YAR MAKIYAYA CHAPTER 9

YAR MAKIYAYA




CHAPTER 9



Wata sabuwa inji y’an cha cha , rashin sani yafi dare duhu ,shiyasa nace in every family akwai secret nasu amma shin Baban Junaidu zai rik’e wannan sirrin har abada? Wai ena zamu samo Suraj ne kam? Dan samo amsoshin tambayoyin nima JIDDAH nayi tattaki zuwa KADUNA garin gwamna 🚘

****** ******* ******

“Ya kasance sabon abu a garemu daga ni har Yaya Junaidu ganin manyan gine gine na alfarma, tabbas duniyar nan da na cikin Belel akwai banbanci ,iya rayuwar mu kiwo muka sani se gashi abubuwan da kawai a labarai muke ji yau muna ganin su. Mukan hango jirgin sama a chan sararin samaniya yayinda yake wuce wa sai kaga muna d’aga masa hannu amma yau sai gamu cikin filin jirgin sama dake Borno state. wannan sabon al’amari ne.

“Na so muyi tafiya by road but gaba d’aya tun bamu je ko ina ba na gaji shiyasa na yanke shawara mu bi jirgi kawai” Cewar Mom ita de Laila Murmushi kawai tayi.

KADUNA STATE.

“Wow! Amma gaskiya kun shammace ni ,nayi zaton se gobe zaku iso.” Cewar Ummin Habeeb dake rungume da Mom.

Murmushi mom tayi yayinda ta zube kan kujera tace “gajiya nayi tun bamuje ko ina ba , finally Allah ya kawo mu lafiya” Ummi Murmushi tayi ta ce “yes I can see that. Laila da Junaid de suna tsaye sai lokacin Ummi ta juya suka had’a ido da Laila baki ta sake kamar taga abin mamaki da kyar ta Saki murmushi tace
” I have to say Lallai Suraj ba baya ba wajen iya zab’e ,Masha Allah! Babu makawa nasan wannan ita ce surukar tawa” tana gama rufe baki ta rungume Laila tayi Murmushi Mom ma murmushin tayi , Ummi ta dubi Junaidu tayi Murmushi tace

“Haba d’a na ya naga kana d’ari d’ari haka nan? Ka Saki jikin ka nan gida ne duk inda kaga dama zaka shiga yadda kake yi a Belel” kai Junaidu ya girgiza ya nemi waje k’asan carpet zai zauna Mom ta umarce shi da ya zauna a kujera ,kamar mai tsoron wani abu ya d’an d’osana cinya ya zauna ita kuwa Laila sam Ummi ta k’i barin ta se jan ta a jiki take. Wannan sabon yanayi ne ga Laila jin yanda soyayyar mahaifiya yake bayan shekaru da dama.

Tun fitar sa daga mota yake tsaye yana waya a jikin motar , idanuwan sa ne suka sauk’a kan motar Suraj dake ajiye cikin jerin motocin dake parking lot , slight Murmushi yayi sannan ya k’arasa jikin motar don ya tabbatar da cewa motar Suraj d’in ce kuma yana isa yaga ita d’in ce ,kai ya girgiza ya juya ya nufi cikin gida.

  Daga sallama ya nufi gefen Ummi ya jingina kanshi a kafad’ar ta yace “I missed you Momma” fuskar shi ta d’an Mara tace “baka jin kunya ne kai? God’ai god’ai da kai , Toh in ka manta in tuna maka auren K’anwar ka ake shirin yi yanzu ka girmi shagwab’a. Wata dariya Habeeb yayi wanda yasa har Junaid ya d’ago kai baki a sake  , Habeeb ya mik’e ya ja hannun Junaid suka haura upstairs Ummi ta k’ira d’aya daga cikin masu aikin gidan Zainab tace ” wannan y’a tace Laila ki kaita d’akin dake fuskantar na Sapna that will suit her sannan in har kina so much shirya ki tabbatar babu abunda tayi lacking, in fact daga yau komai nata ke zakiyi shit ,sauran ayyukan duk na soke miki make her feel at home,” daga durk’ushe Zainab tayi Murmushi tace “in Allah ya yarda ranki shit dad’e Zan yi abinda ya dace “. Murmushi Ummi tayi tace “Da kyau!, Laila y’a ta tashi kije nasan duk a gajiye kuke an kusa kammala abinci kafin nan ki watsa ruwa Ki huta” kai Laila ta jinjina ta mik’e Zainab ta shige gaba tana bin ta a baya.

  “Razia! Raaaziya!!! Tunanin me kuma like yi haka? Whats bothering you?”. Murmushi mom tayi tace “Ammm babu komai  kawai tunani nake ko Suraj ya zo nan ?”

Ummi tayi Murmushi tace “daman nasan se haka! Ni kaina da na Gan shi shi kad’ai nasan akwai matsala in babu dalili Suraj bazai zo nan ya zauna shit kad’ai ba tun da Habeeb na chan, anyways ki kwantar da hankalin ki Suraj yana nan ,basu dad’e da fita ba shit da Sapna , yanzu kije ki huta tukunna anjima se muyi magana duk naga kin gaji” kai Mom ta girgiza ta mik’e ta nufi wata k’ofa. Kai Ummi ta jinjina tayi Murmushi kafin ta d’auki wayar ta tayi dialing wata lamba wanda ga dukkanin Alamu number ta K’asar waje ce , saida ta sake k’ira a Karo na biyu aka d’aga wayar

“K’ani na barka da war haka, hope komai lafiya de ko?” daga d’ayan b’angaren wanda ta k’ira da K’anin ta yace 
“Lafiya lau Babbar yaya , komai yana tafiya daidai Yaya y’ay’an nawa? Hope Sapna ta daina fushi da uncle d’in ta de ko?” 
Murmushi Ummi tayi tace “y’ar ka tana fushi da kai kuma tace se ka dawo fishi zai k’are, Kai kam kana da debt da yawa a kan ka *Rasheed*  in two weeks za’a d’aura auren Sapna amma kafin nan *akwai wani abu ne da naci Karo da shi d’azun nan kuma gaskiya abun ba karamin bani mamaki yayi ba ban san ko zargi na zai iya zama gaskiya ba but you’ve got to see this first, ina so kazo dan Allah*

  Ajiyar zuciya Rasheed yayi  sannan yace “throughout wannan satin ina da appointments da wasu manyan companies a nan London insha Allah friday evening Zan taho and please kar ki fad’a wa Sapna uncle zai zo Zan shammace ta ne , I know she love surprises” Murmushi Ummi tayi kawai ,suka yi sallama ta ajiye wayar sannan ta nufi upstairs.
Good news! Suraj yana KD, amma bamu tab’o Laila ba bare muji ya take fama da sabon muhallin da ta tsinci kan ta a ciki. Dan haka nace bari na karkad’e y’an matan k’afafu na in garzaya d’akin Laila +

*******           *******      *******

     A inda Zainab ta bar Laila a nan take tsaye wuyan ta na lilo daga b’angare zuwa b’angare  bata san ta inda zata Fara ba, ta kai mintina fiye da biyar se cizar yatsa take daga bisani ta nufi k’ofar bathroom wanda yake rabi a bud’e, ta tuna Zainab ta fad’a mata band’aki ne ,turawa tayi ta kutsa kai ciki bata san lokacin da ta hangame baki ba, komai na ciki zaka yi zaton da gold aka yi shi , ga warm jacuzzi sai tiririn k’amshi ke tashi ,durk’usa wa tayi ta sa hannu a ruwan tana dariya, sannan ta mik’e tana kallon shimfid’add’en farin tile dake k’asan bathroom sannan tana shafa shi da k’afa tana ja da baya , wata k’ofar ta hango ta nufa a hankali ta bud’e, farin bulb ne a ciki shiyasa d’akin yafi wanda ta baro haske tana shiga wasu madubi ne masu tsayin gaske su uku daga b’angare uku na d’akin a cikin ko wanne tana iya ganin full reflection d’in ta, daga b’angare d’aya kuma babban wardrobe ne mara marfi cike da towels da bathrobe  iya k’ayatuwa wajen ya k’ayatu  Laila ta mance zancen wanka daga ta tab’a wannan se ta tab’a wancan duk tsawon lokacin nan babu abunda ta yi se bawa idonta abinci.

     “Kai! Habeebu gaskiya Zan che naga wautar ka sosai! Cewar Junaid dake fama da roasted chicken.

Habeeb dake gefe yana  Danna laptop ya d’ago yana dariya yace “Me ya faru  Junaid?”

Haba Abokki na ! Yanzu  wannan kaza da kana da wayo da baka gasa ta ba ,kaga da an sha kiwo dan kwai zatayi aradu!!!” Habeeb bai san lokacin da ya zame  k’asa ba tsabar dariya har yana rik’e ciki yace “Toh yanzu Kai Junaid  gashi da ba’a yi kiwon ta ba aka d’an gasa ta ai bakin ka ya motsa gashi har wani maik’o bakin ka yayi se kace d’an Amarya nashanasha abunka “. Washe hak’ora Junaid yayi ya ce “gaskiya”. Habeeb shafa k’asumbar sa yayi yana dariya k’asa k’asa
“Ni dai kayi ka gama kayi wanka muje mu ci abinci dan yunwa nake ji” Junaid ya d’ago yace 
  “Chabd’i jam! Yanzu ni ina Zan k’ara wani abincin? Kaza sukutum na cinye a cikina kai de kaje kaci ni kasan da yanzu ina chan Belel ina kiwo yanzu gashi ku abun kiwo ma sede a cinye shi.”

    Mik’e wa Habeeb yayi ya Mak’e. kafad’a yace “ga chan kaya na ajiye maka in kayi wanka ka saka ni zan sauk’a k’asa in kaga dama ma ka kwanta kayi ta mafarkin kiwo.”

Wanka kuma? Kashe kawai in d’an wanke jiki na amma yaushe ma nayi wanka?” Junaid yana gama fad’in haka ya hau gado yayi d’add’aya Habeeb kuwa ya fice se dariya yake.

  Taho wa take tana y’ar wak’ar ta shima ya taho suka jame babu wanda yayi magana tsakanin su se sak’on harara da suke aika wa juna gashi ta k’ura masa ido

“Wayyo Allah ! Daga dawowa har na Fara had’uwa da masu bak’ak’en ido! Allah ka tsare mu sharrin y’an sa ido”. Cewar Habeeb cikin d’aga murya. Murgud’a baki Zainab tayi tace “Oh ni Zainab yau kuma birin k’auyen nan ne ya dawo? ba mamaki don na hango ido a rami!”

  Tana kai nan ta cigaba da tafiya Habeeb da ya cika da haushi ya rufa a guje ya bita ” ke mara mutunci waye Birin ? Ita ma gudun ta sa iya k’arfin ta, ta bud’e k’ofar Laila ta shige sannan ta d’an lek’o tace “Kai mana! Kai ne biri kaje kitchen akwai tarin ayaba nasan bazaka rasa yunwa ba Biri kawai and!!!” Habeeb yana kawo wa k’ofar ta rufe ta ciki da sauri ta sa lock ta jingina jikin k’ofar tana maida numfashi. Cike da jin haushi Habeeb ya nufi downstairs yana huci.

   “Me ya faru Habeeb naga ranka a b’ace haka?” Mom ce ke tambaya Ummi kuwa ko d’ago kai bata yi ba Habeeb se cewa yayi

“Me zai sa nayi fushi banda wancan kazamar Allah kuwa wataran sai na sauya mata kamanni a gidan na”. Se lokacin Ummi ta d’ago ta kalleshi tace 
“Kar Ka soma! Don’t you dare ! Zan b’ata maka rai Habeeb in ka tab’a Zainab” Rai a b’ace ya wuce kitchen ba tare da ya ce komai ba yana shiga yaga stew se b’ararraka take a kan cooker , shafa kan sa yayi yana shu’umin Murmushi spices rack dake ajiye a gefe ya kalla yayinda ya sa hannu ya d’auko gishiri da borkono ya zazzaga a ciki duk, ya gauraye sannan ya fice ba tare da ya bar wani abu da zai sa a gane wani al’amari ba. Fresh yoghurt ya d’auka daga fridge ya fito yana sha hankali a kwance Ummi kuwa tana bin shi da kallo  daidai lokacin k’ofa ta bud’e duk suka maida hankalin su ga k’ofa.

    Kyakkyawa ce ajin farko suna Kama da Ummi kam, mayafin kan ta take cire wa tana k’araso wa , yayinda mayafin ta ya bar kan ta sannan ne ta d’ago suka had’a ido da Mom ,da gudu ta je tayi hugging d’in Mom

“Mommeeeee ! Mommy ! Am glad you are here ! Ummi meyasa ba’a k’ira ni a waya ba ai da tun tuni na dawo,” Murmushi Mom tayi tace “yanzu kam ai gaki kin dawo”

  Da baya da baya ta cara tafiya tana dariya tace “Mom ! Yau akwai labarai masu dad’i kawai ki shirya ” kai mom ta girgiza tana dariya ita kuma *Sapna* ta juya zata haura bene.

   Da gudu ya shige gaban ta yana k’urban Yoghurt d’in idon sa cikin nata ya d’aga gira d’aya ita ma tayi kwaikwayon shi kafin tace  ” Ya ka tare mine hanya ni ka matsa min in wuce!” Tsaki Habeeb ya ja

“Tsk, in kuma nak’i fa? K’arama da ke baki iya girmama na gaba da ke ba!” Daidai lokacin Zainab ta fito tana ta rakub’e wa a bango Habeeb ya bar kallon Sapna ya juya yana kallon ta , saida ta wuce su ta juyo tace “duk da ita k’arama ce gashi ta fidda mijin Aure gashi Kai babban har yanzu kana cinyar Ummi abin kunya, in kana so a girmama ka Toh ayi zuciya a fito da matar aure ,kuma ga shawara ka auro kyakkyawa saboda kar a haifo taron birirrika”

Sapna har k’asa ta kai tana dariya Haber kuwa Robar yoghurt d’in ya wurga wa Zainab ya kuskure ta a hannu ,cikin b’acin rai Mom ta daka masa tsawa ,da gudu ya haura sama yana dariya k’ofa aka bud’e hakan yasa Ummi ta d’ago kai tana Murmushi tace ” *Suraj*!! Shigo manaa ya ka tsaya?…..Mom dake zaune ido kawai ta k’ura masa har ya k’araso falon yayinda masu hidimar gidan suke shigowa da ledoji da kuma jakkunkunan shopping duk suka  tsaya suna jiran a basu izinin kai kayayyakin inda ya kamata, sedai Suraj hankalin shi na kan Mom wanda tun kallon farko bata sake d’ago kai ta kalle shi ba. Ummi ce ta katse shirun ta hanyar gyaran muryar ta kafin tace +

  “Na san Sapna ta wahalar da kai d’a na, go freshen up, koma menene anjima after dinner zamu yi magana   we’ll sort everything out. Kai Suraj ya girgiza ya wuce zuwa d’akin sa.

  “Raaaziya!! Me haka please? Ki duba yadda yaron nan ya sauya am sure bai taho nan don ya b’ata miki rai ba ko kuma ya bak’anta miki ba he’s just desperate and looking for yadda zai yi ,yanzu ma in ya rasa fuska daga gareki wancan yanayin damuwar zai koma.” Murmushi Mom tayi tace “Na fahimce ki ba fushi nake da Suraj ba
Kawai mamaki nake yadda ya iya tafiya ya kashe wayoyin sa haka nan ko da yake shikenan ,ni bari in duba Laila ita kad’ai ne” 
“Yawwa in kin je se ki taho da ita dinner is ready by now nasan tayi sallolin ta kuma ta shirya.” 
“Hakane ” Cewar Mom.

     Zaune take k’asan gado ta had’a kai da gwiwa , Mom ce ta shigo ,ga mamakin ta sai taga yadda Laila ta Zo babu abunda tayi ko wanka bata yi ba balle har ta chanja kayan da Ummi ta aiko mata. Daidai lokacin Ummi ta shigo d’auke da glass d’in fresh juice ,ita ma turus tayi baki sake kafin ta k’araso gefen Mom ta tsaya a tare suka dubi juna

“Is she alright?” Ummi ta tambaya , Murmushin tausayawa Mom tayi ta nufi inda take ta zauna gefen gado gami da dafa kafad’ar Laila tace “me yake damun ki haka y’ata gaba d’aya kin takura kan ki , gashi tun d’azu ko wanka bakiyi ba miye matsalar?”
D’ago wa Laila tayi ta dubi Mom da manyan idanuwan ta amma kafin tayi magana Ummi dake tsaye ta saki glass d’in hannun ta ya fad’i k’asa *Tas* ya fashe hakan yasa duk daga Laila har Mom suka Mik’e tsaye suna kallon Ummi ,

  “Lafiya kuwa? Me ya faru haka?” Mom ta tambaya.

*”Her eyes…. Idanuwan ta they look just exactly the same! “*

A hankali take  maganar Mom bata ji komai ba sedai ta lura Ummi tana magana saboda lab’b’an ta suna motsi.

“OUMMI HABEEB! Lafiyar ki kuwa? You look totally lost” Cewar Mom 
“A’a… Ammm…. Babu kkkomai kawai stress ne kin san shirye shiryen bikin y’a mace gaba d’aya ban samu Hutu ba ,ji nayi kaina yana Sara wa shine glass d’in ya sub’uce, yanzu zan je in kwanta zan turo Zainab ta gyara wajen nan , zan turo miki Sapna domin ta taimaka wa Laila”

Kai mom ta jinjina tace “Toh Allah ya sauwwak’e, gaskiya kam ya kamata ki huta tunda yanzu gani nan komai zai miki sauk’i. Kai Ummi ta jinjina ta juya da sauri ta fice Mom ta dad’e tana kallon hanyar da tabi kafin ta juyo ta dubi Laila da Murmushi tace

“Ina jin ki ,fad’a min miye matsalar?
Kai a k’asa tace “ban gane komai ba, babu bokatin wanka duk har d’ayan d’akin “

Murmushi Mom tay tace “ai bakya buk’atar bokatin wanka y’ata muje in nuna miki komai, Toh banda Zainab ma da shirme

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *