DAN ADAM CHAPTER 17
KADUNA Munira tana zaune ta kurawa talabijin ido, saidai gaba daya hankalinta baya tare da kallon, Tasleem da Haris sai wasa da keke sukeyi ko kusa basu da wata matsala. Babban damuwarta bai wuce na auren da Deen ya sanarmata zaiyi ba da macen da sai su share awanni uku cikin dare suna waya, har yau batasan wacece ba saidai babu irin cin kashin da bata gani daga gurinsa tun soma soyayyarsa da yarinyar. Tunaninta ya katse sa’ilin da wayarta ta dauki k’ara. Ganin lambar yar uwarta Atika mai aure a Ringim yasa ta rage k’arar talabijin gami da dauka. Bayan sallama ko gaisawa Atika bata bari sunyi ba ta soma magana. “Wai kuwa Munira kinsan abinda ke shirin samunki kuwa?” Munira ta kara gyara zamanta kafin ta saki murmushi mai ciwo. “Na sani Yaya, to ya zanyi? Aure kaddara ce ai, shi ya sani.” Atika ta saka salati. “Ikon Allah, oh ni Fatima, ba dai kema sun shanyeki kamar yanda suka shanye Deenin ba? Wallahi na tausayawa rayuwarki Munira, cab!” Munira ta ji gabanta na dukan tara-tara. Daman ya lafiyar giwa…. “Yaya wai me kikeson cewa? Ko kina da labarin wacce zai aura ne? Ni wallahi nan da kike gani ko sunanta bazan iya kawomiki ba don a Yanzu bai daukeni wata abar ba yanzu ballantana ya sanarmin.” “To wallahi Munira bacci bai ganmu ba, tashi tsaye ya dace muyi da addu’a, Deeni ba kowace zai aura ba face Dijar Baba Yahuza.” Jin zancen ta yi tamkar saukar aradu, wani salati ta saka da karfi kafin kuma ta yi wurgi da wayar ta zube anan ta hau kuka. A guje yaranta suka yo kanta tare da Asiya mai tayata aiki. “Lafiya Hajiya?” Ta kasa barwa cikinta, ta sanarwa Asiya matsalar da ta ke ciki yanzun. Asiya ita kanta hankalinta ya tashi ainun, daman ta zargi hakan tsakanin Dija da Oga, ita take ganin yanayin muamalarsu a gidan. Ta yi ta bawa Munira hakuri, karshe dai ganin yaranta sun shiga damuwa ta mike ta dauki wayarta da ke faman ruri ta yi daki. Atika ce, nan ta shiga bata baki da nunamata addua kadai ce mafita “Yaya ai ni na hakura da zama da Deen ma.” “Me kenan kikayi idan kinyi hakan Munira? Ashe ma ta ci galaba kenan, kada ki soma wannan bahagon tunanin.” Daga haka sukayi sallama. Munira ta cigaba da kuka har ta gode Allah, lallai DAN ADAM butulu ne, kayi mishi alheri ya sakamaka da sharri, ko a mafarki bata ta6a hangen haka ga Dija ba, bata ta6a kawowa zata ci amanarta har haka ba. Wannan rayuwa da me ta yi kama? Ta jima cikin wannan hali har dawowar Deen daga wurin aiki bata iya komai ba. Daman ba wani nemanta ya ke yi ba yanzun, taso zuwa ta sameshi saidai kuma ta ga rashin alfanun hakan. Wannan yasa ta zuba ido ganin yanda lamuran zasu cigaba da kasancewa, mik’awa Allah lamarin shi yafi kamar dai yanda Yayarta ta ce.+ *** *** *** ABUJA Intisar sanye cikin riga doguwa ‘yar kanti, ta ci kwalliyarta daidai misali ta fito daga kicin dauke da kwanukan abinci ta jera saman tebur inda Haidar da Faruk ke zaune. Ta gaida Faruk ya amsa shima ya gaisheta. Abin ma ya basu dariya. “Ba dariya, matar yaya ta ke ai.” Haidar ya harareshi da wasa. “Sai yanzu ka sani?” Dariya kawai ya yi, Intisar dai bata saba irin wasan da Faruk ba don bai fiye sakarmusu ba, murmushi kawai ta danyi. Bayan ta gama(serving) dinsu ta bar wajen. Saida suka kammala ci sannan suka wuce masallaci bayan dawowarsu ne suka zauna a falon Haidar. Haidar ya dora kafa daya kan daya. “Ina sauraronka.” Faruk ya mik’a mishi waya. Haidar ya kar6a yana kallo, ido waje kuma ya ke kallonsa. “Wannan kamar Ummi yar aikin Mami.” Faruk cikin jin zafin yar aikin da ya kirata ya jinjina kai. “Yes itace, a wurina ba ‘yar aiki bace, budurwar da nake shirin aure ce, ita kuma nake son ta zama surukarku.” ABUJA Intisar sanye cikin riga doguwa ‘yar kanti, ta ci kwalliyarta daidai misali ta fito daga kicin dauke da kwanukan abinci ta jera saman tebur inda Haidar da Faruk ke zaune. Ta gaida Faruk ya amsa shima ya gaisheta. Abin ma ya basu dariya. “Ba dariya, matar yaya ta ke ai.” Haidar ya harareshi da wasa. “Sai yanzu ka sani?” Dariya kawai ya yi, Intisar dai bata saba irin wasan da Faruk ba don bai fiye sakarmusu ba, murmushi kawai ta danyi. Bayan ta gama(serving) dinsu ta bar wajen. Saida suka kammala ci sannan suka wuce masallaci bayan dawowarsu ne suka zauna a falon Haidar. Haidar ya dora kafa daya kan daya. “Ina sauraronka.” Faruk ya mik’a mishi waya. Haidar ya kar6a yana kallo, ido waje kuma ya ke kallonsa.+ “Wannan kamar Ummi yar aikin Mami.” Faruk cikin jin zafin yar aikin da ya kirata ya jinjina kai. “Yes itace, a wurina ba ‘yar aiki bace, budurwar da nake shirin aure ce, ita kuma nake son ta zama surukarku.” “Kasan abinda ka ke cewa kuwa?” “Kwarai kuwa, Ummi nake so da aure.” Haidar ya dan yi jim kafin ya girgiza kai cikin sauyin yanayi, “Bazai yiwu ba.” “Saboda ita ba mutum ba ce?” Faruk ya jefamishi tambayar rai a 6ace. Haidar ya dafa kafadarsa. “Cool down mana, ba nufina wai wani abin daban ba, saidai matsayinku ya bambanta, wannan abu ba mai yiwuwa bane, ka chanja tunani Faruk, da kamar wuya su Daddy su yarjemaka.” Faruk ya murtuk’e fuska. “Haka kake gani?” Haidar da mamaki ya ke kallonsa. “Kai baka gani?” Ya girgiza kai gami da kwantar da kai jikin kujera. “Ban ta6a hangen hakan ba, ban kuma sani ba ko don na riga na yi nisa a kaunarta ne yasa ban gano ba? Ni yanzu kai na zo ka ban shawarar wanda ya dace na soma tunkara tsakanin Hajiyarmu da Daddy?” Haidar ya shafi goshinsa yana kara duban hoton Ummi sannan ya dubi Faruk. “Ka sanarwa dukkansu alokaci guda. Ni a raayina, banga aibu a auren Ummi ba, na lura yarinya ce nutsastsiya sannan tana da kyawun hali da na fuska. Matsalar dai iyayenmu, idan sun amince shikenan, bansan raayin Babban Yaya da Dakta ba.” Faruk ya dan ta6e baki. “Nifa zan zauna da ita. Shawara kawai daman na zo nema awajenka, ka kuma tayani adduar samun nasara akansu.” Haidar ya gyada kai yana dan murmushi. “In sha Allahu, mai Ummi, zan tayaka. Amma wacece H din da ka zana?” Faruk ya dan dara gami da kashe ido daya. “Hasiya, real name dinta ne. Sunan mum dinta ta ci, amman ta rasu yanzu.” “Kai Nawan.” Cewar Haidar gami da ba shi hannu suka cafke kamar wasu abokai. “Wato komai nata ka sani? Duk ta yaya?” Faruk ya gutsira mishi labarin Ummi, ya dora da fadin. “Tausayinta ne ya soma rinjayar zuciyata har na soma jin sonta a raina.” Shi kansa Haidar ya tausayamata. “Allah Sarki, rayuwa kenan, kowa da inda Allah Ya ajiyeshi, babu wanda yafi wani a wajenSa sai wanda yafi tsoronShi. Allah dai Ya datar da mu.” “Ameen broda. Ni bari na k’arasa, waya nakeson zuwa na siyo.” “Na wa kenan?” Murmushi Faruk ya yi, Haidar ya dafa kafadarsa yana tayashi murmushin. “Lallai na yarda da Dakta ke cewa irinku da bakwa soyayya idan kun tashi yi to zakuyi mai ban mamaki.” Abin ma sai ya bawa Faruk dariya, har wajen mota ya rakashi sannan sukayi sallama da zummar duk yanda Faruk sukayi da iyayen zai sanarmishi. Hajiya Babba ta ajiye wayarta a gefe bayan ta gama amsawa ta dubi Ikram wacce ke zaman jiranta ta kammala. “Ina jinki.” Ikram ta yi gyaran murya ta soma magana. “Hajiya daman akan Ihsan ne.” Cike da mamaki ta dubeta. “Meyafaru da Ihsan din? Ko ta gaji da mu ne?” “A’a, daman…” (Ta kwashe tun farkon sadda Ihsan ta soma son Faruk har zuwa jiya da ta shiryamishi party na taya murnar ranar haihuwa. Hajiya Babba bayan gama sauraronta ta numfasa fuskarta dauke da damuwa. “Tun ba yau ba nasan yarinyarnan tana son Sadauki, saidai banga alamun Sadauki yana sonta ba.” Ikram itama ta jinjina kai, tasan gaskiya ne. “Amma Hajiya bakya ganin a haka ya aureta idan yaso son ya shiga a hankali?” “Kina ganin zai yarda? Banason abinda za’a zo zumunci ya lalace, matukar akayi aure ba da son ran daya ba to shakka babu zai shafi zumuncinmu abinda bazan ta6a fatan naga ranarsa ba kenan.” Ikram ta yi mamakin abinda Hajiyarsu ta ce, duk da tasan gaskiya ne, amma ai ya dace ta duba alak’a. Ita shaida ce akan yanda Hajiya ke tsananin kaunar dannata, batasan 6acin ransa tun yana karami kamar yanda ta samu labari daga yayyunsu. Ta bude baki zatayi magana Hajiya ta dagamata hannu. “Ya isa hakanan, sai naji ta bakinsa, banason yi mishi katsalanda a lamari irin haka. Musamman lamari irin wannan na aure.” Jiki a sanyaye Ikram ta mike zata fita daga dakin, ta dakatar da ita. “Maganar ta tsaya iyaka nan, ban yarje miki sanarwa Ihsan ba.” Ikram da ta rasa bakin magana, kai kawai ta gyada sannan ta fice har lokacin mamakin Hajiyarsu bai saketa ba, ko babu komai naka ai naka ne, saidai batasan hukuncin da zata yanke ba. Mintuna k’alilan da yin hakan, Faruk ya dawo gidan a gajiye, kai tsaye sashensa ya nufa ya yi wanka ya sanya doguwar jallabiya ruwan madara da wando kafin ya dauki wayar da ya siyowa Ummi na kamfanin HTC ya sanyata a chaji. A karshe ya nufi sashen Daddy. Acan ya iske Hajiya, suka gaisa kafin su shiga hira da iyayennasa. Can Daddy ya dubeshi. “Son shekarunka talatin a duniya, ya ci ace zuwa yanzu ka soma tunanin aure.” “Ai ina jin ya samu matar aure, bai kai da fad’amana wacece ba ko Sadaukina?” Murmushi ya yi yana mai shafar sumar kansa. “A ina take?” Fadin Daddy kenan yana mai gyara zamansa don yasan dagasken ne don dannasu koda wasa bai ta6a zancen kowace mace ba. “Ba ta yi nisa da mu ba sosai Daddy.” Hajiya da Daddy suka dubi juna, kafin su dubeshi. “Ko ‘yar gidan Alhaji Hamza? (Makwafcinsu)” Ya yamutsa fuska. “A’a, asalima ita ba ‘yar garin nan bace.” “Wacece kenan?” Hajiya ta tambaya. Ya yi shiru can kuma ya sunkuyar da kai. “Zan kawomuku ita ku ganta cikin satinnan In sha Allah.” Suka gyada kai lokaci guda. “Allah Ya kaimu.” Fadin Daddy. Faruk da Hajiya suka amsa da amin, ita kuwa Hajiya ta soma tunanin kodai Ihsan ce? Washegari Ummi ta kammala aikinta, tana shirin barin wajen Hajiya ta shigo, bayan ta gaisheta ta dakatar da ita da fad’in. “Ina jin zuwa Asabar zaki koma fa, ba don naso hakan ba sai don Madina da ta takura da zama ba mai tayata wasu hidindimun, ta ce yanzu ba wata matsala. Zuwa gobe za’a kawomin wata.” Gaban Ummi ya fad’i, jikinta ya yi sanyi matuk’a. Shikenan ta kusa rabuwa da ganin sanyin idanunta. A fili ta k’irk’iro murmushi wanda ya yi kama da na yak’e. “To Hajiya, Allah Ya kaimu.” “Amin.” Daga haka ta bar wajen da saurinta, tana zuwa (garden) ta zauna a kujerar da ta saba zaman wanki, ta ajiye bokitin mai dauke da tsummokarai, shiru ta yi tana tunani kafin ta daga kanta tana duban barandar dakin Faruk, shikenan ta kusa daina sakashi a ido koyaushe? Hawaye suka zubomata, ta jima tana shararsu kafin ta daurewa zuciyarta ta cigaba da aikinta. A ranar haka ta wuni jiki babu kwari, daidai da Binta ta lura da hakan, tambayar duniya ta yi mata saidai amsar daya ce. “Babu komai.” Koda dare ya yi, ta taimakawa Binta da shirya tebur har lokacin bata da wani kuzari, abincin ma kasa ci ta yi sosai. Binta sai kai loma take yi, can ta dubeta. “Wai menene matsalarki ne?” Ta numfasa. “Na fadamaki babu komai, kaina ke ciwo.” Daga haka ta dan ja guntun tsaki ta mike. “Ni na k’oshi ma.” . Binta na kallonta ta wanke hannu ta bar kicin din zuwa daki. “Um, ai shikenan idan ta yi wari ma ji.” Daga haka ta cigaba da cin tuwonta. Ummi na tafe a sanyaye, wasa takeyi da jelar dankwalinta, yayinda ta fad’a duniyar tunani, ko kadan bata san inda take jefa kafarta ba, tasan dai hanyar dakinsu ta nufa. Babban damuwarta bai wuce Faruk ba, da kuma irin yanda take tunanin ko aurensu mai yiwuwa ne ko kuwa dai kawai iyakar soyayyar ce? Bata ankara ba ta ji ta yi karo da mutum har goshinta na ta6a kirjinsa, ta yi saurin ja baya a tsorace, sai kuma ta yi ido hud’u da hasken rayuwarta. Wani hadadden murmushi na gefen kumatu ya sakarmata. Sanye yake da riga marar hannu mai hula da wando(3quarter). Ta sauke idanunta kasa sannan ta russuna cikin rawar murya ta gaisheshi ya amsa sannan ya dubeta. “Zo, ke na fito nema daman, na lek’a daki ban ganki ba.” ‘Gwara da Allah Yasa ka ganni a hanya.’ Ta ayyana a zuciyarta. Ya soma tafiya zuwa samansa. “Biyoni.” Ta yi sakato tana dubansa. Har ya taka matattakala uku, ya juyo yana dubanta. Tana tsaye cak, ya dan yi jim yana karemata kallo, ita dinma shi ta ke kallo a sace, can kuma sai ta daga kafafunta da sukayi mata nauyi ta soma bin bayansa. Ganin haka ya murmusa ya cigaba da tafiya tana biye da shi tana waige, cikin sa’a Binta ta zo wucewa da sauri ta sauka ta nufeta. “Ina zuwa don Allah, Yaya Faruk ke kirana, ki rufamin asiri.” Ta yi maganar cikin rad’a, Binta ta gyada kai tana dariya ciki-ciki don wannan soyayya tasu burgeta take yi, daga haka Ummi ta juya. Tuni gogan ya shige, a falo ta iske baya nan, tun da take bata ta6a yiwa sashensa kallon tsanaki ba, ko sadda Sa’a ta yaudareta ta kawota wajen KB, sam ba’a cikin nutsuwa ta ke ba. Falon adon fari da bulu ne, ya tsaru iya tsaruwa. Anan kasan (tiles) ta durk’ushe kamar yanda kowace yar aiki ta saba a gaban masu gida. A haka ya fito rike da kan waya da kwalinsa ya iso ya zauna saman kujera. Da hannu ya yi mata nuni da gefensa. “Dawo nan Malama, saikace ba dakinki ba?” Ta saci kallonsa kawai ta dan yi murmushi kafin ta mike cikin tausayawa rayuwarsu, shikenan sun kusa yin nisa da juna duk da hausawa kance garin masoyi ba ya nisa. A kasa ta zauna saman kafet, shima ya zamo ya zauna a k’asan ta dubeshi saidai babu abinda ta ce. “Kamar kina cikin damuwa Ummina, sanardani abinda ya faru.” Mamaki ya kamata yanda har ya fahimci yanayinta. Ta girgiza kai. “Bakomai.” Ba don ya yarda ba ya gyada kai sannan ya mik’amata wayar. “Rik’e.” Ta bude tafin hannu ya dora mata a kai. “Naki ne.” Ga mamaki ta dubeshi. “Ai..ai ni ban iya amfani da waya ba.” Ya gyada kai da murmushi saman fuskarsa. “Nasan da hakan shiyasa na kiraki don koyamiki.” Ji ta yi ranta ya yi wani mugun sanyi, saidai fa haduwar wayar ya tsoratata, bata ta6a ganin irinta ba. Jin kamshin turarensa ta yi daf da ita, hakan yasa ta dagowa a razane ta dubeshi, ya matso gefenta hankalinsa naga wayar, ya kar6a daga hannunta ya soma nunamata da yacce zata cire (pattern) wanda ya sakamata saboda tsaro. Sannan ya shiga ya soma da gwada mata budo sak’onni, da amsa waya, har gwada kiranta ya yi ta ga sunan “Hubbyna.” Ya fito, bata san dai yanda zata fadi sunan a baki ba. Amma tasan wani abun ya ke nufi na soyayya. Sun dauki kusan mintuna fiye da talatin a haka har saida ya tabbatar ta iya yanda yake so, har (whatsapp) saida ya nunamata yanda zata amsa sak’onshi da mayarmishi da amsa, lambarsa kadai ce a wayar na gaba daya layukansu hudu masu tsada da ba wata diya mace da ta ta6a mallakarsu haka. Bayan ya kammala ya mik’amata kwalin. “Mun gama da wannan Ummina, yanzu maganar aurenmu ce ya ragemana.” Ta lumshe ido tana mai jin kamar ta saki ihun kuka, ya matsa yana fuskantarta. “Gobe juma’a nakeson bayyana ki ga su Hajiya matsayin wacce nakeso da aure.” Ido waje ta ke dubanshi, hawayen da ta ke dannewa tuni ya fito ya soma sauka saman fuskarta. Ji ya yi wata iriyar kasala ta saukar masa, ya runtse ido cikin kasalalliyar murya ya ce. “Please stop it mana, na tsani ganin hawayenki ya zuba Ummi akan kuma dalilin da bai taka kara ya karya ba. Idan ke kin kasa jarumtar jure koma menene zai zo wanda bana fatansa ma, ni ya kikeson nayi ne? A’a Ummi, wallahi Faruk bazai iya daukar wani tsawon lokaci batare da Hasiya ba. Na soma gajiya, ni ban iya wannan rayuwar ta 6oye abinda zuciya da gangar jikina ke muradi ba. Bazan iya ba, gobe ki shirya, ina zuwa.” Mik’ewa ya yi ya koma daki ta bishi da kallo cikin jin wani shauki na kaunarsa. ‘Kaico, Yaya Faruk an kusa rabamu.’ Ta fad’a a ranta, jikinta yana bata cewa komai ya zo karshe, watakil harda zamanta cikin zuri’ar tasu gaba d’aya, tasan maganar Antinta ya kusa tabbata wanda ta ce.6 ‘Karki manta matsayinmu awajen mutanen nan, mu ‘yan aiki ne, ba su daukemu komai ba face wannan Ummi. Bar ganin suna mana dariya, duk sadda muka bari wasu lamura suka afku ranar zasu tunamana cewar mu kaskantu ne awajensu, ranar zasu tunamana matsayinmu na marasa galihu.’ Hannunsa ta ji saman fatar fuskarta yana sharemata ruwan hawaye. Ta dubeshi, fuskarsa kai ka rantse bai ta6a dariya ba. “Kinaso muyi fad’a kenan, na tsani nayita nanata magana d’aya. Karki so ki ji yanda nakejin zuciyata idan kina kuka, amma ke naga kamar kin fison damuwata.” Karo na biyu da ta ji tana son fadamishi damuwarta. “Kayi hakuri Yaya Faruk, saidai gani nakeyi kamar an kusa yimin katanga da kai.” Ya zubamata ido baice uffan ba, hannunsa tuni ya sauke daga saman fuskarta. Can kuma ya soma magana. “Fata nagari lamiri, ki saka a ranki in sha Allah babu wani abu da zai yanke alak’armu har ya zuwa aurenmu da rayuwar auren. Banaso kina kawo komai a ranki. Yau idan da dama, kada ki rage bacci ki tashi mu yiwa junanmu addua akan Allah Ya za6amana abinda yafi alheri. Kin iya karanta istihara?” Ta girgiza kai. “Ban iyaba, saidai ina da Hisnul muslim.” Ya gyada kai. “Ki yi adduar istihara a yau Ummi, in sha Allah zamu ga daidai a lamuranmu. Ga wannan.” Ya mik’amata wata leda, ta sa hannu ta kar6a. “Shi nakeso ki saka gobe idan na kiraki a waya, kinji?” Ta gyada kai. “Yauwa.” Daga nan ya sallameta ya yi mata rakiya har suka sauka daga matattakala sannan ya tsaya ta wuce. “Zan kiraki.” Ya fada da muryar rad’a. Ta dubeshi ta murmusa ya yi mata alamun (kiss) da baki, a kunyace ta wuce da sauri. Daga haka ya koma sama. Bayan ya kammala dukkan wasu ayyuka, ya soma duba kyaututtukan da yan uwa da abokan arziki suka ba shi, sai a yau ya samu wannan damar. Turaruka sunfi komai yawa, agogo kuwa kusan biyar ya samu, wasu kuwa kayan kwalam ne har da katina kala-kala. Hankalinsa ya kai ga na Ihsan, yasa hannu ya dauka ya bude. Kamshi ya soma ziyartar hancinsa….!