WATA BAKWAI CHAPTER 12

WATA BAKWAI CHAPTER 12

  Da safe tunda tai sallar asuba ta kasa bacci. Ta saba a wannan lokacin ko basuyi waya da ammar ba zai mata text kamun ta koma bacci. Wanka tai tasa kaya. Kwalliyar datai bamai yawa bace. Ta koma ta kwanta. Tuno ammar kawai wani zafi zuciyarta take. Saboda kuskuren da sukai ta aikatawa. Kalar kalaman da suka dinga gaya juna da igiyar aure akanta da ta dabaibayega ga barin ko da daga murya ne ga namijin daba muharraminta ba. Ballantana kalamai masu zafi. Batai kokarin tarbe hawayen da suke zubo mata ba. Qwanqwasa kofar dataji anayi ne ya katse mata tunanin da take. Hawayen dake fuskarta ta goge sosai ta dai daita muryarta sannan tace “shigo” a hankali. Turo qofan yayi. Harya tako yazo bakin gadonta ya zauna bata dago ta kalle shi ba. Batai zaton shi bane saboda tasan laifin datai masa. Da ka yanda ko kallonta baya sonyi duk jiya. “Hussy…….” Ya kirata da wani yanayi da saida taji yarr a jikinta. Dagowa tai ta kalle shi. Fuskar shi dauke da mamaki yace “kukan me kike?” Wasu hawayen taji suna shirin zubowa. Kamin tai wani abu ya tallabi fuskarta da hannayensa. Baya son kukan nan ko kadan. Yace “Everything is gonna be okay…..banson kukan nan kinaji!” Daga mishi kai tai alamar eh. Ya lumshe idanuwansa ya bude su. Cikin taushin magana yace “hussy banson ana amsamin magana dakai, idan na miki magana ki bude baki ki amsa ni” “Kayi haquri” Ta fada muryarta na rawa. Sakin mata fuska yai. Duk yanda yake jin son ce mata ya yafe mata ta daina damuwa ya danne. Kwali ne gefe bama ta kula da shi ba. Ya dauko ya dora akan jikinta. Ya soma magana “Kiyi hakuri da daga hannuna danai akanki. Ki yafemun….” Bude baki tai zatai magana dan bataga me yasa yake bata hakuri ba ya daga mata hannu alamar ta saurare shi kawai. Yaci gaba da fadin. Kiyi hakuri da wannan wayar. Akwai sim da komai a ciki. Nasa a kawo miki irin ipad dina.Cikin week din nan. Munyi alqawari da Saurayinki…….! Yanda ya ja kalmar saurayinKI din saida yasa ta dan razana. Kamin ya ci gaba da fadin “so zaki iya daraja dokokin Allah dayake kanki na aure badanni ba dan banda wannan mutuncin a idanuwanki har zuwa lokacin da alqawarinmu zai cika” Shiru husna tai wasu hawayen nason zubo mata. Idan har tace baida daraja a idonta karya take. Tayi shiru ne kawai dan tasan yanzun bazai yarda da duk wani abu dazai fito bakinta ba. Kuma bataga laifinshi ba Jin tayi shiru ta sadda kanta qasa yasa shi saka hannu ya dago da habarta. “Kar hawayen nan ya zubo fa” Ya fadi. Wata sumba mai taushi ya manna mata a kunci. Sannan ya sakar mata fuska. STORY CONTINUES BELOW Jin wani dumi da wajen ya dauka yasa husna kai hannu ta shafa ta tabbatar babu abinda ya samu wajen. Yana kallonta gira ya daga sama cikin alamar tambaya sannan yace mata. “Gogewa kikai?”1 Kai ta girgiza masa. Da sauri tace. “A.a” saboda ta tuno kashe dinshi. Daure fuska yai. Tai raurau da ido kaman zatai kuka. “Ki shirya zamuje wajen Nas” Bai jira amsarta ba ya tashi ya fice. Ta sauke wani numfashi. Dan tun jiya wani tsoro tsoronshi take jima. Yanzun sai taji ya rikita mata lissafi duk ta daburce. Hannu takai zata sake taba kuncinta ta fasa. * Wajen Nas suka wuni. Yauma kaman jiya bacci yake yi har dare da suka taho bai farka ba. Wani sha mata kamshi yake. Tunda yabata wayar magana bata sake hadasu ba. Fuskarshi normal. Kawai dai batajin dadin yanda yake shareta. Sai takejin lefinta like a fuskarta. * Suna hawa sama ta soma takawa zuwa bangarenta ya kira sunanta. Wani yarr taji. Muryarshi ta wani kara budewa ganin ta juyo yace. “Zo” A hankali ta taka inda yake ta tsaya. Matsawa yai kusa da ita sosai ya hade space din data bari. Kan kirjinshi take sauke numfashi. Zuciyarta na wani irin dokawa. Kanta a kasa. Saida yadan kwanto kanshi sannan ya sumbaci kuncinta. Cikin kunne a hankali yace mata. “Ki kalle ni” Yanayin yanda take ji da yanda yai maganar ne ya sata kasa musama umarnin shi. Idanuwanta ta sauke cikin nashi da suka wani shige ciki. Wani irin dumi taji gaba daya jikinta ya dauka da tasan ba zazzabi bane. “Good night” Ya fadi muryarshi tana wani amsawa cikin kunnuwanta. Kamun ta gama sanin me yake faruwa yabar falon. Kujerar wajen ta kama ta zauna. Tana maida numfashi. Batasan meke damunta ba. Tadai san kafafuwanta ne basu da karfin kirki. Takai mintina goma a wajen sannan ta iya tashi ta koma dakinta da wani yanayi da ya dasa mata. * Juye juye kawai yake kan gadon shi. Rabon dayaji wannan yanayin harya manta. Hussy…..huddy ya rasa meye hakane yakeji. Bai taba zaton cewar zai sake samun soyayya ba sai yanzun.Abin har tsoro yake bashi. WATA BAKWAI 7 kawai ya dauka.Alqawari abune mai girma. Bacin raine ya saka shi ya dauki alqawarin da yake jin bazai iya cika shi ba. Abinda yasan ya zama dole a gare shi yanzun shine ya koyawa hussy soyayyarshi. Hakan abune mai matuqar sauqi a wajensa. Duk da kishi yana damunshi. Yana kishin ammar da yasan ta gama furtawa kalamai da baya son zuciyarsa ta soma qiyasta masa. Yanzun daya ganta. Yanayin yanda ta nuna rauni. Idanuwanta….komai nata ya kasa jurewa. So kawai yake yajita a jikinsa. Addu.a ya dinga yiwa huddynsa. Tabarshi da kewarta da yasan har abada bazai daina ba. Sai dai yanzun yana jin ya karbi rashinta a abu rubutacce. Yanzun yakan mata addu.a fiye da da. Kuma yana godiya ga Allah daya bashi damar sanin ta a rayuwarsa. Ya sauke ajiyar zuciya ya lumshe idanuwansa. Ya so huddy so mai yawa. Ya tuna wani lokaci can baya. *** *** Hawaye yaji suna bi masa fuska. Why? Meyasa za.a canza wannan tsarin a zamaninsu. Bai taba son sarauta ba. Babu komai cikinta sai wahala da rikici. Duk ya gama sakankancewa akan mulki bazai taba juyowa kanshi ba. Duk a ture wannan ai bashi bane babba da za.a nada shi a matsayin magaji. Dafa mishi kafada yaji anyi. Hannunta ya fita daban dana kowa.Don yakanji tabawar da duk zata masa har ranshi. Juyowa yai ya kalleta. Hannu tasa tana goge mishi hawayenshi. “Yaya kana so nayi menene? Ka daina. Komai ya faru akwai dalili. Hikimomi na Ubangiji suna da yawa sosai. Sun wuce tunani. Ba zamu taba fahimtar hakan ba. Sai dai muyi qoqarin gode mishi da addu.a ya kawo mana komai cikin sauqi” Baya taba nuna rauni a gaban mutane. Amman huddy dabance. Duk da qarancin shekaru irin nata in tana wani abun har mamakinta yake Janyota yai ya zaunar da ita gefen shi. Yanda yakeji a kanta yanzun yasa sai dole yake bari jikinsu na haduwa. Idan ita da karancin shekaru a tattare da ita. Shi babu. A hankali yace “huddy ba zasu fahimta ba. Bana son nauyi. Bana son mulkin nan saboda yana da rikici sosai. Zasu iya komai kan shi. Bana so wani abu ya sami………” Kamin ya qarasa ta rufe mishi baki da hannunta. Cikin idanuwanshi ta kalla sannan tace “Allah yasa zabin dayai maka shine mafi alkhairi a lahirarka da duniyarka. Allah ya daukaka ka. Daukaka mai daraja yayana. Karkaja da Ikon Allah. Ka gode masa kawai”1 Alhamdulillah! Ya furta a fili. Duk da hawayen da yakeji bai hana shi murmushi ba. Allah ya kai Rahma kabarinki hudisa. Zai iya rantsewa yanajin muryarta cikin kunnuwanshi tana masa dariyarta kan abinda yakeji game da hussy Da murmushi a fuskarshi Bacci ya dauke shi cike da mafarkin hudeesa da husna. Da wuri ya shirya yau saboda zuwan su mumyn Nas. Ya fito zuwa babban falonsu. Wayarshi ya dauko.Ya kira num din husna dayai save tun jiya. Ringing biyu tai ta dauka. Cikin sanyin muryarta tai mishi sallama. Ya amsa “kin tashi lafiya?” Ya buqata. “Alhamdulillah” “Ina babban falo” “Owk tam barin fito” Bai amsa ba ya kashe wayar. Ya sauke wani numfashi da baisan dalilinsa ba. * Shigarta simple cikin doguwar riga irin ta mutanen sudan pink wacce tai matuqar karbarta. Har inda yake ta qarasa. Ta samu waje ta zauna. “Ina kwana ta furta a hankali” Sai lokacin ya dago ya kalleta.Ta mishi wani irin kyau daya kasa fadi. “Hussy” yaja sunanta. Saida taji wani iri kaman ko yaushe. Indai zai kira sunan ta haka. Muryarsa na shigarta har bata son tasirin da take mata. “Mun gaisa yanzun fa” Yace da yanayin gajiya a muryarsa. “Hmm yaushe zamu tafi wajen nas?” Ta tambaya tana sauya maganar. Tunda ta samu yau ya soma mata magana ba kaman jiya ba. “Sai su mumynsa sun qaraso” Ya amsa a taqaice. Jingina tai da kujerar sosai. Kowa yai shiru. Can ya nisa yace “hussy kiban labari shirun nan ya isheni” Yakan bata mamaki haka rannan wai ta bashi labari. Ita kam wanne labari zata bashi. Dan dai yau bata son su wuni irin jiya. Tana son yadan mata magana ta samu damar da zata sake bashi hakuri. “Wanne irin labari kake so?” Ta ce tana maida hankalinta kansa. Gyara zama yai ya kalleta yace “ko wanne iri ma” Yanda yai da fuska ya bata dariya sosai. Ya sake wani tabare fuska. Saita tsinci kanta da son ja masa hancinsa da ya burgeta. Wani irin kallo yake mata data kasa fahimta. Shikuma abubuwa da yawa ne suke yawo a zuciyarsa. Kewar huddy. Yana mamaki yasan soyayya. Amman akan hussy ya rasa ma ko meye a yanzun. Dan wannan ya girmi so. Yakanji yanayi da dama kan huddy. Amman ba koyaushe yake kallonta yaji yana son jin duminta jikinsa ba. Sai in ita ta taba jikinsa. Amman hussy. Ko kallonshi tai da idanuwanta din nan a cikin kwanaki kadan da suka wuce sai yaji jikinsa ya dauki dumi. “Dariya ko? Zo nan” Ya fada yana nuna mata gefen shi. Da sauri ta hadiye dariyar ganin yanda fuskarshi ta sauya babu alamun wasa. STORY CONTINUES BELOW Idanuwansa ya zuba mata yana mata wani kallo. Duk sai takejin ta daban. Ga kunya da taji ta rufeta babu dalili. Ammar yakan kalleta sosai haka. Batare da taji komai ba. Amman prince ishaq. Kominsa dabanne. Shi kanshi dabanne. Da ta tsane shi amman yanzun tsanar sake kala take a hankali. Bata taba zaton cewar zata rasa kome take ji game dashi ba. Muryarsa tafi komai tasiri a kanta.Qamshinsa intaji sai taji kaman harda duminsa. Hakan nasa ta son jinta kwance kan faffadan qirjinsa. “Zakizo da kanki ko ni inzo?” Maganar shi ta katse ta. Dakyar ta matsa kusa dashi inda ya nuna mata. Kafarshi daya ya maida kan kujera ya gyara zama yanda zai fuskance ta. Yana son yanda manyan idanuwantan nan ke fitowa waje inta tsorata. Da sauri tace. “Dan Allah kayi hakuri” “Inyin hakuri dan kinmun dariya?” Ya bukata yana kallonta. “A.a kayi hakuri dan girman Allah. Ka yafemun” Sarai tun farkon maganarta yagane me take nufi. Shiru yai kaman yana nazarin me tace. Bayan tun shekaranjiya ya gama yanke hukunci. “Dan Allah….. ” Ta sake fadi muryarta na rawa. Dan tana tsoron me zatace ma Allah inta mutu a yanzun. Laifinta mai girma ne. “Fine…. ” Yace yai shiru. Ganin bashida niyyar sake cewa wani abu yasata fadin. “Haba mana gentle. Fine fa kawai kace” Wani juya mata idanuwanshi yai a yangance yace. “You need to sweat a bit more….fine for now” Batace komai ba. Zata dauki fine din a yanzun. A hankali zai furta ya yafe mata da kan shi. “Uhum ina jinki” Ya fadi yana sake gyara zama. Muryarta a hankali tace.1 “Nikam wallahi na rasa labarin dazan baka. Film? Littafi?” Daga mata kafada yai alaman duk wanda yai mata. Muryarta a nutse ta soma bashi labarin “Knock knock by james hardley chase” Tunda ta fara idanuwanshi ne kafe kan labbanta. Yanayin yanda suke motsawa da duk kalmar da take fada. Idan kaganshi zaka rantse wani abu yake karanta daga labban nata. Kula tai kaman ma ba sauraranta yake ba. Fuskarta kawai yake nazari. Hakan yasa tace. “Wai kana ma jina ne?” “Inajinki mana. Massino ya zauna daram kan power yana controlling duka unions” Tai mamaki dan bata ma zata yanaji ba. Langabe kai tayi tace masa. “Zan karasa maka anjima. Bakina ya gaji” Baice mata komai ba kallon fuskarta kawai yake. Labbanta da bai taba karema kallo ba ya zuba ma ido. Ba karamin ja mishi hankali sukai ba. Hannunshi yakai yasa yatsan shi ya zagaye yana dangwalo man dake lebenta. Husna ta wani daskare waje daya. Banda bugun zuciyarta da take ji har cikin kunnuwanta. Kallon yatsan yai. Da man daya dangwalo a jiki. Ita kuma shi take kallo. Ga mamakinta a nashi leben na kasa ya shafa sannan a hankali kaman mai gwada wani abu ya tsotse leben daya shafa ma man. Wani dumi taji jikinta ya dauka. Kawai so yake ya dandana labbanta kuma wannan ba lokacin daya kamata bane. Babu yanda za.ai ya hada bakinshi da yarinyar da bata son shi. Ko ya yake ji akanta kuwa. Hakan ya sashi dandana kalar man da yasa yaga labbanta sunyi wanu pinkish kala mai haske. Zakin dayaji me yasa shi yamutsa fuska. Kallon ta yai cikin ido yace. “Zaqi…. I mean man dake lips dinki” Harshenta tasa ta laso kaman bata taba sanin yanda man leben yake ba. Wani numfashi yaja dayasa kallon shi sosai. Ringing din wayarsa ya katse su daga duniyar da suka shiga…….! Wayar ya dauka. Mumyn Nas ce hakan ya tabbatar mishi da isowarsu.+ Dan haka yace ma hussy ta dauko alkyabbarta ta saka su jira qarasowarsu. Sai bayan ta fito ne ya kalleta yace “me kikaci?” “Bana jin yunwa” ta fadi. Lokaci daya fuskarsa ta sauya zuwa yanda ta saba ganinsa farkon aurensu kamin ta san fara.arsa. “Muje dining room din” Ya umarta. Yanayinsa ya nuna mata ba zai karbi wani uzuri ba dan haka tai gaba yana binta har suka qarasa. Zama yai yace mata “Maza ci wani abu da sauri kamin su qaraso” Babu yanda zatai haka dolenta ta danci plantain da dankalin turawa.3 Ga kunyarsa da ta tsinci kanta ciki saboda kallon da yake mata. A hankali tace “kai ba zakaci komai ba” “Na sha malt banjin saka ma cikina wani abune” Ya furta yana miqewa. Binsa tai a ranta tana fadin. Wato shi baya son sakama cikinsa wani abu. Sai ita yai ma dole. Suna fita babban falo sukaji sallama. Tare suka amsa. Da fara.ar prince ishaq ya qarasa ya tarbo su yana fadin “mumy sannunku da isowa” Cikin sanyin murya husna tace musu “barkanku da isowa” Mumyn nas ta kalleta tace “Ma shaa Allah. Sannu in-law” Dan bata taba ganinta ba. Sanda akai auren tana england dubo kanwarta da akaima dashen koda. “Ku qaraso ciki mana” prince ishaq ya fadi. Yana shirin juyawa yaji an taho da gudu ana fadin “yayaaaaaa” Kamin ya qarasa juyowa ta ruqunqume shi kaman zata karya shi. Ya lumshe idanuwansa ya budesu a hankali. Wanni aikin sai auta.Baisan da ita za.azo ba. Wani son kanwarshi yaji ya cika masa zuciya fal. Yayi kewarta sosai. “Auta saikin karya shi ke yaushe zaki natsu ne bakya ganin antynki tsaye” mumyn nas ta ke fadi tana murmushi. Auta ta sake prince ishaq tana dariyarta cikin tabara tace “mumy ai na dade banga yaya bane shisa. Laaaa antyyy wlh kin hadu” ta qarasa wajenta tana riqo mata hannu. Shafa kanta husna tai tana murmushi farat daya yanayin yarinyar harya shiga ranta. Tai bala.in kama da nasir. Waisu haka suke da shiga raine? Ta tambayi kanta. * Bayanda prince ishaq baiba ko hutawa su danyi. Mumyn Nas taqi tace suje asibitin dan da sun ganshi ba jimawa zasuyi ba komawa zasuyi. Husna tace “Haba mumy da wuri haka na dauka zaku kwana ne ai” Wai ai kam yau zamu juya in-law. Ba zamanmu nasir yake buqata ba. Addu.a ne. Tunda duk gaku anan din. Da munga yanayin jikin nasa zamu koma in shaa Allah” Haka suka haqura tunda mumyn nas sam taqi jinsu. Suka nufi asibitin. * Suna bayan mota zaune ita da prince ishaq kasancewar mota daban daban ce data su mumyn Nas tace mishi “kana ganin ya kamata auta taga Nas kuwa. Kaman shekarunta sunyi qanqanta taga tashin hankali har haka” Dan autar kam duka bata fi shekaru bakwai ba. Murmushi yai. Hannunta ya riqo.Ya hada yatsun su waje daya. Yace “ki yarda dani hussy a rayuwa irin tamu auta taga abubuwa da yawa. Wannan ba komai bane.” Saita tsinci kanta da sake riqe hannunta cikin nasa sosae. Tana mamakin hargitsi dake cikin sarauta. Lallai mutane na kuskure kan mulki. Daga nesa saikaita sha.awarsa har kana jin dama kaine matsayin. Sai yanzun take lura babu komai cikin mulki musamman na sarauta banda rashin kwanciyar hankali da tarwatsar farin ciki. * Har suka qarasa asibitin suna riqe da hannun juna saida suka fito ne sannan. Nas yanata bacci a fadar likitansa. Daqyar ma suka barsu suka shiga gabaki daya da sunce ba.a son hayaniya ta tashe sa anfi so ya farka da kanshi saboda magungunan da ke aiki. Sunkai mintina ashirin zaune shiru kawai. Kamin mumyn nas ta miqe. “Allah ya bashi lafiya” ta furta a sanyaye. Su duka suka amsa da amin. “Is he gonna be okay?” Auta ta tambaya muryarta can qasa. Tsugunnawa prince ishaq yai yanda tsahonsu yazo dai dai. Ya dafa kafadunta cikin taushin murya yace mata “we don’t know yet. Amman muna masa addu.a.” Husna ta faki ido tadanyi qasa ta mintsine shi a baya. Yaji zafi ya dake kawai ya miqe. Ta riqo hannun auta da idanuwanta suka cika taf da hawaye. Tajata jikinta. A hankali tace “karki damu zaiji sauqi in shaa Allah. Kinga bacci yake. Daya tashi zan kira mumy a waya ku gaisa.” Kai kawai auta take daga ma husna saboda kukan da yake neman cin qarfinta. Hada ido sukai da prince ishaq ta galla mishi harara. Duk shi yaja. Wannan yar yarinyar saboda Allah. * A wajen mota sukai sallama da su prince ishaq aka tafi a mayar dasu airport subi jirgin dazai koma kano qarfe 12. Saida suka shiga mota su kadai sannan ta juyo ta kalle shi sosai a dake tace “meke damunka?” “Me nai maki zaki mintsine ni” Ya buqata shima a dake. “Saboda me zaka fada ma auta cewan ba lallai bane nas ya tashi. Baka ga tai qaranta ba?” Husna take fadi ranta a bace. Shi sai yaga ta qara kyau yanda ta dage tanata masifa. Baisan sanda dariya ta kubce masa ba. Ta sake hade rai duk da kyau da taga ya qara mata. Inyai dariya takan bayyana farin cikin a fuskarsa da wani kwarjini naban mamaki. Bata san lokacin data ja mishi hanci ba. Ya ture hannunta yana fadin “oww hussy da zafi fa” Ammar! Zuciyarta ta furta a hankali. Dannewa tai ta kalli prince ishaq dake gabanta. Tace “abinda kai baka kyauta ba sam” Da yanayin muryarta yace “ni bazanyi qarya ba” Dariya ya bata sosai. Ya tsaya yana kallonta. Komai nata yasha ban ban dana huddy. Komai da yake ji a kanta dabanne da yanda yaji akan huddy. A lokaci daya kuma su dukansu sunyi tarayya a zuciyarsa wajaje daban daban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *