DAN ADAM CHAPTER 18

DAN ADAM CHAPTER 18

  Wani hadadden agogo ne sai kuma zobe na azurfa. Murmushi ya yi sadda ta ci karo da kati mai dauke da kalaman so. Ya bude ya karanta. “My friends told me that falling in love would be the most beautiful feeling in the world. After I fell in love with you, I realized that even the most beautiful feeling in the world would look ugly against your love. Frm Ihsan Modibbo.”+ Ya ta6e baki kadan, ya cigaba da daga sauran katinan, duk kalamai ne na nuna soyayya. ‘Ya tabbata tana sona din kenan?’ Ya ayyana a ransa kafin ya lumshe ido. Baya fatan shiga matsala saboda ita, a rayuwarsa bai ta6a shaawar kasancewa da kowace mace ba face Umminsa, ta makaro, bayajin zata samu wani gurbi a zuciyarsa, saidai kuma ta dan ba shi tausayi. Ya dan ja guntun tsaki sannan ya mik’e ya tsallake kayan ya shiga harkar gabansa. Ummi kuwa tana shiga daki ta tarar Binta na zaman jira. Binta na ganinta ta mike ganin yanda jikinta ya ke duk a sanyaye. “Lafiya?” Ba ta ce uffan ba, sai kayan da ta ajiye saman katifa ta zauna, batasan lokacin da kuka ya kufcemata ba. Binta wacce ta sandare tana kallon waya hankalinta ya komo ga Ummi. “Me ya faru wai? Ki gayamin don Allah mana.” Ita dai Ummi kukanta ta ke, ji takeyi inama yau ace mahaifiyarta na raye, ta rungumeta ta rarrasheta ta kuma bata shawarar da zai taimaki rayuwarta. “Allah Ya ji k’an ki Ummana, Allah Ya yi rahma agareki, na taso ban ta6a jin dumin uwa ba, na taso cikin wahala da tsanani na rayuwa har zuwa sadda aka maidani ‘yar aiki. Babu wani mahalukin da ya ta6a rungumeni ya ji. matsalata ya rarrasheni ya min addua acikin shak’ik’aina, Babana bai ta6a tarana ya yimin fad’a akan rayuwa ba, ko sau daya bai ta6a sakarmin fuska ba, asalima kyamata yakeyi, bai ta6a tambayar Ummi ko kin ci abinci ba, Ummi zan saki makaranta, Ummi ki kula da kanki, Ummi ki tsare mutuncinki, ko sau daya babu wani cikin yan uwana da suka ta6a nunamin kulawa ko k’auna. Babu, babu su Ummana, Ummana nasan da kina raye da wasu lamuran zasuyi sauk’i agareni, ayau ga wata rana babba da nake bukatarki Ummana, saidai kinmin nisan da bazan iya kamoki ba, kin koma ga Ubangijinmu da ya fini kaunarki, babu wani da ya ta6a ban cikakken tarihinki da kyawawan dabi’unki, asalima saidai ayita aibatamin ke, ana miki kazafi. Nayi rashinki Ummana, Allah Ya yi rahma agareki.” Daga haka ta k’ara sautin kuka mai tsanani, ta cukuikuiye jikinta wuri guda, a rayuwa koda a gaba wata sila tasa Antinta Amina da yar uwansu juyamata baya, koda shima Faruk zai juyamata, bazata ta6a mance da tarin kaunar da suka nunamata ba. Sun nunamata itama DAN ADAM ce. Faruk ya gwada mata cewar itama ta cancanci komai a rayuwa, ya dauketa a mutum, haka nan danginsu gaba daya, banda matsala ta Ihsan da kishiyar Mami, babu wani abu da ta ta6a fuskanta na cin zarafi cikin zuri’arsu. Watakil a gobe zama da su zai k’are. Ta daga kai tana mai duban dakin, sheshshekar kukan da ta ji ne ya tunasar da ita cewar bafa ita daya bace a dakin. Ta kai duba ga Binta, kuka takeyi kwarai. Ta share hawayenta tana mai dukar da kanta k’as. “Meyafaru Binta?” Binta wacce zuciyarta ta cika da dumbin tausayinta ta dago kai tana dubanta. “Shakka babu ke abar a tausayawa ce Ummi, saidai ki yi hakuri, komai na rayuwa mai wucewa ne, babu abinda ya ke dauwamamme a duniya. Wataran sai labari, Ummi akwai wadanda idan kika ji matsalarsu sai ki gane naki ba komai bane, za ki gane ke lallai kina cikin rufin asiri, ina wadanda suke kare rayuwarsu a wahala babu ko digon jin dadin rayuwa? Ummi akwai matsalolin da suka sha gabannaki, wata ma iyayenta na raye uwa da uba, amma bata ji dadinsu ba ko kusa, kuma tana gabannasu. Ina ji a jikina za ki auri Yalla6ai in sha Allahu, kuma za ki ji dadi a rayuwa. Ki cigaba da mik’a lamuranki ga Allah, in sha Allahu zai magance miki. Nima ina so ki sanyani cikin layin masu kaunarki, har abada bazan cutar dake ba, wanda mukayi a baya ma, ina neman afuwarki, ajizanci ne na DAN ADAM.” Ranta ya dan yi sanyi da jin zantukan Binta masu dadi. Haka ta cigaba da yi mata ‘yan nasihu da misalai da wandanda suka fita shiga matsala kuma cikin ikon Allah ya wuce kamar baayiba. A karshe Ummi ta labartamata yanda Faruk ya ce na ta shirya gobe zai kaita gaban iyayensa matsayin wacce zai aura. ‘Tirk’ashi!’ Shine abinda Binta ta fad’i a ranta, a fili kuwa don ta kwantar mata da hankali. Ta nunamata bawani abu bane, ya dace ta koyi jarumta tun daga yanzu. Ta k’ara bata shawarar tashi tsaye da addua, inda ta tabbatar mata itama zata tayata. Ummi ta yi godiya sannan ta jawo ledar suka bude. Wani hadadden Atamfa (pink) ne mai turuwa, a wani 6angaren mai dan haske-haske, anyi dinkin riga da zani, koda Ummi ta daga rigar ta girgiza kai. “Anya rigar nan zata yimin?” “Tsaf ma kuwa, tashi ki gwada kedai.” Ba musu ta gwada, ai kam ba karamin kyau ya yi mata ba. Ta cire suka cigaba da duba ledar, harda dan kunne da sark’a fashion mai kyau da agogo, harda turare kala uku da kayan kwalliya, abin bai tsaya anan ba har dasu takalmi fari kalar mayafin da ya sanyomata. Binta banda washe baki babu abinda takeyi, ita kuwa mai abin jikinta sanyi ya k’ara yi. Wayar ta k’ara dagawa tana juyawa. “Kai Ummi ki godewa Allah, kin samu mijin da ya iya kula da matarsa wallahi.” Murmushi Ummi ta yi. “Kai Binta, har ya zama mijina?” “Haka nake miki fata ‘yar kanwata, nidai nasan gudunmuwar da zan baki a wannan lokacin idan ya zo.” Dariya kawai Ummi ta yi gami da girgiza kai, a ranta fatan hakan ya ksance takeyi. Sun dan jima tare da Binta kafin ta mik’e ta yi mata sallama don ta soma hamma na jin bacci. Bayan fitarta ta maida kayan cikin ledar ta yi gefe da su. Alwala ta d’auro ta gabatar da nafila, ta jima tana addu’o’i kafin ta shafa ta koma makwancinta. Wayar ta k’urawa ido tana jujjuyawa, ta yi nisa cikin tunani wayar ta dauki k’ara. ‘Hubbyna.’ Shine sunan da ya fito, wani ajiyar zuciya ta saki gami da yin murmushi. Kafin ta dauka kamar yanda ya koyamata yacce zata yi. Sallama ta soma yi mishi ya amsa. “Ba ki yi bacci ba, meyasa?” Ta ji daddadan muryarsa har cikin jini da bargonta. “Bakomai.” Shiru ya dan biyo baya can kuma ya yi magana. “Ina fatan ba kuka kikayi ba?” Da mamaki karara akan fuskarta ta girgiza kai. “Ni..ni banyi kuka ba.” Ya yi murmushi mai sauti. “Ni kuma jikina ya bani kinyi kuka Ummina, amman dai shikenan. Ya kika ga kayan, sunyi miki ko a chanja?” ‘Ni na isa nace basuyi ba?’ Ta fada a zuciyarta batare da sanin ya fito fili ba. “Har kin yi yawa indai awajen Umar Faruk ne. Ni ban ajiyeki nan kusa ba fa. Amma yanzu duk bazaki gane hakan ba sai bayan aurenmu.” Ta lumshe ido tana mai jin wani kaunarsa sabuwa fil a cikin ranta. “Inama hakan zata faru Yaya Faruk.” Furucin ya yi mishi dadi, ya fahimci ta soma sakin jiki da shi. “Zai faru in sha Allahu Ummina, ki kwantar da hankalinki har zuwa ranar da Umarul Faruk zai mantar da ke dukkan bakkan ciki da iznin Allah, ranar da zamu kasance mata da miji abin so da alfahari. Matukar ni ne mijinki, bazan k’ara barin ki cikin hali na damuwa ba. Watakil sai kin gaji da ni, don daga ranar da na aureki, na daina zuwa aiki.” Dariya sosai ya bata, sai gashi ta shiga yinta kwarai. Ya lumshe ido gami da k’ara rungume daya daga cikin kananun filon dake saman gadonsa. Shi kadai yasan yanda ya ke jin dariyarta. Ta tsaida dariyar cike da jin kunya. Murya kamar na wanda baya son magana ya ce. “Naso ace kina gabana kike dariyar nan Ummi, yana daga cikin abinda ban ta6a gani ba daga gareki, kuma zanso na ganin.” Ta sunkuyar da kanta tamkar yana ganinta ta hau wasa da igiyar hular t-shirt din dake jikinta. “Saida safe Yaya Faruk, bacci nake ji.” “Ko na zo?” Ta zaro ido kamar yanda ganinta, ya yi ‘yar dariya. “Matsoraciyata, na tabbatar kin tsorata. Shikenan saida safe, kiyi mana adduar fa.” “To.” Daga haka sukayi sallama. Ta bi wayar da kallo tana murmushi. A karshe ta ajiyeta gefe, mikewa ta yi ta yi nafila sannan ta karanta istihara tana kallo a takarda kafin ta shafa ta kwanta. WASHEGARI….!!!! Cikin ikon Allah ta tashi da jin kwarin gwuiwa a zuciya da gangar jiki, kaso sitti na damuwarta ya ragu. Bayan Magriba ya shigo gidan, kai tsaye sashensa ya soma nufa. Bayan ya yi wanka ya nemi Ummi a waya, tana zaune tana harhad’a kayanta sanin da ta yi cewar gobe Asabar kuma a ranar Hajiya ta sanarmata shine na komawarta Kano, wayar ta katseta. Hannu tasa ta dauka, tasan ko waye mai kiran, gabanta na dukan tara-tara ta dauka da sallama. Ya amsa sannan ta gaisheshi. “Ki shirya Ummi, na dawo ina sama, da zarar na kammala abinda nakeyi zan sauko mu je.” Ji ta yi kamar ta saki fitsari, ta daure ta gyada kai don bakinta ya yi mata nauyi. Shaf ta mance ma waya ce suke yi. “Ummi, meyafaru kuma?” Ya tambaya a sanyaye. Sai lokacin ta dan samu ta yi magana. “Bakomai, zan shirya.” Ya yi murmushi mai sauti. “Ko kefa.” Daga nan sukayi sallama. Ta yi k’uri tana duban wayar kafin kuma ta ajiyeta. “Allah ka saukaka mana.” Ta fada a fili, tana mai amsawa kanta. Shigowar Binta ya katseta, ta amsa sallamarta. Binta ta k’araso. “Naga fa Yalla6ai ya dawo.” Ummi ta yi murmushin karfin hali. “Munyi waya yanzu, yana nan kan bakansa, yanzun ma cewa ya yi na shirya.” Binta ta jinjina kai. “Sai ki tashi, hakanan za ki je kedai kiyita addua a ranki.” Ta saka kayan, Binta ta gyaramata fuskarta, ta yi mata daurin dankwali mai hawa-hawa irin na zamani. Ta taimaka mata da sanya dan kunne da sark’an. Sai kuma ta saki baki tana kallonta. “Masha Allah, wallahi Ummi na k’ara ganin abinda Yalla6ai ya hango wajenki, Ummi bakiyi kalar ‘yan aiki ba.” Ummi ta girgiza kai bata iya cewa komai ba don a yanzun ita kadai tasan yanayin da ta ke ciki. Ji takeyi kamar ta gudu tsabar rud’ani. Binta na sambatu tana feshe mata jiki dq turare, hakanan mayafinta shima ta bi ta fesheshi sannan ta yafamata akanta. Takalmin ta mik’omata ta sanya, banda Masha Allah babu abinda Binta ke kira don iyakar haduwa ta hadu, kai ka rantse dinkin aunata akayi. “Ni ganinki nakeyi kin saje da mutan gidan, babu wani bambanci.” Anan ne Ummi ta murmusa don gani takeyi kawai zolaya ce don Binta ba laifi akwai barkwanci. Suna nan zaune Binta ta bata baki wayarta ta dauki k’ara. Ta yi sakato tana dubanta, ganin zata katse yasa Binta mik’amata. “Ki d’aga mana.” Ta kar6a hannunta har rawa yakeyi ta d’auka. A kunnenta ta kara, bai bari ta ce komai ba sai cewa da ya yi. “Fito.” Ji ta yi cikinta ya bada wani sautin k’ululu. Tuni ya katse kiran, ta mik’awa Binta wayar sannan ta dubeta idanunta har sun ciko da kwalla. “Don Allah ki tayani addu’a.” Tausayinta ya kama Binta, Binta ta rik’e hannunta. “Allah Yana tare da ke, na tabbatar zai taimakeki, ki saki ranki. Komai na Allah ne.” Ummi ta mike jikinta a sanyaye ta fita. Ido hud’u sukayi da shi yana tsaye a bakin matattakala ya sanya kafarsa daya jikin bango yana danne-dannensa a waya. Ya yi mata kyau kwarai dagaske haka kuma ya bata mamaki, sai kace wasu Amarya da Ango duk yasa su yin shigar kaya masu kyau, shi dinma wani boyel fari k’al yaa sanya da hula wacce ta dace da kayan. Tunda idanunsa suka sauka akanta, ya kasa daukesu, daskarewa ya yi a wajen kawai don ya yi kamar zuciyartasa ma tsayuwar ta yi. Haka har ta k’araso wajenshi ta tsaya gefe tana wasa da jelar mayafin. Yasa hannu ya dago ha6anta, idanunsu cikin juna sannan ya kauda hannunsa. “Kinyi kyau matuk’a.” Ta lumshe ido gami da kauda kanta cikin bugun zuciya mai sauri. To Faruk ina wani kyau a wajenta idan aka had’asu? Gaba daya ganinta ta keyi wani tsami akansa, ta k’ara raina ajinta kwata-kwata, har ta hangowa kanta irin kyamar da za’a nunamata yau. Watakil ma su Ihsan su yi mata dariya. Idanunta ya yi kwal-kwal. Hannu ta ji yasa ya janyo mayafinta ya dan rufe kusan rabin fuskarta da shi. “Muje.” Ya yi maganar cikin dusashshiyar murya. A hankali suka soma takawa, Faruk shi kansa dakewa yakeyi don ba shi da yak’inin samun goyon baya, yana dai ji a jikinsa kawai zai yi nasara idan Allah Ya so. Haka har suka shigo falon Hajiya, babu kowa, daman hakan yafi buk’ata, yasan a wannan lokacin Hajiya na sashen Daddy, kai tsaye kofar zuwa sashen Daddy ya shige. Anan kofar falon ya dakata gami da umartar Ummi da tsayawa anan. Ba musu ta tsaya, ta bishi da kallo har ya shiga da sallamarsa, kirjinta ta dafe jin irin yanda ya ke bugu fiye da baya, addu’o’i kawai ta ke karantowa. Daddy da Hajija suka amsa sallamar dan nasu fuska a sake. Ya karasa yana taku a kasaitance ya zauna a gefen kafafun Daddy ya gaishesu. Suka amsa suna k’are mishi kallo. Daddy ya kasa hak’uri ya tofa. “Wai ni kodai wajen surukartawa za ka tafi ne? Wannan ado haka?” Ya shafi k’eyarsa da murmushi saman fuskarsa, Hajiya na dariya. “Daddy na je na dawo, kuma tare muke da ita ma yau za ku ganta.” Sai Hajiya ta hau salati. “Kai Sadaukina, haka kuma akeyi babu sanarwa? Maimakon ka fad’amin a shirya?” “To yanzu dai ai magana ta k’are tunda daman ya sanarmana a satinnan zai kawota, kinsan halin d’annaki komai nashi daban ne.” Cewar Daddy yana duban matarsa kafin ya maida dubansa ga Faruk. “Tana ina ne?” Faruk ya dubesu, su dinma shi suke kallo fuskokinsu a sake. Hakan ya k’ara mishi wani k’arfin gwuiwa, ya mik’e tsaye ya nufi hanyar waje. Ya dubi Ummi wacce ya tabbata a rud’e ta ke. “Addu’a zakiyi, Allah na tare da mu.” Ya fada cikin muryar rad’a. Ta gyada mishi kyau kafin ya bata hanya. “Bismillah.” Dagowa ta yi ta dan bude fuskarta ta dubeshi kamar zata yi kuka, ya jefeta da kallo mai sanyaya jiki, dole ta maida ta rufe fuskarta sannan ta saka k’afa da sallama, shima ya biyo bayanta. Iyayen suka amsa fuskarnan a sake, suka zuba mata ido har ta k’araso ta zauna, Hajiya dai gani ta ke kamar muryar da kuma tafiyar ba yau ta soma ganin irinta ba. Ta dai danne, ta amsa gaisuwar surukarta ta wacce ke ta bad’ad’a k’amshi. Kafin su kai ga tambayar wani abu, Dakta Ridwan ya yi sallama ya zo gaida iyayensa. Ya dubi Ummi sannan ya dubi Faruk yana ‘yar dariya. “Ikon Allah, ashe na zo a daidai, da rabon ayi da ni.” Sukayi dariya iyayen, shi kuwa gogan murmushi kawai ya yi. Dakta ya gaisar da su Daddy sannan aka zauna yana fadin shi fa sai ya ga fuskar surukarsu. Ikram ce ta shigo rik’e da hannun yaron Dakta, Ma’aruf, wanda ke faman rigimar zuwa wajen ubansa. Nan itama ta yi sararo tana duban Ummi. “K’araso mana, yau fa babbar bak’uwa mukayi, matar Sadaukin Hajiya.” Ikram ta dubi Hajiya, Hajiya ta kauda kanta, to me za ta ce? Idan Faruk ya ce ga wacce ya ke so ya zata yi? Batun Ihsan ne sai yanda sukayi da shi. “Mene sunanta ne?” Daddy ya tambaya. “Hasiya.” Cewar Faruk, Ummi ta lumshe ido jikinta na rawa, tana gudun ace za’a bud’e fuskarta. Ikram ta saki hannun Ma’aruf sannan ta karaso tana yar dariya na dole. “Nidai sai naga fuskar Antina.” Kafin Ummi ta yi wani yunk’uri, ta d’an bud’e mayafin ta lek’a. Zaro ido ta yi gami da bud’e mayafin gaba daya tana salati. “Me…” Kowannensu ya mak’ale tambayar da ya yi niyya sakamakon fuskar Ummi da ta bayyana agaresu. Daddy yana mata kallon sani don tabbas yana ganinta jefi-jefi a gidan, saidai baisanta a suna ba ko matsayi. Hajiya ta ji jikinta ya yi mata nauyi ta dubi Faruk, shi dinma ita ya ke kallo, gaba daya alamun tausayi, tsoro da kuma firgici sun bayyana saman fuskarsa. Ta maida kallonta ga Ummi wacce ta ke kuka sosai ga jikinta da ke kad’awa kamar mazari. “Meke faruwa ne?” Fadin Daddy yana dubansu. Hajiya ta kasa kwakkwarar magana, karshe ma ta mik’e ta nufi dakin Daddy. Ikram da ta ke duban Ummi duba na tsana ta nunata da yatsa. “Daddy wannan ba kowa bace face ‘yar aiki, a gidan Mami ta ke a Kano shi ne ta dan zo nan, ita Yaya Faruk ke son kawomuku matsayin suruka alhalin ita din ba…” Wani kyakkyawan mari ne ta ziyarci kuncinta daga uban gayya, ta rike kuncinta wanda ba karya ta ji marin matuk’a. Ya nunata da yatsansa mai rawa, idanunsa sun kad’a ainun. “Koda wasa, koda wasa ki ka k’ara wannan kuskuren sai kin raina kanki! Yaushe raini ya shiga tsakanina da ke?!” Dakta cikin 6acin rai ya ke dubansa. “Ba ka da hankali Faruk! Akwai wani abu a kwakwalwarka, ina kai ina wannan? Akanta har ka d’aga hannu ka mari k’anwarka?!! Haba Faruk!! Wannan zubda k’ima har ina?!!!” Faruk ransa ya yi mugun 6aci, ya girgiza kai yana duban Dakta. “Na yarda k’ima da komai nawa su zube, sannan don Allah ba kai na kawowa Ummi ba, da ta yi maka da bata yi maka ba, wannan ruwanka.” Tsananin mamakinsa ne ya kama su, tunda suke da shi basu ta6a ganin kalar tashin hankali har haka akan fuskarsa ba sai a yau d’in, haka koda wasa bai ta6a yiwa wani cikin yayyunsa rashin kunya ba ko dai mayar musu da magana. Daddy kallonshi ya ke yi yana nazari, shi yasan waye Faruk, mutum ne mai tsananin hakuri, kusan duk a yaransa daga Usman(Babban Yaya) sai shi a fannin hakuri, yakan hakura da abu duk son da ya ke mishi matukar wani cikin yayyunsa ya nuna baiyi ba saboda tsantsar kauna ta jini d’aya da ke gudana tsakaninsu. Ya maida dubansa ga Ummi yana nazari, can kuma ya dubi Ridwan. “Wuce gidanka.” Dakta daman a fusacen yake, hannun dansa ya rik’e ya bar falon bayan ya jefi Ummi da mugun kallo wanda batasan ma yana yi ba don kanta a sunkuye ya ke tana faman kuka da sheshshek’a. Itama Ikram mara mishi baya ta yi a guje tana kukan marin da ta sha. Daddy ya dubi Ummi. “Tashi ki je Hasiya.” Ummi ta mik’e tana had’a hanya ta fita, tasan daman lamarin ba mai yiwuwa ba ne sam, tun yanzu ta soma fuskantar tashin hankali ina kuma ga idan ta koma Kano? Daddy ya zauna sannan ya dubi Faruk wanda ke tsaye yana duban hanyar da Ummi ta bi cike da matsanacin 6acin rai, har lokacin bai daina jin dacin maganganun yan uwansa ba ga matar da yafi so duk duniya. “Zo ka zauna.” Cewar Daddy cikin kwantar da murya yana mai mishi nuni da gefensa. A hankali ya taka ya zauna a k’asa rai a jagule. Shiru na yan mintuna ya biyo baya kafin Daddy ya soma magana….! Ihsan tsaye a falon Hajiya Babba ta yi tana jin yanda ‘yar hatsaniya ke tashi a sashen Daddy, ji takeyi kamar ta je ta ga abinda ke faruwa. Tana nan tsaye Dakta ya fito a fusace, ko lura da ita baiyi ba haka ya fice, bata kai ga cewa komai ba Ikram ma ta sanyo kai, hawaye sha6e-sha6e saman fuskarta, a guje ta yi saman Hajiya, baki sake ta dubi saman, tana shirin maramata baya Ummi ta fito itama cikin shigar da ta mugun kad’a hanjin cikin Ihsan, gabanta ya hau duka da sauri-sauri. Suka dubi juna ido cikin ido kafin kuma a sanyaye Ummi ta soma tafiya, har ta bar wajen bata iya ce mata uffan ba, ta dafe kirji wanda ta ke ji kamar zai fad’o. “Me Ummi kuma ta ke yi a sashen Daddy, da kuma shiga irin haka?” Ganin babu mai amsamata ne yasa a karshe ta yanke shawarar bin bayan ‘yar uwata tasan ko menene zata ji.+ Daddy ya dubi Faruk cikin kwantar da murya ya soma magana. “Tun tashinka ban ta6a kamaka da laifi na k’arya ko yaudara da makamancinsa ba Faruk, hakazalika ka kasance mutum wanda bai 6oye abinda zuciyarsa ke so.” Daddy ya danyi shiru sannan ya cigaba da magana. “Ni ba k’aramin mutum bane, ba alfahari ba, Allah Ya azurtani da yara masu d’abi’u kyawawa hakazalika masu iyakar kokari wajen kiyaye dukkan wasu dokoki na Ubangijinsu, wannan karon sai aka samu akasi, zuciyata ta kasa nutsuwa da za6inka na matar aure, ina ganin kamar da wata manufa ta daban ka ke son auren wannan baiwar Allah da idan a batu na dukiya ne da jin dadin rayuwa, to kai din kana sama da ita, ina so ka gayamin tsakani da Allah, wane irin so ka ke ji ga yarinyar nan? Bazan lamunci tozarta DAN ADAM ba, don kowanne akwai darajarsa ta musamman, bazan lamunci ka aureta daga baya azo a samu matsala ba. Ka fadamin gaskiyar abinda ka ke ji game da ita.” Faruk ji ya yi kamar ya d’aga Daddy ya cillashi sama yana ca6e don dad’i. Ya dan saki fuska. “Tsakani da Allah nake sonta Daddy, asalima kaunarta ta samo asali ne daga tausayinta da nake ji, wallahi ba ni da haramtacciyar nufi akanta.” Daddy ya yi murmushi gami da dafa kan Faruk. “Tun da kake a rayuwa, ka ta6a zuwar min da wata buk’ata na k’i?” Hakoransa a bayyane yana murmushi ya girgiza kai. “Aa Daddy.” “To wannan ma bazan k’i ba, matuk’ar na yi bincike akan yarinyar na samu kyakkyawan magana, baka da matsala. Ni mai aura maka Hasiya ne.” “Da SHARADI.!” Suka tsinci muryar Hajiya daga bayansu, Faruk a rud’e ya ke dubanta, ta karaso idanunta na zubda ruwan hawaye ta zauna saman kujera. “Ki ka ce me?” Daddy ya fada da mamaki yana kallonta. Ihsan ta iske Ikram a daki tana kuka da sheshshek’a, wai yau Yayansu Faruk mai hakuri shine ya mareta akan wata banza yar aiki Ummi? Wannan abu da cin rai ya ke. “Ke wai meke faruwa? Tashi ko sanardani don Allah, ni gaba daya na shiga rud’ani wallahi, naga Ummi da wani shiga mai ban mamaki.” Ikram ta mik’e zaune tana dubanta cikin dacin rai. “Za ki ganta da fin wannan ma wallahi muddin ba ki bud’e baki kin fayyacewa iyayenmu yanda ki ke ji game da Yaya Faruk ba, a yau Yaya Faruk ya kawo Ummi gaban su Daddy matsayin wacce ya ke so da aure. Har akanta ya mareni.” Ihsan daskarewa ta yi tana duban Ikram, ji take kamar jinin jikinta baya gudana yanda ya dace, kamar wata sokuwa ta bude baki ta na kallonta. Ikram ta fayyacemata duk yanda akayi tun daga farko har zuwa marin da akayimata da rikicin Dakta da Faruk. Hawaye ne kawai ke kwararowa daga saman fuskar Ihsan ta kasa kata6us. Abin ne ta ke masa kallon mafarki. Ummi dai ‘yar aiki, Ummin da ta ke ganin ta fita a komai na rayuwa, ta fita kudi da ilimi kai harma da yawan dangi kuma wadatattu da sauransu. Faruk matashi abin so da shaawa ga duk wata mace mai lafiya, matashi irinsa da ko ‘yar shugaban k’asa ko wani basaraken, bata isa ta yi mishi kallo daya ta kauda kai batare da ta yabawa tsarin halittarsa ba, mata nawa ne ke son dace da samunsa? Su nawa ke rububi da fatan inama ace suna da damar da zaisa ya kasance a matsayin mijin aurensu? Ta girgiza kai tana sheshshek’a tana mai cigaba da sak’e-sak’en zuci. Abin kaico, ya buge a auren ‘yar aikin gidansu, wacce zai iya samun dubu da suka fita komai ya aura. Abin kunya ne da takaici ace wai suna takara akan namiji daya tilo ita da’yar aikin gidansu, wannan kam raini ne da kaskanci agareta, wannan zubewar k’ima da ajinta ne a idanun kawayenta da duk wanda yasan irin mutuwar son da ta ke yiwa Faruk. Ikram kasa zaman dakin ta yi ta fito falo don ta ji da nata zuciyar dake mata wani irin daci, ga kuma tausayin Ihsan din da ta ke ji. Wasu lokutan so baima san kan wanda ya dace ya fad’a ba, ba don zargi babu kyau ba da sai ta ce anya kuwa ba wani siddabarun Ummi ta yi ga yayannata ba? Idan ba haka ba, ina shi ina wata Ummi? Ko diri da kyawun fuskarta ne ya d’ebeshi? Ta jefawa zuciyarta tambayar, sai kuma ta girgiza kai. Kayya da kamar wuya, idan don hakan ne kadai akwai wadanda suka ketare Ummin masu kaunarsa amman bai za6esu ba. Hajiya ta share hawayenta don daga daki ta ji dukka abinda ke gudana, hankalinta ya tashi jin wai yau yaranta sun samu sa6ani akan zancen auren Faruk. Ga kuma a gefe da ta ke tsoron abinda zai rushen k’akk’arfan. zumuncinsu da kanwarta Madina. Ba zata ta6a amincewa hakan ya afku ba, don Ummi kuwa, kwarai yarinya ce mai hankali, ta cancanci zama matar d’anta don a halayya bata ta6a kamata da wani dabi’a mai muni ba, hakanan bata ta6a cin amanarta ba, daidai da Madina ta sha yaba hankalin yarinyar. Ta dubi mijinta kafin ta maida dubanta ga Faruk wanda ya sunkuyar da kansa cike da jin wani mugun tashin hankali. Yana fargabar abinda zai fito daga bakin Mahaifiyartasa. Baya fatan ace itama bata goyi baya ba, to amma a maganarta, ta nuna goyon bayanta saidai ta ce da sharad’i. “Kwarai kuwa Abban Ridwan, akwai sharad’i. Na amince ya auri Ummi, amma ina so itama Ihsan ya aureta!” Gaban Faruk ya bada sauti mai k’arfi, ya juyo a razane yana duban Hajiya, fuskarta a daure wanda hakan ya nuna babu alamun wasa a zancenta. “Ita Ihsan din ce ta ce tana sona?” “Na tabbatar kasan tana sonka Sadauki.” Daddy ya yi shiru. Faruk ya girgiza kai a gigice. “Ni bana son…” “Kaga, tashi ka tafi zan nemeka.” Cewar Daddy, Faruk ya mik’e ransa babu dadi ya fita, bai ta6a sha’awar zama da mata biyu ba, ta ya ya Hajiya za ta k’ak’aba mishi Ihsan alhalin tasan bai ta6a sonta ba? Asalima bai ta6a soyayya da wata diya mace ba sai Ummi. Hankalinsa ya koma ga Ummi, a wane ta ke ciki ne? Kai tsaye ya nufi wajenta don bincikawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *