DAN ADAM CHAPTER 4

DAN ADAM CHAPTER 4

Anan ta iskesu tsaitsaye ana hira banda babban yaya wato Yaya Usman da ke zaune cikin mota tare da Faruk wanda gaba d’aya ya matsu su koma gida don jinsa yake a gajiye. Ihsan ta bita da kallon harara, hakan yasa ta kauda kanta. “Kanki ake ji.” Ta fad’a a ranta. Ta dubi wata doguwar budurwa siririya bak’a, bata san itace Ikram ba ko kuma Baraka, don sunayensu kawai Amina ta sanarmata ba ta nunamata su ba a fuska. “Ga wannan a ina zan ajiye?” Ta dubeta, sannan ta nunamata motar da yatsa batare da dogon bayani ba. “Kinga, saka anan.” Ta dubi Yaya Haidar dake nunamata boot wanda yasa hannu ya bud’e. Ta karasa ta ajiye gami da fad’in. “Allah Ya tsare hanya.” Daga haka ta juya ta bar wajen. “Adnan ina mutuniyata ne? Ban ganta ba.” Adnan ya yamutse fuska yana duban farar budurwar siririya da tayi mishi magana, wato Baraka. “Wa kenan?” Ya tambaya cikin basarwa kamar bai fahimci ko wa ta ke nufi ba da gaske. “Abokiyar fad’arka mana, your lil sis.” Ya harareta, ya gane Iklima take magana akai. “Ai kinsan hanyar gidansu ko? Sai kije.” Baraka tayi dariya. “Kwarai ma kuwa wallahi, idan ma kana ganin kamar bazan iya zuwa ba zaka sha mamaki. Kada fa ka manta k’awata ce, mun riga mun saba da uta adalilin (whatsapp group) da muke ciki tare. Zo muje Ihsan ki rakani.” Ba musu ta ja Ihsan suka tafi. Hajiya Binta suka soma gani a falo tare da Usman, Jabir da Hanif, gaba daya kallo ya daukemusu hankali. Sallamarsu ce ta sanyasu maido hankali garesu. Ta soma shan kamshi yayinda ta amsa ciki-ciki. Suka karasa suka gaisheta. Saida ta k’arewa suturar dake jikin Baraka kallo sannan ta numfasa, ta riga tasani iyalan Hajiya Fatima ba su ta6a zama a baya wajen suturu da sauran kayan more rayuwar duniya. “Baraka ko?” Baraka fuska a sake ta amsa. “Eh ni ce Umma.” “Sannu, yanzu kuka zo?” “Za mu tafi ne dai, ina Iklima?” Hajiya Binta ta nunamusu hanya. “Ku shiga tana d’akinta.” Suka shige ta bi bayansu da kallo cike da jin wani tuk’uk’i a ranta, dole Madina ta dunga yi musu wani gani-gani kasancewar daga ita har Lubna, ba wasu ‘ya’yan masu kudin azo a gani bane, a komai dangin Hajiya Madina sun k’ere musu, yana daga dalilin da yasa suke matukar kishinta. A gefe kuma tana tak’ama da cewar ita din fa jinin Alhajinsu ce, shi kansa Alhajin koda hira akeyi da ya shafi danginsu, sau da yawa yakan yabawa bajintar mahaifin Madina, da irin yanda ya iya rik’e iyali da sauransu. Wannan yasa ko kad’an acikinsu babu mai kaunar suyi wata doguwar hirar da ta shafi dangin Alhaji Modibbo. Babban burinta yanzu, bai wuce yaranta su kasance wasu shahararru ba a fannin kudi, ta ci buri akan Iklima wannan yasa ta haneta abota da dukkan wani jinin talaka, dukkan abokan Iklima ‘ya’yan wasu ne. Koyaushe tana hanyar biki da party. Babu laifi takan samu samarin masu ji da kudi saidai da yawansu ba da aure suke sonta ba, saidai wata manufarsu ta daban. Idanunta sunyi masifar budewa wanda hakan nai ta6a damun Hajiya Binta ba, acewarta, idan bata kasance wayayyiyar ba, a ina har zata samarwa kanta miji dan zamani. Acan kuwa su Baraka suna shiga Iklima ta rungume Baraka tana ihun murna don sosai kawarta ce, kusan halinsu yazo d’aya na son gayu da samari. “Shegiyar gari, daman kinzo shine ko ki nemeni?” Baraka tana dariya tace “Afuwan tawan, kinsan tun dazu na so shigowa Allah baiyiba, ina su Yaks?” Fad’in haka yasa ita da Ikliman suka tuntsire da dariya ita dai Ihsan ta zama ‘yar kallo, ko ita da suke tare da Ikliman basu hira mai tsayi har haka, lallai ba karamin sabo Baraka da Iklima sukayi ba. “Yana inda yake, kwana biyu munyi fad’a ma, zan baki labari kedai. Ina mijina?” Cewar Iklima tana mai kashe mata ido d’aya, Baraka ta ja guntun tsaki tana dariya. Ta fahimci Faruk take nufi, tun daga sau daya da ta ga ta dora hotonsa a dp lokacin shi kuwa yana gani ya shigo har dakinsu ya hauta da fad’a har yakai ga mangarinta, yace tayi gaggawar goge dukkan hotunansa a wayarta. Daga ranar bata kara dora hotonsa. Daga ranar Iklima ta makale akan lallai ita fa sai ta hadata da shi, hakuri kawai ta bata ta gwadamata Faruk sam ba irin nasu bane don ba shi da wannan rawar kan akan mata. “Kedai ki kama kanki baruwana na gayamaki.” Cewar Baraka. Iklima tayi dariya. “Ina ruwanki? Bazan kama ba sai randa kika bani lambarsa.” Ihsan duk bata fahimci komai ba saida ta ji Baraka na fadin. “Kizo muje da kanki ki tambayeshi, ga shi can a waje.” Ai sai Iklima ta zaro ido. “Dagaske?” “Wallahi.” Cewar Baraka cikin dariya, tuni ta ja dankwalinta ta rufe kanta, daman riga ‘yar kanti ce a jikinta sai siket ruwan madara na leshi da dankwalinsa. “Muje wallahi na gaisheshi na tambaya.” Suka kamo hanya Baraka cikin dariya ta na fad’in. “Kamar gaske, bakisan wanene Yaya Faruk ba wallahi.” Gaban Ihsan ya fad’i, me Baraka ke nufi? Wato Iklima batun Faruk take? Aikuwa ba zata sa6u ba, saidai su yi BIYU BABU. Muddin ita bata samu soyayyarsa ba, to babu wata ta jininta da zata samu, ta gwammace ya je ya auri bare akan tana ji tana gani ya auri wata jininsu. A ganinta, itama fa tana da aji, ba zai yiwu ta zauna wani namiji na sha mata kamshi ba, ta tsani dukkan wani namiji mai ji da kansa, baruwanta da kyansa, idan kyau ne, akwai wadanda suka fishi da suka nuna suna sonta tana sha musu kamshi. Anan kofar shiga sashen Alhaji Modibbo suka ga takalman Mami da Hajiya Babba, wannan ya tabbatar musu suna ciki. Da rawar jiki Iklima take tafiya, Allah-Allah takeyi ta had’u da Faruk ko don shima yasan da zamanta. Ta tabbatar ba kowane namiji ne zai iya dauke idanu daga kanta ba. Haka suka karasa bakin motar, alokacin Haidar da Adnan ne kawai tsaye sai Ikram wacce ta jingina jikin mota tana danne-dannen waya. Iklima suka gaisa da Haidar, Adnan sai dauke kai yakeyi. Itama bata bi ta kansa ba ta dan lek’a motar, kasancewar akwai wadatar haske a farfajiyar gidan hakan yasa ta hangi Faruk dake zaune a mazaunin direba ya d’ora tafin kafarsa akan kujera, kansa jingine jikin kujerar yayinda kunnensa ya sanya (Earpiece) yana shan sauti. Idanunsa a lumshe. Wani wawan ajiyar zuciyar Iklima ta saki, ta ko’ina Faruk ya had’u. Ta gaida su Yaya Usman suka amsa mata fuska a sake kafin tayi ta wajen Faruk tana gaisheshi. Ko kusa baisan ma tana yi ba saida Usman ya cire mishi kunne d’aya na (Earpiece) sannan ya juyo da rinannun idanunsa, da alamu ma bacci ya soma. “Au bacci kakeyi ma? Ana gaisheka.” “Ina wuni.” Ta k’ara fad’a. Ya juyo ya zubamata idanu, ai ji tayi kamar ta saki fitsari tsabar yanda kallon ya kad’ata, duk inda take zaton Faruk a kyau da komai, ya wuce nan. Kansa kawai ya gyad’a mata sannan ya dauke kai. Ji tayi ta kasa koda kwakkwarar magana, to ta ina ma zata iya furta mishi wani abun har ya kai ga tambayar lambarsa? Ba zata iya ba, hakan yasa ta koma ga su Baraka wadanda ke yi mata dariya har Ihsan wacce ba karamin dadi abin ya yi mata ba. “Wace ne?” Faruk ya tambaya ba tare da ya bud’e idanunsa ba. “Iklima, step-sister dinmu.” Cewar Adnan. Ya yamutse fuska. “Har yanzu Hajiya bata fito ba? Wallahi na soma bacci.” Kafin waninsu yayi magana, sai ga Mami da Hajiya tafe suna hira, Yaya Ridwan ne yayi magana. “Ai idan iyayenmu mata suka had’u wallahi har mamaki suke ban, ko kusa basu kaunar rabuwa da juna.” Faruk da Usman suka d’an dara, kamar ba zasu karaso ba haka suke tafe suna hira. Ganin dai da gaske basu da niyyar tahowa ya sanya Faruk dannan hon, wannan ya maido hankalinsu wajensu. Ya koma can gefen mazaunin direba yana fad’in. “I can’t drive wallahi, bacci ya soma kama idona.” Haidar ya bude mazaunin direba ya shiga yana fad’in. “Ai nayi mamaki ma da ka iya kaiwa war haka, kodayake na dole ne. Mutumin da wani sa’in takwas ma yayi bacci.” Murmushi kawai Faruk yayi ya kara lumshe idanunsa sannan ya budesu. Hajiya Babba ta karaso ta shiga, ganin haka yasa yanmatan sallama da juna, bayan shigarsu Iklima ta zubawa Faruk ido kamar ta had’iyeshi, tsaf ya lura da kallon da take jifansa da shi, wannan yasa a sannu ya zuge gilas wanda ya kasance mai duhu, shi ya yi mata katanga daga dubansa. Ta sauke ajiyar zuciya, ta juya ta kama hanyar ciki bayan ta gaishe da Hajiya Babba, sun kara sallama da Baraka. “Maganar banza ce kikeyi, wacce ba zata ta6a kasantuwa ba matukar Binta na raye wallahi. Da kinsan yanda nake kishin Madina da danginta, da baki soma tunanin son Faruk ba Iklima.” Cewar Hajiya Binta tana faman hura hanci fuska a murtuke kamar bata ta6a bud’a hakoranta ba don dariya. Iklima ta tur6une fuska tana kunkuni ta mik’e ta barta tana faman bud’e wuta. “Eh lallai, gwara tun wuri na tashi tsaye kafin kema ki rikita lamurana, shawarar Hadiza zan bi.” Ta karashe tana daukar wayarta, Hadiza ta dannawa kira sannan ta mike ta fad’a d’aki. Suka gama kulla-kullarsu akan yanda Alhaji zai shigo hannunta sai yanda tayi da shi, da kuma irin nau’ikan muguntar da za’a yiwa Madina a lalata rayuwar ‘ya’yanta, itama a dusasar da tauraronta dake haskawa a idanun Maigidan da surukarsu. Haka suka ajiye wayar cike da jin wani nishad’i ko babu komai itama tana dab da samun matsayi babba. ☆☆☆ Haka rayuwa tayita tafiyarwa Ummi, yau dadi gobe babu dadi. Yawanci matsalarta bai wuce Ihsan ba don Mami matukar zata yi abinda ta sanyata to fa babu ruwanta da harkarta. A wannan halin ne wata ranar Asabar ta tashi da ciwon mara marar misali, tun tana dauriya har ta kasa, ko tashi ta kasa yi balle ta kai ga aikace-aikacenta. A wannan hali Ramma tayi sallama ta shigo bisa umarnin Mami da ta dubo ko lafiya bata fito ba har ga Ramma ta rigata zuwa. Ganinta ba lafiya yasa ta fita ta sanarwa Mami. Kafin su dawo ta soma jin ta da lema, saida Ramma ta d’agata ne suka fahimci abinda ke faruwa. Ramma ta taimaka mata bayan ta kar6o (Always) wajen Mami, ta gwada mata yanda zatayi, saida ta kimtsa sannan suka rankaya kemis da Ramma. Tun daga wannan ranar Ummi ta fahimci girma ya hau ta, Ramma ta k’ara jaddada mata hakkokin da suke akanta yanzun wadanda ta riga ta sani don a makaranta duk ana koyardasu. Mami bata yarda da kazantar kunzugu ba, hakan yasa ta bata (pads) cikin na Ihsan wacce ta rigata somawa tuni. Saida tayi kwanaki hud’u sannan tayi wankan tsarki. Daga wannan lokacin ta k’ara kame kanta ta zama mai kula sosai da takatsantsan musamman ma ga sallolinta. ☆☆☆ A KWANA A TASHI…! A kwana a tashi ba wuya a wajen Ubangiji, har ga shi ana sauran kwanaki hud’u bikin Haidar da Intisar. Wannan ya janyo Ihsan komawa gidan Hajiya Mama don taya ‘yar uwarta shirye-shirye. Alokacin tuni su Hajiya Babba sun iso Kano don anan za’a yi sha’anin bikin kasancewar mijinta, Gen. Ahmad Danzaki, uba ga su Usman, shima dan asalin Kano ne. Mami ta yiwa Ramma da Ummi kyautar atamfa turmi d’aya na anko. Ramma ta had’a ta kai musu dinki wanda ya zauna d’as a jikinsu. Ana washegari za’a soma biki, suka ziyarci Hajiya Mama wacce ke fama da shirye-shirye. Amina ta ji dadi kwarai na ganin Ummi. Anan gidan Mami ta barta tare da Fahad suka fita zuwa babban shagon siyar da kayayyakin kicin, hakanan su Ihsan suma sun fita wajen gyaran Amarya. Ummi ta dubi hannun Amina da suka sha kunshi. “Anti na kasa dauke ido daga kunshin nan naki wallahi, yayimin kyau sosai.” Amina fuska a sake ta amsa mata sadda take gyara zaman tsintsiyar hannunta wanda take shirin yin shara. “Idan kina so muje na rakaki sai na dawo, wallahi yarinyar ta iya kunshi, baki ganta ba kuma ba wata babba ba.” Ummi ta zaro ido, ga koshi ga kwanan yunwa. “A’a, banason fad’an Mami, idan suka dawo basu tarar da ni ba ai nasan ba zata kyaleni ba.” Amina ta dara kadan. “Kedai akwai matsoraciya, ni na fadamaki har babban gida sai sun shiga tunda Gwaggo ta zo (surukar Mami kuma yar uwar mahaifinta). Na tabbatar su da mu gansu a gidan nan sai Magriba. Bari nayi shara na rakaki, keda kike fara tas ma ai sai ya fi yi miki kyau a kaina.” Ummi tayi tsuru da ido bata kara cewa komai ba, tana kallo Amina ta kammala share tsakar falon, ta wanko hannunta sannan ta yafa gyale. “Muje.” Ummi ta girgiza kai. “Ai baki isa ba, tunda har kina so wallahi sai kinyi, saidai wani ikon Allahn ya hana. Idan kudin kike ji, kada wannan ya dameki, zan biya.” Dakyar ta shawo kanta ta amince suka tafi. Babu nisa sosai, saida Amina ta ga an soma yi sannan ta taho bayan ta rok’i alfarmar mai kunshin akan ta sanya a raka ta gida. Ba wani mai yawa akayi mata ba, saidai duk kushen mai kushe bazai kalli hannu da kafafun Ummi ba ya ce baiyi kyau ba. Bak’in lalle ne, hakan yasa babu jimawa sosai ya bushe adalilin iskar dake kad’awa. Ta wanke a gurguje, alokacin anyi sallar la’asar, gaba daya fargabanta bai wuce na kada ya zamana su Mami sun dawo ba. Saidai cikin ikon Allah daga su Mamin har su Intisar babu wanda ya dawo. Amina ta rude ganin yanda Ummi tayi kyau. “Kai amman lallen nan yayi miki kyau sosai masha Allah, sauranki kitso.” Ummi ta murmusa. “Anti nikam banason kitso wallahi bansan dalili ba.” Amina ta harareta kad’an. “Eh mana, don kinga kina da gashin ne ai, amma idan kana da kyau saika k’ara da wanka. Gashinan yanzu kunshi yasa kin fito a Mace.” Sukayi dariya. Koda Ummi ta idar da sallah, tare suka shiga kicin tana kallon yanda Amina ke had’a girke-girke. Abin sai ya bata sha’awa matuka, don duk iyakar girkinta a gidan Mami, bai wuce dahuwar kwai da indomi ba. Amina ta bata shawara akan ta k’ara zage damtse wajen lura da yanda su Mami da Ramma ke girke-girke. Anan suka shantake wajen hira, har Amina na labarta mata batun wani saurayinta wanda shi kadai take saurara, har a yanzu haka ya soma matsawa da batun turo magabatansa. “Allah Sarki, toh Anti ki ba shi dama mana.” Amina ta murmusa. “Ba anan matsalar take ba, dangin mahaifina ne abun ji, kina ganin yanda suka wancakalar da lamuranmu, ina gudun kada azo a samu matsala ne.” Ummi ta gyada kai. “In sha Allah babu abinda zai faru, ki gwada ba shi dama.” “Ai ko na k’i ko na so babu yanda na iya, tunda dai ina kaunarsa haka kuma Innarmu ta ba shi wannan damar har ta sanar da ni muddin ya kara tuntu6arta da maganar zata kwatanta mishi gidan su Mahaifina, kinga kuwa ai bani da ta cewa sai addu’a.” “Gaskiya kam, Allah Ya yi miki za6i.” “Amin, bari mugani, idan banyi lattin gama dahuwa ba, zan kaiki ki gaida Inna.” Wani sanyi ya mamaye kirjinta. “Toh Anti.” Ba haka suka so ba, don lokaci k’urarre suka kammala, alokacin kuma Mami suka dawo, duk da haka ba su bar gidan nan ba sai bayan Isha’i, wannan yasa Amina yi mata alkawarin duk randa suka k’ara zuwa zata yi kai ta. Koda Mami ta ganta da kunshi babu abinda tace, illa iyaka ta tambayi yanda ta samu kudin, ta shaidamata Amina ce ta biyamata, daga wannan bata k’ara uffan ba. Washegari ya kama ranar Kamu wanda za’a gabatar a wani tsadadden dakin taro wanda ake ji da shi sosai a birnin Kano, wajen da sai wane da wance. Tun misalin karfe uku na rana, dakin Mami kaf suka shirya, a ranar ma Ummi ta kara fashin makaranta wanda ko kadan ba haka ta so ba, saidai tasan Mami ba barinta zatayi ita d’aya. Daya cikin kayan da aka dinkamata tun farkon zuwanta ta sanya don kuwa Ramma ta sanar da ita cewa sai ranar yini za’a sanya anko. Tsari da kwalliyar wajen ya burgeta kwarai, banda wak’a babu abinda kakeji yana tashi a filin taron, waka marar sauti sosai, acikin nutsuwa akeyinta. Har shagala tayi wajen kallon gogaggun yan boko mata wadanda suka ci ado har suka gaji, sai faman fara’a suke kowacce na harkar gabanta. Tana nan zaune tana rarraba idanu, ta ji an dafa kafadarta. Amina ta gani, suka washewa juna hakora, haka kawai itama Ummi ta tsinci kanta da tsantsar farinciki kai kace bikin wani nata akeyi. Amina ta ci kwalliya kamar ba ita ba duk ta chanja. “Kedai Ummi kina da ban haushi, bansan meyasa bakyason gyara fuskarki ba wallahi, kalli dai yanda yanmata suke cakarewa, amma ke inaga ko hoda bakya shafawa, kodai baki da ita ne?” Ummi tayi dariya har hakoranta suka bayyana a fili. “Anti nida ban iya kwalliyar ba?” “Ai ba lallai sai kinyi mai zafi ba, ko hoda kadai kika shafa kika saka jan baki mai kala a le66anki ya wadatar, ji yanda kika hadu, wallahi da ace kina kwalliya na tabbata sai kin fi haka.” Ummi ta rausaya ido tana dariya. “Ko?” Suka dara gaba d’aya. + Babu jimawa sosai Amarya ta iso filin da Angonta. Baki bud’e Ummi ta dubi Amina, alokacin wuri ya hargitse, k’arar kid’a ya yawaita da ihun mutane da masu daukar hoto. Ta so ta tambayi Amina daman namijin na zuwa kamu? Saidai babu damar hakan sakamakon hayaniyar da tayi yawa awajen, sunyi kyau matuk’a. Gaba dayansu fararen kaya suka sanya, Haidar cikin farar shadda, yayinda itama Intisar ta had’e cikin shadda dinkin doguwar rigar da ta sha aiki. Su Ihsan da sauran kawayen Intisar suna take musu baya, hakanan shima ango, abokansa na Abuja da na nan Kano kalilan cikinsu sun samu halara, yayinda wasu suka barwa gobe daurin aure. Ba anko sukayi ba, saidai shadda brown kowannensu ya saka, na wani yafi na wani turuwa. Sunyi kyau kwarai, sai kirari ake yiwa Ango da Amaryarsa har suka isa mazauninsu. Duk raba idanun Ummi bata ga yayyun Haidar ba da kuma Faruk. Har akayi nisa da sha’anin, mata ne kawai da daidaikun matasan wajen wadanda dukkansu yan uwansu ne na Adamawa sai kuma yan uwan mahaifin Haidar Danzaki da ma’aikata. Sun jima sosai a wajen, an ci an sha, har saida aka kusan tashi sannan ta hangi mota ta faka daga can gefen na amarya da ango. Su biyar ne suka fito daga motar, Yaya Ridwan ne sai wasu wadanda suka fi kama da abokansa, a hannunsa kuwa, wata kyakkyawar yarinya ce wacce bata fi shekaru uku ba tana bacci saman kafad’arsa. Har aka tashi daga wajen babu Faruk da Babban Yaya. Duk da irin gajiyar da Ummi ta kwaso, wannan bai hanata watsawa jikinta ruwa ba kafin ta chanja sutura ta kwanta. ☆☆☆ Washegari ya kama ranar da za’a daura aure da kuma yini. Tun safe da mutanen dakin Mami suka farka, babu wanda ya koma bacci. Daga Maigidan har sauran yaransa maza, shirye-shiryen karyawa sukeyi su wuce d’aurin aure, yayinda Mami itama ke shirin tafiya gidan biki. Ummi kuwa, ayyukanta ta shiga yi cikin sauri-sauri bisa umarnin Mami, don kuwa a son Mami, tafiso tana can a daura aure maimakon ace bata isa ba. Itama Ramma sanin da tayi na cewar Mami da wuri zata fita ne, yasa ta shiryawa da wuri, bata da wani aiki a kanta mai yawa kasancewar yaranta sun je k’auye. Wannan karon dai Ummi ta ji maganar Amina, don kuwa ta shafe fuskarta da hoda sannan ta sanya jan baki kalar ja sai kwalli data zizara a idonta. Ita kanta tasan tayi kyau, irin kyawun da bata ta6a ganin ta yishi ba, ko don ba kwalliyar takeyi ba? Ankon bikin da Mami tayi musu ne a jikinta, ya zauna d’abas kamar a jikinta aka d’inkashi, ya fito da kyakkyawar surarta wanda ita kanta batasan tana da diri mai kyau ba kamar haka. Har ta dauki mayafi ta yafa sai kuma ta ga sam ba zata iya ba, hakan yasa ta janyo farin hijabinta wanda ya hau sosai da atamfarta mai adon fari da koren fulawoyi. Kiran da Mami ta kwalamata ne yasa ta amsawa da sauri don bata da masaniyar cewa Mamin ta shigo falon domin itace a fadar Alhajinsu. “Masha Allah.” Shine furucin da Ummi tayi a ranta, duk iyakar yanda take ganin ta fito tayi kyau, sai ta raina shigarta ganin shigar Mami, ba irin ankonta bane a jikinta. Wani tsadadden leshi ne ruwan madara mai duwatsu dinkin doguwar riga da zani ta sanya, anyi aiki a gaban rigar leshin wajen kirji, banda kamshi babu abinda kakeji yana tashi a falon. Hannunta rike da jaka da mayafinta. Ta dubi Ummi duban tsaf kafin cikin sakin fuska tace. “Ashe dai kin iya kwalliya.” Abin ya bawa Ummi mamaki, kodayake dai tasan yau Mami cikin farinciki take. Ramma dariya tayi kawai, itama tayi tsaf da ita tana rike da karamar jaka na kaya wacce ta tabbatar na Mami ne. “Shiga ki cewa su Hajiya Binta idan sun shirya su fito mu wuce.” “Toh.” Sannan ta kama hanya da mamakin wannan irin iko na iyayen gida irin Mami, wato bata damu da ta sanarmusu su shirya ba tun farko saida ta tashi tafiya. Sashen Hajiya Binta ta soma zuwa, a zaune ta sameta tana latse-latsen waya ko wanka batayi ba. Ciki-ciki ta amsa sallamar Ummi, gabanta na dukan tara-tara, ta durkusa ta shaida mata sak’on Mami. Kamar ba zata ce komai ba saidai ta dubeta a wulakance har saida ta ji ta muzanta. “Ki sanar da ita cewar tana iya tafiya, don banason had’a tafiyata da shirgi.” Ummi dai toh kawai ta furta sannan ta mike. “Tsaya Ummi.” Cewar Iklima wacce ta fito daga d’aki cikin shirin shadda ruwan k’asa mai turuwa, dankwalinta a hannu da ribuna. Gaba daya suka dubeta. Ta dubi Hajiyarta. “Ni zan bisu yanzu mu tafi.” Hajiya Binta ta bita da mugun kallo, ta tabbatar wannan rawar kafar da takeyi bai wuce na son ganin Faruk ba, ita kuwa ta ci alwashin koda Iklima zata mutu, ba zata ta6a bari ta auri jinin Mami na kut da kut ba. “Banyi miki iznin binsu ba, ke wuce ki isar da sak’ona. Tana iya tafiya.” Ummi jin haka yasa ta juya gami da dan ta6e baki, da sauri ta kara gaba batare da ta jira jin yanda zata kaya tsakanin ‘ya da uwarta ba. Kai tsaye dakin Anti Amarya wato Hajiya Lubna, ta nufa. Ita kam babu laifi tana da tsafta itama duk da cewa ko rabi-rabin kafar Mami bata kama ba, bata falon sai yaranta. Babu wanda ya yiwa Ummi kallon banza, saidai kuma basu bada muhimmanci akanta ba don hankalinsu ya tafi ga kallon wani film na yak’i da ake haskowa a (Mbc Max). Ganin haka yasa ta kara magana. “Don Allah ina Anti Amarya? Mami ce ta aikoni wajenta.” Hassana ce ta dubeta. “Me za’a ce mata?” Ummi ta sanarmata, Hassana ta shiga dakin mahaifiyarsu. Ummi ta cigaba da nazarin falon, ta lura dai kusan duk girmansu daya da na Hajiya Binta, Mami ne komai nata ya fita daban mai yiwuwa kuma don itace farkon zama a gidan kafin zuwansu. Hakanan ta kasa bambance falon wanda yafi shan kaya acikinsu, don kowanne falo akwai nasa kyawun na musamman. Tunaninta ya katse bayan fitowar Hassana. “Tace sai zuwa anjima yanzu kanta yana sarawa ta sha magani ne.” “To, Allah Ya bata lafiya.” Daga haka ta mike ta fita. Mami tuni sun shiga mota, itama shiga tayi sannan ta sanarwa Mami sakon data samu wajen kowannensu bayan ta yiwa sakon Hajiya Binta kwaskwarima inda tace kawai sai zuwa anjima zata taho. Danliti yasa hancin mota ya fita daga harabar gidan. Sunci sa’a don kuwa ba’a kai ga daura aure ba an dai tafi. Motoci cike makil ne a kofar gidan har babu wajen fakin, dole daga nan waje Danliti ya saukesu sannan yayi gaba don neman wajen ajiye mota. Gidan a cike yake da yan uwa da abokan arziki na jiki sosai, Ummi banda rarraba ido yanda zata ga Amina babu abinda takeyi, saidai ko kusa bata hangota ba. Ga waje da mutane ba kadan ba ballantana tace zata nemeta. Haka ta hakura ta nemi gefe guda saman tabarma anan tsakar gidan ta zauna tana kalle-kalle. Kwalliya iri-iri, da wadanda suka burgeta da wadanda ko kusa basu burgeta ba take gani, a haka Ihsan ta zo ta wuce, har ta gaji da haduwa sai daukar ido takeyi. Ummi ta bi takalminta da kallo wanda yake da tsini sosai, jinjina kai kawai tayi tunanowa da Tasleem ta ‘Yar Bariki wacce ta tsinci Ihsan kwanaki tana labartawa Adnan yanda labarin yake, har take mishi batun takalman da Tasleem ke sanyawa. Toh ita kam bata ga marabar takalmin da Ihsan ta kwatanta da wannan dake kafarta ba. Da ace itace ai babu abinda zai hanata karyewa a kaita d’ori, sai ikon Allah. Ta jima sosai anan zaune, kafin ta soma jiyo gud’a sosai yana tashi daga hancin tsoffin dake a wajen. “An d’aura.” Shins furucin da ta ji a bakunansu. Nan kuma ta ga tawagar kawayen Amarya dake a tsakar gidan sun karasa falo suna faman ihu da gud’a. Haka aka cika mak’il a falon Innar su Mami. Ganin da tayi ba zata iya lek’e ba yasa dole ta hakura ta koma da baya ta raku6e jikin bango ta zubamusu ido. A haka tawagar angwaye kuma kusan yan uwan juna gaba dayansu, don da yawansu daga Adamawa suke, yan uwansu ne sai kuma Abokai suma babu laifi. Bata ci wuyar hangen Ango Haidar ba, ya cakare cikin farar shadda wacce ta sha aiki mai tsada. Sai wani shek’i yakeyi. Hakanan kusan gaba daya tawagarsa fararen kaya ne jikknsu idan ka cire yayyun Ango da kaninsu Faruk, wadanda sukayi ankon shadda ruwan madara. Sunyi kyau har sun gaji da haduwa, Ummi ta karemusu kallo, tabbas ‘ya’yan Hajiya Babba abin so ne ga dukkan wata diya macen da take ji da kanta ita din mai aji ce. Idanunta suka fi karkata ga Faruk wanda ta ga kamar an kara matso kyawunshi, a yau yafi koyaushe haduwa domin kuwa fuskarsa yau a sake take hakanan hakoransa a bayyane har gefen kuncinsa na dama ya lotsa. Ya sanya farin tabarau a idonsa, ta sauke ajiyar zuciya, koda ace batasan me ake kira da hadadden namiji ba, to shakka babu akan Faruk ta sani. Cikin sa’a kuwa shima idanunsa suka sauka akanta daidai lokacin da yake gyara zaman agogonsa. Haka kawai ta tsinci yanayinta ya sauya adalilin kallon da yayi mata wanda ta tabbatar haka kwayar idanunsa suke, ba wai da gayya ya yi ba. Ga mamakinta fuskarsa bata sauya daga murmushin da yakeyi ba duk kuwa da cewar sun hada ido da shi, ta numfasa ta kauda kanta har suka shige zuwa Falo wajen iyayensu .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *