twinkles kamar yadda kike glitter, she so cute, dama na fad’a miki I want a baby just like you, God has answered my prayers, Thank you kinji, Allah yayi miki albarka”, dariya tayi tace “Amin Amore, Kaji Ammah na cewa in huta”, yace yanzu zan k’araso ne ai, babu mai hanani ganinki, you rest well kinji, take care of yourself and twinkle for me”, ido lumshe  ta amsa da “sure I will do that”, ajiyar zuciya ya sauk’e tareda sauk’e wayan ya juya yana kallon Massa da gaba d’aya hankalinshi ke kan driving, hira suka shiga yi har suka isa gida dab da magrib, saida suka fara yin sallah masallacin dake jikin gidan kamin su shiga gida, har mamakin matan dake gidan yayi kamar yau ake taron sunan,  kukkutsawa ya riqayi suna gaisawa har ya samu ya shiga d’akin da ya San Batuul na ciki, wani irin serene and peaceful k’anshi d’akin yake, ga wani d’umi da d’akin yake, manyan burners d’in turaren wuta na k’asa a angle d’in d’akin har biyu, Batuul na kwance kan gadon itada jaririyarta, jingina yayi tareda k’ofan yana kallonsu tareda ajiyar zuciya, duk wani numfashi da zaiyi yana jin so da  k’aunar halittun nan na Allah guda biyu da suka zama part of rayuwarshi cikin lokaci kad’an, a hankali ya tako ya k’araso bakin gadon tareda zama yana kallonsu, jin mutum kan gadon ya sata bud’e lumsassun idanunta ta sauk’e kanshi tareda mishi murmurs hi, murmushin shima yayi mata yana matsawa kusa da ita, tashi tayi tazauna tace “sannu da zuwa”, baisan mey zai mata ya nuna mata farin cikinshi ba, hannu yasa ya zagayeta tareda rungumota jikinshi, murmushi tayi tareda yin lamo jikinshi tana jin dad’in d’umin dake jikinshi, kamar wacce ta tuna da wani abu tayi maza ta tashi daga jikinshi tana kallonshi, kallonta shima yakeyi dan wannan kallon nata bayason irinshi, langab’ar da kai yayi tareda d’age girarshi d’aya yana jiran jin mey zatace, a hankali har idonta ya fara kawo ruwa tace “your scent?, ban sanshi ba”, gaba d’aya ya manta da ya rungume Ajiddeh, k’anshin turarenta ne dake jikinta ya kama mishi kaya shine Batuul taji yanzu, marairaicewa yayi kamar shima zaiyi hawayen shima yace “Fatima I went to her, ba kince in dawo da ita ba?”, wani irin fad’uwa gabanta yayi, wlhy ta manta da tayi mishi zancen ya dawo da Ajiddeh, hannunta dake zagaye jikinshi ta k’arasa warwarewa, hannayen yayi maza ya rik’o yana girgiza mata kai yace “No Fatima, kefa kikace in dawo da ita, I gave you my word and I honoured it, for you, for your happiness”, a hankali ta sauk’ar da idonta hawaye na gangarowa tace “I didn’t say anything”, ta fad’a tana kawar da kanta, hannu yasa ya tallabo fuskarta yace “Look at me kinji, plsss”, a hankali ta dubeshi yace “ya kikeso inyi Fatima?, I want you happy, mey kikeso inyi to keep you happy?”, jiki a sanyaye tace “just love me, always”, ta fad’a tana lafewa jikinshi, hugging d’inta yayi yana kissing goshinta yace “In sha Allah Fatima, to the best of my ability kinji?”, kai ta gyad’a mishi kawai, saida aka k’ira isha kamin ya fita bayan yayita kwantar mata da hankali lokacin Farida da Aunty Amna sun shigo d’akin, Ranan Suna da asuba a masallalci bayan an idar da Sallah aka rad’awa Baby suna A’eesha(Fareeda), Sadiq ne ya fara k’iran Fareeda ya fad’a mata sunanta aka sawa Babyn, ihu ta saka, ta rasa ina zata saka kanta dan murna, duk wani angle d’in gidan saida tabi tana fad’awa kowa sunanta aka maidawa Baby, kasa hak’ura tayi su dawo daga Masallaci ta tafi bakin gate  tana jiran dawowansu, yana shigowa yaji an rungumeshi, kuka ta fashe da jinta jikin Abu, ta dad’e da sanin son da yake mata amma bata san har ya kai haka ba, da murmushi a fuskanshi ya d’agota yana kallon yanda hawaye ke zarya, ya had’e rai yace “zakisa twinkle ma ta zama cry baby ko, to zan fasa”, dariya tasa tana girgiza kai tace “Na daina, kaga ko, nayi shiru”, ta fad’a tana share hawayenta, dariya shima yayi yana shafa kanta yace “that’s my lil sis”, dariya tayi ta sake komawa jikinshi tace “Yaa Abu I love you for being the best brother ever”, “I love you too”, ya kama hannunta suka shiga ciki, a d’aki Batuul ta fito wanka kenan Ammah ke fad’a mata sunan Fareeda aka maidawa Babyn, sosai itama taji dad’i, a nan take bawa Batuul lbrn Abu ne ya sawa Farida inkiyarta ta Farida lokacin da aka haifeta sbd son da yake mata, yaso Farida ya zama shine ainahin sunanta amma lokacin Abui ya mata hud’uba da A’eesha, shine sai Faridan ne ya bita, yanzu haka ba kowane yasan asalin sunan Faridan ba, Addu’a tayi musu Allah ya k’ara musu zumuncinsu, Farida ce ta shigo riqe da wani k’aramin chest box, Batuul ta mik’awa box d’in tace “You know I love you ko?”, dariya Batuul tayi tana saka kayanta tace “sai yau kike jin tunamin da son da kike min?”, Farida ta mik’a mata akwatin tace “This is for Lil Farida”, karb’a tayi taga golds ne ciki, mirmushi kawai tayi ta ajiyeshi gefe dan batasan mey zatce mata ba, tare suka gama shirinsu, sosai akayi shagalin suna, Batuul da Baby suka samu kyaututtuka sosai, sai ranan Ammah ke jin Komarwa Ajiddeh ganinta tazo sunan itama da kyaututukanta, Ammah sam ba haka taso ba, amma jin Batuul  ce tayi insisting dawon nata ta hak’ura, dama dan ita take k’in komawan Ajiddeh, bayan wata hud’u suka tarkata suka koma UK har Ajiddeh +
*FOUR YEARS LEAP*
Daaaddddyyyyy, she let you take them?”, yarinya k’arama y’ar shekara hud’u da ke zaune kan comfy bed ta baza colouring books d’inta kan bed d’in ta fad’a tareda mik’ewa tana wara ido, da ganinta kasan cike take da murna, dariya yayi ya zauna kan gadon shima yana zube mata chocolate packs da bottle of nutella d’in dake hannunshi, with excitement ta yarda crayon d’in dake hannuta ta hawo kan jikinshi ta zagaye duka hannayenta biyu wuyanshi biyu tace “Dad how did you get em?”, ta fad’a tana kai hannu zata karb’i packet d’Raffaello packet d’aya, bud’ewa yayi ya mik’a mata, saida tayi pecking duka cheeks d’inshi biyu kamin ta jefa size bite d’in bakinta tana lumshe ido, kamin ta gama shanyewa ya bud’e mata nutella jar d’in tareda soka mata craft stick ciki, ido ta sake warawa tana lashe bakinta ta karb’i jar d’in daga hannunshi tace “Daaaaddddyyy”, kallonta kawai yakeyi yana murmushi ya amsa da “Yesss Twwiinnkkllee”, tayi dippping stick d’in ciki takai bakinta, saida ta lashe tace “Daddy life is always better with nutella jar”, kai ya kad’a mata yana dariya dan yasanta da son zak’i yace “Really?”, kai ta kad’a mishi tace “Yessss, and do you know what makes life the best?”, kai ya kad’a mata alamar a’a tace “having the best Dadddyy like mine, you make life the best Daddyy”, ta fad’a tana kawo mishi craft stick d’in bakinshi tareda d’age mishi girarta d’aya kamar yanda yakeyi shima, ido ya lumshe yana jin k’aunar yarinyar har numfashinshi, ko kad’an bai damu da har yanzu bata samu kannai ba dan son da yake mata na sashi ya manta da wasu damuwanshi, baki ya bud’e ya lashe nutellar, daidai nan Batuul ta shigo rik’e da glass cup cikeda fresh milk, kallonsu kawai ta tsaya yi da mamaki da kuma chocolates d’in da suka baza kan gadon, ita sam bata ma san da yana d’akin ba, sake shigewa jikinshi twinkle tayi ta kanainayeshi tana sadda kai k’asa, zama tayi bakin gadon bayan ta k’araso cikin d’akin batareda ta kallesu ba ta ajiye cup d’in kan drawer tace “zimme gone yay”(“sauk’o ki d’auka ki sha”), a hankali ta janye jikinta daga na Abu, da ganinta kasan batada gaskiya, har ta mik’a hannu zata d’auki cup d’in ta fasa ta d’ago idanunta masu haske ta sauk’esu kan Batuul da ta zauna babu wasa fuskanta, kamar zatayi kuka har idonta ya cicciko tace “Mommah am sorry pls, imma not gonna take chocolates again”, batareda Batuul ta kalleta ba tace “nyiro gone yay na woko”,(“Nace ki d’auka ki shanye ko?”), jiki a sanyaye ta mik’a hannu ta d’au cup d’in tareda kaiwa bakinta tana yatsina fuska ta fara shan madaran da aka tafasa da spices(cinnamon da cardamom), kurb’a ta dinga yi kamar baza ta shanye ba, saida ta shanye fiyeda rabi snn ta kalli Abu dake zaune yana kallonta ta langab’ar mishi da kai tanason ya taimakata ta bar shan madaran nan haka, tsaresu da Batuul tayi da ido yasa shi shima langab’ar mata da kai tareda lumshe mata ido, alamun tayi hak’uri kawai ta shanye tunda Batuul ta kasa ta tsare, maida cup d’in tayi bakinta ta shanye sauran da ya rage hawaye na sauk’o mata, Sai da ta gama shanyewa tass snn ta karb’i tumbler daga hannunta ta mik’e zata fita daga d’akin batareda tace musu komai ba, raurau twinkle tayi da ido tana kallon Daddynta dake zaune, hannu yasa ya rik’o Batuul, bata juyo ba snn bata ci gaba da tafiyan ba, cikin sanyi taji muryar twinkle na cewa “Mommah kanadi tay plsss, I promise not to take chocolates again, don’t be angry plss Mommah, Daddy tell her I promise not to”, “( Mommah kiyi hak’uri, nayi alk’awarin bazan sake shan chocolates ba, kar kiyi fushi dani kinji Mommah, Daddy ka fad’a mata nace bazan sake ba plsss”, muryan Abu taji shima ya kwaikwayi yadda twinkle d’in ke magana yace “Mommah kanadi tay, gadero diyen ba plssss”, (“Mommah kiyi hak’uri baza mu sakeyi ba”), juyowa tayi tareda dubansu d’aya bayan d’aya har suna jin dad’in ta huce fushin da takeyi duk faces d’insu yayi lighting da smiles, “Dinner is ready”, ta fad’a tareda juyawa ta bar musu d’akin, raurau twinkle tayi da ido tana kallon Daddyn nata, ido ya lumshe tareda mik’a mata hannunshi, pan d’in grilled salmon d’in dake hannunta ta ajiye kan dinning table d’in, ta juya zata koma kitchen d’in ta hangosu suna sauk’owa kan stairs, shigewa tayi ta fito riqe da bowl d’in ta ajiye kan dinning d’in shima, har sun zauna a lokacin, kujera taja ta zauna, saida ta fara serving Twinkle kamin tayi serving Abutturab da kanta, A nutse suka fara cin abincinsu bayan sunyi addu’a, Kallon plate d’in kawai twinkle keyi riqe da fork a hannunta, kallon Abutturab Batuul tayi snn ta sake kallon Twinkle da ta k’urawa Plate d’in abimcin nata ido kamar mai son ganin wani abu jikin marinated olives d’in dake cikin abincin, da ganinta kasan abu na damunta, kujerarta ta matsar kusa da ta twinkle tana k’arb’an fork d’in dake hannunta ta gutsoro salmon fillet d’in tareda kaiwa bakin twinkle d’in, “Mommah jirero waltike dikkin ba fan3ma?, wande g3ran3mi, plsss”, (“Mommah nayi alk’awarin bazan sakeyi ba dagaske kinj?, kar kiyi fishi plsss”), tayi maganar hawaye na gangarowa fuskarta, har cikin ranta takejin rashin dad’in ganin hawayen twinkle, da saauri ta d’auketa ta d’aura ta cinyarta tareda rungumeta tana rocking d’insu tace “Its okay baby, g3rang3i dei Twinkle, wande yir3mi, baby nyiro g3ranyin ba, bei b3rim”, (“its okay baby, banyi fushi ba Twinkle, karkiyi kuka baby, bazan iya fushi da baby na ba, kici abincinki”), ta fad’a tana kai mata fork d’in bakinta, wani irin murmushi ne yayi escaping lips d’in Twinkle jin Mommah d’inta bata fishi da ita, a hankali ta bud’e bakinta ta saka mata abincin ciki, tana taunawa tana share hawayen dake kan fuskarta, saida ta gama taunawa snn ta kalli Daddynta dake kallonsu tace “Dadddy g3raz3i wono, am happy”, (“Dadddy tace batayi fishi dani ba, naji dad’i”), murmushi yayi mata tareda mik’o mata hannunshi yana cewa “High five”, tana dariya ta mik’a mishi suka tafa, suna tafawa tace “Goals yeah?”, kai ya kad’a mata yana mata Thumb up, daga haka ta maida hankalinta kan abincin da Batuul ke bata, tab’are fuska Abu yayi yace “Wannan son kan naku dayawa, you guys are eating and no one is concerned about Daddy?, am hurt Twinkle, I will also go to my Ammah to feed me”, ya fad’a yana langab’ar da Kai, dariya Twinkle tasa tace “Daddy you look an old smurf”, dariya yayi yace mata “Tell your Mommah I want to b fed by her”, kallon Batuul da tayi kamar bataji abinda yake cewa ba tayi tace “Mommah my Daddy wants you to feed him too”, hararar wasa tayi mata tace “Sannunki mai Daddy”, kujerarshi ya matso dab da ta Batuul yace “Glitter yanzu kin dena caring about me ko, kullum komai sai Twinkle, babu komai nima zan nemo wacce zata rik’a caring about me nima”, ido Batuul ta zaro tace “Amor rigima dai kace kake jin yi, ko breakfast we had it together, we fed each other fa, yanzun ma its because ina feeding Twinkle ne, bara in gama da ita sai in baka, kasan I can’t take it ka samo wata mai kula min da Kai, nida  ita ma mun isa haka, plss kaji?”, tafad’a tana langab’ar mishi da kai tareda zumb’uro d’an bakinta, kamar jira takeyi ya matso da kujerarsa kusa da nata tareda sunkuyowa yayi brushing lips d’inshi kan nata, ido ta wara tana janyewa tareda yi mishi alama da Twinkle fa na nan zaune, murmushi yayi yace “nima d’in bazan iya kallon wata ba bare har ta kular miki dani, Inajin dad’ine in kikayi feeding d’ina, and then those lips, kinsan bana iya resisting d’insu ko, I love everything about it, ke kuma kullum sai ki rik’a pouting d’insu, they tempt me to”, ya k’arasa maganan yana kallonta yana son ta d’ago su had’a ido, murmushi kawai tayi tana ci gaba da bawa Twinkle abinci, saida ta tabbata ta k’oshi snn ta juyo ga Abu ta fara bashi dan taga bashi da niyyan ci, tare suka ciyar da junansu abinci cikeda kwanciyar hankali, Daidai suna gamawa aka k’ira sallah Isha, Twinkle da Abu tare suka tafi masallaci Batuul tayi a gida, tana idarwa ta shiga had’a musu kayansu da zasu yi tafiya gobe dashi, suma  bayan sun idar da Sallah sukaje gidan Ajiddeh, tayi kyau abunta duk ramar nan ta b’ace, cikeda Murna Twinkle ta hau jikinta, tunda sukazo take ta surutu, Ajiddeh ma ta dinga biyeta, bata sauk’a daga jikinta ba saida zasu tafi, saida ta rakosu bakin mota ta rad’awa Twinkle magana a kunne, a mota Abu ke tambayan Twinkle mey Ajiddeh ta fad’a mata, sam taqi fad’a mishi tace “Mummy said I should tell Mommah first”, haka ya hak’ura, Batuul kam tunda taga har an idar da sallah basu shigo gida ba tasan mayb ya kai Twinkle yawo ne dan sun saba hakan, suna komawa gida ta tafi da gudu jikin Batuul tana mik’a mata ledan dake hannunta da Ajiddeh ta bata, karb’a tayi ta duba mey ke ciki, tana gani tasan inda sukaje d’in dan duk lokacin da taje ire iren abubuwan da take batan kenan, da murna ta zauna kan cinyar Batuul ta zagaye duka hannayenta biyu jikinta ta sunkuyo dai dai kunnenta snn tace “Mommah, Mummy ye nyiro gulnge wa Disney world California wo sadin wono” (Mommah, Mummy tace in fad’a miki zaki zata kaini Disney world Carlifornia tunda muna summer ne yanzu”, Babanta ta nuna mata tace “Daddy ro gulle, shima deciding sidin”, (“ki fad’awa Daddy, shi zaiyi deciding”, ba musu ta sauk’o ta fad’a mishi yadda sukayi da Ajiddeh, ya jawo hannunta yana d’aura ta kan cinyarshi yace “Twinkle I don’t like America you know?”, jiki a sanyaye ta kad’a mishi Kai, yayi murmushi dan yasan tsoro taji zai hana zuwan, yayi murmushi yana kamo cheeks d’inta duka biyu yaje “But we will be going to Paris”, ihu ta saka tana rungumeshi tace “I will see small Mommah there”, yace ” Yeah But after coming back from Nigeria, then we  go to Paris”, pecking duka kumatun nashi tayi tace “I love you Daddy”, shima pecking d’inta yayi yana cewa “I love you more Twinkle”, “Daddy can I tell Mummy we will b going to Paris not California?”, yace “You will tell her tomorrow, its late now, okay?”, kai ta kad’a mishi tana k’ok’arin sauk’a daga jikinshi, Batuul dai na zaune tana jinsu batace komai ba, saida suka gama hirarsu wajen 8:15 tacewa “Twinkle ta tashi taje tayi mata wanka ta kwanta dan gobe zasuyi tafiya, a nan toilet d’in d’akin tayi mata wanka ta nad’ota cikin towel, lokacin Abu shima ya tafi yin nashi wankan a d’akinshi, saida ta gama shiryata tsaf snn sukayi addu’an bacci a tare, daga gefenta ta kwanta tana karanto mata stories of the Sahabas daga wayarta, dan har sun gama na prophets, jin ta dena tambaye tambaye hakan ya tabbatar mata da tayi bacci, ta gyara mata kwanciya tareda pecking d’inta snn ta sake tofe duka d’akin da addu’a, k’asa ta sauk’o ta samu Inna Halima(Mai kula da Twinkle da Ammah ta samar musu) a kitchen tana y’an goge goge, sanar mata tayi da ta kwantar da Twinkle, ta bar aikin haka ya isa taje su kwanta, saida ta kashe komai ta tabbata everywhere is safe ta koma sama itama, d’akinta ta koma dan yin wanka, tana k’ok’arin cire kaya ta mirror ta hango mutum kwance kan gadonta, k’ara ta saki zatayi waje yayi maza ya kamota, sam bata lura dashi ba lokacin da ta shigo, rungumeta yayi yana mata magana k’asa k’asa a kunne, yasanta da saurin tsorata amma bai tsamman yanzu ma zataji tsoro ba tunda d’akin duk haske ne, a kunne ya rad’a mata “Shhhhh Glitter, sorry kinji?, banso na tsorataki ba”, har lokacin jikinta na b’ari, bata d’ago daga jikjnshi ba tace “I tot kana d’akinka fa”, ya kamata suka zauna kan gado yace “its been long nayi wanka da kaina, keh nake jira kizo muyi tare”, lafewa ta sake yi jikinshi tana turo baki  tace “shine ka tsoratani ko?”, murmushi yayi yace “Sorry Fatima, ki rage tsoron nan kinji banaso babu kyau, beside ba ke kad’ai bace, Lil champ d’ina is there, kar tsoronki yayi affecting d’inshi”, ya fad’a yana k’ok’arin rage mata kayan dake jikinta, tace “Amorrr, watanshi fa d’aya duka duka amma shine har an fara zumud’inshi, haka akayi tamin a cikin Lil Farida ma”, ya shafa cikin nata yace “I wish duk wata zaki bani sabon Baby ba, da nafi kowa murna, inason yara Fatima, kamar 12 or more, inason in ganshi kamar wani mini nursery, duk motsi inji yara kusa dani, i know i can’t pay you but bakina bazai gaji da yi miki addu’a ba, Allah yayi miki albarka”, tausayi ya bata, tasan yana da son yara, gashi ita kuma Allah bai sake bata wani cikin ba sai bayan shekara hud’u, Ajiddeh kuma har yau shiru ko b’arin wata batayi ba, har yau suna zaryan zuwa asibiti, rungume shi tayi tace “Amorrr, In sha Allah the best will happen kaji, Alkahairi da Albarka muke nema ba yawansu ba, in mukayi addu’a komai daidai zai tafiyar mana”, muemushi yayi yana sake matseta a jikinshi, tare sukayi wanka sukayi shirin kwanciya bayan sunyi addu’o’insu, Washegari suka tashi da shirin tafiya Nigeria su dukkansu, suna isa Abuja suka sake boarding wani plane d’in to Maiduguri, banda Ajiddeh dan tace ita su barta a gidansu, in yan gidan nasu sun tashi zuwa zata biyosu su taho Maidugurin tare, da farko yaqi amma sbd magiyar da ta riqa mishi ya hak’ura, a gidanshi na can dake Old GRA suka sauk’a, daga gidan Ammah da gidan Aunty aka turo musu abinci dan su sunyi kwana biyu da zuwa,  suna idar da Sallah Magrib suka shirya suka tafi gidan Aunty sbd zumud’in da Batuul keyi na son ganin yan gidansu, a parlour suka tarar da kowa, duk sun k’ara girma baki d’ayansu, da gudu Twinkle ta haye jikin Baba dake parlour dan tanason tsohon sosai, lokaci lokaci take sawa Abu ko Batuul su k’ira mata shi suyita waya, sama ya d’agata yana cewa “Ashe amaryar tawa na hanya shiyasa nake ta jin k’anshi ko ta ina”, dariya tayi tana ajiye mishi jakan turaren da tayi ta rigiman ita zata d’auka tace “Handsome granny, this is for you”, dariyan sunan da ta k’irashi yayi yace “Na manta ashe Baturiya ce, How was your journey?” kamin tayi magana Aunty ta d’agata ta baya tana cewa “Abinda ya kawoki kenan dama, ki gama kalle Handsome granny ko, toh ina nan babu mai kallar min shi,  harta fara rigiman a sauk’ta ganin chocolate pack a hannunta yasa tayi shiru tana murmushi, Dariya suka sa su dukkan Aunty tace “Sarkin kwad’ayi, wato kinga chocolate shine kikayi shiru ko, ungo karb’i ya daifi ki sha ki barmin Handsome granny d’in”, Nan su Abu suka zauna sukayita hira, sosai Aunty da Baba sukayi murnan ganinsu da result d’in da Batuul ta nuna musu na kammala makaranta, ta gama degree d’inta da first class honour, tho su Ahmad da Sa’eed sunje graduation d’inta da yake a UK suke karatu suma amma ba gari d’aya ba , sai albarka suke saka musu, anan Batuul ta Bawa kowa tsarabar da sukayo musu , har d’an kwalla Batuul tayi ganinta cikin y’an uwanta after years, kasa hakuri tayi gobe tazo ta gansu saida tazo a yau, har d’an kwalla ta share tana tuna rayuwarsu ta baya, da a dane da yanzu itace gefen Baba , But life has to move on, yau itace da tata y’ar tana raino, a ranta ta dinga furta “Alhamdulillah”, k’arfe tara sukayi haramar tafiya gidan Ammah, Abu a Twinkle ne suka fara shigowa, turus ya tsaya ganin Farida zaune parlour da titsetsen ciki( shekararta d’aya da aure itada Affan d’inta) zaune ta tasa fruits gaba tana ci kanta ko d’an kwali babu, da gudu Twinkle ta je ta rungumeta tana fad’in “Small Mommah, Daddy didn’t tell me you are here”, rungumeta tayi tana jin dad’in ganinsu dan dama zuwansu take ta jira tun d’azu taqi tabi Aunty Sadiq kuma taqi baccu, da murnarta tace “Lil me, kin girma, Mommah na kula dake sosai”, tayi dariya tace “Mommah are you too getting me a new lil smurf, Daddy said Mommah too is getting me a new Lil smurf?”, ta fad’a tana tab’a cikin Faridan, muryan Abu ne ya katsesu yace “Yanzu shi  Usman(Affan) dinne ya barki kina yawo tsakanin Nigeria da Paris a condition d’innan naki, marairaicewa tayi tace “Yaa Abu I was missing you all shine da naji zakuzo ya had’ani dasu Aunty Amna muka taho a tare, kuma I will be coming for Yaa Sadiqs wedding, inaso ayi duk shirye shiryen tare dani shiyasa nazo tun yanzu, shima next week zaizo”, d’an tsaki yaja yace “Ai zanyi magana dashi inji inma ke kika matsa mishi da sai kin taho d’in”, ya fad’a yana k’arasa shiga ciki, cikin d’aga murya tace “Dagaske nifa ban matsa ba Yaa Abu, ko ka tambayeshi he will tell you same”, ko juyowa baiyi ba ya k’arasa ciki, A bakin kitchen ya had’u da Ammah tana fitowa, take murnarshi ta fad’ad’a ya rungumeta yace “Barka da gida Ammah”, Ammah tana dariya tace “Da girmanka kana shirin tarb’o second child d’inka baka bar rungumata ba”, ya marairaice fuska yace “Bazan tab’a canjawa daga Abutturab d’inki ba, kema you will always be my Ammah komai yawan yaran da zan haifa”, ya fad’a yana pecking goshinta, tayi murmushi tana shafa kanshi tace “Inasu Bittin?”, yace “suna parlour”, k’arasawa sukayi parlour suka tarar da su duk sun zazzauna sai hira sukeyi gwanin sha’awa, Abu ya dubi Ammah yace “Ammah dubi yarinyar nan at this her condition aka barta take yawo haka”, marairaice fuska Farida tayi tana duban Ammah with pleading eyes, Ammah tace “Toh ai ko ba yanzu ba zata dawo gida yin jego, shine dasu Amna zasu dawo Usman d’in yace ta biyosu”, harara ya sakarwa Farida  yace “Samun guri dai, dan zaka haihu sai kayi ta yawo”, daga haka ya mik’e yayi side d’in Abui, Farida kam ko d’agowa batayi ba tasan intayi magana sabon fad’ane kuma,  Batuul kam dariya ta dinga mata k’asa k’asa, ba a jima ba Sadiq ya shigo gidan shima, nan sukaci gaba da hirarrakinsu, Batuul kam sai tsokananshi takeyi ya kusa zama ango, Gashin nan da yake tarawa duk ya ragesu ya k’ara girma into a responsible mutum sosai amma duk da haka saida ya biyesu dan shima d’in gwanin tsokanan ne, Twinkle kam sam taqi zuwa wajen Ammah, tana b’oye jikin Farida duk maganar da take mata na tazo taqi, tana ganin an kawo kwab’ab’b’en jan lalle tayi maza ta mik’e daga jikin Farida tace “Will you do it for me Granny? I want to look beautiful”, Ammah ta dubi Abu dake shan fruit Salad tace “badai har yanzu turancin nan kake mata ba Abu, haba inata magana yarinya tak’i zuwa”, Batuul ce tayi maza tace “Tana fa jin Kanurin Ammah, haline dai da take dashi”, Ammah tayi maza tace “Hali irin na Babanta ba, shima haka yake ai da yana k’arami ayi ta mishi magana yana jin mutane yaqi kulasu, amma dai keh ba turan cin nan kikeyi mata ba ko, dan wannan ai asara ne yaro ya taso baijin  yarenshi”, Batuul tayi murmushi tace “Da kanuri nake mata magana”, Ammah tace “Kin ko kyauta, hakan yafi ai, Turanci da larabci ai ko a makaranta ka koyesu amma yarenka in bakayishi tun a gida ba babu kuma Inda zaka samu ka iyashi”, ta dubi Twinkle tace “ja’ira da da nake ta miki magana kina jina kika k’i kulani shine saida kika ga lalle ko kike cemin a miki, you want to look beautiful, toh ko me zakiyi baza ki fini kyau ba bare ki samu k’wace min miji, zo zauna ayi miki, tsohon mijin naki ya biyani”, duk wannan maganan da kanuri tayi mata shi, kallon Batuul tayi tana son tace mata taje d’in, kai ta gyad’a mata alama taje snn tace “wande nan fuun Nasaran(English)nduro mananimi, fanema naaa?”(Kada ki sake yiwa kowa magana da turanci nan gaba kinji?”), kai ta gyad’a mata tace “Yo Mommah”, ta nad’e mata hannun riganta da yake dogo son ta tafi kusa da Ammah ta zauna, saida aka fara mata a hannu kamin a fara yiwa Ammah, taso ayi mata na k’afa amma a al’adar kanuri yara ko y’an mata basa yin lallen k’afa sai dai matan aure, sam Batuul tak’i yadda da ayi mata shi, sai wajen sha d’aya sukayi musu sallama akan gobe zasu dawo suci gaba da ziyara har gidansu Shehuri, har parking lot suka rakosu, Twinkle kamar a barta ta kwana dan ta sake da Ammah kuma ta bata chocolates masu dad’i, ana fitowa Twinkle ta hango wata mota tace itakam Sam a ciki zasu tafi gida, babu yadda suka iya haka Sadiq ya koma ya d’auko musu key d’in motar, Batuul kam na ganin motar  saida gabanta ya fad’i, shekara biyar yanzu amma tana iya tuna komai about motar, Sadiq na kawo key d’in suka shiga, sai tsokanan Twinkle yakeyi da turanci, ta had’e rai tace “My Mommah said I should not speak Nasara again”, Sadiq ya kwashe da dariya yace “And you just did”, tayi maza ta riqe baki tace “Sorry Mommah”, Batuul kam shiru tayi tana ta tunane tunane zaune cikin motar, har suka d’au hanya bata ce komai ba sai Twinkle da Abu ke hiransu, Pidgin motar Twinkle ta bud’e tana saka hannu ciki, wani d’an kwali ta ciro a ninke cikin pidgin d’in sai k’anshi yakeyi, Abu tana nunawa tace “Daddy see what I found”, Hannu ya mik’o daga baya ya amshi d’ankwalin yana kallo da ido, ido Batuul ta wara ganin d’an kwalin, takan manta da kayanta koda bata rabu dasu ba, in har ba ganinshi tayi ba mancewa takeyi dasu, Ammah wannan tana ganinshi ta tuna komai da ya faru da ita a ranan da ta sakashi, ranan da ta fara had’uwa da Abutturab, ranan ta fara shiga motarsa, ranan komai na rayuwarta ya canja, a hankali taji bugun da zuciyarta keyi ya fara daidaita, hannun Abu masu d’umi taji cikin nata, ajiyar zuciya ta sauk’e tana   jin wani abu na ratsa duka sassan jikinta, ido ta lumshe ta bud’e snn ta kalleshi tace “You still remember?”, murmushi yayi yana kawo hannun nata daidai bakinshi yayi kissing snn yace “Ban tab’a mantawa ba Fatima, Ban tab’a mantawa da rana d’aya da nayi spending tare dake ba, they are my most treasured  moments and memories I always keep to reminisce, ranan da kika saka kayan nan ranan na fara had’uwa dake, ranan da sonki ya zama a part of my breathing,ranan na fara d’aukanki a motata, ranan nasan komai nawa ya canja, hankalina bai sake kwanciya ba saida na mallakeki a matsayin matata, son da nake miki is something da ban san ya akayi na fara shi ba kuma bansan ya zan gama shi ba, abu d’aya nasan ina fata yanzu, to be with you till my last breath Fatima, I can’t imagine life without you yanzu because inasonki dayawa, I love you a lot”, murmushi tayi idonta na cika da kwalla ta kwanto ta jikinshi tace “I love you more Yaa Abu, I will be with you In sha Allah”, “In sha Allah” shima yace yana sake kissing hannun nata, Twinkle dake wasa da iPad can baya bata san ma mey ake ciki ba, kamin su k’arasa gida har tayi bacci.
ALHAMDULILLAH, For every beginning there must be an end, Allah ya nuna mana  k’arshen *BATUUL*,

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *