DAN ADAM CHAPTER 15

DAN ADAM CHAPTER 15

  Ba su suka dawo gidan ba sai bayan Magriba. Yana fakawa suka fito kowacce hannunta rik’e da leda wanda kayan mak’ulashe ne zalla. Ihsan bayan sun danyi gaba ta dubi Ikram. “Wai duk wancan kayan zak’in da Yaya Faruk ya loda na shi ne sho d’aya?” Ikram ta harareta. “Meya hanaki tambayarsa?” Ta yi dariya. “Mezai kaini gangancin nan?” “Wai ma, kina ganin dai ya mik’o mana na Hajiya, kinsan dai nasa ne ko? Amma dai bansani ba ko anjima zai je hira.” Ta k’arashe cikin zolaya. Ihsan ta buga tsaki gami da k’ara d’aga kafa. “Ke dama ai ba’a hirar arziki dake sai kin kwafsa a wani 6angaren.” Ita dai Ikram da dariya kawai ta bita. Shi kuwa gogan kai tsaye sashensa ya nufa, saida ya yi sallah ya fito ya lek’a su Hajiya kafin ya koma sashensa ya fito rike da ledar Ummi wacce ya yo mata siyayya. Daidai lokacin da ya kwankwasa mata, Binta ta fito daga bandaki, zaro ido ta yi domin mamaki da ya cikata. Me Yalla6ai ke yi a bakin k’ofar dakin Ummi har yana kwankwasawa? Ta so ta yi magana saidai ta kuma la6ewa don ganin wannan abin Al’ajabin. Ummi ta shafa adduarta, idar da sallar isha’in ta kenan, mik’ewa ta yi ta nufi k’ofar gami da bud’ewa. Suka dubi juna ta gaisheshi, ya amsa fuskarsa dauke da murmushi. Ledar ya mik’amata. “Ajiye wannan sannan ki zo ki sameni.” Gabanta ya fad’i, ta dubi ledar sannan ta dubeshi. “Kar6i mana.” Jiki a sanyaye ta kar6a. “Nagode.” Ya yi gaba gami da fadin. “Ina jiranki.” Ta juya ta koma ciki har lokacin jikinta babu kwari. “Anya batayi wauta ba? Meyasa ta kar6a batare da tunanin kada wani abin ya biyo baya ba?” Ganin dai babu wanda ya ganta, yasa hankalinta ya dan kwanta. “Anyi na farko, in sha Allah shine na karshe.” Ta fada a fili, sanin da ta yi babu wani aikin da bata yi ba ne ballantana wani ya nemeta yasa ta saurin mik’ewa bayan ta daga hannu sama. “Ya Allah ka taimakeni yau wannan bawa naKa ya fahimceni.” Daga haka ta shafa sannan ta fice. Akan idon Binta, Ummi ta fito ta wuce, ganin Ummin na shirin waigowa ne yasa ta saurin komawa baya yanda bazata ganta ba, saida ta tabbatar ta bar wajen sannan ta shiga tafa hannuwa tana salati. “Tabdijam! Ashe dai duk jirgi daya ya kwasosu da Kb? Duk wannan shiru-shirun na wofi ne? Kuma wai Ummi?!” Tayi maganar a fili cikin nuna tsananin mamakinta. Lallai DAN ADAM mai wuyar gane hali ne. Saida ta lek’a dakin ta gama bud’e ledar ta ga kayan mak’ulashen da ke ciki sannan ta fita tana had’iyar yawu. “Ina yarinya, wannan kam dole nima ki bani rabona.” Acan kuwa Ummi ta iske Faruk durkushe gaban ruwa yana sanya tafin hannunsa na dama yana wasa da shi, fuskarsa a sake. Jin shigowarta yasa shi kallonta, ta kauda idanunta ta karasa bayan ta rufe k’ofar. Mikewa ya yi ya koma ya zauna, itama ganin haka ne yasa ta zama a dayan kujerar kamar yanda sukayi wancan karon saidai a wannan karon ya sanya kujerun suna kallon juna, hakan yasa shi bawa k’ofa baya ita kuwa tana fuskanta. “Na yi zaton bazaki zo ba ai.” Babu abinda ta ce sai wasa da gefen hijabinta da ta ke. “Ummina.” Ba ta amsa ba sai kirjinta da ke lugude. “Wai meyasa ne kike kasa sakin jiki da ni? Idan da magana a bakinki ko fad’a.” Ta ga dama ta samu, hakan yasa ta daurewa ta dubeshi. “Don Allah Yaya Faruk ka yi hakuri ka kyaleni.” Ta sauke idanunta daga kansa kafin ta cigaba da magana a raunane. “Wannan abu ne da ko a mafarki ban ta6a ganin ya faru ba, ‘yar aiki da auren d’an masu gida, kayi hakuri domin Allah, komai dake a ranka game da ni ka ajiyeshi gefe. Ni bazan iya abinda ka ke so ba, banason saka kaina cikin kowace matsala. Ka gafarceni amman idan akwai inda na kuskuro a maganata.” Tun soma maganarta ya zubamata ido hannayensa biyu dunk’ule wuri guda. Ya lura iyakar gaskiyarta ta ke fad’a ba kuma don bata sonshi ba. Ya girgiza kai. “Meyasa ni ban ta6a hangen matsalar da kike yawan ikrari bane Ummi? Kina da tsoro, nasan kuma abinda ke tsorata ki wanda sam bai dace ba. Na farko dai nasan iyayena ba zasu hanani aurenki ba matukar na nuna musu ke ce za6ina, su din sun kasance maso abinda nake so, haka kuma yan uwana na tabbatar ba zasu hanani rayuwa da ke ba Ummi, koda ace kuma basu yi na’am da ke ba, to fa hakan ba zaisa na k’i aurenki ba muddin iyayena sun yarjemin. Batu na gaba, ni ban daukeki daban da ni ba, Allah ne Ya haliccemu duka, ina yi miki kallo daidai da matsayina, ki ture dukkan wadannan kananun matsalolin Ummi, ki sauk’ak’awa zuk’atanmu, nasan kina jin abinda nake ji duk da cewar ba ki kama koda rabin k’afata ba.” Shiru ya dan biyu baya, ya rankwafo kadan ya soma magana cikin rad’a. “Kin yarda kin amince na sanarwa Hajiya…” Bai kai ga karasawa ba ta hau girgiza kai tana dubansa da idanunta wadanda suka ciko da kwalla. “A’a, a’a, don Allah kada ka fadawa kowa idan ba haka ba zan gudu.” Ya dan hade gira jin kalmarta na karshe. “Saboda kada ki aureni ne za ki gudu?” Ganin yanda muryarsa ta chanja da kuma yanayinsa yasa ta yin shiru gami da duk’ar da kai. Ya lumshe ido. “Shikenan, tashi ki tafi.” Ta kasa motsawa, sai ta ji bata kyauta mishi ba, shi kuwa har lokacin bai bude idanunsa ba, dagaske bai ji dadin furucinta ba, kenan akan ta aureshi, ta za6i guduwa? “Ka yi hakuri don Allah.” Ya tsinci muryarta, da sauri ya bude ido don kuwa muryar ta nuna alamun kuka takeyi. Kukan kuwa takeyi, ya girgiza mata kai. “No Ummi please, banson hawayenki fa. Ni na hakura.” Faruk ya cigaba da kasheta da dad’ad’an kalamai wadanda nan take suka kashemata jiki suka sukurkuta ta. Allah Ya mishi baiwar iya lafuzza masu dadi da saurin sace zuciya wanda shi kansa bai sani ba sai a yanzun da ya fad’a cikin soyayyar Umminsa. A wannan zaman da sukayi saida Faruk ya ci galaba don kuwa Ummi ta dan saki jikinta sun yi hira mai dadi har da dariya. Kowannensu yana jin zuciyarsa sakayau, gaba daya ji sukeyi tamkar a duniyar babu sauran bil adama sai su biyu tallin tal! A karshe ya duba wayarsa da ta soma k’ara, yayansa Likita ne(Ridwan). Ya dauka. Bayan sallama ya tambayeshi inda ya shiga, ga shi kuma a falon Hajiyarsu bai ganshi ba. Ya dubi fuskar Ummi wacce ke dan satar kallonsa, murmushi ylm a yi ganin ta kauda kanta. “Hira nake yi da surukarku amma ina nan zuwa.” Daga haka ya katse kiran ya bar Ummi da sakin baki. “To sarkin tsoro, rufe bakin.” Yana fadin haka ya mik’e tsaye. “Bari na wuce Dakta ya zo. Sai mun hadu gobe kuma in sha Allahu ko?” Ta girgiza kai alamar aa. Ya ja dan guntun tsaki. “Kinga dadin waya kenan, da sai mu sha hira, amma dai ba wani abu.” Daga haka ya yi mata sallama ya wuce, itama barin wajen ta yi da saurinta. Tana shiga dakin ta fidda hijabinta ta zauna, a yau ji take dukkan shawararwarin Antinta babu daya da ta iya dauka, ji take kamar ana k’ara rura mata wutar kaunar Faruk. Ta matso da ledar ta bude, ta yi mamakin ganin kayan kwalam har da su meatpie nad’e a jikin tissue guda uku, ga wani kullin leda karami wanda tana budewa ta ci karo da alawoyi kala-kala. Harda su cake da robar ice-cream manya biyu. “Assalamu alaikum.” Da bude kofar da sallamar nata duk lokaci guda ne, ta daure ta 6oye razanar da ta yi, ta amsa mata. Karasowa ta yi tana mai zaro ido. “Ke Ummi yau asirinki dai ya tonu, ashe kema ‘yar hannu ce, naga ma kusan kin fi Sa’ade sa’a don kuwa ke kamun babban goro kikayi.” Ummi da ta rasa meke mata dadi a duniya ta cigaba da kallonta tana ji kamar ta saki fitsari. “Me..me..kike so ki ce?” Binta ta yi dariya kadan lokacin da ta zauna tana mai sa hannu ta janyo ledar. “Eh lallai dole ki rude, ki kwantar da hankalinki ki ci arziki, ai ni idan har za ki dunga yagamin abinda kika samo to fa kar kiji komai don ba ko da matsala da ni. Ki bi sannu dai da mutan gidan da su Bala(mai kula da shukoki), su ne abin ji.” Ta fiddo meatpie ta gutsira. Ummi dai banda innalillahi babu abinda take fada a ranta, Binta ta ganota saidai ta to musu mugun fassara, to daman ina zata aminta cewar soyayya na tafi tsakani da Allah, namiji kamar Faruk zaiyi mata? “Wallahi babu makamanciyar abinda ki ke zargi tsakanina da Yaya Faruk.” Binta tana taunar meatpie ta watsamata harara. “Wai kina zaton ban ganku sadda ku ka shiga wajen wanka ba? Haba Ummi, wannan ba abin rufemin bane, nifa makwafciyarki ce, idan ban rufamiki asiri ba wa zai rufa? Tun yaushe ya soma nemanki?” Ran Ummi idan ya yi dubu to ya 6aci don jin wannan mummunan zaton da Binta ta yi mata. “Ina miki rantsuwa da Allah abinda kike tsammani tsakanina da Yaya Faruk ba haka bane.” Binta ta yi sakato. “To menene? A banza zai kawowa ‘yar aiki kayayyaki har haka batare da cewa yana da buk’ata akanki ba? Haba Ummi, ko kunnuwana sun kai dubu bafa zan yarda da abinda ki ke fad’a ba. Kedai ki saki jiki kawai arziki ne ya zo miki, idan ma kin ci sa’a nan gaba ya daga darajarki a gidannan.” Ummi ta runtse ido, ta fahimci Binta ta yi nisa cikin zargin abinda ba haka ba. Bai kuma kamata ta barta da wannan bahagon tunanin ba. “Tsaya ki ji gaskiyar magana, amma don Allah ki rufamin sirrina.” Binta ta tsaya tana dubanta. “Karki damu, ki saki jiki ki sanarmin, wallahi zan bar zancen a tsakaninmu.” Ummi ta kwashe abinda ke faruwa ta sanarmata. Binta wacce ta daskare awajen ta kasa ko kwakkwarar magana, mamaki ne ya cikata kwarai dagaske, ba don ya ganewa idanunta ba da sai ta iya karyata Ummi nan take, saidai kuma har zuciyarta ta aminta da hakan. Ta cigaba da karewa Ummi kallo, ba k’arya tana da kyawun gani a yaba kuma a so, amma abin mamakin, akwai fiye da ita masu son Faruk saidai wai ace basu isheshi kallo ba sai ita? Ummi duk ta k’ara tsorata ganin irin kallon da Binta ke bin ta da shi, ga dukkan alamu bata yarda da zancenta ba ne. Wannan yasa ta kara riko hannunta. “Wallahi iyakar gaskiyar kenan, na gayamaki banda wannan babu abinda ke tsakaninmu, na rasa kuma yanda zanyi ya bar shiga harkata.” Binta ta jinjina kai gami da sauke ajiyar zuciya. “Tab! Babbar magana. Amma kin kusa kiyi wauta wallahi Ummi, da ace ni na samu wannan damar da babu ta yanda zanyi watsi da ita. Aure fa Ummi? Auren ma da matashi irin Yalla6ai Faruk? Gaskiya ki sake tunani, ki cire tsoro kamar yanda yace din ki tabbatar kin ba shi goyon baya. Karki damu ni don na rufamiki wannan asirin to ba komai ba ne wallahi. Idan ma na ce zan tona ai na shiga uku don nasan nima korata zaayi.” Ta karashe da dariya, Ummi kuwa ta murmusa, hankalinta ya kwanta kadan. Ta dibarmata kusan rabin kayan sannan Binta ta fice zuwa dakinta bayan ta kara jaddada mata akan kada ta sake ta bari wannan dama ta kufcemata. Ummi da to kawai ta bita. Ihsan tunda ta ji abinda Faruk ya ce wa Dakta hankalinta ya tashi, ji ta ke kamar ta yi tsuntsuwa ta je sashensa ta ganewa idonta ko dagaske ne. Wai ashe dai yana da budurwa wacce ya ke so ta ke zaman jiran gawon shanu? Sam bazai yiwu ba! Sai a yau ta ji tana son bin shawarar Ikram, wato ta sanarwa Faruk yanda ta ke jinsa a ranta. Ta numfasa. ‘Shi kadai ne mafita.’ Ta ayyana hakan a zuciyarta. Mintuna biyar da haka, sai ga shi ya shigo falon. Suka dubeshi. Haidar ya ce. “Ina shirin bin sahu na ga ‘yar gidan taka sai kuma gakanan.” Faruk wanda tun shigowarsa ya ke murmushi ya zauna a saman kafet kusa da kafafun Babban Yaya, hannu yasa ya dauki ayaba guda cikin wanda suke ci. “Yanzu Dakta saida ka tonamin?” “Ana 6oye abin farinciki ne?” Cewar Dakta. Ya girgiza kai yana ‘yar dariya. “Yanzu fa na soma yak’in, ban kai ga cin nasara ba.” Sukayi dariya gaba daya har Ikram, Ihsan ji ta ke yi tamkar ta fashe. Gaba dayansu sun yarda don tunda suke da kaninnasu basu ta6a jin ya yi musu zancen kowace mace ba sai a yau din. “Dariyar me akeyi?” Fadin Daddy wanda shigowarsa gidan kenan daga waje, ya yi bak’o. Bayan ya karaso ya zauna suka dubeshi. Babban Yaya ne ya soma magana. “Daddy kaninmu ya samo maka suruka fa.” Da mamaki ya dubi Faruk wanda banda murmushi da taunar ayaba babu abinda ya ke yi. “Dagaske?” Faruk bai amsa ba. Daddy ya ji dadi a ransa. “Kai Masha Allah, na ji dadin wannan lamari. Ai gwara ka soma shirin auren kafin na yi maka na dole.” Aka dara, Daddy ba ruwansa matukar yana da lokaci yakan zauna da iyalinsa suyi hira da dariya. Hajiya Babba ta sauko itama tare da wata budurwa da uwarta ta aiko daukar mata mayafai, bayan ta sallameta ta dawo wajensu, alokacin Ihsan ta sulale ta bar falon don tsabar takaici. Nan itama aka fesamata, murmushi kawai ta yi tare da addu’ar nemawa danta za6in Allah. Daga nan kuma hira ta 6arke, Ikram tuni ta ankara babu Ihsan a falon hakan yasa ta bi bayanta. A can karshen gadonsu ta risketa ta sanya kanta cikin filo tana kuka har da sheshshek’a. Ta karasa ta zauna a gefenta. “Ya Salam, haba Ihsan, meyasa haka?” Ihsan ta mike zaune idanunta jage-jage da ruwan hawaye. Ta ja majina. “Kinga lokaci ya k’uremin ko Ikram? Da ace na bi shawararki da banga wannan rana ba.” Ikram tausayinta ya mamayeta, ta dafa kafadarta gami da girgiza mata kai. “Aa, lokaci har yanzu da sauransa Ihsan. Na fadamiki ki cire kunya ki sanarwa Faruk abindq kike ji game da shi koda ta hanyar kafar sadarwa (whatsapp)ne. Kada ki karaya da wuri.” Haka ta yita lallashinta sannan ta fita wajen yan uwanta. Tana fita Ihsan ta dauki waya ta kira Maminta. Ko sallama bata iya yi ba ta fashe mata da kuka gami da labartamata abinda ake ciki. Mami ta shiga damuwa ainun. “Ihsan kina kyautatamasa kuwa kamar yanda nace?” “Babu abinda bana yi Mami, har gyaran dakinsa hana Ikram nayi na ke yi, amma wannan duk ba ya gani, ni yanzu na yanke shawarar sanarmishi irin illar da sonshi ya yiwa zuciyata.” Mami ta karya murya. “Kina ganin hakan zai fi?” “Eh Mami.” Mami ta jinjina kai, kwarai kuma tasan Faruk yana da mutunci, bazai so damuwar ‘yar uwarsa ba. “Shikenan, ayi hakan. Amma ki san abinda za kice dai.” Haka ta yita lalla6a diyarta, bata son abinda zai ta6a farincikin ‘yar tata ko kadan. A karshe ta sanarmata cewa an soma shirye-shiryen tafiyar Adnan Dubai inda ya za6a. Maganar ta yi mata dadi, hakan ya rage zafin da zuciyarta ke yi ta dan samu nutsuwa. Falon da bata koma kenan ba! *** *** *** RINGIM TSAFI GASKIYAR MAI SHI… Kwarai wannan zance haka yake, don a kwana uku kacal! Dija da uwarta sun yi dukkanin k’ulla-k’ullarsu sun dauke hankalin Deen tsaf daga kan matarsa, kacokam zuciyarsa ta koma ga Dija. A yau lahadi ya yi shirin zuwa Ringim, don tun cikin ranakun aiki ya ke son kawomata ziyara tana hanashi. Yau kam ko sanarmata baiyi ba sai ganinsa sukayi. A kofar gidan ya faka motarsa, ya kirata a waya ya sanarmata yana kofa. Ta yi mamaki har da tsalle da ihunta na murna, Baba Habiba itama ranta sakayau. Ta taimakamata ta shirya sannan ta mik’amata turare da kwallin da suka kar6o. “Saka ‘yar albarka.” Tana dariya ta soma da kwallin sannan ta feshe jikinta da turaren mai kamshin ‘yan bori, wanda aka tabbatarmusu cewar Deen zai ji ba kamshin da ya fi so anan duniya sai shi. Daga haka ta fita ta sameshi, ai kuwa yana ganinta ya budemata kofa ta shiga. Nan take ya ji wutar kaunarta na k’ara ruruwa cikin ransa, sun sha hira inda ya matso dab da ita yana jin kamar ya sanyata jikinsa saidai ganin idanin mutane dake kansu yasa ta tsawatarmishi. Ya sanarmata cewa da zarar ya koma zai turo magabatansa, wannan yafi komai yi mata dadi don ta lura ya shiga hannu ta yanda shi kansa kwata-kwata ya bar shakkar dangin Munira su ji labari. Ya sha hira sannan ya tafi, a daren ya k’ara dawowa, har suka gaisa da Malam Yahuza wanda ya yita mamakin ganinsa kuma da sunan ya zo wurin diyarsa. Koda ya shiga ciki ya tambayi Habiba, ta sanarmishi ai da aure ya ke sonta. Hankalinsa ya tashi da wannan amsa da ya samu, ya so nuna rashin goyon bayansa saidai ba shi da wannan isar a gidansa, sai ma ya tsinci bakinsa da furta kalaman nuna jin dadin al’amarin ba don har cikin zuciyarsa hakan bane. Ita kuwa Dija da Deen murzar juna sukayi son ransu, dakyar suka rabu. Washegari Baba Habiba ta nufi wajen aminiyarta ta sanarmata komai, shewa Saude ta yi don abin ba k’aramin dadi ya yi mata ba. “Kice lokaci ya yi? Ai karku damu da abinda mutane zasu ce matar mutum fa kabarinsa, atoh.” Dariya Habiba ta yi tana dan waige-waige. “Wai ina Mariya ne ban ganta ba tun zuwana?” Saude ta murmusa. “Mariya kuma da farin jini, tana nan zaune Dauda dan gidan Zinaru ya aiko kiranta.” Habiba ta dan yi jim. “Anya Saude? Dauda fa kamar na ta6a ji ya yiwa wata budurwa ciki?” Saude ta girgiza kai. “Bar mutane da shegen karya Habiba, yaron nan har nan ya ke zuwa mu gaisa, kar kiso kiga irin kyautatawar da ya ke yiwa Mariya. Kuma banda abinki, yarinya da bata fi shekara tara ba?” Habiba ta jinjina kai. “Shikenan, amma gaskiya ki saka idanu.” Saude ta gamsu da zancenta.2 *** *** *** ABUJA Washegari Faruk da wuri ya tashi kawai don ya ga Umminsa. Ai kuwa yana sanya kai a falon Hajiyarsa na sama ya yi tozali da ita tana aikin shara. Ta dago kanta jin sallamarsa, ta amsa a hankali sannan ta russuna ta gaisheshi. “Lafiya, kin tashi lafiya?” Ta amsa da murmushi dauke saman fuskarta. “Alhamdulillah.” Ya dubi falon sannan ya dubeta. “Kai Ummi, duk girman falon nan haka kike share shi? Sannu kinji? Karki damu na wani dan lokaci ne.” Ta dubi hanyar dakunan mutanen gidan, (Hajiya tana sashen mijinta)sannan ta dubeshi cikin murya k’arama ta ce. “Ka yi hakuri ka kyaleni don Allah kaga a falon Hajiya ne, komai zai iya faruwa.” Ya ta6e baki yana mai gyara tsayuwarsa. “Ke ni na soma gajiya da wannan tsoron naki, me kike tsoro ne alhalin wataran gidana zasu daukoki su kawo? Kalli,(ya dubi jikinsa sannan ya maida dubansa gareta, ko wanka banyi ba na zo kawai domin na ganki ki ji dadi shi ne kike korata, why?” Maganar ma ta so bata dariya saidai kasancewar ba a nutse ta ke ba yasa bata dara ba, wato don ta ganshi ta ji dadi? “Na ganka amma don Allah ka bar…” Jin motsin murda kofar dakin kwanan su Ikram ne yasa ta saurin juyawa ta cigaba da shara. Ihsan din ce ta fito daga ita sai riga iyaka gwuiwa da dogon wando (cotton) na bacci. Kanta ko hula babu, Faruk ya juyo yana dubanta. Ta karemishi kallo daga shi sai dogon wando na bacci da singilet, yana tsaye hannuwansa cikin aljihun wandon, ya kauda kansa daga gareta, ta fito cike da mamakin abinda ya kawoshi da safe bayan ta riga tasan baya fitowa sai ya yi wanka ya shirya, ta kai dubanta ga Ummi, shara take yi abinta, babu wani abu da ta gani wanda zai sa ta tsargu cewar akwai wata a k’asa, saidai zuciyarta ta kasa nutsuwa akan ganin da ta yi mishi tsaye kuma shi kadai tare da Ummi. A sanyaye ta gaisheshi, ya gyada kai, daga haka ya juya ya fice. Ta bishi da kallo kafin ta dubi Ummi wacce ta yi kamar batasan wainar da suke toyawa ba. Karasawa ta yi ta tsaya a gabanta tana mai take tsintsiyar, Ummi abin ya bata haushi, ji ta ke kamar ta tureta ta fadi k’as. Saidai a fili bata nuna komai ba, ta dago ta dubeta fuskarta ba walwala babu kuma fushi. Ihsan ta watsamata kallon tsana don ta lura yarinyar kamar ta k’ara gogewa a yan kwanakin da ta yi a Abuja. “Tun yaushe Yaya Faruk ya shigo?” Abin ya so bawa Ummi dariya, ta barwa cikinta. “Yana zuwa kika fito falon.” Ihsan ta dan yi sakato tana dubanta kamar dai bata yarda ba don jikinta ya bata akwai wani abun, sai kuma ta ja tsaki. “Koma dai menene, mutum ya kiyaye yasan matsayinsa.” Ummi ta dan rausaya kai. “To me ya kawo wannan maganar kuma?” Cike da mamaki Ihsan ta dubeta. “Eh lallai, har anzo ga6ar da zan fadi magana ki tuhumeni akanta? Lallai wuyanki ya soma kauri.” ‘Tukunna ma dai Ihsan, matukar zaki cigaba da gasamin magana za kico karo da fin haka.’ A fili kuwa ta ce. “Allah Ya baki hakuri.” Wawan tsaki ta ja ta yi gaba ta zauna saman kujera gami da kunna talabijin, daman abinda ya fito da ita kenan, kallon wani(series)na ‘yan Philippines wanda bata samun kallo da dare sai karfe takwas na safe suke maimaicin sati duk ranar lahadi. Ummi murmushi kawai ta yi sannan ta cigaba da shararta zuciyarta wasai. Zaune ta ke a (Garden) tana wanke kayanta kala daya, tana yi tana dan wak’e-wak’enta. Bata da masaniyar cewa Faruk na daga barandarsa yana kallonta, a gabansa abin zane ne. Ya jima yana dubanta da murmushi dauke a saman fuskarsa kafin daga bisani ya hau zanata. Iyakar fuskar kawai ya zana, bayan kammalawarsa ya mike ya sauka. Ba zato ta ji shi zaune a gefenta saman kujera. Ta dubeshi gabanta na dukan uku-uku sannan ta dubi hanya. “Kar6i wannan kiga, hoton matar da zan aura ce.” Gabanta ya fadi, ta dubi takardar da ya kanannad’e sannan ta dubeshi, shi dinma ita ya ke kallo da son lura da yanayinta. Murmushin yak’e ta yi. “Hannuna da ruwa, kada na jik’a maka.” “Kar6i ba komai.” Ta sa hannunta wanda ya soma rawa ta kar6a. Koda ta bude, kallon tsoro ta yiwa zanen don kuwa wani kishi ta ke ji yana sukar zuciyarta. “Ta yi kyau, Allah Yasa alheri.” “Ameen, nagode.” Ya fada yana dubanta, ya tabbatar bata kalli zanen sosai ba, wannan alamu ne na tana sonshi kuma tana kishinsa hakan kuma ya mishi dadi. Ya dan lek’a fuskarta. “Za ki halarci bikin?” Ji ta yi kamar ta kai mishi bugu, ashe komai da ya ke fadamata a baki ya tsaya? Daman itama ta yi wautar daukar zantukansa ta saka a rai. Yaudarar kai kenan. Ta kauda fuskarta gefe. “Um.” Ya yi wani murmushi. “Mungode.” Daga haka ya bar wajen, ta bi bayansa da kallo, daidai da fatarsa fara k’al kalar ‘ya’yan hutu ne, ina ita ina shi ne? Bata kyautawa kanta da rayuwarta ba da har ta bari kaunarsa ta shiga ranta. Ta k’ara duban takardar cike ba tayi wata-wata ba ta d’aga da zummar yagawa saidai me? Karo ta ci da wata mai kama da ita, ta zaro ido tana k’ara duba sosai, shakka babu ita ce, har dan lotsawar kumatunta. Kunya ta kamata, shikenan Faruk ya gane tana kishinsa tunda har ta kasa 6oyewa. Kamar ance ta daga kanta, sukayi ido hudu da shi daga barandarsa. Ya kashemata ido daya, ta yi saurin mikewa ta bar wajen tana murmushi tare da mamakin yanda akayi har ya isa ga dakinsa, kodayake ba wani nisa ne daga nan ba. Ta adana takardar cikin kayanta, saida ta tabbatar ya bar wajen sannan ta koma ga aikinta. Ihsan ta dubi Ihsan fuska a washe. “Kina ganin hakan yafi?” Ikram tana murmushi ta gyada kai. “Kwarai kuwa, ke kanki kusan komai zai fi zuwar miki da sauki, kinga cikin kyautar da za ki ba shi sai ki isar da sak’onki ta nan.” Ihsan harda tsalle ta yi ta rungume Ikram. “Yaushe ya kama ranar haihuwar tasa?” Ikram na dariya ta amsa. “Jibi ne, sha shida ga watan (March), kada mu sanarmishi batun fatin, ya kasance mun bashi mamaki, saidai ya dawo gida ya tarar da komai.” Sukayi dariya. “Daidai kenan.” Cewar Ihsan. “Naji, taso muje mu yi shawara da Hajiya.” Koda suka je, batun fatin kawai suka sanarmata, nan kuwa ta basu goyon baya dari bisa dari don Faruk tun yana da shekaru ashirin rabon da ayimishi wani birthday party. Ta taimaka musu da kudade suka soma shiri da sanin Daddy da yayyunsa maza har ma da matansu. Duk uban gayyar ma baida labari, asalima ya mance da wani batun ranar haihuwarsa da ta kusan zagayowa. *** *** ***

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *