YAR MAKIYAYA CHAPTER 15

YAR MAKIYAYA CHAPTER 15





 

Now that we are free from Ameer and company finally Suraj da Laila sun samu kwanciyar hankali. + Bacci take mai lafiya har k’ara luntsuma wa cikin bargo take hankali kwance , yana fito wa daga bathroom ya zauna gefen ta ya k’ura mata ido , ruwan da ke diga diga jikin shi ne yasa ta bud’e ido saida ta gama mutsitsika fuska ta zauna kawai suka had’a ido, wani shu’umin Murmushi ya sakar mata wanda babu shiri yasa ta koma ta kwanta gami da jan blanket ta rufe fuskar ta. Sosai ta bashi dariya ya d’an rik’e bargon zai bud’e ta Amma yaji ta rik’e gam gam ,dan haka ya sure ta daga ita har blanket d’in zuwa bathroom ya ajiye ta, kasa tsayuwa tayi ta zame ya rik’o ta yana dariya a hankali ya ce

“Kiyi sauri Mun makara zamuyi sallah da k’adangaru”. Langab’ar da kai tayi ta marairaice kafin tayi magana ya rufe bakin ta da hannun sa yace “Na fahimta” saida ya jira tayi wanka sannan ya d’auko abin sa suka dawo d’aki ,bata b’ata lokaci ba ta zira Abaya ta sa hijab Suraj ya ja sallah, saida suka idar tukunna ya taimaka mata ta shirya **** **** **** “Razia pls kar ki ajiye wayan nan! Ki saurare ni, ban kyauta ba na sani ,na fahimci abunda na aikata ba daidai bane pls come back” Ko k’ala Mom bata ce ba ta ajiye wayar ta tana kuka. Jikin Dad yayi sanyi ya k’ura wa wayar sa ido cike da mamakin k’arfin hali irin na Razia don bata tab’a masa haka ba,yasan dole ne yasa tayi hakan dan haka dole ya je Egypt ya bata hak’uri. Ta wani b’angaren kuma ga mai martaba shima har yanzu bai huce ba komai baya tafiya wa Dad yanda ya kamata he needs them both, gaba d’aya yaji duniyar tayi masa d’aurin minti. Kusan Sau uku wayar tana ringing ba’a d’aga ba se a karo na hud’u ya bud’e ido ya mik’a hannu ya d’auki wayar. Laila na bacci dan haka ya zame jiki ya koma gefe “Suraj” ta k’ira sunan shi cikin sanyin murya “Mom? ” ya fad’a sannan yaci gaba da cewa “Mom meyasa kika tafi? Nai ta k’iran wayar ki shiru ba kya d’aga wa and……. “Na sani Suraj bani da zab’i ne, bazan iya ganin ka cikin wannan yanayin ba shiyasa na tafi and your Dad, halayen da yayi adopting gaskiya ba daidai bane, saboda haka na yanke shawara in har father and son baza su gyara ba I have no reason to stay.” Suraj bai k’ara magana ba ita ma Mom haka , ganin ya kasa magana yasa mom ta kashe wayar.

Ajiye wayar yayi ya k’ura mata ido kafin daga bisani ya fice daga d’akin ya nufi downstairs, Habeeb dake zaune k’afa d’aya kan d’aya ya d’ago kai ya dubi Suraj kafin yace “Finally!! Ango ka fito! In ka manta Toh ni bazan manta cewa yau juma’a ne ba sannan ka duba time yanzu, kawai ka je ka shantake ka manta da batun masallaci. Zaro ido Suraj yayi ba tare da ya ce komai ba ya koma ya shiga wanka, yana goge jikin sa ya shafa mai sannan ya sa kaya bayan ya feshe jikin sa da body spray na Fog ,farar shadda ya sa ya sa cufflinks sannan ya k’afa hula ,Gosh ! Suraj yayi kyau sosai turaruka masu k’amshi ya feshe jikin sa dasu sannan ya nufi kan gado inda Laila take kwance ya d’auki wayar sa kana ya sumbace ta a goshi ya sake rufe ta da blanket sannan ya fice Habeeb na hango shi ya mik’e suka fita. “Suraj! Kaga yadda kayi kyau kuwa? Kai gaskiya barin nemo wata y’ar beb nima in yi auren nan, ko ma zan huta takaicin gorin Zainab.” Dariya Suraj yake har ya kusa manta hanyar da zai bi, Habeeb ya watsa masa harara yace “me kuma ya baka dariya? Look am serious wallahi kawai ni kasan matsala na ban iya hira ba rannan a Kaduna wata chika ruwa ta watsa min harda jan tsaki a gaban Sapna shine na sha Alwashin bani ba hira amma zan d’auki darasi a wajen ka.

Ni wai tukunna ma Yaya akayi ka fara soyayya da Laila? I mean it was so sudden kuma kun yi sa’a ra’ayin ku d’aya game da juna isn’t that amazing?!” Shide Suraj dariya kawai yake Habeeb se zuba yake bai ma san sun iso masallacin ba. Dawowar su daga sallar juma’a Laila tana falo tare da Umma Hauwa se dariya take da alama barkwanci ne da Umma Hauwa sosai Da sallama ya shigo falon Habeeb na biye da shi ,yana d’aga kai ya hango ta takure kan one seater har k’afafun ta duk ta nad’e su sannan ta rik’e tea mug se dariya take ,kasa d’auke idanuwan sa yayi daga gareta “Barka da dawowa yallabai” Cewar Umma Hauwa dake k’ok’arin mik’e wa zata bar falon. Suraj ya amsa ba tare da kallon ida take ba, inda Laila ke zaune ya nufa amma kafin ya k’arisa Habeeb ya dafa kafad’ar shi yace “Shit man! Ni zan wuce Kaduna nan da thirty minutes zan iya rasa flight in nayi wasa I think sedai ince Allah ya bada zaman lafiya Amarya se wani jik’on! Zaro ido Suraj yayi kafin yace “wai da gaske kake ne? Bazaka tsaya kaci abinci ba?” Mak’e kafad’a Habeeb yayi yace “A’a a k’oshe nake tun yaushe Umma ta cika min plate na tada shi! Dama ku ya rage ku ci abinci dan haka enjoy, ni zan tafi. Hannu yasa a aljihu ya Ciro Makullin mota ya ce “Toh muje in yi dropping d’in ka a airport d’in ” inji Suraj. Habeeb yayi Murmushi yace “Ah haba wlhy na yafe yi zaman ka driver zai kai ni zamu yi waya anjima” yana kai nan ya juya yayi hanyar fita Suraj ya girgiza kai yana dariya. Habeeb kuma ya nufi gida sai mu ce safe journey *THREE MONTHS LATER* + Rayuwar Suraj da Laila ta kasance mai matuk’ar ban sha’awa ga duk wanda ya gan su, abunda yake so shi take yi haka shima, soyayyar su tayi taking new level mara misaltuwa. Mom tana Egypt bata dawo ba saboda haka Dad ya bi ta kuma aka yi sa’a ta hak’ura suna shirin dawowa Nigeria. Ko Yaya labarin Saeed da Ameer? Wannan kuma se ku biyo ni……. “Laila please! Yi hak’uri ki bani da gaske bazan dad’e ba” Cewar Suraj dake k’ok’arin k’arban wasu documents a hannun ta. “Jiya haka ka ce bazaka dad’e ba har saida nayi bacci na tashi gashi ni tsoron wannan k’aton gidan nake yi kawai ka tafi da ni” Murmushi yayi yana kallon ta kafin ya zauna bakin gado yace “Fine! Shiga ki yi wanka shap shap ki shirya mu tafi” yayi maganar yana kallon ta.

Da sauri ta ajiye file d’in ta shige bathroom. Dariya yayi ta yi kafin ya d’auki file d’in ya fice da sauri. Ko shower bata nufa ba taji horn d’in mota da sauri ta fito d’akin bata ganshi ba, da gudu ta nufi wata k’ofa wanda ta sada ta da balcony ta tsaya tana kallon motar har ta fice sannan ta dawo d’aki rai a b’ace ta shiga wankan. Yana tuk’i kafin ya bar harabar gidan ya hango ta tsaye shima yaji ba dad’i amma bazai yiwu ya tafi da ita aikin da ya shafi business ba balle ma ya kamata ta saba da zaman gidan yanzu kam tunda ga su Umma Hauwa kawai rigima ce irin nata wanda baya k’are wa. Tana fitowa diga wanka ta busar da gashin ta sannan ta gyara, closet ta bud’e tana neman kayan da zata sa amma duk sun mata nauyi , Long sleeve shirt d’in Suraj ta hango mak’ale a hanger ta d’auko bayan ta sa bra ta saka rigar wanda ya rufe pant dake jikin ta sannan ta fesa turare ta haye gado ko breakfast bata yi ba don tashin su kenan k’arfe goma Suraj d’in ya fita bayan ya sha coffee kamar yadda ya saba. Remote ta d’auka ta kunna TV tana daga kwance tana kallo. (kamar ba Lailar da take wuni kan tsauni cikin dabbobi tana kiwon su ba, a haka in ka ganta se kayi zaton dama chan wata ajebo ce bata san gajiya ba). K’arfe sha biyu ya dawo gidan yau baiga Laila da Umma Hauwa ba kamar yadda ya saba dan haka ya yi upstairs, da Sallamar sa ya shigo ta amsa ba tare da kallon inda yake ba taci gaba da kallon ta. Murmushi yayi ya k’araso kusa da ita yana k’are mata kallo, tayi kyau sosai da tasa rigar shi she looks beautiful and geeky , babu yanda bai yi ba amma ta k’i kula shi. Mik’e wa yayi ya kwance necktie d’in sa ya cire cufflinks sannan ya zare rigar shi yana kallon yanda take satar kallon shi abun dariya yake bashi amma ya basar. Da gangan ya rik’e ciki ya saki k’ara “Ahhh!! Wayyo cikina!!!! Ohh! A firgice ta nufo shi tana d’aga shi “me ya faru da kai?!! Ta tambaya harda hawaye Bushe wa yayi da dariya sannan ya matse ta a jikin sa sannan ya d’aga ta suna fuskantar juna numfashin su na garaya, k’irjin shi ta buga ta tab’e baki tace “Wannan wanne irin wasa ne ka tsorita ni”. Kashe mata ido yayi yace “da gaske y’ar fullo na??” K’ai ta kawar gefe yayi Murmushi yana cire buttons d’in rigar jikin ta Intimately yana gamawa ya cire rigar ya sa a jikin sa ya ja da baya yana mata dariya. “Ka ban riga na ! Ta fad’a a shagwab’e. Dariya ya sa yana ja da baya yace “Rigar ki? Yaushe ya zama naki? Gaji da full closet amma zaki sa min kaya na?” Buga k’afa tayi tace “ai kayan ka nima nawa ne don Allah ka bani riga na!”

“Shikenan zo in kin isa ki karb’a” yana kai nan ya gudu ta bi bayan shi tana dariya ,sun dad’e suna zagaye d’aki ta kasa kama shi ,jiri ta fara ji ga murd’a da cikin ta ke yi babu shiri ta yanke jiki ta fad’i k’asa, Suraj da farko yayi zaton ita ma zolayan shi take Amma se yaga da gaske bata motsi. Da gudu ya je ya daga ta yana jijjiga wa amma shiru , babu shiri ya d’auke ta kamar y’ar baby ya kwantar kan gado ya d’auko simple jallabiya ya zira mata ya rufe mata kai sannan ya d’auke ta cikin sauri zuwa mota, Umma Hauwa hankalin ta ya tashi dan haka ta d’au mayafi ta bi bayan shi , ita ta bud’e masa k’ofa ya sa Laila sannan ta shiga shima ya zagaya ya tada motar suka d’au hanyar asibiti….Doctor’s cabinet “uuum….. Mr Suraj ba wani abun damuwa bane , as a married woman such is bound to happen. To cut it short! Matar ka Layla is two months pregnant, we’ve examined her babu wata matsala domin akwai k’oshin lafiya tattare da ita , for now zata d’an huta later on se ku tafi kafin nan zan briefing naka about yanda ya kamata a kula da ita , her workouts routines , abincin ta and many more “. + Ko da kallo d’aya kasan Suraj ya gama nutse wa kogin farin ciki domin kawai jin doctor yake se washe hak’ora yake ya kasa zaune ya kasa tsaye abun har ya baiwa doctor mamaki har key d’in motar sa ya bari sai dawo wa yayi ya d’auka shi kuwa doctor ya girgiza kai yana dariya… A hankali ya turo k’ofar d’akin da take ya shigo umma hauwa ta juyo tace “A’ah! Babana, ina ka shiga haka? Naga likita yace yanzu zamu iya komawa ko?” Kai ya jinjina yace “eh Umma hauwa na je na biya wasu kud’ad’e ne yanzu zamu tafi daman likita ya ce a bari ta d’an samu hutu shiyasa zamu iya tafiya yanzun” Nan take ta mik’e kamar ana mintsinin ta se had’e rai take babu dalili Umma hauwa ce ta fara fita don haka ya matso daf da Layla yace “Madam! Me ya faru kuma?” Kawai wuce shi tayi bata ce komai ba shi kuwa ya bi ta da kallo yana murmushi kafin ya fice yabi bayan su. Ranar de duk surutun ta suraj ya nema ya rasa haka ta zauna a d’aki sedai in lokacin sallah yayi tayi shi kanshi tun yana damuwa har ya jona ta sukayi ta zaman shirun tare. Washegari A kasalance ta tashi tana mik’a kusan k’arfe bakwai na safe, yana zaune a bakin gadon yana k’okarin cire jallabiyyah d’in shi. Janyo shi tayi ya kwanto sannan tace “yunwa nake ji ” Zaro ido yayi waje yace “yunwa??! Yanzu?……” Kafin ya k’arishe maganan ta mik’e rai a dak’ile ta fice “oooooh not again! Yanzu kuma me na ce? Tun kafin na k’arisa magana ki mik’e kin tafi in nai magana ace its because of pregnancy, ya Ilahi yanzu da sassafen nan me zaki ci?” Maida jallabiyan shi yayi sannan ya mik’e ya bi bayan ta yana murmushi “look fulani, kwantar da hankalin ki yanzun nan ki fad’i duk abunda kike so da hannu na zan girka miki but please kar ki yi fushi baya miki kyau ki fad’a ina jin ki komai kike so a shirye nake” Mak’e kafad’a tayi tace “ni yanzu bana wani jin yunwa nide kawai kar ka fita yau ka zauna tare da ni”. wata ajiyar zuci ya sauk’e kafin ya sake kallon ta yace “Sorry baby this request of yours can’t be granted i have a project to attend to” D’ago ido tayi kafin tace “me kenan? Ni kamin magana da yaren da zan fahimta don Allah.” Dariya ce ta kufce masa kafin yace “yau kam ina da wasu ayyuka amma nayi miki alk’awari in shaa Allah gobe from dusk till dawn muna tare” Haka suka yi ta ja in ja har ta hak’ura ta barshi ya shirya fita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *