DAN ADAM CHAPTER 12
ABUJA Ranar da ya kama na yini da(mother’s day) ranar akayi sanya ankon atamfa mai fari da bulu. Sunyi kyau matuk’a. Gaba daya abin ya burge, sai bayan magriba kowa ya soma shirin tafiya wajen fatin. Abin nasu ya yi kyau matuka, su Ummi a gida aka barsu rainon yara, har saida suka yi hira suka gaji suka soma gyangyadawa sannan suka soma dawowa. Alokacin suka koma dakinsu suka kwanta. Washegari kuwa tun asuba basu koma bacci ba, suna kicin suna dirkar aiki na hada karin kumallo. Sai wajejan tara suka kammala komai suka mik’amusu. Wajejan sha daya na safe sunyi wankansu tsaf, Aisha ta hada Ummi da wankin Tahir. Haka ta kar6a don ba ma su yawa bane sosai. Wajen garden inda ta ga anan suke wanki da shanya ta zagaya ta soma yi. Tare suke da Amina suna hira inda Amina ke labartamata batun aurenta da ya taho, Sa’a ta zo ta sanarwa Amina kiran Hajiya Mama. Wajen ya rage Ummi kadai cike da tunanin duniya. To ita meyasa bata ta6a jin son wani ba ne? Ga dai maneman suna tururun zuwa har da yaran manyan dake layin makarantarsu masu son ta kulasu saidai ko kad’an babu wanda ta ta6a saurara, maganar Antinta ta fad’omata a rai. “Kema auren nan ya dace kiyi Ummi, shi kadai ne jin dadinki, ki tara zuri’ar kanki.” Abinda tace mata kenan a wannan hirar da sukayi. Ta girgiza kai tana duban wani dan lilo dake a wurin. ‘Babu wanda nake so a raina yanzu Anti.’ Ta ayyana a ranta. Haka ta k’arasa wankin ta mik’e ta nufi wajen shanya, tana cikin shanyar ne ta ji sallamar mutum agefenta. Da sauri ta dubi wajen jin muryar namiji. Ta gane ko wanene duk da batasan sunansa ba, amman cikin bak’in Adamawa ya ke. Kana ganinsa shima kaga bafulatanin usuli, ta gaisheshi ya amsa da harshensa mai sirkin yare biyu(Hausa fulani). “Sannu, ina daga can ina ganinki tun dazu ai, ya sunanki ne?” Mamaki karara ya bayyana saman fuskarta, baiyi kama da saurayin arziki ba, yafi yin kalar ‘yan duniya. Ta k’ara kare kirjinta da ya zubawa ido don kuwa doguwar rigar jallabiya ce jikinta kusan duk ta jik’e agarin wanki. Murya na rawa batare da ta k’ara kallonsa ba ta amsa. “Ummi.” Ya lura da abinda ta yi din sai kawai ya yi murmushin duniyanci ya shafi ha6ansa. “Wow, kina da suna mai dadi fa. Ni sunana Kabir but you can call me KB. Ke ‘yar uwar su Daddy na Baraka ce?” Ta girgiza kai don ta k’osa ya bar wajen. “Aa, ni ‘yar aiki ce.” Ya zaro ido da mamaki. “Yar aiki? Kike da wannan kyan?” Ya ta6e baki “Gaskiyar magana bebi kin fi karfin zama yar aiki. Idan za ki ban had’in kai to zakiji dadin rayuwa son ranki.” “Innalillahi…” Ta karashe a fili. Zaiyi magana, Amina ta katse hirar ta hanyar gaisheshi. Suka dubeta don basusan ta iso ba, ya amsa ba don yaso zuwannata ba, ya wani tamke fuska gami da fadin. “Sai wani time din bebi, zan nemeki.” Daga haka ya fice, da sauri Amina ta nufota gami da rike kafadarta a tsorace. “Mene hadinki da Kb? Kinsan kuwa ko wanene?” Itama Ummi duk sai ta k’ara rud’ewa. “Wallahi shi yazo nan yanamin magana.” Ta zayyanemata yanda sukayi. Amina ta numfasa. “Nagode Allah da ba ki ce komai bayan wannan ba, ki yi kokarin nisantarsa, yaron dan iska ne fiye da tsammaninki. Akwai sadda ya ta6a zuwa gida Hajiya Mama basunan sai ni kadai, wallahi Allah ne kawai ya kwaceni daga hannunsa, ya so 6atamin rayuwa. Ki kiyaye Ummi, nasan halinki, ki k’ara akan wanda nasanki na tsare mutunci.” Ummi ta dubeta. “In sha Allah Anti zan kiyaye.” Ta taimakamata wajen k’arasa shanyar sannan suka nufi ciki. Da gudu Sa’a dake la6e ta koma ciki. Kai tsaye dakinsu ta nufa kicin ta nufa inda Binta ke goge-goge ta fesamata yanda Kb da Ummi sukayi harma da nasihar Amina gareta. Binta ta ja tsaki. “Banza da ita, ta samu damar da muke nema ta yi watsi da shi, ji dai yanda ya nemeki sau d’aya kuma ya dawo ya juyamaki baya sai zagi idan ya zo kamar gidan ubansa.” Sa’a ta yi kwafa cike da jin takaici. “Bari kawai, ni su Ummin ma sunfi ban takaici su basu yarda ba masu tsoron Allah. Gulma ce dai, ta ciki na ciki.” Binta ta ajiye tsumman hannunta. “Ke, ga hanyar samun kudi wajen Kb. Mezai hana tunda ya ganta ya kyasa, mu kai mishi ita kinga kuwa ba karamin kud’i zai bamu ba.” Sa’a ta yi shiru tana nazari, tasan Kb akwai sakin aljihu musamman akan mace. Ta dubi Binta suka kyalkyale da dariya sannan suka cafke. “Shegiya, kina ja wallahi. Bari zan sameshi a 6oye mu ji yanda zaayi.” Cewar Sa’a, Binta ta jinjina kai cikin gamsuwa. Da yamma kuwa duk ana ciki ana shan kid’a da rawa kasancewar an daura aure kuma ba wani(event) da suka shirya zasuyi sai dinner wanda Ango ya shirya kayansa. Sa’a ta yi nasarar ganin Kb a farfajiyar gidan yana amsa waya can gefe, da sauri ta karasa wajensa tana fadin. “Yalla6ai.” Ganinta yasa ya ja guntun tsaki ya daure fuska, saida ya kammala waya ita kuwa na waige-waige bata hangi wani mai ganinsu ba. “Lafiya?” Ta dubeshi tanq murmushi. “Lafiya kalau, daman wata magana na zo maka da ita.” Ya daga kafada. “Ta mecece?” “Dazu na ganka kana magana da Ummi, nasan kuma ka kyasa dw ita ne. Idan babu damuwa ni zan kawomaka Ummi, idan har ka yarda za ka biyani.” Wani sanyi ya ji a ransa, sai lokacin ya sakarmata wani shu’umin murmushi ya sosa kai yana duban farfajiyar gidan, babu wani mai kallonsu sai tsirarun ma’ikatan gidan dake harkokin gabansu. “Idan kudi ne, kinsan bani da matsala da su. Kedai ki cika alkawari.” Ya kara dubanta fuska babu wasa. “Kada kuma ki kawomin rainin hankali idan ba haka ba kinsan sauran. Ki zauna cikin shiri, yau da zarar kowa ya tafi wajen(party) ki yi yanda zakiyi ki kawomin ita sashenmu, zan iya biyanki ko nawa ne.” Daga haka ya fiddo dubu biyu ya damk’a a hannunta. “Ga wannan ki sanyawa wayarki kati, ai kina da lambata ko?” Ta gyada kai farinciki ya cikata ganin dubu biyu, wanda idan ta yi wayasan ko nawa zai bata. “Eh akwai.” Daga haka suka yi sallama fuskar kowanne a sake. Faruk dake daga sama yana dubansu ta windo, mamaki ya cikashi, shi yasan wanene Kb, yasan kuma illarsa ga diya mace. Babban abin daure kan menene hadinsa da Sa’a? Ko har ita din ma akwai abu tsakaninsu? Ya girgiza kai cike da jin tsanar Sa’ar domin ita ta bada fuska. Ya juya ya koma falo cikin yan uwansa kusan sa’anninsa kuma bak’in Adamawa aka cigaba da hira kafin duk su fito waje don shan iska. Misalin takwas duk an soma tafiya wajen party da zaayi a Nicon, su Ummi dai na tsaye a farfajiyar wajen sai kallon kwalliya sukeyi. Kowacce ka gani ji takeyi da kanta, duban kanta takeyi a had’add’iya. Wajen sai kamshi kakeji, matasan ma kuwa da alama har da samarin wasu cikin yanmatan. Duk wadannan ba su suka damu Ummi ba face ta inda zata ga 6ullowar Faruk. Shi kadai zuciyarta ta kwadaitu da gani batare da tasan tak’amaiman dalili ba. Daga gefensu ta ji Ikram na balbale Ihsan da fad’a. “Wallahi zakiyi asarar fatin yau matukar kika kafe sai tare da Yaya Faruk za ki je, idan ma kin shirya tafiya gwara tun wuri ki taho mu tafi don wallahi a yanda nasa halin Yaya Faruk zai iya cewa ya fasa. Mun tafi na daukarmaki komai a waya.” Daga haka ta yi gaba. Ihsan ta yi saroro, ganin dai dagaske Ikram take yasa ta bin bayanta da gudu-gudu, abin sai ma ya bawa Amina da Ummi dariya. “Wallahi yanzu lamuran Ihsan dariya sukeban.” Cewar Amina. Ummi ta ta6e baki. “Ato, tunda ta maida kanta wata tsiya ba.” Saida suka ga tafiyar kowa amma basu ga na Faruk ba. Hankalin Ummi ya tashi, ranta ya sosu, ta so kwarai ta ga tafiyarsa, ta kwadaitu matuka da ganin kalar wankansa. Haka suka koma falon, iyayen daga Hajiya Babba sai Inna da wasu dattijai mata yan Adamawa ya rage, suna sama, suka tattara komai sannan suka wuce 6angarensu. Suna zaune anan sai ga Sa’a ta shigo. “Ummi, ki zo Adnan na nemanki.” Da mamaki ta dubi Amina. “Na dauka Adnan ya wuce.” “Tabbas nima naga shigarsu mota.” Sa’a ta yi yak’e. “Dawowa ya yi, wai ki zo sak’o zai ba ki daga Mami.” Basuyi tunanin komai ba don babu wanda ya kawo Sa’a zatayi hakan cikinsu, Ummi ta mike da sauri yana gyara zaman daurin dankwalinta na atamfa, don sauri ko hijab bata tsaya sanyawa ba ta zura takalmi tana fadin. “Bari naje.” Amina ta kishingida tana fadin. “Wash!” Gami da lumshe ido, Sa’a ta kunce gefen zaninta ta yi amfani da hodar da Kb ya bata ta wuce sadaf-sadaf ga Amina ta shek’a mata a hanci, Amina kafin ta yi wani yunkuri bacci ya sureta. Da sauri Sa’a ta bi bayan Ummi. Ita kuwa Ummi kai tsaye waje ta nufa saidai bata ga mota ba, hakan yasa ta zuwa wajen fakin motoci nan ma bata ga mota ba sai guda daya, da alama da mutum ciki sakamakon kidan da ke dan tashi amma zuwanta aka kashe. Zata nufi wajen Sa’a ta karaso tana kiranta. Ta tsaya gami da juyowa. ‘Yauwa ina Adnan din?” Sa’a ta dubeta. “Yanzu na ganshi ya nufi sashensu, shima nemanki yakeyi.” Ummi ta jinjina kai. “Munyi sa6ani kenan, bari na je.” Da sauri ta nufi hanyar sashensu Adnan, Sa’a ta saki dariya yanda ba zata ji ba, ta bi bayanta. “Adnan?” Ya furta a hankali, a iyakar saninsa Adnan baya nan sai Kb wanda ya bari yana shiryawa amma don tabbatarwa ya dauki waya ya dannawa Adnan kira, koda ya dauka ya tabbatar mishi yana farfajiyar wajen taron. Ya tsaya yana tunani, kada dai cutar Ummi zasuyi? “Oh No!” Ya fad’a da karfi sannan ya fito daga motar cikin zafin nama. Ita kuwa Ummi kai tsaye saman ta nufa ta hau kwankwasawa, aka budemata, ana budeww daga bayanta ta ji an hankadata cikin dakin sai jikin KB. Kafin ta kai ga duban wanda ya hankad’atan ta ji an rufe k’ofar har da sanya muk’ulli. A gigice ta d’ago tana fadin. “Adn…” Maganar ta makale a fatar bakinta ganin Kb daga shi sai gajeran wando. Fisge jikinta ta yi da karfi jikinta ya soma rawa. Ya soma nufota da murmushi yana shafar gefen fuskarsa. “Helloo bebi.” Ta nufi kofa da sauri zata bude, saidai ga mamakinta ta ji kofar gam! Ya kamo k’ugunta yana dariya. “O’o, guduna kikeyi?” Ta fisge jikinta, tuni ta soma kuka tana ja baya. “Don Allah ka yi hakuri ka kyaleni.” Ya jinjina kai. “Ki yarda da ni zan kyaleki.” Ya cigaba da nufota tana ja baya. “Don ke na k’i tafiya wajen party fa Bebi.” Faruk na hayowa sukayi kici6us da Sa’a tana saukowa tana dariya, ganinsa yasa ta sakin ihu don tsoro, jikinta ya dauki rawa, tunda ta ke bata ta6a ganin Faruk a yanayin da ta ganshi yanzun ba, gaba daya idanunsa sun kad’a, fuskarsa tamkar bai ta6a dariya ba. Ya shak’o wuyanta, cikin kakkausar murya yace. “Ina Ummi?” Muguwar shak’ar da ya yi mata ne yasa muk’ullin dake rik’e a hannunta ya fadi don sunyi da Kb da zarar ya kammala zai nemeta a waya ta bud’esu, jin faduwar abu yasa shi kai dubansa k’asa. Da sauri ya dauka ya dago ya dauke fuskarta da lafiyayyun mari har biyu sannan ya nufi saman da gudu, tuni Sa’a ta gudu ta bar wajen. Daidai lokacin da Kb ya rungumo Ummi da karfinsa na da namiji yana sumbatar wuyanta duk kuwa da irin turjiya da duka da cizo da ya ke sha, bai fasa abinda yakeyi ba, alokacin Faruk ya bude kofar ya hankadata ya shigo. Baiyi wata wata ba ya janyoshi ya wanke mishi fuska da mari. “Are you out of your senses?!!” Ya k’ara janyo ya kai mishi naushi a baki. “Baka da hankali KB?!! Kazamin jikinka kake hadawa da na Ummina?!! Kayi kadan wallahi!!!” Ya cigaba da bugunshi, Kb babu karfin haka ya yi ta jibguwa. Da dai Ummi ta ga yana shirin kisa a guje ta yi kansa ta shiga tsakani gami da rike kafadarsa a gigice tana kuka. “Don Allah Yaya Faruk ka yi hakuri, ya isa ka rabu da shi.” Ya watsamata kallon da ya kad’a hanjin cikinta. Ya fisgi hannunta suka fita, bai tsaya ko’ina dq ita ba sai wajen(swimming pool) dinsu, wajen babu kowa. Ya saki hannunta ta fada gefe tana kuka sosai. “Ga irinta! Ga irinta nan!! Yau da kina gaban iyayenki, wane shege ne zai shigo ya nemi 6ata rayuwarki…” Sai kuma ya yi shiru har lokacin cikin zafi ya ke, ya dauki kujera daya ya yi jifa da ita da karfi har ta 6alle. Ummi ta fahimci ya fusata, ko me za ta ce bazai ta6a fahimta ba, mutane nawa ne a gaban iyayennasu ake lalatasu, wasu ma ubannasu ne da kanshi? Ya zauna saman kujera ya dunk’ule hannu wuri daya gami da dafe goshinsa har lokacin bai huce ba, babu abinda ya ke hangowa sai Ummi a jikin KB. Maganarta ta katse tunaninsa. “Wallahi bani da laifi, yaudarata sukayi.” Daga nan ta labartamishi dukkan abinda ya faru, sai kuma lokacin ya dan samu nutsuwa duk da daman ya zargi hakan. Ta cigaba da kuka mai shiga zuciya. Ya kasa daurewa ya mik’e ya isa gareta gami da yin zaman durshen agabanta yana lankwashe kafafuwa. Ta dago idanunta jajaye ta zubamishi, shi dinma ita ya ke duba. Sakonni kala-kala ta ke amsa daga gareshi duk da yanda idanunsa suka kad’a don 6acin rai, hakan bai hana ta ganin wasu abubuwa masu wuyar fassaruwa ba, masu kashe jiki ba. Shima awajensa ji yakeyi yau bazata wuce ba sai ya sanarwa Ummi abinda ya ke ji gami da ita, idan ta san amsoshin ta k’aramishi ilimi a kai. Ta sauke idanunta tana tuna furucinsa na dazun. “Ummina.” Hannunsa ta ji a saman ha6anta ta razana don har lokacin fargaba bai barta ba na abinda Kb ya yi mata. Ya cire hannunsa da sauri don ya gani hakan. Ya fiddo hankicif ya mik’a mata. “Share fuskarki, yau zan gayamaki abinda ban ta6a fad’awa wata diya mace a doron k’asa ba Ummi.” Ya yi magana tamkar mai rad’a, ta dubeshi, shima ya zubawa gashinta ido wanda ya tabbatar garin kwatar kai ta baroshi a can, ya maida kansa gareta yayinda ta ke bin umarninsa. Gabanta sai lugude ya ke yi, shiyasq bataso ta ra6eshi, don duk sadda suka hadu suka rabu, dakyar tunaninsa ke barinta ta sake. Ya soma magana…..! Ummi shekaruna ashirin da tara a duniya, amma bazan ce miki yau ga wata mace da nakejin irin abinda nake ji ba akanki ga ita ba.” Ta dubeshi a matukar kaduwa. Ji ta yi kamar ta shid’e don tsoro. Idanunsa sam babu wasa sai ma wani kankancewa da suka k’ara yi yana mai dubanta duba na saurayi a gaban budurwar da ya ke mutuwar so tamkar numfashi. “Yes, ki kalleni sosai Ummi, ina a cikin hayyacina ba wani abu na sha. Amsa za ki bani please, idan har kin sani, idan ma ba ki sani ba ki tayani nemowa.” Hawayenta suka zubo tuni ta sunkuyar da kanta k’asa. “Ban ta6a runtsuwa batare da na tunaki ba tun farkon ganin da nayi miki a gidan Grandpa (Alhaji Atiku Modibbo), ban kuma ta6a jin faduwar gaba aduk sadda na tuna wata diya mace ba sai a kanki, ban kuma ta6a gajiya da kallonki ba Ummi. Kin ga nan.” Ya yi nuni da kirjinsa, ta d’ago ido ta bi hannunsa wanda ya d’aurawa agogo na bak’in fata da zobunansa na azurfa biyu. Ta maida kanta ta sunkuyar har lokacin tsoro da firgici bai saketa ba. Faruk ya cigaba da magana tamkar ba muryarsa ba. “Koyaushe kina cikinsa, bansan kuma dalilin da yasa har abada bana fatan fitarki a ciki ba. Na rasa amsar abinda nakeji akanki, na baki yau zuwa gobe, ki taimaka ki nemomin amsa, zan nemeki.” Ya yi shiru yana cigaba da kallonta ita kuwa ta kasa koda kallonshi. Har ta gaji da shirun ta dago ta dubeshi. Murmushi tattausa ya sakarmata wanda saida ta ambaci ‘Subhanallah’ a ranta adalilin kyawun da ya yi, bata ta6a ganin murmushi irin haka a wajensa ba, kallon ma na musamman ne Faruk ke jifanta da shi. Ta maida kanta kasa, ya daure fuska shima. “Ki k’ara kula sosai Ummi, KB dan uwana ne don d’a ne ga cousin din Hajiyata amma ban aminta da ki kara shiga huldarsa ba duk da nasan cewa wannan karon tilasta ki aka so yi, ita kuma Sa’a barin gidan nan ya zamto mata wajibi, yanzun ma ba don dare ya yi ba, da a yau sai ta bar gidannan.” Daga haka ya yi shiru, can kuma ya mik’e tsaye yana kakka6e jiki. “Kinga kin janyomin chanja kaya, fatin ma ba zan iya zuwa ba zan yi tsaronki.” Ita dai mamaki ya hanata cewa uffan duk da kalamansa sunyi mata dadi matuka saidai iyakar tunaninta ta kasa gano amsoshin tambayoyinsa. Hannun da ta ga ya mik’o mata ne yasa ta dubansa da sauri, murmushi ya sakarmata, wani yadi bak’i sidik yasa mai ratsin yellow, sai hula. Farar fatarsa ta fito ainun, ta mik’e batare da ta kama hannunnasa ba. “Saida safe. Ki kara kula please.” Bai kara sauraranta ba don yasan ba abinda zata ce ya juya ya fice domin zuwa kashe mota da kwaso wayoyinsa don dagaske ya ke jin tafiyar ta fice aransa. Ta bishi da kallo har ya 6acewa ganinta. Ta numfasa, sai kuma ta tuno abinda ya faru da ita yanzu, kai tabbas koda ta ji hirar su Sa’a bata ta6a tsammanin zata ci amanarta har haka ba ta yaudareta. Sai kuma ta tuno Antinta, ko me zata zarga akan dadewarta? Da gudu-gudu ta fito ta nufi dakinsu. Murdawa ta yi ta shiga, saidai kuma ta yi mamakin ganin Aminar na kwasar bacci, ta sauke ajiyar zuciya, watakil ta yi jiranta bata zo ba. Ta shigo gami da sanyawa kofar mukulli don gudun abinda zai kara faruwa da ita. Saida ta dauro alwala sannan ta rufe kanta ta kwanta lamo tana tunane-tunane. A hankali kuma ta cigaba da kuka, ba don Allah Ya jefomata Faruk ba, da a yau kashinta ya bushe, da ta rasa mutuncinta na ‘ya mace. Ji ta yi nan duniya ta tsani Kabir tsana tsantsa, shi kadai ne ya ta6a yin wannan yunk’urin a kanta, ta tuna sadda ya tsotsi wuyanta da sauri ta mike ta cire kaya ta je ta wanke jikinta don bai bar kamshin turarensa ba. Saida ta tabbatar kamshin ya bar jikinta sannan ta k’ara dauro alwala ta fito, saida ta yi nafila ta nunawa Allah godiyarta da Ya tserar da ita sannan ta yi addu’o’inta ta kwanta. Sai kuma sabon tunanin Faruk ya namayeta. Gani takeyi kamar a mafarki ba gaske ba, kamar kuma tana karanta litattafan hausa na soyayya da ake yawan yi na yan aiki da soyayya da dan masu gida. Ta runtse ido ta budesu, tabbas komai a zahiri ne, ya faru kuma a yau din, ga Faruk wai yana gayamata kalamai dad’ad”a har ya ke sanarmata yanda ya ke ji akanta bai ta6a ji akan kowace mace a doron k’asa ba. Ta lumshe ido ta budesu don dadi, ya tabbata dai abu daya su ke ji. A haka har bacci ya dauketa bata ankara ba. Washegari har ta farka ta yi sallah Amina bata motsa ba, abin har ya soma bata tsoro, karshe dai itama baccin ta koma. Amina dai bata farka ba har sai da gari ya yi haske, kanta ya yi nauyi, lokacin Ummi tana bandaki tana wanka, a ranar ne zaa kai Amarya gidanta misalin karfe hud’u. Ta yi shiru da son tuna abinda ya faru can kuma ta tuno yanda Sa’a ta shigo kiran Ummi, da kuma hodar da ta shak’a mata bacci ya yi awon gaba da ita. Ai da sauri ta mike ta fita kan babu ko kallabi. “Ummi! Ummi!” Yan aikin basu nan sun tafi ciki don kama ayyukansu, Ummi na jin muryar Amina ta fito tana gyara mazaunin daura kirjinta don ta kammala dama. “Anti kin tashi?” Amina ta waigo, ganinta yasa ta karasa a guje cikin tsoro tsantsa. “Ummi, na farka, gayamin ina Sa’a ta kaiki jiya?” Ummi ta dubi hanya sannan ta kama hannun Amina. “Ki kwantar da hankalinki, ki yi sallah zan ba ki labari.” Ta tuna ko sallar asubahi bata samu damar yi ba, ta matsa Ummi ta wuce, sannan ta fada zuciyarta ta dan sanyaya ganin Ummin lafiya, amma tana son tarar Sa’a don ta ji nufinta. Bayan ta idar ta dubi Ummi wacce ta ke sanya riga doguwa’yar kanti sabuwar da suka sayo, baki da orange ne adonta, ta yi kyau daidai gwargwado duk da ba wani kwalliya ta yi ba. Ta cigaba da addu’ointa sai bayan ta kammala ta shafa sannan ta juya ga Ummin. “Ki sanarmin, meyafaru jiya?” Ummi ta soma bata labarin har tana zubda hawaye, itama Amina har hawayen saida ta zubar tana mai yin salati. “Innalillahi… Wannan masifa da me ya yi kama? Ashe ba’a banza ba ta shak’amin hodar da ta fiddani a hayyacina.” Ummi ta zaro ido. “Hoda kuma?” Amina ta ja majina ta share hawayenta. “Tabbas, hoda ta shak’amin duk don kada na yi wani yunk’urin, saidai batasan cewa ba Amina ke karewa ba, Allah Shi ke kare bayinSa kodayaushe. Wallahi tun farkon ganina da Yaya Faruk ya ke burgeni don alamu sun nuna yasan mutuncin DAN ADAM. Ba shi kadai ba, dukkan yaran Hajiya Babba haka suke. Ki k’ara yi mishi godiya Ummi don ba karamin taimako ya yi miki ba. Ita kuma Sa’a na tabbatar tunda har Yaya Faruk yace zai hukuntata, to babu makawa. Kb kuma ki k’ara nisantarshi, biki kuma ai ya k’are, nasan ba za mu k’ara kwana biyu ba za mu tattara mu tafi.” Ummi ta jinjina kai, tana son gayawa Amina yanda sukayi da Faruk saidai tana tsoron abinda zata ce, a karshe dai bayan fitowar Amina daga wanka ta daure ta soma labartamata abinda Faruk yace. Amina na shafar mai bata ko katseta ba, haka kuma fuskarta bata nuna wata alama ta razana ba. Bayan kammala bayanin Ummi ta saki murmushi. “Ai daman nasan za’a rina!” Shine abinda ta fada wanda ya yi matukar razana Ummi har ta kasa daurewa ta kalleta, Amina ta jinjina mata kai alamar tabbas dagaske ta ke. “Eh, nasan ke da Faruk kuna SON JUNA, ganewa ne kawai bakuyi ba.” Ummi ta dafe kirji ta zaro ido. “So kuma?” Amina bata k’ara kulata ba saida ta sanya kaya, ita kuwa ta yi mutuwar zaune kawai tana bin ta da kallo duk inda tasa k’afa. Sai lokacin ta dubeta. “Muje mu gaida su.” Ummi ta girgiza kai ta rik’o hannunta. “Wallahi ba inda za muje sai kin amsamin, me kike nufi da muna son juna?” Amina ta dara ta koma ta zauna gami da cire wasa a maganganunta. “Ummi kina jin Faruk a ranki, daidai da kallon da ku ke jifan juna da shi abin a tambaya ne. Karki 6oyemin abinda na sani, kina son Faruk so na AURE. Hakazalika shima yana sonki, kuma ya sani nafi zaton gwadaki kawai yakeso ya yi ya ji ko ke din kina sonsa. Bar wannan batun, Faruk ya fi karfinki Ummi, ina gujemiki matsala. Wallahi na daukeki tamkar ciki daya muka fito, bana son abinda zai sa a ci mutuncinki. Karki manta matsayinmu awajen mutanen nan, mu ‘yan aiki ne, ba su daukemu komai ba face wannan Ummi. Bar ganin suna mana dariya, duk sadda muka bari wasu lamura suka afku ranar zasu tunamana cewar mu kaskantu ne awajensu, ranar zasu tunamana matsayinmu na marasa galihu. Ki cire Faruk a zuciyarki Ummi, babban goro sai magogin k’arfe, ina gujemiki shiga matsala. Abinda ya shafeki ya shafeni. Sannan ina so duk juyin duniya idan Faruk ya nemi amsa ki tabbatar mishi cewar babu wani abi da kika fahimta game da hakan haka kuma ke babu abinda kikeji game da shi. Kinji?” Ummi ta yi iyakar kokari wajen maida kwallar da ya tahomata, ta aminta hakan ne tana son abinda ya yi mata nisa. Ta yi murmushin yak’e. “Naji Anti kuma in sha Allah zan dau abinda kika shawarceni akai.” Ta murmusa. “Nasan da ciwo Ummi, amman gwara kiyi jinya daya da k janyowa kanki jinya na har abada…..” Ta gyada kai tana murmushi. Daga haka suka fita, kai tsaye wajen iyayen suka shiga suka gaishesu sannan suka fito. A hanyarsu ta zuwa taimakawa su Binta da aiki ne suka hadu da Faruk ya shirya zai wuce aiki. Ummi ta dan saci kallonsa, shi dinma idanunsa akanta. Suka gaisheshi, ya amsa. “Fatan babu wani matsala?” Ya cewa Ummi, ta girgiza kai a tsorace. “Kinji?” Ta yi shiru, ya k’ara maimaitawa. Hakan yasa ta dubeshi da mamaki. Ya kashemata ido daya daman fuskar ya ke son k’ara kallo daga haka ya wuce. Amina ta kama baki. “Mun shiga uku, Yaya Faruk da gaske ya ke fa.” Ummi dai ba bakin magana don gaba daya ya kashemata jiki. Suka karasa ciki, sunyi mamaki na rashin ganin Sa’a, sai Binta ke basu labari ai tun daren jiya ta harhada kayanta ta bar gidan ba anan ta kwana ba. Suka ta6e baki, anan Amina da karfin hali ta yi ta yiwa Binta nasiha har tana nunamata ba yi bane abinda sukeyi don abokin 6arawo 6arawo ne. Sai kuma Binta ta hau borin kunya da fad’an wai kazafi akayimata batasan komai ba. *** *** *** Ummi shekaruna ashirin da tara a duniya, amma bazan ce miki yau ga wata mace da nakejin irin abinda nake ji ba akanki ga ita ba.” Ta dubeshi a matukar kaduwa. Ji ta yi kamar ta shid’e don tsoro. Idanunsa sam babu wasa sai ma wani kankancewa da suka k’ara yi yana mai dubanta duba na saurayi a gaban budurwar da ya ke mutuwar so tamkar numfashi. “Yes, ki kalleni sosai Ummi, ina a cikin hayyacina ba wani abu na sha. Amsa za ki bani please, idan har kin sani, idan ma ba ki sani ba ki tayani nemowa.” Hawayenta suka zubo tuni ta sunkuyar da kanta k’asa.+ “Ban ta6a runtsuwa batare da na tunaki ba tun farkon ganin da nayi miki a gidan Grandpa (Alhaji Atiku Modibbo), ban kuma ta6a jin faduwar gaba aduk sadda na tuna wata diya mace ba sai a kanki, ban kuma ta6a gajiya da kallonki ba Ummi. Kin ga nan.” Ya yi nuni da kirjinsa, ta d’ago ido ta bi hannunsa wanda ya d’aurawa agogo na bak’in fata da zobunansa na azurfa biyu. Ta maida kanta ta sunkuyar har lokacin tsoro da firgici bai saketa ba. Faruk ya cigaba da magana tamkar ba muryarsa ba. “Koyaushe kina cikinsa, bansan kuma dalilin da yasa har abada bana fatan fitarki a ciki ba. Na rasa amsar abinda nakeji akanki, na baki yau zuwa gobe, ki taimaka ki nemomin amsa, zan nemeki.” Ya yi shiru yana cigaba da kallonta ita kuwa ta kasa koda kallonshi. Har ta gaji da shirun ta dago ta dubeshi. Murmushi tattausa ya sakarmata wanda saida ta ambaci ‘Subhanallah’ a ranta adalilin kyawun da ya yi, bata ta6a ganin murmushi irin haka a wajensa ba, kallon ma na musamman ne Faruk ke jifanta da shi. Ta maida kanta kasa, ya daure fuska shima. “Ki k’ara kula sosai Ummi, KB dan uwana ne don d’a ne ga cousin din Hajiyata amma ban aminta da ki kara shiga huldarsa ba duk da nasan cewa wannan karon tilasta ki aka so yi, ita kuma Sa’a barin gidan nan ya zamto mata wajibi, yanzun ma ba don dare ya yi ba, da a yau sai ta bar gidannan.” Daga haka ya yi shiru, can kuma ya mik’e tsaye yana kakka6e jiki. “Kinga kin janyomin chanja kaya, fatin ma ba zan iya zuwa ba zan yi tsaronki.” Ita dai mamaki ya hanata cewa uffan duk da kalamansa sunyi mata dadi matuka saidai iyakar tunaninta ta kasa gano amsoshin tambayoyinsa. Hannun da ta ga ya mik’o mata ne yasa ta dubansa da sauri, murmushi ya sakarmata, wani yadi bak’i sidik yasa mai ratsin yellow, sai hula. Farar fatarsa ta fito ainun, ta mik’e batare da ta kama hannunnasa ba. “Saida safe. Ki kara kula please.” Bai kara sauraranta ba don yasan ba abinda zata ce ya juya ya fice domin zuwa kashe mota da kwaso wayoyinsa don dagaske ya ke jin tafiyar ta fice aransa. Ta bishi da kallo har ya 6acewa ganinta. Ta numfasa, sai kuma ta tuno abinda ya faru da ita yanzu, kai tabbas koda ta ji hirar su Sa’a bata ta6a tsammanin zata ci amanarta har haka ba ta yaudareta. Sai kuma ta tuno Antinta, ko me zata zarga akan dadewarta? Da gudu-gudu ta fito ta nufi dakinsu. Murdawa ta yi ta shiga, saidai kuma ta yi mamakin ganin Aminar na kwasar bacci, ta sauke ajiyar zuciya, watakil ta yi jiranta bata zo ba. Ta shigo gami da sanyawa kofar mukulli don gudun abinda zai kara faruwa da ita. Saida ta dauro alwala sannan ta rufe kanta ta kwanta lamo tana tunane-tunane. A hankali kuma ta cigaba da kuka, ba don Allah Ya jefomata Faruk ba, da a yau kashinta ya bushe, da ta rasa mutuncinta na ‘ya mace. Ji ta yi nan duniya ta tsani Kabir tsana tsantsa, shi kadai ne ya ta6a yin wannan yunk’urin a kanta, ta tuna sadda ya tsotsi wuyanta da sauri ta mike ta cire kaya ta je ta wanke jikinta don bai bar kamshin turarensa ba. Saida ta tabbatar kamshin ya bar jikinta sannan ta k’ara dauro alwala ta fito, saida ta yi nafila ta nunawa Allah godiyarta da Ya tserar da ita sannan ta yi addu’o’inta ta kwanta. Sai kuma sabon tunanin Faruk ya namayeta. Gani takeyi kamar a mafarki ba gaske ba, kamar kuma tana karanta litattafan hausa na soyayya da ake yawan yi na yan aiki da soyayya da dan masu gida. Ta runtse ido ta budesu, tabbas komai a zahiri ne, ya faru kuma a yau din, ga Faruk wai yana gayamata kalamai dad’ad”a har ya ke sanarmata yanda ya ke ji akanta bai ta6a ji akan kowace mace a doron k’asa ba. Ta lumshe ido ta budesu don dadi, ya tabbata dai abu daya su ke ji. A haka har bacci ya dauketa bata ankara ba. Washegari har ta farka ta yi sallah Amina bata motsa ba, abin har ya soma bata tsoro, karshe dai itama baccin ta koma. Amina dai bata farka ba har sai da gari ya yi haske, kanta ya yi nauyi, lokacin Ummi tana bandaki tana wanka, a ranar ne zaa kai Amarya gidanta misalin karfe hud’u. Ta yi shiru da son tuna abinda ya faru can kuma ta tuno yanda Sa’a ta shigo kiran Ummi, da kuma hodar da ta shak’a mata bacci ya yi awon gaba da ita. Ai da sauri ta mike ta fita kan babu ko kallabi. “Ummi! Ummi!” Yan aikin basu nan sun tafi ciki don kama ayyukansu, Ummi na jin muryar Amina ta fito tana gyara mazaunin daura kirjinta don ta kammala dama. “Anti kin tashi?” Amina ta waigo, ganinta yasa ta karasa a guje cikin tsoro tsantsa. “Ummi, na farka, gayamin ina Sa’a ta kaiki jiya?” Ummi ta dubi hanya sannan ta kama hannun Amina. “Ki kwantar da hankalinki, ki yi sallah zan ba ki labari.” Ta tuna ko sallar asubahi bata samu damar yi ba, ta matsa Ummi ta wuce, sannan ta fada zuciyarta ta dan sanyaya ganin Ummin lafiya, amma tana son tarar Sa’a don ta ji nufinta. Bayan ta idar ta dubi Ummi wacce ta ke sanya riga doguwa’yar kanti sabuwar da suka sayo, baki da orange ne adonta, ta yi kyau daidai gwargwado duk da ba wani kwalliya ta yi ba. Ta cigaba da addu’ointa sai bayan ta kammala ta shafa sannan ta juya ga Ummin. “Ki sanarmin, meyafaru jiya?” Ummi ta soma bata labarin har tana zubda hawaye, itama Amina har hawayen saida ta zubar tana mai yin salati. “Innalillahi… Wannan masifa da me ya yi kama? Ashe ba’a banza ba ta shak’amin hodar da ta fiddani a hayyacina.” Ummi ta zaro ido. “Hoda kuma?” Amina ta ja majina ta share hawayenta. “Tabbas, hoda ta shak’amin duk don kada na yi wani yunk’urin, saidai batasan cewa ba Amina ke karewa ba, Allah Shi ke kare bayinSa kodayaushe. Wallahi tun farkon ganina da Yaya Faruk ya ke burgeni don alamu sun nuna yasan mutuncin DAN ADAM. Ba shi kadai ba, dukkan yaran Hajiya Babba haka suke. Ki k’ara yi mishi godiya Ummi don ba karamin taimako ya yi miki ba. Ita kuma Sa’a na tabbatar tunda har Yaya Faruk yace zai hukuntata, to babu makawa. Kb kuma ki k’ara nisantarshi, biki kuma ai ya k’are, nasan ba za mu k’ara kwana biyu ba za mu tattara mu tafi.” Ummi ta jinjina kai, tana son gayawa Amina yanda sukayi da Faruk saidai tana tsoron abinda zata ce, a karshe dai bayan fitowar Amina daga wanka ta daure ta soma labartamata abinda Faruk yace. Amina na shafar mai bata ko katseta ba, haka kuma fuskarta bata nuna wata alama ta razana ba. Bayan kammala bayanin Ummi ta saki murmushi. “Ai daman nasan za’a rina!” Shine abinda ta fada wanda ya yi matukar razana Ummi har ta kasa daurewa ta kalleta, Amina ta jinjina mata kai alamar tabbas dagaske ta ke. “Eh, nasan ke da Faruk kuna SON JUNA, ganewa ne kawai bakuyi ba.” Ummi ta dafe kirji ta zaro ido. “So kuma?” Amina bata k’ara kulata ba saida ta sanya kaya, ita kuwa ta yi mutuwar zaune kawai tana bin ta da kallo duk inda tasa k’afa. Sai lokacin ta dubeta. “Muje mu gaida su.” Ummi ta girgiza kai ta rik’o hannunta. “Wallahi ba inda za muje sai kin amsamin, me kike nufi da muna son juna?” Amina ta dara ta koma ta zauna gami da cire wasa a maganganunta. “Ummi kina jin Faruk a ranki, daidai da kallon da ku ke jifan juna da shi abin a tambaya ne. Karki 6oyemin abinda na sani, kina son Faruk so na AURE. Hakazalika shima yana sonki, kuma ya sani nafi zaton gwadaki kawai yakeso ya yi ya ji ko ke din kina sonsa. Bar wannan batun, Faruk ya fi karfinki Ummi, ina gujemiki matsala. Wallahi na daukeki tamkar ciki daya muka fito, bana son abinda zai sa a ci mutuncinki. Karki manta matsayinmu awajen mutanen nan, mu ‘yan aiki ne, ba su daukemu komai ba face wannan Ummi. Bar ganin suna mana dariya, duk sadda muka bari wasu lamura suka afku ranar zasu tunamana cewar mu kaskantu ne awajensu, ranar zasu tunamana matsayinmu na marasa galihu. Ki cire Faruk a zuciyarki Ummi, babban goro sai magogin k’arfe, ina gujemiki shiga matsala. Abinda ya shafeki ya shafeni. Sannan ina so duk juyin duniya idan Faruk ya nemi amsa ki tabbatar mishi cewar babu wani abi da kika fahimta game da hakan haka kuma ke babu abinda kikeji game da shi. Kinji?” Ummi ta yi iyakar kokari wajen maida kwallar da ya tahomata, ta aminta hakan ne tana son abinda ya yi mata nisa. Ta yi murmushin yak’e. “Naji Anti kuma in sha Allah zan dau abinda kika shawarceni akai.” Ta murmusa. “Nasan da ciwo Ummi, amman gwara kiyi jinya daya da k janyowa kanki jinya na har abada…..” Ta gyada kai tana murmushi. Daga haka suka fita, kai tsaye wajen iyayen suka shiga suka gaishesu sannan suka fito. A hanyarsu ta zuwa taimakawa su Binta da aiki ne suka hadu da Faruk ya shirya zai wuce aiki. Ummi ta dan saci kallonsa, shi dinma idanunsa akanta. Suka gaisheshi, ya amsa. “Fatan babu wani matsala?” Ya cewa Ummi, ta girgiza kai a tsorace. “Kinji?” Ta yi shiru, ya k’ara maimaitawa. Hakan yasa ta dubeshi da mamaki. Ya kashemata ido daya daman fuskar ya ke son k’ara kallo daga haka ya wuce. Amina ta kama baki. “Mun shiga uku, Yaya Faruk da gaske ya ke fa.” Ummi dai ba bakin magana don gaba daya ya kashemata jiki. Suka karasa ciki, sunyi mamaki na rashin ganin Sa’a, sai Binta ke basu labari ai tun daren jiya ta harhada kayanta ta bar gidan ba anan ta kwana ba. Suka ta6e baki, anan Amina da karfin hali ta yi ta yiwa Binta nasiha har tana nunamata ba yi bane abinda sukeyi don abokin 6arawo 6arawo ne. Sai kuma Binta ta hau borin kunya da fad’an wai kazafi akayimata batasan komai ba. *** *** *** KADUNA