DA KAMAR WUYA CHAPTER 4 BY ZULAIHAT IDRIS MISAU

DA KAMAR WUYA CHAPTER 4 BY ZULAIHAT IDRIS MISAU

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

har yanzu guy din nan bai daga waya ba fah!!?” Hafiz ya fada bayan ya sauke wayarsa daga kunne.+

Tsaki ashir yaja, bayan ya share bakinsa da tissue, yana ture plate din gabansa. ” Ina kuke tunanin ya shiga?”

Kafada Hafiz ya daga ” I don’t known, tun dazu dai da muka rabu dashi a gidansu alim, kan daddy na nemansa, bamu sake ganinsa ba. Gashi  ko picking calls din ma bayayi. “

” duk rainin hankalin hayder, baya kin daga waya. Maybe daddy ya aikeshi ne.” Inji Hafiz omer

” kai I don’t think so. I’m filling some thing is wrong ” junaid ya fada

” kun tambayi su Yaya Ahmad? Ko sun San inda yake?”

” they don’t known where he is.”

” let me trace his number. ” junaid ya fada yana fito da wayarsa a pocket.

” a kwai dan iska, da kasan da tracing din ka barmu cikin damuwa.” Amin ya fada

” I totally forget, sorry. “

For some second junaid ya dago yana kalonsu. ” I can believed yana cikin gidan nan.” 

” are u sure? ” kai ya kada.

” OK Le’s cheek Abdul part. Don nan ne kawai bamu duba ba.” Ashir ya fada yana mikewa tsaye.

Dai dai lokacin hayder ya fito daga part dinsu Abdul. Da kallo suka bishi, kallo daya sukawa juna suka tabbatar some thing is wrong with him.

Wurinsu Ahmad ya isa, suka gaggaisa, ganin yanayinsa duk suka shiga tambayarsa lafiya? Murmushin karfin hali yayi ” I’m not filling fine. ” ya fada cikin muryarsa mai dadin sauraro da Jan aji.

Rungumeshi Ahmad yayi, yana tambayar abinda ke damunsa. Kansa ya nuna masa,. ” kasha magani ko muje hospital? ” ta tambaya cikin nuna tsantsar kulawa.  ” no I’m ok. I take a drug. Fatan samun sauki sukai ta masa. Kafin ya nufi cikin friends dinshi.

” what is wrong with u?” Junaid daya tareshi tun kan ya iso, ya fara tambayarsa. Kamar yadda ya fadawa su Ahmad haka suma ya gaya musu. Duk da junaid bai yadda da abunda ya fada ba, amma ya bashshi a hakan.

Kayan ciye ciye ne burjik a wurin, don duk abinda aka ci a wurin sai da ta diba musu, a kyawawan containers. Ba suba har su Ahmad ma sun samu.

Cake din daya hango a gefe, ya janyo. Cake din ya burgeshi da gani zai yi dadi. Duk da cake ba cimarsa ba ce, musamman cup cake, amma wannan ya bashi shaawa. Sai da yakai daya bakinsa ya gutsura bayan yayi bismillah. Ya kalli Hafiz omer da tun dazu yake kallon hayder yana karantar yanayinsa. ” ina cuka samu wannan delicious cake din?”

Amir ne ya amsa shi da ” Anty hubby, kasan jiya da muka rabu dakai gidan mommy Hauwa muka je, so mun samu tana aikin cake din, kamshi ya ishemu, kasan hali, ta hanamu dandane, wai na lunch ne, baa ce taba kowa ba. She promise us, zata ajiye mana namu after lunch, she keep her promise.” Ai kafin amir yakai aya hayder ya furzar da cake din bakinsa, ruwan dake hannun Hafiz ya fige, ya fara kuskure bakinsa dashi. Kallonsa suka tsaya yi baki bude, cike da mamaki, duk da sun San ba shiri tsakanin hubby da hayder amma sun San abun bai kai haka ba.

Dariya Hafiz yayi ” na banza, don na tabbata wani ya wuce ciki.”

” Allah ya kyauta. Naga ranar da zaku daina wannan abu kai da Anty. Ko ba komai ai you have to respect her, she is elder, and aur friend sister.” Hafiz ya fada

” a kwai abunda ke damun kwakwalwar yaron nan, Ku barshi kawai.” Hafiz omer ya ce

” waye yaron?” Hayder ya fada yana kallon Hafiz omer

Dariya Hafiz omer yayi tare da daga hannun serenader ” sorry. “

Junaid dai na daga gefen hayder yana kallon ikon Allah. Duk da bai ji dadin yadda hayder yayi ba, amma ko a fuska bazaka gane hakan ba.

Kiraye kirayen sallar da suka jiyo, yasa suka nufi masallaci don gudanar da alwala da sallar magrib.

               *******************

Da sallama suka shigo, su Anty samira da munaya, sai sauran yan uwansu da suka dawo daga wurin lunching, basu kai ga shiga part din Mmn samira ba. Suna tsaye a harabar wurin ana maida yadda akayi, a wurin lunching, Su hubby suka shigo. Kadan daga cikinsu suka amsa musu sallamar.

Ganin yadda suka kuresu da ido, yasa su hubby suka gaishesu in jam’u. Har sun wuce samira ta ce ” kai Allah mun gode maka, yanzufa yan matama kwantai suke, balle zawarawa, shiyasa sai kiga ana neman likawa jamaa dole.” Ta fada da karfi yadda su hubby zasu jiyota.

” oho!!! Kuma!! In ta wuce kan mijina, ta fada kan kowama, bai daman ba.” Munaya ta fada tana hararar bayan hubby.

Basu kai ga jin karashen maganar ba, suka shige, duk da su yusra basu San kan zancen ba, sun dauka hira kawai suke, amma ita hubby ta San da ita suke. Ranta ya baci amma bata da lokacin batawa a Kansu. Koma mai zasu ce, sun dade basu fada ba.

                *****************

Alhaji Jamal bai shigo gidan ba sai to 12am. Allah yasa Hajiya ranar ita keda girki. Hakan ya bata damar tattaunawa da mijin nata, a tsanake.

Abdul Karim kam bai samu shiga wurin Mmn samira ba, ana idar da sallar isha’i, suka fita da arif daya iso daga legos, lokacin da suka shigo gidan already late. Anty samira ma data kirashi hakuri kawai ya bata, kan zasu hadu da safe.

Hayder ranar raba dare yayi yana addua. Tare da kai kukansa ga mahaliccinsa. Don har ga Allah baya jin son hubby ko digo a zuciyarsa. To yarinyar da ko soyayyar yan uwantaka bata hadasu ba, ina ga soyayyar aure? Hankalinsa ya dan kwanta, ganin har ya bar gida, zuwa in da suke kwana, saboda baki, Hajiya bata masa maganarba. Yana fatan Allah yasa kunnensa ne bai jiyo masa dai dai ba.

                *******************

Tagumi mommy Hauwa ta zabga bayan ta gama jin bayanin bakin Alhaji Munir. Gaba daya lamarin ya isheta ya daya, amma kullun a kazo maganar aure sai ran kowa ya tashi, mu samman wannan karon.

Ajiyar zuciya mommy Hauwa tayi tare da kallon maigidan nata. ” da kamar wuya, wai hurguwa da auren nesa!!! Wannan hadin gaskiya bayyi ba, kowa yasan tsakanin hubby da hayder kamar masu ganin hanjin juna, tun tasowarsu, har zuwa yanzu. Sannan hubby ita take gaba dashi a haife, ta ina zaa fara wannan danyen aikin? Kudai canza dabara gaskiya, kar azo ayi abinda za ayi dana sani.”

Zama Alhaji Munir ya gyara, tare da fuskantar mommy Hauwa da kyau. ” kin ban mamaki, ban taba tunanin wannan magana zata fito daga bakin kiba. Har kin manta da halaccin yar uwarki gareki? A tunanina ko yayayyen yaro Hajiya ta bukaci hada Ummi dashi bazaki ja da ita ba, balle danta na cikinta. Meye sharuddan da ya can -can-ci a ba namiji aure? Wannene hayder bai cika ba? Ban zama butulu ba, bazan taba manta alkhairi Hajiya da mijinta ba, kai harda su Alhaji babba, irin karamci da mutunci, da soyayya da suka nuna min, tun haduwata da omer, har zuwa jajur cewa da sukayi wurin ganin na aureki, har zuwa yanzu. Ni ko mai zan musu in biyasu? Babu!!! Na dade ina rokon Allah ya bani ikon saka musu da abunda suma zasuji dadi  komai kankantarsa. Auren Ummi da Yusuf ba karamin dadi ya min ba, duk da kalubalen da ni kaina nasan dasu. Haka ma yanzu ina son ki Sani, daga ke har Ummi ba shawararku nake nema ma. Umurni nane dana mahaifina, gobe in sha Allah bayan sallar jumaa zaa daura auren Ummi da hayder. Don haka duk abunda ake bukata ki natsu ki rubuta, gobe in Allah ya kaimu aje a siya. Don Sunday zata tare dakin mijinta, kamar sauran yan uwanta.”

” bana kin hadin nan, kamar yadda kake fada, hasalima nafi kowa murna. Abu daya zuwa biyu ke damuna. Sanin halinsu, sai nake ganin zaman nasu kamar da wuya a samu yadda ake so.” Mommy Hauwa ta fada tana sauke ajiyar zuciya

” addua zaki bisu dashi, ita suke bukata. Lokacin da zasu shirya kina ina? Karki manta ko ba komai yan uwan juna ne! Aure ya wuce duk inda kike zato. In sha Allah sai kin ce gara da akayi. Hakika nayi dacen suruki daya tamkar da dubu., hayder yarone, amma mai halin manya. Ke kanki abunda kika sani ne, ba yarinta a tare dashi, sai kamala, da mutunci, da sanin ciwon kai,da sanin ya kamata, Ga kamewa.” Murmushi mommy Hauwa tayi ” hakane kam, sai dai yarinyar taka fa zaa sha fama.”

” don’t mind her, barni da ita. Su gwaggo da tawagarta na nan isowa gobe, a gyara part din can su sauka a ciki, don gayya zatayi, kamar yadda ta fada min a waya. Tayi farin ciki sosai da jin wannan maganar.”

” ai fa? Bikin mutuniyarta, don ma lokacin yazo a kure.”

” haka ne!!; Ummi da gwaggo kam ai sai Allah, don ma ba kiji yadda take murna ba, ke kyace an mata albishir da gidan aljannah. “

” mutuminta ne Hayder, abun ya zama mata biyu. Takwara da balarabenta.” Mommy Hauwa ta fada tana murmushi

Murmushi Alhaji Munir yayi, tuno drama din gwaggo da hayder. Gwaggo akwai son hira, ga jininsu ya hadu sosai da hayder, hayder ba Hausa sosai, gwaggo ba larabci, so in kaji hirar dole kayi dariya, mu samman yadda yake takar karewa sai yayi Hausa, in ya kakare gwaggo na dariya zata murda nata larabcin ta masa bayani yanda zai gane. In kana kusa, ba kayi wasa ba har fitsari sai kayi a wando, don dariya.”

Hayder daga turanci, French, sai larabci sune manyan yaren da yake ji in yanayi kamar a bakinsa aka kirkiro. Hausa yana jin duk abinda zaka fada, mayar wane sai a slow. Don gidansu gaba daya baa wani yare banda arabic. Friend da sauran yan uwa da basa ji, sai dai suyi turanci. A school nema ya samu ya ji hausar don a gida ko iyayensu mata basu isa suyi musu Hausa ba, dokar Alhaji Jamal ce, dole a kiyaye a zauna lafiya.

            **********************

Yauma tun daga sallar asuba, Alhaji Jamal bai dawo gidansa ba. Hakan yasa basu hadu da Abdul Karim ba.

Koda ya shiga cikin gida, Hajiya kaka bata samu damar mayar masa da yadda akayi ba, saboda yana tare dasu arif. Anty samira kuma suna part din yara matan gidan. Ko da sukaje gaishe da Hajiya ita ma bata nuna masa komai ba. She act normal kamar yadda ta saba, duk da taji zafin jin cewa baya son hubby.

                  *****************

Part din Alhaji Jamal ta ja hayder don gidan ba masaka tsinke da jamaa.

Duk da faduwar gaban da yake, bai yadda ta gane tashin hankalin da yake ciki ba. Bata kawo komai ba, ganin ya dan fada mata, ta daukeshi matsayin stress.

Kallonsa tayi cikin natsuwa. ” meye matsayina a wurinka? Da sauri ya dago yana kallonta cike da far gaba.

Sunkuyar da kansa kasa yayi, yana jin zuciyarsa na karyewa. Saboda tuno girman matsayinta a wurin shi.

” matsayinki gareni ya wuce yadda labba da harshena zasu bayyana, kamar yadda girman hakkinki a kaina ya girmama, har musulunci ya mana umurnin kyautatawa gareku,  saboda girman matsayinku, ya sanya aljannarmu a kalkashin kafafunku, wanda sai kun daga kafin mu samu damar shiga aljannah, wadda take burin duk mai imani.”

Murmushi Hajiya tayi, tana kokarin maida hawayenta. ” ina neman alfarma a gareka, zaka iya mun?”

” umurni kawai zakiyi, bakya bukatar alfarma a gareni. Ni da duk abunda na mallaka muna kalkashin ikonki ne, duk abinda kika ce, matukar bai kauce wa shariar Islam ba, an gama.”

Hawaye mommy dake kokarin mayarwa suka fara bin kuncinta. Hakika hayder ya cika dan halas da daya tamkar da dubu, abin alfaharinta. Hakika tana daya daga cikin iyaye masu saar yaya a duniya. ba abunda zata ce sai Alhamdulillah.

” an taba mutuncina, an yi challenging dina in har na cika yar halas in aura ma ummi.” Tayi shiru tana goge hawaye

Da sauri ya taso zuwa inda take zaune, rigarsa yasa yana share mata hawayenta, bai damu da kwalin da ya samu wurin zama a fararen kayan jikinsa ba. Ya fara lallashin Hajiya.1

” in wannan ne ki kwantar da hankalinki, na miki alkawarin zan auri Habiba, kamar yadda kika bukata.”

” na gode hayder Allah ya maka albarka, ya baka yaya na gari, ya baka abinda bazai kareba, ya karemin kai daga dukkan sharri.”

“Amen “ya fada

” ka je ka fara shiri, don in an sakko masallaci zaa daura auren. Sunday zata tare, already an samu gidan da zaku zauna, yanzu zan je mu gani, bayan daurin aure sai kuje kuma, in akwai gyare gyare ko wani abu da ake bukata. Sauran kayan lefe duk zanyi in sha Allah sai kayi alfahari da wannan auren.”

” na gode sosai, amma ki bar min kayan lefen zanyi da kaina, in kunyi estimate din amount din kwa gayamin in bayar.”

” shi kenan.” Hajiya ta fada a part din ta barshi, don ya kulle tunda ba kowa. Tana fita ya hada kanshi da gwuiwa ya saki wani marayan kuka. Rabonsa da ya samu kanshi cikin irin wannan tashin hankali da bakin ciki, har ya manta.

Sai daya sha kukanshi, ya shiga toilet din daddy ya wanke fuskarsa, ya nufi masaukinsu.

Zuciyarsa cike da tsana da jin haushin hubby. Adduar yaye bakin ciki yayi ta maimaitawa saman labbansa har ya isa. Sultan guise inn dake kusa dasu. Don tunda aka fara biki, shida su Hafiz omer sukayi kaura zuwa can.

               ******************

Gida yayi kyau, well polished. daga Hajiya har su, Hajiya Balkisu gidan ya burgesu.  Duplex ne, falo biyu a kasa, kowanne da toilet dinsa. Sai kitchen, store, sai dan karamin daki a karamin falon. Sama kuma dakunan bacci ne guda uku da falo daya. Kowanne  bedroom da toilet dinsa. Gidan akwai fili sosai, da motoci kusan goma zasu iya parking, yasha interlock. Ga shuke shuke na fruit da flawers, sai dakin maigadi da toilet. Gidan na Unguwar malali ( sami close) sabon ginine baa dade da gama shi ba. Yaji finishing na zamani, komai high quality standard na gidan.

Nan take Hajiya ta biya kudin 2 years bayan sun koma office din kanin mijin Hajiya Balkisu.

Kiran mommy Hauwa Hajiya tayi ta shaida mata an samu gida, ta turo masu furnitures din su auna.

                *****************

Kuka take harda birgima, su Hajiya salwa sun sha lallashi har sun gaji.  Da bulala mommy Hauwa ta shigo dakin, kan hubby tayi gadan gadan cikin fushi. ” dan gidanku, me yasa shi da ya gaya miki, baki masa wannan haukar ba? Sai mu da kika raina? Ana lallashi kina kara botsarewa.” Da sauri Hajiya tunba ta tare mommy Hauwa ” haba ki bar yarinya ta yi kukanta! Taya zaa bugeka a hanaka kuka? Don haka karki fara dukanta.

Hubby da tun shigowar mommy Hauwa da sharbebiyar bulala, ta boye bayan salamatu. ” don Allah karki bugeni, na daina, amma ki cewa daddy ya aura min koma, wane ne, ko kuturune, ko makaho, duka na yadda amma banda hayder don Allah..,……..Murmushi mommy Hauwa tayi, duk da dunbin tausayin yar tata. ” hayder din dai da baki so, shine. Gara ma ki kwantar da hankalinki, don ba abunda zaa fasa.”+

” kiyi hakuri, kiwa iyayenki biyayya, matukar sunyi don Allah ba don wani abu na duniya ba. To in sha Allah zakiyi alfahari da hakan. Ballantana Sani kanki ne, duk abunda su kayi, sunyi ne don maslahar, da kuma kyakyawan manufa.”

” Allah rainani zai kara yi.” Hubby ta fada tana kara sake kuka.

Duk yadda su Hajiya suka so daure dariyar data taso musu kasawa sukayi. Cikin dariya Hajiya salwa ta ce ” banda abinki Ummi, yanzu kuma ai ke ce a kasa. Maganar raini duk bata taso ba, dole ki masa biyayya don aljannarki na kalkashin kafarsa. In kina neman aljannah to dole ki ajiye komai ki rungumi aurenki.”

Ta bude baki zatayi magana mommy Hauwa ta buge bakin. ” rufawa mutane baki, ana magana kina mayarwa, kamar saoinki. Allah ki shiga hankalinki dani. Shi bai yi kukan bai son kiba, sai ke? Yana yaro dashi son kowa kin Wanda ya rasa, an hadashi da uwar mata.”

” aa Hajiya Hauwa!!!! Yarinyar tawa kike kira uwar mata, duka duka nawa ummin take? In kyau ne, nima ai baa nunama diyata ba.”

Dirin shigowar motoci gidan ya sa hankalinsu ya koma can. Hubby zamewa tayi daga jikin salamatu ta shige dakinta, kuka ta saka iya karfinta ta fada saman gadonta, ta ci gaba daga inda ta tsaya.

Su gwaggo ne, da tawagarta. Lallai kam gwaggo tayi gayya kamar yadda ta fada. Kun San mutanen karkara da son zuwa bikin nesa!  Balle sun samu motoci available. Direct part din da aka gyara musu aka wuce dasu. Tare da cikasu da kayayyakin abinci, da na sha, da duk wani Abu da zasu bukata.

               ******************

Hafiz omer ya samu a reception. Da sauri ya nufo hayder ganinsa a hargitse. Rungumeshi hayder yayi yana sauke ajiyar zuciya. Cike da tashin hankali don bai taba ganin hayder a yanayin da yake ganinsa jiya zuwa yau ba. Na yanzu is worse.

” what is happened? Don’t Tell me is notting, tun jiya na lura some think its not right? Hafiz omer ya fada yana dan bubbuga bayansa.

Sakinsa yayi, tare da Jan numfashi. Hafiz omer ido ya zuba masa cike da damuwa. ” ka gaya musu, a kwai daurin aure a sultan bello masjid, after sallar jumaa.” 

” daurin auren wah?” Hafiz omer ya tambaya. Ko kafin ya karasa tambayar hayder ya wuce sama, zuwa dakinsa. Da kallo Hafiz omer ya bishi, yadda yake hada steps 2 to 3, ya haye.

Kai Hafiz omer ya kada tare da cewa ” Allah ya kyauta”  wayarsa ya Ciro ya shaidawa su junaid. Don  duk a tunaninsa daurin auren daya daga cikin yaran abokan daya daga cikin  daddies dinsune.

Yana shiga direct toilet ya wuce, wanka yayi tare da dauro alwala, duk da lokacin, ba lokacin nafila bane. Bayan ya shirya cikin daya daga cikin kayan da suka dinka don fitar bikin su Ummul khair.

Shadda ce, mai matukar kyau da tsada milk color. Duk da dan fadawar da fuskarsa tayi,   yayi kyau  sosai. Time ya duba to 1pm daga hannu yayi, ya karanto suratul fatiha x7, sai  karshen suratul bakhara. Sannan ya fara jero adduar jagorancin ubangiji, game da lamarinsa da hubby, ya bashi ikon yima iyayensa biyayya.

            ********************

Zamewa tayi daga kan gadon, ta kifa kanta cikin pillows ta saki kuka mai tsuma rai, har numfashinta na shishshidewa.

Gwaggo ta matso kusa da ita, cikin tausayawa, da sanyin jiki. ” haba takwara, aure an riga da an daura. Balarabe dan uwanki ne, kin san shi, kin San daga inda ya fito. Yanzu ba abinda ya rage face kiyi biyayyaya ga Allah da manzonsa. Kiyiwa iyayenki, da mijinki biyayya.”

Maganar gwaggo ta kara sa hubby kara fashewa da kuka, ji take kamar gwaggo ta watsa mata ruwan zafi, jin tace wai hayder mijinta. Dago fuskarta data jeme, tayi ja, ido sun kunbura, don kuka, cikin dasashshiyar murya da bata fita sosai ta bude baki zatayi magana, ko harafi daya ta kasa furtawa. Sai hadiyar zuciya take.

“Ayya har yanzu kukan ne, bai kare ba? Ki bar kukan nan haka zai cutar dake. Aure ne an rigada an daura, ba mu da abin yi, a yanzu. Na fahimce ki, kiyi hakuri da abinda iyayenki suke so, in sha Allah zakiyi alfahari da hakan.” Inna shatu ta fada tana shigowa dakin.

” Allah na tsaneshi?” Hubby ta fada cikin dashewar murya.

” to sai me in kin tsaneshi? Mu muna son sa, kafaffiya. Mommy Hauwa ta fada

Harara gwaggo ta watsawa mommy Hauwa. ” ana lallaba yarinya kina neman ballo wani ruwan?”

Daukar abunda ya kawota tayi ta ficewarta.

               *******************

Gaba daya mamaki ya cika su Ahmad da daukacin jamaar da suka San gidan Alhaji Jamal.

Daurin aure kam yayi jamaa sosai. Abdul Karim gaba daya hankalinsa ya tashi, ganin abun yake kamar almara.

Haka ta kasance gasu junaid da sauran abokan hayder. Da kallo suka dinga binsa.

He act normal, amma deep down his heart, shi kadai yasan yadda zuciyarsa ke suya. Duk yadda suka so jin Karin bayani daga bakinsa, basu samu ba.

Haka sukaita gaisawa da abokan su Alhaji Jamal da sauran family and friends. Kowa na masa Allah ya sanya alkhairi.

Rungumeshi Ahmad yayi, yana masa congrat. Abdul Karim dai ya kasa ko kwakwkwaran motsi, sai bin hayder da kallo yake, da sauran iyayensu da kakanni kowa ka kalla yana cikin matukar farin ciki, da anna shuwa.

A haka suka dungumo zuwa main house.

             *******************

A tsakiyar bedroom din Mmn samira, Hajiya Fatima, da wasu mutun biyu da suka mata rakiya, suka ajiye kwalayen sweet, dabino, da biscuit.

Buda daya daga cikinsu ta rangada har sau uku. “Cika alwashi sai dan halas, taka haye baya i’yawa. Allah yayi, alkawarin Allah ya cika, mai kyashi, da hassada sai kallo. Da daya tamkar da dubu, farin wata sha kallo, yaro mai halin dattako, kyau baa fika ba, haka ma arzikin baza a gwada dakai ba, balle ilmi da aiki dashi. Na Habiba Allah ya yarda.” Guda ta kara sawa.

Hajiya Fatima ta kalli Mmn samira, da yan uwanta da suka zuba musu ido suna kallon ikon Allah. ” ki kwantar da hankalinki, Habiba yanzu haka ta zamo mata ga Aliyu hayder. Wannan goron albishir ne, da kuma godiya.”

Kallonta Mmn samira tayi, ta kalli kayan sweet din dake tsakiyar dakinta. Cikin sanyin jiki ta kauda kanta. ” Allah sanya albarka.”

” amin in da gaske kike.” Daya daga cikin matan da suka zo da Hajiya Fatima ta fada

” alhamdulillah tun da an barmin jikana. Meye kuma na bita da kulli?” Hajiya kaka da ta shigo ganin abinda ke faruwa ta fada.

” babu kam!” Hajiya Fatima ta fada tana juyawa don barin dakin. A bakin kofa suka ci karo da Abdul Karim na shigowa, a hargitse. Kallo daya ta masa ta dauke idonta suka wuce, zuwa part din Hajiya.

Jikin Mmn samira yayi sanyi, tabbas bata kyauta ba, bata taba tunanin Hajiya zata zartar da wannan hukuncin ba, nadama da dana sani su suka lullube zuciyarta. Da bata bi zugar su samira da hajiyanta ba, da duk haka bata faruba. Koda Abdul Karim bai auri hubby ba, da ta kwantar da hankalinta an rabu cikin mutunci da ganin kimar juna. Amma yanzu wa gari ya waya. Ta bata da matar da take iyaka kokarinta na kwato mata hakkinta, ba tare da laa kari da zamowarta kishiyarta ba, kasan cewarta mara baki.

Shihowar Abdul Karim ya dawo da ita daga dogon tunanin data tafi. ” me yake faruwane mama?” Ya fada bayan ya zauna kusa da ita.

Hajiya kaka ta amshe ” meko ke faruwa, banda Allah ya kubutar mana dakai daga auren juya, second hand. Ai sai  Ka godewa Allah. “

Wani kallo ya zubama Hajiya kaka kafin yakai kallonsa kan Mmn samira, da jikinta ya kara sanyi. Daya daga cikin kannen Mmn samira ta fara koro masa bayanin duk yadda abun ya kasance.

Kai ya rike, hawaye na bin kuncinsa. ” kun cutar dani wallahi, koda na ce ita ba irin matar da nake so ba ce, ai ban ce bazan aureta ba ko? Haka kurun Ku yanke min wannan danyen hukuncin. Ai da sai Ku bari satin da daddy ya diba min su cika kuji matsayata ko? Kun San yadda nake sonta? U have no idea?”

” innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Yanzu Abdul mu kake cewa mun cutar dakai? Me yasa tun farko ka ce baka sonta, ina kai da bakinka ka gayawa yar uwarka hakan. Shine don ka raina mana hankali zaka zo ka canza managana, salon kasa a mana dariya. To tun wuri ka cireta a rayuwarka, don ta zama mallakin kaninka.” Hajiya kaka ta fada

Idonsa da suka kada su kayi jajur ya daga ya sauke su kan Hajiya kaka. ” ina samiran tazo ta gayamin gidan uwar da na ce mata ban son hubby? Ya fada yana waige waige

” ya rage naku kuma, aikin gama ya gama. Ni kaina sai da na bada shawara aka ki saurarata. Yanzu wa gari ya waya? Hakuri kawai zaka dauka, aikin gama ya gama, ka dauka Dama can ba matar ka ba ce.” Cikin yan uwan Mmn samira ta fada.

Mmn samira kam ta kasa cewa komai. Sai Karin nadama, da dana Sani dake nukur kusarta.

” idona idon samira, sai naci mutuncinta, munafuka kawai.” Abdul Karim ya fada yana barin dakin cikin fushi da bakin ciki.

” a kan wata banza can kake kiran, yar uwarka da munafuka? Ko Anty babu?.” Hajiya kaka ta fada tana bin batansa da kallo.

                ******************

Ko kafin su iso main house, su Hafiz sun kira daukacin friends dinsu dake garin Kaduna, sun shaida musu daurin auren hayder da walimar da zasuyi a gobe Saturday after magrib.

Suna isowa sun samu wasu daga friends din har sun iso. Kowa cike da mamaki, misamman wa ‘anda su kayi secondary school tare.

Direct part din Hajiya suka nufa, bayan gaisuwa, hayder yasha albarka, sannan suka shiga part din Mmn samira, sai part din Mmn Yusuf. Wadda itama daga baya taga rashin dacewar abunda sukayi. Ko ba komai tana jin hayder a zuciyarta kamar yadda take jin yayanta. Da tasan abun a kansa zai kare, da ta amince Abdul fatta ya auri hubby, in yaso a hada da nata zabin.

Gidansu bubby suka dun guma, don gaisawa da su mommy da sauran yan uwan hubby kamar yadda al’ada ta gada.

Sun samu tarba mai kyau, kamar a hadesu, musamman gwaggo data zage su kayi ta kashe hotuna da su hayder. Bakinta har kunne, don ji take tafi kowa murna da wannan Abu.

” yanzu da wannan Ummi ke kira da yaro? Wannan ai sai ya sabata a wuya ya kaita, Zaria ya dawo, baiji komai ba.” Inna Maryam ta fada

Hajiya salwa ta yi dariya ” kin San yaran yanzu akwai saurin girma, kamar ana basu takin zamani. Kalli su junaid? Wa zai ce Ummi ce yayarsu?”

” babu kam!!” Inna maryam ta fada

Yau kam hayder yaga kara da karamcin katsinawa. Duk da dayawansu ya sansu. Amma yaji dadin karamcinsu gareshi. Sun sha pictures kam, kamar ba gobe.

                  *****************

” don Allah sake trying number din hubby, shirun yayi yawa.” Humaira ta fada tana kallon Aisha

” ina ga kuje gidan Ku gani, don nasan lafiya lafiya hubby bazata kai yanzu, bata xoba, kuma bata kira ba. Ga number dinta baya shiga.” Aisha ta fada

Ummul khair ta mike,” muje ” harararta Aisha ta yi ” kin manta dokar rashin fita, a kanki ko?”

” share don Allah, sharf sharf zamu je mu dawo, ba tare da kowa ya farga da bana nan ba, in har ba Ku kuka fada ba.”Ummul khair ta fada tana daukar mayafi.

” ba ruwana wallahi.” Aisha ta fada

Ummu aiman ce ta shigo. “Ke kuma sai ina?” Ta fada tana kallon Ummul khair dasu yusra

” Hubby’s house. ” ta fada a takaice.

” zauna kusha labari. U can believed what is happened in this house. ” Ummi aiman ta fada tana zama kusa da Ummi sulaim.

” me ke faruwa?” Suka tambaya a tare.

Bowl din hannunta ta mika musu cike da sweets masu dadi, da tsada. Kowa ya zabi Wanda ransa ya masa.

” an daura auren hayder da hubby, dazu bayan sallar jumaa. This is the sweets for their wedding. “

Ummu sulaim ne ta mike da sauri, baki na rawa, ta kalli yayar tata ” ba kyau irin wannan wasan.”

Murmush tayi ” ina wasa da ke ne, da zan maki karya? Go and ask.”

Kuka Asiya ta fashe dashi. Cike da tashin kankali suka juya kan Asiya.

Mayafi Aisha ta jawo, suka fice ita da Ummu sulaim dasu yusra. Suka nufi gidan su hubby.

A compound din suka hadu dasu junaid. ” ta tabbata.? Ummu sulaim ta fada hango su hayder cikin kaya na alfarma, sai kashe pictures a keyi.

” lallai abun da kamar yuwa.” Aisha ta fada

Duk yadda suka so jin yadda abun ya faru ya ci tura, don su kansu su Hafiz ba su san takamai mai meya faru ba. Ummu sulaim duk da ita ce gaba da hayder to tana matukar shakkarsa. Don haka kasa tambayarsa tayi.  Allah ya sanya alkhairi suka musu, tare da shigewa ciki.

Hubby na zaune da daurin kirji a baikin gadonta, bayan hajja kolo ta gama turareta da wasu itatuwa masu matukar kamshi, fatarta sai glowing take. sai da Hajiya salwa ta tsaya a kanta sannan ta yadda a mata gyaran jikin. Don tana jin nauyin matar sosai.

Da gudu gudu suka shigo, ana rige rige. Hubby na ganin su Aisha ta taso da gudu ta fada jikin ummu sulaim, tare da sake sabon kuka.

” oh!!! Ni yau Allah na gode maka, wai ke bazaki gaji da kukan nan haka ba? Tun safe kina abu daya.” Hajja kolo ta fada tana har hada kayan kyaran jikin dake baje a tsakar dakin hubby.

Sai da ta dau some second kafin ta rabu da jikin ummu sulaim, kama hannunta tayi suka zauna. Suma su Aisha sukama kansu mazauni, bayan sun gaishe da hajja kolo. Kallon hubby sukeyi cike da tausayawa ganin yadda ta koma lokaci daya.

” kun ga yadda rayuwata ta kare ko? A rasa wanda zaa hadani dashi sai kanin kanin bayana, wanda a haihuwar kaji, nayi jika, da tattaba kunne dashi. Yaron da na tabbata na taba goyashi a bayana, wace irin rayuwa ce wannan?” Ta fada tana hawaye.

Aisha ta dafa ta ” kiyi hakuri, koma me nene, na tabbata akwai babban dalilin da yasa sukayi haka.”

” ki rungumi kaddararki, Allah yayi hayder shine mijinki, duk da dunbin masu sonki, Allah yasa akayi dashi, alhalin ba Ku kuka sasanta kanku ba, hakan na nuni akwai hikima mai girma a tare da wannan lamari. Duk mu nan waya taba kawo hakan a ransa? Ko da wasa, amma Allah cikin hikimarsa gashi ya tabbata. Just accept the true, and deal with it.” Yusra ta fara

Harararta hubby ta yi da kunburarrun idonta. ” don bake aka aurawa wannan karamin yaron ba, kya ce inyi hakuri mana!!!”

Rungume hubby Ummul khair ta yi tana murmushin maganar hubby ” na dade ina fatan haka ya kasance tsakaninki da hayder. Duk lokacin da kuke drama dinku, kuna burgeni, ina ma ina nan in muku zaman daki. Ko ba komai zan sha kallo.”

Da sauri hubby ta banbareta a jikinta, tana kai mata duka ” ban yafe miki ba kuwa, Muguwa.”

Gaba dayansu dariya suka sa. Ummul khair ta tabe fuska ” nama dauka zaki ce, zakimin tukuicin takwara.”

” in baki rufe min rubabben bakin kiba, zan fasa miki shi wallahi. Allah ya tsare ni, Bakinki ya sari guntun kashinki da haihuwa da wannan dan yaron.” Hubby ta fada tana huci

Hajja kolo dake faman dariyar su hubby, ta kalli hubby still tana dariya ” yaro man kaza, waya gaya miki namiji na kadan? Zako kisha mamaki.”

” barta kawai, ran da muka ganta da turtsi billi, tayi mana bayani ai.?” Ummul khair ta fada tana dariya

Ai da gudu tabar dakin tana dariya, saboda hubby da tayo kanta……..Dariya su ummu sulaim suke wa hubby da Ummul khair. ” na rasa yadda akayi, yarinyar nan ta rainani da yawa.” Hubby ta fada tana kwafa.+

” gaskiya Ummul khair ta fada. Kun matukar dace wa. Nima nayi missing din drama dinku wallahi. A ture batun wasa. He is the perfect match for u. Sai dai wannan karon sai kinyi a sannu, don nasan ba canzawa zakiyi ba, in ba haka ba kyaci na jaki, don karayrawyaki zai yi, daga ke se shi, ba mai karbarki.” Yusra ta fada tana dariya

Tsaki hubby ta ja. ” Allah ya kyauta me jiya tayi, ballan tana yau.”

” wan can karon an turguda kafa, wannan karon kam tabbas, in baki bi a hankali ba, karyaki za’a yi. Bana kusa balle in zo zaman jinya.” Aisha ta fada

” kun zo kumun jaje ne? Ko kunzo Ku kara bata min rai ne? Ku nuna min kuna bayan dan uwanku?” Hubby ta fada cikin bacin rai.

” sorry sister, ba nufin mu haka ba. Amma To tell u the true, we a happy for u.” Ummu sulaim ta fada

Hajja kolo dake kwasar dariyar drama dinsu,  ganin abun nasu bana kare bane, ga lokaci na ta tafiya. ta kalli hubby tare da mika mata hadin da tayi a wani bowl “gashi, ki shiga ki shafe jikinki da wannan.”

Hararar bowl din tayi, “banda na dazu kuma har da wani, nafa gaji gaskiya, dazu haka kikai ta dirzar min jiki, kamar kin samu kayan wanki, ni kam bazan sake ba,.”

” Aisha kira min Hajiya salwa a falon Hajiya Hauwa. ” ya kolo ta fada tana kallon Aisha

Karba tayi ta wuce toilet tana kun kuni. ” kunyi a banza, asarar kudi, da wani abun kukayi da yafi muku.” Ta shige toilet din.

” Zuma sai da wuta.” Humaira ta fada

Hajja kolo ta ce ” ai abubuwan hubby sai a hankali, Allah ya bashi ikon hakuri da ita.”

” miskili kafi mahaukaci ban haushi, shine dai dai da ita, dama kuma ai sun saba, wanda yaji wuya ya sake.” Aisha ta fada

” ya maganar walima, zaki samu zuwa ko ya zaa yi?” Yusra ta tambayi hubby bayan ta fito.

” I don’t no.” Ta fada

” yanzu kam ai sai da izinin mijinta, in ya yarda mai zai hanata zuwa, tunda duk na gida ne.” Hajja kolo ta fada

Yamutsa kumburarriyar fuskarta tayi ” lallai kam zaa rube a gida, in har sai na tambayi wannan yaron zan fita.”

Dariya sukayi Aisha ta ce ” da ko baki kyauta mana ba. Kin manta ke kikayi paganizing komai? Sannan ki ce bazaki ba? Meye a ciki don kin tambayeshi? Naga durkusawa wada ai ba gajiyawa bane.”

” kin san in ba kya wurin ba zaiyi  armashi ba.” Ummu sulaim ta fada

Banza hubby ta musu, don duk haushi suke bata. Don ta lura dadi ma sukaji an aura mata kanin bayanta.

” ki shirya don Allah, zan ma Hajiya magana, sai ta turo a daukeki.” Aisha ta fada tana fita daga dakin. Baya su yusra suka rufa mata, bayan sun ma su hubby sallama.

” ko Janeway zaa kawo, ban zuwa ko ina.” Ta fada tare da bin bayansu da harara.

Dariya humaira, da zata zauna da hubby tayi. ” aikin banza harara a duhu.”

Harara hubby ta aika mata. ” kema tashi ki bisu.”

Harararta ta rama. ” nima sai ki kawo Janeway ai, ki fita dani. Zama daram, har sai randa muka mikawa hayder matarsa.

Robar humra ta jefeta dashi.

Gwalo ta mata ” oho!!! Dai.”

                  ******************

Su hayder daga gidan su hubby,  mai furniture da mommy Hauwa ta hadasu dashi suka dauka, zuwa gidan da zasu zauna.

Duk kansu gidan ya musu kyau. Komai a tsare. Mai furniture ya gama aune aunensa yayi gaba. 

” don Allah hayder ka bani wuridin da kake yi, nima in fara.” Hafiz ya fada

Dariya sukayi, banda hayder da ya harari Hafiz. Dafa Hafiz  amir yayi. ” nafi kowa bukatar wuridin nan.”

” gaskiya you’re very lucky, you bit the whole kangiwa, in just few day’s. ” Hafiz omer ya fada

” gaskiya na maka murna, kun balain da cewa.” Daya friend dinsu ya fada

” ka bude mana hanya, nima kaga yanzu ba wanda zai ce min nayi yarinta, in na daddago aurena.” Hafiz omer ya fada tana murmushi.

” dama kai akawa auren ai da an huta, da tsince yaran jamaa da kake yi.” Alim ya fada yana dariya

Duka Hafiz omer ya kaima alim.

” ko ina sai kun nuna hali ne?” Junaid ya fada yana musu inkiya da ido, saboda basu kadai bane, akwai some friends da bazasu so susan sirrin su ba.

” bar dan banza, in masge shi.” Hafiz omer ya fada cikin wasa

Sai kusan magrib suka bar gidan. Sun tsaya tsara yadda komai zai kasan ce, ya bada tsari da ma’ana.

                ********************

Zaune suke a babban falon gidan Alhaji babba. Dau kacin iyayensu maza, suna wurin, sai Alhaji kawu da aminansa biyu.

Kowacce sanye cikin kaya na alfarma, tasha lullubi da manyan mayafi, sai kamshi daya cika falon tamkar shagon perfume.

Nasiha mai ratsa jiki, Alhaji babba ya musu, bayan ya gama Alhaji kawu ya amsa:—

Ku qudurce a ranku zaman ibada zakuje. Kuma ku sama ranku sabida Allah zaku zauna da mazajenku, ku yadda da qaddara kowane iri a cikin rayuwarku. In har kuka riqe haka to bazaku shiga shahun masu cewa ” duk wacce tace namiji ubane xata mutu marayainiya ba.

komai talaucin mijinki, ko kaushin halinsa,  ko kananun shekarunsa, ku rungumi abinku, ku yi ta mai addu’a, domin wata kamarshi ma take nema bata samu ba.

Ina dada Jan kunnenku, da  kusani, mijinki abin tausayi ne, abin lallashi ne, abin tarairaya ne, gareki domin shine mahadin rayuwar ki, kuma aljannarki.

Kuji  tsoran Allah, kar Ku zama masu

yawan buri da son duniya, kwata kwata duniyar kwana nawa ne, kina tabbacin xaki maimaita shekarun ki na baya? Sannan in kin sameta, kina da tabbacin lokacin da zaki moreta?

Duk halin da kike ciki a gidan mijinki ki godema Allah, domin akwai wacce ta fiki matsala, amma tana godiya ga Allah. Ki tuna Allah da kansa yace ” bayan tsanani sauqi na zuwa”

kuyi haquri da mazajenku, babu abunda haquri baya haifarwa. Musanman a wannan lokaci.  in kin tuna Allah da kansa yayi magana akan haquri. To ashe ko ba qaramin abu bane. In kikayi riqo dashi zaki samu riba mai tarin yawa. Domin Allah yana tare da mai haquri, Kuma haquri haskene. kuji tsoran Allah kar wayewa da ilimin boko, ko yawan shekarunki, yasa ki dinga ganinki dai dai da mijinki. Hakika shine gaba dake, Allah ne ya bashi wannan matsayin, don haka Ku kiyaye.

Allah ya muku albarka, ya Baku yaya na gari, ya sanya yalwa da tsoron Allah cikin rayuwarku.”

Gaba daya suka amsa da “amin” banda amare da jikinsu ya kara yin sanyi. Kowacce kukanta ne ya karu.

Sauran iyayen ma albarka suka sa musu. Sannan aka fito dasu, Kowacce aka nufi, motar da zaa kaita gidanta da ita. Ummul khair da Aisha, abuja aka nufa don kaisu dakunansu. Sai ummu sulaim kano, sai hubby malali.

Hubby tayi kuka kamar ranta zai fita, ga kewar su Aisha, sannan abun da take ganin kamar wasa, yana neman zama gaske, koma ya zama gaske.

Gida yayi kyau, ba karya, su mommy Hauwa sunyi matukar kokari, fiye ma da last time. Don komai sabo suka zuba mata, High quality dakunan bacci biyu da falo biyu. Sai hayder da ya gyara nashi bedroom din da babban falon gasa, sai small bedroom dake kasa. Fadin haduwar gidan hubby kauyan cine, ko a turai sai haka. Bikin yar gata da autan Hajiya, ai kuma kunsan baa magana.

Nasiha sosai su Hajiya salwa suka karawa hubby. Sannan suka tafi, a kabar hubby da kawayenta biyu. Humaira da Khadija.

Hira humaira da Khadija ke yi, hubby kam tana kashin gide, a hadadden Italian bed dinta. Tayi nisa cikin duniyar tunani.

” don Allah Ku tashi muje, mu dan zaga gidan, na dade banga gidan daya burgeni irin wannan ba.” Khadija ta fada, tana mikewa.

Tashi humaira tayi, dama zaman ya isheta, hannun hubby ta kamo. ” please tashi muje.” Mikewa tayi suka fito ko ina sun shiga a sama dakin hayder ne kawai suka samu a rufe. Suka sakko kasa, nan ma sun shiga ko ina, kafin suka yi branch a kitchen.

Katon kitchen ne, yaji cabinet, ka naurorin girki na zamani kala kala, wasu ma su humaira basu san anfaninsa ba. Fridge humaira ta bude, mai 2 door, ” na dade ina ganin irinsa a TV, yau gashi ina ganinsa a fili. Gaskiya kitchen din nan yafi ko ina kyau.”

Murmushi Khadija tayi. ” ai nima abun ya burgeni. Na dade banga kitchen daya burgeni irin wannan ba. Ai in a gidan nan nake, kullun ina nan.”

Kallon TV dake manne a bangon kitchen din tayi. ” Irina kam, ai kullun sai na babbaka girki.” Humaira ta fada.

” mayyar series ba!!! Balle ga TV a kitchen ai kam sai abunda Allah yayi.”

Dariya humaira tayi. ” masha Allah, komai yayi kyau. Allah ya bada zama lafiya, nan da 9month muzo suna.”

Tsaki hubby ta yi, tana maka mata harara, ta fita.

” komai barazanar Amarya, sai ansha manta.” Khadija ta fada tana dariya

Sallamar da sukaji  yasa su fitowa. Mata biyu ne, yan uwan  mommy Hauwa suka shigo da jerin akwatuna, na auren hubby.

1

Sai da suka jera mata su tsaf a dakinta. Sannan sukai mata sallama. Ganin mota free, ga dare ya fara yi yasa su humaira binsu. Tare da ma hubby fatan alkhairi.

               *******************

Mota kusan hudu suka shigo, harabar gidan. Su hayder ne da 6 best friends dinsa.

Sanye yake da kananan kaya. Blue Jens, sai White shirt mai gajeran hannu. Kafarsa sanye da sandal farare,. He look handsome.

Tsayawa sukayi suna kallon gidan, kowa da abunda yake sakawa. Hannu junaid ya mikawa hayder.

” dud Allah ya sanya, alkhairi ya baku zama lafiya, Ni kam ina daga nan.” Ya kalli su Hafiz ” I’m wetting for u hare.” Ya fada yana shigewa motarsa.

Dariyar Hafiz omer yayi ” kai kam Allah yayi matsoraci.”

” naji sai kun fito.” Junaid ya fada

A hankali suka taka zuwa kofar da zata sadasu da cikin gidan. A bakin kofar harder yayi burki, juyiwa yayi yana kallonsu. Hannu ya mika ma ashir dake rike da ledojin kaza, fresh fruit, yeghout, sai chocolate. Mika masa yayi, yana masa kallon tambaya.

Murmushin gefen baki hayder yayi ” na gode, Allah tashemu lafiya.”

Baki bude suka tsaya suna kallonsa.

Gira ya daga musu ” what?”

” kana nufin baza mu shiga ciki ba? Ko ya?” Amir ya fada cike da mamakin hayder.

” na hutar daku, sai da safe.” Hayder ya fada yana shigewa ciki, tare da murzawa kofarsa key.

” kam biji, biji iskar sanyi. Amma yaron nan yama raina mana hankali.”

Hafiz ya fada yana rike baki.

Dariya Hafiz omer ya saka, har yana rike ciki. Suma dole suka tayashi, don abun da haushi, da mamaki.

” in kun gama tsayuwar sai kuja, akwalar kafafunku, mu tafi.” Amir ya fada yana yin gaba.

” garama da bamu shiga ba, da da wane ido zamu kalli Anty hubby, a ce mune yan siyan baki? I wander how she feel, about all this thing. ” Hafiz ya fada

” its true, nima na dade ina wannan tunanin.” Alim ya fada

” abun da kamar wuya, ina imagining yadda wannan zaman zai kasan ce.” Ashir dake kokarin shiga motar da suka zo da ita ya fada.

Dariya Hafiz omer yayi ” ehhhimmm hayder ne fah!!! Muna nan daku, tsaf ze bi da ita.”

Junaid ne ya leko da kansa, ” zaku zo mu tafi? Ko zaku tsaya, shiga abinda bai shafe kuba.”

” I Wonder. ” ashir ya fada

Haka suka ja motocinsu kowa ya nufi makwancinsa.

Malan idi, ya maida get ya rufe.

A kan kunnen hubby suka shigo, tashi tayi, ta murza key a kofarta, tabar key din a jiki. Wanka tayi, tare da shirin bacci. Maganin da Khadija ta bata na ciwon kai, ta dauko ta bude fridge dake bedroom din, ta dauko faro. Tasha, adduoin kwanciya barci tayi, taja lallausan bargonta ta lullube, saboda sanyin ac. In no time bacci yayi gaba da ita. Saboda gajiya, ga rashin isashshen bacci.

Hayder kitchen ya wuce,  ajiye komai a muhallinsa. Sannan ya wuce bedroom din sa. Wanka yayi, tare da shiryawa cikin kayan bacci Mara sa nauyi. Baya tare da yunwa, don haka shima yabi lafiyar gado. Abubuwan da suka faru ne, suka fara dawo masa kamar majigi. Nasihar su Alhaji babba ta tsaya masa a rai. Sai tunowa da dan uwansa, da yayi. Ajiyar zuciya ya sauke, yana tuno ziyara ta karshe da dan uwan nasa ya kai masa, lokacin bai wuce saura sati uku kacal  yabar duniya ba. Magan ganun da sukayi a lokacin suka fara dawo masa, kalma by kalma. Hawaye suka fara zarya a kuncinsa. Adduar da ya saba ma dan uwan a duk lokacin da ya tunasa, yayi. Tare da kara gyara kwanciyarsa. Ya fada tunanin yadda zata kaya shida hubby…….A hankali ta fara bude idonta, da sauri ta mike, tana dauke da adduar tashi bacci a harshenta, da labbanta. Ganin gari har ya fara haske, toilet ta nufa da saurinta.1

Bayan ta idar da sallah, ta zauna tana azhkar, tare da adduoin da bata samu ta tashi cikin dare kamar yadda ta saba ba.

Kanta ta daura a jikin gadon ta fada duniyar tunanin. Bata san ta ina zata fara wannan zamanba. Abu daya ta Sani, bazata taba yadda wani abu ya shiga tsakaninta da wannan yaron ba. yan zuma ya ta kare da rainin hankalinsa, balle yaga gadon baccinta. After all he is her younger brother kuma brother din Yusuf. Ko da yake tasan ko giyar wake yasha shima ba zai tunkareta da wannan ba.

Murmushi tayi, tama tsaya tana bata hawayenta a banza. Zaman gidan nan bai sake da tana zama da brother dinta bane, sannan ta huta da damuwar masu cewa suna sonta, da kuma su gwaggo dake son tayi aure. Yanzu kunnenta shiru. Shi kuma zuwa gaba yana da right da zai yi aurensa kamar kowa, don ita dama ba auren bane a gabanta. Zama dashi tamkar Katanga ce da zata bata kariya ta fanni biyu. Masu sonta da iyayenta. Murmushi ta kara yi, ” I have my freedom, I will do what I want. “

Hayder kam yana dawowa masallaci, muraja’a ya zauna yi, bayan ya kammala azkhar. Sai to 8 tukun ya nufi toilet yayi wanka, ya shirya cikin wasu kananan kaya shirt da trouser masu kyau da asalin tsada. Ya gyara sumar kansa, mai matukar laushi da daukar ido. Kamshi kam baa magana, kamar wanda ya fito daga kamfanin turare.

Hajiya ya kira, suka gaisa, tana tambayarsa hubby, ya amsa da lafiyarta kalau, nasiha ta kara masa sosai, sannan sukayi sallama. Alhaji Jamal ya kira suka gaisa. Sannan ya nufi kitchen don samawa cikinsa abun da zai ci.

Gidan shiru bakajin karar komai, sai na naurar sanyaya daki, dake tashi. kamshin turaren wuta, da sanyin ac dake bada wani kamshi, mai sanyaya rai. Ya shaka yana lumshe ido. Don kamshin ya masa dadi.

Jin gidan shiru, ya tabbatar bata tashi ba, ruwa ya sa a kettle. Ledojin daya shigo dasu jiya ya dauko, kidney kebab ya juye a plate ya sa a microwave. Jin gina yayi da cabinet din kitchen din yana bin kitchen din da kallo, ya masa kyau matuka. Ina ma a ce shida nasrin ne da wannan hadadden gidan, sannan suna a matsayin maaurata. Gabansa ne ya fadi, tunowa da nasrin. Ya zataji in ta samu labarin aurensa? Yasan ba karamin tashin hankali zaayi da ita ba. Don yarinyar tana sonsa matuka, shima zuwa yanzu, ya tabbatar yana jin wani abu dangane da yarinyar.

Ajiyar zuciya ya sauke, abinda ke kara daga masa hankali, wane irin zama zasuyi shida hubby. Baya sonta, ya tabbatar itama haka, kawai biyayya ce, da rashin madafa. Zai bata lokaci yaga iya gudun ruwanta. Ta hakane, zai gane matsayin aurensu a gareta.

Karan kettle ne ya dawo dashi daga dogon tunanin daya tafi. Cup ya dauko ya hada black tea. French bread ya dakko yayi slicing dinsa, ya shafa butter, jerasu yayi a bread toster. Ya dauko trey kenan da zai jera break fast dinsa, yaji wani kamshi ya doki hancinsa. Duk da turarensa daya gauraye kitchen din bai hanashi jin kamshin daddadan turarenta ba.

A bakin kofa tayi burki. Tana sanye da doguwar riga, ta material da mayafinsa. Ba ko pawder a fuskarta, amma tayi kyau sosai, sai glowing fatarnan keyi. ” nan dama akafi auki.” Ta fada under her breath

Ya jita, sarai ya share. Sai da ya jera komai kan trey din, kafin ya dauka zai fito.

Ganin zai wuceta ba alamar zai kulata. Tayi murmushi cikin tsokana ” agric chicken ba gaisuwa.” Kallon sama da kasa ya mata ya wuce abinsa.

Murmushi tayi ” dani kake magana, a sannu zan gyarama zama yaro.” Ta wuce cikin kitchen din, don wata mahaukaciyar yunwa take ji. Tea ta hada mai kauri, ta zuba cake a plate ta haura falonta dake sama.

” good for u, Ashe ka gane, zamane na kowa yayi ta kansa.” Ta fada tana murmushi

“*******************

Ranar gaba daya cikin baki, yan ganin daki, hubby tayi shi. Sai yamma lis ta samu kanta. Hayder kam tun haduwarsu a kitchen da safe basu sake haduwa ba. Hakan ba karamin dadi ya karawa hubby ba.

Next day yan secondary school dinsu suka kawo musu ziyara, Nan ma tasha hidima. Sai dai taji dadin still yadda suka nuna mata respect. Ta dauka aurenta da hayder zai sa su kara rainata, sai taga sabanin haka. Mazan na tare da hayder a main falo. Matan suna falonta na kasa. Taji dadin wannan ziyara, don da yawansu tunda aka gama basu sake haduwa ba.

Sai to 6pm sannan suka tafi. Sai da ta kyara ko ina tsaf tukunna, ta nufi bedroom din ta, wanka tayi, ta shirya cikin English Ware’s Riga da skirt masu matukar kyau. Sun zauna a jikinta tsaf. Wayarta ta dauko tana son kiran gwaggo. Kusan 20miss calls ta gani, abin haushin tana kokarin kira, ta tuna, dazu suna waya da yusra kudinta ya kare. Datanta ta kunna don siyan kati true bank, but network is bad.

Hijabinta ta zunbula ta Zari 2k a bag dinta ta nufi falo. Direct falon hayder ta nufa, yana kashin gide a 3 sitter ya rufe idonsa kamar mai bacci.

Kamshin turarenta ya masa sallama. Bai ko motsa ba balle, ya nuna yaji shigowarta. Tunda ba sallama tayi masa ba.

” agric chicken. ” ta fada tana kallonsa, ko motsi be yi ba.

Bubbuga kujerar tayi kadan, ta kara daga murya “agric chicken.” Tsaki tayi ganin ya mata banza buga kujerar tayi da karfi, tare da ware murya ” agric chicken, kana jina fah!!!.”

Idonsa ya bude a hankali, ya sauke su a kanta. ” kanaji ina maka magana kamin banza, don wulakanci.” Ta fada tana harararsa.

Agogonsa ya kalla 6:35. Lokacin sallar magrib ya gabato. Mikewa yayi ya zauna da kyau. Ganin bashi da niyyar mata magana, haushi ya kara kamata. Sai aika masa da uwar harara take. Ta mika masa kudin ” recharge card nake son ka siyo min, mtn na 1500, airtel na 500.” Kallonta yayi ya kalli kudin da take mika masa.

” karba mana.” Ta fada cikin kaguwa, da jin haushi.

Mikewa yayi, har zai fita, ya dawo, ya karbi kudin, a aljihun gaban shirt dinsa ya saka ya fita.

Da harara ta rakashi. Ganin ya nufi sama yasa ta fito da sauri, ” agric chicken ina kuma zaka? Yanzufa zanyi anfani dashi, kake shigewa ciki.”

Ko waigota be yiba, ya haye abinsa. ” oh!!! Allah,” ta fada tana dafe goshi.

Sai da ya dauro alwala, ta gabanta ya wuce, tana kara jaddada masa, yanzufa take son anfani dashi. Kwafa yayi, bayan ya fita, tare da busar da iskar bakinsa, don ransa a bace yake, da yabi ta zuciya ba abinda zai hanasa mangareta, watan ita a matsayin Senior tazo ke nan, She want to boss him rawn. “A sannu zanyi maganinki” wata zuciyarsa ta fada.

Har akayi sallar ishai, ba hayder ba alamarsa. Hubby takaici kamar tayi yaya. Don ta samu ma wasu daga cikin wanda suka mata miss calls, sun sake kiranta.

Tana son magana da gwaggo. Still rashin kyan network ya hanata, samun damar siyan kati ta waya.

Hayder bai shigo gidan ba sai 9:24 lokacin har ta gaji da jira, ta kulle kofarta. Zagi kam yashashi. Don ranta ya baci sosai.

Kota kanta hayder be biba, shima shirin bacci yayi, yayi kwanciyarsa.

*****************

Hannu ta mika masa ” ina kudina?” Black tea dinsa ya ci gaba da sipping

” agric chicken, da gaske kazo da rainin hankali, taya zan aike ka, baka siyo, abinda na aike kan ba, sannan baka dawomin da kudina ba?”

Kallonta yayi. ” dan aikenki ne ni?” Ya fada yana kafeta da ido.

Gefe ta kauda kanta. ” wa zan aika, banda kai? Ko bayan kai akwai wani yarone a gidan?”

Smacking yayi, still yana kallonta. ” ba recharge card ba money, karfi yaci, in kina dashi kuma bisimilla ki kwata.”

Ido ta zaro. ” tabdijan!!! Kana neman fitina wallahi, kasan kudina ba zai yi ciwon kai ba, don seka biyasu.”

Wuceta yayi, ya fita a gidan.

Kwafa tayi, bedroom ta koma, ta sake dauko wasu kudin, taba malan idi ya siyo mata.

********************

Ta windon bedroom dinta ta leka don ganin abinda ke faruwa.

Tsaki taja. ” kuruci dangin hauka, wa annan ne zaa kira da masu hankali, har a dauki aure a basu.” Ta fada tana kwabe baki. Tun da dama naga ana kafe- kafe da aune -aune, nasan za’a rina. Tsayawa tayi tana kallon yadda suke buga basketball din, sai ife, ifensu daya karade gidan.

Kitchen ta nufa, ta daura abincin dare. Wanda tun zuwanta, daga ita sai malan idi maigadi take dafa abincinta, sai ko in sunyi baki. Hayder da kansa yake dafa abinda zai ci, baya damuwa da rashin sa masa abinci da takeyi. In takai abinci falonsa to su junaid ne sukazo, ko bakinsa maza, a nan kam tana kokari, don duk abunka in kazo baxaka gane irin zaman da sukeyi ba. Abinci kuwa, zata dafa taba bako, batajin kyiwar girki, in ba lokacin cin abinci kazo ba, zata kawo maka juice, ruwa, da snacks. Wannan koyarwar gwaggo ne. Bata yadda bako yazo ya tafi baisha ko ruwa ba. In ma yaki sha. Ta dinga mita, har sai mutun ya kurba. A cewarta mugun bako ne, zai zo ka kawo masa abu yaki ci, ko sha.

Sai kusan magrib suka bar gidan. Yauma 9 ta wuce taji dirin bike din hayder alamar ya dawo kenan. Kwanciyarta ta gyara tare da lumshe idonta. Tana jin kewar Yusuf. Tabbas mutuwa mai tonon asiri, da yanzu tana tare da masoyinta, mutuwa ta mata yankan kauna, a dai dai lokacin da tafi kowa bukatarsa. Ya tafi ya barta, cikin gwagwarmayar rayuwa.

*****************

Yau kwana biyar ke nan, da tarewar hubby. Tana zaune a falonta na kasa. Indian series take kallo a tashar zee world.

Nocking din da taji, yasa ta mikewa, ta zura hijab dinta dake kusa da ita.

Hajiya kaka, da samira ta gani. Cikin faraa ta tarbesu, tare da masu iznin shigowa.

Kitchen ta nufa don kawo musu abin motsa baki,. Da kallo Anty samira kebin falon. Iyakar haduwa ya hadu. Gaba daya tunda ta shigo daga get, jikinta yayi sanyi, ga wani kishin hubby data ji ya kara darsuwa a zuciyarta. Ta rasa me yasa yarinyar ke darata a komai. Yadda take jin labarin haduwar gidan, har yafi yanda ake labarinsa.

Hajiya kaka ta rike baki, tana kallon Anty samira. ” aljannar duniya, ki ce Hajiya ta tatse Jamal tas. Don wannan dukiya da aka zuba a nan, yafi karfin arzikin Munir.”

” ehemmm!!!! Kema kya fada, duk anyi ne don muji haushi.” Anty samira ta fada cike da kyashi

” sunyi ta banza kuwa, don baa taba canzawa tuwo suna, har gobe a tuwonsa zai zauna.” Hajiya kaka ta fada

Hubby ce ta shigo da babban trey dauke da cups juice, water, cin cin da cake. Ajiyewa tayi a center table din dake gabansu. Sannan ta zauna. Hajiya kaka ta fara gaisarwa cikin ladabi, sannan ta gaishe da Anty samira.

Hajiya kaka ce ta kalli hubby, duk da katon hijab din da take sanye dashi, bazai hanaka ganin kyanta ba. Fuskar nan sai walkiya da daukar ido take, ta kara haske tayi kyau. ” masha Allah, yarinya, ke kam kakarki ta yanke saka, na dauka zanzo in ganki, cikin damuwa, an hadaki da kanin bayanki, sai naga sabanin haka. Bako jin nauyi kinyi tarayya da yaya, kuma kina yi da kani, kanin ma na bayanki. Kinyi kokari matuka.”

” me ko zai dameta, ta samu santalelen yaro, ana tsotseshi.” Samira ta amshe

Gwaggo ta kara da ” koda yake haka ne, kin san in mutun yayi kwantai, koma wa yazo ba damuwarsa bane, shidai ya jishi dakin aure kawai. Ni kam Allah ya tarfa min alam nasharaha.”

Hubby kam kanta ta sunkuyar, zuciyarta na tafasa. Bawai dama ta manta abinda Anty samira ta mata bane, kawai dai ganin ita ta tako har inda take, bai kamata ta wulakanta taba. Sannan tasan tsaf sune, Ummul aba’ is na aurenta da hayder. Darajar sun tako har gidanta, da darajar furfura, shi yasa ta daga musu kafa. Koba komai suna sama da ita.

” ai kam na tausayawa yaron nan, da yarintarka, a dauki uwar mata a hadaka da ita. Ban taba ganin irin wannan lamari ba. Koda yake sunfi kusa.”

Bataji karar shigowar power bike din saba. Sallamarsa kawai sukaji. A hankali ya tako zuwa cikin falon. Sanye yake da lallausan yadi fari, half jamfa mai gajeren hannu, yayi kyau sosai, ga kamshi na musamman dake tashi a jikinsa.

Kujerar kusa da hubby ya zauna tare da daura kafa daya kan daya, ya jingina hannunsa mai dauke da phone dinsa a hannun kugerar, daya hannun yana shafa sagensa, zuwa gemunsa. Idonsa kar akan su Anty samira.

” babiba.” Ya fada da wata irin murya daya sa hubby saurin dagowa ta kalleshi, cike da mamaki. Lokaci daya ya canza mata kamar ba hayder din data Sani ba. ” go inside. ” ya fada yana mata wani irin kallo. Bata san lokacin da ta mike ta nufi stairs ba.

” hayder wane irin abu ne haka? Bako gaisuwa, ka zauna zaka nuna mana kai ka zama mai gida, mai bada umurni? Ko ni baka gaishe ni ba, ai ka gaida Hajiya kaka ko?” Anty samira ta fada cike da jin haushi.

Kallonta yayi,tare da murmushin gefen baki. “A addinance sallama ya kamata nayi, kuma nayi dazan shigo. Duk da ba dole bace, amma amsata dole ne, cikinku waya amsa min sallamar? Babu?, kuna nan kuna cin zarafin yar mutane.”

Cikin fusata Anty samira ta mike ” in kana rashin mutuncinka karka yadda ka gangaro kaina! Don naga alamar kanka na rawa.?

Murmushi yayi mai sauti ” duk wanda ya siya, dole a siyar masa, bazan dau rashin hankali a gidana ba. Ba yadda zaa yi, Ku tako har gidanta,. sannan kuci zarafinta. In a da kunyi, to ni bazan dauka ba, matukar ba zumunci zai kawo mutun ba, to bana nemansa a gidana, in ba haka ba tamuce ni dashi.”

Hajiya kaka ce ta fara sallalami ” ta tabbata! Ta tabbata! Wallahi ta tabbata. Kaima har an wanke an baka? Yo in ba an wanke an baka ba, a gabana bako kunya da ganin darajar furfura, kake kunfar baki don an taba tsohuwar matarka. Ina abun yake? Kake wani kafafa…”naji kina baki taba ganin aure, irin namu ba? Kin manta da auren manzo Allah, Annabi Muhammad SAW da Nana Khadija?  Yana dan shekara 25 ita tana 40years.  aurenta biyu, da yara biyar. Kafin ta auri Annabi Muhammad SAW. Kin ga ashe ba sabon abu bane, koyine da manzon Allah SAW. After all ke ce silar hakan, banga kuma dalilin zuwa ki tozartata ba, bayan ke kika ja, abinda yasa aka aura mata yaron.”+

Hajiya kaka da ranta ke bace, ya zaayi kamar hayder ya zauna yana gaya mata magana, hankalinsa kwance, kamar mai magana da saansa. ” baka cewa ni na daura auren, mara kunyan banza.”

” ko baki daura ba, ai kinyi sila. Ke daba dan darajar zamowarki kaka ba ta wani bangaren kuma furfurar da kike ikirari, da koda kudi aka ce ki tako kafarki gidannan bazaki fara ba. So leave us in peace. “

” ka rika wallahi, hayder Hajiya kaka kake ciwa fuska? Yanzu zaka iya yiwa Hajiya babba haka? Saboda mun tako gidanka, maganar nan bazata tsaya a nan ba, sai na kai kararka, ai gaba ma da gabanta. ” samira ta fada cikin bacin rai.

” nan kika fi auki dama, an girma baa san an girma ba. Karki fasa kai karar tawa. Amma ki sani bama keba, duk wanda ya kara yunkurin cin fuskar matata, ko da dai dai da bakar magana ne, he will answer to me.”

Takaici ne, ya kume Anty samira, tana jin labarin rashin mutuncinsa, amma bata taba tsammanin yakai haka ba. Don ko da tana gida, ba wani shiri sukeyi ba. Kamar yadda bayayi da mahaifiyarsu, haka ita ma, Karin jin haushin yadda yake treating din mamanta, yasa bata shiga harkarsa.

Hajiya kaka ta kalla. ” tashi muje, kafin ya rufemu da duka kuma, don naga abun nasa ya yi yawa.’

Mikewa Hajiya kaka ta yi, Cike da sanyin jiki, ga takaicin hayder, a cikin jikokin nata ma, shi bai kai saan dan autan subama. Still yana zaune kafa daya kan daya, sai faman shafa sajensa, yake da kyawawan zara zaran yatsunsa, farare Sol dasu. Kai ka rantse maganar arziki yake furtawa, yadda yake maganar cikin yanga da Jan aji. Idonsa kar a kansu.

A fusace suka bar gidan. Tsaki yaja,. Tunowa da drama daya tarar anayi a main house. Abdul Karim da Anty samira, da kyar aka janyeshi yana sai ya mata dukan tsiya, sanadinta tasa ya rasa muradin zuciyarsa. Sai a nan ma suka ji, wasu kulle kullen data hada duk don taga auren hubby da Abdul Karim bai tabbata ba. Da badan shi, da ya janye Abdul Karim ba, da abun ba karamin kazanta zai yiba. Don su Hajiya sun kasa, gashi ba maza a gidan. Cikin ikon Allah sai gashi ya shigo.

Ya tausayawa Abdul Karim, duk da shima tawani fannin yana da nashi laifin. Mikewa yayi ya nufi upstairs, don dama wani documents yazo dauka.

A last step suka hadu da hubby dake rungume da hannu, cikin damuwa da bacin rai. Duk abinda suka fada kan kunnenta, shine dai bata ji mai yake fada musu ba, saboda a cikin natsuwa yake maganarsa, amma daga amsar da suke bashi, tasan ba maganar arziki ba ce. Babban abinda ya kara kona ranta, da yace ta tafi, ita kuma sokuwa, har dabin maganarsa, sai bayan ta tashin ta dinga jin haushin kanta.

Wuceta ya so yayi, tai saurin tare hanyar, kallonta yayi, ya koma ya jingina da jikin karfen benen, ya nade hannayensa duka biyu a kirjinsa. Ya zuba mata fararen idanuwansa.

” meye sunan abunda kayi? ” ta tambaya tana kallon hannayensa dake sarke a juna. Ganin bashi da alamar amsa mata yasa ta kara jin haushi, don ta tsani tayi magana ya mata banza, gashi ta lura halayyarsa ke nan.

” abunda kayi, baka kyauta ba, koba komai sune gaba damu, dole muyi hakuri da duk abunda zasu fada mara dadi. Karka manta Hajiya kaka tamkar uwa take gasu Hajiya. Please don’t do such thing again. “

Wani kallo ya mata data kasa tantance na menene. Ganin zai bangajeta, yasa tai saurin bashi hanya, da ido ta bishi har ya shige bedroom dinsa. Ajiyar zuciya ta sauke. ” oh!!! Allah wannan wane irin yaro ne. Ke nan rashin mutuncin nasa kowa ma bai bari ba kenan.? Maganar ummu khulsum ce ta dawo mata. ” rashin mutuncin hayder sai dai in baka shiga gonarsa ba, amma komai girmanka, bazai daga maka kafa ba. Don haka kibi a hankali, kika fusata shi, wallahi zaki gane baki da wayau, abin da ya miki da, nafila ne dana yanzu, don yanzu yana ganin kina kasanshi, matsayin matarsa, bazaku kwashe da dadi ba. Don haka ki kiyaye, Ku zauna lafiya, banda raini.”  Tana kokarin tuno da ansar data ba ummu khulsum a lokacin. ya fito, ganinta yayi still a wurin. Wuceta yayi ya sauka daga steps din, cikin gudu- gudu, sauri – sauri. Hubby ji tayi kamar ta tade kafar tasa ya fadi.

Ganin tsayuwar bazai mata ba, ta nufi falo, ta dauki trey din data kawowa su Anty samira ta nufi kitchen dashi.

                 ******************

Tana kitchen taji shigowar mota, a tunaninta baki su kayi. Hayder ne ya shigo kallo daya ya mata ya nufi kofar da zata sada ka da waje, ya bude tare dama malan idi bismillah. Malan idi ne ya shigo da wasu manyan ledoji a hannunsa. Gaisheta yayi cike da ladabi, sannan ya ajiye. Haka ya dinga shigo da ledoji da kwalaye har ya gama, sannan ya kalli hayder dake rike da cup din juice ” oga an gama.” Hannu ya daga masa, cikin sauri yabar kitchen din.

Kallonsa tayi, takai kallonta ga shirgin kayan da malan  idi ya shigo dashi. Juyawa tayi ta ci gaba da aikinta. Bebi ta kanta ba, ya fara ciccire ko wanne, yana sa su a muhallinsu. Nama ma mahaka ya jera su tsaf a deep freezer. Anyi shilling dinsu a kananan mazubi da white rapper.  Juice, drinks, da bottle water duk ya jerasu a store.

Duk abinda yake yi tana jinsa, bata ko kalli inda yake ba. ” in kin duba, akwai abunda babu let me know. ” ya fada yana kokarin barin kitchen din.

” wai kai baka iya gaisuwa bane?” Dawowa yayi da baya, yana kare mata kallo. Harararsa tayi ” wannan kallonfa?” Hada rai yayi cikin miryarsa mai kama da an masa dole ya ce ” ni dake waya kamata ya gaishe da wani.?

Baki ta bude cike da mamakisa, ta amsa masa da ” kai ya kamata ka gaisheni, after all kai kazo ka sameni, kaga kenan kai zaka gaisheni.”

” sau nawa kika shigo kitchen din nan, da safe kika ganni, kika gaisheni?”

” taya zanyi dama in gaisheka? Karami ai shike gaida babba.”

Smacking yayi, tare da shafa sajensa.  Idonsa kar cikin nata. ” shi yasa ai ban gaisheki ba, kin san yanzu abin ya juye. Ko da ban gaishe kiba, balle yanzu, da nake samanki.” Ya fada yana gwada mata da hannunsa, daya daga a saman kanta.

” Allah ya kiyaye, in zamo a kasan ka, in mafarki kake, gara ka farka, har gobe ina nan a matsayin yayarka. Dole kuma ka bani wannan girman.” Ta fada cikin bacin rai

” keep dreaming. ” ya fada yana barin kitchen din.

” kam bala’i, me wannan yaron yake nufi? Kar dai auren da yake ganin an daura musu, yasa kansa ke rawa. Lallai kam zai sha mamamki.”

Haka har ta gama aikinta tana tunanin maganarsa.

Ta idar da sallar ishai ke nan tana ninke hijab din da tayi salla dashi. Ya shigo dakin tare da sallama.

Gabanta ne yayi mugun faduwa, don tsawon sati dayan nan da kawota gidan, ko sau daya bai taba gigin shigowa dakinta ba. Hasalima da daddare  kafin ya dawo ta rufe dakinta. Da kyar ta hadiye yawun bakinta tana binsa da kallo. ” lafiya malan? Meya shigo dakai nan.?

Dakin yabi da kallo, komai tsaf, gwanin shaawa, ga kamshi mai dadi na tashi. Lallai su mommy Hauwa sun kashe money, ya fada a ransa. Don shi kansa dakin ya burgeshi sosai.

” me kike tunanin zai kawoni dakinki?” Ya fada yana isa wurin dressing mirror dinta.

” koma menene, ka gaggauta ficewa a dakin nan. Kuma ya zama fist and last da zaka shigomin daki.”

” really.? ” ya fada yana daddaga turarukan dake wurin, yana gani, tare da kaiwa hancinsa ya shinshina ya ajiye, ya dauki wani.

Tsayawa kawai tayi, tana kallon ikon Allah Don abun nasa ya fara daure mata kai. Kirjinta sai dukan tara tara yake, don bata san da wadda yazo ba.

” gobe Hajiya zata aiko miki da yar aiki, in kuma bakya bukata ki kira, ki shaida mata.” Ya fada

Ajiyar zuciya ta yi, tare da ajiye hijab din a mazauninsa.

” OK, naji sai da safe.” Ta fada tana nuna masa kofa.

Juyowa yayi ya jingina da jikin dresser din hannunsa duka biyu dafe da gefe- da gefen dressen. ” I will travel tomorrow. ” ya fada idonsa a kanta.

” Allah kiyaye hanya.” Ta fada, still tana nuna masa kofa.

Kudi ya Ciro a aljihun rigarsa. Bunch din 1k ya ajiye mata. Ya juya zai fita. Sunansa data kira yasa ya juyo, yana kallonta.

Kudin ta dauka, ta nufi inda yake tsaye. Mika masa tayi ” I don’t need you’re money. ” kudin ya kalla, sannan ya kalleta, juyawa yayi yatafi ya barta da kudin a hannu. Kiransa ta fara, amma ko waigowa beyi ba. Tsaki ta ja, tare da komawa ciki ta murzawa kofarta key.

                 ****************

Washe gari, jirginsu hayder ya tashi zuwa Paris, shida Hafiz, da amir.

Hajiya ta kawowa hubby yar aiki, mai suna Mariya, ta ji dadi sosai, don dama zaman gidan ya fara isarta. Musamman yanzu da yan ganin daki suka fara sauki.

Kwanan hayder biyar da tafiya, hubby ta koma islamiyarta. Ko da ta gayawa hajiya maganar islamiyya, tambayarta tayi hayder ya sani? Ta  ce mata eh!! Kawai. Ce werta no need da zata tsaya har sai ta tambayi hayder, No way.

Islamiyyar daga 10 to 12pm, kafin ta tafi, sun gama komai na gyaran gida, tayi saa Mariya bata da kyuiwa, akwai aiki. Tana dawowa zata daura musu lunch. Dadinta ba nisa tsakaninta da school din.

                  *****************

Zaman gidan Alhaji Jamal yanzu ya sauya salo, duk yadda yaso yaga ya sasanta iyalan nasa, abun ya faskara. Don haka ya kai kararsu wurin Alhaji babba.

Alhaji babba da kansa ya tako har gidan dan nasa. Nasiha sosai ya musu, tare da rokonsu dasu manta duk wani abu daya faru, su yafewa juna.

Sannan ya shaida musu ya ba Abdul Karim da Abdul fatta nan da 2month kowannensu ya fitar da Matar aure.

Hakan ne ya kawo dan sassauci. Musamman tsakanin Hajiya da Mmn samira. Sai dai Hajiya ta Riga tayiwa kanta alkawarin bazata taba sake mata kamar da ba. don an shata ta warke. Kuma maciji baya sarin mumini sau biyu a rami daya. Yanzu tasan yadda zata zauna da kowaccensu. Dama Mmn Yusuf kowa yasan inda ya ajiye dan uwansa.

                ******************

Satinsu hayder biyu, suka dawo cike da nasarorin abinda ya kaisu. Sunyi saukar safe. Main house ya fara isa yaga Hajiyansa kafin ya nufi gida.

Ko da ya shigo gidan, bai ga motar hubby ba, bai kawo komai a ransa ba. Malan idi ne ya shigar masa da kayansa, Tare da masa sannu da zuwa.

Karar TV da yaji a falon hubby na kasa yasa shi nufar can. Cikin sallama ya shiga. Mariya dake zaune a kan carpet tana kallon Hausa film. Ta amsa tare da gaisheshi cikin Ladabi. Ta dauka bako hubby tayi, don bata san shiba. Ta ce ” Anty bata nan.” Kallonta yayi yana juya maganar a ransa.

Cikin muryarsa mai dadi, cike da muskilanci ga hausar sai a slow ya ce ” ina taje.”

” ta tafi makaranta, amma ta kusa dawowa.”

” makaranta, makaranta, ya fara juya Kalmar a bakinsa, kamar mai son gano maanarta.”

Jin yana ambatar makaranta, Mariya ta dauka bai gane bane, don taji hausar tasa wani iri, da ganinsa kuma ba bahaushe bane. Ta ce ” makarantar islamiyya, nan kusa ne, ba nisa, yanzu zata dawo.” Wucewa tayi da sauri, ita a dole zata kawowa bako ruwa, kamar yadda hubby ta umurceta in anyi baki.

Ranshi a bace ya haura sama. lokaci yayi da zai takawa yarinyar nan burki. Yan zune ya kamata tasan waye Aliyu hayder…………..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *