SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 24
Washe Gari Nazeefa tun Wuri ta tashi ta Fara girka musu break fast, tana gamawa ta daura abincin da zatakaiwa Su Mansur asibiti, around 9:AM ta gama komai+ Kiran Ameerah tayi tace sun shirya ta kasance cikin shiri tace Alright Kiran Faeez tayi tace plz Bro in baka komai kazo kakaimu hospital tana magana cikin sanyin murya, OK Yace aiko yanzu na fito wanka Ganinan zuwa, Waigawar da zaiyi saiga mubeen a bayanshi, Dafashi yayi yace naji komai Kabari naje na kaisu kaji Faeez beyi jayayya dashi ba yace OK To, mubeen toilet ya shiga yai wanka yasa kaftan Mai kyau ya fito, Yazo ya sanar Da iyayanshi zaije gidansu Nazeefa, Sukace saiya dawo Faeez kuwa binshi da kallo yayi a zuciyarshi yace Wahalalle, ka gama yaudarar yarinya yanzu gashinan Alhaki ya kamaka, se Binta kkeyi, tsaki yayi ya fito ya dauka dan bike dinshi ya fita Wajen frnds dinshi mubeen ne yana tafe yana smiling yana tino fuskar Nazeefa dauke da smiling, Shi duk ya kosa ya ganta cos yana missing dinta sosai dinnan Knocking din gate sukaji anayi Nazeefa da murnar nan Ta je ta bude tana Bro Sannu da zuwa hade da murmushi, 4eyes sukai da Mubeen tuni ta hade rai tace meye kawoka nan gidan? A daidai lokacin Su Umma kuma suka fito Dan haka ta kasa karasa maganar ta, Wurgamai hatara tayi shidai murmushi yayi, Mubeen tsugunnawa yayi ya gaisar dasu suka Amsa da Lafiya lau ya gajiyan jiya yace Alhamdulillah Key Dad din Su Nazeefa ya mik’a mai Yace Giwa Hospital zaka kaimu, Yace Ok ba matsala baffa, Rufe ko Ina na gidan sukai sannan mubeen ya fito da motor range rover ce, Nazeefa ce ta fito da kololin abincin tasa a boot, Sannan ta bude mazaunin gaba da zauna, Sukahau kan titi ya Fara tafiya Sunyi tafiya kadan Nazeefa tace ya biya ta ta chan layin akwai kawarta zasu tafi tare Mubeen beyi musu ba Ya biya ya dauketa sannan suka Kama hanyar asibitin Nazeefa ce tace Sannu kawata, Ameerah tace yauwa, Nan ta gaisar da iyayen nazeefa cikin girmamawa suka amsa cikin murmushi cos daga ganin yarinyar kasan Alhamdulillah tanada hankali, kallon Umma tai tace Wallahi kuna kama Da Nazeefa, duka motar harda mubeen Dariya sukai saboda wawtarsu iri daya da Nazeefa suna abu irin they don’t care dinnan Suna tafe but kowa da abun da yake ayyanawa a zuciyarshi, Da yake Ameerah ta gane Mubeen kallo daya tamai aranta tana kalleshi harda wani gemunshi kamar ba shi ba, Yar karamar tsaki taja da ba Wanda ma ya ankara Sunyi tafiya kadan suka karaso Asibitin, Waje mubeen ya samu Ya ajiyesu yace zai koma gida cos bazai Iya shiga asibitin ba, idan yaje mezaicewa mubeen Umma ne sukai gaba, Ameerah da Nazeefa kuma suka dakko kololin Abincin, Mubeen ne yai magana cikin sanyin murya yace ga number na nan idan kungama Ku kirani na maidaku gida! Wani harara tamai da seda ya jingina jikin motor sannan tace uban wayace kazo? Mutun se shegen shisshigi mtsww Ameerah tace Kai kawata meye haka, Number kawai? Tace Eh din tai gaba abunta, Ameerah kuwa ya bata tausayi Tace bani number idan mun gama Zan kiraka inshaa Allah nan take ya bata tamai flashing yace Yagode Wani Suna zanza? Tace kasa Ameerah yace OK Malama Ameerah Tafiya ta somayi yabi bayanta da kallo, yace Allah mai iko ashe in kawance yai kawance wasu har kama sunayi, Dan Wannan kam sunyi kama sosai da Nazeefa dan har dabi’unsa kusan daya though bezauna da itaba Amma yana tinanin tanada sauqin Kai shige motar yayi ya koma gida abunshi Ameerah da sauri takaraso wajen Nazeefa tace kai kawata meye haka, har yanxu fushi dashi kkeyi? Nazeefa tsaki tayi tace ke muje Ameerah tace ihm harna amsa number mubeen, Xare ido Nazeefa tai kamar zatace wani Abu kuma setai shuru amma se juya maganar take na meye na amsan number shi kuma? ***** Kama Ward din da aka kwantar da Mansur suka nufa, Yana ganin Nazeefa and her parent ya tashi daga kwanciyar da yake, Kallo daya sukaimai sukaga yayi fari sosai ya rame Sannu da jiki sukaimai ya gaisheshu yace Jiki Alhamdulillah Nazeefa kuwa se satar kallonshi takeyi, kullun Kara kyau yake Mata, Sun Dade a hospital din sosai se hiransu sukeyi, kwasam Sega Hajiya Bilkisu da Sarki se su Hassan da Hussaini dasu Jameela Mum Mansur ne tace Masha Allah dama yanzu muke hiranku sai gashi kunzo+ Hajiya Bilkisu tace Ayya, Nan ta gabatar musu da mahaifan Nazeefa, Kara gaisawa sukai sosai, Sarki yace Masha Allah ba shakka tabbas kuwa wannan ne Malan Nalado me flour, ya kake ya bayan saduwa, yace Alhamdulillah, hira suka shiga Sosai kamar dama sunsan juna *** Bangaren Mubeen kuwa tun dawowarshi gida kasa sukuni yayi, Ranshi sai rayamai yake kodai ya nema Ameerah ce cos Nazeefa yasan confirm tamai Nisa wata zuciya kuma tace keep on trying ai ba aure tayi ba, Da tinanin nan ya wuni, Bangaren Mansur kuwa Cikin ikon Allah Jikinshi yayi Sauqi kamar ba shi ba Magana yakeyi sosai, Dan sunsha hira dasu Hassan sosai kowa hankalinshi ya kwanta Cin abinci sosai yakeyi koda aka sake dubashi ba BP. heart din ma ta koma normal shape dinta, Dan haka Doctors din suka kira iyayanshi akan su daure su cikamai burinshi, so that ya samu yai rayuwa mekyau sukace in shaa Allah Washe Gari nayi suka sallameshi ya dawo gida Mansur yaji dadi Sosai, Ana Sallamarsu ya Kira Nazeefa ya sanar da ita, Alhamdulillah tace” Yace please zakizone? Uhmm uhmm tace tana magana tana shagwaba tace kasan bazan iya zuwa ba, Gidan fa cike yake da mutane, yace ina ruwanki dasu Dan kawai ta kwantar mai da hankali tace Alright Chan yamma zanzo Wani murmushi yayi sannan yace I love you Please be online muyi chat cos I surely miss you, Smile tayi tace OK love you too **** Bangaren Mubeen Kuwa dama Already da yan kudadenshi, Wani hikima tazomai na why not filin da yake dashi ya gini babban Makarantar islamiya da boko wanda za’a amfana ko bayan ranshi, cos yanzu yayi nadama sosai Abunda da zai amfane rayuwarshi kawai zaiyi Wani Me gini ya Kira yake tambayarshi in zanyi gida kaza kana tinanin nawa Zan kashe? Me ginin yace Yallabai Ina zuwa na duba Nan take yai calculating, ya kirashi ya sanar dashi, Dr Mub33n yace Alright gobe by 9:AM kazo hospital din da nake aiki ka sameni yace inshaa Allah *** Mansur da Nazeefa Chat sosai sukai irin na masoya Bangaren iyayan Mansur kuwa tunda ga hajiya bilkisu da Sarki, Dad mansur ne yace Alhamdulillah tunda kunanan. Gobe in Allah ya yarda Zamuje Mu nema aurar Nazeefa cos naga sunason junansu, Mansur na Chan ma besan abun da akeyiba cos yana daki suna tinanin bacci yakeyi Ashe yanata buga chats dinshi da muradin zuciyarshi Hajiya Bilkisune ta dan hada rai tace Nazeefa kuma bayan munyi alkawarin Zaku auramai Suhailat, Sarkine Mijin Hajiya Bilkisu yace ban yarda da hakan ba, me yasa kin fiye son kankine Shuru tai kamar Mai nazarin wani Abu, Suhailat tanaji ance baza a aura Mata mansur ba ta shige toilet kuka tayi sosai kamar ranta zai fita, Ya zatai da son Mansur, Wanda ta dade tana ajiyarshi, lalle kam ramin mugunta idan zaka ginashi kayi dai dai Kai Su kuma Hassan da Hussaini room din Mansur suka shiga suka sameshi yana Waya Hussaini ya fizge wayar yace To romeo hassan yace ko kuma Ango ba! Nan suka Fara Mai tsiya sukace Angon Nazeefa yanzu Su hajiya suke maganar gobe za aje maganar Nazeefa Mikewa yai zumbur yace are you serious? Sukace da gaske Wallahi Rungume pillow yayi yana dariya yace I’ll soon be ANGO, ANGON ma na Nazeefa Wow Hussain yace gaskiya kam I’m happy for you ko ni da banda Wanda Zan aura da ita Zan aura Hassan ma yace KO ni WallahI cos yarinyar tayi sosai, Mansur yace eh din ya isa haka Adena kiran sunar matata Kar gabanta yaita fadi LOL Hussain Dariya yayi yace Kaji Mansur dinnan Mansur yace hhh ni da nakeji kamar anyi ma Dukansu dariya sukai, Hussain yace ANGO ANGO, Wani irin tafiya Mansur ya Fara yace Ku biyo bayana, Hassan ne yace Wallahi ana ganinka silent amma bakaji fa… Hussaini yace kabarshi rudin soyayyane ke dibanshi, Mansur yace eh din naji dai Washe Gari Sarkine ya zaunar dasu Mum mansur yace shi ga shawara, why not ayi abun gaba daya tunda yaran sunason junansu sosai+ Mum mansur Sukace yes tabbas kuwa, And kuma iyayan suma na tabbata sunsan sunason junansu Sarki Yace to Alhamdulillah ayi abun gaba daya kawai ko bikin za’asa befi asa 2months ba, idan ma hidiman amaryar nan zanyi komai dakaina inshaa Allah Dad mansur yace Masha Allah, hassan ya kira yace yakiramai Mansur, Mikewa yayi ya shiga room din Mansur ya sameshi yanasa shaddanshi geznah, Hassan yace Ina zaka kuma? Yace Wajen Matata, Hassan yace lalle kafimu zumudi to kazo SARKI na Kira gabanshine ya fadi yace Allah yasa ba maganar Wata suhailat za’ai maiba Biyo Hassan sukai wuce falo suna murmushi Dukansu Zama sukai, Mansur ne ya tsugunnar dakai, Sarki ne ya soma magana kamar haka, Mansur da farko naso na aurama suhailat amma gaskiya bazaiyuba saboda naga irin soyayyar dake tsakaninka da Nazeefa, Mansur dai kanshi na kasa bece komai ba Jamila da suhailat kuma suna labe, Sunaji maganar da sarki yakeyi gabansu ya fadi, Suhailat kuma wani irin zufa taji yana keto Mata, yanzu shikkenan ta rasa mansur, kasa rik’e kukan da takeyi tayi Dan haka ta Shiga toilet taci kukanta, Yanzu samarin da take wulakantawa da wani ido zata kallesu, Lalle mugunta yiwa Kai ne *** Sarkine yace sai ka kirasu ka sanar dasu zuwa gobe magabatanka zazuzo, kuma duk abunda kke bukata ka rubuta munshi kafin mutafi, Mansur kusa Da sarki yaje sosai yace nagode **** Waye ne Sarki, nasan zasuso kuji dangartakar dake tsakaninsu, Sarki Wan mahaifin Mansur ne, uwarsu daya ubansu daya, su biyu tal aka haifesu, sun taso cikin so da kulawar juna, atakaice kenan Mansur daki ya shige ya Kira number Nazeefa, Yanata ringing bata daukaba, Kira yake tayi kusan 4 missed call bata daukaba, Text yai mata, baby nah kina Ina, I missed you I want to see you anjuman nan akwai Labari.. yai Mata sending Nazeefa kuwa nachan ta tsunduma cikin Tinanin Mubeen kardai ace yanason Ameerah ne Shugo daki tayi taga phone dinta na haske, dauka tayi ta Fara duba missed call sannan ta bude text din dayai mata, Smiling tayi tace Allah yasa good news ne Calling dinshi tayi Shima yadan ja aji gab da ze tsinke yai maza yai picking har yana bigewa a hannu, Yana karawa a kunne yai Mata wani sound ouchhh Zafi, Tace Mansur lafiya kuwa? Smiling yayi yace duk bake bace kikasa na bige a hannu Wani Yarrr da ido tayi kamar yana kallonta tace sorry swt hrt Yace thanks love, Ina Kika shiga? Tace ina kitchen ne, Yace are you sure? Tace yes love Yace I’m damn missing you da Zan Iya da nazo na ganki anjuma Noooo noooo basai kazoba tace just jiyafa aka sallemaka ka, Ka huta yace Baki missing dinaba kenan Tace No nafi kowa missing dinka Yace banga alamaba, tace soon zaka gani Nan sukaci hirarsu ta soyayya, Albishirinki yace Mata Tace goro, Yace fari ko ja, tai murmushi tace fari Sol…yace kwana kadan ya rage ki zama property Dina, I mean goben nan iyayena zasuso maganar aurenki, Wow Alhamdulillah tace a mind dinta, kashe wayar tayi ta wuce dakin Mom dinta ta fada kanta tace Umma, Gobe magabatan Mansur zasuzo Ummantane tace Ni ki dagani Yar nan Nazeefa ta dagata tace sorry umma, bin ta kallo tayi tace yaran yanzu kunyarsu kadan ne, mu lokacin da akai mana muita guduwa Lol Nazeefa dakinta ta wuce da gudu, Burinta ya kusan cika wow Ummanta kuma daga Hannu tayi tace Alhamdulillah Nazeefa tsayawa tai a mirrow ta kalle kanta tace yeah it’s my time, Murna kawai taji yanayi amma idan ta tina da mubeen se taji ranta na baci Mansur kuwa tunda akace gobe za’aje gidansu nazeefa na maganar auransu kasa natsuwa yayi, Kiran Abdallah yai ya sanar dashi Abdallah ango Yacemai ina maka murna, Sannan mansur yace kana inane? Abdallah yace Ina gida kusa da madam, Mansur yace ahh ahh se anjuma dole naji muryanka yai kasa kasa ashe madam ta kasa ta tsare Abdallah dariya yayi yace kasama baki KO? Zamu hadu bye ***Nazeefa kuwa tsaye tai a dakin tana tinanin mezatai ma! Muje Zuwa