Cikakken tarihin maryam booth
SUNA: MARYAM ADO MUHAMMAD
INKIYA: MARYAM BOOTH
SHEKARA: 28 OCTOBER 1993 (shekaru 29)
AURE: BABU
AIKI: JARUMAR FIM, CEO BOOTH COLLECTION
MATAKIN KARATU: MASTERS
GARI: KANO
KASA: NIGERIA
WACECE MARYAM BOOTH
Jaruma maryam ado Muhammad wacce akafi sani da maryam booth ficecciyar jaruma a masana,antar shirya fina-finan hausa kannywood hadi da nollywood
HAIHUWA
An haifi Maryam booth ne a cikin garin kano sannan mahaifinta yakasance Dan kasar Scotland ne Mamanta Kuma Yar Nigeria ce bafulatana
Kana Maryam booth da mamanta da Kuma kaninta Ramadan booth dakuma yayanta Ahamad booth duk sun kasance jarumai ne a masana,antar kannywood
Suna daga cikin manya kuma sanannu a masana’antar shirya finafinai na kannywood.
Karanta Cikakken Tarihin Rabi’u Rikadawa (Baba Dan Audu)
FARA FILM
jarumar ta fara Shirin film tun tanada shekara 8 a duniya a wani Shiri mesuna suna
_dijan gala Wanda akayi a shekarar 2002
KARATUNTA
Maryam booth Tayi karatu nursery da primary a makarantar ebony dake kano sanna. Kuma tayi karatunta na secondary a makarantar Ahmadiyya Secondary School dake kano.
Sannan Kuma ta tafi kasar malesia Karin karatu, tayi degree a kasar malesia, ta karanta business administration a makarantar mantissa college dake kasan malesia.
Sannan tadawo Nigeria tayi karatun masters a bayero University dake garin kano inda ta karanta Management and Cinematography
KYAUTAR GIRMAMAWA
Maryam booth ta samu kyautar girmamawa da dama a tarihin rayuwanta
Kamarsu
•best supporting actress 2020 (afrikan movie academy award)
Dadai sauransu
AURE
Maryam booth har yanzu batayi aure ba. Amma a yadda ta shaida tana dab dayi a duk lokacin da tasamu miji na gari mai rikon amana da gaskiya
KARIN BAYANI
Sannan Jarumar ta kuma ziyarci kasashe da dama kamar su
-Saudi Arabia
-Malesia
-Dubai
-Egypt
-Scouttland
-America
Dadai sauransu
Sannan tambayar da akafi yiwa jarumar shine yaushe zakiyi aure
YARUKA
Sannan jarumar tana jin yaruka da dama kamarsu
_turanci
_Hausa
_fulatanci
_yaruba
_igbo
HADAKA
kana Jarumar Maryam booth tafito a Fina-finai tare da manya manyan jarumai dake kannywood kamarsu
*Adam a zango
*Ali nuhu
*Rahama sadau
*Ibro (marigayi)
*Halima atete
*Ramadan booth
*Zaraddin sani
*Hadiza gabon
*maryam yahaya
*Umar m shareef
Dadai sauransu
JERIN FINA FINAI
Maryam booth tayi Fina-finai da dama a tarihin ta na film kamar su
_sakanin-mu
_Yar aljanna
_Bayan Rai
_Dijangala
_Yan Mata
_Son Mai So
_Tuwon Tulu
_Nadawo Gareki
_Ijaabaah
_Sani Nake So
_Bani Bace
_Duniyar Mu
_Alawiyya
_Burina
_Ankwa
_Dattijo
_Bani Adam
_Gani Gaka
_Dare
_Garin Dadi
_Karkimanta dani
Dadai sauransu.
KarantaCIKAKKEN TARIHIN YUSUF SASEEN
Sannan fim dayafi birgeta daga cikin fina finanta shine karkimanta dani wadda tafito tare da shamsu dan,iya da Ali nuhu
NOLLYWOOD
Sannan kuma jarumar maryam booth ta fito a fina-finan nollywood wadda ake shiryawa a kudanci Nigeria kamarsu
•milkmaid da
• son of caliphate
Dadai sauransu
Karin bayani dangane da cikakken tarihin maryam booth a YouTube Nw Hausa Tv