Cikakken Tarihin Sani Danja

Cikakken Tarihin Sani danja

SUNA: Sani Musa abdullahi

INKIYA: Sani danja

SHEKARU: 20 April 1973

AIKI: Jarumi, darakta, furodusa, mawaki, dan rawa

MATA: mansura isah

YARA: hudu

GARI: Kano

KASA: Nigeria

Cikakken Tarihin Sani danja
Danja

 

WANENE SANI DANJA

Sani musa Abdullahi wadda akafi sani da sani Danja ko Danja yakasance jarumi, mai shirya fim, mai bada umarni, mawaki sannan kuma Dan rawa.

Sani Danja na daya daga cikin manyan jarumai dasuka bada gudumawa kuma suka tsaya tsayin daka Wajen habakar masana’antar shirya fina finan Hausa wato kannywood.

Daga bisani jarumin yafadada harkarsa inda ya tsallaka izuwa masana’antar shirya fim na nollywood kamarde sauran jaruman irinsu Ali nuhu, rahama sadau dakuma abokinsa yakubu Mohammed.

Karanta: CIKAKKEN TARIHIN ALI NUHU

HAIHUWA

An haifeshi a ranar 20 ga watan aprilu a shekarar 1973 ( 20 April 1973) a karamar hukumar fage dake jihar kano.

KARATUNSA

Yafara makarantar primary a Yan sanda special school daga bisani ya koma zuwa makarantar capital primary school ya kammala karatunsa na primary, Yayi makarantarsa na secondary a A makarantar rumfa college dake garin kano.
Bayan kammala makarantarsa na secondary ya zurfafa karatunsa izuwa makarantar FCE dake kano yasamu kwalin NCE.

FARA FIM A KANNYWOOD

Sani Danja yashigo masana’antar shirya fim na Hausa a shekarar 1999 inda yafara da shirinsa nafari mai suna Dalibai.

Jarumin yasamu nasorori dadama a harkarsa ta fim yakuma mallaki kamfanin shirya fim nashi nakansa mai suna 2Effect.

Danja yashirya finai dama, kuma yabada umarni a fina finai dadama cikin harda
*Daham
*Gidauniya
*jaheed
*Jarida
*Manakisa
*Nagari
*Kwarya tabi Kwarya
*Wasiyya
Dasauransu

KARANTA: CIKAKKEN TARIHIN ABUBAKAR BASHIR MAISHADDA

NOLLYWOOD

A Masanatar nollywood kuwa jarumin yafarane fitowane a shirin mai suna “Daughter of the river” (‘Yar ruwa).

 

Cikakken Tarihin Sani danja
Sani Musa danja

JERIN FINA-FINAI

kana jarumin ya fito a fina-finai da dama kamarsu
*Albashi a shekarar 2002
*Gwanaye a shekarar 2003
*Daham a shekarar 2005
*Budurwa a shekarar 2010
*Kukan Zaki a shekarar 2010
*Yar agadez a shekarar 2011
*Bani Adam a shekarar 2012
*Gani Gaka a shekarar 2012
*A Cuci Maza a shekarar 2013
*Da Kai zan Gana a shekarar 2013
*Fitattu a shekarar 2013
*Dan Magori a shekarar 2014
*Duniyar nan a shekarar a shekarar 2014
*Hanyar Kano a shekarar a shekarar 2014
*Daga Allah ne a shekarar a shekarar 2016
*Buri uku a duniya a shekarar 2016
*Fanan 2021

HADAKA

Kasancewar jarumin daya daga cikin manyan jarumai a masana’antar jarumin yayi hadaka da manya da kananan jaruma cikin masana’antar kadan daga ciki sune:
*Yakubu Mohammed
(Babban abokinshi)
*Ali nuhu
*Mansoora isah (matarsa)
*Hadiza Gabon
*Marigayi wanke wanke
*Aina’u Ade
*hajara usman. Dasauransu

Saide kasancewar yanzu Danja yaja baya da shiri a masana’antar dayawa daga cikin sabbin jaruma basu samu fitowa dashi cikin shiri ba.

AURE

Sani musa Danja ya Auri fitacciyar jarumar nan Mansura, inda sukai haifi yara hudu (hudu).

Saide a shekarar 2021 sun sanar wa kafafan yada labarai cewa rabuwarsu dajuna itace mafi alkhairi agaresu kuma yasaketa a shekarar.

Zaku iya ziyartarmu a shafinmu na YouTube domin samun Karin bayani dangane da cikakken tarihin sani danja

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *